Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aiken da akayi mata ko ta bi bayansa.


"Ji min shirme Radhiya kina tsaye ashe kina kallonsa maimakon ki kaishi wurin Mairaman. Dauko filas din wajenta in zuba masa kunun nan da zafinsa"


Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta shiga dakin. Yana zaune daga gaban Mairama tana tambayarsa mutan gida da hanya.


"Mamaki nayi da naji muryarka fa. Amma dai kowa lafiya ko?"


"Ummi kada ki damu lafiya kalau."


Dagowa yayi yana kallon Radhiya tana neman flask din ruwan zafi. Yana gabanta amma da yake hankalinta yayi nisa bata kula ba. Ummi ce tace "wai har kin dawo ne?"


"Ban je ba, Yadikko ce tace na dauko flas za ta zubawa Hamma kunu"


"Yi maza ki kai mata kije ki siyo min in samu yayi tofin kafin ya fita"


Ita Awwab ya tsare da ido yana tambayar Ummi "aikenta kika yi?"


Bayani Ummin tayi masa yaji dadi yana fatan Allah Yasa a dace. Da ido ya kalli Radhiya yana nuna mata ta zauna ta girgiza kai.


"Bari naje na siyo Ummi ina zuwa"


"Daga zuwanka, barta ba nisa bane da wurin"


Tashi yayi ya sake cewa shi zaije. Ummi tace to ya bari ko ruwa yasha kafin ya fita. So yake kawai ya tashi ya samu kebewa da Radhiya don ba da niyar kwana yazo ba. Gabadaya ya shagala da kallonta. Takwanshe kafafu yayi ya tallabe kansa da hannuwansa da ya dora akan cinyoyinsa ya zuba mata ido. Hanata sakat yayi ta kasa dago kai saboda tsoron idanunsa take yi yadda suke matukar tasiri a kanta.


Wayar Ummi da ta soma ringing ce ta sa ya dena kallon nata na dan lokaci ta tashi da sauri ta fita. Shi ya mikawa Ummin wayar ganin sunan Mami shima ya tashi ya gudu yana dariya bayan ya amsa mata kiran ya saka mata a kunne.


"Dana kika biyo da kiran nan ko? Yanzu ya iso bai yi rabin awa a gidan nan ba"


Sai da Mami tayi dariya tace "nifa ina jin mu saka ranmu a inuwa kawai yaran nan sun gama mana komai sai dai ma su jira mu"


Labarin yadda suka kwashe dashi bayan ya dawo daga sallar asuba tare da Major ta bata suka rinka dariya. Yana shiga gidan yayi sa'a tana falo shine yake fada mata zaije Sumaila. Da ta tambayeshi ko lafiya shine yace wai Alheran bata da waya kuma ya san cewa irin haka ne yake sa 'yan mata su ji babu dadi sa'anninsu suna da abu su basu da shi.


"Akwai waya a hannun Ummin taku ai"

Ita ce amsar da ta bashi.


Sosa keya yayi yace "So nayi na bata a matsayin gift na gama secondary school"


"Ina ta Karami da Ibrahim? Duka tare suka gama"


"Ibrahim yana da waya. Emzee kuma zan saya masa. Tunda ita ce babba shiyasa zan fara bata"


"Ba sai kaje Sumailan ba, nan da 'yan kwanaki zaka gansu sun zo biki"


Fuskarsa tamkar zaiyi kuka yadda ta dage tana neman kure shi. Tsokanarsa ta cigaba da yi daga karshe dai yace mata wai kewar Ummi ke damunsa.


"Kewar Umminka kuwa duk gidan nan banga mai cike maka gurbinta ba. Sai ince a dawo lafiya ko"


Amsar tayi yadda yake so amma kuma ta makale masa a rai. Ko dai Mami ta gane wani abu ne? Kai da wuya shi yasan baya yin yadda kowa zai san yana yiwa Alheran zazzafar soyayyar da take nukurkusar zuciyarsa.


Daya motar ya dauko Mami tana korafin ranar zai takura mata yace tayi hakuri bazai kwana ba. Jinsa kawai tayi sai kace Katsina zuwa Sumailan tafiyar awa daya ce. To gashi dai a gidan Malamijo tare da Alheran Radhiya.


Yana fitowa har ta kusa kure layin nasu ya bi bayanta da sauri. Sai da ta dan tsorata da taji muryarsa da ya kira sunanta. Ta juyo a nutse yayi mata nuni da gidan da hannunsa.


"Ki jirani a wurin zaman nan ina zuwa"


Wani salihanci ne ya saukar mata a yau din, babu musu ta koma ta zauna akan tudun nan tana jiransa. Hamma Awwab ne ya tambayeta ko zata aure shi. Tunanin maganar kawai sai da ya sanya zuciyarta kadawa tsigar jikinta ta tashi. Kankame jikinta tayi tana jin yadda farinciki ke mamayarta.


Magana take yiwa kanta ita kadai tana murmushi "lallai ta kare min, dreba kuma nake so"


Shagon babu nisa bata dade ba Awwab ya shigo da katan din ruwan roba mai manyan robobi. Za ta tashi yace ta bari ya kaiwa Ummi ya dawo.


Gabanta ke dukan uku-uku wannan karon da ya kuma dawowa. Zaman me zasuyi take tambayar zuciyarta. Zance!


Bai dauke idonsa daga kallonta ba har sai da ya zo gabanta ya durkusa a tsugunne. Kallon kofofi biyun da za'a iya shigowa wurin a same su take yi ta shiga gidan da ta fita tana addu'ar kada Allah Ya kawo kowa.


"Amsar tambayata nake jira"


Rufe fuskarta tayi da hannu sai murmushi da yake manne akan kyakkyawar fuskarta.


Ba burinsa bane ta chanja daga Alheran din da ya sani don kawai matsayinta a wurinsa ya chanja. 


"Na takuraki ko?"


"A'a"


Tsoro ne ya dan darsu a zuciyarsa da sauri yace "Baki amince ba ne?"


"A'a"


"To menene?"


Kofofin ya ga tana bi da kallo kafin tace "Hamma ni kunya nake ji kada wani ya shigo"


"Sai ki bani amsar da nake jira in tashi. Nima bakiji kafafuna ba sun fara sagewa" ya kare maganar yana marairaice mata.


Tsokanarsa ta fara yi kawai don ta ja nasa rai "kasan sojoji an sanmu da dauriya ya kamata kaima ka gwada jarumta ko na rabin awa ne"


Idan ta kara minti daya yana jin kila zama zaiyi kawai a wurin ya lankwashe kansa gefe "habaaa mana"


"Na amince" din da yake jira ta fada kamar mai rada ta rufe kanta tsaf baya ganin komai a fuskarta. 


Tashi yayi ya zauna a gefenta a kan tudun "wahhhsh, da kin kara jan lokaci sai dai ki daukeni idan mun tashi"


"Kai" ta waro ido tana dariya. Ta ina za ta dauke shi.


"Seriously, sai ya tuna min da punishment din primary dinmu a Sokoto. Frog jump haka kawai don a wahalar da mutane mu kasa tafiya"


Da yake taji mugunta ta sami abinda take so sai dariya "yanzu harda zaman babur akeyi yafi frog jump wahala"


"Bana fatan sanin yaya yake tunda ya saka ki wannan dariyar nasan ba abin kirki bane"


Gyara zama yayi sosai ya kira sunanta domin yana son suyi magana ta nutsuwa da fahimtar juna "abinda zan fada miki ina so kiyi masa kyakkyawar fahimta kinji" ya kafa mata ido.


"To Hamma"


Nannauyan numfashi ya sauke saboda mahimmancin maganar da yadda ta rinka cin ransa har ya kasa zama dole ya biyota ayita ta kare.


"I love you Alheran Radhiya, I miss you a duk lokacin da kika bacewa ganina. Da zan iya da na dora hannunki kinji yadda kike hana zuciyata samun nutsuwa saboda tunaninki"


Tamkar ana zubawa jikinta ruwan dumi haka take jin saukar kalamansa suna kwantar da duk wani abu da yake yawo a ranta sai shi kadai da tunaninsa.


"A cikin kwanakin nan da na kara saninki na fahimci kina da kishi" gefensa ta dan kalla kamar zata yi magana sai ta fasa. Tabbas tana kishinsa, kishi ba na wasa ba kuwa "gashi ni kuma na hadawa kaina zafi ina zaman zamana. Ban san inda zan kai mata biyu ba amma Alheran bazan iya rabuwa da Ghazalatu ba don ina sonki"


Sake kallonsa tayi sai ya ga kwalla ta soma taruwa a idonta. Har cikin zuciyarsa yake jin komai na kanwar tasa. A zahiri zai iya boyewa amma a zuciyarsa yasan soyayyar gaskiyarsa tana hannun Alheran "kada kiyi kuka please. Ban zo gareki ba sai da nayi ta tunanin what will be the best for the three of us. Look at me!"


Umarnin yayi mata tsauri a yanzu da ya gama da zuciyarta amma bata iya ketarewa ba ta dago idanunta hawayen zuna zubowa batare da sauti ba. Da zai iya da ya rungumeta sai dai ko da suka tashi nesa da gida Mami na aiki sauran tarbiyarsu ta koma ga mahaifinsu baiyi musu da wasa ba. Bai bar yaransa dabi'un nasara sunyi galaba a kansu ba ta hanyar yawan kulawa, tsawatarwa, ja a jiki da kaiwa Allah kuka. 


"I love you! I love you!! I love you!!!....kafin komai ki bar wannan ya zauna a zuciyarki. Kin tuna ranar da nace idan kin sha abin bakina zan tambayeki wani abu?"


Jikinta a sanyaye ta gyada kai "kiyi hakuri amma alfarma zan rokeki da wannan damar. ALHERAN DON ALLAH KI YARJE MIN NA FARA AUREN GHAZALATU."


Jin maganar tashi tayi tamkar saukar aradu a tsakar kanta. Tsiwa take son tayi masa ko tayi bore ko dai tayi wani abin domin nuna masa cewa bata yarda ba, zuciyarta ma bazata barta ba sai ta kasa sakamakon raunin da take iya karanta a idanunsa da suka soma chanja launi.


"Mummyn Ghazalatu sister din Mami ce iyayensu daya. Daddy dinsu kuma cousin din Mami ne kuma cousin din Daddy. Iyayensu maza duka ukun brothers ne. Shekararmu biyu tare da ita sai yanzu muka yanke shawarar fada a gida bayan bikin su Zahra. Kina ganin na kyauta idan nace mata na fasa saboda ke?"


Roko ne yake yi duk da bai furta yadda zata gane a magana ba amma ta gane a yanayinsa. Duk kishinta tana da hankali kuma tasan daidai. Indai zata zama mallakinsa itama wallahi zata iya hakura ya fara aurenta. Da dai ace da ita ya fara haduwa da labari ya sha bambam amma tunda ita ce tazo daga baya hakuri ya zame mata dole.


"A'a" tace a nutse don ta bashi kwarin gwiwa. 


Farinciki ne ya bayyana a fuskarsa ma'abociyar yawan murmushi "Don Allah kin yarda zaki jirani ko na shekara daya ne na fara aurenta sannan na aureki?" 


Runtse idanunta tayi wasu zafafan hawaye na gudu ta gyada kai don babu bakin amsawa.


Ajiyar zuciya ya saki yana hamdala. Daga Ghazalatu har Alheran yasan babu wata saliha a cikinsu. Ko yasha giyar wake bazai ajiyesu a gida daya ba ma. Rigima ce gagaruma ya hadawa kansa amma baya jin akwai yadda zaiyi ya sabule ko daya a cikinsu. Dukkansu akwai babban al'amari tsakanin iyayensu da nasa kuma babu wadda aka tura masa. Da kansa ya nemi soyayyarsu saboda haka dolensa ya tattaro duk wani karfin hali na maza ya dorawa kansa idan yana son zaman lafiya dasu.


"A yau zan koma Katsina in sha Allah babban kakanmu ya dawo jiya bamu hadu ba na taho. Ina komawa zan fadawa Daddy komai don ya fada masa"


"To" yaji tace muryarta tana rawa. Tun ba'aje ko ina ba tasan cewa tana da kishiya.


Zoben da yake karamin yatsansa na farar azurfa mai matukar kyau da harafin A an rubuta cikin kayataccen rubutu ya cire ya dora mata a tafin hannunta "a hannuna yana nufin Alheran, da sunanki na saye shi da albashina na farko. Amma yanzu sunansa Awwab. Don Allah ina rokonki kada ki bawa kowa chance din neman aurenki. I know naso kaina da yawa amma nayi haka ne don kada wata rigima ta tashi da zata shafi iyayenmu."


Son zuciya daban, zahirin rayuwa daban. Tana da kaifin tunanin taya shi hango faruwar abu mara dadi a danginsu idan ya guji 'yar uwarsa ta jini saboda ita. Wani girma ne na musamman taji ya bakunceta ta kara karfafa zuciyarta. Murmushi tayi masa bayan ta goge hawayenta duk ta dame idanunta da hijab din da kwalli.


"Kin amince?" Ya sake tambayarta yana kallon kwayar idonta da nasa jajayen idanun da damuwar tsoron rashin amincewarta ta haddasa.


"Eh"


"Zaki jirani?"


"Eh"


"Babu ke babu Kawu Zakari da sauran sojoji da likitoci fa"


Dariya suka sa a tare ta sake cewa "eh"


"Do you love me?"


Nauyin maganar taji ta dukar da kanta "eh"


"Say it" yace cikin muryar umarni.


Kafada ta noke tana dariya kasa-kasa "ni dai bazan iya ba"


"Zan kira ki fada min a waya"


"Idan Ummi taki bani fa"


"Rufe idonki ki ga wani abu"


Rufewa tayi ya fito da wayar da ya saya mata taji karamar kara ta bude ido daya a daidai lokacin da ya sake daukarta a hoto.


"Mu gani, nayi kyau?" tace a kagauce tana son ganin yadda hoton yayi.


"Kin bata min hoton da kuka. Da a haka zakiyi sojan abu kadan kuka?"


"Kaine kake sani kukan nan amma ni bana kuka"


"Na soyayya ne so ba damuwa, bazan baki hakuri ba ma" yace yana dariya.


Kallonta yayi ta sanya zoben a yatsan kusa da karamin ta dago masa hannunta tana tambayarsa ko yayi mata kyau. Ya yaba sosai ya ja mata kunne akan kada ta taba cire shi wai na alkawari ne. Wayar ya mika mata taki karba wai Ummi zata yi fada.


"Kinsan da ita na fake na taho garin nan da kunya mu koma tare. Muje na kaiwa Ummin da kaina a baki. Daga nan har na koma aiki sai kunnenki yayi ciwo da wayata"


"Idan baka kira ba ma kuka zanyi"


"Seriously? Kina sona haka"


Bata iya amsa masa da baki ba sai kai da ta daga cikin farinciki mara misaltuwa.


**********


A cikin gidan Alh Baba mahaifin Ghazalatu ya danyi karamin gini mai daki biyu, toilet biyu da kitchen saboda iyalinsa idan sun zo gari. Ana gobe zasu dawo daga Umara Gambo da sauran yaran nasu suka iso. Ghazalatu ma komawa tayi ta tayata gyare-gyare. Ana gobe Awwab zai taho wurin Radhiya cikin dare suna hira da mijinta ya sako zancen Ghazalatu.


"Ki duba ki gani sa'ar Fauziyya ce gashi suna shirin aure ita sai taron abokai babu wani tsayayye. Tafiyar nan Alhaji kusan kullum sai yayi min fadan wai mun sangartasu gashi bai ji wata magana game da aure ba"


Murmushi ya ga matar tasa tayi ya tsaya yana bin ta da kallon mamaki.

"Ko gobe kana iya fadawa Alhaji ya fara shiri anyi masa kwacen mata"


"Ahhh garin yaya labari ya wuceni?" Yace cikin farinciki.


Nan ta labarta masa yadda suka yi da Awwab ranar da ya dawo. Shiru Daddy Haroun yayi har Mummy ta fara tunanin ko zai ce ita ta hada.


Da sanyin jiki tace "Babu hannuna fa a ciki Daddy, wai ashe shiru suka yi 'yar banzar yarinyar nan tace sai ta gama makaranta."


"Abinda ban gane ba shin Awwab din Major kike nufi ko wanne?"


Gambo da saurin fushi ta soma harzuka "Awwab nawa garemu? Idan baka so ne sai inji saboda dan yayata ne kake kinsa ko me"


Ya san halin matarsa da saurin hawa kamar farashi kuma dai daga dawowarsa bai shirya rigima da ita a wannan daren ba.


"Idan Hassana yayarki ce ni kuma ko ban aureki ba kin san dai kanwata ce. Akwai maganar da naji game da Awwab din ne shiyasa kika ga haka amma gobe dama munyi da Major zai zo muyi magana da Alh Baba sai mu fara clearing issue din"


"Wani abu ne ya faru da Awwab din?"


"Kinsa batun matar nan da yaranta da yake ta damuwa dasu iyalin sojan da suka je Liberia tare?"


"Sosai kuwa, Ghazalatu ma har gidan iyayenta taje ta kwana. Shine tafiyar da nace maka sunyi da Mami din"


"Yarinyar wajenta Major yayi min magana akan yana son hadasu da Awwab. Gobe zai zo a gaban su Baba Karami ya gabatar da zancen domin aje ayi magana da iyayensu. Ni da kaina na fara sanar dashi tun a saudiyya"


Ko a jikin Mummy Gambo wannan bayani "rashin sanin tsakaninsa da Ghazalatu ne ya janyo amma tunda yanzu sun fada ai shikenan"


"Idan kuma ya riga ya fadawa iyayen yarinyar fa?"


"Sai aje a basu hakuri. Daddy ba wani abu bane ba fa na tada hankali don Allah."

**********


An wayi gari Major yana shirin tafiya gidan Alh Baba inda zai hadu da nasa mahaifin, baban Mami da ake kira Baban Biyu saboda sune manya a 'ya'yansa don bai sami haihuwa da wuri ba sai da ya auro mahaifiyarsu. Cikon na hudun nasu suna Germany ya rasu kuma bisa umarnin Alh Baba jikokinsa biyu daya na wurin mace dayan kuma na namiji za'a aurawa Zahra da Fauziyya.


Mami ke fada masa tafiyar Awwab din da ya sulale ya gudu Sumaila duk da Major ya fada masa zasu je gidan Alh Baba da ya dawo daren jiya. Dadi yaji har ransa "kice ko yau aka bukaci sadaki na mika kawai. Allah Yayi musu albarka. Sun gama min komai"


Amare Zahra da Fauziyya sun fara gyaran jiki. Wata mata ke yi musu anan cikin gidan. Da Major zai fita sai Zayyana kadai a falo itama zaman jiransa take yi. Hajiyar shagwaba ta rinka marairaice masa wai ya bata kudi Ibrahim yace mata anayin kanwar amarya day jiya da suka yi waya. 


Dariya yayi harda kyakyatawa "shi Ibrahim din da kansa ya fada miki haka?"


"Eh Daddy don Allah ka bani kudin yadda za'ayi min nawa invitation card din"


"Kece amaryar?"


"Nice mai gayyata amma kuma bani da outfit da zai dace. Please Daddy"


Hularsa ya cire ya dan sosa gaban kansa. Yanzu idan yace mata ba'ayi da wahala ta yarda. Ta rinka jero masa tambayoyi kenan shi kuma fitar ce a gabansa.


"Jeki ki fadawa Mami kuyi shawara kafin na dawo"


"Thank you Daddy" ta rungume shi tana murna sannan ta wuce sakin Mami.


Daddy Haroun da Gambo ne karshen zuwa falon na Alh Baba. Sun shigo Major yana gaisawa da surukansa Bilal wanda zai auri Fauziyya da Fawaz mai auren Zahra. Su dinma zuwansu kenan yiwa Alhajin barka da dawowa. Suna fita bayan gaishe gaishe tsakanin su Mummy Gambo da iyayensu ta tashi ta koma bangarensu.


Falon akwai 'yan uwansu maza manya wadanda duka tushensu daya ne banda iyayen nasu guda uku. Hira suka taba kadan ana tambayar iyalan juna da dan abinda ba'a rasa ba.


"Mustapha" Alh Baba ya kira Major wanda ya tattaro hankalinsa ga uban nasu "Dan uwanka yayi min zancen akwai yarinya 'yar wajen abokin aikinka da kake son hadawa aure da Muhammad ko?"


"Eh Alhaji"


"Major nace me zai hana mubi abin a sannu kada a takura yaron nan saboda son kara kulla zumunci azo a bata shi"

Daddy Haroun yace saboda yana bukatar damar kawo zancen Ghazalatu.


Murmushi Major yayi "in sha Allahu wannan matsalar ina tsammanin ta riga ta kau. Maganar da nake maka yana hanyar Sumaila zai je wurin yarinyar"


Baba Karami shine mahaifin Major kuma ya fada masa komai kafin ya kawo zancen nan. Murmushi yayi irin na dattijai "to idan sun hada kansu Alh Baba ina ganin ba sai an tsaya bata lokaci ba ko yaya kace?"


"Kwarai kuwa, ya kamata ya ajiye iyali hakan ne zai sa ko ina yaje gida zai nufo ba yawon kasashe ba"


Daddy Haroun sai ya rasa yadda zai bullowa lamarin. Kafin ya fito sai da ya tabbatar da magana daga wurin Ghazalatu. Shirun ba zai zama alkhairi ba kada aje ayi hukuncin da zai jawo matsala a gaba.


"Jiya Gambo take fada min Awwab din da Ghazalatu sun daidaita kansu ashe. Ina ganin me zai hana mu jira ya dawo aji ta bakinsa"


Murmushi sosai Alh Baba yayi yana nuna farincikinsa bisa yadda al'amura suka kasance. Lallai ba karamin kara hade zumunci za'ayi ba idan akayi wannan auren saboda iyayensu duka 'yan dangi ne.


"Wannan shine tuwo na mai na" inji Baban Biyu.


"Kai da baka san da wannan din ba kake kokarin nema masa auren wata?"

Baba Karami ya tambayi Major wanda zancen gabadaya yazo masa a bazata.


"Wallahi ban sani ba Baba"


"Tunda abu yazo da haka Mustapha ita waccan yarinya a barta. Ko bai aureta ba daga ko ina zaka iya tallafawa rayuwarsu. Idan yaso sai ya auri kanwarsa" Baban Biyu yace yana bin 'yan uwansa da kallo domin neman amincewarsu.


Hankalin Major tashi yayi sosai bai taba zaton da faruwar wannan lamari ba. To garin yaya shi bai sani ba kuma Mami ma baya tsammanin ta sani.


"Gambo cewa tayi tana so a hadasu ko sun hada kansu ne? Wallahi ni ban taba jin zancen ba. Babarsu ma bana jin ta sani"


Daddy Haroun sai ya ga tambayar kamar yana nufin kirkira suka yi shi da matarsa sai yaji ransa ya sosu "ba wani abu ne na jayayya ba Major, tunda da alamu kafi son ya auri ita waccan yarinya sai ayi haka din."


Sassauta murya Major yayi duk kuwa da cewa nasa ran har yafi na Daddy Haroun baci "ba zamuyi haka ba, mamaki kawai nake yi nace ban sani ba amma ba wai na karyata bane."


"Duk da haka ya auri wadda ka zaba masa tun farko ita Ghazalatu ayi maganarta daga baya idan ta sami wani"


"To iyayen 'ya'ya. Idan kun gama yanke baku hukuncin sai ku saurari nawa. Mustapha, Haroun, nawa hukuncin shine Muhammad zai auri Ghazalatu. Ita kuma wannan yarinya tunda bamu riga mun shiga ciki ba Allah Ya bata wani. Bazan so wata baraka ta taso a cikinku ba saboda wannan dalili. Hakan yayi ko?" Ya juya ga Baban Biyu da Baba Karami. Duka su biyun sun nuna amincewarsu.


Major bai yi shiru ba duk da haka saboda ance mai daki shi yasan inda yake yi masa yoyo. Shine yasan Zayyan kuma shi yasan me yasa yake kwadayin hada alakar auratayya a tsakanin zuri'arsu. Burinsa su dunkule ta yadda ko bayan ransu a gaba zuri'arsu zata zamo daya. Wannan shine tanadinsa ga Awwab kamar yadda yadda yake da kudirin hada Ibrahim da Zayyanatu.


"Alhaji ku gafarceni ban tari numfashinku ba. Ina neman alfarmar don Allah a bashi damar hadasu duka. Yarinyar da nake magana a kai Radhiya ban baro kakaninnta ba sai da nayi musu alkawarin hadata aure da Awwab"


"MUSTAPHA!!!"


Baba Karami ya daka masa tsawa da kakkausar murya. Duk cikin iyayen nasu ma shine mara fada amma yadda ya kira sunnan dan nasa ya bashi tsoro.


"Alh Baba ya yanke hukunci, mu mun amince sai kaine da ka haifi Muhammadu kake son nuna mana iyakarmu? Da can wane dalilin ne yasa kayi musu alkawari batare da kayi shawara da kowa cikinmu ba?"


"Ku gafarceni Baba in sha Allahu yadda kuka ce hakan za'ayi. Zanje na basu hakuri."


Babu abinda Daddy Haroun bai sani ba game da labarin dan uwan nasa shiyasa yaji tausayinsa da yace ya riga ya fadawa iyayenta. Ai da kunya ace kuma ya koma yace musu an fasa "Baba don Allah kuyi hakuri kada maganar nan ta janyo rikici. A bar Awwab ya auri yarinyar. Ghazalatu kuma ko cikin 'yan uwa sai a sama mata wani"


"Ka bar wannan magana Haroun in sha Allahu Ghazalatu zai aura. Zanje nayi musu bayani"


Alh Baba ma nasa ran ya soma baci yace "nace na gama magana kuma nan da wata uku za'ayi auren. Idan ya dawo ka turo min shi. Ku tashi ku tafi kuma kada ku yarda maganar nan ta kai kunnen iyalanku. Biki ne dasu ku barsu su gama a nutse bana son kananan maganganu"


Sun fito Major ya rasa abinda yake yi masa dadi. Daddy Haroun yana son farincikin 'yarsa ta wani bangaren yana duba cikin tsakar da dan uwansa zai shiga. Jikin motar Major suka tsaya drebansa ya taso da sauri  Daddy yayi masa alama da ya basu wuri. 


"Major ka bani lokaci zanyi magana da su Alhaji. Babu girma ka koma ka cewa mutanen nan an fasa ko abu makamancin haka"


Murmushi yayi kansa ya kulle yana neman mafita "ka bar maganar, nine nayi abu bisa rashin sani dama saboda haka zanyi kokarin daidaitawa. Tunda sun hada kansu da kanwarsa bamubda dalilin cewa wani ya hakura" yayi maganar da tunanin cewa idan da gaske hasashen Mami akansa da Radhiya gaske ne ita za'a ce ta hakura kenan saboda ita ba danginsu bace? Kuma da kunya matuka ya kalli idon Daddy yace tasa 'yar ta hakura.


"Mafi dacewa Major ya auri su biyun. Ka sa min ido zan sake magana dasu."


Shima Major yayi wannan tunanin to amma yanayin aikin Awwab din anya auren mata biyu lokaci guda zai haifar musu da da mai ido kuwa? Kansa yaji ya soma sara masa yayi sallama da Daddy Haroun ya shige mota domin tafiya gida.


A hanyar ma dai tunani yake ta yi yana neman mafitar da ta dace. Iyayensu idan ya koma garesu ma bai san me zai ce dasu ba kamar yadda bai san me zai ce da iyayen Radhiya ba.


Gajeren tsaki yaja a lokacin da ya dauko waya ya fara laluben nambar Awwab. Gara dai yaji ta bakinsa kafin yasan me ya kamata yayi kuma.


**********


Ayuba yana zaune gaban Ummi Mairama ya gama yi mata addu'a yana tofawa idanun yace "Adda Mairama anya ba sihiri bane wannan makantar? Ciwon kan nan da kike ji tun jiya sai nake ganin kamar addu'armu ce take ci."


"Allah Yasa Ayuba, amma ni kuwa waye ya tsaneni haka da zai yi min asiri?"


Roba biyu ya yiwa tofin ayoyin tsari da neman sauki ya kuma tofa mata a kan fuskarta sannan ya tashi zai fita.


"Ka turo min yarinyar nan bana jin ko abinci ta baiwa Awwab sai suru....suruuuu"

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment