Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Captain Onomza da ko cikin sojojin ma ana tsoronsa saboda baya sassautawa mara gaskiya shine Maikudi zai kawowa wargi.


A take habo ya kama Maikudi. Major ya kawar da kansa su Baffa jiki ya hau tsuma. Da sunsan abin zai hada da sojoji babu abinda zai fito dasu daga rugarsu.


"Ka fahimta wanna ko"


"Kuyi hakuri yallabai yanzu me kuke bukata?"


"Bundle him up"


Mutum biyu ne suka taho kan Maikudi aka cukwikuye shi guda ya saba shi a kafada yayi gaba dashi.


Major da Captain Onomza suka sake gaisawa Captain din yace zai kira shi ya tabbatar masa a daren yau kafin gari ya waye Maikudi zai fadi ina kudaden marayun suke. Gidansu na Kano ma zai fadi me yayi dashi haka zalika idan yana da hannu a dauke kafar da 'yan uwan Innar Zayyan suka yi shima duk zai fada da bakinsa. Da sassarfa suka bar lungun sannan Major yace su shiga gidan.


Jume bata yi mamaki ba bayan ya gama mata bayanin me aka yiwa dan nata. 


"Yanzu sai yaushe zaku sake shi?" Ta tambaya cike da jimami ga matarsa da yara suna kuka don labari ya iso gidan tun kafin shigarsu ma.


"Sati daya zaiyi in sha Allah"


"Yanzu babu wani abu da zaku iya yi a fitar dashi?"


Wani murmushi Major yayi da ya tabbatar musu babu wani abu da zasu yi da zai sa ya fito da Maikudi. Dole Jume taji babu dadi amma dan nata yana bukatar saiti ita kanta ta sani. Su Major sun tafi akan idan da wani abu zai nemesu.


"Uhmm nace ko zaka nemi Mal.Aminu. Aminin Malam ne da suke zuwa Nijar din tare, dashi akayi komai na auren Malam din da ita Innar Zayyanu"


Godiya Major yayi mata suka rabu zasu dawo washegari a raka su gidan Mal. Aminu.


Captain Onomza baiyi sanya ba wurin ganin Maikudi ya samu tarba irin wadda ta dace da macuta irinsa. A wannan daren ya bambance aya da tsakuwa, ya gane waye soja da hatsarin dake tattare da shiga hurumin sojoji ko da a bayan ransu ne. Mutane ne masu hadin kai da tsayawa juna domin kare martabarsu koda a bayan idanunsu ne. Abinda ya kara tunzura Captain Onomza shine takaicin ace dan uwa na jini ne da wannan muguntar. Kuma ya rasa wa zai ha'inta sai iyalin Zayyan dinsu.

********** 


Matafiya suna ta shiri an gama wanka da cin abinci. Ummi da Mami ake jira basu gama hirar da suka dauko ba bayan wayar da suka gama da Mama Zainab. Zuwansu asibiti jiya likitan da suke gani ya gama bincike akan likitocin da ake kira neurosurgeons inda cikin sa'a ya sami wani kwararre da zai je Kuwait sati biyu masu zuwa. Likitan dan asalin kasar Philippines kusan yawo yake kasa kasa yana duba patients. Matsalar dai bata wuce samun shiga gurbin appointment dinsa ba karamin abu bane. Yini guda suna ta cuku cuku aka cusa Hadir a matsayin patient na karshe da zai gani a wani babban asibiti a Kuwait. Ba komai yaja hankalinsa ya karbe shi ba sai dadewar da Hadir yayi da lalurar da kuma jin cewa soja ne da ya sami rauni a filin daga. Tsananin rabo da addua suka sami alfarmar nan. Kudi dai Zainab zata kashe ba na wasa ba abu ya tasarwa miliyan tara. Zuciyarta ta karye hankalinta ya tashi. Idan ta bayar da wannan kudaden hakika zata tagayyara jarinta. Allah Ya taimaketa akwai kayan da tayi order daga China dake kan ruwa da basu sauka ba. Sune zasu riketa idan tayi sa'ar kasuwa.


Mami ta kwantar mata da hankali za ta sanar da Major domin nauyin ba nata bane ita kadai. Ummi bata bata lokaci ba itama wurin neman Innawuro a waya. Shanu biyar cikin abinda iyayen nata suka bata bayan ta koma hannunsu manya manya ta roki alfarmar a saka a kasuwa a ga nawa zasu samu. Dama ajiyarsu take saboda karatun 'ya'yanta da auren Radhiya idan ya taso.


"Abinda za'ayi Mami ku tafi da Karami domin su hadu da Ibrahim su taimaka mata. Bikin namu na kwana daya ne ana kai amaren washegari zamu tafi Kanon mu jira har su tashi"


"Baiwar Allah wallahi ina tausayin Zainab. Hadir ya godewa Allah bana jin zai taba haduwa da matar da zata kaunace shi rabi rabin yadda Zainab take yi"


Murmushi Mairama tayi ta bata labarin da Zayyan ya bata tun yana raye na ainihin waye saurayin Zainab din. Sun sha dariya su biyun yadda abotar su ta kasance.


Kowa ya shirya sun fara fitowa amma babu Radhiya har Mami sai da tayi cigiya.


"Tana kwance inda tayi sallar asuba tana bacci"


"Bacci kuma?" Mairama tace tana mamaki don Radhiya ba mai baccin safe bace musamman ma dai na yau da su Mami zasu koma.


"Taso ta Fauziyya tazo kuyi sallama"


Mami tayi saurin hanata "A'a wallahi ku dauko kayanku mu tafi. Nasan bai wuce gajiya ba" 


Kusan kwana tayi tana kukan hotunan wayar Awwab. Duk da ya goge takaici take don me yasa ya tsaya har mace ta saka masa abinci a baki. Wannan ma salon ya jawo musu zagi ne ace yayanta bashi da kamun kai. Ko mutum nawa ne suka gani? Mata nawa ya bawa ko suka bashi abinci a baki? Alawar da ya bata ma sai da ta tuna ko sun taba yin haka da wata kafin ita. Wannan yafi tsaya mata a rai taci kuka ta godewa Allah shine fa bacci yayi awon gaba da ita da asuba.


Ghazalatu dama jira take kowa ya fita daga dakin ta zauna kamar tana gyara daurin dankwali. Zahra na fita ta fiddo wayarta taje ta zame hijabin Radhiya da babu dankwali ta kasansa a hankali wani bangare na kan ta ya bayyana tayi saurin daukarta a hoto tana kunshe dariyarta. Awwab zata nunawa kawai don ta rage karfin alakarsu duk ta yadda ya samu.


Awwab da yasan yadda ya rabu da kanwar tasa ya shigo tsakar gidan ya kai sau biyar ko zai ga gilmawarta. Da yaji ance bacci take yi hankalinsa tashi yayi fiye da zatonsa. Ta yaya zai tafi bai sake ganinta ba sai nan da sati biyu. Walwalar fuskarsa gabadaya ta bace yana jin kansa sukuku suka fito. Rakiya harda Malamijo shima yana cigiyar jikarsa mai fitina akace tana bacci.


"Kun taba jikinta kuwa lafiya take babu zazzabi? 'Yar sojan ce zata yi bacci har goma na safe indai ba kwaya ta soma sha ba". Dariya ya basu sosai.


"Mami ko dai bata da lafiyar? Hancinta na gani yayi swelling da saman idonta" inji Zayyana.


Ummi tace "ko ma meye ku bari su tafi a taso ta don yanzu tana zuwa sai ta bata musu lokaci"


Ba dai kukan ta sake yi ba Awwab ya tambayi zuciyarsa. Tamkar kada su tafi haka ya rinka ji. Ghazalatu motarsu ta koma Zahra ta shiga wadda su Mami suka zo don kada a barta ita daya.


Kusan awa daya da tafiyarsu bayan Radhiya ya soma damunta saboda kwanciyar kasa ta bude ido tana mika. Dakin shiru babu kowa ta tashi da sauri babu jakunkunansu sun gyare dakin da katifar. Nauyin bacci gareta shiyasa bata ji motsinsu ba. Gabanta na dukan uku-uku ta garzaya dakin Hajjo wurin Ummi.


"Ummi sun tafi ne?" Tace cikin tashin hankali.


"Ina hankalinki ne, babu sallama babu gaisuwa"


Fita tayi ta dawo cikin sauri ta gyara kuskurenta sannan ta maimaita tambayar da ta riga tasan amsarta tunda bata ga Mami ba kuma babu kayanta.


"Sun tafi kina can kina bacci. Ko baki da lafiya ne?"


Hawaye ne ya taho mata tayi kokarin boyewa "shine basu tashe ni ba?"


"Kiji dadin isarsu da surutu ba. Sun wuce da Karami zai zauna a Kano..."


Alamun kukan Radhiyan taji ta dakata tare da mika hannu inda take jin sautin tun yana tashi a hankali har yayi karfi. Wani irin kunci da bacin rai take ji hade da gagarumar kewar Hamma Awwab. Me yasa bai ce a tasheta ba sunyi sallama. Me yasa daga zuwansa zuciyarta take shiga mabambantan yanayi daga tsananin farinciki sai bacin rai irin na jiya da ta ganshi da mata. Yau kuma don bai damu da ita ba yayi tafiyarsa.


"Ke menene?"


"Ummi ba komai" ta amsa muryarta na sake karyewa. Ta dauki kanta jarumar mace mai dauriya amma lokaci kalilin ta zubar da hawaye fiye da tunaninta. Ita kanta bata san me ya sameta ba sai an mata karin bayani.


Tun Ummin ta na rarrashi har ta koma fada amma taki cewa komai sai kuka. Daga karshe karamar wayar da Mami ta bar mata ta dauko. Ba kudin sayen bane dama ta rasa sai dai karancin wadanda zata kira. Emzee da Radhiya kuwa taki saya musu ne duk da tasan ana yayinta sosai tana jiran su gama sakandire.


"Ungo ki kira Mami da sauran 'yan uwanki ku gaisa kiyi musu sallama kinji 'Yar sojan Daaadaa"


Ba wuya anci galaba a kanta. Bare kuma rarrashi daga Umminta sai tayi dan murmushi.


"Kyalesu ni na fasa tunda basa son tawa sallamar" ta basar a zuwan taba damu ba.


"Ke dai ki karba kafin ki zo da kanki na hana"


Sautin dariyar Radhiyan taji ta girgiza kai. Wannan yarinya sai addu'a. Radhiya na kira da taji ta shiga sai kuma kunya ta kamata ta mannawa Umminta wayar a kunne. Dauka Mami tayi tana fada mata inda suke yanzu.


"Tsakanin ke da Maman yara bansan wanda ya koyawa yarinyar nan shagwaba ba. Ba karamin abu kesa aji kukanta ba. Yanzu kuwa kukan gaske take min wai bakuyi sallama ba"


"Allah sarki Radhiyata, bata wayar mu gaisa"


Karba tayi ta gaisheta kamar ba ita ke kukan ba ta kuma gaisa da Zahra "ina su Adda Fauziyya?"


"Suna daya motar da Hamma ke ja. Yanzu zan fada mata ta kira ki"


Katse wayar tayi ta kira Fauziyyan ta fada mata. Ita kuma tana jiran Zahran ta turo mata nambar take fada musu wai Radhiya tayi kuka da bata gansu ba.


Motar sai ta koma hirarta da kewarta da suke yi. Ghazalatu haushi ya kamata kamar wadanda aka yiwa asiri kowa ya bude baki sunanta yake kira. Awwab tuki kawai yake yi kamar ruwa ya cinye shi. Matsananciyar damuwa ya shiga na son sanin dalilin kukan da kewarta da take ratsa shi ta ko ina. Yana ji suna hira da ita wannan ya karba ya bawa wannan amma bata yi cigiyarsa ba, shima bai nema ba tunda yana tuki ne.


Daurewa kawai tayi bata neme shi ba duk a cikin fushin idan kowa baice a tasheta ba shi ya kamata yace. Ummin tana jin yadda muryarta ta sauya cikin jindadi ta gama wayar ta tashi ta tafi yin wanka.


Sun isa Kano shabiyun rana. Mama tayi musu abinci tace su ci kafin su wuce. Aka zubawa Awwab ya kalli plate din yaji gabadaya yunwarsa ta tafi. Cin abincinsa da Alheran a soron gidan Malamijo yake muradin maimaitawa. Kasa daurewa yayi ya fita ya bar Abdallah da su Ibrahim suna cin abinci. Mami da Mama kuma suna can suna tattauna yadda al'amarin aikin Hadir zai kasance. Cikin motar ya koma ya zauna a baya sannan ya kira Fauziyya yace ta turo masa nambar da zai kira su Ummi. Dariyar shakiyanci ta rinka yi masa ya fara fadan da bata sanshi dashi ba tayi saurin katse kiran ta tura masa.


Bugu biyu Ummi ta shafa wurin daukan kira ta kara a kunnenta. Muryar Awwab taji ta tambaye shi yaya hanya. Sun taba hira kadan kamar ta fuskanci me yake jira ta kwalawa Radhiya kira.


Bata tambayi ko waye ba ta karba "hello"


Shiru yayi yana jindadin amon sautin daddadar muryarta. Ita kuwa ta gaji da hello hello din tace "Ummi anki magana fa"


"Ko ta katse, duba zaki ga nambar Awwab ce ki sake kira. Mami tace ta saka nambar kowa"


Tashi tayi da gudu ta bar dakin, Ummi sai shiru taji ta koma inda suka kwana tana jin wani nauyi a ranta. A hankali tace "Hamma"
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: "Kukan ne har yanzu baki dena ba?" Yace a hankali yana jin farinciki na shigarsa saboda jin muryarta.


"Ni ba kuka nake ba"


"Shine daga tashinki kika soma damun mutane da waya ina jin ko wanka bakiyi ba"


"Ba kune ba sai kuka tafi bakuyi min sallama ba"


Siririyar dariya taji yayi "Silly girl. Cewa zakiyi nine na tafi banyi miki sallama ba ko ba haka kike son fada ba zaki basar?"


"Inji wa? Ni da munyi fada da kai"


"Ke abu baya wucewa a wurinki ne? Kuma ba na goge ba. Wai ma in tambayeki fushin na meye?"


Daburcewa tayi ta rasa me zata ce masa har ya sake maimaita tambayar "uhmm to ai zaka janyo mana ace yayanmu ne kai kuma kaje ana baka abu a baki"


"Ba ma ki da kunya, kema fa na baki har sau biyu"


"To ai ni kanwarka ce" tayi maganar da wasiwasin iya matsayin da take so daga gareshi kenan ko kuwa.


"Tunda dai bakya so na dena. Da Ghazalatu kadai zamu rinka yi"


Kit ta kashe wayar zuciyarta na tafarfasa. Ai sai yaje su karata ita dama meye ya dame ta dasu. 


Kallon wayar hannunsa yayi yana tambayar kansa meye tsakaninsa sa Alheran. Ta wuce kanwa shi kansa ya sani amincewa ta rage. Lokaci yayi da zai dena yaudarar kansa don bazai iya ba. Bashi da karfin zuciyar jurewa. Kallo daya yayi mata ranar da ya fara ganinta a gidan Mama aka kwance duk wani notin jikinsa. Sake kiranta yayi wayar na hannunta dama tana nadamar kashewar da tayi kada yaki sake kira.


"Ke da na hana tashi idan muna magana shine kike katse min waya."


Baki a kumbure tana fushi tace "kayi hakuri"


"Bakin naki zan like tunda baya son yi min magana bashi da amfani"


"Ashe rabon wani ma zai nemi nasa ya rasa ne" tace tana dariya da tayi tunanin abinda ta taba son yiwa Gwaggonta Salame wata rana da taji ta zagi Umminta. Wurin Hanne taje lokacin tana auren Malamijo da niyar karbar super glue ta saka mata a kunu tayi rashin sa'a ya kare.


Jin kansa yake cikin nishadi yace "Ki gwada ki gani idan Ghazalatu bata zane min ke ba"


" 'Yar soja ce fa Hamma ko ka manta ne"


"Na dai ce bazaki yi sojan nan ba kuma kin yarda"


Bata sanin tana shagwaba sai maganarta ta fito kamar yanzu da tace "to gaskiya ka dena cewa bakina bashi da amfani"


Fuskarta kawai yake haskowa tana magana. A kasalance yace "fada min amfaninsa guda daya sai na kyale shi"


"Shan sweet in rage maka" tace da sauri ta dora hannu akan labbanta ta rufe bakin tana jin matsananciyar kunyar kalamanta. A karo na biyu ta sake katse kiran tare da kashe wayar. Kan katifar ta hau tana shure-shuren kafafu kamar zata yi kuka tana mai kunyar maganar da tayi da yanayin da tayita cikin wata irin siga mai tsayawa a rai.


Wani irin dumi yake ji yana ratsa shi tun daga tsakiyar kansa har kafa. Ya runtse idanunsa yana hangota cikin zuciyarsa. Abin takaici bashi da hotonta ko daya a wayarsa. Bazai iya sati biyu bai ganta ba shiyasa ya fara neman abinda zai fake dashi ya koma Sumaila cikin kwanaki kadan.


**********


Mal Aminu yayi bakinciki mara misaltuwa da jin yadda Maikudi ya yi da dukiyar marayu bayan Captain Onomza ya fadawa Major.


Gidan Zayyan na Kano yana nan tsahon shekaru ya zuba 'yan haya a cikinsa. Kudin da ya rinka aikowa da kudin hayar dasu ya tamfatsa katon gida mai bene a nan Sakkwaton a cikin wata sabuwar unguwa da yanzu ta fara cika. Bai kuma yi jayayya ba saboda dukan da yaci ya fada musu cewa yan uwan Zayyan na Nijar sun dauka iyalinsa duka sun rasu kamar yadda ya fada musu. Mal Aminu jikin girma bazai iya doguwar tafiya ba amma ya baiwa Major cikakken sunan gidan da zai nema da garin da suke.


Harka ta zamani da kwarewa Major ya bayar da cigiyarsu ta hanyar amfani da sojoji ta bangaren Captain Onomza. Zasu koma Katsina su bayar da sati daya ko biyu idan babu wata nasara da kansa zai je Nijar din nemansu. Ko a haka baya jin ya biya Zayyan fansar ransa.


**********


Kwana biyar da komawarsu Awwab Katsina. Kullum zai kira Ummi ke dauka Radhiya ta kirkiri wani abin da zai hanata karba. To ta karba tace me. Ta barshi da muguwar kewa ya gaza yin abin kirkin da yayi niyya wato zagayen gidajen 'yan uwa. A rana duk inda yayi biyu ko uku sai yace ya gaji. Sai dai fa duk dare suna tare da Ghazalatu wanda hira da ita ke debe masa kewar Alheran kadan. Yana takaicin yadda baya iya sake mata kamar da kuma hirar ma yana yi ne don kada ya wulakanta ta. Abin yazo ya fara damunsa ga tunanin Radhiya da rashin jin muryarta. Mafita ya nemawa kansa zuciyarsa kuma tayi na'am da shawarar.


Major yayi musu bayanin yadda ake ciki Ummi har kuka sai da tayi. Saboda abin duniya Maikudi ya kasheta ita da 'ya'yanta da bakinsa ya rabasu da danginsu. 


Su Malamijo kuwa sauki ya samu daga shi har amarensa. Yau gidan an tashi da kukan Asabe tayi rantsuwar ko ana ha maza ha mata sai Malamijo ya saketa don bazata yarda ya kasheta da ciwo ba. Fafur taki karbar girki ita takarda take jira shi kuma yace bai gama cin sadakinsa da kudin da ya kashe na aurenta ba. Rigima taki ci taki cinyewa duk jama'ar gida yanzu sun san lalurar da ta kwantar musu da uba.


Nene tana gogawa Radhiya maganin makeron da ta karbo wanda a cikin sati kan har ya fara hadewa yayi baki ta hanata fita kallon rigimar da take son taje ta yi. Kunkuninta ta gama da zumbure zumbure ta hakura.


"Ni kuwa tun zuwanku Radhiya kinje gidan Gwaggonki Salame?"


"Gaskiya kada kice inje Nene bazan iya zuwa ba"


"Akan wane dalili"


"Ita da ko Malamijo bata zo ta duba ba sai nice zani?"


"Wannan kuma tsakaninsu ne. Ina ruwanki ko ke kika haifa masa ita?"


Ranta dai bai son zuwa ta soma jan hanci Nene ta dungure mata kai "me tayi miki kike gudunta rigimanatu"


Duk wani abu da zata iya tunawa da Salame ta taba yi musu ta rinka daukowa kawai saboda neman dalili. Karshe tace "kuma harda aurewa Ummi baban Danmama. Ai da na sani Ummina zai aura don ma dai bana so kawai kuma ana ta cewa an kusa biki fa sai Ummi ta makance ita kuma Gwaggon ya aureta."


Tashi tayi jin rikon Nenen yayi sauki ta suri hijabinta ta tafi kallon kwal uwar daka a tsakar gidan nasu. Nene ko bi ta kanta bata yi ba sai dogon nazarin da ta samu kanta da yi. Tabbas anyi haka amma tun lokacin bata jin wani yayi tunani a kai ma. Makantar Mairama farat daya tazo duk da an san tana ciwon ido. Bata mantawa ita Mairama ta bawa firinjinta ta sayar wani lokaci suka je asibiti akace babu komai a idon nata. Ko dai da hannun Salame tunda tafi kowa sanin abinda ya taba hadasu da marigayi Zayyan. Saurin kawar da tunanin tayi. Duk bakin halin Salame ace harda makanta kanwarta saboda namiji? Kasa nutsuwa tayi ta nemo yaro cikin yaran gidan ta bashi wayarta ya kira maigidanta. Tayi masa bayanin zarginta ne tace ya kamata a nemo kaikayi koma kan mashekiya.


"Haba Marka ina amfani wata ta warke wata ta makance? Yanzu dai tunda kin fara tunanin haka ki hadani da Mairama ko Radhiya din zan sanar dasu add'o'i da Ayatusshifa a karanta mata ana tofawa a ruwa tasha ta wanke idon. Zamu tsananta addu'a in Allah Ya yarda zamu sami makarin abin indai sihiri ne. Amma kada ki fada mata kada ki tada rigima idan zargi ne kawai. Ki bari mu gwada mu ga ikon Allah"


Godiya tayi masa ta ajiye wayar zuciyarta tana karfafa mata zarginta akan Salame.

***********


Washegari kuwa Nene bata yi kasa a gwiwa ba ta nemi Ayuba. Duk cikin yaran gidan shine ya tashi da ustazanci yana ma koyarwa a Islamiyya. Bayanin mijinta tayi masa shima ya hada da nasa ilimin da kansa ya siyo ruwan roba c'est bon babba yayi mata tofin nan yadda ya kamata. Ranar shi wuni tana sha tana shafe ido. Nene tace mata su gwada ko za'a dace ne ta karba da murnarta.


Bayan kwana biyu Ummi ta fara jin jikinta yana canjawa tafi jindadinsa sosai gashi ruwan tofin saura kadan. Radhiya ta nema saboda ta jiyo muryarta tana cewa Malamijo yau kwadayi take ji yana rantsuwar kada ta bishi gonar da zai tafi a lokacin.


"Kin raina min uba ko" ta tambayeta bayan ta amsa kiran.


Sanye take da riga da skirt na atampa ta gama shirinta da hijab ruwan madara wanda ya dace da kayan iya gwiwa za ta bishi gona tayi barna.


"Ummi balance dayet muke bukata"


"Allah Ya shirya min ke, zo ki dauki kudi ki siyo min ruwa irin wanda Ayuba yayi tofi a ciki. Ki siyo guda uku sai a ajiye"


Murmushi tayi "Ummi kin fara gani ko dan dishi dishi?"


"Ke dai ki sakani a addu'a ido ya bude na ganku ke da kaninki" 


"Amin Ummi, wayyo dadi"


"To wuce ki tafi banda yawo" sai ana jaddada mata kamar karamar yarinya.


Tsokanar Ummin tayi tace "Ina zani ko azahar ba'ayi ba inje basu gama abinci ba balle na sa rai da balance dayet din"


Muryar Malamijo ta ji yana magana daga soro ta yi murmushin mugunta. Daga masa hankali zatayi tayi ta binshi yana fada ta dage gonar zata je tunda a kafa yake zuwa. Sai sun isa wurin shagon da zata je sannan zata rabu dashi. 


Da dan gudunta ta taho kamshi da idanun da suka kafeta a gaban Malamijo suka kashe bakin da jikin nata baki daya.


Wani murmushi Awwab yayi mata ta mayar masa idanunsu sarke da na juna. Malamijo bai kula ba yana ganinta yace  "Allah Ya taimakeni yau ga yayanku na Katsina yace sako ya kawo muku ke da Mairama. Idan kika sake kika biyoni zai koma da kayansa sai in ga karyar cin balanciye din"


Ficewa yayi ya barsu a tsaye. Wani irin kallo yake yi mata taji ta takura.


"Muje wurin Ummi din" tace bayan ta juya masa baya saboda wani nauyinsa da take ji.


"Wait"


A nutse ya tako ya dawo gabanta ya tsaya. Jeans navy blue da layin fari da ya dusashe daga tsakiya ta gaba da shirt mai maballai ruwan toka ya lankwashe dogon hannunta zuwa rabin hannun. Fuskarsa a gyare sai hancinsa ya kara fitowa. Kanta ta sunkuyar ta ma kasa kallonsa.


Da wannan muryar tasa mai kauri da tafiya da hankalinta yace "baki tambayeni me ya dawo dani ba, ko dama kinji a jikinki zan zo?"


"Ba wurin Ummi kazo ba?"


"Basarwar ce?" yayi tambayar yana son sake hada ido da ita.


Hijabinta ta janyo gaban fuskarta zata rufe ya girgiza mata kai.


"Ahhh" yace yana mata alamar ta bude baki.


Kafada ta noke tare da murmushi.


"Please Alheran"


Sake nokewa tayi yace "dadin abin tare muke da My G tana mota"


"Ahhhhhh" tace da sauri har tana bashi dariya domin kuwa ya gama tabbatarwa ba shi kadai bane ya fada wannan kogin da baya fatan fita. 


Irin sweet din rannan ce dai wadda ya taho da ita daga Germany ya fito da ita daga bakinsa ya kankance ido yana kallonta "See what you did. Kin cikani da surutu kinsa na kusa shanyewa"


A bakinta ya saka mata kunya tasa ta rufe ido da tafin hannunta.


"Kinsan wani abu" ya bijiro da maganar don kawar da hankalinsa daga kallon bakinta da take shan sweet din dimple dinta da yake matukar burgeshi yana ta sake shigewa ciki.


Kai ta girgiza masa ya dawo gefenta ya tsaya "ta kare miki Alheran auren dreba ya tabbata a gareki"


"Ni dai a'a"


"Are you sure? Ko da dreban mutumin da kike shan sweet din bakinsa ne?"


"Ya Allah" tace yadda yake yi idan yaga abin mamaki tana jin wani irin farinciki mara misaltuwa.


"Na sani ai bazaki so kada ta kare miki ba in dai shine"


Kokarin saita kanta tayi ga murmushinta yaki bacewa "inji wa"


"Ba sai munje nan ba kawai ki amince kamar yadda na amince"


Cike da shagwaba tace "Ni dai wallahi...."


"Me? Ba haka bane?"


"Alawar ce ta kare" tace tare da yi masa gwalo ta soma tafiya da sauri.


"Zaki aureni?"


Ita ce tambayar da taji ya jefa mata a daidai lokacin da kafarta daya ta fita daga soron. Tsayawa tayi a wurin ta kasa gaba ta kasa baya har ya karaso inda take ya rabe ta gefenta ya wuce har cikin tsakar gidan da sallama yana kiran Ummi.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Ummi kamar daga sama ta tsinkayi muryar Awwab. Yadikko ce ta amsa masa suka gaisa ta nuna masa dakin Hajjo.


"Shiga tana ciki"


Radhiya ta hango tsaye ta kasa yanke shawarar komawa taje

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment