Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

katon falon zaka san gida ne na wanda ya isa duniya take damawa dashi. Dakunan da zasu zauna ta nuna musu da kanta su Radhiya suka zo gaishesu ita da Zayyana da Hibbah wadda tayiwa gidansu kaura duk da cewa Maman tasu tana gari. Duj inda 'yan mata suka hadu sunfi jindadin kasancewa tare musamman idan tasu tazo daya. 


Rahima wanka ta shiga yiwa kanwarta Khadi yarinyar tana ta yi mata rashin kunya 

"Ki dena tabani"

"Kin kona ni"

"Sai na fadawa Umma"

"Ni ki bani sabulun da kaina dan wanke"


Radhiya tuni ta hasala ta fada bandakin tace Rahima ta fita ta karbo mata kaya. Wani irin kallo ta yiwa Khadi yarinya ta bare baki za tayi kuka ta daure fuska "kina yi min kuka zan cillaki ta taga kowa ya huta mara kunyar kawai"


Yadda bata ga alamun wasa a fuskar Radhiya ba sai ta hadiya kukan dama na samun wuri ne tayi mata wanka kamar tayi amai ace yarinya kamar wannan tana kashi a wando ga wani kai a daddage babu gyara anyi kitson roba da yawa sun warware. Zuge sauran tayi ta zuba mata shampoo akan ta soma kukan sai ta fadawa Umma saboda bata yarda a taba mata kai ko Salamen sai tayi ta lallabata tunda tana ji da ita. Radhiya bata sake bi ta kan rarrashi ba sai da ta wanke kan nan tayi mata wankan. 


A kasa kuma Rahima dakin da suke taje a gaban Salame ta durkusa tace a bata kayan Khadi.


"Kin wanke wadancan ko kuwa ni zaki kawowa na wanke?"


"Yanzu zan wanke Umma"


Hajjo tuni ta fara zuwa wuya a kufule tace "Salame idan kinsan zuwa kikayi ki tsangwami yarinyar nan ina mai tabbatar miki yanzu zan kira Malamijo a mayar dake gida. Shashancin banza da hofi kai. Rahima ga jakarta can bude ki dauka"


Ummi tana wurin ita abin na Salame yanzu tausayi ne take bata saboda ta hana kanta sakewa ta hana wasu. Rahima da ta duba kayan ashe na babbar Salame ta dauko garin haushin an hanata zuwa da dukkansu. Rigunan sunyi girma haka dai ta dauki wata riga zata saka mata ga pants din duk na babbar. A kanta Salame ta huce haushin rashin dauko kayan daidai tana ta yi mata fada saboda bata san yadda zata yi ba.


Ummi ta kada kai "Rahima anjima bayan magariba kizo na aikeki dasu Zayyana"


"To Ummi" tace a sanyaye ta fita.


Tana cikin hawa benen Emzee na saukowa a gurguje yake tafiya suka kusa karo tayi saurin matsawa gefe. Idanun nan nata ne suka sauka a kan fuskarsa wadda a take murmushi ya maye gurbin bacin ran da ya sauko dashi saboda ganin Salame da yayi a cikin tawagar 'yan Sumaila.


"Kawar Soja daga ina?"


"Ni dai ba kawarka bace"


Murmushi yayi ya nade hannuwansa a kirgi ya tsare hanyar wucewarta "nima ba kawancen kawai nake so ba harda...."


Da sauri ta dago gabanta na faduwa "harda me?"


Kansa ya dukar daidai fuskarta "harda idanun Rahima...zan samu?"


Rikicewa tayi ta samu ya dan matsa ta kwasa a guje yana ta cewa tayi a hankali kada ta fadi. Sai da ya ga ta bace masa ya dan rankwashi kansa "Muhammad Zayyan kalau kake kuwa?" Ya tambayi kansa don ya rasa yadda akayi idan ya ganta daga bugun zuciya sai kasa controlling kansa da bakinsa da yake yi. Kai ya girgiza ya sauka ya dauki mota ya fita.


Bayan magariba kuwa Ummi ta bawa Zayyana dubu ashirin da biyar tunda ita ce babba tace dreba na jiransu su siyowa Khadi kayan sawa kuma kada su manta da takalmi, pants da brush. Sahad ya kaisu suka kwaso kayan da ya dace. Rahima tana da wata dubu daya cikin kudin da Ummi ta basu rannan suka siyo kayan kwalliya ta sayawa Khadi packet din ribbons na dari shida za ta yi mata kitso sai ta saka mata. Gida suka wuce da murnarta bayan sun nunawa Ummi tasa musu albarka ta wuce ta kaiwa Salame. Ba karamin dadi Salame taji ba don bata da komai sai dari uku amma dayake ta saka hassada da kyashi a zuci sai ta kyabe baki.


"Ki fada mata ina komawa gida zan turo mata kudinta don nafi karfin cin arzikinta yanzu ma don na manto jakar ne kuma a ciki kudina yake"


Tashi Rahima tayi zata fita Salamen ta kuma kiranta "ina kuma zaki je? dawo nan ki kwanta kusa dani"


To ai ko numfashin kirki bazata iya ba bare bacci a gabanta a tsorace take sosai Yadikko ta kama hannunta ta kaita bakin kofa ta ce ta wuce wurin yayarta Radhiya ta rufo kofar. Tana dawowa tasa hannu ta dauke Salame da wani gigitaccen mari. A kidime ta dago kai ga kannenta don ma Khadi tayi bacci. Hajjo tace tayi mata daidai.


Rai a bace sosai Yadikko ta nunata da yatsa "ba ni na haifeki ba Salame amma ina tsammanin rikon da nayi miki ya bani matsayin uwar da ta isa dake. Nayi miki rantsuwa daga yau har mu tafi idan kika sake yin wani abu domin cusgunawa Mairama ko Rahima sau naci mutumcinki la'ada waje. Mutuminyar banza wadda bakinciki ya yiwa tsatsa a zuci."


"Shiyasa taki gaba taki baya babu wani cigaba a rayuwarki" Hajjo ta kara da nata. 


Sunyi mata tatas don sai da tayi hawaye Yadikko ta kyaleta tana jin zafin wannan mummunar halayya ta Salame yarinyar da a da can tafi kowa shiru shiru a gidansu ashe macijin sari ka noke ce.


Da rana Ummi ta bawa Yadikko katinsu na shiga wurin taron haka ma ta baiwa Tante wanda zata bawa nasu mutanen. To dayake dama da yawansu sun zo ne akan ainihin na gidan ba wannan ba da gwamnati ko muce sojoji suka shirya ba sai ba'a sami rikici ba. Katin ba yawa garesu ba kuma dai bazasu so suje su bawa kansu kunya ba. An gama hada masu tafiya su Mami suna gidan Emzee tun safe da yasa kafa ya fita basu sake ganinsa ba.


Kafin sallar magariba sai ga Arifah da Mom dinta da gudu suka rungume juma ita da kanwarta Radhiya. Matar Alh Salisu itama ta iso aka fara shirin fita domin karfe takwas za'a fara taron.


Sai da Ummi ta shirya mijinta bayan kyakkyawar kulawar da ya samu tamkar kada ya tashi saboda yadda yake jin matar tasa a rai. Sababbin kayansa da suka dace da mukaminsa ta taimaka masa ya saka ta saka masa sabuwar farar safa da bakin takalminsa tafiyayye cover shoe. Ya sake gyara fuska sai wani annuri yake fitarwa. Sai da ta kammala dashi sannan ta fita itama ta shirya don tare zasu tafi.


Lace ne ta saka army green da digon gold a jiki. Mai kwalliya Mama ta dauko amma aka ce tayi mata matured kwalliya ba mai cika fuska ba kamar karamar yarinya. Tayi kyau matuka ta fito a Mairama Fillon Zayyan babu wata makusa sai hassadar makiya. Mayafinta gold ne sai takalmi heel da wata karamar dinner pause itama gold ga farin gilashinta ya sake fito da kyakkyawar fuskarta, hannuwa da kafafu sun sha jan lalle mai kyau da tasa 'yarta Rahima tayi mata. Matan manya ne suka fito ita da Mami, Mama, Tante, Mom din Arifah da Matar Alh Salisu. 


Fita suka yi kowacce ta shiga motar mijinta abin gwanin ban sha'awa sojoji na mara musu baya. Mutum biyu aka kara daga Nijar sai kuma Mubaraka yayar Zayyan da  matar Badaru. Yadikko kuma ta bawa Salame, Ayuba da Bature kati don Laila ita dama tuni Ummi ta bata nata tana tare dasu Radhiya ana ta shiri. 


Kowa ya gama nasa shirin suka fito Radhiya ta saka wata abaya mai masifar kyau da daukar ido ja da bakaken stones. Covershoe mai madauri ta saka baki sai purse da ta saka wayarta da hoda. Duka dama abayar suka zabi sakawa sai dai kowa tata daban. Ummi ta fito da 'yarya Rahima don itama ta saya mata wata baka mai duwatsu pink.


Idan kaga matan sai ka juya ka kara babu wadda bata yi kyau ba. Jawad da Femi a gida aka barsu saboda taron babu yara suka fito aka shiga motocin da suke jiransu.


Mazan ma ba'a barsu a baya ba sun hade duka cikin suits kamshi na dukan kamshi su ma suna gamawa sai Nicon Hilton inda za'ayi taron a wani babban dakin taro da yake cikin hotel din.


Decoration din wurin komai green ne da white an kawata shi fiye da zato ga ma'aikata a tsaye suna jira a shigo su nunawa kowa seat dinsa saboda akwai number a jiki. Awwab da Yousuf a matse suke da ganin amarensu abin takaici number din seat dinsu ya nesanta su da juna. Radhiya wata faduwar gaba taji da suka hada ido yana zaune kusa da Yousuf rike da waya a hannu. Ya hade cikin three piece armani suit khaki color da coffee coloured necktie ga brown din cover shoe. Daga inda yake a zaune ya daga wayarsa ya dauketa a hoto ta sadda kanta kasa a kunyace su Zahra suna mata dariya. 


Bayan an zazzauna kamar minti goma MC KDM sunan mai gabatar da taron wanda baya zuwa kowane irin taro dama sai na manya yace kowa ya tashi shugaban kasa zai shigo da first lady. Wurin zamansu daban aka zauna bayan national anthem da akayi. Ummi duk ta damu ina Karami sai da Zayyan yace ta kwantar da hankalinta dan nata yana nan za ta ganshi. An shiga taro ka in da na in hankula suka karkata suka koma ga MC da abubuwan da ake gabatarwa. Salame kallo daya ta yiwa Zayyan bata kara ba domin zuciyarta sai da tayi barazanar ballo mata kirji kuma abin takaici ga Alh Salisu a gefe sai taji duk ta muzanta a cikin mutane saboda kayan da ta saka na taron gidan Malamijo ne ganin kanta tayi wata koma baya a cikinsu.


Duhu hall din yayi a take hasken screen da za'a gabatar da tarihin Zayyan ya mamaye wurin. An fara da nuna hotunansa yana matakin farko a soja sai dariyar manyan baki kake ji kadan kadan saboda daga hoton kadai zaka iya gane cewa Zayyan Tureta ba karamin fitinanne bane. A hankali aka zo kan aurensa duka ana nunawa ne KDM yana bayani. An tsayar da hoton akan shi da Daddy da Baba Hadir ranar tafiyarsu Liberia. Daga nan ya cigaba da narrating rayuwar da Zayyan yayi sai da gwamnoni biyu suka zubar da hawaye musamman da aka zo video din fitowarsa daga motar da ta kaishi Nigerian Embassy lokacin da ya hadu da Excellency da Awwab. Su Ummi sai hawaye yasa hannu ya rike nata a hankali tace "I love you Sojana"


"I love you too Fillo" ya maida mata iya jin kunnenta.


An kare video din da wani hotonsa ne shi da Ummi, Radhiya da Emzee a falon gidansa bayan sun koma. Fitilu aka kunna mutane sai sharbar hawayen jin labarin al'ajabi na wannan soja.


MC yace kowa ya shirya domin ganin wasan da sojoji suka shirya domin murnar dawowar jan gwarzo jarumin jarumai.


Wata murya suka ji inda mai ita yake commanding Cadets 'yan uwansa da kowa ya shiga layi. Tsit hall din yayi kamar ruwa ya cinyesu lokacin da aka saka wani kida irin na band din sojoji sai gasu nan sun fito mutum arba'in cikon na arba'in da dayan shine commander din wannan parade din wato Cadet Muhammad Zayyan Tureta. 


Sun sha training ba na wasa ba daga shi har sauran shiyasa babu kuskure ko na motsi daga garesu. Bindiga ce a hannunsu duk da ba harbi zasu yi ba suka yi wani wasa da ita da ya burge kowa a wurin. Komai nasu tare kidan yana chanjawa da umarnin Emzee. Karshe mutane suka ga wadanda suka gama parade din sun matsa Emzee ya sake bada umarni sai ga wasu suna fitowa cikin tsari suka shiga sahu suka yi wani layi layi sai da suka durkusa kowa ya gane sun rubuta Nigeria ne ai kuwa mutane a tare suka karanta 

"NIGERIA"


Wasu suka fito a bayansu suma suka dunkule a kasa aka sake karantawa.


"WELCOMES"


Sai na karshen suma cikin gwaninta suka yi nasu layin tare da durkusawa.


"ZAYYAN"


Habawa sai wuri ya kaure da tafi da murna KDM yace

"Da wannan nake gabatar muku da tauraron wannan rana Major General Zayyan Muhammad Tureta"


Chanja kida akayi yazo ya haye stage din bayan ya yiwa dansa abim sonsa Emzee kallo daya tak yana tsaye ya kame sauran suna nan inda suke.


KDM yace ko yana da abin fada ga dimbin 'yan Nigeria da suke wurin da masu kallo live a gida.


"Thank you Nigeria you have given me 22years worth of love in a single night. Long live Nigeria, God bless my country"


Wani hawayen Mairaman Zayyan ta fitar batare da ta sani ba. A nan tsaye aka barshi shugaban kasa ya taso zai bashi award. Hularsa ya cire ya mika masa hannu sai da Mr President ya bawa kowa mamaki domin bai karbi hannun ba sai rungumar Zayyan da yayi sannan ya karbi award din daga hannun Chief of Army Staff ya mika masa.


Rahima babu inda take kallo sai Emzee da yake tsaye har lokacin a kame babu gajiyawa taji wata irin azababbiyar soyayyarsa tayi mata kamun in ba kai babu rayuwa. It was a moment da bazata taba mantawa ba a rayuwarta har abada. 


Bayan Zayyan ya zauna ne su Emzee sun koma mazauninsu Chief of army staff din da kansa ya gabatar da shirin Military Voice yace suna alfahari da wannan yunkuri na sanar da duniya sadaukarwar da sojoji da iyalansu suke yi. Sannan gashi sun sake ganin inda yake bukatar a duba domin tallafi ga wadanda suke cikin mawuyacin hali.


Sake yin duhu wurin yayi sai ga Radhiya tana gabatar da shirin sannan aka nuna bangarori daban daban a ciki wanda ya janyo zubar hawayen mutane da dama a wurin. Iyayenta da mijinta were so proud haka ma 'yan uwa.


MC KDM sai cewa yayi Radhiya ta fito tace wani abu game da shirin nan nata. Dif tayi kamar ruwa ya cinyeta ta kasa motsi.
[7/4, 7:40 PM] +234 806 334 4334: A bangaren Yousuf da Arifah kwatancen hanya ta rinka yi masa a kunyace har su ka iso titin da zai sada su da gidan inda daga nan ya gane hanya. Ciki ya shiga tunda masu gadin sun gane motarta kuma tana ciki. Duk ta daburce saboda auren nasu yazo da wuri basu gama sabo sosai dashi ba. Ya san da hakan shima shiyasa yake kokarin dinki duk wata kofa kafin su fara rayuwar auren sosai.


"A love yanzu yaya zaki yi dani?"


Fasa bude kofar tayi ta waigo kadan "me ya faru?"


"Kin taho dani gashi bansan hanyar komawa ba kuma bani da ko cent a jikina da zan nemi taxi. Ga dare..." yace da wani irin yanayin da zaisa a tausaya masa.


"Kaine fa kace zaka rakoni in karbi motar. Yanzu yaya kake so ayi?"


Kwantar da kansa yayi baya ya jingina da kujerar yana kallonta "Nima ki rakani" 


"Yanzu su Mom zasu dawo ace ina naje?"


Bude bangaren shi ta ga zaiyi cikin yanayin ko in kula yace "tunda haka ne muje kawai na kwana a dakinki kinga gobe sai mu shirya daga nan mu tafi zaifi sauki"


Idanu ta zaro tana kada hannu "wasa kake yi amma"


"Gadon naki karami ne? To ba sai ki kwanta a kasa ba ni ki bani gadon tunda nine bako"


Dariya ya bata ma yadda yake maganar tace "rufa min asiri...ko za ka kira Yayana yazo ya daukeka?"


"Ni bazan shiga rayuwar kanwata in hanata samun kulawa daga mijinta ba"


"Hmm Y love rigima kake ji naga alama"


"Ko daya" yace yana kamo hannunta ya rike yana murza yatsun.


"To ka dauki motar ka tafi da ita"


"In bata a hanya gobe ace ba'a ganni ba...naki"


"Bari na nemi dreba ya mayar da kai"


Bata rai yayi "bana so"


"Ya zamuyi to?" Tace tana tura baki don tsoronta daya kada iyayenta su dawo a gansu sai ace bata da kunya musamman Mom dinta. Bata san yaya akayi ba ya janyota rabin jikinta a cinyarsa ya rungumeta sosai yana shakar kamshin jikinta mai dadi. Kansa yana gefen wuyanta sai numfashinsa kawai take ji yace.


"Mhmmm mon amour" yana jin kamar su kwana a haka   "...inata baki haske, inata baki haske kinki ganewa."


Yadda hausar tasa ke fita da abinda yace ne ya sakata dariyar dole "kana ta bani haske..."


"Eh mana amma baki gane ba....kowane ango yana tare da matarsa ni tawa tana nuna min halin hausawan Nigeria"


"Ban dau haske bane" tace a hankali tana kokarin zamewa sai gashi tar an hasko wata torchlight mai mugun haske sosai cikin motar ta barin da yake. 


Arifah gabadaya ta gigice don kunya ta fasa guduwa sai ma kara kankame shi da tayi a kunyace bata son ko waye a tsaye ya ganta a haka. Yusouf kuwa ko a jikinsa sai ma sauke glass da yayi rabi har lokacin tana cikin jiikinsa. Security din yace da pidgin english "na Madam i dey find I never see her comot from the car"


Ko kalma daya bai fahimta ba sai ma kullewa da kansa yayi yace "pardon?" Sai kuma kawai ya dan taba kafadarta


"Ba fa na jin yaren nan ki kore shi kafin nayi masa ido daya na ganin matata"


Yadda yake bata rai ma abin dariya ne.  Haka ta daure ta dago kanta kadan "Oga Sunday I dey come"


"No wahala" mutumin yace tunda ya tabbatar tana nan ya juya abinsa.


Kokarin tashi daga jikinsa ta soma yi "Y love bari na hadaka da driver please"


Sake riketa yayi ta kasa motsawa "ke kuwa ki dau haske mana A love, biyoki nayi fa don mu taya juna murnar aure"


Duk wasu dabarunsa ta gama ganewa. Ko Radhiya kanwarta ai tasan ta wuce ayi mata wannan wayon bare ita. Wace murnar aure zata yi a kofar gida. Hannunta ta mika masa na dama ya riko da nasa ta dan daga hannun sama da kasa tana jinjinawa "congratulations on your...."


"Rike kayarki tunda baki daukar haske ga abinda nake nufi" yace yana kai mata wani irin kiss da ya hanata motsawa.


Dirin motocin da suka ji daga waje ne ya tayar musu da hankali su duka ta tashi daga jikinsa da sauri.

"Yanzu ya zamuyi?"


Tashin hankali karara a fuskarsa yace "nima ban sani ba, ba gidanku bane"


A tsorace take amma dole tayi dariya don ya fita rikicewa. Shiyasa yaso ta dau haske tun dazu ya samu ya gudu saboda Yousuf mutum ne mai kunya sosai. Ko lokacin da yaso Radhiya wannan kunyar ita tayi ta cutarsa ya kasa fada da wuri ashe rabon Arifah Nasiruddeen ne. Saurin kiran Awwab yayi yace yazo ya dauke shi su tafi.


***********


Bayan fitar Radhiya daga falon da sauri ya biyo bayanta amma bai ga alamunta ba. Da gudu ta shiga cikin gidan tana ji kamar za'a gane me tayi. Awwab zai kirata kenan don shi bai ki yau ya kwana a gidan ba Yousuf ya kira. 


"Ni gaskiya bazan zo ba rakiyar taka tayi kadan ni kuma yanzu na fara" yace masa yana dariya.


Yousuf ya kalli motocin su Baban Arifa "Kada muyi haka mana Awwab ni da na baka kanwata ya kamata ka kyautata min" 


"Ni ba kanwar na baka ba"


Daga murya Yousuf yayi amma kana ji kasan kawai damuwa ce "kada kasa na dage bikin nan sai ta gama ècole"


"Daidai kenan, sai ayi bikin da baby dinmu mu shiga gida mu uku ko hudu" bai san me ya dami Yousuf din ba amma dadin tsokanarsa yake ji yana dariya lokacin da Raji da Bilal suka fito kowa da murmushi saman fuskokinsu.


"A love kiyi masa magana" Yousuf yace da Arifa kamar yayi kuka.


Tana karbar wayar ta soma magiya don tana iya hango kallon da Mom dinta take sakar mata bayan ta fito daga mota. Yousuf sai ji yayi wani gumi na neman saukar masa duk sanyin garin. Tare da Arifah suka matsa wurinsu suna musu barka da dawowa.


"Yousuf ba dai sawa tayi ka kawota ba ka biye mata kai kuma?" Cewar Mom tana musu kallon daidai.


Awwab na jin muryarta da hannu yayiwa su Raji alama suka shige mota yaja suna dariya yau sun sami abin tsokanarsa. Rakiyar yau bata yi ba sai dai ko gobe a sake.


Yousuf yace da Mom "na ga ta karbi motar ne ga dare. Su Awwab nake jira zamu tafi suna hanya"


"To babu damuwa bari na wuce"


Excellency da mutanensa yayi gefe suna magana yana yiwa ango da amarya murmushi yace su shiga ciki kafin Awwab din ya karaso. A ransa kuwa dariyar yadda Mom sarkin takura ta ritsa su yake yi. Tunda anyi aure ba shikenan ba, ko don tayi sa'a ba sai da safe ya dawo mata da 'yarta ba.


A cikin gidan ma kamar yana kan kaya hankalinsa bai kwanta ba saboda hawa da saukar da Mom ta rinka yi sai da Awwab ya kira shi. Da sauri ya fita daga gidan yana sauke ajiyar zuciya.


Kai daren ranar kamar yayi ihu saboda yadda su Awwab suka saka shi a gaba da tsokana. Mami tana jiyo hayaniya daga dakin Awwab inda suke kwana kamar wasu yara. 


"Irin haka basarwa ake yi Yousuf" Awwab yace yana mike bayansa akan gado saboda gajiya.


"Zan rama duk kuyi ku gama. Kuma matsa min na kwanta yau nan nake so."


Ture Awwab yayi tsakiya dariya ta hana shi tabuka komai har Yousuf din ya kwanta a wurin mutum biyu don da gangan ya bude hannuwa wai baya son takura.


**********


Fauziyya da Zahra sun riga Radhiya shiga daki. Rahima da Zayyana wani dakin suke kwana a kasa yanzu saboda yayyensu dake saman a dakin Radhiya ga yara biyu.


Yadda take sauke numfashi Zahra ta tambayeta ko gudu tayi ta gyada kai.


"To dai mutum ya girma guje guje ba naki bane amaryarmu" Zahran tace mata.


"Kyaleta fa tayi abinta nan da sati biyu ko da kudi nasan da wuya ta iya daga kafa"


"Me zaisa Adda Fauzi?" Radhiya tace da iyaka gaskiyarta.


Zahra tace "Kyale wannan yayar taki kin santa sarai da tsokana"


Tawul ta dauko za ta cire kayanta ta shiga wanka Fauziyya ta fara yi mata kallon mara gaskiya saboda a takure take wanda ba halin ta bane.


"Amaryar Hamma kada kice min janbakin nan ya goge...gaskiya ina jin ba mai kyan kika saya ba. Ni fa shiyasa abu designer bai dameni ba, ance baya fita da wuri sai an goge shi amma ke lips dinki kamar baki shafa komai ba. Kalli ki gani" ta juya tana nunawa Zahra da tsokana.


Radhiya ta rasa yadda zata yi sauran abinda basu gane ba ma sun gane don ba karamar kunya taji ba, shikenan Hammanta ya janyo mata. Turo baki tayi kamar za ta yi musu kuka "to ba...ba...uhmmm tissue na saka na goge"


Fauziyya ta saki fuska "ohhh irin makeup remover dinnan ko? Please nima bani nagoge don ni sanyi nake ji bazan iya wanka ba"


"Fauziyya ki kiyayeni ko in kira Ya Bilal yazo ya kwashe mana ke kowa ya huta. Mutum yana fama da kansa amma baki baya shiru" cewar Zahra amma daga ita har Fauziyyan dariyar tsokana suke yiwa Radhiya. Yau mai balotelli an dinke mata baki.


Cikin dariya Fauziyya tace "wai ma in tambayeki, makeup remover din baya goge fuska iyakarsa baki kawai?"


Sai yanzu Radhiya ta fahimci ina suka dosa da wannan tambayar da dariyar. Aka yiwa wani ma ta rama bare an shiga gonarta. 'Yar dariya tayi tana sunkuyar da kai tace "sauran yana bakin Hammana shi ya goge min"


Idanu Fauziyya ta zaro Zahra kuwa dariya harda rike ciki. Suna son juna idan an hado kamar kar a rabu saboda irin wannan dramar.


"Kika bashi ya shanye?" Fauziyya tace fuskarta kadai sai tasa mutum dariya.


Radhiya ta gimtse dariyarta ta zauna kan gado ta dora kafa daya kan daya tana daukar wayarta. Sunan da ta saka masa Mon Chèri (my sweetheart) ta nemo tana nunawa Fauziyya "In kira shi ki tabbatar?"


"Zahra ki fadawa su Mama tun wuri kada gobe labari ya wuce goge lipstick a bashi matarsa"


"Ba tambayata kika yi ba Adda Fauzinmu" tace da shakiyanci.


"Ah to matambayi baya bata gashi nan an dora ki akan hanya yadda zaki gane" cewar Zahra har lokacin dariya take yi sosai ita da Radhiya. Katse dariyar suka yi a dole da suka ji ance 


"Schatzi" daga cikin wayar hannunta.


Su duka ukun suka kalli wayar harda ita da ta kira bata sani ba kafin suka fice daga dakin a guje suna dariya sai ka rantse yara ne masu kananun shekaru. Awwab da yaji shiru sai ya kashe wayar yana tunanin kila bata san ta kira ba saboda dare yayi.


Da suka koma dakin ma suna kallon juna sai su kwashe da dariya Fauziyya na

3 Comments On KU DUBEMU
avatar
aisha-5-7-4-8

1 year ago

Reply

Gaskiya novel inan akwai dadi

avatar
muzanbil

1 year ago

Reply

Replying to aisha-5-7-4-8

Da gaske

avatar
salma-6-3

1 year ago

Reply

Masha Allah tabarakallah Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment