Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwakwar da Yadikko ta bani wancan zuwan da mukayi Sumaila"


"Da kike ishi mutane da kuka harda yaji"


"Ba'a kyauta min bane...da kinga kan nan bazaki so ace nawa bane"


A hankali sai ga Mairama tana dariyar shiriritar Radhiya.


**********


Bayan kwana biyu da zuwan su Major Kano suka shirya harda su Zainab sai birnin Shehu. Da yake Zainab 'yar gari ce dadewa bata sa ta manta hanyar gidan ba. Sun so bata saboda gyare gyaren da aka samu kadan. Sojan da ake turowa kudi ya riga ya bar garin ma ta banki yake turawa MaiKudi kudin.


Alhamdulillah gida ya cika da yara ko ta ina. Ibrahim yana tura Hadir gefensa Major ne yana fada masa dawowar Awwab nan da kwana goma.


Matan ne suka fara shiga aka amsa musu. Sun gaisa Mami ta tambayi Jume wata yarinya ta nuna musu dakinta.


"Fada mata abokan aikin marigayi ne da iyalansu suka zo"


Yarinya ta ruga sai gasu sun fito tare Jume tana musu marhabin da lale. Tabarmi uku aka shimfida musu suka zauna aka gaisa.


"Jama'a ina kuka shige duk shekarun nan ba'a jin duriyarku?"


Kunya ta kamasu duk da kowa dai da nasa uzurin. Sun dan yiwa Jume bayanin da zata iya fahimta Major yana dariya yace "ina Alheran ne?"


"Wai, 'Yar soja ai tana rugar Barkindo, da yake dai akwai bikin yayarta 'yar wajen Mubaraka nasan suna tafe in Allah Ya so"


Kallon juna suka shiga yi sai Mami ta gyara tambayar "aka ce mana bayan Mairama tayi aure ita ta dawo nan wurinku"


Itama nema suke su juya mata kai ta kwalawa Matar Badaru kira "kinji wai 'Yar soja suke cigiya ni duk ban fahimci zancen ba, nasan Badaru yana ciki turo min shi ya musu bayani."


Tsayawa tayi suka gaisa sannan taje ta dawo tare da maigidanta. Shima ya gaisa dasu a mutumce Major yayi masa bayanin yadda suka yi da sojan da yake turo musu kudi akan cewa Mairama tana gidan miji, Radhiya kuma tana nan.


Badaru ya rike baki abin da daure kai "Yallabai gaskiya ka binciki mutumin da yayi maka karairayin nan tun wuri"


"Ban fahimceka ba"


Mami da Zainab har sun fara damuwa ganin yadda iyalan gidan su ka canja fuska su ma.


Badaru ya gyara zama ya soma yi musu bayani "zancen da nake muku Mairama tayi akalla shekara shida ko ma fi da makancewa, Radhiya da Zayyan kuma suna tare da ita a can wurin dangin babarta. Sai dai mutumci irin nata wallahi har ila yau tana turo mana yaran idan sun sami hutu"


Kuka wiwi Zainab da Mami suke yi. Zuwa yanzu sai dai su ce sun ga jiya sun ga yau a auren soja. Makanta, yanzu ace Mairama ta makance babu ido.


A sanyaye Major yace "ban tari numfashinka ba, wane Zayyan kake magana a kai?"


Jume tace "Zayyanu karami kanin Radhiya"


Mami ta zaro idanu "aka ce mana ta haihu jariri babu rai"


A fusace Jume tace "wai uban waye ne da wadannan karairayin? Yarinya tana fama da lalura da rashin miji anbi an dabaibayeta da karya. Rashin waiwayarta da kuka yi yafi komai damunta, bata da masaniyar inda kowa yake cikinku gashi dangin ita mahaifiyar Zayyanu suma shiru rabonmu dasu tun sunan 'Yar soja"


Zuciyar Major tuni ta kawo wuya ya daga waya zai kira dan sakon nasa sai ga Maikudi ikon Allah. Su Maikudi an karo wulakanci yana shiga yana fita duk wata yana jin 'yan chanjinsa a aljihu. Saboda son zuciya ma sai ya dena 'yar fafutukar da yake tunda dai albashin nan yana shigowa babu fashi.


"Yauwa Maikudi gara da Allah Ya dawo da kai da yanzu."


Idanunsa akan bakin ya kula akwai maiko a tare dasu "hee...hee baki muka yi a gidan ne. Sannunku da zuwa."


Matarsa ya shiga kwalawa kira "ya naga babu ko 'yar mantina dinnan a gabansu? Wannan ai halin karanta ne. Waye nan a cikin yaran azo a nemo musu abin sha mai sanyi"


Ran Jume ya fara baci tace "to dan ayi jikan na'isa, mu duk bamu iya ba sai kai. Ni zo ka jiye min baki ke neman Radhiya wai an fada musu a gidan nan take"


A take kuzarinsa ya fara raguwa "ki fada musu inda take su je mana"


"Mutanen nan fa abokan Marigayi ne, shi wannan yace ya dauki lokaci yana aiko da kudi kuma ance a gidannan ake karba" Badaru ya kara masa haske


Abinka da munafuki gumi ya soma yi kamar an kwara masa ruwa "indai don Allah suke yi sai abar tone tone su sake mata kyautar tunda sun dawo. Ni bari na shiga ciki na gaji"


Wani irin kallo Major da Hadir ke yi masa. Ashe Jume ma tasha jinin jizkinta. Ai kuwa bazata barshi ba indai haka ne. Kankace ido tayi ta kaurara murya 


"Maikudi kada kace min kana da masaniya akan maganar da mutanen nan suke yi"


Ja da baya ya soma yi a tsorace "Ni kuma? Daga shigowata? Uhmm nayi nan akwai mai son ganina a waje" kafin su farga ya fice da sauri. 


Yau da ace Hadir na da lafiya Maikudi sai ya yabawa aya zakinta. Major ma tashi ne dai baiyi ba amma ko ciki daya suka fito da Zayyan sai ya nuna masa yayi kuskure.


"Ku tashi mu tafi" yace dasu gabadaya.


Jume tana kuka matan gida da Badaru suna salati suke basu hakuri.


Babu alamun wasa a fuskarsa yace "Ku bani nambar waya da zamu nemi kwatancen inda Ummin Awwab take. Shi kuma wancan kafin na turo masu kama shi a fada masa nasan iya abinda na turo saboda haka ina bukatar kudin nan...da gaggawa"


Ransa yayi matukar baci ne yaki amincewa da masaukin da Jume tace ayi musu a gidan. Giginya hotel suka yi masauki washegari sai ga Badaru da sassafe ya kira yace zaiyi musu rakiya har Rugar Barkindo.


**********


Saboda yanayin matsanancin zafi da ake fama dashi yau gidan har Ardo suna zazzaune a karkashin katuwar darbejiyar da ta yiwa tsakar gidan inuwa suna taba hira. 


Yammaci ne na asabar Radhiya tasan cewa Zakari zai zo kawo wani sabon maganin ciwon ido da aka rubutawa Mairama a asibitin Bauchi inda yake aikin lab wato dakin gwaji. Gyaran nono ta gama wanda ta cire man shanu sannan ta je tayi wanka. 


Shiryawa tayi cikin riga da skirt ta saka hijabinta iya gwiwa don zuciyarta tana raya mata yau kawun nata zai fada mata abinda idanunta suke ganin yana boyewa...soyayyarta.


Har kofar gidan Ardo aka rako su Major suka firfito kowa da nasa tunanin. A yayin da rayuwa tayi ta garasu ita Mairama kauye ta fado. Kauyen ma ruga da abubuwan cigaba suka yi mata karanci fiye da ko ina.


Fitowarsu ke da wuya sai ga Emzee nan da wani abokinsa sun dawo daga kiwon shanun Ardo. Sanda ce a wuyansa amma shirt da dogon wando ya saka suna ta hirarsu ta samari.


Ba Major da Hadir ba, hatta Mami da Zainab sai da gabansu ya fadi da ganinsa. Wannan banda haske babu ta inda zaka ce ya baro mahaifinsa.


Kawunsa ya hango ya yi saurin barin abokinsa ya taho "Kawu Badaru yaushe ka iso"


"Tare da bakin Umminku nake. Yi maza ka shiga kayi mana iso"


Gaishe su yayi cikin gurbatacciyar hausarsu ta tsantsar fulani ya shiga ya fada musu. Mairama ta auna ta auno ta kasa gane su waye zasu zo nemanta tare da Badaru. 


Radhiya da ta tabbatar zuwan bakin zai hanata sakewa da Zakari ta shiga tura baki. Innawuro tace tayi shimfida sannan aka ce su shigo.


Zainab da Mairama kowacce wai dakewa take yi kada suyi abin kunya a gaban 'ya'yansu amma da sauri suka shiga gidan.


Mairama tana zaune akan tabarma ga sandarta a gefe ta yafa mayafi kalar kayanta. Daga bayanta kuwa babu tantama Alheran Radhiya ce wadda ganin 'yan gayu suna shigowa yasa ta manta da batun Zakari ta shiga washe baki.


Mairama tana ji Innawuro tana yi musu barka da zuwa amma yaran kadai ke amsawa. Manyan kuwa Mairama suke kallo da take ta murmushi a hankali a zatonta babu mai ji tace "Ke su waye ne sai kamshi nake ji"


Mami a gabanta ta zauna tana kuka ta kama hannunta da makanta bata hanata ayyuka irinsu yin fura ba da nata lallausan hannun. Zainab kuwa a gefenta ta zauna ta rungumo Mairama a jikinta. Rasa gane me yake faruwa ita da kowa na gidan suka yi.


Radhiya da ta kurawa Major da Hadir idanu ta saki ihu kamar an tsunguleta.


"Yasin Ummi na ganesu na hoton nan ne"


Mami tasa hannu ta shafa fuskar Mairama tace "Ummin Awwab"


Duk da bata gani sai da idanunta suka kara girma gabanta ya tsananta faduwa, baki na rawa tace "Mami??? Ke duba hotunan akwai wannan a ciki?" Ta fada tana kankame hannun Mami kamar zata kuma tafiya.


"Ai shikenan tunda baki ce a duba dani ba" Zainab tayi maganar da wasa cikin kukan da yaci karfinta.


Mairama fashewa kawai tayi da kuka su ukun suka rungume juna suna hawaye sauran jama'ar wurin suna tayasu mazansu da matansu.[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: Duk dauriya irin ta Ardo sai da ya matse kwalla ganin yadda hatta mazan kowanne ido yayi jajir.


Mairama ce ta fara magana cikinsu "ina Awwab dan Ummi? Nasan ya girma yanzu? Anyi masa aure ne?"


Zahra tace "Mami ashe da gaske dai Ummin Hamma Awwab mu bata sonmu"


Mairama sai dariya ta kufce mata ta daga hannuwa ta tashi tsaye tana cewa "Zahra, kece ko? Ina Fauziyya da Ibrahim abokin fadan wannan yarinyar?"


Fauziyya da Zahra suka matso suna rike hannuwanta tace "kuji min yara yaushe zan ganeku da hannu kawai, haka ake yi" ta fada tana rungumesu.


Muryar wata shagwababbiya da hausarta ke fita kamar mai waka saboda yadda yaren Germany da turanci ya kama mata baki taji tana cewa "Daddy ni kowa baya sona, she even asked for Hamma that is not here"


Ibrahim kallonta yayi ya tabe baki, yarinya yar shekara sha hudu kamar yadda yaji Mami ta fada sai ta dage tana zuba tabara Daddynta yana biye mata.


Emzee kuwa murmushi yayi bai ce mata komai ba. A gidan Ardo shine karami bai saba ganin haka ba shiyasa yadda tayi ya burge shi. 


Mairama sai ta sake dariya ta rasa ina zata kai farincikin da yake cikin zuciyarta.


"Such a sweet voice, wace ce wannan?"


Zayyana dadi ya mamayeta ance muryarta da dadi ta tafi da sauri ta ture Fauziyya da Zahra ta shige jikin Mairama tana cewa cikin tsantsar mamakin wannan 'yar kauyen "Daddy she speaks English too"


Ibrahim ya kwalo idanu a hankali yace "ji min rainin wayo."


Sai kuma suka tsinkayi Radhiya muryar tayi kicin-kicin da fuska tana kallon Zayyana "ke yarinya iya bakinki wallahi, Ummina ma 'yar boko ce har secondary ta gama ehe"


"Zaki fara ko?" Mairama tace tana zaunawa har lokacin Zayyana na jikinta ba ta fahimci dogon zancen Radhiyan ba.


"Ai gara na fada mata gaskiya tun wuri kada ganinki a kauye yasa ayi miki kallon wata local"


Haba wuri sai ya kaure da dariya harda Major. Sai lokacin Mairama ta gama gane su waye a wurin kunya ta kamata. Halin Radhiya sai ita.


Zainab tana cewa ta zo Mami ma tana kiranta sai ta rasa wurin wa zata je. Zainab tace "jeki dai dama ita ce mamanki, ni Zayyan zan dauka nafi kama da maman maza"


Rufe fuska tayi da hannuwanta tana kallonsu a fakaice sai wani blushing take "wallahi kun sani jin kunya...duk sona kuke yi"


Wata dariyar ta basu Mami ta janyo hannunta ta zauna a kusa da ita "haka kika koma Alheran din Awwab? Wannan idan na wuni dake cikina sai ya kulle"


"Indai wannan ce baki ga komai ba" cewar Innawuro.


Kowa a cikinsu yana cike da tsananin farinciki. 'Ya'yansu ma ko da basu gama sanin mahimmancin iyayen nasu a wurin juna ba sun amince wannan haduwa ta faranta ran iyayensu su ma dole su ji dadi.


"Idan kun gama kukan da dariyar ya kamata a gaisa kuma haka" Ardo yace dasu don ya dakatar da zubar hawayen matan.


Sai kuma aka soma gaisawa ana tambayar yaya bayan saduwa. Mairama ta fuskanci bangaren da take jin a nan su Major suke ta saki fuska.


"Daddy ina fata duka kuna lafiya"


"Lafiya kalau Ummin Awwab" yace a sanyaye.


Dan bata rai tayi cikin wasa "abokinmu tun shigowarku banji ko tarinka ba, ai shikenan."


Dif taji shiru ya rasa wurin babu mai cewa komai cikinsu. Hantar cikinta ta kada a sanyaye ta rike Zainab "ba dai....Subhanallahi, ba dai shima"


Wani irin kuka Zainab ta saka tana jin ciwon lalurar Hadir har kokon ranta. Jikin Mairama ya gama saki ta sadakar kila shima babu rai.


Radhiya da Emzee sun gane shine akan kujerar amma su din ma basu iya bata amsa ba. Major ne ya danyi gyaran murya ya soma maganar da kafin ya kai karshe wurin ya sake rikicewa.


"Hadir gashi nan muna tare sai dai tsahon shekarun nan da bamu tare ya yi su ne da paralysis sannan baya iya magana."


Sai da ta dan sami nutsuwa daga wannan tashin hankalin abinda yake ci mata rai shekara da shekaru ta kasa daurewa cikin karyewa da dashewar murya tace  "uhmmm...uhmm nace babansu Karami. Kuna tare ya rasu ko?"


Major da Hadir da dukkansu da suka san labarin abinda ya sami Zayyan daga bakin shi kowa gabansa ya fadi. Mairama da ba ganin fuskokinsu take yi ba ta cigaba da magana.


"Ko baku san ya rasu ba ma?"


"Mun sani Ummin Awwab, muna tare" Major ya amsa da sauri.


Ajiyar zuciya tayi harda guntun murmushi "Alhamdulillahi, da hankalina ba karamin tashi yake ba da tunanin kila ba'ayi masa sutura kamar kowane Musulmi ba. Nace ko irin mutuwar nan ce ta su da yawa. Ance ramin kawai ake guda daya. "


Major Mustapha shiru yayi ya rasa me zai fadawa wannan baiwar Allah. Allah ne ya cece shi a lokacin aka fara kiran sallar Magariba Ardo yace kowa ya tashi. Mazan waje suka tafi wurin masallacin da yake gefen gidan akwai butoci cike da ruwa.


Ibrahim ya dauko daya ya duka a gaban Hadir zaiyi masa. Emzee yana tsaye a gefe yana ta kallonsa.


"Za kayi masa?" Ibrahim ya tambaye shi yana murmushi.


Murmushi Emzee yayi ya gyada kai.


"Gashi" Ibrahim ya bashi butar.


Emzee ya karba "ka tsaya ka rinka gani kada nayi ba daidai ba"


Da taimakon Ibrahim din Emzee ya yiwa Hadir alwala. Kukan zuci yake yana murmushin zahiri. Yau dan Zayyan dinsa ne yake masa alwala.


Bayan sun gama ya kuma cewa shi zai tura shi cikin masallacin. Dadi ya kama Ibrahim don ba karamin ji da babansa yake ba.


Da suka idar da sallah ma Emzee din ne ya sake turo shi zuwa bakin kofar, Ibrahim sai ya tsaya daga waje ya kama kujerar suka daga shi sannan aka sauketa a kasa saboda tudun da yake wurin shigar.


"Sunana Ibrahim Hadir"


Takalminsa yake lalube wannan ya bawa Hadir damar ganin fuskarsa sosai yana murmushi tamkar an ajiye mahaifinsa a wurin.


"Muhammad Zayyan Tureta"


Wani dagen gira Ibrahim yayi "amma Zeezee naji ana ce maka ko?"


Emzee mai wuyar sabo ya sami kansa da kwashewa da dariya "Zeezee kuma kamar wani mace, Emzee ne."


Ibrahim sai yaji yana son zolayarsa "ni dai kafi min kama da Zeezee haka zan rinka kiranka"


"To Surbajo babu damuwa"


Hadir yana jinsu yana dariya a hankali musamman da ya ga Ibrahim yaji dadi yana cewa zai fadawa Umma kakarsa cewa yazo garin Fulani an saka masa suna irin nasu. Emzee ya gimtse dariyarsa suka koma gidan. 


Major ne karshen komawa ya tsaya amsa wayar Awwab da yake ta mita an tafi ba'a jira dawowarsa ba.


"Idan kaso ranar da ka dawo a tare dasu zaka kwana babu mai hanaka"


Daga daya bangaren Awwab yana kwance a dakinsa na hotel a Austria washegari goman dare zai sake wani trip din zuwa Germany ya shafi habarsa.


"Duk dadin ya wuce yanzu. Kun hadu da Ummin?"


"Muna rugarsu a Bauchi"


Tashi yayi zaune da murnarsa "ta tuna ni Daddy?"


"Kai ta fara tambaya"


Wani sanyi yaji a ransa don Allah ne shaida bai taba mantawa dasu ba musamman ita Mairama mamansa ta biyu. Karshen haduwarsu ranar da duka su ukun suke ta kuka daga karshe ya gane halin da nasa mahaifin yake ciki. A wurinsa yaji rasuwar babansa Zayyan mutumin da yake matukar so.


"Daddy Alheran fa?"


"Ita ma baka manta da ita ba?"


Dariya yayi, a shekara goma watanni ne babu tsakaninsu. Babban abinda yafi tunawa da ita shine fada da kuka. Sauran kuwa sai abinda Ummi ta bashi labari. Da kuma hotuna da ta nuna masa nasu lokacin suna tare. Tabon inda ta taba yakushinsa yayi dan siririn layi mai dan duhu daga gefen girarsa ya taba.


"Ban manta ta ba Daddy. Ko za ka bawa Ummin waya?"


"Ka kira ta Mami sai ta hadaku"


**********

Duhun dare ya soma kawo rashin wuta ya sa aka kunna fitilun kwai guda uku aka ajiye a tsakar gidan. Bishiyar tana kada musu iska daidai gwargwado aka zauna mayar da zancen yadda kowa yayi rayuwarsa bayan rabuwa. Wannan karon Innawuro ce ta cewa yaran su tafi gidan Baffa Gide saboda kula da tayi hirar tasu mai taba zuciya ce.


Radhiya tace su taho kowa ya tashi kamar gaske. Suna fita bakin kofar Zayyana tace da Fauziyya "nan gidan basu da wurin da zamu buya"


"A buya kuma, kunyi gamo ne a hanya?" Radhiya ta tambaya tana waige.


Murmushi Zahra tayi yanzu an girma suna jin kunya. Ibrahim kuwa sai yace "kinga magana zasuyi mai mahimmanci idan bamu tsaya munji ba wallahi za'ayi ba mu"


Haba Radhiya ta rike tana jinjina kai "Allah ko? To amma zunubin laben wa za'a rubutawa a cikinmu? Ni dai shekarata goma sha tara da sauran kuruciyata."


Fauziya da Zahra har Ibrahim sai dariya. Emzee da ya saba shi kam bai ga komai ba. Salati suka ji Inmawuro tayi da karfi tana kuka gabadayansu babu babba babu yaro suka dawo suka tsaya a siririyar hanyar karasa shiga cikin gidan. Duhu da girman maganganun suka hana a gano su.


Duk da sun ji yadda iyalin Major da na Hadir suka kare a Kano bai hanasu sake kokawa iyayensu ba. Jin labarin da Mairama ta bayar a karon farko a rayuwarta ta fadi yanayin zaman gidan mahaifinta. Tayi haka ba don ta tona masa asiri ba sai don su Mami su fahimci ainihin yadda al'amura suka kasance mata. Ga wanda bai san Malamijo ba sai a suna bazaka taba hangowa jikokinsa ma talauci da kuncin rayuwa ba. Dabbobinsa tarin arziki ne da shi kansa bai san dashi ba. Ko shanu ashirin ya sayar a yadda suke da girma kosassu zai iya ajiye abincin shekara a gidansa kuma su wadata da abubuwa da dama da bai taba tunanin ya basu ba.


"Abinda ban fahimta ba Ummin Awwab shin gidan da Zayyan ya gina a Kano me ya faru dashi?" Major ya tambayeta


Jan numfashi Hadir yayi da karfi sai da suka kalle shi. Rashin damar bawa Mairama takardun nan kusan shine ya haddasa masa hawan jini. Bai ma san ko Zayyan ya bata na wurinsa ba. Shi dai burinsa wadda aka bashi ajiya ya sadar da ita ga masu hakkinta. Takardun suna cikin wani akwatinsa da yake tunanin babu wanda ya taba bude shi tunda ya koma gida.


A nutse ta warware musu komai da ya wakana tsakaninta da Maikudi. Kunya kuwa ta kama Badaru kamar ya bace daga wurin saboda abinda yayansa ya aikawa matar kaninsu.


Major rai ya kara baci ba don duhu ba sai an ga jijiyoyin kansa da suka dago.


Mami tace "Wallahi mutumin nan sai  munyi da gaske. Ta kowace fuska da zai toshe miki jindadi sai da yabi. Mu fa aure yace kinyi kuma baki haifi dan cikinki da rai ba sannan Radhiya tana hannunsa shine muke aikata mata kudin makaranta ta hannunsa"


"Banten uba" Radhiya tace a harzuke tana kumfar baka daga inda suke tsaye. Hanyar shiga ciki tayi Emzee da Zahra suka rikota.


Idanu sun rufe ta shiga kokawar fuzgewa "ku cikani"


Zainab suka gani a gabansu suna sunkuyar da kai kasa tace duk su dawo su zauna tunda annobar labe ta kamasu.


"Ban hanaki wannan zagin ba" Mairama tace da Radhiya cikin fada.


"Ai wallahi Ummi sai dai fa kiyi hakuri yau daya dai. Hmmm gaya miki ne banyi ba da idan munje hutu fa duk inda ya ganni sai ya rankwasheni ko ya makeni. Inata hakuri, inata hakuri. Wata rana yana rankwashina na tafi a gabansa na dauki Bushira lokacin tana karama na maka ta da kasa. Shine fa ya dena dukana. Yo ashe harda ke bai kyale ba"


"Ya isa haka Radhiya kiyi hakuri tunda magana ta fito ba zamu bar masa hakkin marayu ba" Mami tace da sigar lallashi.


"Uhmhum" kawai ta amsa ba don ta hakura ba.


Badaru ya ari baki ya basu hakuri sannan ya kara da cewa "dole ne na sake neman su mutanen Nijar din. Bana yi musu zaton wadanda rasuwar Zayyan zata sanya su watsar da iyalinsa. Allah Yasa su din ma ba wani abin yaje ya fada musu ba. Don ni yanzu lamarin nasa ya fara bani tsoro kuma."


Sunje sunyi sallar isha sun dawo sai ga yara biyar suka shigo gidan a tare rike da kwanukan abinci. Biyu yaran babban dan Innawuro ne sauran ukun kuma na mai binsa mace. Tun a masallaci lokacin Magariba Ardo ya sanar da dan nasa da kuma mijin 'yar suna da baki ayi abinci na gani na fada.


Farantai da cokula Radhiya ta dauko sai ruwan sanyi da aka aiki Emzee ya siyo a wani shago daga bakin titi Ibrahim ya bishi.


Anci an sha hira taki karewa Innawuro ta sa Radhiya da Emzee tayata gyaran dakunan saukar baki. Su Mami da ko baa fada ba da Mairama zasu kwana. Badaru, Major da Hadir Baffa Gide yazo ya tafi dasu gidansa. Ibrahim da Emzee a dakin Emzee din da yake daga hanyar waje. Sai 'yan matan su hudu a dakin Innawuro. Dreban da ya kawo su shima an sama masa masauki. 


Da asuba kaji goma aka yanka domin yi musu abincin safe. A gaban Hadir Major ya fadawa su Baffa da Ardo cewar auren su Zahra ya matsu suna neman izini su tafi da su Mairama zuwa bayan biki. Radhiya da Zayyan kuma a bar masa su zai nema musu makaranta su fara jami'a a.


"A yi haka kuwa?" Baffa Gide yace yana kallon Ardo "a son ranmu dai suyi zamansu da yaran a tare damu har Allah Yasa duka suyi aure."


"Abinda baffanta Gide ya fada gaskiya ne. Ita ga matsalar idanu ga marayunta gara suna tare damu. Lokaci lokaci idan kun bukaci su zo su kwanan muku biyu sai a turo su"


Ransa dama ya bashi da wahala kai tsaye su bari ya daukesu. Sai dai kam yaci alwashin bazai yarda alkawarin da ya daukarwa kansa na cigaba da kula da bayan Zayyan ya tashi ba.


Sauran labarin da ya kasa bayyanawa jiya na ainihin yadda Zayyan ya rasu ya fada musu. Baffa Habubakari sai da yayi kuka don tausayi.


Cikin damuwa da fami ga gyambon zuciyarsa yace "Bazan taba iya kallon idanun matarsa in bata wannan mummunan labari ba. Tana da hakuri amma ina ganin sai ta tsaneni da iyalina. Yau da nake raye ku ke ganina Allah ne Yayi da sauran kwana na amma Zayyan shine sila." 


Ya nuna Hadir "wannan bawan Allah da lafiya kalau yake wallahi kunji na rantse zaiyi komai don ganin 'ya'yan Zayyan sun koma karkashin kulawarsa. Sai dai shima lalura ta same shi ne da ya cigaba da kokarin kare rayuwata kamar yadda dan uwansa ya fara. Ku taimaka ku barni na kyautatawa bayan Zayyan sannan kuma na saukewa Hadir nauyin da nasan da yana da lafiya bazai taba bari na dauka ba"


Jikkunansu sunyi sanyi da maganganun Major. Ardo ya kira Innawuro yace "kece uwar Mairama kakar 'ya'yanta me zaki ce game da batun da bawan Allahn nan yazo dashi?"


Nazari Innawuro ta soma don abun da yake nema ba karami bane. Mairaman da mahaifinta ya gagara rikewa, dan uwan tsohon mijinta ya tozarta ta yaya zasuyi saurin amincewa bare. Idan a gaba gori ya taso ko wani abu makamancinsa fa. Bafillatani duk talaucinsa akwai pride. Basa son zubar da mutumcinsu gaban kowa saboda babu azo aji dadin takasu.


"To na amince amma Zayyanu kadai zaku dauka. Dalili kuwa kun dai ga irin halin 'Yar Soja wallahi zama da ita akwai dadi akwai wuya. Mairama kuwa bana son nisa da 'yata ko kadan."


Hadir ya kafe Major da ido har ya fahimci so yake ya cigaba da rokonsu. Ai kuwa bai fasa ba yana ta kawo hujjoji.


"Kayi hakuri amma indai ka ga 'Yar soja ta bar garin nan to aure ne ya dauketa" Innawuro tace don ta kawo karshen muhawarar.


"Na ji na amince" Major ya amsa batare da dogon nazari ba.


Baffa Gide ya kalle shi da mamaki "kada kace min aurenta zakayi."


Mafita daya ya hango ya

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment