Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamata ayi domin fara aikin da ya dawo da Radhiya Baban Arifah ne kan gaba. Abinda take shirin yi ya kayatar dashi matuka inda ya dauko mata hayar kwararren cameraman aka hadata dashi. Arifah kuma ta zabi zuwa a matsayin wadda zata yi co-ordinating komai saboda ya tafi bisa tsari tamkar shirin film ba kara zube ba. Da connection din Excellency ya samu aka nemo masa wasu cikin makotansu Zayyan wadanda mazansu suka rasu a Liberia dasu zata fara.


Yau litinin suka gama shiri zasu tafi Kwara state can karamar hukuma Moro. Suna airport kafin jirgin ya sauka Radhiya ta matsa gefe suna hira da Awwab. Rigima take yi masa tun jiya wai ya dawo.


"Schatzi saura kadan fa na gama. Ko baccin kirki bana yi saboda saurin da nake yi na dawo wurinki."


"Ya za ka dena bacci sosai salon kaje kayi mistake a kara maka kwanaki ko"


"Ya Allah, yanzu yaya kike so ayi?"


"Ka rinka bacci, cin abinci akan lokaci da tunanin ina nan ina kuka saboda ba ka nan"


Tamkar yasa hannu ya daukota ta cikin wayar haka yake ji "Do you miss me that much?"


"Every second Hammana" ta amsa masa da murmushi.


"Ki kula min da kanki okay, banda kula likitoci kuma."


Dariya tayi mai sauti yana jinta har ransa "yanzu ko asibiti idan ba dole ba ai bazani ba saboda ta kare min"


Shima dariyar ta bashi. Yana so yaji tace ta kare mata dinnan cikin shagwaba "I love you Alheran"


Kalmar da har yau take yi mata wuyar maida masa a kunnensa kenan. Nauyi take ji sosai sai dai ta kare da me too. Tun yana korafi har ya hakura.


"Chèri ka turo min hotonka amma yanzu zaka dauka please kafin mu tashi"


"Ba yadda na iya dake" yace sannan ya katse kiran. Shi ba ma'abocin daukar kansa a hoto bane sai dole yanzu ma abokin aikinsa ya bawa ya dauke shi ya tura mata. Bayan kamar minti biyar ta turo masa wani. Daukar kanta tayi tayi kyau sosai dimple dinnan ya fito ta hada da nasa a photo college wani frame mai kyau. Akan hotonsa ta rubuta Alheran Schatzi a nata kuma Awwab Chèri. Sun tafi zasuyi boarding ta sake kiransa.


"Ka saka shi wallpaper dinka. Idan ka dawo zan duba. Yanzu zamu shiga kayi mana addu'a. Yaya Arifah tana gaisheka"


"Whoa, ki dan tsaya mana in amsa kowanne kafi ki cigaba"


"To ai yanzu zamu tashi"


"Allah Ya tsare Yasa kiyi ki gama a sa'a kuma Ya sa mana albarka a ciki. Ki gaishe da Arifah"


"Amin" tayi ta cewa har aka bada umarnin a kashe waya tana masa hira sannan ta kashe.


Arifah ta kalleta tana murmushi "ba fa zaki rigani aure ba duk wannan lovey dovey din naku sai na riga"


"Nima zan fi so babban yayan nawa kada yazo bikina yana gwauro"


Dariya suka yi tare kafin su dora hirar Yousuf da Awwab. Magana dai tsakaninsa da Arifah ta kankama don yace ta fada a gida zai zo wurinta amma da maganar aure so gara a sani tun wuri. Tante ma sai da ta kira Radhiya ta dan yi mata tambayoyi game da Arifan sun gamsu ana jiran komawarsa Nigeria su karasa daidaitawa.


Jirgi na sauka da suka fito motoci biyu na jiransu daga gidan gwamnatin Kwara. Gwamnan mutumin Baban Arifah ne kuma ya fada masa dalilin zuwan nasu. A cikin gidansa aka tanadar musu masauki. Bayan sunyi wanka sunci abinci aka kaisu suka gaishe shi sannan suka kama hanyar Moro inda Radhiya zata yi hira da Maman Dolapo matar da ta fara yi mata wanka ranar da aka haifeta.



 
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Ummi da Emzee suna magana akan tafiyar Radhiya Daada ya shigo falon yake fada musu wayar da yayi da Alh Salisu yanzu. Kamar wasa ya ce Halifa ya bashi labarin program din nata shi kuma cikin hira ya fadawa matarsa. Shine take cewa abin zaifi kyau idan suka sami wanda zaiyi directing daukar komai. A yadda tace masa ya kamata aikin yayi kyau a haka ne zai burge masu kallo kuma a sami damar isar da sakon yadda ya dace. 


"Yanzu yaya kake ganin zamuyi gashi tace suna hanyar garinsu Maman Dolapo" Ummi tace bayan ta nuna gamsuwarta akan shawarar da matar Alh Salisu ta bayar.


"Kya tambayi kaza hanyar rafi Fillo. Ni ba don ma kada nayi karya ba da nace muku meye hadin director da daukar video. Naga su Directors ma'aikatan office ne"


Emzee da ya kwana biyu baya fara'a sai gashi yana dariya "Daada kamar masu harkar film din Hausa yake nufi"


"Ina na sansu, ni dai so nake aikin nata yayi fice yadda take so ace 'yar Zayyan ce nima ina so ince nine baban Alheran. Tunda an bata kudin aikin su ma zasu so ganin abu mai kyau. Zan kirata yanzu su koma kai kuma na baka daga yau zuwa gobe ka nemo min wanda zai yi mana directing din"


"Yes Sir" Emzee ya tashi ya kame tare da sarawa mahaifinsa ya fita. Gidan Mama yaje wurin Ibrahim ashe Ibrahim din fushi yake yi dashi bai ma sani ba.


"Ka huce daga kumburin da ka ke yi ne kazo nema na?"


Shiru Emzee yayi kafin ya dan shafa keyarsa "kayi hakuri mana Ibrahim. Tun a Kano nace maka babu komai"


"Ai shikenan fita zanyi ni ka gaida gida Mama na ciki. Idan kuma kwana zaka yi sai na dawo" sa kai Ibrahim yayi zai fita fuskarsa a daure.


Ba haka Emzee yaso ba. Tun daga Sumaila yake cikin kuncin maganar da yaji daga bakin Nene Marka shine har suka gama kwanakinsu a Kano baya sakin fuska. Sai da ta kai Ibrahim ya fara zargin ko Kanon ne baya son zuwa a dole ya shiga kirkirar murmushi. Dayake da wuya ransa ya baci shiyasa wannan karon ya kasa mallakar kansa. Makantar shekara goma da Umminsa tayi bazai taba mantawa ba.


"Surbajo tsaya don Allah" ya kamo Ibrahim kagin ya fita daga dakin.


Shi kuma ya sake hade rai "gidan nawa kakannin ne baka son zuwa shine...."


"Haba kai kuwa wallahi ba haka bane" Emzee yace hankali a tashe baya son ya batawa dan uwansa.


"To yane?" 


Hannunsa yaja ya zaunar dashi a gefensa "Zauna mana".


Da gaske Ibrahim baiji dadi ba shiyasa ma ya wayance ya baro gidan bayan an gama murnar tashin nasu. Shine abokin Emzee na farko wanda har yau bashi da kamarsa. Abokan sirrin juna ne wadanda suke kokarin koyi da iyayensu. Duba da wannan da kuma gudun wancan zargi da ya darsu a zuciyar Ibrahim din ya sa Emzee fada masa abinda yaji.


Baki Ibrahim ya rike yana mamakin wannan labari "tab, inama dai Radhiya ce taji wallahi da anyita ta kare. Yanzu kai bazan so ka soma fadawa su Ummi ba rigima ce kawai za'ayi gashi Nene tace bata tabbatar ba"


"Amma da gaske fa wai Daada take so yana auren kanwarta." Tsaki yayi ransa yana kara baci "seriously man abin nan ya dameni fa"


"Ai dole amma zancen gaskiya shawarar da zan baka kada ka bari yayi affecting alakarka da Halifa. Ni sai yanzu na gane yadda ka rinka shareshi kafin mu bar Sumaila"


"Kuma kasan Allah bana jin dadin yadda nake masa. Kawai ji nake idan ina kula shi naci amanar su Ummi"


"Tunda Malamijo yace zaiyi bincike ka bari yayi. Shine fa babansu nasan ko don abinda ya faru da majalisar dinkin duniya ta mayu bazai bari irin haka na faruwa a gidansa ba"


Dariya sosai Emzee ya rinka yi suka mayar da hirar kan shirun da gidan yake yi saboda rashin Radhiya. Kofar dakin suka ji an kwankwasa sai muryar Zayyana tana tambayar ko Emzee ne a ciki. Tare suka fito da Ibrahim suka zauna tana tsaye da Daada karami a hannu Emzee ya karbe shi.


"Zan wuce dakin Mama naji kamar muryarka Ya Emzee. Yaushe kazo?"


"Ban dade ba ko Mama bata san ina gidan ba. Ya su Mami...zan ma dai shigo ai"


Shi kadai take kallo ta dauke ido daga saitin Ibrahim tace "DK na kawowa Mama ya tashi daga bacci bari na mika shi na koma girki nake yi"


"DK kuma?"


Ibrahim yayi saurin cafewa "ta dage a rinka kiransa DK wai Daada Karami saboda a bambanta shi da Daada. Sai nake ga hakan yafi ko?"


Tabe baki tayi ta wani juya idanu irin na 'yan mata masu tasawa suna jin kansu ta murguda baki "uhumm Ya Emzee sai ka shigo kaji akwai story" wucewa tayi ta kai DK wurin Mama tazo ta sake cewa Emzee sai ya shigo sannan ta fita.


Rufe kofarta yayi daidai da dariyar Emzee harda rike ciki. Ibrahim ya bata rai kuwa "me kake yiwa dariya?"


"Babu komai wani labari na tuna" yana kokarin danne dariyarsa saboda yadda damuwa ta mamaye fuskar Ibrahim sosai.


Kamar mai shirin kuka yace "Kaga ka dena dariyar nan muyi magana sosai. Ka lura da abinda Zayyana tayi min ko? I can't remember the last time da tayi min magana ko ta amsa min." 


Wata muguwar dariyar Emzee ya kuma yi sai da Mama ta fito. Gaisuwar ma da kyar yake mata yana kallon Ibrahim dariya na cinsa.


"Sojoji fa baku da kirki idan kunso mugunta. Yanzu wannan dariyar ta mene?" Mama ta tambayeshi don tasan ba abu bane da ya saba.


"Mama ki sa mana albarka kawai"


Kai ta girgiza ta koma ciki kawai. Ibrahim kuwa tashi yayi zai bar wurin Emzee ya riko shi.


"Dawo mana muyi magana dan uwa"


"Kana wannan dariyar kamar sabon kamu"


"Ba dole inyi ba ina kallon fadan masoya"


Duka hannu bibbiyu Ibrahim yake kai masa "ni da Zayyana? Amma ka cuceni ma. Kai baka ga yadda take murguda min baki bane?"


"Ibrahim wai kana nufin baka san kana son Zayyana ba?" Ita ce tambayar da Emzee yayi masa da ta shige shi ba zato ba tsammani. 


"Matsalarka kenan ko yaya ka sami chance sai zancen soyayya. To ni dai kada kaje kayi min sharri bance ba"


"Naga ka damu ne saboda ta dena kula ka. Kana magana kamar kayi kuka duk dan tale bakin nan kaima sai da kayi min yanzu"


Ya fuskanci kamar tsokanarsa Emzee yake yi kawai ya tashi "meye laifina don na damu? Kanwata ce fa. Ko gaba kake so muyi bayan kasan matsayin masu gaba a addini"


Haba Emzee ya rike shima yana tashi "da gaskiyarka kuma fa. Bari naje dai naji nasan story din nata baya wuce tayi sabon saurayi. Zanyi mata fada kuma akan wannan halin da ta tsiri yi maka"


Duka zancen dena shigar Ibrahim yayi daga lokacin da Emzee yace labarin saurayi zata bashi. Ransa har ya soma baci.


"Yanzu hirar samari kake yi da karamar yarinya Emzee, gaskiya bai dace ba. Muje idan kai bazaka iya yi mata nasiha ta dena kula samari ba ni zan iya."


"Ta dena kula kowa sai kai ba" Emzee yace a hankali yadda bazai ji ba.


Bangaren Mami suka je. Jawad yana ta wasansa a falo shi kadai sai motsin Zayyana a kitchen. Saboda tana tsammanin shigowarsu tunda ta dawo daga kai DK bata cire hijabin jikinta ba dan madaidaici iya kugu saboda saukin aiki da kare jikinta. Wannan tarbiyar Mami ce kaf dinsu har Radhiya ta koya musu zama da mayafi ko hijabi a kusa saboda samarin dake gidajen uku. Idan daya muharraminki ne to fa sauran biyun ba haka bane. Yana daga cikin kuskurenmu a fake da 'yan uwantakar da aure zai iya shiga tsakani 'yan mata suyi ta saka kaya su matse jiki iyaye na kiran wanta ne ko kanwarsa. Bayan zamanin yanzu ko muharraman ba kowace shiga ce ake iya bayyana a gabansu da ita ba saboda yadda shaidan yayi tasiri a kwakwalenmu.


Lekowa tayi ta amsa sallamarsu sannan tace tana zuwa. Kwashe abincin ta yi ta fito tana sanar dasu yanzu Mami da Fauziyya suka tafi asibiti. Jikin Fauziyya babu dadi tayi ta amai tun safe ko tashi bata iyawa.


Da dukkan gaskiyarsa Ibrahim yace "Wane irin ciwo ne yake damunta haka kullum sai ace bata da lafiya" don duk laulayin da ake cewa tana yi yayi zaton ana nufin ita mutum ce mai yawan rashin lafiya.


Zayyana sai ta sake biris dashi ta tambayi Emzee ko zai ci abinci yace ya koshi labari yazo ji. Shagwabe fuska tayi Ibrahim yaji wani azababben bacin rai da bai san dalilinsa ko daga ina yake ba ya dirar masa a zuciya. A gaban Emzee take wannan kwabe fuskar...to me take so yayi mata? Maganarta ya tsinkayo tana cewa

"Hibbah ta takura min Ya Emzee wai zata fadawa Alhajinsu ya hadamu a kaimu Dubai karatu. Ita bata ma gama ba amma take nacin kada na karbi admission din Baze. Yanzu idan taje ta fada akayiwa Daddy magana fada zaiyi min nasan" ta kare maganar muryarta na rauni.


"Ki fada mata ba kya so kawai na kula tana da rawar kai." Emzee yace bayan gajeren tunani.


"Na fada fa har kusan fada muka yi taki yarda. Jiya da mukayi magana da Ya Halifa..."


A fusace Ibrahim ya harareta bai ma san yana daga murya ba yace "Halifa kuma? Me ya hadaki waya da Halifa?"


Idanunta ne suka yi kwal-kwal za tayi kuka ta kara narkewa za ta kai kararsa wurin Emzee.


 "Ya Emzee ka ...."


"Emzee pls bamu wuri yarinyar nan is trying my patience" Ibrahim yace yana hade girar sama da kasa. 


"Anzo wurin" Emzee yace da shakiyanci ya dauki Jawad yayi waje abinsa.


Tsilli Zayyana tayi da idanu a tsorace saboda babu alamun wasa ko kadan a fuskar Ibrahim.


"Zayyana" ya kira sunanta rai a bace. Wai har waya take da Halifa shi yana zaune hoto.


A hankali ta dago idanunta suka sauka acikin nasa. Nasa sun kankance da kishi ita kuma nata sai girma da suka kara cike da hawaye. Fuskarta so cute bakin nan ta gama shirin kyabe masa shi da yayi mata magana mara dadi ta saki kuka. Kamar wanda aka sokawa kibiya haka idanun Zayyana da fuskarta suka shiga zuciyar Ibrahim. Abin da bai yarda shi yake ji ba game da ita ya yunkuro masa gabaki daya. Fadan da ya so yi mata ya makale a makoshi sai samun kansa yayi da narke fuska irin nata.


"You look beautiful" yace da taushin murya idanunsa a kanta.


Tsigar jikinta ce taji ta tashi ba shiri ta tashi a guje za ta bar falon ya sake cewa.


"Zayyana me yasa kika dena yi min magana?"


"Ba kaine ba" tace fuskar nan a shagwabe.


Da sauri yace "Na dena"


"Me din?"


"Ko ma meye please kada ki sake yi min irin haka"


Murmushi tayi da ya sake tafiya da sauran kuzarin Ibrahim ta shige daki ta barshi yana ta sakin murmushi shi kadai. Da dan gudu ya koma gida ya sami Mama da Emzee suna hira. Wani tsalle ya daka ya mikawa Emzee hannu suka tafa.


"An kashe boss kenan" Emzee yace yana dariya.


Kafadarsa Ibrahim ya daka yana nuna masa Mama. Girgiza kai tayi abinta tana murmushi tasan ko ma meye da kansa zai dawo ya fada mata don baya iya boye mata komai. Ba don kada tayi azarbabi ba ma sai tace yayi mata kama da sabon shigar soyayya.  


Da kyar Ibrahim ya nutsu suka yi maganar daraktan da ya dace su nema. An sha buge bugen waya da abokan Ibrahim na Kano kafin Allah Yasa suka sami nambar wani Nafi'u Bigman. Shi Bigman ba'a ma gama sanin sunansa cikin daraktocin ba amma akwai kokari da himma duk da bako ne a harkar. Rashin suna da yayi yasa bashi da ayyuka a gabansa har ya amsa gayyatar gaggawa da aka tura masa. Bai yarda aikin gaske bane sai da Zayyan yayi magana dashi yaji muryar babba. Emzee yayi masa sauran bayani aka bukaci ya tafi Kwara jibi sannan aka bashi nambar wayar Radhiya. Karamin aiki ne ya koma babba domin tana gama yi masa bayani yaji gabadaya ta kwadaita masa son aikin. Email dinsa ya tura musu a take Arifah ta tura masa sauran bayani da kuma tsarin kalmomin tambaya na hira da Radhiya zata rinka yi musu. Kusan kwana yayi yana bincike mai zurfi akan harkar rayuwar sojoji da irin matsalolin da suke fuskanta na yau da gobe. 


Gari na wayewa ya nemi Assistant dinsa suka tafi Kwara. Shi da ba kowan kowa ba sai gashi a gidan gwamnati ana karrama shi. Takarkar contarct wadda Ibrahim ya tsara aka tura musu suka yi printing a take Bigman yasa hannu Radhiya ma ta saka sai Arifah da Assistant dinsa a matsayin shaidu. Gyare gyare suka kawowa aikin ta fannin yanayin presentation da dialogue (maganar da zasu rinka yi idan camera na kansu). Karin bayani yayi musu cewa ba shirin film bane amma ko documentaries ana tsari sosai kafin ayisu idan ba haka ba zai zama kara zube karshe a kasa isar da sako sai asarar lokaci da kudi.


Wannan abu ya yiwa Radhiya da Arifah dadi. Sun dauki lokaci a wani falo da aka basu suka gama gyara komai washegari sai wurin Maman Dolapo.


Motar da aka basu bus ce wadda camera man ya sako kayan aikinsa suka taho tare da dan gari wanda yake musu rakiya da kwatancen da aka basu. Layin da suka shiga a cabalbake yake da ruwa kamar tsakiyar kasuwa. Tambaya ya rinka yi har aka kaisu gaban wani gida mai karamar kofa da shago a jikinsa. Babbar mace ce zaune a kan benci a kofar shagon da aka zubawa provision irisu kayan shayi da lemo. Ganin mutane cikin shigar alfarma ta fito da sauri tana dariya ciniki yazo. Da pidgin English tace musu.


"Una welcome, wetin u wan buy?" (Sannunku da zuwa. Me zaku saya?)


Zuciyar Radhiya ta bata wannan ce Maman Dolapo din haka kawai sai taji kwalla ta taho mata. Shagon fa babu wani abin arziki a ciki duk kankantarsa ko rabi bai cika ba.


"Mama Dolapo?"


"Yes, yes" tace a dan tsorace don bata ganesu ba kada ace 'ya'yanta sunyi laifi ne.


Hoton da Ummi ta bata ta ciro daga jaka ta mika mata "kin gane wannan da kuka zauna a Sokoto Mairama."


Hoton ranar sunanta ne da akayi da su Ummi da yawancin matan da suke makotaka dasu. Namiji daya ne a cikinsu Awwab yana manne da Mama saboda a hannunta Radhiya take ya dora nasa hannun ya tallefota ta kasa.


A take Maman Dolapo ta saki kuka tana tuno shekaru masu yawa da suka gabata. Idanu ta zubawa Radhiya kafin  cike da rashin yarda tace "kene yarinya wannan ko?" Ta nuna Mairama.


Kai Radhiya ta gyada da mamakin yadda matar tayi saurin ganeta. Ji tayi ta tattarota gabadaya ta rungume tana ihun murna. Makota kuwa da masu shaguna aka taro a kofar gidan tana kuka tana dariya tace 'yarta ce tazo daga Sokoto. Cikin gidan ta ja su ta rasa inda zata saka kanta don murna. Nan ta tura aka kira Dolapo daga garejin da yake aikin makanike da sauran yaranta. 


Duka bayanin Radhiya ta gane ga kukan da taci na jin dawowar Zayyan daga prison. Canja kaya taje tayi aka hada yaran duka sannan aka fara shirin daukar kashi na farko na shirin Military Voice. Ana dora camera akan Radhiya a kofar gidan inda zata gabatar da gidan waye suka zo jikinta ya fara bari. Anyi ya kai sau biyar sai tayi kamar zata daure sai murya ta fara rawa. Arifah ta gaji ta kira Awwab.


"Matarka fa zabuwa ce ta kasa yin abinda ya kawota sai rawar jiki take yiwa mutane"


"Bani ita" Yaso ace tare suka zo Allah bai nufa ba.


"Schatzi" ya kira sunanta a hankali.


Hawaye ne ya digo mata ba shiri "Hammana"


"Mw kike tsoro hmm? Ashe baki damu da rayuwar da families din sojoji suke yi ba."


"Na damu mana"


"Then do your best my baby..go on and make soldiers proud"


Wani irin dadi da karfin gwiwa taji gami da kunya tace masa "kayi ta min addu'a har mu gama na sake kiranka"


"Alwala ma zanyi yanzu kinji. Jeki kada ki bata musu lokaci"


Rigar da ta dora akan kayanta mai karamin hannu da tambarin makarantarsu ta gefen dama a gaba kuma an rubuta AZM Tureta. Gyara tsayuwarta tayi ta gabatar da kanta da kyakkyawan murmushi.


"Alheran welcomes you to the Military Voice"


Daga nan tsarin Darakta Bigman da kalaman da Arifah ta rubuta ta rinka bi har suka shiga cikin gidan inda Mama Dolapo take zaune a tsakiyar 'ya'yanta guda shida. Ta amsa tambayoyi game da sunayensu, aikin mijinta da shekarar da ya rasu. Sai kuma irin yadda suka rayu da wahalhalun da ta jurewa domin 'ya'yanta.


"A iya zaman da kuka yi da mijinki ko zaki iya fada mana wane abu ne yafi tsaya miki a rai game da aikinsa na soja"


Kwalla Mama Dolapo ta share tana murmushi mai ciwo tana magana da pidgin dai wanda a wurin tacewa zasu rubuta abinda take fada da turanci mai kyau a kasa saboda mutane su fahimta "kinsan kowane maaikaci yana fita yaje wurin harkokinsa ya dawo gida ga iyalansa. Idan tafiya ce zai ce kwana kaza zanyi na dawo. Amma mu indai miji yace zashi aiki fieldwork to fa dake matar dashi sai kun ga juna kawai musamman wurin rikici ne. Mafiya yawan lokuta duk inda sojoji suka je kai taimako na tsaro indai wata mushkila ta taso da za'aji rauni ko rasa rai da wuya idan ba cikinsu bane. Mu muna gida muna jiran tsammani bayan ko su a junansu sun sani kila fa idan na tafi nine bazan dawo ba ko abokin aikina wane. Babban tashin hankali shine kiga wasu sun fara dawowa baki da cikakken bayani game da naki mijin. Kullum kina cikin shiri kiyi wanka kiyi girki ki gyara gida kina sa rai yau ne, gobe ne, jibi ne zai dawo gareki. Idan da rabo ya dawo idan babu kuma sai dai sakon mutuwarsa" ta karashe da wani irin matsanancin kuka.


Cameraman din sai da ya kawar da fuskarsa ya goge ido. Haka Darakta Bigman, Assistant dinsa, Arifa da Radhiya kowa ya zubar da kwalla.


"Kin taba nadamar auren Soja"


"Ko kadan, bana fushi da aikin mijina don nasan ba kowa bane jarumi kamarsa. Damuwata bata wuce yadda rayuwa ta koma mana ba bayan ransa. Mata da yawa da muka rasa mazajenmu ance za'a bamu wani abu to amma lokacin wai babu kudi. Shekaru ashirin da biyu kenan tun ina zuwa Sokoto har na hakura na dena."


Radhiya tace "abu na karshe, kina da wani sako da kike son mikawa ga  gwamnatin kasar nan?"


"Ina dashi....KU DUBE MU 'yan Nigeria!....a kullum kwanan duniya ana mutuwa kuma muma din mazajenmu kwanakinsu ne suka kare. Sai dai abin dubawa shine umarnin kasarsu da son kare rayuwar miliyoyin jama'ar cikinta ya kaisu ga rasa rayukansu, su bar iyalai babu gata. Ku tuna da marayu da zawarawan da sojoji suke bari, ku tuna da su kansu sojojin domin damu dasu babu abinda za'a biyamu ya maye mana gurbin kewar da muke kwana mu tashi da ita idan suna bakin aiki. Abu daya kawai nake so shine kasarmu ta dena mantawa damu da sadaukarwar mazajenmu. Bakunan al'umma su rinka yi musu addu'a a duk inda suke domin su sake samun kwarin gwiwar yin aikinsu."


"Maman Dolapo mungode"


"Mune da godiya"


Ana dauke camerar daga kansu Radhiya taje ta rungume Maman Dolapo tana hawaye. Wai a haka ma don matar ta sakaya wasu abubuwan ne.


Kafin su tafi envelop ta dauko a cikin jakarta. Sakon Ummi ne a ciki na dubu hamsin ta mikawa Maman Dolapo da kuma katin da aka buga da wuri na walimar da suka shirya ta dawowar Zayyan domin ta bawa matan wadanda suka zauna tare. Dubu dari dama Ummi ta ware musu ita da Christie saboda idan ka cire su Mami bata da tamkarsu kuma a zamansu na barrack din. 


Washegari gidan wani soja mai konanniyar fuska suka je. Duka duka bai fi shekaru talatin da biyu ba. Nasa labarin ma ya tabasu inda yace an tura shi aiki ne cikin garuruwan da ake yawan rikici. Wataninsa bakwai ya dawo gida bayan wata biyar da dawowar tasa matarsa ta haihu. To ba shiba kusan kowa ya tabbatar jariri ba nasa ba. Mata da ta ga an ganota tace laifinsa ne baya bata kulawar da ta dace. Tun aurensu sau nawa ya taba yin wata guda tare da ita. Yayi bakincikin abinda tayi masa iyayensa suka raba auren ya sake tafiya aiki. A can kuma wuta ta kama a wani ginin maaikata bayan rikici ya balle suka je kai dauki. Nan ya kone sosai da kyar aka samu ya rayu amma rabin jikinsa da fuska sun kone. Aikin da yake ji dashi dole ya hakura sannan shekara biyar kenan duk inda ya nema ya rasa saboda munin halittarsa. Babu wanda yake tunawa da cewa mutum shida ya tseratar daga gobarar nan kafin zuwan motar kwana-kwana. Lokuta

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment