Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shaka yayin da Salame ta dage ta zabgawa Khadi duka a gadon baya ta fashe da kuka. Rahima ta tafi da sauri ta bude kofar ta daukota Emzee ya yiwa Salame wani disgusting look. Gaban motar ya riga ya fara wani abu sama-sama mara dadin ji ga hakoranta  masu kore daga samansu. Sannan abin haushi dubi yadda ta daki karamar yarinya haka. Kayan jikinta kuwa ya rasa abib fada. Shi dai ya tabbatar Ummi ta sasu sayen kaya ready made na mutan Sumaila shi da Ibrahim da Laila suka je. Haushin abinda Ummin ta yi mata dazu shine yasa taki saka kayan wai tafi karfinsu.


Khadi 'yar banza ta tasha hannu ba musu ta gudu wurin yayarta ta lafe tana kuka. Jikin Rahima na rawa dreban ya dawo. Ajiyar zuciya Emzee yayi yana kallota ta saman motar.


A hankali yayi mata magana yana kallon yadda ta rikice sosai "ki bisu zan taho yanzu okay"


Kai ta gyada da sauri ta tafi daya motar tana tsoron kada Salame tayi mata wata maganar ko tace su koma gida. Ita kuma zuciya a baka saboda bacin rai yau rashin m din na Khadi akanta ya kare a gaban wannan yaron na Mairama. Muryarsa taji ya gama goga hannuwansa da juna.


"Lets get going Gwaggo"


Dauke kai tayi yana ganin dreban yayi waje kawai ya cire hularsa da riga daga shi sai wando da vest. Bayan motar ya ajiye rigarsa da kyau ya dora hular a kanta don kada ta fado ya shiga ya zauna ya daura belt. Salame ta kalle shi tana tunanin dalilinsa na tube riga bata gama sannin me ake ciki ba ya fizgi motar a guje ya fita da ribas sai da cikinta ya kada. Wata irin cin taya yayi da burki yayi kwana tamkar mai shirin zuwa Sumaila a awa guda daga Abuja ya kwashi motar ya hau titi. Gudu yake na karshen rashin hankali sai dai kaji qeeeyyyyy quuuuu....yaci taya ko ya taka burki sai motar tayi kamar za ta hantsila. Salame tana kallon yadda ya murtuke fuska kuma jikinsa baya motsawa amma ita sai dai tayi gaba yif ta dawo baya yif jikinta yana ta mazari.


"Kai dan ubanka tafi a hankali ko ka saukeni"


Idan motar za ta amsa to Emzee ya amsa. Salame sai da ta kai ta daga hannu za ta doke shi yayi mata wani razanannen kallo tare da taka burkin gaggawa sai ga kanta ya tafi saura kiris ta doki glass. Hannunsa yasa ya tareta don ba jini yake son fitar mata ba. Burinsa ko ta halin kaka ya fanshi wani abu na makantar Ummi na shakara goma. Tsanar Salame ke kara ruri a zuciyarsa zai bincika ya tabbatar da sa hannunta. Idan akwai ko su Ummi basu sani ba da shi da Addarsa sai sun yi mata abinda zata ji rayuwarta tayi kunci. Yanzu haka ranar zuwa Sakkwato biki suke jira shi da Radhiya su barwa Maikudi abinda bazai manta ba. Ba wani abu bane kuma yafi taba zukatansu sai wulakancin da ya yiwa Umminsu ga wahalar haihuwa ga radadin mutuwar miji da taji.


Kowa ya sani a Nigeria biyu ga watan junairu ana tsaka da sanyi ne amma banda Salame matar Haji Indararo. Gumi take kashirban tana yiwa Emzee tofin Allah tsine. Lokacin da suka isa wurin yayi sa'ar ganin wata motar na fita yasan zai sami wurin parking. Katinsa ya nuna aka wangale gate ya shiga Salame tana ta numfarfashi. Yana tsayawa ta kama kofa zata fita taji a datse.


Ashe harda hawayen wahala tayi bata sani ba cikin fada tace "shegen yaro mai kama da ifiritu bude min"


Emzee a soja yake baka ganin wani abu wai shi sani ko sabo a tattare dashi sai murmushin mugunta "kinfi kowa sanin cewar ina da uba mijin kanwarki....ko ince mutumin da kike so?" Ya yi mata wani kallon gefe.


Jikin Salame ya bugu saboda tukin da ya yi amma abinda yafi daga mata hankali bai wuce maganar da yayi ba. A ina yaji? Mairama ce ta fada masa ko waye? Karfin hali tayi ta daure fuska.


"Rashin kunyar taka har ta kai haka Karami? Irin tarbiyar da Mairama take baku kenan ashe, kun tashi ba ku ganin girman kowa"


Juyowa Emzee yayi ya mata wani kallo mai firgitarwa kamaninsa sun sauya gabadaya...soja mazan fama.


"Kada ki kuma ambaton sunan Ummina domin tunda take bata taba nakasa dabba ba bare mutum"


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Salame ta fada a tsorace jikinta yana tsuma baki na rawa "me...me kake nufi? Sharri za ka yi min kace ni na makanta ta?"


Sai da kansa ya sara a lokacin domin dama bugun cikinta yayi ya bata tsoro domin jin gaskiyar lamari kuma yaji abinda yake so kafin ma ya tambaya. Duk da yana zargin tabbas ita ce amma yanzu da ya tabbatar sai da abin ya girgiza shi matuka. Ba ya kaunar Salame ko na digon sakan saboda bata cancanci a sota ba. Umminsa tana makance tsayin shekaru Salame tana gidan miji tana ciki da haihuwa taci me kyau tasha me kyau lokacin gwamnatinta na ci a zuciyar Alh Indararo.


"Kuruciya tasa ban fahimci me kika yi ba shiyasa ban tona miki asiri ba tun lokacin da kika saka mata...." yace don ya kara tunzurata yana bude dash board.


Sabon gumi na yake tsattsafo mata jin sirrin boye da ko da kanta bata zancen a zuci yau Emzee ya bankado shi. Harda sanyi ta rinka ji yana ratsata ya cigaba da lalubensa kamar ba ta cikin motar.


Hakoranta sai sarkewa suke yi don tsoro tace "to yanzu kuma uban me kake lalube bayan ka gama yi min sharrin"


"Bindiga"


Idanunta kamar zasu fado karshen tsoro ta kai sannan ga uwa uba wani mahaukacin zawo da ya matsota saboda tsoro. 


"An...an. fada. Maka idan...idan ka kasheni. Mairama zata yi murna ne?"


Bude pin din motar yayi "kin zata harbinki zanyi? Allah Ya kiyaye ba'ayi min wannan tarbiyar ba"


Budewa tayi da sauri ya leka da kansa ta inda ta tashi "uhmm nace ba....nagode da kika tabbatar min da zargina akan waye ya makanta min uwa"


Salame sai bude baki tayi tana masa kallon tsananin mamaki shi kuwa ya zura hannu ya janyo kofar ya rufe ta bangaren da take sannan ya kifa kai akan sitiyari yana kokarin mayarda hawayen bakincikin da suke neman zuwar masa. Dago kai yayi ya nemi wayarsa sai ya ga har lokacin tana tsaye. Da kallo daya ya karasa razana ta ta wuce ciki wurin da ake ta karbar baki za'a fara abinda ya tara jama'a.


Yau ranar farinciki ce dole ya saita kansa. Ibrahim ya kira bugu daya ya dauka.


"Bro turo min Rahima" yace da wata iron murya can kasa.


"Bangane ba. Ba tare kuke ba?" Zai sake magana ya hangota tare da Zayyana zasu zauna "kana ina ne na ganta"


Kwatanta masa inda yayi parking Emzee yayi Ibrahim yaje inda suke ya fadawa Zayyana ita kuma ta fada mata. Tana tashi bayan ta ajiye Khadi akan kujerarta ta hango Salame amma da ta ga hankalinta baya gareta sai ta wuce ta tafi.


Ya gama saka rigarsa kenan yana gyara zaman hular a kansa ta bullo. Shagala Emzee yayi da yadda Rahima take tafiya cikin nutsuwa. Yanayin da ya shiga mai wuyar fassara soyayyarta ta mamaye masa kowane lungu da sako na zuciyarsa. Duk kunya ta isheta saboda yadda ya kafeta da ido har ta karaso.


"Mu zauna a nan ko mu shiga ciki?" Yace yana fatan ta amince su zauna.


"Za'a nemeka ai"


"Okay muje" sun fara tafiya ya ga dacewar ya bata hakuri akan abinda yayar mahaifiyarsa tayi musu "Rahima kiyi hakuri akan abinda ya faru dazu. Na saka ki zaman jirana kuma bani na kawoki ba"


Ita da tasan mahaifiyarta ce tayi sai tayi saurin cewa "ni ya kamata na baka hakuri"


"Akan me? For being a good girl me jin maganarrr.....maganar wa dinki kika ji?" Ya zuba mata idanu.


Murmushi tayi kanta a kasa "Ya Emzee?" 


"Nope" tsayuwa yayi ya hanata tafiya "Rahima wane matsayi kika bani?"


Kasa magana tayi tambayar tayi mata nauyi duk da amsarta tana jin tamkar ta amayo masa ita ne ko za ta sami saukin wannan soyayya da tayi mata mugun kamu.


Kamar yayi mata kuka saboda taki magana "gobe zan koma Kaduna da sassafe. Please Rahima ki fada min ni waye a gareki kafin na tafi....idan ba haka ba retire zanyi tun kafin na fara aikin na dawo ga filin yaki nan in your beautiful eyes muyi ta fafatawa."


Zuwa yanzu ko fuskarta baya iya gani ta shige cikin mayafin ta rufe kanta gabadaya sai murmushi kawai take yi. Da kyar ta iya cewa "ni wa dinka ce to?"


"My heart..." yace da sauri "ke fa?"


Babu wanda zai wuce ya gansu baiyi musu kallo na biyu ba. Kana ganinsu ka ga masoyan da suka mutu akan juna kuma suka dace sosai da juna. Emzee fari ne kamar yayarsa ga kyau ga jikin matashin soja. Rahima kuwa baka ce fatarta tafi kama da wankan tawarda don da kadan Zayyana ta fita haske. Kyakkyawa ce sosai tafi Halifa da sauran 'ya'yan Salame nesa ba kusa  ba sai dai su nuna mata haske. Round shaped eyes dinta sunfi komai daukar hankali akan fuskarta. Kamaninta sosai da kakarta Iya shiyasa take ji da ita.


"Kinyi shiru Rahiman Muhammad"


Sautin loudspeaker suka ji za'a bude taron da addu'a Rahima ta daure tace "to me kake so nace Muhammadun Rahima?"


Murmushinsa dariyar farinciki ya koma yana kallonta da adoration "kince komai....realy? Kin yarda Muhammadun Rahima ne ni? Daga ni fa babu kari"


Dariya tayi ta cikin mayafin tana gyada kai. Zuciyar Emzee ta cika da soyayyar kanwarsa da bai san suna da alaka ba ko kadan. Da sauri sauri suka karasa hall din za ta wuce bangaren mata ya bi bayanta da sauri yana maida numfashi tamkar wanda yayi tsere taji yace "Ina sonki Rahiman Muhammad"


Juyowa tayi suka hada ido kowa da kayataccen murmushi a saman fuskarsa sannan suka nemi wurin zama.


**********

Taro ya soma kankama bayan addu'o'i da mika godiya ga Allah mai gabatarwa Ibrahim Hadir ya gabatar da manyan baki na musamman. Ba kowa bane illa manyan aminai 'yan uwa ga Zayyan kowa da matarsa. Excellency baban Arifah, Major Daddy, Baba Hadir sai kuma Tante da mijinta mahaifin Yousuf. Wadannan mutane kowannensu ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar iyalin Zayyan shiyasa idan suna ganin ya kyautata musu wurin ceton rayuwarsu ya kan ce babu kyautatawa mafi tsada da daraja sai wadda za kayi a bayan idon mutum idan ya mutu. Wannan kyautatawar kayi ta ne ba don ganin ido ba bare kasa ran a saka maka. A gefe guda ga duka 'yan uwan Zayyan mata uku da maza biyu domin Maikudi bazai taba iya zuwa ba duk da Zayyan ya bukaci hakan. To da wane ido zai kalli su Mairama, Daddy da har yau bai manta kalar bacin ran da ya gani a idanunsa ba, da uban gayya Zayyan wanda ya mare shi. Ya kure Zayyan iyakar kurewa kuma ya tabbatar abinda yayi musu bazai taba gogewa a zukatansu ba. Son zuciya da kwadayi ya mayar dashi mujiya a cikin ahalinsa. Yana ji yana gani sai dai yayi ta dari dari dasu domin tsanarsa da yake gani a idanunsu. 


Captain Onomza shima yazo ga jama'ar Rugar Barkindo, na gidan Malamijo da abokan arziki. Sannan mutumin da Zayyan ya dauka da matukar mahimmanci a rayuwarsa wato Chibuzor da matarsa da 'yarsu su ma kayan jikinsu irin na wadanda su ka yi ankon fari da green din. Sai kuma Maman Dolapo da Christie ma sun zo kafin shigowar Emzee suka share hawayensu dasu Mama. Ga Alh Salisu da nasa iyalin abin sai son barka.


Ibrahim ne yake magana da turanci da hausa domin kowa ya fahimta ya sanar da cewa akwai gajeren wasa da abokan Emzee zasu gabatar mai taken A Soldier's Dream (Burin Soja).


Drama ce mai kayatarwa wadda ta janyo wurin yayi shiru aka zuba musu idanu daga kan stage. Sojoji ne rataye da bindiga da 'yan jakunkunansu sunyi shirin tafiya filin daga. Gefe guda matansu da iyayensu suna ta kuka da yara. Idan ka ga yadda suke gabatar da dramar da matukar ban tausayi. Sun rabu da iyali suna ta kuka sannan sunje yakin an kashe da yawansu. Nan ma wurin dawowarsu mata da yawa suka rinka suma duk wadda ta ga babu mijinta. Mutane kuwa sai share hawaye domin an shigar dasu cikin rayuwar da basu santa ba kuma a da babu wanda yake damuwa da sanin nata.


Da dramar ta kare Radhiya ma duk yadda ta ga abubuwa a Military Voice lokacin da suke dauka sai da tayi wani kukan. Bayan an gama tafa musu Ibrahim ya bukaci wadanda ake taro dominsu su hadu wuri daya.


Zayyana dauke da DK wanda kayansa harda hula babu bambanci da na Daada da Emzee anyi masa komai dan karami daidai da jikinsa suka je wurin Daada. Wani envelop da Ummi tayi wrapping mai dan tudu Zayyan ya daga hannun DK da yake jikin Zayyan ya dora masa a kirjinsa.


"This is for you my son"


Su Daddy suna kallo babu wanda yasan menene a ciki. Wani ya sake daukowa ya fi wancan girma da dan nauyi ya mikawa Zayyana.


"Kallabi tsakanin rawuna Zayyanatun Zayyan ga naki"


Sai da ta rissina tace "Allah Ya kara budi Daada Ya saka da alkhairi"


"Amin" su Excellency suka ce suna murmushi.


Wani dan karami sosai Zayyan ya mikawa Emzee "Soja dan sojoji kaima ga naka"


Godiya yayi sosai shima aka fara daukarsu a hotuna sannan kamar hadin baki aka shiga miko musu gifts kowa da abinda yake badawa. Family picture aka tashi dauka aka hada iyalan Zayyan, Daddy, Baba Hadir, Excellency duka wasu a tsaye wasu a durkushe. Zayyan ya dan gama waigensa ya hango Chibuzor ya kira shi da hannu shi da matarsa.


"Sir this is a family picture" yace yana sake ja da baya.


"You are my family Chibuzor" Zayyan yace yana yi masa murmushi tare da nuna masa inda zasu tsaya kusa da sauran yaran nasu.  Chibuzor bai taba tunanin karamcin Zayyan ya kai haka ba. Yana da masaniyar yadda addini da yare ke kawo tawayar kyakkyawar alaka a tsakanin 'yan Nigeria amma ga wani babban soja masoyi ga mutane da dama ya rungumi kowa hannu bibbiyu.


An gama hotuna aka fara cin abinci wanda yake serve yourself anyi shi a wadace kowa yaci ya koshi. Duk wannan abu da akeyi Salame tana rakube ko motsin kirki bata son yi saboda ko yaya ta ga giftawar Emzee sai cikinta ya duri ruwa. Yanzu idan ya bude baki a wurin nan ko kafin ta koma Sumaila ta kade har ganyenta don bata san me zasu yi mata ba. Ana yiwa Zayyan kallon mai kirki amma tana da yakinin cewa ba karamin mataki zai dauka akanta ba.


Kallon kowa take yi daidai ana ta shagali wannan na hira da wannan, wancan da waccan amma babu wanda ya rabeta...abin bakinciki shine harda 'ya'yan cikinta. Idan Rahima ta gudu saboda yadda take takura mata meye dalilin Halifa da Khadi? Shi dai bai tsaneta ba amma baya kaunar halayenta ko kadan. Khadi kuma yarinya ce da ta goge a rashin kunya amma yau fushin nata saboda ta doketa ne. Salame sai ta ji ta very, very lonely abin ya tabata fiye da zato da tsammani. Kamar ance ta daga kai su ka hada ido da Mairama. Tun dazu da take gaisawa da mutane hankalinta yake kan Addarta. Yadda ta zauna ita kadai a table din mutum takwas an wareta kamar babu ita a wurin itama sai taji babu dadi. Fushin da take yi na kudin Rahima da ta karba dazu ya gushe. Murmushi tayi da su ka hada ido a karo na biyu sannan da hannu ta nuna mata inda ake dibar abinci. Wai don kada a rainata sai ta dauke kai ta juya mata keya.


Ashe Mama na kallonsu ta tuntsire da dariya.

"Oh ni Zainabu Abu inama ina da 'yar uwa mace muma mu hau sama mu fado."


"Haka ma zaki ce?" Mami tace tana murmushi.


"Abin naku ne kamar hadin baki. Kina yi dasu Gambo gefe daya ga Salame suna bugawa da Mairama"


Ummi ta sake kallon Salame "babu abu mara dadi kamar ace kai da 'yan uwanka bakwa jituwa. Yawanci kuma duk sai ki ga hassada ta fi komai ruguza mana zumunci"


"Ni zan fada muku haka don ina da tabbacin Hussaina da tayi ta ingiza rikicinmu da Gambo ba wani abu bane ya tunzuruta sai ganin wai muna da kudi mun wareta" Mami tace tana tuno bacin ranta.


"Amma dai dan Adam babu godiyar Allah. Sai ki ga muyi ta takurawa kanmu domin mu kyautata musu amma basa gani" cewar Mama 


Mami ta mike "Yo ina kudin yake banda dai ana yiwa rogo kallon kitse. Kunga ni mijina bai ci komai ba yau tun safe kuma na ga mazajenku sun saka shi a gaba da hira ku taimaka kuyi musu signal ko su tashi ko na zuba masa shi kadai" 


Ummi da Mama suka sa dariya Mama tace "yayi matar Major Allah Ya bar mana ke. Ana kwasar jikokin ma ashe a gefe ana ta dabbaka kauna"


Dariya Zainab ta basu suka mike tare kowacce ta zubawa mijinta abinda tasan yana so. Ummi na kai wa Daada nasa ta koma ta zuba fried sphagetti da wani sauce din naman sa da albasa, attaruhu da koren tattasai an yanka su manya manya, naman kuma dogo a tsaye ta hada da potato salad ta tafi mazaunin Salame. Ajiye mata tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun. 


"Meye wannan za ki wani turo min abinci" ta sha kunu


Ummi ma daure fuska tayi ta ja plate din "idan ba kya so sai na dauke"


Da sauri Salame ta janye yawunta ya gama tsinkewa "barshi dai....kada kiyi zaton zanci da dadin rai ne don dai kawai ba kyau wulakanta abinci ne. Kuma ga bakinku ana kallonmu kada na kunyata uwar gayya Mairama matar Zayyan mai kudi"


Ummi gimtse dariya kawai tayi tana ganin yadda idanun Salame suke walainiya akan plate din. "Bari na baki wuri kici"


Wani iri Salame taji bata so ta tashi amma bazata nuna ba "haka kika iya dama naki bola wasu can bare sun fimu matsayi."


"In zauna kenan kike nufi?" Ummi tace a ranta kuwa dariya ce fal take dannewa.


Baki fal da taliya da nama Salame tace "In kin so tunda ai ba sai kin nunawa duniya bama shiri ba"


A zuci Ummi tace "da baki girmeni ba da nace baki da kunya ma...kina so kina kaiwa kasuwa"


A can kujerun karshe daga bari daya Yousuf ne da Awwab suke hira duk yawanci akan bikinsu ne da shirin da su ka tanadar masa. Dinner din da zasuyi basa bukatar taimakon iyaye da kudinsu suke son yi gasu duka babu wanda ya waye da harkar biki a Nigeria.


"Ka bari idan mun koma gida muyi maganar da Bilal tunda shi dan gari ne" inji Yousuf 


"To shikenan. Yanzu dai shawara nake nema. Ina tunanin sayen mota amma kuma Alheran da zan barwa idan na tafi aiki itama ba zama zata yi ba."


"Kawai ka barshi sai ta gama ta dawo nan din kunyi settling sai ka saya idan ba haka ba wa zaku barwa? Tunda akwai motocin nan a gida kawai ka bari"


Arifah su ka gani ta nufosu da plates biyu Yousuf yayi saurin tashi ya karbo suka koma wani table din yana yiwa Awwab gwalo wai ga inda ake kula da miji. Arifah kunya taji ta kai masa duka a hannu ya rike hannun yana kallonta kamar su bar wurin nan ya samu damar nuna mata soyayya.


"Ehemm da mutum a nan dai...albarkacin kanwata bari na baku wuri"


Tashi yayi ya fara tafiya Radhiya ta kira shi kamar tasan ita zai nema. Tambayarsa tayi ina yake ya fada mata sai gata da plate guda daya da robar maltina.


"I am starving Hammana"


"Me yasa kike zama da yunwa" yace yana gyara mata kujera ta zauna.


"To ba kaine nake ta nema ba muci" tace tare da turo baki.


Bakin yake kallo yana lumshe idanu "kici abincin ni kuma ki bani bakin cin abinci yunwarsa nake ji"


Kunya Radhiya taji har ta rasa inda zata sa kanta. Awwab kuwa yadda take yi ga dimple dinta yana ta shigewa ya burgeshi sai da yasa hannunsa a wurin.


"I love this...." kanta ta sunkuyar yasa hannu ya rike kunnuwansa "sorry baby ina takura miki ko? Lets eat amma kinsan bazan ci na bakinki ba ko" ya kashe mata ido.


Bata fuska tayi "Ewwwww ka zama kazami dai"


"Kinga laifina an aura min ke"


Hannuwa ta nade a kirji tana cika tana batsewa yana mata dariya. Kawu Zakari ta hango ai kuwa ta daga masa hannu tana dariya za ta rama.


"Kawu Zakari tun dazu nake ta nemanka"


Fuskar Awwab ba shiri ta sauya ya bata rai kamar wanda aka yiwa duka. Yau dai ya ga wannan Kawu Zakarin. Dan kyakkyawan bafillatani ya karaso ya mikawa Awwab hannu. Radhiya sai sakin murmushi take sai da ta ga Awwab ya koma abin tausayi ta dena jansa da hira.


"Me yasa baka zo Antyn tamu ba ne?"


"Tayi nauyi bana so ta wahala"


Ba kunya Awwab ya saki fuska "ashe kayi aure"


"Eh muna da yaro daya ma ga na biyu a hanya" Kawu Zakari yayi murmushi.


"Kai Madallah wannan abu yayi kyau Allah Ya bar kowa da masoyinsa" Awwab yayi maganar farinciki ya mamaye fuskarsa abin dariya.


Radhiya tana dariya harda hawaye don yanayin relief din da ta gani akan fuskar Awwab kamar wanda aka yiwa bushara. 


Kawu Zakari yayi murmushi "mijinki yana da barwanci Radhiya. Ana kirana bari na baku wuri"


Sai da ya tafi Awwab ya kalleta "to dai kinji yana da aure matarsa tana shirin haihuwa ta biyu"


"Dadin abin nima ina da auren nan and God knows I love my husband"


Wani irin kallo yayi mata sai kuma kunyar abinda yayi ta kama shi ya cire hularsa ya rufe fuska tana jin muryarsa sai ka rantse kuka zaiyi "did I just make a fool of myself a gaban crush dinki Alheran?"


"Eh mana" itama ta yi kamar kukan zata yi.


Hular ya cire ya ajiye a gefe yana murmushi "laifinki ne Schatzi yanzu duk inda na ganshi sai na tuna da wai likita kike so"


"Hamma Awwab" ta kira shi bata so ko kadan ya rinka tunanin akwai wani kafinsa ko bayansa don babu.


Hannuwanta ya kamo ya rike "na'am"


"Kai na fara so kuma kai kadai zan so har abada in sha Allah" tace da wani irin yanayi.


Zuciyar Awwab ta sake yi mata wani babban masaukin "Alheran ki sassautawa zuciyata kada sonki yayi mata illa"


Bata sake magana ba ta nuna masa abincin. Spoon biyu ta sako amma yaki yarda sai dai suci da daya duk da tana kunya ga iyayensu ko ina amma haka ya tilasta mata suka ci babu magana sai kallo mai cike da ma'anoni.


DJ ya soma nasa aikin ana sako wakoki wuri ya kaure sai rawa wurin masu jini a jika. Ana soma wakar Nura M Inuwa ta amarya 'yar amana jikin Radhiya ya fara mazari tana hango 'yan mata musamman na Nijar 'yan uwansu ga Zahra can da Raji ana ta nishadi ta mike tsaye.


"Ina zuwa?" Awwab yace jikinsa na bashi rawa zata yi.


Wurin rawar ta kalla da ka tayi masa alama.


Maltina ya cigaba da sha hankali kwance "zauna Schatzi please"


"Hamma manaa" ta langabe kai.


"Allah bazaki je kiyi rawa a wurin nan ba"


Idanu ta zaro "harda rantsuwa?"


"Kinga ya dace?"


Juyawa tayi ta hango Yousuf yana cewa Arifah wai zaiyi rawa tazo tayi masa video.


Kuka take shirin yi tace "Ka gani fa kowa yana yi"


"Mu ba kowa bane. Sunana Awwab sunki Alheran...don't tell me you expect me to seat here and watch you dance a gaban mutane"


"To...to..." kasa karasawa tayi sai dai ya sani ran ta ya baci. Dauke kai yayi ta gama kunkunin ta yana tunanin ma harda hawaye amma yaki bari ta tashi saboda indai akan tayi rawa gaban mutane ne ya yarda tayi ta fushin ya rarrasheta daga baya.


Tana ji tana gani wakar ta kare aka sako wata Awwab ya tashi dama magrib ta gabato "ki jirani a nan zanje na shigo da mota ciki na kiraki mu tafi"


Shan kunu ta sake yi harda kawar da kai gefe ya sunkuyo da kansa wurin kunnenta "you still look sweet" ya yafi. Murmushi tayi duk da ba wai ta hakura bane. 


To filin rawa ma Zayyana na hada ido da Ibrahim yana zaune da robar ruwa a hannunsa ya sha kunu yana mata nuni da ta fita da hannu. Kafada ta noke ya kuma hade girar sama da kasa dole ta fita tazo wucewa ta gefensa ta murguda masa baki.


"Naji

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment