Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki kira shi maye? Haba kinsan yara sai hakuri ki zaunar dasu mana a zuba musu abincin"


Ummi Mairama ce tayi maganar saboda zata wuce ta hango Salamen. Wani farinciki taji a ranta duk da rashin jituwar dake tsakaninsu tana kallon yadda 'yar uwarta ta chanja. Rashin lokaci saboda shirin biki da kuma hani daga Nene Marka duk da bata san dalili ba ya hanata zuwa gidanta bayan idonta ya bude. Isowarta taji suna wannan rigima da yaran.


Batare da ta dago ba, har yanzu tana duke saboda bayanta da ya amsa garin saurin dukan yaron taji wani uban kamshi mai sanyi da ya mamaye wurin wanda ke fita daga jikin Ummi tace "barni da shegu basu da aiki sai cin abinci. Gudun kwadayi yau sukunbiya na saya musuuuuuu" bakin ya makale ta kasa shiru duk da ta kai karshen kalmar.


Ido ta tsaya gogewa da hannu babu kunya babu tsoron Allah sakamakon gamon da tayi bayan ta dago. Wata take gani kamar kanwarta cikin shiga ta kece raini ta wuce sa'a. Daga sama har takalmin kafarta sai da ta bisu da ido tana jinjina kyau da haduwa irin na suturar da mai ita.

"Mairama? Mairama kece ko dai kama ce?"


Sassanyan murmushin nan nata mai kara kawata kyakkyawar fuskarta ta saki "Adda Salame nice mana"


Tsananin mamaki bai bar Salame ta dakata haka nan ba sai da ta ciro hannu tana yawo dashi a gaban fuskar Mairama wadda farin gilashinta ya karawa kwarjini.


"Kina ganin me nake da hannuna?" Tace baki na rawa.


Ummi sai ta kama hannun ta rike. Nata yayi laushi sosai saboda gyaran da akayi musu a salon. Na Salame kuwa sai dai ayi shiru ayi kurum inji dogaran sarki. Kanta da lamba...a daiyi shirun kawai. 


"Adda idanuna sun bude cikin hukuncin ubangiji. Zamuyi magana dai ina da baki" ta fada tana yin gaba da sauri.


"Banten uba, kai!!!" Salame tace a gigice gabadaya ta kasa gane me take yi. Ko dai gizo ne tayi mata ba ita din bace a zahiri? A'a Mairama dai kanwarta ita ce da wannan shigar ta chanja tayi kyau haka kuma wai TANA GANI? Zuciyarta bugu take yi kawai kamar wadda tayi tsere ga bakinciki da takaici sun taru sunyi mata rubdugu.


Zaninta karamar yarinyar ta sake ja tayi nisa a tunani taji cikin kuka tana cewa "Umma, umfafa ta kare"


Wata mahaukaciyar mangara ta kaiwa yarinyar wadda take rike da zanin leshin da dama da kyar ta hade shi a jikinta saboda ciki. Yadda yarinyar tayi gaba ta fadi haka ta tafi da zanin babarta Salame a hannu. Sai ga Salame matar Alh Indararo a tsaye da dan sket dinta na ciki ya fita hayyacinsa saboda tsabar jigata da kodewa. Dan lace din da akayi masa cin baki dashi ya barke yana reto a jikin kafafunta wurin gwiwa bari daya ne dinkin bai gama fita ba. Kuma gashi na silk mai santsi wani zare zare nan duk ya fara fita daga inda dinkin lace din ya fita. Bata ma ankara da wuri ba sai da babbar 'yar tace "Umma ina zaninki?"


Baki ya goge da ashar har ta gama hado shi zata lafta mata ta ga mutane sun zuba mata ido wasu suna ta dariya. Sai a lokacin ta hango shi a hannun mai kuka. Kafafunta ta kalla kunya matsananciya da muzanta suka dirar mata. Ga ciki ga dan lace suna neman kayar da ita haka ta tafi da uban sauri ta finciko zanin ta daura mutane suna ta dariya. Duk masifarta sai ta rasa abin cewa ta shiga neman wurin buya saboda kofar gidan babu wani wurin wucewa an cika makil.


Lokacin da Radhiya ta fita Awwab yana tsaye a gefe suna magana da daya daga cikin mutanen Nijar din amma da yake tun zuwansa hankalinsa gabadaya yana kan kofar yana fatan fitowarta shiyasa tana leko da kanta ya hangeta. Ajiyar zuciya ya saki da ganin fuskar da yake matukar so da kauna. Ita kuwa sai waige waige take tana yi tana komar da kanta saboda mutane. 


Alh Sidi ne ya fara ganinta daga inda suke tsaye ya tabo dan uwansa Alh Ghoumar yana murna "kaga Alheran"


Alh Ghoumar ya juya shima yayi sa'ar ganinta "Allah mai iko, ka ga kamaninta da tamu Alheran din?"


"Dalilin da yasa na ganeta ma kenan"


Tana wannan leken taji an kamo hannunta an ja ta gaba. Zata yi magana ta ga Emzee ne. Ita fa bata san da wasu baki ba Hammanta tazo gani. Yana rike da ita bai saketa ba sai a gabansu. Kanta ne ya nemi juyewa dama ga yara sun yanyame motocin saboda kyaunsu ga kuma su kansu mutanen da yawa suna ta fitowa daga mota. Kukan Mammee da ta rungumeta har yafi na dazu domin yadda Radhiya take diban yanayi sosai da yayarta. Murmushin da Radhiya tayi ya kara karya mata zuciya saboda lotsawar kumatun sak na yayarta ne.


Emzee yana yi mata bayani su ma suna ta yarensu suna dan hadowa da Hausa saboda jikokin nasu. Fada musu yayi su dan kara hakuri suka ce babu komai sun san gida ne na taro gashi ba'a san da zuwansu ba. Radhiya dai yau harda jin kunya yadda mutanen nan dukkansu suke ta rungumarta matan. Mazan ma ita dai taji wani ya kamo hannunta babba ne kuwa abokin wasan Zayyan sai dai kafin ta motsa taji wani tattausan hannu ya janyota baya sannan ya dawo gabanta ya tsaya tsakaninta da mutumin. Babu mai fahimtar mai Awwab yayi ko dalilinsa sai wanda yasan tsakaninsa sa Radhiya. Abinda yaji ya ratsa shi kuwa shima sai da yayi nadamar taba hannun nata. Daga inda yake tsaye yana kallon wannan runguma zuciyarsa ta tsinke da yaga mata sun kare kada a fara da maza. Kishin da ya yunkuro masa ba kadan bane. Allah ne Ya taimake shi ya taho da wuri yau da sai anyi abinda zai mutu bai manta ba, wato Alheran dinsa a jikin wani. Babu ruwansa da alakar dake tsakaninsu tunda ya tabbatar babu muharraminta ciki idan aka cire kakaninta biyu Alh Ghoumar da Alh Sidi. Sauran duk wanda ya tabata ya taba masa mata ne. 


Ummi da kanta ta rufo mayafi ta leko kiransu. Mutane suna darewa wadannan jama'a guda wadanda dukkansu kowa ka kalla kasan ya taka wani abu a duniya na arziki mazansu da matansu suka shige inda aka nuna musu. Tabarmi ne sababbi manya aka shimfide musu suka zazzauna babu girman kai da jin su din wasu ne. Mammee ta rike Ummi tana ta sharar hawaye. Rabon da su hadu shekara goma shatara tun ranar sunan Alheran Radhiya.


Wurin minti goma ana ta matsar kwalla Ummi an fama mata rashin gwarzon namiji masoyin kwarai Zayyan uban 'ya'yanta.


"Mairama yaya bayan saduwa? Kiyi hakuri. Don Allah ke da 'ya'yan nan kuyi hakuri" Alh Sidi yace yana duban su duka su ukun.


Salame da kunya ta korota sashen mazan gidan nasu taci karo da wannan abin al'ajabi. Wurin gabadaya wani irin kamshi yake yi. Sakato tayi tana kallon mutanen. Maza biyu cikinsu wato su Alh Ghoumar sun dora rawaninsu na al'ada a kawunansu. Sauran kuwa sai ka rantse wasu larabawa ne. Buzaye ne gaba da baya da kudi ya kara gyarawa rayuwa suka kara fitowa. Bakinta bai iya neman abin fada ba na nuna mamaki taji muryar marainiyar wayonta Mairama.


"Don Allah ku dena bamu hakuri ba laifinku bane. Kaddara ce kawai da kuma abinda Kawun yaran nan yayi mana"


Kallo ta bita dashi suna zaune tsakiyar mutanen da ita da 'ya'yanta. Zuciyarta har wani girgiza tayi da ta kalli Emzee. Itama sai ya tuna mata da nata tsohon mikin na son mijin kanwarta. Babban abin da ya daure mata kai shine sanin da tayi Mairama ta makance suna kauye ita da gayyar yaranta. To tana ina ne ta warke kuma suka yi fes dasu ba yadda take tsammanin ganinsu ba? Ga wani kyakkyawan saurayi tsaye a gefe ya tokare kafarsa daya da bango shi kuma ko waye? Tambayoyi take ta yiwa kanta tana neman amsa ido rufe.


 "Matsa a wuce" taji ance daga bayanta. Matsawar tayi kuwa aka fara shigowa da tray-tray na kayan abinci da abubuwan sha. Duk abinda za'a tanada Innawuro ce ta kwance gefen zaninta ta bada kudi masu yawa har su Yadikko sai da suka yi mamaki. Bafillatana tana zaune haka cikinsu ana dariya ashe dukiya ce a jikinta. An dibar musu cikin abincin bikin sannan aka siyo tsire da balangu mai yawa da lemukan roba da ruwa masu sanyi.


"Shiga ku gaisa mana 'yan uwan Marigayi ne daga Nijar" Hajjo tayi maganar tana wucewa ciki ita da su Nene Marka suka gaisa da bakin aka gabatar musu da abinci. Kamar zata hadiyi zuciya ta juya batare da ta cewa kowa uffan ba ta bar wurin. Su dinma babu wanda ya kula da ita suna murnar ganin juna.


"Bari mu baku wuri kuci abinci don Allah. An tafi kiran babana sai ku gaisa"


"Ki bar mana yaran idan tashi zaki yi"

Wata mata mai faram faram tace cikin hausar da tafi kama da ta Kanawa. Ilai kuwa ashe aure ne ya kaita Nijar ita ce amarya cikin matan Alh Sidi amma mutuniyar Kano ce.


Ummi tana murmushi tace dama wa ya aiketa. Inda Awwab yake tsaye ta kalla "dan Ummi zo muje kaci abinci"


"Bazai ci cikinmu ba? Tare muka taho shima bako ne" saurayin da suke magana dazu dashi yace yana dariya.


"Wannan naku ne kada ka damu dani" Radhiya ya kalla ta wani nutsu kamar ba ita ba "taso ki zuba min".


Ummi na jin haka tayi gaba abinta tana murmushi suka tashi aka basu wuri domin su samu su sake musamman mazan. Emzee ne kawai bai tashi ba yana aikin amsa musu tambayoyin da suke yi masa game da rayuwarsu.


Kofar da zata fitar dashi waje Awwab ya bi ba wadda zata sada shi da ainihin tsakar gidan ba. Radhiya sai tabi bayansa suka fito yayi hanyar inda ya ajiye tasa motar. Baya ya bude mata babu musu ta zauna shima ya zauna a gaba bangaren dreba kafafunsu suna waje. Lallen kafarta ya kalla ta saka daya daga cikin takalman da ya kawo mata tayi matukar kyau.


"Shigar da kafarki ciki"


Zumbura masa baki tayi sannan ta dauke kafafun.


"Me yasa kika dena daukar wayata yau kwana biyu?" Ya tambayeta da wannan deep voice din tasa.


Shagwabe fuska tayi kafin tace "to ba kaine ka dena kirana ba saboda ka koma Katsina wurin....wurin"


Fada yaso yi mata na hora shi da tayi ta hana shi jin daddadar muryarta idan tana shagwaba ko ta hado wani shirmen nata sai ya kasa. Ganinta kawai da yadda tayi masa kyau ya kawar da komai.


"Wurin wa?"


Harara ta galla masa tana juya idanu ita anyi mata laifi sai dai gabadaya abin da tayi sauke masa kasala yayi "ai ka fini sanin wa nake nufi. Wurin My G mana ni kuma ka manta dani"


Bushewa yayi da dariya damuwarsa ta ragu sosai. Babu wani abu da yake tunani sama da mallakar wannan yarinyar da take gabansa a matsayin matar aurensa.


"Kema G dinki ce ashe"


"A'a wallahi" tace da sauri, hakan ma yana kara bashi dariya har wani kada hannuwa take yi "taka ce kai dai"


"Yanzu dai kishin dreba kike yi" ya dage mata gira "Allah sarki kanwata ta kare miki gashi dreban nan bazai barki ba sai kin amsa sunan matarsa"


Tsuke baki tayi tana dariya kunya ta rufe ta. A hankali ta daga kanta suka hada ido tayi saurin rufe fuskarta da hannuwanta. Yatsun sun sha lalle kamar ya rikosu.


"Schatzi"


"Uhummm"


"I miss you"


"Zaka sa naji kunyarka Hamma"


"Kuma I love you"


Mayafi tasa ta rufe fuskar yanzu tana so ta tashi ta gudu tana gudun kada yace ya hanata.


Langabe kai yayi yace "Baki bani amsa ba ko daya. Kenan bakiyi missing dina ba kuma ba kya sona" 


Radhiya ba wayo yana fadin haka ta dago da sauri "ba fa kaji nace haka ba"


"Kina son nawa ne? Ba ni kadai nake abuna ba"


"Kai Hamma Allah bance ba" ta fada kamar tayi masa kuka.


Shi kuma ya sami na yi ya cigaba da cewa "do you love me?"


"Eh mana" 


Yadda maganar ta fito a bazata haka itama ta fita daga motar harda tuntube ta kutsa ta cikin mutane tana jin kunya ta barshi da yi mata dariya.


Wayarsa ce tayi ringing sai a lokacin ya kula ashe Mami ta kira shi sau biyar. Sunyi da ita suna zuwa zai hadata da Ummi tunda sun kasa samuta ya manta shaf. Bai yi tunanin amsawa ba yana gudun fada ya rufe motar ya koma ta bangaren da bakin suke don ya bawa Emzee ya kai mata. Ko da ya shiga ma sai yayi sa'a tana wurin dasu Nene tana basu labarin makantar da tayi da warakarta kwanaki kadan da suka wuce. Wayar ce ta sake shigowa ya mika mata yana cewa Mami ce.


Karba tayi ta kara a kunne da sallamarta sai dai maimakon muryar Mami sai taji Fauziyya tana kuka sosai tana cewa "Hamma ka dawo gida ba lafiya"


Ummi na jin haka ta mike tsam ta fita ta kofar waje saboda ko ina na gidan hayaniya akeyi ta sami gefen wani gida da bishiya a jikin gidansu ta tsaya. Hankalinta a tashe yake tace "Fauziyya me yake faruwa?"


Gabanta ne ya fadi. Da farko kamar bazata ce komai ba sai da Ummin ta soma yi mata fadan cewa itama babarsu ce.


"Ummi tun dazu Mami da Zahra suke kuka. Bansan me yake faruwa ba amma har Umma Hussaina da Mummy sunzo sunyi fada da Mami"


Zantukan Fauziyya sun daure mata kai matuka ta kasa fahimtar me yake faruwa kamar yadda itama Fauziyyan bata gama ganewa ba. Kwantar mata da hankali tayi tace mata gobe zasu taho in sha Allahu da Awwab.


Da ta koma su Mammee suka ce zasu tafi Kano su kwana biyu sannan su koma Nijar. Ummi bata ji dadi ba. Niyarsu matan su kwana a wurinta tun farko amma sun fuskanci hakan wahalarwa ne gareta saboda yanayin biki da ake yi a gidan babu masaka tsinke.


"Yara muka zo gani dake kuma Alhamdulillah mun gani duka kuna lafiya. Sai dai muna son muji yaushe ne zaiyi muku daidai mu turo ku taho Niger domin ku hadu da sauran 'yan uwa"


"Ba don bikin da zamuyi a Katsina na yara har biyu ba da tun yanzu zaku tafi dasu" Ummi tace tana kokarin boye damuwar da ta shiga tun bayan wayarsu da Fauziyya.


"Kema sai kinje Mairama ba yaran kadai ne namu ba" Mammee tace sauran suna dariya.


"In sha Allahu muna gama bikin zan sanar daku Mammee"


Sallamar Malamijo ce ta katse zancen nasu. Bai yarda ya zo wurinsu ba sai da ya shiga cikin gidan yaje ya chanja kaya. Kayan da zaisa gobe na daurin aure ya sako saboda motocin da ya gani sun tayar masa da hankali. Ya saka babbar riga yana ta baza hannuwa. Saboda karfin hali ya sami irin farin abin nan da akan gani malamai sun ninka sun daure hularsu dashi na ustazai shima haka yayi ya fito ko karya babbar rigar baiyi ba don ya kara cika ido.


Wurin bakin yaje ganinsu ya sake tayar da hankalinsa yasan lallai ba bakin rainawa bane.
[7/4, 7:39 PM] +234 806 334 4334: **********

Yau falon na Alh Baba ya cika sosai sakamakon yawan wadanda aka zauna dominsu. Jikokin da abin ya shafa suna cikin gida sai an gama da iyayensu za'a nemesu.


"Wace magana nake ji haka cewa jiya Gambo taje gidan Mustapha da Husaina yau kuma da Azumi ana rigima?"


Babu wadda ta iya yin ko da tari ne saboda kwarjinin iyayen nasu. Alh Baba ya kara hade rai yace Mami ta fada masa me ya faru. Kai a kasa ta zayyane masa komai. Gabadayansu sun nuna fushi akan abinda kannen nata suka yi mata tare da Azumi.


"Naga alama a kokarina na son inganta zumuncin zuri'ata al'amura suna kara tabarbarewa. A zamaninmu dai mace ko namiji sai dai ace ga wane za'a hadaku aure kuma ayi auren a zauna lafiya. To amma na kula daku da 'ya'yanku abin ba haka yake a wurinku ba"


Baba Karami ya kalli su Mummy "Gambo baku kyauta ba ko kadan abinda kuka yiwa Hassana har gida kuma a gaban 'ya'ya. Ko bata girme ku ba ai ta ci darajar auren yayanku"


Sun hadu sun yi musu fada akan abinda ya faru sannan Alh Baba yace to tunda abu ya koma kowa kanta ta sani da 'ya'yanta zai kira yaran ya sake tambayarsu. Duk abinda suka yanke shikenan.


Kana ganin yadda yake magana kasan akwai bacin rai sosai a tattare dashi

"Zabi ya rage tsakaninku da 'ya'yanku bazan sake saka muku baki ba balle inyi bakin jini"


"Alhaji kayi hakuri don Allah. Muma kaine ka aurar damu in sha Allahu duk yadda kace akansu haka za'ayi" Daddy yace sauran 'yan uwansa suka nuna amincewarsu.


Alh Baba sai kuma yaji nauyin yadda duk da yafi kowa sanin cewa son kansa ya nuna akan komai amma gabadaya yaran da iyayensu kai hatta kannensa kowa ya amince ne domin biyayya a gareshi. A tunaninsa wannan hadin kara dankon zumunci zaiyi amma zamani ya chanja. Bai manta ba daren jiya da Baban biyu yake ce masa auren hadi yanzu a cikin goma daya akan samu ana zaman lafiya. Biyu ayi zaman hakuri sauran bakwai din kuwa duk mutuwa suke yi wani lokacin ayi rabuwar da zata shafi har jikoki. Ya bashi shawara cewa idan jikokinsu sun hada kai a junansu a barsu suyi aure haka kuma masu nema a waje su ma a basu dama.


Haka suka shigo masa Zahra, Ghazalatu da Fauziyya idanunsu a kumbure suna kan kuka ma. Awwab kuwa kallo daya yayi masa ya dauke kansa. Damuwa da bacin rai sun rufe kyakkyawar fuskar yaro mai yawan fara'a da wasa da dariya. Anya ya yiwa 'ya'yan Hassana da Mustapha adalci kuwa? Yara har uku yana neman tauye musu hakki akan abinda ba addini ba. Don dai kawai Baban Biyu yana da kawaici amma ace jikokinsa har hudu duka ya nuna shine mai ta cewa akan makomar rayuwarsu kuma nasu kakan ya nade hannu ya kyale shi.


"Matso nan Fatima" ya yafito Zahra da hannu. A tsorace take ta tashi ta koma kusa da kafarsa ta zauna. Ya kira Fawaz shima yazo ya zauna daga daya gefen nasa.


"Kana son auren kanwarka?"

Shiru Fawaz yayi na 'yan dakiku kafin ya girgiza kai yace baya so. Haj Azumi tayi gajeren murmushi. Tun a gida tayi ta nanata masa idan yana son kansa da arziki kada ya yarda a aura masa yarinyar da bata sonsa. A nasa bangaren shi dai baya kin Zahra amma kuma ba soyayya bace tsakaninsu shiyasa bai ga amfanin aurenta ba.


Alh Baba ba haka yaso ba amma dole ya karba tunda a gaban iyayensu ake yi.

"Fatima waye shi wanda kike so din?"


Kasa magana tayi ya mayar da tambayar ga Major. Shi din ma bai wani san kan zancen sosai ba shiyasa Awwab ya fada masa yadda suka yi da ita dazu.


"Yanzu zuri'ata zan hada da kabilu?" Yace cikin wani irin yanayi.


Baba Karami yayi saurin gyara murya "Alhaji kada mu koyawa yaran nan kin 'yan uwansu musulmi saboda bambancin yare da al'ada. Mun sani cewa babu haramci a tarayya dasu sai ma kara karfin alakar dake tsakanin musulmi da dan uwansa."


"Haka ne, idan mun tashi daga nan a kira shi a waya yazo da magabatansa idan yana sonta. Daga yanzu na soke maganar aurenta da Fawaz."


Mami harda hawayen dadi. Lallai mai hakuri shi yake dafa dutse yasha romonsa. Bata taba tunanin zata sauyi irin wannan game da auren Zahra ba sai gashi ya samu cikin ruwan sanyi.


"Fauziyya da Bilal fa? Akwai wani korafi makamancin haka tsakaninsu?"


Bilal yaro mai tsananin kunya yace indai bata da wanda take so yana son aurenta. Fauziyya ma bata bashi kunya ba tace ta amince. Haka ya sanya farinciki a zukatansu.


"To uban gayya da aurensa ya janyo mana wannan tone-tone. Na baka izini Muhammad ka nemi amincewar Ghazalatu da waccan yarinyar ayi aurenku rana daya babu wadda zata jira wata"


Yana dire maganarsa Ghazalatu ta dago jajayen idanunta "Alhaji ina da magana"


"Ina jinki"


"Ni dai na hakura ko wani zaka zaba min zan amince amma banda Yaya Awwab"


Tsawa Daddy Haroun ya daka mata ta fashe da kuka. Tana da kishin da bata jin zata iya zama da Radhiya da take gani kamar wata kaskantacciyar yarinya. Amma ba wannan ne ya janyo mata kin amincewa ba sai zugar mahaifiyarta wadda itama Hussaina ce ta ingizata kan cewa su hada Ghazalatu da nata dan Nura. Hussaina gani take ta sami dama da zata dandali arzikin gidan Gambo yadda ya kamata. A zahiri Gambo da Mami sun fi ta rufin asiri. Sai dai bata sani ba Mami a nata gidan kafin Major ya sami lafiya har ya fara aiki guminta ake ci. Ita kawai gani take suna da kudi ne suke son hada nasu 'ya'yan ita ko oho. Mummy Gambo an hau dokin zuciya ba bata lokaci ta amince bayan sun bar gidan Mami a jiya.


"Saboda ance ya auri wadda mahaifinsa ya nema masa?" Baban Fawaz ya tambayeta.


"Ni dai kawai bana so ne yanzu"


Alh Baba yace "babu wanda zan tilasta a cikinku na gama wannan yayin. Tunda ba kya so Allah Ya kawo miki naki rabon. Kai kuma ku gama magana da waccan ina bukatar amsa da wuri" yana kaiwa nan yace duka ya sallamesu su tashi su tafi. Ghazalatu kuka kamar ana yankar naman jikinta amma tasan halin Mummynta da masifa. Idan ta kuskura ta komawa Awwab sai taji babu dadi. Hussaina duniya shar ta kira Nura tace ya fara yakin neman soyayyar Ghazalatu ita ta gama nata aikin.


Awwab bai jira kowa ba ya fita ya bar gidan. Jin kansa yake kamar an zare masa wata kaya da ta tokare shi. Lallai zuciya bata da kashi. Bai tantance zafin so ba sai akan Alheran. Kinsa da Ghazalatu tayi ko kadan baiyi masa ciwo ba don tunda Mummy taje gidansu sau biyu tana cin mutumcin mahaifiyarsa yasan ko ya aureta wani kaso mai girma na kimarta ya riga ya sauka daga idanunsa.


Sallar magariba ya tsaya yi kafin ya shiga gidan. Shigarsa tayi daidai da isowarsu Mami a motar Daddy. Zahra ce ta tuku su Fauziyya na gaba su Mami na baya. Idan ka ga Zahra fuskarta tamkar wadda aka baiwa kujerar Makka. Murmushi ne yaki tafiya kamar an zana mata shi har tsokanarta Daddy yayi yace shima sai ta nemi amincewarsa sannan zai kira Imam Abdulwahab mahaifin Raji.


Kunya taji ta ruga cikin gidan kai tsaye ta tafi dakin Mami. Ummi ta gani akan sallaya ta fada jikinta tana ta dariya.


"Zahra me muka samu irin wannan murna haka"


"Ummi Alh Baba ya amince"


"Da me?" Mairama ta tambayeta tana tayata murna tun kafin taji.


Sallamar Mami yasa ta kasa cewa komai ta tashi ta koma nasu dakin da tsalle. Sai da Mami ta idar da sallah ta fada mata yadda al'amura suka juya. Ummi bata ji dadin fasawar da Ghazalatu tayi ba kuma ga dukkan alamu Mami da 'yan uwanta basu shirya ba. Indai haka ne kuwa to babu makawa Radhiya ma bazata auri Awwab ba. Meye ribarsu ayi auren da ya taba zumuncin iyaye.


Fauziyya da Zahra ma sallah suka shiga yi suka sami Radhiya ta dukunkune kanta ta cure wuri guda tana baccin wahala. Tayi kuka ne har ya saka mata ciwon kai shine bacci ya dauketa. Zayyana ta fito daga bandaki ta yayyenta kowacce da murmushi a fuskarta. Zahra ta rungumeta tana dariya itama tana tayata ta tabbata abinda yasa su kuka dazu ya wuce. Ihunsa ya tayar da Radhiya da kyar ta iya bude ido sun kumbura tayi musu sannu da zuwa.


Fauziyya ta tuna cewa dazu maganganun su Mummy su ma daga dakin Awwab sun ji bare kuma ita da suka bari a nasu dakin. Sai taji tausayinta ya kamata "kinyi sallah kuwa ko sai nazo nayi miki balotelli?"


Murmushi tayi kanta kamar ya tsage ta daure "da almakashina a jaka"


Dariya suka yi su duka yanayin dakin yana chanjawa daga shiru shiru zuwa na 'yan mata wadanda ke tsaka da jindadi. Da bin bango Radhiya ta je tayi alwala ciwon kai yayi tsanani ga zazzabi. Bayan ta idar Zahra ta taba wuyanta ganin duka jikinta yayi la'asar.


"Radhiya baki da lafiya kika zauna shiru a daki. Bari na karbo miki magani"


Da saurinta ta fita taje dakin Mami tana tambayar panadol. Ummi sai da taji babu dadi tasan halin Radhiya da saka abu a rai. Karshenta kuka ta rinka yi ya janyo mata zazzabin da ciwon kai.


"Nemo min Awwab yazo ya kaita clinic dai. Ga

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment