Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciro daga ledar ta mika mata "jeki ki saka wadannan gani nan zuwa. Ko hoda kada ki shafa sai nazo"


"To Mama" tace ta fita da murnarta taje ta nunawa su Zahra su ka tayata murna.


Yadi ne mai kala biyu. Mara adon light purple ne anyi mata skirt dogo da dankwali. Rigar kuwa yadinta duka zanen filawoyi ne manya pink da light light purple kamar skirt din. Tsayinta ya wuce gwiwa da kadan anyi mata dogon hannu mai dan fadi daga kasansa. Kadan akayi mata shape don kada ta kama jiki ba wani ado a jikinta sai maballai guda hudu na wuya amma tayi kyau musamman a jikin Radhiya. Wani juyi ta rinka yi tana jindadi su Zahra na zuga ta har Zainab ta shigo tace suyi sauri wanda basu ci abinci ba su je su ci nan da awa daya ko kasa da haka su Mami zasu iso. Duka su ukun su ka fita aka barsu su kadai.


Hoda, kwalli da janbaki pink mara duhu ta shafawa Radhiya a fuska bayan tayi mata lining da jagira pink mai duhu a leben. Simple make up ne amma fuskarta tayi kyau. Cikas din kawai kanta ne. Zainab ta daura mata dankwalin da kanta ya danyi tudu daga keya sannan ta mika mata hijab mai kyau da kananun duwatsu a kasansa pink irin kayan. Iyakarsa ya sauko kirjinta da kadan. Radhiya harda hajijiya a gaban mudubi.


"Mama nayi kyau ko?"


Murmushi tayi ta yaba sosai da 'yar tasu "kinyi kyau amma don Allah bana son baragada kinji ko. Wannan hayaniyar da saurin fushi ko fada ki ajiyesu. So nake naga kina taku daidai yadda babu wanda zai raina min ke"


"Idan nayi sanyi da yawa bazan kai labari ba a makarantar sojoji Mama. Anfi son mu da dakiya da fada saboda gudun raini"


"Allah nagode Maka. Har yanzu kina jiran zuwa sojan ne bayan miji zan samo miki"

 

Da murnarta tace "Likita?" 


"Idan ba likita bane ba fa?"


"Gaskiya Mama ki barshi kawai. Idan ba likita ba sai dai ko soja irina. Sauran duk na rainasu, kada ayi auren su rinka kawo karata kullum"


Hannuwa Zainab ta tafa tana dariya, yanzu ta gama cewa ta dena shirme gashi ta hade fuska tana buga kayanta a ganinta kuma ba laifi bane.


"Jeki kici abinci kada azo ana jiranki"


Kallon kanta ta sake yi yadda tayi kyau abinci zai iya goge mats jambakin ta dawo tayi zamanta akan gado "bana jin yunwa"


"Ashe kuwa za'a tafi a barki" Zainab tace tana yin gaba.

 

Ba don taso ba ta tashi itama. Tana saka kafa a falon ta tuna abinda Awwab yayi mata sai ta juya suka kusa karo da Zainab.


"Wuce muje kici abinci" ta umarceta.


Gani tayi babu alamun Awwab din sai ta saki ranta ta fara gaishe da Hadir da yake kallon labarai sannan ta tafi gaban dinning table inda kayan tea suke za ta hada taji Zainab tana tambayar ko Awwab ya shirya.


"Da kyar idan ma ya tashi Mama, shi fa idan yana gida yafi zaman daki yayi bacci saboda yanayin aikinsa" Zahra ta bata amsa.


Radhiya ta saki murmushi "kice kamar dai mu sojoji ashe nasa aikin shima baya samun isasshen hutu". Suna mata dariya za ta fara abin nata ta mayar da hankali ga abinda take yi. Madara da milo ta zuba a cup din nata ta mika hannu za ta dauki sugar Awwab ya bude kofar dakin ya fito. Wani hadadden kamshi ke tasowa tun kafin ya iso tsakiyar falon. Yayi kyau cikin wani lallausan yadi ruwan madara. Rabonsa da manyan kaya ya kwana biyu sai jiya da Daddy ya bashi su guda biyu dinkakku da zai taho. Su Zainab ya fara gaisarwa sannan ya amsa gaisuwar kannensa da Radhiya da jikinta yayi sanyi saboda kada a sake irin ta jiya.


Tana tsaye ta kasa karasa abinda take yi balle ta ja kujera ta zauna. Jiya ke mata yawo a ka yadda ya bata abinci a baki kamar wata baby. Runtse idanu tayi tana son kawar da tunanin daga zuciyarta taji ya janye kofin daga hannunta.


"Kawo na karasa hadawa naga ba kya sauri"


Sakar masa tayi da sauri ya ture robar sugar din ya kara mata madara da milo ya fara zuba ruwan zafi.


"Hamma ya isa haka" tace da ta ga ya wuce rabi.


Bai saurareta ba sai da ya cika kofin ya ja kujerar gefenta ya zauna. Kujerar kusa dashi ya tura mata baya da kafarsa ta zauna tana waigen baya. Babu mai kallonsu Zainab da Hadir labarai suke gani a tashar Channels. Zahra da Fauziyya suna hirar angwayensu dake korafin sun makale a Kano. Zayyana kuwa ta tafi dafa indomie.


Wani irin kallo yayi mata sau daya ya dauke kansa, tayi masa kyau sosai har yana tsoron kada kallon da yake mata ya wuce gona da iri "namu ne mu biyu"


Turo baki tayi "Habaaa Hamma don Allah yunwa nake ji"


"Okay fara sha ki bani" yace yana tura mata kofin.


"Ni a'a, ka shanye na hada wani"


Lumshe idanu yayi yana mata murmushi "wannan zamu sha, jiya dama ance abincin da na rage miki dawo dashi kikayi. Ko muyi kama-kama da shima baki bari munyi ba"


"Na shiga uku" ta furta a hankali tana cike da kunya ta tura kujerarta baya za ta tashi ya bata rai.


"Ki dena tashi idan muna magana bana so"


Zama tayi tana ta zumbura masa baki ya sha rabin tea din ya mika mata ta karba ta bishi da harara.


"Baka saka suga ba ni kuma dashi nake sha" ta mika hannu zata dauko robar ya riga ta daukewa.


"Da zaki a haka, try it."


Samun kanta tayi da bin umarninsa ta sha tea din shi kuma ya tashi ya koma daki bai taba doyar da aka soya da kwai ba. Tana nan zaune ya dawo da ledoji masu kyau a hannunsa da tambarin wani babban kamfani a kasar Germany. Su Zainab ya fara mikawa ta karba da murmushi ta bude. Turaruka ne na alfarma na mace da na namiji ita da Babansu Hadir da agogo set shima na mace da namiji.


"Harda dorawa kanka wahala Awwab?"


"Ku sa mana albarka kawai Mama"


"To Allah Ya saka da alkhairi Yasa kafi haka. Allah Ya baku masu yi muku a nan gaba"


"Amin" kowa ya amsa harda Radhiya.


Leda ta biyu ya mika mata "na Ibrahim da Emzee, suna ina ne ma?"


"Leka ta window wankin mota ake mana"


Komawa yayi dinning table din ya zauna a inda ya tashi Radhiya ta kafe shi da ido.


"Ya?" Yace yana gimtse dariya don ya kula ta fara cika tana jiran nata.


"Ina nawa?"


"Me din?"


Kai tsaye tace "Abin cikin ledar" 


"Kina harar tawa zan baki abin cikin leda? Wanda na siyo da sunanki ma zan je in kaiwa Ummi tayi sadaka dasu"


Kallon shirts da agoguna da Zainab ke fitarwa da sunan Emzee da Ibrahim yasa ta sake hade rai harda kwalla. Ita da tafi kowa cika baki akan Hamma Awwab amma ita ce ko tsinke bai bata ba. Abincin ma fushi tayi dashi ta ture. Sai yaji ta dan bashi tausayi ya gama dariyar abinda yake shirin kulla mata kawai don ya tsokaneta ya matso da kansa yana mata magana a hankali.


"Kin yarda daga yanzu ko me zamu ci zamu ragewa juna har na koma?" yayi dan murmushin rigimarsa da Mami a baya "da ko me naci sai na rage miki Mami tayi ta fada wai ba komai zaki iya ci ba. Ni kuma tana barin wurin sai na tura miki a baki ko yaya ne ki cinye"


Murmushin da tayi masa jinsa yayi har ransa saboda yadda take lumshe idanu batare da tayi la'akari da tasirin hakan gareshi ba "to ai kaine baka yi min bayani ba kawai kasa ni jin kunya jiya."


"Silly girl me akayi na jin kunyar? Kinsan me kike yi min kuwa da?"


Radhiya ta girgiza kai.


Yafito ta yayi da hannu ta sake duku kanta tana shakar daddadan kamshinsa "abin bakina kike cirewa ki saka a naki idan na hanaki"


Hannuwanta ta saka a gefe da gefen kumatunta ta bude baki da idanu duka a lokaci daya. Tana ta jiran Hamma Awwab ya dawo gashi ya dawo ya hadata da jin kunyar da bata taba sanin tana da ita ba. Abin bakinsa fa yace! Yanzu tana tashi kuma zai ce ta zauna ko yayi maganar yadda kowa sai yaji. Gara kawai tayi kamar bata ji komai ba ta bawa kanta shawara. Daurewa tayi kamar bata ji nauyin maganar ba tace


"Yanzu dai kasan bazan ci abin baki ba"


"Sure?" Yace yana mata kallon gefen ido.


"Na fa girma"


"If you say so" ya rausaya kansa sai kuma ya tashi tsaye "kinsan me? sai na sa kin karbi abin bakina kafin na koma Katsina"


"Idan naki fa?"


"Ki tambayeni duk abinda kike so. Amma nima idan nayi winning zan tambayeki"


"Ka shirya bani tsarabata kawai" tace tana dariya ta tashi tayi waje da sauri. Sai da ta rufe kofar falon ta dafe kirjinta da yake bugu kamar zai ballo. Kofar ta kalla ta jingina da bango tana girgiza kai

"Abin baki? Hmmuhmm, kai lallai ma Hamma Awwab dinnan idan ba bazan karba ba" kunya ta ji kamar me amma ta daure sosai tana bashi amsa saboda kada ya gane zancen na shigarta tana bashi wata ma'anar daban.


Emzee yana kallonta shi ya gama wanke motar Mamansu Zainab har ya fara taya Ibrahim da yake wankin bus din da zasu tafi Sumaila a ciki. Dauraye hannuwansa yayi Ibrahim ya bata baya bai hangota ba ya karasa gabanta.


"Ke da wa Adda?"


Dantsen hannunsa ta riko tana dariyar jindadi "Emzee yau na koyi basarwa"


Yasan Addarsa da shirirta "na tayaki murna, wa kika basar?"


"Hamma Awwab mana, wai kasan me yace min kuwa?"


Yatsunsa na nuni ya sanya a kunnuwansa ya toshesu "bana son ji don Allah"


Shan kunu tayi tana harararsa "me yasa?"


"Rike kayanki, hirarku ce" ya bata amsa yana komawa wurin Ibrahim. Haka kawai jikinsa ya bashi wani abin jin kunyar Awwab yayi don abinda zai korota waje ita kadai ba karami bane. Shi kuwa bai tashi jin ko ma meye ba a saka shi jin kunyar da za ta jima bata barshi ba su kuma su cigaba da harkokinsu.


**********
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Shadaya da rabi mutanen Katsina suka iso. Radhiya sai murna ta ga Umminta ta kara kyau. Mairama hadaddiyar mace ce da rayuwa ta yiwa cikas. Kwanakin da tayi a Katsina da kulawar Mami yasa jikinta ya kara kyau kamar ba ita ba. 


Zahra da Fauziyya na ganin Ghazalatu suka sa ihun murna don basu san da ita za'a zo ba. Mami tace bata san lokacin da zasu girma ba irin wannan tsalle da suke yi. Ita Ghazalatu hankalinta yana kan Radhiya dake zaune a gefen Umminta ana mata tsiyar Ummin na tureta bata ma san tana yi ba. Gaisawa suka yi aka dan taba hira Mami tace gara su zo su dau hanya saboda a ranar suke son dawowa.


"Ku tsaya kuci abinci an gama tun dazu"


Mami tace "muci abinci muji bacci kenan, ni kin sanni da na koshi sai na fara neman wurin kwanciya"


"Shiyasa nake jin alamun kinyi ukun yadda na sanki ashe" Mairama tace tana murmushi.


Yaran dariya suke yi Zainab tace lokaci ne ai, shekarunsu na soma ja zasu fara ajiye kiba ko da ta girma ce.


"Mama banda ni a kibar, mu sojoji ina muka ga lokacin yin kiba muna faman guje-guje a daji"


Sai da kowa ya dara Fauziyya ta tabo Ghazalatu "kinga kanwar Hamma ko, Radhiya ake ce mata. Yini daya kika yi da ita sai cikinki ya kusa ciwo don dariya"


"Na ganta". Gabadaya ranta babu dadi tun da ta ga wacece Alheran din da Awwab yake ta rawar kafa a kai. Tayi zaton wata 'yar yarinya zata gani da bata fi Zayyana ko kasa da haka ba. Dama jiya saboda wannan budurwar mai idanu a tsatstsaye ya taho Kano ya barta.


Shigowar Awwab da Abdallah wanda ya kawo su Mami dan Hussainarta daga waje kenan daidai lokacin da Mamin take ce mata.


"Idan ke soja ce bakiyi kibar ba mijinki da ba soja ba zaiyi ne"


Tsuke baki tayi tana kada yatsa "No, no, no, no , no Mami. Ni likita zan aura fa. Kinsan shima aikinsu babu zama bazaiyi kibar ba"


"Mara kunya" Mairama tace tana daka mata duka a baya. Su Ibrahim an sami abinda ake so suna ta dariya. Zainab ta maimaita musu abinda Radhiyan tace dazu wai ta raina kowa idan ba soja da likita ba.


"Mama mu dasu aikin ceton rai muke yi shiyasa kowa bai kai mu ba"


Mairama sarkin kunya sai ta soma tsoron kada Radhiyan ta fadi wani abin da yafi wannan. Ta tuna ranar da tace mata tana abu kamar ba bafillatana ba. Ita kuwa ta ce dama ba ita bace, su Sakkwatawa ne.


"Ku barni da ita kwanannan zanyi mata miji a aurar da ita mu huta" inji Zainab.


Tun shigowarsu Awwab yake kallon yadda take ta zuba surutu. Dauke kansa yayi ya kalli Ghazalatu ya sakar mata murmushi ta maida masa.


Ibrahim ne yace "Mama ki samo mata malamin makaranta kawai"


"Tabdi, yo ni malamin makaranta ba sai dai na zane shi da dorinarsa ba. Tsorona zai rinka ji"


Fauziyya da ta saka musu ido ita da Awwab tun jiya kuma take fatan hakan tace "ina jin zaki fi dacewa da dreban jirgin sama"


Mami da Zainab har Mairama sai su ka yi murmushi. Ko dai Fauziyyan ta ga wata alama ne take hasashen abinda suke shiryawa. Awwab da yake shan ruwa cire kofin yayi yana son jin amsarta. Abinka da 'Yar soja ta hade rai "ke kadai ce bakya sona Adda Fauziyya. Me zanyi da dreba sai kace ta kare min?"


Kowa yayi shiru yana kallon Awwab da ya zuba mata idanu harda Ghazalatu da misalin na Fauziyya ya kona mata rai. Bata san suna yi ba bare ta gyara zancen.


Zahra ce ta tace "mun ganku a rana ke da Hamma Awwab tunda shima dreban jirgin ne"


Ba arziki Radhiya ta tashi yana tsaye ya harde hannuwansa a kirji. Tayi zaton zaiyi fushi sai ta ga shi ya fara dariya kafin sauran "wato mu sai ta karewa mace za ta auremu ko"


"Wayo Adda Fauziyya tayi min ba haka nake nufi ba. Maimakon tace pilot yadda zan fahimta"


"Sannu Queen Elizabeth wato sai anyi turanci zaki fahimta" Ibrahim yace.


"Ka kiyayeni Surbajo" A dolensa yayi shiru da yaji abin zai dawo kansa.


Tsokanarta suka cigaba da yi tana karewa kanta. Awwab yana kallon Ghazalatu yace da Radhiya "ki shirya zata kare miki kwanannan kuwa don sai kin auri pilot. Kafin nan kuma ki zamarwa matata 'yar aiki"


Mama da Zainab suka kalli juna suna gyada kai da murmushi. Bakin mota suka firfito Mami da Ummi zasu bi karamar motar sauran kowa yace bus din da Awwab zai tuka zasu shiga. Radhiya da jikinta yayi sanyi tana jin babu dadi akan maganar da tayi tace ita ma motarsu zata shiga sai ta zauna a gaba.


"Koma cikin 'yan uwanki Radhiya" Zainab tace tana turata bakin daya motar. 


Awwab ta kalla ko zaiyi magana sai ta kula hirarsa kawai yake yi da Ghazalatu. Juyowa yayi ya kalli Radhiya duk ta zama wata salihar karfi da yaji "ina zuwa" ya cewa Ghazalatu ya taho inda take tsaye a jikin motar.


"Zo in nuna miki wani abu"


"Wai ba fushi kayi da abinda nace ba kake yi min magana"


Murmushi yayi "Silly girl, kawai sai nayi fushi bayan nasan ta kusa kare miki kwanannan...auren dreba ba fashi"


"Shine ka barni inata damuwa, kuma a gaba zan zauna inyi ta ganinka tunda yau zaku dawo"


Wurin wata katuwar fulawa inda Ghazalatu ke tsaye suka nufa. Suna jiran iyayensu su gama maganar da suke yi su dau hanya ne shiyasa basu tafi ba.


"Dama babu mai zama wurinki ne nima inyi ta kallonki"


Dariya tayi fuskar Ghazalatu ta hade tsaf da kishi. Awwab yasan me yake bata mata rai don yanzu ta gama fada masa ita bata son yadda yake yiwa Alheran dinnan bayan ba karamar yarinya bace. Domin ya kwantar mata da hankali yaje ya kira ta.


"My G, ga Alheran kanwata. Alheran ga Ghazalatu kanwata kuma matar da zan aura"


Sai yanzu hankalin Ghazalatu ya kwanta sosai. Ta kurawa Radhiya ido sai ta ga yarinyar ko a jikinta sai ma dariyar ta take yi fuskarta ta tana wani annuri.


Dage girrarta duka biyun ta rinka yi yadda ta saba idan zata yi tsokana 

" Eyye eyye Hamma shine kace zanyi aiki a gidanka? Naji zan rinka tayata indai itace matar"


"Bana bukatar house girl so kiyi zamanki" Ghazalatu tace tana shan kamshi.


Fuskar Awwab kadai zaka kalla kasan kalaman basuyi masa ba.


"House girl?" Yace yana kankance idanu.


Ta fuskanci ransa ne ya baci sai ta wayance "naji kace za tayi min aiki ne dazu"


"Lallai wannan 'yar wulakanci ce" Radhiya tace a ranta. Ita bata san maganar wasa bane da zata yi tunanin da gaske aiki zata je yi mata. Hamma Awwab yafi karfin komai a wurinta tunda yake son Umminta da babanta da ita kanta. Kuma ba wani abu bane a wurinta ta taya matarsa aiki amma wallahi ba dai taje a house girl ba. Idan bata gwaba mata magana ko yaya bane tasan bazata ji dadi ba shiyasa ta ajiye katon murmushi a fuskarta tace "ko babu albashi zanyi miki aikin ma, kinsan mu 'yan kauye bamu san komai ba sai bautawa 'yan birni"


"No ki barshi fa bana bukata, idan ina so Yayana zai nemo min"


" Yes dai inzo inyi ko babu komai zan hutar da Hammana barnar kudi"


Hannuwansa ya zuba a aljihu yana kallon ikon Allah. Rigima ke neman tashi tsakaninsu daga su gaisa.


Daure fuska yayi yace "ku wuce ku shiga mu tafi"


Suna zuwa bakin motar Ibrahim zai bude gaba ya shiga saboda yana son Awwab ya koya masa tuki Ghazalatu ta riga shi budewa itama tana son zama kusa da masoyinta. Radhiya da ta fisu iyawa tayi sauri ta shige ta kofar bayan ta haura gaba. Awwab kansa sai ganinta yayi ta kusa fado masa garin sauri. Gyara zamanta tayi ta ballawa Ghazalatu da Ibrahim harara suna tsaye suna kallon abinda tayi.


"Ni dama ga wurina can kusa da Zeezee" Ibrahim yace yana shiga bayan inda Emzee ke yi masa dariya.


Ghazalatu ta kalli Awwab tana jira yayi magana "kace ta koma baya ina son muyi magana"


"Idan muna dawowa sai ki zauna a nan din kinji."


Tsabar bakinciki ji tayi kamar tasa ihu. Mami daga cikin tasu motar tace ta shiga su tafi rana tana kara yi. Hararar Radhiya tayi ita kuma tayi mata gwalo.


"Bansan mutum nayi ba sai naji a jikina"


"Alheran" taji yace muryarsa a dake sannan ya kalli Ghazalatu da take ta cika tana batsewa "ki shiga ki zauna mu tafi"


Daurewar da yayi yasa ta shige ba don ta hakura ba. Radhiya da take kusa dashi kuwa ji tayi kamar ta koma baya ita ma. Tukinsa kawai yake yi wanda baya masa dadi saboda bin bayan Abdallah da dole sai yayi tunda bai san hanya ba.


Motar duk sai tayi musu shiru mai bakin tsoro ya hanata magana Zayyana har ta soma gyangyadi a jikin Zahra. Su basu ma san me yake faruwa ba sai Ibrahim da yake tunanin saboda zaman gaba ne kawai.


Can dai taji shirun ya isheta ta dago a hankali ta saci kallonsa. Titi dai yake kallo har yanzu babu wannan sakin fuskar.


"Hamma" Radhiya ta kira sunansa a tausashe.


"Kar ki dameni please"


Shiru tayi ran sojoji ya baci. Ita kadai zaiyi fushi da ita bai ji masoyiyar tasa tana kiranta housegirl ba. Tura baki tayi ta juya duk jikinta tana kallon waje. Shima satar kallonta yayi yayi gajeren murmushi. Da gaske dai Alheran dinsa bata chanja ba sai ma abinda yayi gaba. Su mata abin rigima baya yi musu kadan ya kula. Su biyun kowa matsayinta daban to me ya kawo rigimar. Ko don Ghazalatu tace mata house girl? Shima kalmar bata yi masa dadi ba. Duka su biyun sai yayi aikin basu hakuri kenan. Haka kawai zasu tayar masa da hankali kamar wasu kishiyoyi. Ta mudubi ya hango Ghazalatu ita ma fuska babu wakwala kamar ma kuka take shirin yi. A take ya jinjinawa masu mata biyu.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Sun isa Sumaila karfe biyu na rana a gajiye saboda tashin wuri da suka yi. Emzee ne ya koma jagora da suka shigo garin shiyasa tasu motar take gaba. Awwab ba tsayawa Emzee din ya fita da sauri saboda magana da yake son yi wa Ummin tasu. Gefe ya ja ta ana kokarin fitowa da kayan da ita kanta bata san da zamansu ba a boot.


"Ummi wai kuwa sun san zamu zo da baki?" Yace yana rage murya.


"Na fadawa Innawuro da ta kira nace ta sanar dasu tunda kaga ba waya gareni ba. Menene?"


Da damuwa a fuskarsa yace "kada muje a rasa abinda za'a basu nasan bazaki ji dadi ba"


Murmushi Mairama tayi. Zayyan dinta akwai hankali da nutsuwa ga zurfin tunani. Rashin abin tarbar baki tabbas zai iya faruwa don tasan halin gidan nasu "to yanzu me ya kamata ayi?"


"Idan kina da kudi kawo naje na siyo gurasa da tsire kawai"


Karamar jakarta ta mika masa. Dubu uku ya cire cikin kudin da Ardo ya bata ne da zasu taho. Ya tafi tana ta masa addu'a a zuciyarta.


Radhiya kuma ta kama kofa za ta bude Awwab ya danna central lock. A zuciye ta juyo "bude min"


"Ko nima balotellin zaki yi min ne? Zai fi miki sauki akan wannan juya idanun" bayansa ya juya "Ghazalatu zauna magana zamuyi"


Murtuke fuska tayi itama ya kallesu ya tabe baki. Mata, mata halinku sai ku.


Su Zayyana duk sun fita sun bi bayan iyayensu cikin gidan. Basu san me yasa ya tsayar da su Radhiya ba amma ko ma meye tabbas basu ga alamun wasa a tare da yayan nasu ba.


"Kun gama fushin ko har yanzu da saura?"


Ghazalatu dama jira take yi "don na biyoka shine zaka wulakantani akan wannan yarinyar kamar wata kishiyata? Tunda muka zo sai kayi mata magana sau uku baka yi min daya ba. Sannan nazo shiga gaba ta shige duka ka kyaleta. Idan wani abu ne tsakaninku gara ka fada min da wuri na san matsayina. Amma bazai yiwu ta rinka jin kanta kamar wata a wurinka ba tana neman shiga tsakaninmu"


"Kin gama? To bari kiji in fada miki. Alheran wata ce a wurina Ghazalatu kuma bazan yarda kici mata mutumci ba. She is my sister kamar yadda na dauki su Zahra haka ita ma na dauketa. Idan ma kishi zakiyi ba da ita zakiyi ba. Ki bari sai kin hadu da wadda take da matsayi irin naki a wurina"


Dazu gani take wannan Ghazalatun take ko wa tayi mata rashin mutumci amma maganar Awwab ta yanzu tafi kona mata rai akan komai duk da cewa gaskiya ce ya fada. Ita din kanwa take a wurinsa amma meyasa kalaman nasa suka yi mata zafi haka. 

Daga haduwa dashi kwana daya kawai take neman matsayi fiye da abinda zai iya bata. To me ma take nema ta tambayi zuciyarta. Ranta taji ya cunkushe gabadaya taji ta tsani zaman da take yi tare dasu a motar. Dago kai tayi kamar ba ita bace zuciyarta take kai kawo a abinda ta kasa gane zahirinsa ta kalli Ghazalatu.


"Matar Hamma kiyi hakuri don Allah. Haushi naji da kika kirani house girl. Ke da kishiya sai dai mota in sha Allahu"


Awwab kallonta yayi yadda ta nutsu tana magana kamar ba ita ba. Suka hada ido tayi masa wani murmushi da ya tsaya masa a rai yaji kamar ya dora hannunsa a kumatunta da ya lotsa.


"Kaima kayi hakuri bazan kara ba"


Tana kaiwa nan ta kama kofar zata bude sai ya cire lock din ta fita tare da duka tunaninsa kamar ta zare masa duk wani kuzari da yake jikinsa. A katon soron gidan ta ya da zango jikin wani dan tudun siminti da akayi domin zama. Abinda ya bata mamaki bai wuce kukan da ta fashe dashi sosai ba. Ji take idan bata yi ba ma zuciyarta zata iya bugawa. Kukan na meye? Oho, itama bata sani ba. Abu daya ne kawai ya tsaya mata a rai kalmomin Hammanta na karshe wai Ghazalatu ta jira sai ta hadu da mai matsayi irin nata a wurinsa sannan tayi kishi. Tsaki taja tana jan hanci "Mtswwww in kun ga dama ku cinye juna karewarta, aikin banza. Dadinta dai nima Kawu Zakari ina komawa zai ce yana sona. Mu za'a yiwa burga da wata soyayya? Maza na fita filin yaki ko su je ceton rai a asibiti kai ka makale a jirgin sama kamar tsuntsu wa zai so ka idan ba wannan mai kwalakwalan idanun

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment