Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai, rawa ce ban yarda ba" taji yace yana murmushi.


Rahima dama bata shiga ba don bata iya ba tayi zamanta sai jakunkunan su Hibbah da Zayyana da su ka bar mata. Karamar wayarta kirar samsung sabuwa mai torchlight ce a hannunta tana game din snake jikinta ya bata kallonta ake yi ta baya. Juyawa tayi a hankali ta ga Emzee yana murmushi.


Kujera yaja a kusa da ita ya juyata ya ware dogayen kafafunsa ya zauna ta yadda gabansa ne ke fuskantar bayan kujerar ya dora hannuwa a samanta kansa akan hannuwan.


"Kinsan saurin da na rinka yi kuwa da naje raka abokai na?"


"Meya faru?"


"Kawai waka na jiyo nace Allah Yasa kada Rahiman Muhammad tayi rawa if not tear gas zan saki a wurin nan bayan na kai su Daada gida"


"Meye tear gas kuma?"


Yadda tayi tambayar kadai yasa shi shagala da kallonta kafin ya yi mata bayani. Kanta a kasa take dariya da yace shi fa kishi gareshi "samarinki nawa ki kawo numbers dinsu yanzu duk na kirasu na fada musu anyi miki miji"


"Goma ne ba yawa kasan ba wani farin jini gareni ba" Rahima tayi dariya saboda kafin ta kai karshe ya kusa tuntsirewa daga kan kujera.


Gyara zamansa yayi yace yana bata fuska "Kasheni ki huta" 


Shiru yaji tayi ya kira sunanta bata amsa ba. Tashi yayi ya dawo gabanta ya tsuguna yana leken fuskarta. Hawaye ya gani suna gudu akan fuskar da yake matukar so yaji hankalinsa ya tashi. Ya san iyakarsa ba don haka ba da ya rungumeta ya rarrasheta.


"Rahiman Muhammad?"


"Uhmm" tace da muryar kuka.


"Na bata miki rai ne?"


Gyada kai tayi "eh"


Zuciyarsa yaji tayi masa nauyi "Ya Salaam me nayi miki?"


"Cewa kayi fa na kasheka" ta fashe da kuka sosai.


"Oh my God...am sorry kinji wasa nake yi"


Soyayyar da suke yiwa juna ba ta wasa bace. Kowa na damuwa da damuwar dan uwansa. Hankalinsa ya tashi da kukanta ita kuma bata kaunar wani abu ya gifta tsakaninsu musamman mutuwa a yanzu da take jin ta samu farinciki irin wanda bata taba tunanin akwai ba.


Irin matar da yake mafarkin samu mai shagwaba ya gani a tattare da Rahima saboda yadda take yi da fuska da muryarta "To ka dena cewa in kasheka" 


"Na dena...ban karawa"


Wayar hannunta ya karba ya saka numbarsa yayi dialling layinsa yana cewa "in chanja miki waya?"


"A'a wannan ma sabuwa ce. Sai mun gama WAEC za'a bani wata" tace da murmushi tana tuna abinda Ummi tace mata ranar da ta bata wannan din.


"Ajinki nawa? No shekarunki nawa kada ace ina koyawa yarinya soyayya fa" Emzee yace yana dariya.


"Ajina hudu a primary kuma shekarata 13"


Kallonta yayi yasa yatsansa a baki ya ciza "da gaske? 13 amma kika iya kallon soyayya? Wannan idan kika 20 na zama sorry"


Rahima sai dariya take irin wadda bai taba gani tayi ba hankalinta a kwance "kuma babana yace kada na kula kowa sai nayi 25"


"Ba damuwa nima ba kulaki zanyi ba aurenki kawai zanyi sai ki karasa primary din a gidana" ya amsa mata don ya fuskanci tsokanarsa kuma take yi.


Kalmar aure da ya sako ita ta kashe mata baki. Ya samu ta fada masa ainihin shekarunta wato sha shida da ajinta a makaranta. A take yayi mata alkawarin yana yin POP zai fadawa Daada a nema masa aurenta.


Ko da wasa Rahima bata kawo cewa Emzee bai san ko ita wacece ba. Dadin hira ya saka shi mantawa da yi mata wannan tambayar tunda ta tabbatar masa da cewa tana nan a gidan sai bayan bikin Radhiya.


**********


Wayar ta kalla tana ringing tasan Awwab ne ta kuma tura baki kamar yana wurin sannan ta dauka "fito mu tafi" kawai yace.


Tafiyar kurame suka yi zuwa gidan ashe an fara komawa saboda iyayensu maza sun ce a gida za'ayi magriba babu wanda za'a bari a wurin taron. Yasan Yousuf da Arifah zasu tafi yau ma zaiyi rakiya shiyasa bai neme shi ba. Suna zuwa gida sai nishadinsa yake fushinta kamar baya damunsa ya fito ya zagaya ya bude mata itama ta fito. Hannunta ya kama kai tsaye ya wuce falon da su ka je jiya da ita.


Wayarsa ya dauko ya bude wakar yar amana ta youtube sannan ya kama mayafinta ya cire ya ajiye akan kujera.


"Kinsan wahalar da nasha kafin na sami wakar nan a youtube kuwa? Ni bana gane me suke cewa da kyar naji ance 'yar amana shine na nemo miki" idanunsa ya dora a kanta yana ganin yadda tayi kyau sosai kamar wata 'yar tsana "baby ga 'yar amana ki tashi muyi rawa"


Shan kunun ne ya kare ta soma dariya da Awwab yayi playing wakar.


"Wai da gaske nemo min kayi Chèri?"


"Anything to see your smile Schatzi" ya janyota jikinsa yana shafa gefen fuskarta.


Tsigar jikinta ke tashi ta soma rawar jiki ya rungumeta tsam a jikinsa.


"Calm down ba yau zan baki tsoron ba ai. Rawa zamuyi kuma bazan bari ki fita a falon nan ba sai kinyi"


Sai yanzu take jin kunya sosai "Hammana na tuba kayi hakuri" 


"Baby I want to see you dance...ba wai don na hanaki ba dazu wannan bazan taba yarda dashi ba amma between us harda kafi rawa zamu rinka yi a gidanmu"


"To ai dai nan ba gidanmu bane kayi hakuri" tace ido wiki wiki tana nadamar yi masa gardama don ya hanata rawa.


"Tunda ance sai anyi biki zaki tare kowa sai ya rufe ido kawai a barni duk inda kike muna tare"


"Naji amma na fasa banda rawa...kunyarka nake ji"


Fuskar tausayi yayi "Inje gida inyi kuka?" 


"A'a"


Kashe wakar yayi ya kunna wata ta cikin wayarsa da yake yawan kunnawa idan yana tunaninta lokacin da suka yi fada mai suna You and I. Kidanta cikin taushi yake tashi babu hayaniya ko kadan sai kalmomi masu tasiri a zuciya. Takalmanta ya fara cire mata matsu tsini shima ya cire nasa sai safa. Wani irin riko Awwab yayi mata ya duko da kansa ya hade goshinsu. Hannuwansa na kugunta nata a kafadarsa sun zagaye wuyansa a hankali yace "hau kan kafafuna"


Runtse idanunta tayi ta dora kafa daya a hankali tana jira taji ko zaice tayi nauyi ko ta cire sai taji yace "dora dayar"


A tsaye take amma akan kafafun mijinta sannu a hankali yake bin kalaman wakar yana fada a saitin kunnenta yayin da yake tafiya a nutse suna takun rawa amma shi yake yin duka motsin. A haka suka kwashe kusan minti hudu bai nuna gajiya ba yana rike da ita suna musayar numfashi har wakar ta kare.


"Duk lokacin da kike son yin rawa baby zan tayaki, a gaban wasu ne kawai ban yarda ba saboda ina kishinki. Da sonki na girma a zuciyata kina tunanin akwai ranar da zanso bata miki rai da gangan?"


Girgiza kai tayi a hankali kalamansa na shigarta sosai kawai ta rungumeshi tana masa kukan da ake kira na kissa batare da tasan ma'anarsa ba. Idan an barta bata san dalilin hawayen nata ba idan ka cire tsantsar soyayyar Captain Muhammad Awwab Mustapha.


Habarta ya dago suna kallon juna ta kasa tsayar da hawayenta.


"Kukan na meye?"


"I. Love. You Chèri"


Kamar jira yake ta fada ya soma kissing dinta sosai. Karatu suka ji alaman an kusa kiran sallah ya dawo dasu duniyar da suke ya shafi gefen fuskarta "Da nasan hanaki rawa ne zai sa naji da kanki kin fada min wadannan kalmomin da na dade da cewa ban yarda da rawa ba"


Duka ta kaiwa kirjinsa ya saketa ta dauki takalminta ta saka sannan ta bude jakarta ta fito da janbaki za ta kara sakawa.


"Ana kiran sallah za ki sake kwalliya?"


Kunya taji tayi saurin mayarwa sai da ya matsa mata tace "Jiya Adda Fauzy cewa tayi wai an shanye min janbaki" 


"Mata. Mata sai a barku...an fada min kuna zuwa ma ganin tafiyar amare washegarin da aka kaisu ko" yace yana tsareta da ido.


Ba karamin rikicewa tayi ba kuwa don babu karya ko ita sun gama JS3 da akayi bikin wata 'yar ajinsu kawayensu suka ce wai azo aje gulma. Da ita aka je din amma babu abinda chanjin tafiyar kawar tasu ya sa mata a rai sai tunanin ko duka mijin yayi mata. A lokacin ta yiwa kanta alkawarin idan tayi aure miji ya kawo mata wargi sai dai su daku don ba kyalewa zata yi yaci zalinta ba. Murmushi ne ya subuce mata da ta tuna lokacin da sharrin kuruciya.


Hannuwansa duka ya dora a ka "Na shiga uku kin taba zuwa kenan nima za'a zo mana"


Da sauri ta rinka cewa bata je ba yana cewa sai ta fada masa gaskiya. Nan aka fara kiran sallah ya fita kamar ya tafi da ita. Ciki ta wuce ana ta layin alwala a waje mazan ma suna nasu.


Gidan sai bayan isha ya dan daidaita inda Daada da su Daddy da iyalansu suka zauna a falonsa suna hira. Mama ce tace ita dai sai ta bude gift din DK daga bangaren da matan suke zaune yaran nasu suka soma murna suna jira a bude. Mami ce ta farke abin suka ga takardu ne a ninke. Ta bude ta karanta tana wani irin murmushi ta mikawa Mama. Ita kam hawaye ne ya zubo mata na farinciki Baba Hadir na kallonsu yace "Zainab?" Da alamar tambaya yaji me ya faru.


Ibrahim ta bawa takardun yaje ya mika masa falon yayi shiru sai da ya karanta ya kalli Zayyan.


"Yayi. Yawa" ya daure yace shima muryarsa na nuni da taba masa zuciya da abin yayi.


"Babu ruwanka da kyautar uba da da kuyi mana addu'a Allah Yasa yaci gajiyarsa."


Amin kowa yace ana mamakin Zayyan ya mallakawa Zayyan Hadir gidansa na Kano. Wannan ya biyo bayan dogon nazarinsu shi da Ummi sun san cewa duka sunfi Hadir karfi yanzu kuma Daddy yana da gidan kansa a Katsina.


Mama ta karbi na Zayyana ta bude a take su ka bude baki da mamaki.


"Zayyan meye haka ne?" Daddy yace yana kallon dankareren saitin gwal din da ya mallakawa Zayyana. Dankunne, sarka hade da zube da manyan abin hannu guda biyu iri daya biyu iri daya na kudi har dubu dari biyar.


"Kada ku shiga tsakanina da 'ya'yana ba ku na bawa ba"


Mami ta share kwalla tana jinjinawa zumunci irin na Zayyan da matarsa mai goya masa baya.


Gift na karshe na Emzee mukullin mota ne sabuwa fil. Zayyan yace "waccan sai ta zama ta Ibrahim shi kadai. Allah Yayi muku albarka 'ya'yana"


Saidai ayi ta cewa amin domin babu sauran godiya a tsakanin wadannan iyalin. Kaya Zayyan ya chanja zuwa farare irin na Daddy da Baba Hadir ga matansu kayansu iri daya suka zauna akan 3 sitter mazan a tsaye kowa a bayan matarsa aka dauki hoton tarihi na iyali uku masoyan juna.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: *KUYI HAKURI DA RASHIN YAWANSA BANA JINDADI NE YAU. NAGODE*







Idanun Salame sunyi zuru-zuru saboda asirinta da wadannan 'ya'yan na Mairama suka sani. Daga nan kuma bata san yaya za ta kare ba. Radhiya kashe wayarta tayi bayan ta gama magana da Emzee ta koma kallon Salame tana ta hawaye.


"Me Ummi tayi miki Gwaggo? Mata nawa ne suka taba son wani Allah bai kaddari zamansu tare ba kuma suka hakura?" Matsowa ta rinka yi inda Salame ke tsaye gumi na karyo mata. Wannan shi ake cewa kada Allah Ya kaimu ranar da za'a tsare mutum ana masa tambaya akan laifukan da ya binne. Ya Allah Ka rabamu da hisabi irin wannan da za'a tono komai da komai da muka taba aikatawa a rayuwarmu domin WALLAHI da matukar wahala mu haye.


Kuka Radhiya take yi amma muryarta kowa naji a cikin gidan saboda karshe ranta ya kai kuloluwar baci "Kinsan tsananin da yake tattare da makanta kuwa? A lokacin Ummi ta rayu ba miji ga marayu sannan babu wadatar abincin da zata ci ta ciyar da yaranta. Gwaggo kina kallo sai da ta sayar da duk wani abu da ta mallaka muka dena karatu saboda neman magani." Kukanta ya kara tsanami ta matse kirjinta "sau nawa....sau nawa ina rokon Ummi ta barni nayi bara ko talla saboda bama koshi da abincin gidan Malamijo tana hanawa. Ba don Allah Ya dube mu su Innawuro sun zo ba kina jin da watarana bazata amince ba ko don kada yunwa tayi mana lahani. Sai Allah Ya sakawa Ummi Gwaggo" ta kare da fashewa da wani irin kuka. Rabonta da kuka sosai irin haka tun ranar da Ummi tace kada ta amsa cewar tana son Awwab. Yau ga abinda yafi rabuwa da Awwab kaji ko ka ga mutumin da baya kaunar mahaifiyarka kuma yake neman ganin bayanta.


Jiki na rawa ga tsoro amma Salame bata so ta nunawa Radhiya sai cewa tayi "idan kin gama sharrin sai ki fita ki tafi in kuma zaki rama mata ne to na fara jin didif a jikina sai na san cewa kin haifu"


Kallon da Radhiya tayi mata da jajayen idanunta kallo ne mai firgitarwa da nuna kwarewa wurin fitina da sanin yadda zaka rama abu cikin ruwan sanyi.


"Ummi tayi mana tarbiya wadda ni ko Emzee bazamu taba watsa mata kasa a ido ba in sha Allah. Gwaggo Salame ke ba sa'ar yi na bace domin kin girmi mahaifiyata ma...amma.... zan hadaki da wanda yafi cancanta ya hukunta ki" tana kaiwa nan ta daga waya ta soma kiran mahaifinta Zayyan Tureta.


Duk wannan abu da suke yi Alh Indararo da Maman Danmama suna kofar dakin sai dai su basu kula da tsayuwarsu ba sannan shima yana so ya gama gane kan zancen kafin ya afkawa Salame.


A can hostel dinsu kuma Emzee bayan ya gama nasa kukan shima babu wanda yake so da burin saukewa nauyin zuciyarsa sai mahaifinsa. A take shima ya soma kiran wayar Zayyan din.


**********


Yana zaune a dakin Jume kan tabarma yana cin abincin da ta dafa masa da kanta suna hira. Abin mamakin da ya gani bai wuce sabon fenti ba ciki da wajen gidan ana ta gyare gyare wanda yawanci jikokin gidan samari keyi.


"Wai ni wannan gyaran Jume waye zaiyi amarya ne?" Zayyan ya tambayeta yana dariya.


" 'Yan uwanka ne suke son yin gyara saboda bikin Alheran mana. Ita ce fa jikar farko ta bangaren namiji a gidan nan ka ga kuwa mune da biki"


Dadi yaji sosai "Allah Ya saka da alkhairi Jume nagode"


Dan harararsa tayi "meye haka kamar wanda aka yiwa wani abu. Kai dai ka gama ci ga 'ya kayayyaki can da suka hadawa amarya."


"Harda wata wahala kuma?"


"Ashe ba 'yarsu bace indai abinda suka yi sunansa wahala"


Saurin bata hakuri yayi ya gama cin abincin sannan ya mika mata wata leda mai kauri. Budewa yayi ya dauko kullin kudi guda uku kowanne dubu dari biyar biyar yace gashi nan ta bawa yayunsa Badaru, Rayyan da Maikudi. Sannan ya dauko kananun kullin su kuma dubu dari bibbiyu ne yace na matan ne su ma su uku. Wannan duk cikin kudin da aka bashi ne wanda yake ganin idan bai nemi lada ya raya zumunci dasu ba yayi asara kuma bai godewa Allah da ya dawo dashi gida lafiya ba.


Jume sai kwalla tasa zani ta goge "Zayyanu da wane bakin zanyi maka godiya kuma in cigaba da rokon yafiya akan zaluncin da nayi maka?"


Baya son tana yi masa haka domin uwa ya dauketa "kisa min albarka kawai Jume abar maganar. In Allah Ya yarda ke kuma hajjin wannan shekarar zamu je dake da Mairama"


"Ayya...ayya Zayyanu...Allah Ya jikan Innarka da Malam. Na cutar da baiwar Allahn nan ashe nice da moriyar danta" tace tana kuka sosai. Cikin wanda ta ya fara bata na dubu dari biyar din ta dauko ta mika masa kuma tana sane saboda ta gano Maikudi ya taho dakin amma ya tsaya daga waje saboda ya hango Zayyan.


"Wannan ka rike kayanka Zayyanu don wallahi ko kwabo bazan baiwa Maikudi ba." 


Da sauri Zayyan yake dubanta "haba Jume me yayi zafi haka?"


"Komai ma. Zayyanu komai da komai yayi zafi daga lokacin da Maikudi ya danne dukiyar marayu sannan saboda bakin hali da tsantsar mugunta ya aika da sakon mutuwarsu har Nijar ya dakile masu tallafa musu"


Maikudi yana daga waje yaji kamar ya rafka ihu. Shigowa yayi ya rakube a gefe ya durkusa amma ya kasa cewa Jume da kanin nasa komai. Ita kuwa kallon banza take masa saboda irin abubuwan da yayi da irin yadda itama ya rainata.


"Saboda kaji ana zancen kudi shine ka taho ko? Ka gani..." tace tana dorawa Zayyan kudinsa "to na bashi kayansa ban kuma lamunce ya baka ba ko da a bayan idona ba. Yau ba don dawowar abokansa ba ina da yakinin haka za ka yi ta gina kanka da dukiyarsu batare da nadama ba"


Zayyan kama bakinsa yayi tunda ita da danta sunfi kusa. Ba don zumunci domin Allah ake yinsa ba ko inuwar Maikudi bazai sake kallo ba. Mutumin da baiji tausayin matar da akace mijinta ya rasu ba ga danyen jego. Mutumin da yayi amfani da emotional sentiment din Mairama yasa ta hakura da takardun gidan mijinta akan wasikar da ya bar mata kafin ya tafi. Zumunci akwai dadi akwai wahala sai mutum ya daure ya kai zuciyarsa nesa. 


Wayarsa yaji tana vibrating ya dauko sai lokacin ya kula da missed call din Radhiya da na Emzee. Tashi yayi ya saka kudinsa a aljihu yace da Jume yana zuwa. Wurin dakin Innarsa yaje ya tsaya zai kirasu Maikudi ya biyo shi da sauri. Dukar da kai yayi saboda mugun kwarjinin da Zayyan yayi masa. 


"Yaya akayi?" Zayyan yace da dakakkiyar murya.


Kamar wanda aka tsuma a cikin ruwa don kunya Maikudi ya dago kai yana hada hannuwa "Zayyan ka duba girman zumunci..."


"Wannan ka biyo kenan Maikudi..." ya zura hannu ya dauko kudin ya mika masa "gashi na riga nayi niyya dama"


Ja baya Maikudi yayi "ba kudinka nake so ba Zayyan. Nasan akwai kunya in kalli idanunka ko na iyalinka in roki gafara amma ku taimaka don Allah. Kawu Aminu yace dama akwai ranar da zanji kunya gashi ko shekara baiyi a kasa ba lokacin yazo"


Zayyan yaji wayarsa ta sake vibrating kallo daya ya yiwa Maikudi yace " 'ya'yana suna bukata ta zamuyi magana anjima"


Bai jira cewarsa ba ya daga wayar gabansa ya fadi saboda jin muryar Radhiya tana kuka.


"Daada" tace lokaci guda tana kara sautin kukanta.


Faduwar gaba yaji sosai da sauri ya rinka watsa mata tambayoyi "Alheran menene? Ina Umminku? Me ya faru?"


Salame na jin ta ce Daada hankalinta ya sake tashi don Zayyan ne mutum na karshe da zata so yasan wannan abu. Jikinta ya hau bari musamman da idanunta su ka sauka akan Alhaji Indararo da Maman Danmama. Radhiya ko a jikinta sai ma kara kwantar da murya da tayi.


"Ummi tana gidan Malamijo"


"Ke kuma kina ina?"


"Gidan Gwaggo Salame" ta fada tare da kara sautin kukan kamar lokacin ma dukanta ake yi.


Cikin fada yace "Can nace kije ko nan mijinki ya tura ki?" 


"Kiji tsoron Allah Radhiya me nayi miki kike kara kuka haka" Salame tayi maganar tana komawa kalar tausayi sosai. 


Shi kuwa Zayyan kukan 'yarsa har kokon ransa yake jinsa. Lallabata ya koma yi don yaji me ya faru "Alheran dena kukan ko waye ya taba min ke ba kyalewa zanyi ba"


Ba kunya ta sakarwa Salame murmushi sannan tasa speaker ta kure volume din wayar "Daada dukana tayi da wayar rediyo fatar bayana ta cire..."


"Laaaaahhhh kuji min yarinya...ba Rahima nazo duka ba kika tare? Ni ina ruwana da 'ya'yan gidanku me zai kaini dukanku...." idanunta har sun fara tara kwalla saboda wani sauyin numfashi da take iya jiyowa na Zayyan ransa ya soma baci.


"Wai don na gane ashe tana sonka kuma ita ta makanta Ummi don ta auri Alha...."


Salame kasa hakuri tayi tasa hannu ta toshe bakin Radhiya saboda yadda Zayyan yace "ME???" da karfi.


Alh Indararo yana jin haka shi kuma ya wawurota ji kake tas-tas ya tsittsinka mata mari. Zayyan da ya zata tasa 'yar ake duka a kidime ya kashe wayar ya kira Mairama.


Baiwar Allah bata san me ake yi ba tana tare dasu Innawuro ana hira ta dauka. Abinda bata taba ji ba wato Zayyan ya daga mata murya taji a yau. Zai iya hakuri da komai banda taba masa 'ya'ya ba kuma wai don bashi da kara ba sai don yasan wacece Salame a da lokacin da bata ji kunyar kai masa kokon barar soyayya ba alhali yana neman kanwarta. Abu na biyu kuwa bai wuce shekarun da ya kwasa cike da tsananin kewar iyalinsa. Yanzu da ya sami dama ta biyu ba zaiyi wasa da ita yana ji yana gani 'ya'yansa suna zubar da hawaye ba. Bashi da uwa ba uba sai mata sai su. Baya fata amma ya sani ana chanja mata amma jininsa bazai iya taba chanja shi ba.


"Kije gidan yayarki Salame ki dauko min Alheran sannan gobe zanzo na dauketa mu koma gida"


Tashi tayi ta matsa daga cikin mutane hankali a tashe "Sojana ban fahimceka ba"


"Nima ban fahimta ba Fillo.."yace cike da damuwa "Alheran ta kirani yanzu wai Salame tana dukanta da wayar rediyo...."


Ko karshen zancen bata tsaya ji ba ta koma ciki da sauri danunta sun kada sunyi ja. Nanatawa take yi yau ko ita ko Salame...ta gaji da wannan halayya da take nuna mata. Rahima ma a yanzu ba bari zata yi ta tabata ba bare kuma Radhiyanta. Wani dauke kai da take yi akanta ba shine yake nufin bata son abarta ba. Bata hada son 'ya'yanta da komai sai dai sanin rayuwa da kyaun hali yasa bata sangartasu da soyayya ba.


"Mairama ina zaki haka lokaci guda kin fita hayyacinki" cewar Yadikko tana tasowa ta riketa.


"Gidan Salame zani Yadikko. Kuzo muje kuyi shaida ayi min tsakani da ita domin na rantse zan nuna mata duk abinda nake yi ba wai rashin sanin ciwon kai bane. Idan zumunci dani ne bata so a yau ni da kaina zansa wuka na datse shi uban kowa ma ya huta"


Mama cire DK tayi da take shayarwa ta mikawa Laila ta dafa Mairama "kiyi hakuri ki fadi me tayi miki"


Kowa ya ga Mairama yasan tana cikin bacin rai dama ga ta da zuciya. Hakurinta da yawan kau da kai shine yake sawa a ga kamar bata da fushi.

"Babansu Karami ya kirani yanzu wai Salame tana dukan wannan yarinya da wayar rediyo"


"Me kika ce?" Malamijo yace da sauri yana nufosu. Hayaniya yake ji har soro shine ya fito.


Cikin kankanin lokaci Malamijo, Nene Marka, Yadikko da Hajjo su ka hadu da Mairama zasu tafi gidan Salame kowa ya kasa gane me yake faruwa. Mairama ta kira Radhiya amma tana dauka kuka kawai ta rinka yi bata ce komai ba. Zasu fita ta ga Mama Zainab a tsaye bata da niyar binsu.


"Yanzun nan in fada miki ana dukan 'yarki amma ki tsaya a nan Zainab" cewar Mairama.


Gani tayi abin ya shafi danginsu bai dace ta tura kai ba "Kuje ku dawo Ummin Awwab"


Fushin nata kan Mama ya nemi komawa tana ta kumburi tace "kada kije din...kuma sai na fadawa Mami" fuuuu tayi gaba tana sababin da babu wanda ya santa dashi.


Nene Marka tace "maza Zainabu dauko mayafinki wannan 'yar uwar taki bata iya fushi ba ko kadan"


Duk da babu nisa motar Mairama  suka shiga sabo mutane dreba ya ja su.


**********


Bayan marin da Alh Indararo ya rinka saukewa Salame zuciyarsa a sama har yana haki ya nuna ta yatsa "naji komai kuma nasan komai. Sai yau na fahimci yaya akayi na aureki Salame"


Radhiya gefe ta koma abinta bayanta na zugi tana jiran isowar su Ummi saboda Daada yace ta jira gasu nan zuwa.


Kuka yaki zuwar wa Salame sai kumatunta duka biyun da ta rike zugi da radadi na shigarta. 


Cigaba yayi da fadansa sa'arsu daya babu yara a gidan kamar anyi shara. Dama na Salame ne masu zama su ma yau Radhiya tayi musu jan ido babu ko daya.


"Lallai biri yayi kama da mutum. Salame ko ina shan giya me zai kaini aurenki bayan tun kina gidan Idris na sanki. Sau nawa nake bawa matana labarin yadda yake zuwa wurina neman bashi saboda ya auri hatsabibiyar mata mai bani-bani wadda ta raina shi. Kinsan talaka ne amma kike amfani da son da yake miki kika tatike shi. Ranar da zaki haifi Rahima ma idan baki sani ba ni na bashi aron mota aka kaiki asibiti. Sannan ragon suna da kika matsanta masa shima bashi ya nema a wurina sai da ya shekara uku ya iya hada min kudin ragon."


"Alhaji me ya kawo wannan tone-tonen? Kada kace ka yarda da zancen yarinyar..."


Mugun kallon da ya jefa mata yasa ta koma tayi lakwas "Salame kyan dan maciji asirinki ya tonu" ya nuna Maman Danmama "ga uwargidana nan ki tambayeta

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment