Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wahala. Nasan kunyi mana halacci da kawaici amma in sha Allahu bazamu bari naku hakurin ya kare ba"


Kuka sosai Zainab ta saka tana ji suna cigaba da maganar tana ta magiya.


Shi kansa Hadir din hawaye yake fitarwa. Babansa ya sake bata hakuri "kina da kuruciyarki ta yaya zamu barki da mutumin da bazai iya yi miki komai ba sai zame miki nauyi. Abu na biyu Hadir ne karfinmu mu kanmu. Yana kwance yanzu mu ma rayuwar wahala take mana ta ina zamu ajiyeki? Yau da gobe sai Allah 'yata Zainab, watarana zaki bukaci fiye da Hadir amma aure yayi miki dabaibayi. Zaki so kulawa da kowacce mace take muradi a gidan aurenta. Sannan ko mu iyayensa zamu iya gajiyawa balle mata. Komai fa sai anyi masa hatta gyara kwanciya.  Kudin aikinsa kuma bamu da yadda zamuyi mu taba hada rabinsa ma. Zuwana Sakkwato uku akan maganarsa sun ce babu kudi a barikin"


Zainab daga gaban wannan take zuwa gaban wancan tana kuka tana roko akan su barta da mijinta. Kwarai ta basu tausayi amma basa son nuna son kansu da rashin dattako. Hadir sai rufe ido kawai yayi zuciyarsa tana kuna sai da yaji mahaifinsa ya kira sunansa.


"Hadir, ina mai umartarka da ka sauwakewa Zainab kada mu zama masu daukan alhaki, ka amince"


"Kada ka sakeni, don Allah ku barni da aurena" Zainab ta fada cikin tashin hankali.


Kifta ido Hadir yayi babansa ya sake cewa " ka amince cewa kai Hadir ka yiwa Zainab matarka saki daya?"


Wannan karon ma ido ya sake kiftawa yana zubar da hawaye. Zainab yaji ta fado a jikinsa ta kankame shi tana kuka bata san ma me take yi ba "Wallahi ban saku ba, babu inda zani"


Mamanta da Umman Hadir kukan suke tayata saboda tausayi. 

"Zainab kiyi hakuri"


"Ba fa zan je ko ina ba ai ba da bakinsa yayi sakin ba"


Babanta gani yayi abin yana daukan lokaci an kasa rarrashinta ya tashi ya mareta. Ta rike kunci baban Hadir yana cewa don me zai mareta "yaya take so muyi mata ne? Duk wani bayani anyi amma da gangan taki ganewa. Ki tashi maza ki hada kayanki yau dinnan ma zamu koma"


Karamin hauka Zainab tayi ranar har suka bar garin gashi ance ta bar Ibrahim saboda Hadir yaji saukin rabuwa da ita shima.


Sau biyu tana guduwa Kano bayan sun koma sai da babanta yayi mata kaca kaca karshe ya yi mata aure. Lokacin Hadir ya kusa shekara biyu a kwance. Ranar da aka kaita a ranar ta nuna mijin da wuka tace ko ya saketa ko ta kashe shi ta kashe kanta. Bai tsaya bata lokaci ba yayi mata saki ukun da ta bukata.


Iyayenta sunyi fushi sosai da ita ta koma wata iri ita kanta saboda tashin hankali. Sai da kyar ta samu suka hakura bayan an sake saka mata rana da wani ma'aikacin kamfanin man fetur a Port Harcourt. Wannan karon babanta yace idan ta sake kashe aurenta ko taje Kano bazai yafe mata ba. Mijin nata mutumin Sakkwato ne amma a can Port Harcourt din zasu zauna. 


Ba don taso ba akayi auren. Mutumin mai suna Musa Waziri yana matukar son Zainab shiyasa baya fushi da ita. Yana da kudi shi ya canjawa iyayenta gida ya samarwa yayyenta maza biyu aiki a branch din gidan mansu suka samu rangwame daga kangin talaucin da suke ciki.


Ranar da ta tare tayi kuka kamar ranta zai fita. Gani take taci amanar Hadir shiyasa har shekaru suke tafiya tsakaninta da mijinta bata taba wata doguwar walwala ba. 'Ya'yansa 'yan mata biyu da ya rabu da mahaifiyarsu su kadai ne suke samun kulawarta. Wannan dalilin shi ya karawa Musa hakuri da ita da halinta na rashin son sa. Duka wani hakkinsa tana saukewa amma soyayya da fara'arta sai yayi watanni bai gani ba.


Hadir yana nan kwance sai gashi da suka samu kaninsa yake kaishi idan yayi ciniki a kasuwa kudi sun samu. Gashin yana taimaka masa wurin jin dadin jikinsa saboda yawan kwanciya.  Magana ce dai da wuya yake iya hada kalma daya kwakkwara. Ibrahim yana girma ya gane waye Hadir a wurinsa a hankali ya gudu daga cikin gidan ya koma dakin mahaifinsa. Sannu a hankali indai ba yana makaranta ba komai na Hadir ya dawo gareshi. Idan aka kaishi hutu wurin Zainab baya iya sati biyu ya rinka cewa Abbansa kenan dole a mayar dashi da wuri.


A haka shekaru ke tafiya a haka rayuwar wannan iyalin ta wargaje gabadaya daga aikin soja. Miji ya koma kan wheelchair ga ciwon zuciya ya kama shi da gaske saboda yawan tunani. Uwa ta sake aure bisa dole amma zuciyarta tana ga tsohon mijinta sannan dansu ya taso a wata bahaguwar rayuwa bai san komai ba tunda ya fara wayo sai jinyar mahaifinsa. 


A bangaren Hadir rashin iya magana ya nemi iyalin Zayyan yana damunsa sai ya kwana yana kuka idan ya tuna rasuwar aminin da ya dauka tamkar dan uwa. A irin lokutan ciwonsa ke tashi a kasa gane kansa. Zainab ma bata taba mantawa dasu ba amma kunyar nemansu take yi a yanzu bayan shekaru sun ja ta dan dawo cikin nutsuwarta. Bata san Zayyan ya rasu ba haka nan bata sani ba ko shima ya dawo kamar Hadir. Mami kuwa sunan garinsu kadai ta sani ta ina zata fara nemanta. 


Babban abin dubawa shine komai na rayuwa duk yadda ka kai da matsuwa dashi sai Allah Ya nufeka da yinsa. Mukan kwadaitu da gabatar da wani abu mai girma a garemu amma sau tari sai wasu abubuwa suyi mana shamaki dasu. Yanayin rayuwa bai mantar da Zainab mutanen da suka yi zaman amana ba amma halin da ta tsinci kanta yasa damuwarta ta danne hangenta. Burinta daya ne a rayuwa...ta komawa Hadir!


**********


"Ni na kashe shi...ni nayi ajalin Zayyan..ina zan saka kaina? Hassana na kashewa Alheran mahaifi. Meyasa nima ban mutu ba?"


Kuka ne irin na mazan da suka ga tashin hankali muraran ba labari ba. Babban soja mai ji da jarumta shine yake zubar da hawaye kamar yaron goye.


Farfadowarsa kenan daga allurar anasiziya da aka yi masa kafin a shiga dashi theatre. Tsahon sati biyu da kwanaki da yayi a asibitin Katsina kafin likitan da zaiyi masa aikin kafar yazo daga asibitin koyarwa na Zaria yayi su ne a cikin halin rashin sanin inda yake. Irin kukan da Mami tayi na fili da na zuci bazai fadu ba. Major Mustapha soja yayanta kuma uban 'ya'yanta shine wasu cikin masu zuwa dubiya suke kirawa hauka. Dole ace yana hauka don idan har zaka zauna dashi na minti biyar ido biyu surutan da zaka ji yana yi kwatakwata babu ma'ana ga wanda baya tare dasu a ranar da abin nan ya faru a dajin Liberia. Labari ne na yaki, tashin hankali da zubar jini. Tsananin ciwon da kafarsa take yi shine musabbabin fitarsa daga hayyacinsa har yake wadannan surutai. An tabbatar musu da cewa zafin ciwo ne kawai.


Asibitin suna kokarin dressing din ciwon amma yadda tsutsa ke fita suna cin namansa daga ciki shi kadai yasan azabar da yake ciki. Dakin kansa wani irin wari yake yi don kannensu maza ke kwana dashi ma. An hana Mami kwana sai dai tazo ta wuni ta koma gida.


Kudi sosai suka kashe akan ciwon nasa. To yau dai Allah Yayi likita yazo an yanke kafa dan abinda aka bari iya rabin cinyarsa ne. Sauran naman duk ya zagwanye saboda infection.


Abinda yake fada ya tadawa Mami hankali. Cikin nutsuwa ta matsa kusa dashi tana tambayarsa me ya sami Zayyan din.


"Ni ne dai nayi ajalinsa. Ashe duk mutuncin da yaron nan yake nuna min a dalilina zai rasa ransa. Ya ceci rayuwata ya rasa tasa. Me yasa nima ban mutu ba?"


Mami ta shiga rudani aka sake kiran likita yace su kwantar da hankulansu allura bata gama sakinsa ba. Da kadan da kadan sai da suka kwashe wata uku cur a asibitin nan. Kafarsa ta hade wurin sai dungulmi amma ya gamu da wata sabuwar lalurar da basu ankara da ita da wuri ba wato septicemia. Infection ne na jini da yake samuwa daga infection a wani bangaren jiki sai kwayoyin cutar su gangara cikin jini. 


Da zazzafan zazzabi abin ya fara sai kuma yawan jin sanyi. Da fari magunguna da alluran malaria aka bashi. Yayi sati ana wannan babu wani chanji sai ma gaba da abin ya kara. Bugun zuciyarsa sai ya kara gudu har ana gani dagowar kirjinsa, dama ga muguwar rama da ya hada. Da likitocin suka ga babu sauki akace typoid ce. Nan ma duk wasu allurai da magunguna sai da ya karar dasu.


Hankula sun kara tashi ne ranar da zuciyarsa ta nemi bugawa shine fa aka rinka gwaje gwaje baji ba gani. Jininsa har asibitocin koyarwa na Zaria, Kano da Ibadan an tura domin gano abinda yake damunsa. Rashin wadatar kayan aiki a asibitocin kasarmu ya janyo Major Mustapha ya kusa rasa rayuwarsa. Da kyar aka gano a asibitin Ibadan aka turo musu sakamakon. Sai a lokacin aka fara treatment bayan infection din yaci jininsa sosai har ya fara harin kayan cikinsa.


Da aka sallamo shi haka ya dawo gida kamar mutum mutumi. Yau da lafiya gobe babu. Ya rage surutai sai ma rashin son magana da kebewa daga mutane. Idan ya kalli kafarsa sai yaji ya tsani rayuwa gabadaya. Da bai rasata ba Zayyan bazai dawo daukarsa ba. Da sai su gudu tare su tsira tare. 


Yayi shekara a kwance. An sayar da motarsa da filinsa na nan Katsina duk a siyan magunguna masu tsada domin samun lafiyarsa. 


Wata rana Mami tayi masa zancen su Mairama sai kawai ya saka mata kuka. Taya shi tayi don gabadaya mijin nata yanzu tamkar bashi ba. 


"Da wane ido zan kalleta Hassana? Ko kinsan cewa da don ta ni ne wallahi na gwammace na kare rayuwa a Liberia da na dawo gida na fuskanci matar Zayyan. Na zama silar da bomb ya tarwatsa mata miji shine abinda kike so kiji na fada mata idan ta tambayeni ta yaya mijinta ya rasa ransa?"


"Kayi hakuri Daddy ba manufata ba kenan. Kasan ya barta da ciki ga Radhiya"


Kai ya girgiza "baki san nauyin da zuciyata take ciki bane da kin kyaleni. I feel guilty and I hate myself and.... my life. Idan zaki je nayi miki izini"


Tasowa tayi ta rungume shi tana hawaye "nima me zance mata?"


"Ban sani ba..." yace da raunin zuciya yana kara kankameta.


Kwanaki kadan da yin wannan magana wata rana da daddare suna kwance ta tuna Fauziyya ta kwanta bata yi fitsari ba. A gidansu Major din aka basu wani bangare dakuna biyu masu fuskantar juna. Awwab a wurin samari yake kwana har an mayar dasu makaranta.


Ta je ta kai Fauziyya tayi fitsari ta dawo da sanda saboda kada ta tashe shi. Amma duk da haka sai da ya farka. Inuwarta ya gani ta tuna masa da lokacin da 'yan tawayen nan suka rinka fitowa ta baya da saman bishiyoyi suna harbinsu. Baiyi wata wata ba ya mirgina jikinsa ya damkota. A daidai wannan lokacin jinsa yake kamar a wancan lokacin. Kunnuwansa suna jiyo masa sautin harbi da hayaniya tartar. Wata muguwar shaka ya kaiwa Mami ya sakar mata karfi.


"Captain na kama daya kuzo ku daure shi mu tafi dashi base dinmu" yace da dan karfi.


Mami sai kokawa take tana son yi masa magana ta kasa saboda wuyanta da ya shake tana numfashi sama sama. A daidai kunnenta yace


"Who sent you?"


Wahala ta fara yawa Mami duhu duhu take gani. Da kyar ta samu ta juya ta saka duka karfinta ta galla masa cizo a kirji. Gashin kanta ya damko da karfi ta saki kara. Daga hannu yayi ya kwada mata mari ta sake yin wata karar. Zai kuma marinta haske ya mamaye dakin. Mahaifiyarsa ce ta shigo tare da kaninsa da suka ji ihun Mami. Tana zuwa itama hannu ta cire ta mare shi.


"Kasheta kake son yi ne Mustapha? Sakar mata gashi" 


Tamkar wanda ya tashi daga bacci sai lokacin ya kula da hannunsa da inda hannunsa yake yayi saurin sakinta. A guje ta tashi ta fada jikin Innarsa tana kuka. Wuyanta Innar ta lura dashi saboda farar fata yayi jawur.


"Na shiga uku ni Fatima me zan gani? Ba dai shaketa kayi ba?"


Kansa yaji ya daure wai me yake yi a dakin nan shi da suke tare da su Zayyan a daji. Firgici da tsoro ya kama shi ya soma yunkurin sauka daga kan gadon. Innarsa ta dakatar dashi.


"Kada ka soma matsowa inda muke wallahi." Ta kalli kaninsa "rufe min shi da safe sai a fadawa Alh Baba kafin babanku ya dawo"


Washegari zama na musamman akayi akan abinda ya faru a daren. Mahaifiyar Mami ta shafawa idonta toka tace 'yarta ko dai ta koma gida ko kuma a raba musu daki bazata yarda a kasheta ba. Ko wace ma hakan zata yi shiyasa aka tattara Mami da yaranta ta kuma gidan iyayenta.


Major Mustapha kuma ya shiga wani sabon mawuyacin mataki a rayuwarsa. Iyaye duka sun hadu akan cewa gamo yayi a dajin nan aka shiga banka masa magungunan gargajiya, hayaki da rubutu. Kowa yaji labarin maganin aljanu cikinsu zai bada kudi domin a kawo su gwada. Idan ka ganshi dole ka koka in kasan waye Major Mustapha. Ya rame ya kare sai kashi da tashin hankali. Kuma abu kadan yake tayar masa da wannan abu ya fada cikin dogon tunani yana ganin kamar yanzu abin yake faruwa.


Awwab shine mai zama dashi sosai kafin watarana shima ya shigo daki ya nemi Daddyn nasu ya rasa. Ya zauna jiran ko yana bandaki amma shiru. Haka akayi ta neman Major hankalin kowa a tashe. Mami taci kuka ta more. Sai can kamar ance Awwab ya duka ya ganshi a karkashin gado yana ta rarraba idanu.


"Mami gashi nan"


"Shhhh zasu ganmu."


Mami ta dake ta duka itama "su waye zasu ganmu Daddy?"


" 'Yan tawayen mana"


Kasa magana tayi ta tashi ta koma dakin Innarsa tana kuka. Har yaushe zasu kare rayuwarsu a wannan yanayi? Dama haka ake auren sojan ko kuwa kaddararsu ce haka?


Sauki babu sai daga Allah. A wannan yanayin Gambonsu Mami da mijinta Harun da a wurin Alh Baba suka zo daga Germany inda yake aiki a gidan rediyo a matsayin mai labarai.


Sunyi bakincikin yadda rayuwa ta mayar da 'yan uwansu shine Harun ya shiga newarwa Major da Mami visar tafiya. A cewarsa zai kai dan uwansa asibiti ne tunda babu wani cigaba a gida. Iyayensu dai sun kyaleshi ne amma a iya tunaninsu asarar kudi zaiyi.


Abu na Allah sun tafi Germany a shekara ta uku bayan rasuwar Zayyan. A can ne bincike ya nuna Major yana fama da Post Traumatic Stress Disorder (PTSD). Lalura ce ta kwakwalwa da a lokacin ba'a waye da ita sosai a bangarenmu na Africa ba. PTSD tana samuwa ne ga mutanen da suka yi gamo da mummunan yanayi ko al'amari kuma tana tashi ne idan suka samu kansu a yanayin da zai iya tuna musu da wannan abu. Yawan mafarkin da yake yi da kuma ji ko ganin kamar yanzu abin yake faruwa duka alamominta ne.


Mami tambaya take ba haukacewa yayi ba aka ce mata ba hauka bane sai dai masu ita suna bukatar tsantsar kulawa daga makusantansu don idan abu yayi yawa wasu har kashe kansu suke yi.


A gidan Gambo suka zauna har zuwa lokacin da ya fara jin sauki. Mami ta jajirce sosai wurin kula dashi. Daga baya ta fara tunanin kada su zame musu nauyi tace Harun ya nema mata aiki. To aiki a wata kasar ba'a samunsa kai tsaye. Ta bukaci ko yaya tana son neman kudi kafin su koma saboda kusan karkaf sunyi. Komai nashi ya kare an fara shiga aljihun dangi.


Aikin nanny ya samar mata har yana tsoron fada mata sai ta basu mamaki wurin karbar aikin hannu bibbiyu. Gidan wasu 'yan kasa take zuwa daga bakwai na safe zuwa bakwai na yamma. Tayi su shara, wankin toilet da sauran ayyukan gida hade da raino.

Mutane da dama suna zaton da ance ka fita waje watayawa kake. Aikatuwa take bilhakki mijinta yana kukan nakasa a gefe. A hankali masu gidan suka yaba da kwazonta sai aka basu wani dan bangare karami a gidan. 


Cikin shekarsu ta biyu Harun yaje gida abinda ta hada ta bayar aka dauko musu 'ya'yansu sauran kuma ta aika Sakkwato wurin sojan da Major ya rubutawa sako cewa a bawa su Mairama. Shekara guda cif cikin kudin aikin Mami ake dibarwa Mairama.


Sako ya riskesu daga karyar Maikudi cewa tayi aure sannan dan cikinta baizo da rai ba. Hoton Alheran Radhiya kuwa da suka bukata cikin dakin Jume ya dauko wani da aka yi musu da yaransu gidan wani zuwansu da sallah. Murna sosai ranar da suka amshi hoton. 


Cikin ikon Allah sai ga Mami da ciki. Allah Ya bata 'ya mace Major ya saka mata suna Zayyanatu. Dariya tayi da taji sunan yace idan haihuwa goma zata sake Zayyan da Zayyanatu zaiyi ta saka musu.


A yanzu Major ya sami aiki a wani kamfani shima sannan Awwab ya sami scholarship saboda kwazonsa a makaranta. Harun da Gambo sun koma Nigeria da 'ya'yansu uku Ghazalatu, Hafsa da Imam. Su Mami kuwa zaman jiran kammaluwar karatun Awwab suke su koma su ma. Sun sami rufin asiri daidai gwargwado kuma sai Major yayi watanni lalurarsa bata tashi ba sai anyi zancen Nigeria ranar zai kwana hankali a tashe yana tuna aikin da ya yiwa kasarsa ya kaishi ga wannan rayuwa


**********


HADUWAR ALKHAIRI
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: ***********


"Ke Radhiya, zo kije kantin sauki ki siyo min yis"


Shanyar kayansu da ta wanke take yi nata da na Emzee da Mairama. Kallon Binta tayi tace "ki aiki Emzee ko wani don Allah kinga ni bana fita saboda Ummi"


"Inda na aike kin har wani nisa ne dashi da zaki fara yi min felekenki na tsiya. Ko kuwa nace kije ki zauna ne?"


Zumburo baki tayi "Ummi wanka zata yi idan na gama shanya. Zaki kai mata ruwan ki ajiye mata soso da komai a kusa da ita inji miki aiken?"


Mairama tana daki ta jiyo su ta rinka shafa bango har ta fito.


"Ke!" Tace da tsawa


Radhiya ta juyo tana jira taji Mairama ta umarceta da zuwa kantin ta fada mata kai tsaye ba zuwa zata yi ba. Tunda mahaifiyarta ta makance ta kara hankali da bambance su waye masu kaunarsu da gaskiya. Malamijo ya gina gidansa da turbar nafsi nafsi kowa ta kansa yake yi. Babu wani jinkai na azo a gani saboda rashin wadata su da abubuwan da ya dace. Idan ka cire Yadikko babu wadda take leka Mairama balle ace mata yaya jiki. Dukkansu take kallo tana jin kanta daidai dasu. A duniya bata da sama da Umminta sai Emzee. Shi kuma haushinsa take ji saboda rashin magana. Gabadayansa bashi da walwala sosai yaron saboda tsangwama musamman daga Salame kafin ta bar gidan.


"Ki karba kije ki siyo mata ko ma meye idan kin dawo sai nayi wankan"


Radhiya yarinya 'yar kimanin shekara goma sha daya wadda ta gado zuciya ta mahaifiyarta, barkwanci da jarumtar mahaifinta da kuma jinkai da tausayi nasu su biyu ta kekashe idanu "Ummi ni bazani ba idan na tafi ma zubar da kudin zanyi a kwata ko na sayi danmalelen gidan Fadi. Haka kawai yau babu makaranta kowa yana nan taki aikensu sai ni saboda bata damu dake ba" ta kare maganar muryarta da alamun zata yi kuka.


Mairama ta daga hannu daga inda take tsaye kamar za ta dake ta "kizo ki karba kafin ranki ya baci"


Juya keya tayi ta mika hannu ta baya tana jira Binta ta ajiye mata kudin harda wani kada jiki. Emzee ne yazo ya karbe "ni zanje me za'a siyo miki?"


Binta ta warce kudin "bazaka je ba din, wannan fitsararriyar nake so inga uban da ya tsaya mata a cikin gidan nan. Har ni kike juyawa keya saboda baki da kunya"


Mairama daurewa kawai take yi saboda rashin ido. Itama ta sani an tsangwami 'ya'yanta an hanasu rawar gaban hantsi saboda an ga tana zaune. Amaren Malamijo Hanne da Binta sunfi kowa kaudi da takura musu. Kuncin zuciyarta ne ya taso ta tuna mijinta. Da yana raye waye duk gidan nan ya isa ya taka su? Yadda kowane uba ke kaunar 'ya'yan shima tasan zai so nasa kuma ya kyautata musu rayuwa.


"Karami janyo min hannun yayarka"


Da kanta ta karaso gaban Mairama ta kama hannunta don ta nuna mata ta iso. Hannunta ta shimfide mata a gadon baya, dukan ya shigeta amma ta dake. Mairama kanta ciwo take ji yana addabar zuciyarta "in ce kije aiken ki ce bazaki ba saboda ban isa ba? Ko saboda bani da ido sai yadda..."


Zubewa tayi a kasa tasa kuka "Ummi kiyi hakuri don Allah zanje."


Kudin ta karba daga hannun Emzee tana cewa ya mayar da Ummi daki kafin ta dawo. Rai a bace taje ta siyo yeast din naira hamsin maimakon na ashirin da aka aiketa. Da ta dawo daga bakin kofa ta tsaya ta zura hannu


"Gashi"


"Shigo ki bani" Binta tace da gadara tana fadawa yayarta "kinga fa irin jarabar da muke fama da ita. Uwa makauniya 'ya'ya marasa da'a"


"Mu ba jaraba bane" Radhiya ta maida mata da tsiwa.


Bintu bata bata lokaci ba ta kai mata lafiyayyen mari.


"Uwarki makauniyar nan ma bata isa ba wallahi"


Tana kuka baki bai mutu ba "ba dai uwata ba"


Ran Binta ya kara baci "sai ta wa?"


"Wanda ya tsargu dashi nake" Radhiya ta amsa kai tsaye. Kafin Binta ta ankara ta fice daga dakin. Da sauri ta kamo Radhiya a tsakar gidan tana shirin shiga dakinsu.


Mairama tana jinsu ta yi salati ta sake tashi "me kika sake yi kuma?"


Binta ke dukan Radhiya da zagi amma a hakan cewa take ba dai tata uwar ba. Hajjo ta taho kwatar Radhiya Binta ta sake tunzura ta daga hannu zata sake kai mata duka ga Mairama har ta soma hawaye suka ji sallama.


Amsa sallamar bakuwar suka yi Binta bata kula ba ta kuma daga hannu taji matar da ta shigo tace tayi hakuri kada ta sake dukanta yara sai da rarrashi.


Idanu a soye don itama Binta ba kunyar gareta ba tace "yau ko uban da ya haifi uwarta ne wallahi bai isa ya hanani dukanta ba"


Malamijo wanda motocin da ya gani a kofar gidansa suka saka shi tasowa daga majalisar da yake ko kallon mutanen wajen baiyi ba tunda ya ga daya ta shiga gidansa. Ya shigo kenan ya ji me Binta tace ya kuwa murtuke fuska.


"Ahhh lallai yarinya kwananki a gidana ne ya kare shiyasa kike zagina. To shiga ki kwaso tsiyarki kizo ki wuce na sakeki saki biyu"


Innawuro ta kalli Ali tana jin wani bacin rai. Wato duk tsayin shekarun nan yana nan da bakin halinsa na sakin mata. Ta sani wadda ya saka din tayi laifi amma a bainar jama'a haka ya dankara mata saki.


Shi kuwa ko a jikinsa sai ma binta da yayi da kallo yana son tuna a ina ya santa. Matan gidan da yara hankali ya koma wurin Binta da tayi dakinta tana kuka basu kula da Radhiya da take zaune a kasa ba ko bakuwar da take tsaye. Yadikko har kullum ita ce mai hankalin kuma bata gida a lokacin. 


Mairama ta duka tana mika hannu neman Radhiya da ta tabbatar tana wurin tana kuka.


Cikin kuka da ta gaji da laluben tace "ina kike ne?"


Muryarta kawai Innawuro taji ta saki baki tana kallonta. Babu tantama wannan ce Mairama diyar Mairo don banda kama ta fuska hatta muryarsu tayi shige sosai.


Kafadar Radhiyan tayi sa'ar dafawa ita kuma haushin aiken tun farko ta janye jikinta tana saka kuka mai sautin da bata yi ba a gaban wadda ta daketa.


"Ba ke kika ce sai naje mata aike ba"


"Allah Ya baki hakuri to tashi muje daki"


Mairama ta mikar da Radhiya a daidai lokacin da Innawuro tace "Mairama?"

Malamijo kuma yace "Innawuro?"


Mairama ta juya duk da bata ganinta ita kuma ta juya tana kallon Malamijo ashe tun dazu yana tsaye. Hankalinta duk yayi kan Mairama tace "muna da yawa sauran suna waje. Na shigo ne sanar da zuwan namu"


Yawun bakinsa ne ya kafe, lebbansa suka bushe sai harshe yake ta fitarwa yana lashesu. Duka motocin nan bus uku da canta daya 'yan uwan Mairo ne? Ya sani da kansa ya taba nemansu saboda tausayin Mairama. Amma tuni ya watsar musamman yanzu da rayuwarta take cikin garari.


Innawuro ta dawo dashi cikin hayyacinsa da yaji tana cewa Emzee ya fita ya cewa bakin waje su shigo. Yaron ya tafi yin abinda ta saka

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment