Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

riko wuyansa domin kada ta fadi. Idanunsu cikin na juna ya soma juyi da ita yana dariya itama sai da tayi saboda yadda yake yi mata.


"Nice to meet you Mrs Awwab" yace lokacin da ya direta a gabansa.


Kunyar ce ta motsa saboda yadda ya tsareta da idanu ta kasa magana sai ma juyawa da taso yi ta fita. Hannunta kawai ya janyo ta fado jikinsa ya rungumeta sosai. A tare suke sauke numfashi da ajiyar zuciya yau burinsu ya cika. Kanta yana kirjinsa ya saka hannuwa a bayanta ita kuma nata suna ta wurin cikinsa ya soma magana cikin wani irin salo da shaukin soyayya.


"Alheran don Allah kada mu taba bari fushi ko wata zugar mutane su shiga tsakaninmu. Nasan ni dake are not perfect but we complete each other. Kece zabin Awwab tun kin baby har ranar da zai dena numfashi in sha Allah"


Kalamansa sun kara masa matsayi da kima a idanunta. Batare da ta dago kanta ba ta yi magana don tsokana "har lokacin da aka yi min aski?"


Murmushi yayi "tashinki daga baccin nan da kallon da kika yi min shine lokacin da Awwab ya fara yiwa Alheran soyayyar da yake fatan ta kare a aure"


Murmushin da tayi ne ya janyo shigewar dimple dinta ciki sosai. Abinda Awwab ya dade yana jiran damar yi sai ji tayi ya dora lips dinsa a wurin yayi kissing dinta. Kunya har sai da taji cikinta yana wata irin yamutsewa shi kuwa bai tsaya ba sai pin din da tayi rolling dashi yabi ya zaresu ya zame mayafin. Kansa ya kai gaban goshinta yana shafa gashinta da yake kulle cikin ribbon tayi packing dinsa a tsakiyar kanta ya kuma bata wani kiss din. 


Da wata irin murya yace "rufe idanunki"


Ki tayi sai dai suna hada ido ta runtse nata da sauri saboda bata da kuzarin cigaba da kallon idanunsa. Tana ji yana dan motsi amma bata bude ba taji ya saka hannu ya zame mata ribbon ya cusa yatsunsa cikin gashinta ya sake matso da ita. Bakinsa ya hade da nata a nutse ya jefa mata sweet din bakinsa irin wadda suka taba sha a soron Malamijo. Bata san lokacin da ta bude idanuwanta ba saboda ta gane dandanon alawar. A haka suka sha ta kusa rabi sannan ya bar mata a bakinta ya sake janyota jikinsa.


"Ina jindadi idan muna sharing abu...nafi son ko me naci babyna ma taci. I hope daga yau haka zamu koma yi...it is better than daya ya ragewa daya"


Duk da bakon yanayin da take ji sai da ta tsokane shi "harda abinci ko?"


"Ewww ke fa kazama ce" yana bata fuska da tunanin a tauna abinci daga baki.


Dariya tasa "kaga tuwo zaiyi dadi...."


"Fita, fita ki tafi dirty girl" yace yana nuna mata kofa tare da dora mata mayafinta a ka.


Turjewa tayi "nama fa?"


"Out" ya kuma cewa yana bata fuska ya dago hannu ya biyota ta kara gaba da sauri. Tana bude kofar ya janyota ya rungumeta ta baya kansa na kafadarta "babu abinda zai fito daga bakinki na kyamace shi Schatzi. Idan kin ga dama har kunu musha a haka"


Ita ya bari da bata fuska "shhhh please Hammana dena fada"


"Ko kosai shima zaiyi dadi"


Yatsunta tasa ta toshe kunnuwanta ya sake matseta "juyo kiji last one din"


Kafada ta noke ya juyo da ita da kansa "I love yo baby"


A hankali ta dago kai ta kalle shi idanunta sun kara girma da haske tace "I love you Chèri" tare da shammatarsa ta fice da sauri.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: Ita da Arifah suma nasu shirin suka fara inda da sahalewar angwayen nasu suka amince a hada dinner a Abuja bayan kowacce anyi mata nata bikin na gida. Arifah a Jos za'ayi wasu events din bikin 'yar gwamna guda daya tilo ita kuma Radhiya sai da aka yi ta tunanin inda yafi dacewa karshe Mama tace ayi a Abuja amma yini a Sakkwato za'ayi kamar yadda za'ayiwa Arifah a Jos. Ranar kai amarya kowacce a daukota daga garin mahaifinta washegari suyi dinner dinsu. Daga nan kuma tsugunne bata kare ba domin Tante tana can Nijar da sauran 'yan uwa ana shirin bikin 'ya'yanta Yousuf da Radhiya saboda haka ana wannan dinner din can zasu wuce ayi sabon biki sannan amaren su tare. Dama kuma Tante din ta riga ta sanar dasu Ummi kada a dauko wata mai gyaran jiki zata taho da kawarta tun suna 'yan mata idan sun zo taron Zayyan zata barta a nan. Arifah daga Nijar zasu wuce France shi kuma Awwab ya riga yasa an fara nemawa Radhiya visar Germany can zai tafi da ita suyi sati biyu su dawo Nigeria. 


Tun yanzu kowa jiki ya fara fada masa saboda shirye shirye. Ana ta kai dinkunan biki na amarya , 'yan uwanta da iyaye. Zahra da Raji sun dawo daga Katsina sai hutu ya kara daga wurin aiki amma fa idan ya koma shekarar kaf bashi da hutu. Fauziyya itama sauki ya samu sun koma Katsina sai daurin auren Bilal zai taho da ita.


SANNU SANNU BATA HANA ZUWA


Saura kwana uku daurin auren Arifah hakan na nufi kwanaki hudu ya rage na Radhiya amma har yanzu Awwab bai dawo ba sai bata hakuri yake yi al'amura sun zo ba yadda yayi zato ba. Radhiya tun tana daurewa sai da tayi masa kuka da daddare akan bata fatan a daura auren baya nan. Hakuri ya bata domin wani training aka saka yake jagoranta. Ainihi bashi bane da tuni ma ya dawo gida sai matar wanda zaiyi ta haihu sati biyar kafin ainihin lokacin haihuwarta. Abu yazo da tangarda dole ya dauki hutu. Gashi daga shi sai Awwab ne suka yi wannan course din a Ukraine. Tunda sunsan aure zaiyi shine aka daga masa kafa zai taho ana gobe daurin auren Yousuf. 


Ga abu ya dame shi ga fushin Alheran dinsa sannan Mami da Daddy sun kira shi a lokuta mabambanta kowanne baisan dayan ya kira ba suna jaddada masa idan ya bari aka daura aure babu shi zai ga fushinsu.


Ya gama shirinsa tsaf ranar da zai taho ana gobe daurin auren su Arifah yayi ta kiran Radhiya taki dauka tana ta kunkuni. Text yayi mata mai dauke da dadadan kalamai ya sanar da ita yana hanya zai sauka shadayan dare. Bata yi masa reply ba sai sai kowa ya ga sauyi da walwalarta da ta karu. Tante ta fadawa ya taho tace to maza ta tanadar masa abinci a kai gidan Mami. Yousuf da suka zo da sauran mutanen Nijar shi acan yayi masauki dakin Awwab tare da Raji. Gidan Major General Zayyan kuwa babu masaka tsinke saboda 'yan uwansa na Nijar iyaye su Alh Sidi da Alh Ghoumar. Alh Mousa dai da mijin Mammee da sauran tawagarsu hotel aka kama musu. 'Yan uwa ne aka taru ko ta ina. Emzee ma ya da safe ya iso sai dai gidan Mama ya wuce kai tsaye ga mamakinsa Halifa ma ya riga shi zuwa suna tare da Ibrahim. Sakin fuska yayi kamar babu komai a ransa ya rungumi dan uwansa sai dai har ransa yana jin babu dadi da kuma hangen me zai faru idan gaskiya tayi halinta. 


Sai bayan magariba Radhiya ta dora girkin da Tante tace tayiwa Awwab Emzee da Ibrahim suka zo dauka. Farar shinkafa ta dafa masa tayi shar da ita sai dai baifi minti biyu ya rage ta kwashe ba ta juye mata alayyahu madaidaici a ciki. Gyareshi tayi amma bata yayyanka ba a haka tayi amfani dashi bayan ta cire shi. Ba kuma tsigar nan ta ganye kawai ba, ta hada ne harda itacen inda yayi karfi da yawa kadai take yankewa. Yau dai tayi kamar na mutum biyar ne tunda tasan su Yousuf na gidan. Miyar kuwa farfesun kaza ne da ta barshi ya danyi kauri an yanka dankali amma da girmansa a ciki da caras shima da dan girma sai koren wake. Rahima, Zayyana da Hibbah suna makale wurin koyon girki tayi ta gama. Sai da ta dibar musu suka sama mata lafiya. Ibrahim ne ya fara zuwa kitchen din yace Zayyana tazo ta bashi labarin Khaleel. 


Radhiya da bata gano komai ba tace "ashe dai zatona ya zama gaske da nake tunanin ko saurayinta ne kusan kullum sai ya kirata sai ta gudu don kada muji me ake cewa"


Kashewa Zayyana ido yayi da take ta jin kunya Hibbah da Rahima sun san komai shiru kawai suke yi "zan binciko mana shi Adda Amarya muna zuwa"


Bai yarda ya fita ba sai da ya sakata a gaba. Rahima ce take ta yiwa Radhiya tambayoyi suna tsaye ita da Hibbah ita kuma tana wanke kwanukan da ta bata Emzee ya shigo. Bata ganshi ba sai alama ya yiwa Rahima da suyi shiru. Ido ya rufe mata ta baya sai dai jini baya buya tuni ta gano rabin jikinta ne Zayyan dan Zayyan. Rungume juna suka yi tana ihun murna don har ta fitar da ran zai zo saboda tasan tsananin makarantarsu.


Ya wani kara budewa ya kereta tsaho sosai yana mata dariya ya dan duku kansa "ashe nayi missing dinki Addata yau gaskiya kwanan hira zamuyi kafin Hamma ya daukeki, na fasa bin Ibrahim ma"


"Ka manta ko an daura ina gida har sati biyu?"


"Eh to idan ya bani damar hirar kenan. Muje dakina kiga wani abu"


Suna juyawa Hibba tace "Ya Emzee ina wuni"


"Lafiya kalau mai tale baki number two"


Dariya tayi za ta fita taji Rahima tayi mata wani irin riko tabi bayanta da sauri. Radhiya tayi saurin cewa Emzee ga Rahima tana dakatar da ita su gaisa.


Haba Rahima idanu tuni sun raina fata ashe tunda ya shigo ta tabbatar shine sojan taji cikinta ya kulle saboda girmansa da ta gani. Sai yanzu ya kula da ita a zatonsa 'yar uwar Hibbah ce ko wata dai cikin bakin biki ya saki fuska zai amsa gaisuwar da tayi masa a tsorace suka hada ido. Wani irin yanayi ne da bai taba zato ko tsammani ba ya fizge shi a take a lokacin ya fadada murmushinsa gareta yanayin idanunta tamkar wani maganadisu ya zame masa.


"Kinyi kama da matsorata, yaya sunanki?" Ya tambayeta a kasalance.


Yawu ta hadiya tace "Rahima"


"Rahima zaki zama kawar soja?" ya sami kansa da cewa babu wani tunani.


Duka Radhiya ta kai masa a baya ganin idanun Rahiman sun kara girma duk ta firgice "kada ka tsorata min kanwa dama har yanzu bata sakewa idan Daada ya shigo."


Tana ganin Radhiya ta dauke masa hankali ta fita da sauri ta riga Hibbah zuwa daki. Sai da ta rufe kofa ta soma sauke numfashi da sauri da sauri. Tunda take bata taba ji ko ganin wani abu da ya kwashe mata nutsuwa kamar wannan bawan Allah ba. Danganta abin tayi da tsoron sojoji da take yi ta kai hannunta kirji tana jin yadda zuciyarta ke bugawa.


A kasa kuwa kafin su bar kitchen din Ibrahim ya shigo yana kiran Emzee dreban da zai dauko Awwab motar ta lalace a hanya Raji kuma da yake gida bai san gari ba shine Ummi tace suje su dauko shi. Shi dai Emzee so yayi ya zauna a kira masa yarinyar nan mai idanu bai gaji da kallonta ba.


Da abincin da Radhiya tayi a motar suka je dauko shi. Ibrahim kasa hakuri yayi sai da yace masa yayi jiki saboda aikin nasa yafi yawa a zaune gashi babu inda yake zuwa daga gidan da ake basu kamar hostel idan baka da ra'ayin kama wani ko kana da naka sai office din nasu. Murmushi kawai yake yi yana jin kewar Radhiya amma dare yayi ana neman shabiyu gashi jirgin safe zasu bi zuwa Jos saboda karfe biyu ne auren kuma suna tare da ango. Wanka kawai yayi da sallah yaci abincin nan sosai tare dasu Raji suka kwanta a gajiye bayan ya tura mata text din godiya tunda taki daukar wayar tasa. Ya dena damuwa don ya ma fi son haduwarsu ta gaba da amsa sunan matar Awwab. 


Da safe kuwa ba a nutse suke ba anata shiri. Duka  kayan da zasu saka na daurin auren a jaka suka saka su. Suka wuce airport mota mota sai Jos. Karfe biyu da 'yan mintuna bayan sallar azahar Major General Zayyan Tureta ya karbi sadakin Arifah daga hannun kanin Alh Mousa naira dubu dari da dalleliyar mota. Nan da nan jama'a suka shaida auren Yousuf da Arifa abinda wata uku da suka wuce ko sanin juna basuyi ba bare suyi tunanin wannan rana. His Excellency the Executive Governor of Plateau state Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu ya tara jama'a sosai 'yan siyasa manya a wannan taro mai dumbin tarihi. Ansha hotuna a ranar biyar na yamma suka sake dagewa sai Birnin Shehu. Ga gajiya an dauko ga wata za'a sake dauka gobe. 


Hotel da wani guest inn Zayyan yasa yayunsa kama dakuna da dama saboda yayi mamakin jama'ar da suka zo wannan aure. Da wuri ya biya kudin masaukin saboda haka basu sami wata matsala ba. Mutanen Katsina gayya guda sai kayi mamaki kamar ba su bane masu cewa dole Awwab ya auri 'yar uwarsa don duka kakanin Awwab sunzo su ukun. Malamijo da 'ya'yansa maza kananun ne kadai babu amma ya dauko kowa ga kannensa suma motoci suka ciko da mijin Nene. Ga jama'a guda daga Nijar wadanda suka halarci auren Yousuf jiya. Daga Rugar Barkindo Ardo, Baffa Gide, Baffa Habubakari da su Zakari kusan kowa yazo shaida auren 'yar soja. Mutanen Tureta da su Alh Salisu da duk wanda ya kamata sun zo. Chibuzor dashi aka daura na Arifah kuma yau ma yana tare da babansa Zayyan shima zai shaida. Karfe goma na safe aka saka saboda masu komawa a ranar su iya tafiya. Kusan ma dai kowa juyawa zaiyi suna sa ran da an daura anci abinci a fara tafiya.


Zuwa lokacin Zayyan ya ciko sosai don Mairamansa ba da wasa ta tasarma fito da mijin nata ba. A babban masallacin juma'ar unguwarsu da yake bakin titi za'a daura auren. Wata hadaddiyar mota ce ta tsaya a harabar masallacin sojoji suka yi dafifin kare shugabansu. Mutum uku ne suka fito daga motar wata shadda suka saka iri daya ruwan zuma mai dan karen tsada. Dinkinsu da komai hatta hula da takalmi basu bambanta ba. Suna fitowa aka fara daukarsu a hotuna tun kafin su karasa ciki. Uban gayya ne Major General Zayyanun dan mutan Sakkwato yana ta murmushi kamar shine angon. Har yau da yake shirin aurar da 'ya bai dena tafiya da hankulan mata ba. Daga gabansa rike da wata sanda mai kyau domin samun balance din jiki Daddy Rtd Major Mustapha ne mutumin Katsinan Dikko kunya gareku ba tsoro ba. Kamilin mutum msi tafiyar da komai cikin tsari da haiba. A bangaren damansa kuwa aminin kwarai ne wanda abotarsu ta zame musu 'yan uwantaka Rtd Lt Hadir gaisuwarsa daban take jinjina ga dan mutan Kanon Dabo mai dutsen Dala da Gwauron dutse, Kano ko da me kazo an fika. Hadir Murtala abokin da Zayyan Tureta wadanda sukayi zamani a matsayin zaratan jaruman samari kyawawa. Su ukun nan tarihin rayuwarsu abin duba ne domin kada duniya ta manta da soyayyarsu da sadaukarwa domin kasarsu domin abotarsu. Taku suke maza 'yan uwansu na waigensu domin sun isa a dube su din. Cikin masallacin suka shige ana ta gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki.


Daga waje mintuna kadan bayan shigewarsu wata motar ta iso Awwab ya fito rike da waya a hannunsa yana sanye da shadda fara kal wadda aka yiwa aiki da zare ruwan toka msi duhu. Hula da takalminsa kalarsu daya da zaren sai agogo da links din hannun rigar duka silver masu kyau. Saboda kurewar lokaci ranar da zai taho yayi aski saisaye aka yi masa wani irin gyaran fuska da ya fito da gajeren kwata miliyon dinsa. Matashi ne ajin farko mai tattare da nutsuwa da kamala. Kallo daya za ka yi masa  kasan cewa yau din ta dabance a wurinsa ranar aurensa da Alheran dinsa. A gefensa angon jiya ne Yousuf bayansu kuma Emzee da Ibrahim sanye da wani ubansun yadi da Mama ta dinka musu. Su dinma kamar iyayensu daga sama wato hula har takalmi babu ta inda su ka bambanta komai. A tare dasu Halifa ne shima ya fito fiye da zato. 


A cikin masallacin kuwa wakilan ango da amarya aka nema Hadir da Zayyan su ka matso gaban limanin suka zauna a kusa dashi.  Yadda yake a tsarin musulunci haka aka gabatar da komai inda Hadir waliyin amarya ya karbi sadakinta naira dubu dari daga hannun Zayyan waliyin ango. Addu'a aka yi aka shafa Captain Muhammad Awwab Mustapha ya zama mijin Alheran Radhiya Zayyan Tureta. 


Hamdala ya rinka yi babu tsayawa a lokacin da yaji kammaluwar komai Schatzi dinsa ta zama tasa halak malak. Hotuna ake ta yi da gaishe gaishe na 'yan uwa da abokan iyayensu. Malamijo da tawagarsa kadai sun isa gayya. Gidansu Zayyan aka wuce ya sakarwa 'yan uwansa da matansu Badaru ragamar girkin da za'a ciyar da mutane kafin su tafi. Da farko Mairama yaso su zo su kwana a garin domin yin abincin ita kuma tace dama ce ta nuna musu yana kaunarsu kuma ya yarda dasu. Ai kuwa basu bashi kunya ba domin kowa yaci ya sha anyi abu cikin girma. Kuma sai da Baban Arifah ya samu yazo shima duk da mutanen da ya baro a gida. Maikudi ne dai idan akwai namijin mujiya to shi ne a wannan taron. Yana ta rakubewa a gefe Zayyan sai ya dauke kansa kawai. Daga baya ya ga bai da amfani nunawa duniya akwai baraka tsakaninsu shiyasa ya koma sako shi cikin al'amuran. Da yace Maikudi kuwa sai ka ganshi da mugun sauri ya taho.


Ba su suka sami saukin kebewa daga mutane ba sai lokacin da ya idar da sallar la'asar. Yana zaune da 'yar cikinsa ya ajiye babbar rigar da hula can gefe. Bayan doguwar addu'a ya dauko wayarsa ya turawa Radhiya text din da yake ta son yi tun bayan an daura auren.


(Ina hukuncin matar da bata daukar wayar mijinta? Ki fada mata Awwab ya zama na Alheran kuma ta shirya karbar punishment dinta na share shi).


Hira suke yi da Fauziyya da Zahra rabi suna tsokanarta rabi kuma shawarwari ne suke bata tunda yanzu itama girma yazo. Ita dai jiki yayi sanyi kamar ba ita ba. Wani abin tayi dariya wani kuwa sai dai taji kunya idan sun fada amma ta kasa magana. Duk da ba bikin bane ya taso amma gidan ya rude don ma anyi sa'ar kawowa Ummi masu aiki biyu 'yar dattijuwa da kuma mai sauran kuruciya. 


Sakon Awwab ta karanta suka ga murmushin nata ya koma na daban.


Fauziyya ta dago wuya zata leka wayar "Ango ya miko gausuwa kenan...mu gani me yace" 


Janyota Zahra tayi "ina ruwanki, idan kin matsu kiji me yace nemi naki mijin tunda suna tare kema yayi miki text din. Radhiya tashi ki koma daki kiyi magana da mijinki kinji"


Kasa mikewa tayi Fauziyya ta cigaba da zolayarta sai da Zahra tayi da gaske don ta kula jikin kanwar tasu mai sabon mukamin matar yaya yayi mugun sanyi. Tana tafiya Fauziyya ta tallabe kanta da hannu biyu.


"Jikin ta kanwa yayi la'asar fa Sis. Duk surutunta kinga fa bakin ya mutu. Allah sarki irin matsoratan amaren nan za'ayi"


"Tausayinta kike ji ko tsokana?"


"Tausayin dai...hmmm kazo kayi ciki ka rasa inda za ka tsoma ranka kaji dadi"


Tuntsirewa da dariya Zahra tayi ta gano Fauziyya laulayi ne yasa ta a gaba shine za ta saka mutane itama.


Bayan Radhiya ta koma dakin babu kowa. Gefen da tayi sallah ta kalla ta tuna nasihar da Mama tayi mata a wurin bayan ta umarceta da tayi nafila ta godewa Allah bayan an daura auren. Wata irin soyayyar Awwab take ji tana kara shigarta sosai ta lumshe idanu ta kwanta sannan ta kira shi.


Sautin numfashinsa ne ya sanar da ita ya dauka amma yaki yi mata magana shima nata hawa da saukar numfashin kadai yake sauraro wanda ya kara masa gudun bugawar zuciyarsa.


Ita ta fara kartse shirun nasu ta hanyar gaishe shi da tattausar murya "Hammana ina wuni"


Da kyar ya iya hada kuzarin amsawa yana jin kamar yau ya fara son ta "Matsoraciya yaya kike?"


"Tsoron me nake yi?"


"Daga kinji nace zaki karbi punishment shine kika dawo daga  strike din yi min magana mana"


Kamar yana gabanta ta tura baki "to ba kaine ba"


Katseta yayi don yasan fushin har yanzu na menene "Ko ba ni zan aureki ba kinsan bazan yi missing aurenki ba bare kuma Alheran din ta Awwab ce"


Kunya taji sosai yayi murmushi ganin yau ita ce babu baki "wai ni tun yanzu ina bakin naki ya koma ne? Anya zamu shirya da wannan amaryar kuwa wata bebeya nan da ita"


Ibrahim ne yayi masa alama da hannu motocin da zasu kwashesu sun iso. Ba yadda ya iya sallama yayi mata yace tayi musu addu'a gasu nan fitowa zasu taho. Kafin su iso anyi abinci sosai jiran isowarsu kawai akeyi. Kowa yaci ya koshi kuwa sai son barka aure ya yi albarka sai fatan zaman lafiya ga sababbin ma'auratan. 


A gajiye su ka dawo ana sallar isha kowa sai bacci. Angwayen biyu, Raji da Bilal suna gidan Mami. Ibrahim da Emzee kuwa gidan Mama. Daya ga wata ta matso babu lokacin zama babban taron da ake ta jira ne Allah Ya kawo shi. A haka ma da ba su ne suka shirya ba basu da zama balle kuma na washegarin da yake nasu. 


Dadin abin ma kuma domin tallata shirin Radhiya Baban Arifah ya samu yace a saka wani bangare nashi a wurin taron tunda shugaban kasa zai je. Ita kuma sai ta gaggauta sanar da Supervisor dinta domin ta nema mata izini. Kwana biyu a tsakani matar ta fada mata cewa su uku an wakiltasu zuwa su gani sannan su tayata murnar dawowar mahaifinta. Ranar kwanan murna tayi sai gashi ana gobe taron sun iso. Duk wannan lokacin angon nata yayi wuyar gani suyi nan suyi can saboda ganin sun kammala komai bisa tsari yadda suke so. 


Malamijo da kansa ya hada mutum biyar cikin masu zuwa taron daga gidansa a yara sai kuma Yadikko da Hajjo. Shatar mota yayi musu ana shirin tafiya sai ga Salame niki niki da kaya ita da yaranta wai itama zata je. Ba wani abu bane ya tunzurota kuwa sai labarin da ta samu na cewa Rahima ashe ta bi Mairama. Zuwa zata yi har gidan taci mutumcin yarinyar tunda tana son nunawa makiyanta cewa bata isa ba. Abu na biyu kuma so take taje ta ganewa idanunta wace irin rayuwa Mairama da Zayyan suke yi da akaje daurin auren 'yarsu a Sakkwato aka dawo ana zuzuta taron da angon da Radhiya ta dace da shi. Malamijo bai hanata zuwa ba amma da karamar 'yarta kadai ya yarda taje sauran ya turasu cikin gidansa.


Tunda aka shigo garin Abuja bakin Salame yaki rufuwa tana ta kalle kalle. A tasha dreban ya tsaya aka tura wani dreban daga gidan yaje ya taho dasu. Nan fa cikin Salame ya duri ruwa ganin sojoji da bindiga tun daga bakin gate din wani irin katon gida mai kyau. Jikinta yayi sanyi kalau ba ta fatan ace wannan ne gidan Mairama. Bata gama tunanin ba kuwa aka wangale gate din gidan. Wani bacin rai taji ya tuko ta da fa yanzu gidan nan nata ne ba don bakincikin da Mairama tayi mata ba. Suna shiga Ummi da kanta ta fito tarbarsu da murnarta tare da Rahima wadda tun safe da tace mata Malamijo yace da Salame za'a taho jikinta yayi sanyi. Ummi tana kula da duk motsin yarinyar kuzarinta ya ragu sai kayi mata magana bata ji ba saboda zulumi. 


Ashe kuwa ba a banza ba don suna saukowa daga mota da ta tafi da murnarta saboda tana son Umman nata taje ta durkusa har kasa tana gaisheta. Kusan hambareta Salame tayi kafin ta dangwara mata yarinyar da ta kai shekara uku tana wani irin wari.


"Ki wuce da ita ki gyara mata jiki tayi kashi sannan ki bata abinci "


Jiki na rawa Rahima ta karbi yarinyar da kafarta da komai amma dole ta dauketa ta wuce Ummi ta shiga ciki. Itama Ummin ba ta niyar koyawa Rahima rashin kunya dole ta bi umarnin mahaifiyarta. Sakin fuska tayi tana musu maraba. Salame tana ta wani basarwa ita bata ga abin burgewa ba har suka shiga ciki. Tun daga

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment