Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

remote ya shiga bubbuga mata har se lokacinda ta tashi.

"Ke bakisan lokacin sallah yayi bane?"

"Ka kama ka barni da yunwa laifin waye don banyi sallah akan lokaci ba?" Ta tambayesa cike da rashin kunya yayinda take adjusting position nata don zama. Ledojin ta shiga bi da kallo daga bisani kawai tasa hannu ta janye d'aya daga cikin ledojin da Amal ta had'awa Afzal wanda ke d'auke da Aldeb dasu samosa da wuri ya mik'a hannu ya wabce har yana neman ji mata ciwo.

"Ya haka Malam? Ko abincin ma hana ni ci zakayi?"

"Yes tunda kika d'au wanda ba naki ba" ya amsa ta a takaice, takeaway'n daya tsaya ya sai mata a restor ya wurga mata "Ga naki."

"Lallai ma! D'an wannan zaka bani? Sauran kuma fah? Ka kaisu ina? Ai wannan rashin adalci ne."

"See banida lokacin exchanging words da ke in kinga ya kasa miki bazaki iya ci ba kinada mota kina iya fita ki sai abinda ya miki" yayi maganan had'e da zaro wallet nasa dubu uku ya k'irga ya ajiye mata "Here you go amman kam wannan ba naki bane don ko wacce tabani ma tasan da zamanki amman batace in ragar miki da komi ba" yana kaiwa nan ya tattara abunsa ya kai fridge ya sanya su ciki had'e da sa key ya zira a aljihunsa. Binsa da mumunan kallo Nazeefah keyi yayinda ya zo wuceta ya shige d'akinsa. Mik'ewa tayi ta nufi fridge d'in ta gwada bud'ewa seji tayi ya kulle da key don takaici ji take kaman tasa hannu aka tayi ihu sa'ansa d'aya yasa key da kuwa sede ya tarar da empty goruna next idan ya fito. Kuma wai don rashin kunya har yake ce mata wai wacce ta basa bata ce da ita aciki ba? Hmm wato budurwa ma yake da? Ai kuwa bazata fasa kula samarukanta ba itama face ya dena kula 'yan matansa. Dry abincin nata ta zauna taci ta kora da ruwa sannan ta zarce d'akinta tayi sallah.

***
Wajajen 10:12pm Nazeefah ta ajiye wayarta da take ta faman chatting na asara tun d'azu. Sallan Isha ta idar sannan ta fito parlour don neman abinda zata sa a baki. Afzal ta tarar zaune a parlour da plate na samosa da su spring rolls kusan biyu a gabansa ga kuma flasks da take da tabbacin juice ne a ciki se faman cin abincinsa yake yana kallo. Murmushi ta sakar wa kanta don kuwa a nata tunanin kalan abincin dake gabansa itama ya sai mata. Cike da jin dad'i ta k'arisa dining da mamaki ta tarar da shi empty ko leda d'aya babu akai bale kula to ina abincin nata ita? Kitchen ta shiga ta leqa sede shar ba alaman komi, yau akeyinta. Parlon ta dawo taje tayi tsaye a kansa "Malam where is my dinner I'm hungry" ta sanar dashi cike da gadara kaman wanda bazeyi magana ba yace, "Seki shiga kitchen ki girka abinda ya miki."

"Ban gane inyi girki ba ka ta6a jin inda Amarya tayi girki ne?"

"Aww ashe amarya kike" ya amsa har anan be ko juyo ya kalleta ba balle ya san wani kalan kaya take sanye dashi.

"Wallahi Afzal bana cike da rashin mutunci wannan son kai da mey yayi kama? Kai ka sai wa kanka abinci ni kuma kace min inyi girki? Yanzu baka ji kunya ba."

"I really don't know what you use your ears for I told you wannan duka da kike gani anan bani akayi bawai fita nayi na siya ban sai miki ba and don ke kuma bazan fita da daren nan ba da sunan sai miki abinci ko ki nemi abinda da zaki dafa kici or simply kisha ruwa ki kwanta bana son hayaniya kina iya barmin kai."

"Kai wai rashin mutunci ka gada ko? Mu zuba ni da kai a gidan nan and see who will surrender first aikin banza kawai!" tana kaiwa nan ta nufi d'akinta Cookies ta k'wak'ulo cikin kayakinta ta zauna taci don kuwa ta gommaci ta kwana da yunwa data aikata abinda Afzal yace mata dan kuwa be isa yayi iko da ita ba. Juice nata tasha akai sannan ta cigaba da chatting nata har se lokacinda bacci ya d'auketa. Kamar jiya yau ma Afzal ne yazo ya tayar da ita sallan Asuba, yana mey mamakin sakaci irin nata ace da girmanta amman bazata iya sa alarm ta tashi tayi sallah ba yaso ta koma baccin.

Haka rayuwar nasu ta cigaba da kasancewa ba ci gaban ko k'ala, dai-dai da rana d'aya Nazeefah bata ta6a d'aukan tsinstiya ba da sunan shara iyaka idan d'akinta ya gama baza datti sannan zata d'an share sama-sama. Afzal da bai saba da zama cikin k'azanta da daud'a ba tuni yasa Micheal ya nemo masa me aiki na miji wanda bayan kwana bibbiyu yake zuwa ya share gidan tas ya kuma yi mopping harda goge amman banda d'akin Nazeefah kasancewar dokan da Afzal ya kafa masa. Bugu da k'ari Afzal be fasa siyo musu abinci ba kaman yadda ya d'au alk'awari wa kansa. Abinda ya kama daga kan breakfast, lunch and dinner duk ya d'auke wa Nazeefah ita de aikinta bai fin taci ta sha tayi wanka da bacci sede abinda yake damunta d'aya ne, yawan fitan da Afzal keyi. Ace mutum kullum bai yini a gida? Ya fita tun safe se yamma abinda ke kawosa kad'ai shine delivering abincinta. Bayan tana da tabbacin an basa leave a office balle yace aiki yake zuwa. Shin ina yake zuwa? Toh wallahi itama baza a barta a baya ba. Afzal na fita itama zata d'au wankanta tabi bayansa. Dai-dai da rana d'aya Afzal be ta6a tambayarta ina take zuwa ba koda kuwa ya dawo gida ne ya tarar bata nan harkan gabansa kawai yakeyi idan ta dawo kuwa ko kallonta baiyi bale ya tambayeta daga ina tafito. Tun abun bai damun oganniyan taku har ya soma ci mata rai yana tsaya mata a wuya shin shi Afzal d'innan wani irin miskilin mutum ne? So take yace ze mata magana kan yawon da take wataran amman ina. Rashin hankalin nata har ya kaiga wani sa'in ma mangariba ba a gida take ba amman haka ko d'aga ido ya kalleta bai yi idan ta dawo. Ita ba haka taso abin ba taso ace ya gwada tinkarar ta koda so d'aya saboda su yita ta k'are tayi masa rashin kunya iya son ranta in yaji zafi ya sake ta amman ko shiga harkanta baiyi a gidan.

Kasancewar k'arfe bakwai na safe Amal zatayi jamb nata yau tun shida Afzal ya gama shirinsa, yana cikin shan black tea sega Nazeefah da tun d'azu ya tada ita sallah amman tak'i tashi se yanzu ta fito, yanzun ma sabida ishin ruwan daya isheta ne. Da fari da ta gansa tayi tunanin ko office zasa amman seta gansa sanye da half jumper tabbatar mata da cewa ba chan d'in za sa ba. Lallai ma kuwa sabon iskancin daya koyo kenan, wato yanzu sammako ma ze fara yi toh Allah ya taimakesa ya kawo su ranan da zata tabbatar da zargin da take akansa in har ta tabbatar 'yan matan waje yake bi toh in shaa Allahu zamansu ya k'are don bazata hak'ura ba har seya sake ta, aikin banza kawai. K'arisawa gun fridge d'in tayi ta d'au ruwa ta koma d'akinta shiko yana kammala breakfast nasa ya fice. Already Amal na jiransa lokacinda ya isa, Allah bada sa'a su Mami suka mata sannan tabi bayan Afzal suka fito. Acikin Unimaid tayi jarabawartan, bayan addu'an da Afzal yayi mata ta k'arisa cikin exam hall d'in, Afzal be je ko ina ba zama yayi cikin motarsa kusan na awa biyu da k'ari yana jiran fitowar Amal. Sanin dole zata ji yunwa kaman yadda shima yakeji don kuwa gashi rana ta fito, bayan data gama exams d'in ya wuce dasu restaurant inda suka karya da chips sannan ya sai wa Nazeefah nata. Har gida ya mai da Amal ya komo nasa shima, akan dining ya ajiye wa Nazeefah abincin nata ya k'arisa d'akinsa ya kwanta don biyan baccin da yayi missing.
Bayan kwana uku results nasu Amal ya fito. Tunda Amal taji results ya fito hankalinta ya tashi jira kawai take Afzal ya kirata yace mata ta fad'i. Shiko Afzal a ranan da aka saki results d'in ya shiga website d'in ya duba mata inda ya tarar taci...



RANA D'AYA!
#RD
Love... King Miemiebee👄✨
[12/08, 22:40] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣

💦💦 🍃🍃🍃
*RANA D'AYA!*
💦💦 🍃🍃🍃
May, 2018
beeenovels.blogspot.com

_Written by Miemiebee👄_


*PAGE 1⃣0⃣*


Points har 225, damn! Sosai yaji dad'i ya kuma yi alfahari da ita yana me kasa 6oye farin cikin da ya tsinci kansa a ciki. Layin Mami ya kira take, kasancewar itace ke kusa da wayan yasa ta d'aga, bayan sun gaisa ta kaiwa Amal wayar tun kan ya buk'aci hakan.

"Assalamu alaikum Yaya ina yini?" Ta fad'a lokacin da ta amshi wayan daga hannun Mami tana mey azawa a kunnenta.

"Wa'alaikumus salam Lily, ya kike?" Ya amsa.

"Alhamdulillah ya gida ya Nazeefah kuma?"

"Lafiya Alhamdulillah."

"Toh masha Allah."

"Hmm" ya numfasa had'e da yin shiru, hakan yasa Amal tambayar ko lafiya.

"Results naku ne ya fito" ya sanar da ita cikin wani irin salon daya sa Amal yanke hukuncin ta ma riga ta fad'i exams d'inne.
"Innalillahi!" ta furta yayinda zuciyarta ta buga.
"Ban ci ba ko?" Ta tambayesa a hankali bayan d'an lokutan data d'auka.

"Toh gashi nan de-" ai bata basa daman k'arisa abinda yayi niyya ba ta katse wayar. Ba shiri ta fad'a bayi ta d'auro alwala, tana cikin shimfid'a sallaya wayan ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Afzal ke kira wani tsinkewar zuciyarta ta kuma yi ba shakka ta fad'i d'inne in ba haka ba da tun da ya kira ze sanar da Mami. Nata ya k'are yau, shin ina zata sa kanta? Da wani idon zata sake kallon Afzal?? Hmm har ta hango tokari da habaicin da Mami zata yi mata idan ta gano ta fad'i jarabawar nan. Sanya wayan tayi a silent sannan ta shiga kawo nafilfilu.

Ta 6angaren Afzal daya san rud'ewa irin na Amal kuwa da gan-gan yayi hakan dama ba don komi ba se don yayi dariya kamar yadda yakeyi yanzu, har picturing fuskanta yadda ta rud'e yake a kansa. Two more missed calls ya k'ara mata har anan bata d'aga ba don haka ya tura mata sak'o;

'Lily pick up that phone.' Dai-dai lokacin da take sallame sallan sak'on yake shigowa batayi ta kai ba seda ta gama tofe addu'o'inta sannan ta lek'a screen d'in. Bata kai ga bud'ewa ba se ga call nasa n shigowa ta sani muddin bata d'auka ba ransa ze 6aci, ba don tana so ba ta d'aga had'e da yin shiru. Shima shirun yayi don kanta ta soma magana.

"Yaya don Allah kayi hak'uri" jin yadda ta rud'e shiko ya canza ra'ayinsa na sanar da ita aslin batun ya soma da cewa, "Lily meya faru?"

"Tell me Yaya na fad'i ko?" Ta tambayesa cike da tsoro.

"Your results..." se kuma yayi shiru.

"Yaya don Allah kayi hak'uri wallahi ni kaina ban san ya akayi na fad'i ba please don't tell Mami."

"Am so disappointed in you Lily shin duk abubuwan dana koya miki daman ba ganesu kike ba kokuwa amfani da computer d'inne baki iya ba?"

"Wallahi ni kaina ban sani ba amman kayi hak'uri don Allah."

"Nide nayi asaran biyan kud'in jamb."

"Please kayi hak'uri" ta furta a hankali yayin da takejin haushin kanta.

"Yanzu Lily ki rasa nawa zaki ci se 225?"

"Na shiga uku 225!" ta nanata a rud'e tsabagen yadda ta rikice hankalinta be ma bata taci ba se chan abin ya buga mata kai "225 fa kace Yaya?"

"Eh" ya amsa.

"Toh ai naci ko?"

"Congratulations Lily" ya fad'i yana mata dariya.

"Omg! 225! Yaya I made it! Oh Alhamdulillah" take ta sauk'a k'asa tayo sujudush shukur tana meyiwa Allah godiya sannan ta cigaba da ihun, don kanta tayi shiru.

"Kin gama ihun? Afzal daya nisantar da wayan daga kunnesnsa ya tambaya.

"I'm sorry Yaya ban tsammanin zan iya 6oye farin cikina."

"Sure you can't, ko ni nan na kasa 6oye nawa. Keep it up Lily I'mso proud of you."

"Thank you Yaya but the accolades goes to you, kai ka koya min ababe da dama."

"Duk da haka Lily kinyi k'ok'ari you know what? Kin cancanci kyauta."

"Kai Yaya dagaske?" Ta tambaya cike da kunya.

"Yup kina gida gobe?"

"Eh" ta amsa.

"Good, zan shigo in shaa Allah."

"Toh Yaya seka shigo amman fa ka tsinka min zuciya wallahi na d'au na fad'in ne dagaske har na soma tunanin da wani idon zan sake kallonka" ta fayyace mai.

"Matsoraciya kawai ashe baki yarda da kanki ba."

"Not really kasan shi E exams sa'a ne ba a yi mishi baki."

"Da wannan kuma but even still my Lily is such a clever girl."

"Thank you Yaya" hira kad'an suka ta6a sannan suka yi sallama. Kan Mami da Papi ta fad'a bako sallama ta soma yi masu wak'an taci jarabawar ta inda suka mugun tayata da murna barin ma Papi. Alwala duk suka d'auro sukayi nafillah raka'a biyu don yima Allah godiya.

Washegari kaman yadda Afzal ya d'au alk'awari hakan ya cika yazo ya d'auki Amal ya kaita shopping amman kunya yak'i barinta ta d'au koda abu d'aya a ganinta wai hakan ya zamo rashin godiya taya akan duk d'awainiyyan da yake mata da kuma wanda zeyi mata a nan gaba ace ya kawota shopping ta baje tana kwasan kaya?

"Lily kina son muyi fad'a ko?"

  "Yaya wallah nida nasan nan zaka kawo ni ma da ban biyoka ba tun farko don Allah karka damu am good."

"Lily nifa na kawoki or isn't wrong for a brother to take his sister shopping?"

"Not at all Yaya kawai ba abinda zan iya d'auka anan ne."

"Dalili? Ba abinda ya miki anan? Kin fi son kiyi purchasing products naki online?"

"Waye ubana?" Da sauri ta bige bakinta "Ni ba abinda nake nufi ba kenan kawai deh..." se kuma tayi shiru.

"Look kin de san rantsuwa ko?" Kai tayi saurin gyad'awa tana mey k'ure masa ido "Toh wallahi Lily muddin baki d'au ko da abu d'aya ba anan believe me anan d'in zamu yini inda hali har ma mu kwana."

"Yaya please karka ce haka" tayi saurin fad'i.

"Am damn serious" ya sanar da ita cikin tattausar murya. Yana kaiwa nan ya juya ya je ya zauna gun cashier. Tsaye tayi gun jugum totally out of what to do, daga bisani ta juya ta shiga bin store d'in da kallo wanda ya k'unshi kayan kwalya zalla da turare da makamancin hakan. Yau ake yinta kwata-kwata idan za'a k'irga abubuwan data san amfaninsu a shagon basu fi biyar zuwa shida ba toh me zata d'auka don su rabu da Yayanta lafiya? Chan tunani ta fad'o mata gun turaruka ta nufa tuna turarenta ya kusa k'arewa. Bin su ta shiga yi da kallo tana me bud'e kan tana shinshinawa don samun wanda k'amshin zey mata, chan ta d'ago wani da aka rubuta 'adolfo-dominguez' a jiki. Ba k'aramin k'amshi turaren yayi mata ba gashi nan d'an tsut d'an k'arami hakan ya sata yanke hukuncin cewa bazeyi tsada ba. A nitse cike da jin dad'in ta k'ure Yayanta ta tako gun cashier'n inda Afzal ke zaune daga gefe hanklinsa ya duk'ufa akan wayansa se faman latsawa yake tayi gyaran mrya wanda hakan ya sanya sa d'ago kai.

"Yes where is your basket?" Ya tambayeta, shiru tayi bata ce komi ba "kin d'ai san bana wasa dake ko Lily?"

"Yaya gashi na d'au wannan" ta furta cike da tsoro tana mey fito da hannunta data 6oye a bayanta.

"Mey wannan d'in?" ya tambaya yana bin hannun nata da kollo.

"Turare" ta amsa a takaice. A tunaninta ze hau mata k'orafi setaga yana murmusawa ko dariyan mey yake? Ta tambayi kanta. "Kawo ayi miki billing" k'arisawa tayi ta bawa cashier'n inda ya d'au pointer don gano price d'in.

"N11,765 (dubu goma sha d'aya da naira d'ari bakwai da sittin da biyar)" ya sanar da su. Da idanu na zubewa a k'asa domin mamaki da na Amal sun jima dayin hakan. Dubu goma har da sha d'aya fa taji cashier'n ya ambata kode ya 6ata ne? D'an wannan turare dayake nan kaman a sa a hancin ne har dubu da k'ari lallae se yanzu ta fahimci ma'anar murmushin da Afzal keyi mata ashe de yasan tsadan turaren ne. Ita haushin kanta ma taji shin meya hanata duba price d'in bayan gashi an manna a jiki harda ticket nasa?

"Akwai abinda zaki k'ara?" Afzal ya tambayeta cike da neman tsokana.

"Cashier d'an kawo wannan d'in Yaya zan canza turaren."

"Ina wasa dake ne Lily?"

"Yaya wallahi almubazaranci ne taya turare kad'ai har dubu goma? Don Allah kar ka biya kud'in ni da nasan ya kai haka tsada ma da ban d'auka ba tun farko" Shiru ya mata tare da zaro wallet nasa ya k'irga kud'in ya mik'a masa. Don takaici Amal ji take wane ta kashe kanta, da fesa turaren dubu goma ai gara a baiwa mutum kud'in ya biya buk'atunsa dashi.

    Godiya sosai tayi masa sanda ya sauk'eta bakin lungun gidansu. Tazo dai-dai da shiga gida kenan sega Ameenatu na fitowa daga gidansu nan de suka gaisa inda Azee ke tayata murnan cin jarabawar da tayi yayinda Amal tayi mata godiya.

"Toh daga ina kuma kika fito haka?"

"Wallahi babu nida Yaya ne muka d'an fita."

"Oh Baby! Wannan Yayan naki fa ba k'aramin ji dake yake ba 'yan unguwa har sun soma cewa saurayinki ne."

"Don girman Allah su rufa min asiri ina ni ina Yaya?" Ta tambaya had'e da kwararo idanunta waje. "Wallahi ba komi a tsakanin mu illa soyayyan dake tsakanin Ya da k'anwa."

"Toh deh tayi tsami ma ji" ta amsata cike da gatsine.

"Wallahi Azee babu komai, haba mana kiyi tunani da kanki ina zan kai na miji kaman Yaya? Kema kinsan yafi k'arfina."

"Haka de kikace amman wata soyayyar bata fi wata ba."

"Na amince da hakan amman komin taurin kan zuciya still tasan da wa take yi, ba yadda za'ayi zuciyata ta soma son Yaya da wata manufa so tun wuri ku da 'yan unguwa ku sa hankalinku cikin ruwan sanyi."

"Nifa ban ce komi ba, rana de bata k'arya, tukuna me wannan kika rik'e sekace k'wai a hannu?" Ta tambayeta had'e da zuba ido wa ledan da Amal ta damk'e a hannu.

"Wannan?" Amal ta d'aga tan nuna mat "Ai wannan yafi k'wai buk'atan adana."

"Ko meya saki fad'in haka?"

"Ke matsalarki bawai a baki labari bane kika tashi sekin k'ara gishirin ki a kai ki baza mutum a unguwa."

"Haba k'awas wani asirin kika ta6a bani nayi miki haka?"

"Kar deh?" Ta watsa mata harar.

"Ki yarda da ni wallahi ko Falmata bazata ji batun nan ba."

"Hmm kawai Yaya ya kaini wata shago wai in d'auki duk abinda yamin..." nan de ta baiwa Azee labarin abinda ya faru baki wangalau cike da k'in yarda Azee ta tsaya tana kallon Amal ita kan ma tak'i yarda seda Amal ta nuna mata receipt d'in.

"Wai wai wai gaskiya Yayan nan naki dagaske yake, kut!" Tayi exclaiming cike da k'in yarda.

   "Ai kede ki bari hakan ma wai yana tambaya ta ko da akwai wani abinda nikeso again."

  "Gaskiya Yayan nan naki na sonki Baby kuma kikace ba komi a tsakanin ku kai! Da akwai ayan tambaya."

"Kinga irin halinki da baniso ko?"

"Toh afuwan afuwan yanzu de d'an bani in fesa turaren a hammata na."

"Shamawai! Ni me shi ban fesa ba se ke?"

"Yi hak'uri mana ta Yaya Afzal ke inba ke bama har a kaiki siyayya ki tsaya kina plako ai idan baki buk'atan abubuwan kwalyan mu munayi kuma idan ba son kai bama da kikazo siyan turaren ai ko yan dubu ne seki d'aukan mana da Falmata."

"Eh naji d'in matso kusa in miki feshi d'aya a hijabi amman ko ba a hammata ba Wallahi don koni ba kazai zanna shafa turaren nan ba se idan ta kama. Chan saman wardrobe m zan ajiye." Rok'arta Ameenatu ta rik'ayi har seda Amal ta amince ta bata turaren ta fesa a hammatarta, tamkar k'wai haka Amal ke tattalin wagga turare.

****

Da auren Afzal da Nazeefah wata d'aya da k'imanin sati biyu kenan Afzal yaga fa baze iya da siyan abinci ba kullum bayan gashi shi ba gauro ba. Wannan ma a gefe, hutun da Nazeefah ke samu ya soma yin yawa, na farko ko shara batayi bale mopping da goge-goge don haka ya yanke hukunci daga yau ze dena siyo abinci ita zata soma yi musu girki tunda Allah yayi ya biya sadaki.

Washegari, kamar yadda oganniyan taku ta saba se chan shad'aya saura ta tashi. Tayi brushing ta fito sanye da kayan baccinta gashin kan nan a hargitse wane gidan tsunstu. Dining ta nufa inda ta tarar da shi empty. Dank'aree! Ta furta a zuciye bade abinci Afzal ya sai ba ita ba yau? Juyowan da zatayi se ga Afzal ya fito sanye da k'ananun riguna se buga k'amshi yake. Hannunsa rik'e yake da wata k'aramar saucer wanda ke nuni corn flakes yasha aciki. Gabansa tasha da wuri lokacinda ya zo shiga kitchen d'in tare da kama k'ugunta "Mallam ya ina breakfast d'ina?" Ta tambayesa cike da rashin kunya ko gaisuwa babu. Banza da ita yayi tare da niyyan bin gefenta ya wuce inda ta sake taresa.

"Ban gane ina maka magana ba kana miyar dani 'yar iska where is my breakfast?" Kaman wanda baze amsa ta ba yace "Tunda dumb head naki ya kasa figuring out miki abinda ya faru, abinci ne na daina siya, starting today ke zaki fara girki a gidan nan."

Murmushi kad'ai ta iya ta saki yayinda mamaki ya mamaye mata zuciya. Ko k'ala ta kasa ce masa da kanta ta matsa mishi ya shiga kitchen ya ajiye saucer'n ya fice sannan ta shiga ta dafa indomie sharp sharp taci. Wajajen k'arfe uku Afzal ya dawo, ya d'ibo yunwan duniya ya taho dashi da niyyan cin abinci ya tarar da dining empty, banda plate na macronin da ya sha had'i da minced meat aciki dage gaban Nazeefah tana ci,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment