Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda ka sanni ko?" 


"Kin koma tamkar Innata"


"Bani labarinta"


Emzee sai ya shiga kada kai. Idan abin Addarsa ya motsa fa bata dogon tunani. Yanzu ace daga dawowarsa zai fara bata labari. Ita kuma neman abinda zai zaunar da ita wurinsa take yi kada ta tashi ta dawo ace ya koma inda ya fito.


"Kin yiwa Hamma Awwab godiya ne? Dashi aka je dauko Daada fa naji Mama tana fada"


An tuno mata da Hammanta sai ta tashi tana murmushi "Daada bari naje na dawo kafin nan kaci abincin"


"Sai kun dawo Alheran"


Wani abin ta tuno zata taambayeshi Emzee ya turata waje ta karfi ya rufe kofar.


Ummi tana ajiye tray a gaban Mijinta taji gabanta ya fadi da aka rufe kofar ga kunya kamar wata sabuwar amarya.

Dariya taji Zayyan yayi yana kallon kofar "ina kika samo min wadannan yaran Fillo? Nan fa dabara yayi mata don su bamu wuri"


Sai da tayi murmushi yaji zuciyarsa tana kadawa da tasowar dadaddiyar soyayyarta tace "sakamakon tureni da Tureta yayi ne" ya sake yin dariya.


Ta gama ajiye komai a gabansa zata fara zuba masa tea din domin ya gasa cikinsa ya riko hannunta bai zaunar da ita ko ina ba sai cinyarsa. Kunya matsananciya ta kama ta yayi mata wani irin riko da yaji tana neman tashi.  Rungume tayi ya dora kansa a tsakiyar kirjinta. A hankali taji hawayensa yana jika mata gaban riga. Tallabo shi tayi ta sake rike shi itama nata hawayen yana sauka a kansa da ya cire hularsa.


Sunyi kusan minti biyar a haka sai ajiyar zuciya kawai da take yi. Da taji yana neman dago kansa ne ta sassauta rikon "ga tea ka fara sha sai na zuba maka tuwo"


Bai bata damar tashi ba sai lebbanta da ya shiga zanawa da karamin yatsansa ya soma magana a hankali "ban taba dena sonki ba Mairama, ban manta ki ba da kyautatawarki gareni. Idan kunci yayi min yawa sai na cika zuciyata da ranar da na fara kamaki kin saci mirinda"


Murmushi tayi mai hade da hawaye shi kuwa ya cigaba da abinda yake yi "a duk lokacin da zan ganmu cikin wannan yanayin nasan mafarki ne wanda nake kwadayin cikarsa idan mun hadu a aljannah. Ashe zan sake ganinki matata. Ashe da rabon na sake samun kaina cikin farincikin zama miji a gareki..." hannu yasa yayo kasa da kanta daidai fuskarsa "ban sani ba ko na manta ko zan iya tunawa"


"Me?" Ta tambayeshi gabanta yana lugude wai yau ita ce tare da Zayyan.


"Wannan" ya karasa fada da hade lebenshi da nata. Lumshe idanu kawai suka yi kowannensu hawayen farincikin cikar buri yana saukowa daga idonsa suka sake rungume juna tightly.


**********

Gidan Mami suka tafi saboda Emzee ya hango shigar bakon da suka zo da su Awwab din Mama yasan manyan nasu can suka je. Ilai kuwa sun taru can dinne Excellency ya gabatar musu da Chibuzor wanda ya fada musu sanadin haduwarsu da Zayyan. Wannan ake kira al'ajabi su Major sun koka sun murmusa sun dara duk a lokaci guda. Yayin da matansu suke dakin Mama su ma suna nasu mamakin.


A gidan Mami suma a falo aka baje hirar murna ta kaure sun saka Awwab a gaba sai ya fada musu yaya akayi. 


"I am exhausted ku bari ayi komai a tsanake"


Sallamar Radhiya yaji ya dago idanunsa da suka soma ja saboda muguwar gajiya da yunwa. Jin kansa yake kamar yana yawo a iska babu kuzari ko kadan. 


Emzee ne a gaba ko da ya shigo kai tsaye yaje ya rungume shi.

"Allah Ya baka abinda kake so duniya da lahira Hamma. Thank you"


"Kada kayi min kuka dai bani da karfin rarrashinka" Awwab ya zolaye shi.


Yana sake kallon Radhiya sai ga nata hawayen kamar famfo ya tashi da sauri. Wani irin sonsa take ji ta kuma rasa da wace kalma zatayi amfani domin ya gane girman farincikin da ya saka ta a ciki. Kofa ya nuna mata dama ko zama batayi ba ta fita yana take mata baya suna jin shakiyancin Ibrahim da Raji wai love is in the air.


Wurin tsayuwa yake nema inda zasu samu su kadaice babu yayi gajeren tsaki. Da sunyi aure fa shikenan duk inda yaso zai kaita. Yanzu anbi an  cika ko ina an hana mutane sakewa. Ta kula da yadda yake ta kalle kalle tayi murmushi.


"Hammana"


Dama ya lafiyar kura. Ya gaji tilis wannan kira da tayi masa yasa zuciya da gangar jikinsa duka amsawa.


"Nagod..."


"Shhhhh kada ma ki fara. Idan kina da wani abin cewa dai ki fada"


Idanunta fal kwalla tace "ni me zan ce Hamma"


"Ni ina da abin fada Alheran." Da wata irin siga mai shiga rai yake kara hargitsa ta da muryarsa "I am not a soldier kuma bani da zuciyar da zan taba zama. Kuma ni ba likita bane, bana jurar ganin jini....But I love you so much kin hana min nutsuwa tun daga ranar da na fara ganinki"


Kifta ido kawai tayi hawayenta ya sauko "nima haka Hammana"


Ya ce "wayo ko?" Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi "ina fata kin shirya aurena yanzu?"


Ba shiri ta rufe fuskarta da gefen mayafi tana neman komawa gidan Mami.


Marairaicewa yayi sosai ya koma kalar tausayi ya shagwabe mata yadda take yi ita ma "Come ooon na gaji fa. I need a wife, a friend....uhummm.... I need you." 


Murmushi take yi sosai ta kasa dagowa ta kalle shi ma. Ya duka saitin fuskarta yana neman hada ido da ita tana kaucewa "kin gani ba, ba don kin mayar dani gwauron dole ba da yanzu I have Alheran to hug when I am happy or sad. My Schatzi to kiss when love is in the air right?"


Gabadaya ta rikice masa ta ma kasa gudun ta barshi shi kadai yake ta zuba hirarsa.

"Kinsan me? I am so tired ga yunwa. Mu koma ciki?"


Tausayinsa taji kana ganinsa kasan a gajiye yake sosai kuwa.


"Muje na zuba maka"


"Baki bani amsa ba fa. Na dage ina ta debo zance duk don na burgeki"


Ya bata dariya ta gama kayarta sannan tace "I am all yours Hammana kai nake jira tuntuni"


Amsar tayi masa dadi suka shiga falon tare. Babu kowa su Zahra sun shige dakin Mami su Ibrahim suna dakin Awwab. Zama yayi akan doguwar kujera ta wuce kitchen zuba masa abinci. Akan tray ta hado komai ta dawo sai dai me...Awwab ya mike abinsa wani nannauyan bacci yayi awon gaba dashi abin tausayi. Kallonsa tayi tana jin soyayyarsa tana dada zama sabuwa a zuciyarta.


***********

A kasa Mairama ta zauna Zayyan yana jingine da kujera ta saka plate  din abincin a tsakaninsu sannan ta tashi.


"Ina zaki?"


"Hannu zan wanke" ta amsa tana sunkuyar da kai saboda tunanin abinda yayi mata mintuna kadan da suka wuce. Tasowa yayi shima yace zai wanke nasa hannun.


"Yi zamanka ina zuwa"


Bata dade ba ta dawo yayi zaton ruwa zata kawo masa a roba na wanke hannu sai gani yayi ta zauna ta debo tuwon ta kawo bakinsa.


Yau kam bashi da karfin zuciya ko kadan. Yau daya dai a Zayyan mijin Mairama yake wanda ya kwashi dimbin shekaru yana muradin sake ganinta ko da daga nesa ne. Hannun nata ya kama ya karasa dashi bakinsa.


"Ashe haka tuwo yake da dadi muka rinka cewa bama so da muna yara" taji yace ta soma dariya ya fara bin yatsunta daya bayan daya yana sudewa.


Fillo sarkin kunya sai ta kasa kara diban wani ta bashi. Ya sanya hannu ya dago kanta idanunta a rufe "alfarma nake nema Fillo"


"Babu alfarma a tsakaninmu kaima ka sani"


"Yau daya don Allah ki tattaro duka kunyar nan ko Alheran ce ki bawa ajiya. Mairama kadai nake bukata in nuna mata yadda shekaru ashirin da biyu suka galabaitar da Sojanta"
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: A haka ta gama bashi abincin yaci mai yawa. Yaushe rabonsa da tuwo ko abinci mai dadi? Miya tasha nama da bushasshen kifi yaci son ransa duk loma yana binta da addu'a da kalmomi masu nuni da kewarta da yayi.


Harararsa tayi cikin wasa "kasan dai ba'a son magana ana cin abinci ko"


"Gani nake yi idan nayi shiru kamar zaki bace na dena ganinki" ya bata amsa kai tsaye yana kallon idanunta da suka cicciko da kwalla.


Hannunsa ta kama ta rike gam da hannun hagunta ta cigaba da bashi da daman.

"Babu inda zani Sojana"


Murmushi suka yiwa juna basuyi aune ba ya cinye leda daya madaidaiciya harda karin rabi na tuwon. Nama ma ba kadan ta bashi ba sai da yaji cikinsa yayi masa nauyi don kansa yace ya isa yana dariya.


"Kada na kasa tashi daga wurin nan fa Fillo. Ina zaune kina ta zuba abinci a tumbin da yunwa ta cinye shi."


"Inda kake horon yunwa suke yi maka? Dubi yadda ka rame sosai ko da dai ba kiba gareka ba amma yanzu ana ganinka za'a gane rama ce ba siranta ba" tayi maganar yayin da ta soma hade kan kwanukan zata kai kitchen.


Da wata irin murya mai sanyi Zayyan yace "Mairama...ki kira min su Major muyi magana kafin na saka hakarkarina a makwanci."


"Ka huta don Allah" 


"Yadda kuke matse da son jin me ya sameni nima haka na damu da son jin yadda kuka rayu ke da 'ya'yana da aminai na. Kirjina yana son amayar muku da nauyin da yayi ta dako ko zanji sauki"


Wani irin tausayinsa take ji tana gama kai kwanukan ta wanko hannunta ta dawo ta kira Mami ta sanar da ita.


Su Major so suka yi ya huta ko zuwa gobe ne amma yasan shi dai bazai iya hakurin nan baiji me ya sameta ba.


Har wannan lokaci Baban Arifah yana gidan tare suka dawo falon Zayyan yace a kira masa duka yaran domin su ma sun cancanci sanin ina mahaifinsu ya shiga tsahon lokacin nan. Falon yayi tsit Awwab ne kawai babu. Radhiya dama tana dawowa ta sake komawa gabansa yana daga kan kujera tana kasa. Zayyan ya dube su daya bayan daya ya jinjina kai domin yasan wannan labari yanzu ya fara bada shi har sai duk wanda ya kamata ya sani ya sani. Sojansa ya koma rikakken namiji ma'abocin cikar zati kafin ya fara magana.


"Kwanaki kadan bayan rabuwarmu da Baban Arifah zuwa wuraren karfe daya da rabi na jiya sunana 3810 mazaunin gidan yari da ake yiwa zargin dan tawaye a Liberia"


Major da Baba Hadir sun ji kadan daga labarin daga wurin Baban Arifah amma sauran matan musamman Ummi da Alheran sun dimauce matuka.


Daga lokacin da ya rabu dasu Hadir kawo ga haduwa da rabuwarsa da Baban Arifah da zamansa a wannan prison din ya sanar dasu mahimman abubuwan da suka same shi.  Wahalhalun zaman kurkuku da tsananin begen komowa gida garesu. Kuka duka matan suke yi wurjanjan. Ummi saboda tsananin kaduwa tsigar jikinta har tashi take yi ta kasa zaman falon ta tashi tayi ciki sai sautin rufe kofar daki aka ji.


Murmushi yayi yana kallon kofar da ta bi "banda abin Fillo komai ba ya wuce ba"


Jikkuna sunyi sanyi. Girma, kima da darajar wannan bawan Allah ta ninku a cikin idanun duk wanda yake zaune a wurin. Ga su Daddy dadin ciwon abun duka su ukun fa a garin ceton rayuwarsu ne ya fadawa wannan kaddara mai radadi da sosa zuciya. Idanuwa sunyi kuka ba babba ba yaro  shiyasa Mami ta cewa yaran dukkansu su tashi tunda sauran labarin ba bakonsu bane. A sanyaye suka fice zuwa gidan Mama ita kuma da Maman suka shiga wurin Ummi. Dama kuma tun zuwan su Zayyan din bayan anyi zaman gabatar da juna sallah suka yi shine Daddy ya jagoranci addu'a da suka yi. Emzee da Ibrahim gidan Mami suka wuce su.


Da kyar bayan fitarsu Major yace "Zayyan ka ga rayuwa ni bani da wani bakin magana ko baka hakuri. Nauyi da girmanka nake kara gani ina jin inama ban biyo motar da taje camp dinku ba ranar. Da bazan biku wurin ba kai kuma babu dalilin da zai sa ka koma daukoni har wannan abu ya faru. Nine silar komai Zayyan ka yafeni" ya kare muryarsa tana rawa sosai.


Idanun Zayyan sai suka kada suka yi jazur "ashe ni din ba kaninka bane kamar yadda nayi zato. Matsayin da muka baka ni da Hadir ba shi ka bamu ba"


Sai ga hawaye ya saukowa Major da sauri yace "a'a Zayyan ba haka bane. I feel so guilty"


"Saboda kaninka yayi rayuwar da ko da babu kai ita Allah Ya zaba masa? Hadir kace wani abu mana ka barni inata babatu ni daya"


Wani mashahurin shiru yaji ya ratsa falon ya kalli Hadir ya kallesu duka a dan tsorace yace "kada kuce min wannan mutum-mutumi ne ba Hadir dan uwana ba"


Hadir din ne ya fara dariya kafin sauran su biye masa da kyar ya iya cewa "Zayyyyyan ko" yana kada masa yatsa. Abokin nasa bai chanja hali ba. Suna cikin damuwa sai da ya saka su dariyar dole.


Tashi yayi yaje yana dan dukan kafadar Hadir din a hankali "tun zuwana banjin kayi min magana ba dole na tambaya."


Baban Arifah Excellency yace "ka zauna Mustapha zaiyi maka duka bayanin da ya dace"


Haka ya koma ya zauna yana sauraron Major wanda ya fara da labarin tasa rayuwar sannan ya gangaro dawowarsu Nigeria da sake haduwa da Hadir. Jikin Zayyan wata tsuma yake yi da tashin hankali da yaji rayuwar da suka yi. Wane irin ciwo ne PTSD yake ayyanawa a ransa da ya nemi haukata Major mutum mai dauriya da karfin zuciya? Yanzu Hadir dinsa ne yayi shekaru baya iya motsa komai nasa kuma baya magana...kai rayuwa shine mutane suke kwallafa rai da neman haram bayan idan Allah Yaso sai Ya dauke maka komai Ya barka da ranka. Hadir mutuwar zaune fa yayi kuma aka raba shi da nasa iyalin alhalin yana cikinsu. Sai yaji yafi tausayin aminin nasa akan tasa rayuwar.


Bayan ya gama jin komai ya kalle shi

" To gaskiya shawarar da zan baka shine ko ka bude baki ka fara magana ko kuma kaf tarihin 'yan matanka wadanda zan iya tunawa da wanda ban tuna ba in dora nawa zan kaiwa Zainab mu koma gefe ni da Fillo musha kallo" Zayyan yace a yayin da yake ta kore kwalla da yatsansa. Dariya Baba Hadir yayi ya taso suka sake rungume juna.


Excellency yaji suna kara burge shi "ina zaune ana nuna min wariya. Ai shikenan ba fushi zanyi ba bare na barku. Nema kuke ku nuna min ku ukun kunfi shakuwa ni dan karo ne"


Major ya kwashe da dariya saboda yanayin muryar da Excellency din yayi magana da ita ta ban tausayi.

"Dama ka dena damuwa nima ana nuna min amma ya na iya they are my Ladies"


Aka sake yin dariya musamman da Baban Arifah yace shima dole zumuncin nan ayi dashi mai karfi. Kuma da yake shine babba don har Major ya girma a shekaru yace "na dauki matsayin babban yaya mai fada a ji. Idan kuma aka ki ji to fa na iya displine"


Zayyan yana dariya yace "Ka tuna min da 'yan gidanmu Yaya Babba. Ina ta tunaninsu wallahi. Ko yaya Maikudi don yafi kowa baudadden hali a gidan"


Dariyar da suke yi yaji dif ta dauke har ya soma zargin ko rasuwa akayi a gidan nasu.


"Maikudi ya rasu ne? Ku fada min dama nasa rai da ba kowa zan samu a raye ba"


Major ya sake kallon Excellency "to Yaya Babba ai sai kayi masa bayani mu dai babu ruwanmu ko Hadir"


Excellency ya dan dake "wato zamewa zaku yi? Kada ku manta ku kuka fara naku ma harda duka. Ni me nayi Allah na tuba banda dan tsare shi kuma ba ya fito ba last month"


"A fada yadda zan gane ni dai"


Major ne ya soma bashi labarin yadda ta kasance da Mairama bayan an tabbatar da rasuwarsa a wancan lokaci. Maikudi ya handame abinda ya bar musu kuma don karfin hali yayi ta musu kazafin mutuwa ya rabasu da masu taimaka musu.


Iyakar kulewa da bakinciki Zayyan ya kwasa ga tashin hankali da suka ce masa a makance suka dawo suka sami matarsa. Ashar yake nema da zai turawa Maikudi sai dai takaicinsa daya bai ma san wanda ake yayi ba yanzu.


"Kiyayyar da yake min har ta kai ya cutar min da iyali irin haka?" Yace a raunane. "Kuma meye dalilinsa na yi maka karya kaima" yayiwa Baban Arifah tambayar.


"Barni da karamin dan iska, da yaci uban duka cewa yayi fa wai dan firit ya ganni ya zata buzu ne."


Shi ya bada amsa da seriousness amma dariya suka saka ganin yadda yake kosasshen dan siyasa. Ya kuwa hade rai saboda dariyar da suke yi masa.


Su Mami suna ta bawa Ummi baki a daki su kuma a falo sun cigaba da tattaunawa.


***********


Kiran sallar la'asar da aka soma daga masallacin wani gida a nan kusa da estate din inda suke zuwa jam'i shine ya farkar da Awwab da yake baccin wahala a falon Mami. Yunwa yake ji kamar yaci babu, idanunsa suka sauka akan plate din da Radhiya ta rufe akan centre table bayan yayi bacci. Daukowa yayi ko kuskure baki bai iya tashi yayi ba ya shiga ci da sauri. Ko rabi bai ci ba sai amai kamar zai fitar da kayan cikinsa. Ibrahim da Emzee kakarinsa suka ji daga toilet din da yake cikin falon suka fito. Emzee ya tafi zai taimaka masa shi kuma Ibrahim ya tafi gidan Mama dauko mukullin motarta idan abin zuwa asibiti ne su tafi. 


Yanayin yadda ya shiga falon da sauri shi ya tada hankalin Radhiya tana gyara hijabin jikinta tayi alwala.


"Ibrahim ya?"


Shima gwanin rudewa ne yana ta bincike a falon yace "Hamma ke amai ban san me ya same shi ba"


"Amai?"  Radhiya tace a tsorace tana fita da sauri.


Da shigarta gidan Mami ta hadu da Emzee a falo yana gyara wurin amma bata ga Awwab din ba. 


"Adda fita ki koma gidan Mama" Emzee ya umarceta saboda baya so Awwab din ya leko ta ga yadda ya jigata lokaci guda.


"Don Allah Emzee ka barni na gamshi minti daya kawai" kuka yazo mata.


"Kina so su Mami su zo su ganki a nan ne ace kin biyo saurayi?"


"A'a"


"To ki koma idan ya dawo falo da kaina zan kirawoki kinji" ya koma lallabata saboda yadda ya kula ta shiga wani yanayi.


"To...toh...don Allah kada ka manta"

A sanyaye ta fita ta koma ta tada sallah. 


Ibrahim kuma yaje bangaren Ummi lokacin su Daddy sun taso zasu je suyi sallah sai Excellency ya wuce a bar Zayyan haka sai gobe kuma. Da ya fada musu halin da ya baro Awwab mukullin mota ne bai gani ba zai kaishi asibiti Zayyan ya dakatar dashi.


"Yarona ya bawa kanshi wahala yaki cin komai tun jiya"


"Awwab din da bashi da juriyar yunwa?" Cewar Major.


"Ku bashi abu mai zafi ya sha sai yayi kamar rabin awa sai yaci abinci. Amma banda ci da sauri ko da yawa sosai. Nima da naci na shekara ashirin da biyu gashi da kyar nake tafiya"


Murmushi Ibrahim yayi yana jin Zayyan ya burge shi. Gidan ya koma lokacin su Zahra suna can ya fada musu a hada masa tea. Ita ta hada masa lipton kawai da yaji kayan kamshi da sugar daidai aka kai masa. Wanka kawai yayi da sallah ya sha ya sake kwantawa kansa na juyawa. Bai ga ta ina zai taba iya zama soja ba. Su da suke zama a bakin tituna domin tsaro ga mutane ko su yanki daji ko wuraren tarzoma ayi ta fafatawa babu ci babu sha na tsayin awanni. 


Radhiya na idar da sallah Ibrahim ya fada mata me Daada yace game da Awwab din.


Ya zauna a kan kujera yana cewa "amma fa da gani yana jin jiki...cikinsa a dame sosai abin tausayi. Gaskiya yana bukatar kulawa. Naga kin fimu damuwa ko har an daidaita ne ban sani ba" 


"Allah Ya kaimu yaji sauki sai ka maimaita masa" Emzee yace daga bayansa "Adda ki dafa masa wani abincin mana tunda na gidan ya saka shi amai"


Da sauri ta bar wurin ta koma kitchen din Ummi. Sai da ta tafi Emzee yace da Ibrahim "kana da problem fa, ka ga yadda ka karasa tayar mata da hankali da abinda kake cewa"


Shi bai hango me yayi ba da gaske yace "daga fada mata gaskiya? Kai baka ga alamun yana jin jikin ba?"


"Kai baka iya sakaya zance bane"


"Kamar wani mace ayi ta luguiguita magana saboda wahalar da kai"


"Anya Ibrahim zaka iya soyayya kuwa? Irin janyo hankalin yarinya da dadadan kalamai duk zero kake" Emzee yace da mamaki don Ibrahim kai tsaye yake abu yasha a jikin Mama.


"Magana mai dadi ta wuce ina sonki kina sona mu hade kai kawai a daura aure a wuce wurin? Kakale kakalen soyayya yasa na kasa samun wadda zata burgeni fa"


"Baka hadu da shagwababbiya bane sunfi tsayawa a rai"


"Allah Ya tsareni a rinka tale baki ana karya wuya kamar mara lafiya. Malamin jinya ne ni?"


Emzee yana dariya Zayyana ta banko kofar daki ta fito ashe tana jinsu. Tsaki taja da karfi yadda duka zasu ji ta wuce a fusace. Maganar Ibrahim ta sani sarai da ita yake ba wani ba. Duk da tana shiri da su duka kuma bata da abokan hira idan suna gidan sai su amma fa tafi jituwa da Emzee. A da bata ganewa idan Ibrahim ya fadi magana akan yanayinta amma yanzu an kile anje bodin an hadu da 'yan mata. Ba wannan Zayyan bace mai komai Daddy, ita ma yanzu ta san me take yi.


"Ka ga ka taba min kanwa."


"Da nayi me? Ai banyi komai ba sai na sami wannan bakin na dalle inji wa take yiwa tsaki ni da kai"


Emzee ya mike yana daga hannuwa "my friend da kai fa take. Ba dama tayi magana ka rinka cewa ana tale baki. Mutane irinka gidansu babu wani armashi komai a rinka yi kamar yaki. Irin dan tattalin nan da rarrashi ni ban ga alamun zaka iya ba"


Ibrahim kallon tausayi yayi masa don shi soyayya bacin lokaci ya dauketa musamman da ya dukufa karatun nan baji ba gani.


"Chege Emzee anya kai a NDA dinnan soja kaje zama ko kuwa dai idan kayi graduating buzu zamu shimfida maka a kofar gida ka koma mai bada lakanin mallaka da inganta kauna"


Cakumo shi Emzee yayi ya matse a tsakanin hannu da cikinsa yana cewa Allah Ya kawo shi neman shawara ya ga yadda zai rama.


***********


Sai da Radhiya tayi kusan minti biyar tana tunani kafin ta yanke shawarar me zata dafawa Awwab me sauki da zai ji dadinsa. Fridge ta bude ta fito da mince meat ta juye a karamar non-stick pot sannan ta hada albasa, tumatir uku da attaruhu biyu kanana tayi blending tare da tafarnuwa karama. Juyesu tayi a wani pan ta saki wuta nan da nan ruwan ya kafe. Sai ta dora mince meat din shima batare da ta saka ruwa ba na jikinsa ya bushe ya soma sauya kala sai ta zuba soyayyan mai a kai. Ta yanka albasa babba ta juye a ciki tare da wancan kayan miya ta zuba gishiri da kayan kamshi ta barsu suna suyowa a hankali. Sai da ta ga sauce din nata ya fara haduwa ta kara maggi da curry sannan ta dafa couscous wanda ta sakawa butter da dan gishiri a ruwan dahuwar. Ruwa ne kadan ake sakawa ayi komai cikin sauri kada ya cabe ko yayi tuwo. Yayi kyau sosai a ido ta kwashe ta zuba a karamin flask. Sauce din shi kuma ta zuba a wani bowl ta hada masa komai da plate da cokali ta bawa Zayyana dake zaune tana kunkunin maganar Ibrahim ta kaiwa Awwab.


Fauziyya ta rinka mita saboda abincin dan kadan Radhiya tayi gashi ransu ya mugun biyawa. Da yake hankalinta yana wurin Hammanta ko a jikinta sai cewa tayi idan suna so su jira Hamma ya warke tayi musu.


"Ke wallahi lallaba dangin miji akeyi a zamanin nan" Fauziyya tace tana maka mata harara don sosai tasa rai zata ci.


"Nima dangin mijin ce sai hakuri Adda babu yadda zakiyi dani"


"Don Allah ki taimaka min mana Radhiya idan banci ba bana jin bacci zai iya daukana yau" ta koma kwantar da kai.


Zahra ta bita da kallon tuhuma "anya Fauziyya kalau kike kuwa? Jiya ma fa kinyi mana daga an soya kwai da mince meat kika cinye fiye da rabin wanda aka ajiye a dinning. To ko dan mince meat kika dauko"


"Kada kiyi min fata har yau ina tuna kalar kukan da nayi ina nakuda. A bar zancen na yafe"


Radhiya ta sami na tsokana daga baya ta tausaya mata ta kawo sauran sauce din amma babu cous cous duka ta juye masa ta bata.


Zayyana

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment