Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su bar wurin. Saboda wutar da aka bude 'yan fashin da yawansu sun buya ne a bayan gidaje suna harbin kan mai uwa da wabi.


Sai da suka gama hawa tare da wasu sojojin Zayyan ya rike hannun Emzee idanunsa suka dan kada na dakika kadan "ka taimaka min na maidawa Mairama danta cikin aminci...Allah Ya tsare min kai"


Bai jira komai ba ya kusa kai tsakanin katangar wani gida da na kusa dashi inda ya fi jin harbin ya soma sakarwa 'yan fashin nan harsashi. Emzee tuni ya nemi tsoro ya rasa sai aikin neman lada ya bautawa kasarsa. Harbi suke yi ba kakkautawa sai da suka tabbatar sun kora 'yan fashin suka soma dauko mutanen da suka jikkata a wurin suna dawo dasu bakin titi bayan kiran waya domin a kawo musu agaji.


Duk sunyi futu futu dasu a tunaninsu sun gama Emzee ya jiyo kukan mace daga wani gida. Kutsa kai yayi ya hadu da mata mai tsohon ciki a durkushe tana murkususu. Fita yayi da sauri ya kira Zayyan dake rike da wani tsoho. Wani sojan ne ya karasa da tsohon shi kuma ya bi bayan Emzee. Suna shiga gidan aka rufe kofa 'yan fashin nan su hudu su ka sakawa matar bindiga sannan aka umarci Zayyan ya fadawa yaransa kowa ya bar wurin saboda tsaron rayukansu suka yi garkuwa da su.


Tsananin tashin hankali sun shige shi domin matar gidan tana cikin mawuyacin hali. Zayyan bashi da zabi saboda rayuwar matar da dansa ya bada wannan umarni. Yaransa sun so yin gardama sai yayi musu bayani cikin lauya zance wanda su kadai sojoji ke ganewa akan cewa zasu iya hauro katangar gidan amma su bada lokaci.


Cikin wadanda suka sami tserewa nan da nan labari ya bazu cewa 'yan fashi sun tare hanyar Asaba sunyi garkuwa da wasu sojoji. Yadda labari ke gudu a social media kafin a farga Ibrahim da ke Kano ya sami labarin. Hankalinsa a tashe saboda dazun nan suke chatting da Emzee sai ya ji shi shiru. Baba Hadir ya kira ya tambaya yace baiji labari ba. Shi da Daddy su ka shiga neman layukan Zayyan da Emzee shiru. Headquarter su ka je neman ba'asi amma aka so boye musu. Sau kuma ga 'yan jaridu da gidajen tv zancen kenan dai akeyi. Daddy da Baba Hadir basu bar wurin ba har dare sai da Baban Arifah ya zo sannan aka saki rahoto cewa lallai an sami distress call daga hanyar Asaba sojoji na neman taimako an kama shugabansu Major Gen. Tureta da dansa.


Kan kace meye wannan zance ya zaha lumgu da sakon Nigeria ga masu mu'amala da social media ko sauraron labarai. Fadin tashin hankalin da Mairama ta shiga ma bazai yiwu ba. Tayi kuka har hawaye ya kafe a idanunta. Ga da ga miji ko shekara biyu baiyi da dawowa gareta ba. Duk wannan tashin hankalin kuma ga Radhiya can a labour room da ga jin zancen nakudar dole ta kama ta. Ga Nasr yana wani irin kuka na fitar hankali Mairama ta rasa inda zata tsoma ranta. Tana goye dashi suna asibiti tare da su Mami saboda an hanata zama ita kadai tana fama da tunani.


A can kauyen da sojojin su ka haura gidan cikin dare basu ga kowa ba. Ashe karbe abin maganar Zayyan suka yi aka fasa sannan su ka tafi dasu cikin dajin wai bazasu barsu ba sai sun tabbatar cewa sun tsira. Ana wannan tafiya ga mai ciki ciwo yaci karfinta a wahale tace haihuwa ce suna tsare a wani kango.


"Ku taimaka min" tace cikin tsananin azaba.


"Daada taimaka mata ni zan rinka lekawa in shammacesu mu gudu" Emzee yace ko kallon matar baya son yi saboda tsoro.


Duk da rashin wadatar haske Zayyan harararsa yayi "kai ya kamata ka taimaka mata saboda idonka yafi nawa gani girma ya kamani"


"Laahhh Daada tun ina yaro aka ce na gado ciwon idon Ummi" yace yana matsawa baya.


Zayyan bai ga abinda zai sa shi ganin haihuwa ba don gara a cigaba da fafatawa a wurinsa. 


Dakewa yayi yace "Lieutenant this is a command ka taimaka mata. Ba don chanjin zamani ba nasan cewa haihuwa a lokacinmu da naku da bambamci da ni zanyi komai" ya hadiyi yawu mai daci.


"A BEG MAKE UNA HELP ME"(don Allah ku taimaka min) matar tace tana ciccije lebe ga 'yan fashin suna daka tsawar tayi musu shiru ko su harbe ta.  Emzee na jin haka ya duka a gaban matar nan daga shi sai hasken farin wata yayi abinda bai taba zato ko tsammani ba. Ashe aikin soja ya wuce duk yadda ake tunaninsa. Yau shine da karbar haihuwa abinda ko a tv bai taba yarda ya kalla ba. Yana gabanta tana nishi tana fada masa ya duba ko kai ya fito.


Muryar mahaifinsa yaji ya dafa kafadarsa "Make me proud my son." Ya tashi yayi waje batare da sauraron kiran da Emzee yake yi masa ba.


Tashi yayi zai bi babansa matar tayi wani nishi iya karfinta sai ga da yana neman faduwa dole ya tare ya rike mata shi. Wuka ta dauko a gefen rigarta ta bashi ya yanke cibiya tace masa tun da mutanen suka fara harbi ta boye wukar domin tsaron kanta ashe zata yi musu amfani. 


Karar harbi suke ji daga waje ya tashi da jinjirin nan a jikinsa ta bashi wani mataccen dankwalinta ya zura yaron ya daure shi ta gabansa kamar wanda yayi daurin karaya. Yana fita ya sami maza uku a kwance ashe Zayyan ya shammacesu ne ya karbe bindigar daya. Harbi na hudu yaji ga hasken asubu ya fara ratsowa daidai da tahowar Zayyan daga bayan wasu bishiyu. Murmushi Emzee yayi ya taho gareshi da sauri ya mika hannu zai rungume shi kawai su ka ji sautin fitar bullet sai ga Emzee ya tafi gabadayansa ya fada jikin Zayyan tare da jaririn. 


Da hannu daya Zayyan ya riko shi suka kai kasa ya daidaici mutumin da yayi harbin ya sakar masa bullet a tsakar ka kafin ya fara kiran sunan Emzee a gigici yana kukan da ko fuskar Emzee din baya gani sosai.


"Muhammad kada kayi min haka ban dawo domin in ga mutuwarka ba...Muhammad kada kasa na kasa fuskantar mahaifiyarku" kuka yake yana juya Emzee ga jaririn jikinsa ya na neman a ina aka harbe shi. Ba karamin tsorata yayi ba da ya ji a gefen cikinsa ne ya leka kangon matar ta tashi da dafa bango ya bata jaririnta sannan ya dawo ya goya Emzee su ka fara gudu saboda yana tsoron ko akwai wasu 'yan fashin a kusa. Sai da rana ta fito sosai wuraren karfe goma su ka bullo a bakin titi jikinsa jike da jinin Emzee. Motocin sojoji ne birjik a wurin an baza search party sai fito da 'yan fashi suke yi. Wani ne ya fara hango su da sauri ya soma ihun murna sauran su ka taho aka hadasu su ukun aka zuba a mota zuwa airport saboda a zatonsa Emzee ya riga ya cika. Ambulance ce tazo daukarsu daga airport din Abuja a guje aka tafi dasu National hospital.


A daidai wannan lokacin kuma Allah Ya sauki Radhiya ta haifi 'yarta mace.

Theatre aka shiga da Emzee emergency cikin sa'a bullet din bai taba muhimman organs ba aka cire. Zayyan yana tsaye a bakin kofar Daddy, Baba Hadir da Mairama suka iso. A guje ta rungume shi tana kuka sosai yana bata hakuri akan suyi masa addu'a. Suna kallo aka gangaro shi zuwa dakin hutu idanunsa a rufe.


 Radhiya ko awa batayi da haihuwa ba tace a kaita wurin Emzee da Daada. Yanayin da take ciki na tashin hankali Awwab ya daukota da Rahima  da Mama aka bar babyn a asibiti da Mami. 


Jigum jigum ake zaune Radhiya ta fado dakin tana kuka a jikin Daada yace tayi hakuri. 


"Kai Adda ashe dai kina sona" su ka ji Emzee yace da gajiyayyar murya..


Ita da Ummi da Daada suka yi kansa Rahima tana gefe tana kuka.


Sannu sannu suke yi masa ya kalli Radhiya "Adda ina cikin?"


"Tana asibiti ta taho tarbar Baffanta da kanta" tace tana murmushi.


Sai lokacin Daada ya kula "Taho kinji Innata mun saka ku a tashi hankali" ya rungumeta tare da Nasr da ya makale masa sai da ya ganshi ya dena wannan kukan.


Da kyar Emzee ke magana ya yafito Baba Hadir ya ce "Baba don Allah ka aura min Rahima kafin na mutu."


Kofar fita daga dakin Rahima ta nufa da sauri Daddy ya tsayar da ita "ko sannu baki tsaya kinyi masa ba zaki gudu"


"Ba dole ba daga tashinsa zai matsawa 'yata" cewar Ummi tana harararsa.


"Daddy kasa baki wallahi ni aure nake so"


Daada yace "Anya yaron nan ba anasiziya bace bata sake shi ba?"


Emzee yayi dariya a ransa ya kuma kafe Rahima da ido "idan bata amince ba ni dai ku aurar dani kada in sake zuwa wuri irin wannan ban dawo ba"


Rahima na jin haka ta zaro ido Radhiya ta rike hannunta "ta amince don Allah ka dena yi mana sumbatu"


Dariya aka saka baki daya sannan su ka fita domin barinsa ya huta ita kuma Radhiya ta koma wurin babynta.


Bayan kwana hudu Emzee yaji sauki sosai an nemo 'yan uwan matar da ya karbi haihuwarta. 'Yan jarida har dakinsa matar tana yi musu godiya shi da mahaifinsa tace yaya sunansu.


A tare su ka ce "ZAYYAN"


Ta ce "duka ku biyun?"


Su ka gyada kai.


Jaririnta ta mikawa Daada ta cewa "ina fata wannan Zayyan din ma ya zama soja jajirtacce kamarku wanda zai iya sadaukar da rayuwarsa domin kasarsa. Nagode"


Emzee ma sai da ya karbi yaron ya rungume shi saboda akwai wani bond kasancewar shi ya karbi zuwansa duniya. Bayan sun tafi ne Emzee yake fadawa su Daddy wayon da Daada yayi masa akayi ta dariya. A gefe guda soyayyarsa da aka sakawa comma (,) shi da Rahima ta sake daukar wani sabon salo mai shiga rai.


Awwab da Radhiya suna tare da 'yarsu ya lalace wurin basu kulawa da soyayya. Ranar suna wanda aka yi gagarumin taro yarinya taci suna Zainab suna kiranta (Boubou). Mama bata taba zaton wannan karamci ba ai kuwa tayi rawar gani sosai.


Boubou na ta wata takwas aka sake taruwa domin bikin da aka dade ba'ayi irinsa ba na Barr Ibrahim Hadir da Zayyana Mustapha wanda aka dauro aurensu a Katsina sai kuma Lt. Muhammad Zayyan Tureta da Rahima Idris Sumaila wanda aka dauro a Sumaila. Salame sai da tayi kuka ranar.


Gida flat sama da kasa Daada ya kama musu babu nisa da su Radhiya saboda yace amaren da angwayen akwai danyen kai duka da kuruciya.


Babu wanda ya rakasu gidajensu Emzee ya shiga nasa da yake kasa ya wuce daki kai tsaye inda Rahima ke zauna akan gado an rufe mata fuska da mayafi. Yana shigowa gadon ya hau ya tura kansa karkashin mayafin ya kwanta akan cinyarta. Kunya ta kamata ta soma ture shi.


"Ya Emzee ka tashi don Allah"


Sake gyara kwanciya  ma yayi "saibkin gyara min suna zan tashi"


"Me kake so nace?"


Kamshin da take fitarwa da tsananin kyaun da tayi yasa shi lumshe ido yana budesu a hankali.


"Kin fini sani"


"Muhammadun Rahima ka tashi" tace tana murmushi gashi yaki bari ta budesu daga lullubin.


"Rahiman Muhammadu ina sonki wallahi"


Murmushi tayi tana cewa ya tashi tunda ta fada yace to. Dago kai yayi kamar zai tashi sai ji tayi ya birkitota gabadaya kansa ya rungumeta ya shiga kissing dinta. Da kyar ya tuna ya kamata suyi nafila ya dagota suka yi alwala da sallah. A baki ya rinka bata nama ita kadai take ci yana bin jikinta yana kissing dole ta hakura don ba iya ci zata yi ba. A daren ta tabbata Rahiman Muhammadu matar Muhammadun Rahima masoya daga Allah. 


BAYAN SHEKARA BIYAR


Gidan Daada a hargitse yake da 'ya'ya da jikoki ana ta shirin zuwa Award Night da gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar kasashe da dama na Africa suka shiryawa Alheran Radhiya saboda services dinta to the military.


Captain Muhammad Awwab da gis one and only Scharzi Alheran 'ya'yansu uku Boubou mai shekara biyar, Haidar takwaran tsoho mai ran karfe Malamijo mai uku da rabi sai Fatima (Islam) mai biyu ga karamin ciki. Zahra bayan Femi ta kara da Hassana da Hussaina (Taye da Kehinde) ana kiransu da duk wanda mutum yaso kira, sai Mu'az. Fauziyya bayan Jawad da Sahla ta kara da Mustapha (Ansar) da Iman. Arifah biyu gareta Nasrin da Nasir. Zayyana tayi biyu itama Zayyan (Junior) da Hassana (Mami), iyayen garke Rahima da Emzee suna da Hadir (Little), Idris (Abba), Ibrahim (Khaleel) sai Kauthar don haihuwa take duk shekara maigida kuma ya hana planning. So da kauna yake gwada mata kamar ya hadiyeta.


Anyi taro lafiya an gama lafiya kowa ya koma gida cikin kewar juna.


Tun dare Radhiya ta gama hadawa Boubou da Haidar kaya zasu tafi Katsina dasu Mami gidan zai huta na kwana biyu daga kiriniyarsu Awwab ya gama shirin sabon amarci. Gidan Daada su ka fara zuwa da yaran inda su Mami zasu zo daukarsu. 


Shigowar motarsu ke da wuya DK da yake wasa akan keke ya arta a guje ya shige cikin gida yana kwalawa Daada kira.


"Menene DK?" Ya leko falon daga sama.


"Su Boubou ne Daada" yace kamar zaiyi kuka.


"Taho mu rufe kofa" ya dauke shi suka shige dakinsa ya kulle kofa Mairama tana musu dariyar wannan abu.


Boubou na shigowa ta fara bude daki daki da bindigar wasanta a hannu tana kiran "Uncle DK".


Yadda take matsanta masa da fitina idan yaji tazo baya iya zama. Nasr kuwa boss ne mai zaman kansa ba ta zuwa inda yake dama sai yaso wasa. Idan ka ga ya sake Ibrahim da Zayyana ne a gidan anzo da Mami.


Gajiya Boubou tayi da nemansu ta fada jikin Ummi "Umminaaaa"


"Boubou naaaa" Ummi tace tana jan hannunta zuwa dakin Daada, Radhiya da Awwab suna dariya don sun san sai anyi drama. Ai kuwa muryar Daada su ka ji yana cewa "Zainab ba fa zaki rinka zuwa kina takura kin yaro ba" sannan suka sauko su duka su Mami sun iso ga Baba Hadir da Mama.


"Ummiiii" ta tabe baki tana kukan abinda Daada yace.


"Rabu dasu idan kin zama soja babu ruwanki da kowa" cewar Mama


Ta saki murmushi dimple dinta biyu suka lotsa. Fakar idonsu tayi ta dane bayan DK tana kai masa harbi hannu da kafa "zo muje muyi training Uncle DK kada a kaimu makarantar soja su koromu"


Awwab ya tashi zai rabasu Baba Hadir ya hana sai zama da suka yi suna kallonsu ana dariya manya na fassara lamarin.


Yana daga kwance ta danne shi yace "ni bazanyi soja ba don Allah ki dagani"


Idanunta ta ware a kansa tana sukuwa a bayansa har ta soma tara masa gajiya "to waye zai kareka idan ana fa'a"


Hantsilota yayi yana nishi "ba gaki ba idan kin zama sojan sai ki kareni"


Tayi wani murmushin bada fadi ita ga soja sai kuma ta janyo kwalar rigarsa yana shirin guduwa "idan zan kareka ni me zaka rinka bani to?"


"Boubou wuyana" ya ce ta sake shi da kyar "zan rinka siyo abinci ina kawo miki yadda Daada yake kawowa Ummi Baba kuma yake kaiwa Mama"


"Ahh irin na Abbana da Mamma kenan fa...to na yarda amma wallahi ka goyani" ta haye bayan nasa Nasr ya janyota ta fado,


Dama shima tara shi take yi ai kuwa ta  juya ta ce "Haidar taron dangi"


Barin kayan wasan yayi suka hadu shi da Boubou suka danne Nasr. Baba Hadir na ganin haka ya tashi ya raba fadan ya hadasu da sweet suka tafi yana jin DK yana Boubou ki kyaleni sai ta ce idan ta zama soja ta fasa kareshi.


Awwab da Radhiya basu bi ta kan sauran yaran ba dama nan suka yi niyar barinsu suka wuce gida yana cewa yau zai kwana goge mata janbaki.


Falon ya rage Zayyan da Mairama, Mustapha da Hassana sai Hadir da Zainab su ka zauna hira suna tunowa juna wasu lokuta da suka gabata da yadda rayuwa ta sauya musu. A kowane yanayi sai dai bawa yace ALHAMDULILLAH.













 










 
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment