Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ta zuba masa a plate ta mika masa.

"Gashi inji Adda Radhiya"


Karba yayi tun kafin ya fara ci cikinsa yana dada rarakewa da yunwa. Yanzu kam a hankali ya rinka ci sai abincin yayi masa dadi sosai. Yana gamawa ya kira wayarta kuwa.


"Hammana ya jikin?" Yaji muryarta ta shige shi a nutse 'yan salihancin na kusa.


"Better. Nag...."


"Hey! Ka manta babu godiya ne" tayi saurin dakatar dashi.


A kasalance yace "To me zance na nuna miki naji dadi?" 


"Babu komai ni dai kawai ka warke"


"Love you Schatzi"


"Me too Hammana" ta kashe wayar da sauri kamar yana gabanta. Kalmar nauyi take yi mata bata jin zata iya fada.


Daga masallaci Excellency ya wuce Chibuzor yana mota tare da wani dreba su ka yi ta masa godiya. Su Major ma suka ce to yanzu dai zasu bar Zayyan ya huta ya wuce ciki.


"Ango" yaji Baba Hadir yace da sigar tsokana a kokarinsa na magana.


"Malam ka bude baki kayi tsokanar da gaske naji. Ba kyaleka zanyi ba sai naji ina fada kana fada"


"Kaga wuce wurin matarka. Idan kaso ma magrib da isha kayi naka jam'in da ita" Major yace yana nuna masa kofa. Shi da Baba Hadir kowa ya tafi nasa gidan.


Shima sai ya tafi yana murmushi. Daga falo ya soma jin wani irin kamshi mai shiga rai da bai taba sani ko jin makamancinsa ba. Turaren wuta ne dan gaske irin wanda su Mammee suke aiko mata dashi ta saka a ko ina. Kofar da ya ga ta shiga lokacin da take kuka ya bude. Nan ya sameta akan abin sallah tana addu'a ya zauna a kasa gefenta ta kammala sannan ya tashi tsaye.


"Yanzu me zanyi?"


 "Ka kwanta ko baka yi bacci ba nasan jikinka yana bukatar kwanciyar"


Da yake yamma ce sanyin da aka fara ya karu sosai shiyasa ta kashe AC sai fanka kawai. Kayan jikinsa ta kalla tasan bazai ji dadin kwanciya dasu ba. Kamar yasan me take tunani ya cire rigar ya ajiye akan kujera daya dake dakin. Da farko kunya taji sai dai tana ganin yadda ya koma bata san lokacin da wani irin kuka yazo mata ba.


"Sojana kaine haka?" Ta bi wuyansa da kirji tana shafawa. Ya masifar ramewa fiye da yadda take tsammani dazu da yake cikin riga.


Rigar yayi saurin dauka "bari na rufe kasusuwan nan kada su firgita min mata" sai ya ga ta kama rigar ta mayar ta ajiye ta rungume shi tana jin wani iri a zuciyarta. Wace irin rayuwa Zayyan yayi ne. Ta sani har abada idan ba samun kanta tayi a irin wannan yanayin ba to bata isa ta fahimci ainihin radadin da yake ji a ransa yake ta kokarin dannewa da fara'ar dole ba. Sojoji nawa ne a irin rayuwar sun rabu da iyalansu babu ranar sake haduwa. Nawa ne matan suka sake aure suka sake sabuwar rayuwa ashe mazan nasu suna da rai. Yanzu da tayi aure fa? Da Allah Ya jarabceta da son waninsa fa kuma ya dawo full of hope na ganin iyalinsa. Shikenan duk wannan farincikin sai ya koma ciki ya dawo matarsa ta zama ta wani kila ma da zuri'a a tsakani. Wayyo bayin Allah. Allah Sarki sojojin kasata.


Kuka mai tsanani ta sake fashewa dashi yana shafa mata baya ta dago kanta a hankali "yanzu da nayi aure fa Zayyan? Da shikenan ni da kai..."


Bai barta ta karasa maganar ba domin kuwa shima wannan tunani yana damunsa kuma Ya san wata kyauta ce kawai daga Allah da yanzu labari ya sha bamban. A take ya soma nuna mata wata irin zazzafar kauna mai tsayawa a rai, ruhi da gangar jiki. Soyayya bata tsufa sai dai ma'abotanta su tsufa. A wannan rana abinda suka kwana suna tunawa junansu kenan.


**********


WATAN DA YA GABATA



Malamijo ne ya coge a jikin bango yana ta kamshin turare dan d'uri. Sanye yake da manyan kaya babbar rigar nan kamar a nade shi dukkansa a ciki. Ga jar dara wasu bangarorin sun dan cinye ta koke. To amma dai ita ce ta fi dama dama cikin hulunan nasa. Kafarsa kuwa cover shoe ne na maza mai dan tudu ta kasa da tsukakken baki ya coko gaba.


Wata mata ce ta fito ta kofar gidan da yake tsaye a gefe taci kwalliya foundation tayi kuka. Kallo daya kacal zaka gane irin matan nan ne da ake kira da masu kirar coca cola. Murmushi ta saki da ta ganshi shima ya maida mata jikinsa har rawa yake ya ga mace irin wadda yake so. Amintaccen yaronsa Talle da yake taya shi nemo 'yan mata ne ya tallata masa 'yar makotansu sakin wawa kyakkyawar mace son kowa kin wanda ya rasa. 


Sai gashi kwalliya ta biya kudin sabulu. Matar tayi ta ko ina ga ta gwanar kwarkwasa bata sha wahalar tafiya da imanin Malamijo ba. Da zai tafi kyautar dubu biyar yayi mata a ziyara ta farko. Yana zuwa gida dakinsa ya fada hankali a tashe. Ga mace har mace fa ya samo amma babu guri a gidansa, mata hudu ne a gidan. To yanzu wa zai sallama?


Yadikko dai yana da yakinin duk ranar da ya sallameta 'ya'yansa kaf sai sun masa rashin mutumci irin wanda bai taba tunani ba. Banda Mairama da ta dage yanzu wurin ganin ta hada kan kannen nata babu wata shakuwa a tsakaninsu. Akwai nutsatsu akwai fitinannu duka ya tara amma tarayyarsu daya shine girmama Yadikko da Hajjo da itama tayi nisan kwana a gidan. Atine tsohon ciki gareta, Na'e kuma ko wata uku bata cika ba. Idan ya saketa yanzu ya cuci kansa tunda bai gama more kudin da ya kashe mata na aure ba. Ranar Malamijo kasa baccin kirki yayi tunani ya addabe shi.


Bayan kwana biyu Atine ta sauka aka sami 'yan biyu mata. Da murna Hajjo ta tare shi da wannan zance ya hade rai.


"Don bala'i tun ana daidai din kuma yanzu abin ya koma bibbiyu? Wai ni bazaku barni na sha iska bane? Mata kowa tazo bata da aiki sai haihuwa. Mtswww"


Hajjo tasan halin mijin nasu sarai kuma dayake da ita aka je asibitin ta ga irin wahalar da Atinen ta sha sosai.


"Idan ka gama tsakin sai ka kawo kudin da za'a siyo abubuwan karin jini ayi mata girki mai kyau. Kuma dai wannan karon a daure a bamu na yin kauri. Yarinyar nan taji jiki"


Abin da bai taka kara ya karya ba dama neman rigimar yake ido rufe da daya daga cikin matansa don sosai Hajiyayye ta gama tafiya da imaninsa da wani salon soyayya da take gwada masa. Ji yake kamar bai taba aure ba.


Ya karkace kai ya kankance idanu "Rashin kunya zaki yi min Hajjo? To sai ki kwata tunda da uban mutum muka tara ki yiwa kishiya girkin bikin jiki"


Ranta ya sosu da zagin da yayi mata "Nagode madallah sai dai ka sani uban nawa da bai ajiye ko dan marakin sa ba duniya bata yi masa shaidar auri saki ba."


"Wuyan wata yayi kauri. To sai ki tattara ki koma gidan wanda baya auri saki. Ali mai auri saki kema yayi miki saki daya"


Da farko kunnenta har nema yayi ya toshe saboda abu ne da ta sakankance bazai taba faruwa ba. Shiyasa ma ta saki jiki ma ta saki jiki kuma ta dauki salon Yadikko na ganin sun rungumi duka yaran da babu uwayensu musamman masu kananun shekaru. Barta da fada da rashin barin ta kwana amma duka matan Malamijo bai taba auren wadda take sonsa soyayya ta gaske ba zaman hakuri ba irin na Yadikko kamarta ba. Kuntata musu da yake yi yasa da wahala soyayyar ta fito ana kokarin ci a koshi.


"Me kace Malamijo?" Ta fada a razane.


Shima kuma sai jikinsa ya dan so rissina "nace a tattara a tafi na sauwake miki. Idan akwai nama a gidan tsoho sai kije kuyi ta ci"


Duk wani abu da take tunanin fada masa domin ragewa kanta bakinciki sai ta ga yayi kadan. Zuciyarta tana zafi ta shige dakinta. Mayafi kawai ta dauka ta fita daga gidan batare da ta leka dakin Na'e ba tunda Yadikko ma tana asibiti wurin maijego.


Kafin ta karasa bakin titi sai kuka ya kufce matan. Da kyar take ganin gabanta haka ta tafi gidan iyayenta a cikin gari.


Malamijo kuwa tunda ta fita yaji duk ya shiga damuwa sai dai wayar Hajiyayye a lokacin ta mantar dashi komai sai gashi a washegari ya tura wakilai gidansu. Abin mamaki basu bar gidan ba sai da suka bada sadaki don iyayenta sun ce basu ga dalilin jan lokaci ba.


Yadikko tayi kukan wannan wulakanci da ya yiwa Hajjo taje ta fadawa abokinsa da suka yi hannun riga wato Mal Kallamu. Ko kadan baiji dadi ba amma yasan Malamijo baya jin shawara. Duk da haka yaje gidan basu kwashe da dadi ba kuwa. Abin takaici cikin 'yan matan nam hudu da yayiwa aure lokacin da idanun Ummi suka bude biyu an sakosu. Sauran kuwa zaman wulakanci da kaskanci suke a nasu gidajen. Sun auri mazan da basu san darajarsu ba ko kadan. Kina magana kuma a goranta miki cewa babanki ma yafi haka.


Daga nan dai Malamijo ya shiga gyaran gida amarya zata tare. Yadikko hakurinta ya kare ta kudurta a ranta cewa Atine na yin arba'in zata bar gidan. Yarinya ce karama marainiya. Babu wata mace tsayayyiya da ta gani daga danginta da zasu bata kulawa ita da 'yan biyun nata. Ana sauran kwana biyar ne amarya ta tare Mairama taje kafin ta wuce Abuja. Yadikko sai ta kasa fada mata an saki Hajjo tunda tasan sun shaku daga baya. Kuma ma dai tana gudun ta fada ta hanata nata niyar barin gidan. Ita dinma ba zama take ba tana ta zagayen dangi amma bata leka Salame ba a niyarta sai ta dawo.


Washegarin tafiyarta amarya ta tare. Malamijo ana ta zumudi yayi aski an gyara ko ina. Da kullin kazarsa ya shiga dakin amarya da zummar kiranta zuwa turakarsa sai ya samu bata ciki sai wasu yara dugwi dugwi da yabi ya lissafa su shida cif kwance wasu akan gadon da shi ya biya aka yi mata kayan daki. Wasu kuma an yi musu shimfida a kasa. Juyawa yayi zai fita nemanta yaci karo da wani yaro dan kimanin shekaru sha uku. Bangaje Malamijo yayi ya haye kan doguwar kujerar dakin da babu kowa a kai ya kwanta. 


Abin ya daure masa kai ya tafi dakinsa zai ajiye ledar da hannunsa ya fita neman ba'asi sai ya sami Hajiyayye zaune akan katifarsa da ya sauya saboda zuwan amarya ya saka maigida kar ka taka.


"Sannu da zuwa Angona" tace tana make murya.


"Sannunmu dai" ya daure ya amsa kafin kuma ya soma fada "su waye a dakinki?"


"Dakina kuma? Mtsw anya da mutane a dakin kuwa? Ni dai da zan fito ban bar kowa ba sai yaran namu"


Idanu ya zaro "yaranku ke da wa? Sun kai goma fa inajin"


"Bakwai ne ba yawa. Biyu ne kawai babansu daya. Sauran..."


"Kowa da nasa?" Ya tambaya hankali a tashe.


Murmushi tayi masa tana tasowa gabansa tana rangwada jiki na juyawa.

"Daren yau namu ne ni da kai ka bar batun yara zamuyi maganarsu gobe"


Ledar ta karba ta bude kamshi ya doki hancinta. Kaji ne uku dakwale sun gasu an yanka musu albasa, kabeji da tumatir. Yawunta ya tsinke bata ankara ba ya tsiyayo ta gefen baki akan idanun Malamijo. Haka ya tsaya kamar gunki ta kamo hannunsa ta zaunar dashi jiki na bari zata ci nama. Biyu ta raba naman ta kwashe daya a wata ledar ta ture gefe.


"Wannan yara sa samu su lamusa da safe. Idan ban basu ba gobe bani da zaman lafiya"


Tashi yayi kawai yana tunanin ko bulala zai samo ya tafka mata. Don yana sonta sai a ha'ince shi. Ance sakin wawa baifi a ce tana da yara biyu ba. Kuma don jaraba sai a kawosu su tare a gidan tare. Hannunta da tayi rabon naman tabi ta lashe tas yana neman abin duka bata sani ba ta tashi itama.


"Cin nama irin wannan yafi dadi idan mutum ya rage kayan jikinsa yadda ana gamawa sai a fadawa angwanci ko Malamijo nawa na kaina" ta shiga kifta masa idanu. 


"Zaki ci kwal ubanki ne" yace a zuci ya kama kofar dakin ya fita.


Wurin ajiyar itace yaje ya sami wata sanda ya dauko wata sanda ya dawo ya jingine ta a kofar dakin ya kutsa ciki sai ya hadu da wata dattijuwa a zaune da daurin kirji ta saka ledar naman a tsakanin kafafunta tana ta tauna kashi.


"Ke kuma daga ina" yace yana huci.


"Maigida lafiyarka kuwa?"


Murya dai ta Hajiyayye ce amma wannan ai tafi kama da dattijuwa. Sosai ya shiga kallonta yau babu foundation fuskar ta nuna da kyau. Da gani a kalla tayi arba'in da biyar ko ma fin haka. Kayanta da jibge a kasa ya kalla ya kuma kallonta.


"Ke tashi tsaye" ta kuwa mike tana sunne kai wai ita kunya.


"Ya na ganki a bushe kamar ni? Ina abubuwan jikin naki?"


"Au" ta juya ido "kayan da nake ciko dasu kake nufi? Gasu can. Wai naga bacci zamuyi ne nace bari na cire nasha iska"


"Wai tsaya, kece dai Hajiyayye da muka yi magana yanzun nan kika ce min yaranki bakwai?


"Kai dai ka damu da son sanin yaran nan naka. To zauna muna ci ina fada maka. Su goma sha daya ne amma biyu babansu daya nace ma ko..."


"In kin isa Allah shi tsinan. Kin kuwa san ko ni wanene da zaki cuceni haka? Kalleki fa babu body babu alamar body sai tumulin 'ya'ya. To ki tashi tun muna shaida juna kije ki tashesu ku bar min gidana"


Bata nuna masa ranta ya baci ba tana cin naman da ya soma kasa tace "ka dai yi hakuri mu wayi gari sai su koma gidanmu. Idan na tashesu cikin dare yanzun da wahala suke boye maitarsu. Idan naman kazar bai ishesu ba sai ka ga cikin mutanen gidan nan ana ciwo ya kama wane. Kaga bazan so ba"


Baki na rawa duka makaman yakin nasa suka bace yace "kina nufin wai...wai...wai ku din...kina dai nufin"


"Mayu ba. Nayi zaton ma Kawuna ya fada maka tun lokacin da ka tura wakilanka. Kada ka damu indai zasu ci nama su koshi wallahi babu mai sani a gidan nan. Idan ba haka ba....toh...don shi babban da na taho dashi ma cewa yake wai ya ga cinyoyinka kamar..."


A tsorace ya rike cinyoyin nasa ita kuwa ta ci naman nan duka ta cinye. Tun daga ranar kwanaki shida kenan kullum babban danta wanda ba ma a gidan yake ba zai je gonar Mamamijo ya debo kaji ko zabi kamar biyar su gyare shi da 'yan uwansa a tsakar gidan ayi dabge a ci sauran na gani. Malamijo bala'in tsoronsu yake ji ya kuma kasa fadawa kowa dom yanzu tsorata shi take yi har cikin dare duk da karyar maita tayi. Ya kara ramewa ya tsotse babu mamora a jikin. Hajiyayye banda nama sai tatike shi take da karyar maita yana bata kudi. Su Yadikko nasu ido ne babu mai cewa komai an barshi da sababbin iyalinsa.


**********


Kwana biyu da dawowar Zayyan sun buga soyayya shi da Mairama ko farkon aurensu albarka. Gaishe su kawai yaran ke zuwa yi babu mai zama a bangaren. Su Radhiya ma basa kwana sun koma tsakanin gidan Mama da Mami. A haka ance musu wai su barshi ne ya huta. Yau suke sa ran kiran 'yan uwa a waya a sanar dasu idan ya dawo daga headquarter. Zasu karasa hada duk abinda ya dace ne domin ya zamana komai anyi shi officially.


Awwab yaji sauki kuma nan da kwana biyu yake son komawa ya karasa abinda zaiyi ya dawo kafin hutun ya kare a aura masa Alheran. Raji da Zahra su ma zasu tafi Osun wurin dangin iyayensa. Daga can su je Katsina sannan su koma Germany.


Arifah da mamanta sunzo jiya yau kuma tace akwai fa zuwansu park ita bata hakura ba su shirya zata zo su tafi. A gidan kuwa tayi laasar washegari suna yin sallah suka shirya zasu tafi. Awwab ya dauki Raji a gaban mota sai ,Zayyana da Radhiya a baya. Ibrahim da Emzee a motar Mama sai su Fauziyya a motar Arifah. Wani sabon park ta kaisu na dan wane da wane. Ba tsada bace da shigarsa sai dai masu zuwa da irin abubuwan da ake saidawa kaji pure water guda daya naira ashirin ya sa ba kowa ke iya zuwa ba. Hakan ya kare shi daga zama matattarar 'yan kwaya kowa ka gani yana kokarin nuna shi din ya isa.


Wurin ya kawatu da flawoyi kwantacciyar ciyawa da mutum zai iya zama a kai ko babu shimfidar komai. Ga wani abu kamar korama ruwa yana wucewa da gudu. Akwai manyan bishiyu masu kara masa ni'ima da daddadar inuwa. 


Suna fitowa Emzee da Ibrahim ne suka dauko carpets da za'a shimfida. Raji ya dauko cooler din da aka zuba robobin ruwa da gwangwanayen lemuka cikin kankara. Zayyana da Radhiya kwandunan abinci shi kuma Awwab ya nufi wurin masu gasa nama Arifah ta biyo shi.


"Captain yaushe ne komawar taka?"


"Jibi. Akwai sako ne?"


"Not really.."tace tana dan murmushi. Mayar mata yayi yana jinjina kai.


"Akwai wata a kasa kenan. Haba kanwata kada ki boye min komai"


Radhiya ya gani ta nufosu fuskarta babu walwala. Dama tun a gida ya kula kamar ma bata son fitowar. Shi kuma dama ce yake gani saboda baya samun chance din zama da ita suyi hira. Idan ba'a kirata ba to tana wani aiki. Tayi kyau sosai cikin pakistan da ta saka. Rigar baka da aikin zare pink sai pink din wando mai fadi da pink din mayafin da ta yafa.


"So cute" ya furta a hankali gabadaya hankalinsa ya koma gareta.


"Muna komawa gida zan bada shawarar ayi ayi bikin nan naku kafin a nemi 'yar mutane a rasa" Arifah tace tana dariya.


"Da kin kyauta. Yanzu dai zaki fada min me kike son fada ko we talk some other time? Schatzi akwai kishi yanzu haka sai nayi lallashi"


"Ahhh to bari na gudu kada ta hanani yayanta"


Wurin wasu kujeru da aka baza a karkashin bishiyon Radhiya ta koma ta zauna takaici ya isheta da kishi.


Awwab na jin me Arifah tace ya gama karbae ledojin naman yace "wanne? Emzee fa kaninta ne"


A kunyace tace "ba shi ba...how much do you know about Yousuf? Yana kirana kuma dai nima I like him" 


Da farinciki yace "in sha Allahu baki da matsala kanwata. Maybe maganarki yace yana son muyi"


Amma wannan hadi yayi masa sosai. Tare suka taho inda Radhiya take Arifah ta karbi ledojin don bata da girman kai shi kuma ya zauna a kujerar dake kallonta.


"Schatzi, kishi?"


Tsuke baki tayi taki yi masa magana ya tashi yaje ya dauko musu maltina guda daya ya dawo. Bai ce komai ba ya bude ya sha ya tura mata. Sai da ta dan murguda baki wannan dimple din mai bashi sha'awa ya motsa ta dauka ta sha itama ta tura masa. Haka suka yi har ta kare.


"Zaki kara?" Ta noke kafada. Haushin nata da biyu ne dama. Ga dariyar da yake yiwa Arifah ga tafiyarsa jibi duk ya dagula mata lissafi. Tun bai tafi ba ta soma jin kewarsa. Sati uku yace zaiyi mafi karanci ko yayi wata guda. Duka duka yaushe suka daidaita yake tunanin sake tafiya ya barta.


Yatsa taji ya kada a kusa da fuskarta ta dago daga tunanin da take yi tana kallonsa.


"Indai Arifah kike yiwa wannan fushin ki dena zancen Yousuf muke yi. It seems sun daidaita"


Duk da tana kokarin boyewa ya kula da dadin da hakan yayi mata amma sai ta sake dinke fuska.


"Me kuma nayi? Kinga tafiya ce a gabana bana son wannan fushin"


Kwallah ya gani ta ciko idon ya sosa mata inda yake kaikaiyi.


"Ya Allah" yace ya soma damuwa "Alheran ba kya son na tafi ne?"


Kifa kanta tayi akan teburin gabanta bayan tace eh.


"Kada ki bari hawayen nan ya fito"


"Me yasa?"


"Zaki sani rarrashin da bai kamata nayi ba with a hug and maybe a..."


Dagowa tayi da sauri "na dena don Allah. Sai ta ga yana kallon fuskarta shine ta taba idonta taji danshi "kadan ne ya digo Hammana kuma ba ni na fito dashi ba"


Tasowa yayi daga wurin zamansa yana zagayawa gabanta a hankali "ya na iya tunda ya fito sai na rarrashe ki....come here"


Ba shiri ta mike itama tana ja da bayan "Allah na dena fa...ka tsaya a inda kake"


Bai dakata ba ya cigaba da matsowa "ga wani nan ma yana zuba. Schatzi tana bukatar rarrashi irin wanda ni kadai zanyi mata ko"


Ga kunya tana ji ga zancen yayi mata girma sauri ta kara ta na neman ina sauran suke  "ba hawaye bane ruwa ne"


Idanunsa har wani ciki suka yi yace "kin fara karya ne? Ina kika ga ruwan?"


"Uhmn, uhmm yawu ne kaga" ta tabo idon ta nuna masa.


Cak ya tsaya ya kwabe fuska "ashe baki dena kazanta ba"


Dariya ta koma yi "zaka taka danyen..."


"Stop Alheran, bana son kazantar nan taki"


Ta kuwa cukule tana jindadin yadda ta dawo ita yake gudu "kalli mana ka gani danyen...."


"Schatzi!"


"Oui ma Chérie" ta amsa innocently kamar bata san me take yi masa ba.


"Ko ki bari...."


"Ko kayi me?"


"Kada ki kureni ki ga me zanyi din fa" ya gargadeta da hannu yana dawowa kusa da ita suka soma jerawa suna gangarawa hanyar inda sauran suke.


"To nayi shiru."


"Better. Call me that name again. Dama na gaji da Hamman nan. Su Zayyana su fada kema ki fada babu bambanci"


"Chérie" tace da wata irin siga mai shiga zuci.


"Meaning?"


"Daidai da Schatzi amma french version"


Tsayawa yayi a gabanta ya hanata cigaba da tafiya "idan na dawo bana son ko sati muyi ba'a daura aurenmu ba. So tun yanzu ina fada miki zan sanar da su Baba. Idan kinso ana tambayarki ki sake cewa baki shirya ba"


Dariya ya bata tace masa ko gobe yake so ta shirya. 


"Da kin raina kanki kuwa"


Nutsuwa tayi a ladabce tace "Me yasa? Dukana zaka yi?" 


Sai da tasa shi dariya "Matsoraciya ina kika baro 'Yar Soja nasan da ita ce cewa zata yi bismillah "


" 'Yar Sojan lafiya bayan ta kare min ina nan ina son dreba"


Yana juyowa suka hada ido ta gudu duk kiran da yake mata kunya ta hanata tsayawa. Bata sake bari sun zauna su kadai ba saboda kunyarsa da ta rinka ji. Da ana daukar hotuna kuwa fafur taki yarda ayi musu su biyu.


**********


Rama 'yar asali ba bogi ba Malamijo ya sake yi gabadaya ya sake karewa sai kasusuwa sai kayi zaton mayun gidansa sun fara lasarsa ne. Gidan gonarsa yaje za'ayi lissafin abincin dabbobin da kuma ware wadanda za'a kai Enugu karshen sati.


Yana zuwa babban yaronsa Talle ya soma cewa "Yallabai an fitar da shanun da ka turo a dauka. Gaskiya kayi dabara da kace a rage wasu saboda nan din ya soma matsarsu basa walawa sosai"


A take ya soma zufa duk da sanyin gari "wadanne shanu kenan?"


"Wanda ka turo dan wajen amaryarka mai zuwa daukan kaji ya dauka mana. An bashi ashirin da uku yanzu saboda motocin sunyi kadan zai dawo a cike hamsin din"


Jiri ne kawai ya soma dibar Malamijo saboda tashin hankali jikinsa yana rawa yace "ni ne zan turo a kwashe shanu? Da can a ina suke ban ce a raba ba sai yau?"


"Ba dai karya yayi min ba yaron nan? Kusan awa guda da tafiyarsa"


Kuka Mamamijo yasa bare da ya soma dubawa a gigice ya fahimci manya manyan bijiman sa aka kwashe "da su taba shanun nan ba gara su lasheni ba ita da yaranta"


Talle dai lallashi yake yi Malamijo ya kama hanyar gida fakam fakam yana zubar da hawaye kamar yaro. Daga tarewarta sunci kaji yafi hamsin. Sau biyu ana daukar tumaki duk yayi shiru don tace masa magana na fita ko ita bata cinyeshi ba yaranta zasu ci. Dakinta yaranta ne a ciki ita kuma ta tare a dakinsa sauran matan basu da girki. Sai dai kowacce ta dora abinda ya samu suna kallo ana wadaka da nama kullum. Babur ya tare ya hau don yayi saurin zuwa gida.


Yana zuwa gidan bata dakinsa ya tafi nata. A can yaji tana waya tana kyakyata dariya "Talle baka da kyau. Kasan shawararka ta maita tayi sosai. Tsohon banza yana son ransa da na kada idanu sai kaga yana tsuma. A sayar da shanun nan ko dubu hamsin hamsin ne tunda kace manya ne kowa ya dau rabonsa"


Wani gululun bakinciki ne ya turnuke shi yadda Hajiyayye tayi masa wasa da hankali. Yanzu yana fito da maganar nan magauta sai su sami abin dariya. Ta ina

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment