Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bata fita school ba saboda ba wani serious lectures sukeyi ba, shima Afzal na a gida saboda ba aiki, tana zaune a d'aki ta nad'e k'afa tana tsotsan tsamiyan biri tajiyo wani irin sharp pain a mararta. Tuni tayi watsi da plate na tsamiyan birin ta sauk'a k'asa, da cikin nata ya sake murd'awa ta sa wani d'ankaren ihun da seda Afzal dake parlour ya shigo ba shiri, kanta ya yo da wuri yana tambayarta ko lafiya.

"Yaya call Mami up I think I'm in labor."

"Labor?" Ya sake nanatawa a razane. "Sure!"

"Yaya kayi sauri wayyo Allah cikina zan mutu" nan da nan ya kira Mami. Cikin mintuna k'asa da talatin ita da Mummy suka iso kafin nan ba irin yak'ushi da masifan da Afzal be sha ba. Amal se kuka da k'yar Afzal ya d'agata ya kaita mota Mummy ta biyo su da maternity bag nata duka suka yi asibiti inda akayi delivery room da Amal. Mutum d'aya aka buk'ata da ya shiga cikin d'akin da Amal nan su Mummy sukace Afzal ya shiga amma d'ankaren tsoro ne dashi atapir yace shi baze shiga ba sede cikin d'ayansu ita da Mami d'aya ya shiga. Baze iya jure ganin Amal tana kuka haka ba bayan ba abinda ze iya yi daze tsayar da azaban da take ji ba. K'arshe de Mami ce ta shiga, Amal se ihu take yi muryanta akeji ko ina a cikin asibitin Afzal ko zama ya kasa se safa da marwa yake a haraban d'akin yana mey rok'on Allah ya sauk'e masa matarsa lafiya. Bayan several pushes Amal ta samu kanta, ta haifo zankaleliyar 'yarta. Ana gama kimtsa su akayi ma Afzal magana.

"Congratulations matarka ta sauk'a lafiya ta samu 'yarta both the mother and the baby are in good health zaka iya shiga ganinta." Dr ya sanar dashi da Mummy.

Wani irin sanyi Afzal ya jiyo a jikinsa "Alhamdulillah Alhamdulillah thank you so much Dr." Ita Mummy dan farin ciki tama kasa magana.

"You're welcome" daga fad'in haka yabi gefensa ya fice nan Afzal da Mummy suka k'arasa cikin d'akin. Wajen Amal tasa ya soma nufa had'e da placing mata peck a goshi. "Sannu da k'ok'ari my Rania, Allah yayi miki albarka sannu ko?"

"Ameen Ya Omri" ta amsa a galabaice tana mishi murmushin dole.

"Ga chan 'yar tamu achan" Mami tayi masa nuni da crib da aka sanya baby'n aciki. Nan da nan yaje ya d'aukota, baze iya kwatanta irin farin cikin da ya ziyarci zuciyansa ba a lokacin da ya rik'e baby'n nasa a hannu. Se kaman Amal kawai ya rik'e, yarinyan ba abinda ya rabata da Amal wane kakinta Amal tayi. Se masha Allah kawai Afzal yake ta furtwa har izuwa lokacin da ya dawo ya zauna a gefen Amal. Addu'a yayi mata Mummy ta mik'a masa zamzam da aka jik'a dabino aciki ya bata.

"Rania she looks just like you" ya sanar da ita had'e da mik'a mata ita. Har kuka seda Amal tayi da ta rik'e yarinyar a hannu, yau Allah ya amsa mata addu'arta dan azaban data sha a labor room har cewa tayi ita mutuwa ma zatayi. Amshe baby'n Mami tayi ta mata addu'a itama sannan ta mik'awa Mummy itama tayi mata inda Afzal ya sake amsanta. "Gaskiya 'yar nan ta d'ibo Amal dayawa" cewan Mummy.

"Nace miki kaman Amal kawai na rik'e a hannu ba abinda ya rabasu" Mami tace.

"Alhamdulillah" Afzal ya sake mik'a godiyansa ga mahalicci. Ya rasa wani kyauta zeyi wa Amal wanda zey sanyata farin ciki kaman farin cikin da ta sanyasa a ciki yau. "Rania?"

"Na'am?" Ta amsa mik'a mata baby'n yayi "Wani suna zamu sa mata?"

"Yaya nice zan bata suna? Ai kaine mahaifinta kai zakayi deciding."

"Na baki wannan dama, ki sanya mata duk wani sunan da kika ga ya dace." Shafe fuskan baby'n tayi a hankali had'e da placing mata kiss a kan hanci "Ina son mu sanya mata Nazeefah sunan k'anwata tilo." Gabad'aya wajen seda sukayi mamakin wannan ra'ayi na Amal, barin ma Mummy. Ina ma ace yadda Amal ke son Nazeefah haka itama Nazeefah take son ta? Da kuwa ba abinda ze fiye wa Mummy farin ciki. Duk sunyi murna matuk'a barin ma Mummy da har hawaye seda ta zubar taso ace ta iya ta bawa 'yarta tarbiyya kaman yadda Mami ta baiwa Amal, ta so ace Nazeefah tana da kyawun halatayya irin na 'yar uwarta Amal. Amsan yarinyan Afzal yayi ya mata hud'uba. "Welcome to the family Nazeefah, Allah ya albarkaci rayuwanki."

"Masha Allah" fad'in Mami.

"Allah miki albarka Amal, Ya k'ara muku lafiya keda Nazeefar mu."
Ameen duka suka amsa a gun.




RANA D'AYA!
#RD💕

Love_ king Miemiebee👄





Miemiebee Novels

Wednesday, 14 November 2018
RANA D'AYA!
BY MIEMIEBEE
PAGE 47


LAST AND FINAL CHAPTER DEDICATED TO EVERY SINGLE READER ❤️


"Toh kai Afzal haka akeyi ne? Ka rik'e 'ya tun d'azu ka hana mu kakanninta rik'e ta?" Mami ta fad'a cike da wasa wanda hakan ya sanya su duka dariya a wajen.

"Mami sai de fa kuyi hak'uri dan wallahi duk yadda naso bayyana muku kalan farin ciki da walwalan da nake ciki a yanzu ba ganewa zaku yi ba, dan murna har gani nake kaman mafarki nake, I can't believe that this beautiful here is my daughter and that Amal is her mother, Alhamdulillah Allah abun godiya."

"Tabbas Allah abun godiya ne Afzal" Mummy ta sanya baki.

"Thank you Amal, Allah miki albarka."

"Ameen Yaya" ta amsa da wahalallen dariya, tana wasa da canular'n dake hannunta.

"Toh shin za ayi wa Nazeefar tamu alkunya ne ko da Nazeefan zamu na kiranta? Naga ku iyayen zamani yanzu haka kuke yayi." Mami ta kuma tambaya inda Mummy ta gyad'a kai in agreement.

"Yaya?" Amal ta kira Afzal da ya kafa wa 'yar nasu ido ko kyaftawa ba ya yi. "Yaya?" Ta sake kiransa se anan ne ya amsa gabad'aya hankalinsa yayi nesa da shi.

"Na'am Rania?" Ya amsa yana d'ago kai.

"Baka ji Mami ba?"

"Sorry meney?"

"Za'ayi wa Nazeefah alkunya kokuwa?"

Murmushi mey alfarma ya saki sannan yace, "Rania ni ai se abinda kikace."

"But Yaya I'm asking you now."

"A'a nikam se abinda kikace, don baze yi ace bayan wannan gaggarumin kyauta da kika mun in sake cewa ga abinda nake so ba, this's your moment live in it, idan kina son mu sanya wa Nazeefah alkunyan fine se mu nemi mey dad'i mu sa mata in kuma a'a we all good banida matsala." Kewayawa Mummy tayi ta kalli Mami cike da jin dad'in amsan da Afzal ya bada, inda itama ta juyo tana kallonta suka sakar wa juna murmushi. A gaskiya Allah ya amsa mata addu'an da ta dad'e tanayi wa Amal tun tana 'yar yarinya na cewa Allah ya bata miji nagari wanda ze darajata ya kuma kula da ita fisabilillah.

"Tuna mun wannan suna da kace yana maka dad'i."

"Wanne d'aya?"

"Wannan da muka gani a cikin littafi ranan."

"Wai NIHAL?"

"Yes shi why not muyi mata alkunya da shi you once said you like the name."

"I really do but are you sure? In be miki ba, ba semun sa ba."

"Of course Yaya duk wani abinda yake maka dad'i nima yana mun ko Mami?" Ta kewayo tana kallon Mami da murmushi d'auke a fuskanta. Murmushin Mami ta mayar mata had'e da amsawa "Eh Baby."

"Toh kaga se mu sanya mata shi ko?"

"Thank you so much Amal, Mami har yau bansan da wani bakin zan yi miki godiya ba na tarbiyyattar da Amal da kikayi kika raineta har izuwa lokacin da na zo nayi muku wayo na d'auke ta" dariya suka sa sannan ya cigaba "Allah ya sak'a miki da mafi alkhairi da ke da Papi gabad'aya."

Mami na murmushin jin dad'i ta amsa da "Ameen. So kun yanke shawaran kenan yanzu? Nihal zamu na kiran jikar tamu da 'yar uwata?"

"Yes Mami" yayi saurin amsawa.

"Toh Abban Nihal baka sanar damu ma'anar sunan ba" fad'in Mummy.

"It means gratified; delighted; happy; prosperous; and a blissful person just like she truly is."

"Masha Allah gaskiya sunan yayi ma'ana Allah d'ayyiba ya raya mana Nihal" ta kuma cewa inda duk suka amsa da ameen. Mami ta cigaba "Duk yadda zan so cigaba da zama anan in kula da Nihal hakan baze yiwu ba yau girki na ne ko tukunya kuma ban aza ba, ni zan wuce Mummy seta bi ki kin gane?"

"A'a baza ayi haka ba 'yar uwa" Mummy tayi saurin katseta. "Jikar fari ce fah? Ku ku tafi ni se in koma gida in yi ma Alhj girkin karki damu."

"Wayyo 'yar uwa kin tabbata?"

"Kar kiji komai Allah ya raya mana Nihal."

"Ameen ya Rabbi kai nagode sosai sakillahu bil jannah."

"Ameen wa iyyaki kuje idan na gama girkin se na sa a turo muku naku had'e da kayakin ki kema kokuma yanzu ina zuwa in had'o miki kayakin se insa driver ya kawo miki, wanne kika ga ze fi?"

"Kinga dad'in da muke gida d'aya yanzu ko? In zaki iya had'a mun a yanzun nake ga zefi ga key na site d'ina nagode sosai."

"Toh shikenan bari inyi sauri in had'o miki" ta amsa had'e da kar6an key d'in.

"Ermm Mummy?" Afzal ya kirata. "Na'am?" Ta amsa.

"Kiga ba sekin yi wani wahalan kawo abinci ba already munyi waya da Ummi tace zata kawo abincin so don't worry.

"Ji min d'a, ladan ma se mahaifiyarka ce kake so ta samu wato ko?"

"Toh ai dukanku mummies d'ina ne Mummy" ya amsa yana dariya.

"Toh shikenan breakfast de gobe ni zan kawo ka fad'a mata na rigata."

"Toh ba matsala Mummy thank you."

"Yauwa barin wuce toh, mai jego sena shigo gobe ko?"

"Toh Mummy thank you ki gaishe da gida." Har waje Mami tayi mata rakiya had'e da tuna mata kayakin da take so ta tattaro mata sannan ta dawo ciki. In less than an hour bayan kayan Mami sun iso aka sallami su Amal suka komo gida bayan tabbatarwa da likita yayi da ita da Nihal suna cikin k'oshin lafiya. Wanka me kyau Mami tayi ma Amal da kanta sannan ta had'a mata tea mey kauri ta sha dan samun ruwan nono. Afzal ko na zaune a parlour se pictures yake tayi wa Nihal chan idan ta fara kuka ya bata ruwan zamzam da suka tanadar.
Bayan Amal ta gama shiri Mami ta kira Afzal ya kawo Nihal dan a shayar da ita. Mutumiyar ku kam ta cire mama ta shayar da 'yarta ta kasa se tayi kaman zata sa mata a baki seta fasa, kan Mami da Afzal ne ya gama d'aurewa.

Chan Mami da ta kasa hak'ura ta tambayi ko lafiya "Ya haka Baby?"

"Babu" ta amsa k'asa k'asa cike da kid'imewa.

"Toh ki bata mana baki ji tana kuka bane?"

"Zan bata."

"Toh mey kike jira? In taimaka miki ne?"

"A'a zan iya zan iya" ta amsa cike da tsoro.

"Toh muna jiranki." Setayi kaman zata sa mata a baki seta fasa. "Wallahi Baby zan sa6a miki me ke damunki wai?"

"Mami wallahi zafi zeyi, baki ji yadda yayi tsami ba, rik'e shi ma haka da nake zafi yake mun" Baki Mami ta hangame tana kallonta cike da d'umbun mamaki, Afzal da ya san kayansa kam se kad'a kai kawai yake. Ance aure na sa hankali toh ga har Amal tasa ta haihu amma shagwa6a da rashin hankalin nan nata na nan har yau, Allah taimake shi.

"Dan zeyi zafi se baza ki shayar da 'yarki ba? Ke d'in ba hak'ura nayi na shayar dake ba kema?"

"Toh ai Mami ke kina da dauriya."

"Kinga bana son shashanci kiba 'yar nan nono ta sha tunda ta shigo duniya fa banda ruwa ba abinda aka sake bata."

"Ni wallahi zafi" ta sake cewa tana zum6uro baki yayin da ta shiga cika idanunta da k'walla.

"Ikon Allah toh wallahi inde haka zaki cigaba se Ummi tazo kuyi jegon tare na tabbata idan itace akanki zaki nutsu."

"Ya Omri ina ruwanta a sake bata."

"Ruwa?" Mami ta katseta kafin Afzal yayi magana. "So kike cikin nata ya fashe? Kai kuma Afzal kayi tsaye achan baza kayi mata fad'a bane?" Ta kewayo tana kallon Afzal dake rik'e da feeder'n Nihal a hannu.

"Zan yi mata Mami, Amal yi hak'uri ki bata kinji?" Ya ce da ita a hankali yana mey nufan inda take zaune.

"Aww ma hak'uri kake bata? Lalle kam banga laifin Baby ba kai kake d'aure mata gindi ko ka sata ta bawa yarinyan nan mama tasha ko in kira Ummi tayi mun maganinku duka" tana kaiwa nan ta fice daga d'akin. Se kuka Nihal take Amal na jijjigata, ta kuma bata maman ta sha ta kasa wai ita zafi. A nitse ya k'arisa ya zauna daga gefenta tare da dafe ta.

"Baby na?" Ya kirata, kai ta d'ago a maraice da k'walla cike dam a idonta tana kallonsa. Goshinta yayi pecking a hankali sannan yace, "Yi hak'uri ki ba Nihal ta sha kinji? Yi hak'uri."

"Ya Omri wallahi yayi tsami ta6awa kad'ai nayi ma zafi yake mun" ta sanar da shi a shagwa6ance.

"I know sweetheart but kinga Nihal na kuka badan komai ba kuma se don yunwa help her out okay? I trust you na san ki da dauriya."

"Mu sake bata ruwa zuwa gobe se in gwada breastfeeding nata nasan kafin nan tsamin ya d'an ragu."

"Babe har zuwa gobe? Idan mukayi haka munyi ma Princess adalci kenan? Yi hak'uri kinji? I trust you I know you can do it" lalashinta yatayi yet still Amal ta kasa sawa Nihal mama a baki ita kuma da gajan hak'uri ta k'i yin shiru. Lalla6ata ya tayi har se da ya samu ta amince, rufe idonta tayi gam sannan shi da kansa ya saita kan Nihal ya ajiyeta, tana kama bakin Amal tasa wani d'ankaren ihun da ya mugun razana Nihal har da shi ma Afzal d'in. Sake nonon tayi ta shiga kuka cike da tsoro kaman ba gobe. Da hanzari Mami ta shigo d'akin a kid'ime se gani tayi Amal na hawaye, ita de ta na ganin shagwa6a yau, a hankali Amal ta mayar da bakin Nihal kai tashiga shayar da ita. Nihal bata yarda aka cire maman daga bakinta ba har seda tayi bacci.

Bada dad'ewa ba Ummi ta shigo da abinci, se rawan jiki take ta kasa zama gu d'aya da Nihal duk da cewan barci take, daga ta d'auketa suyi nan se suyi chan. Ita wai tunda take bata ta6a ganin fine baby ba kaman Nihal ba.

*****

"Ka ga hoton yarinyar?" Mummy ta fad'a had'e da mik'a wa Daddy wayanta across the table inda ya amsa. "Kaiii masha Allah Amal tayi k'ok'ari ita ta haifi wannan k'atuwar baby'n da kanta."

"Wallahi ko Alhj da kanta, yarinyar tubarkallah k'atuwa."

"Gaskiya Allah ya raya gobe in shaa Allahu zamu je mu dubata. Sun sa mata suna ko tukuna?"

"Eh sunsa Amal ce ma ta sa."

"Masha Allah ya sunan?"

"Nazeefah, tayi wa 'yar uwarta takwara amma za ana kiranta da Nihal."

"Alhamdulillah Alhamdulillah Allah sarki Amal, Allah ya cigaba da yi mata albarka yasa 'yar uwarta tayi koyi da ita."

"Ameen Alhj wallahi addu'ata bata fin haka kullum."

"Ya Nazeefar har yanzu tana kan bakanta na cewa baza ta dawo ba?"

"Eh tun d'azu ma ina trying line nata amma baya shiga."

"Toh Allah sa de lafiya."

"Amin."

"Jameelah zata kwana achan kenan ko?"

"Eh kasan dake girkinta ne setace ni in taya Amal kwana amma ai kaga idan nayi haka ban kyauta ba tunda de jikarta ce ta farko shi ne nace suje ni zan kula da kai."

"Hakan yayi Hjy Surayya Uwar gida a gidan Alhj Abdallah, Allah cigaba da yi miki albarka."

"Kai Alhj ameen kayi ka gama muje ka watsa ruwa ko baka fad'a ba na san ka gaji."

"Wallahi kuwa kaman kin sani meeting meeting baya k'arewa haka."

Yana gama cin abincin ta sirka masa ruwan d'umi ya watsa suka kwanta. Washegari da sassafe ta tashi ta shiga had'a breakfast na nan gida da kuma wanda zata kai wa su Amal. Tana cikin aikin ne wayanta dake kan counter ya shiga ruri hannunta ta d'auraye tayi drying a jikin towel sannan tayi sauri ta d'aga duda cewan new number ne ke kira.

"Assalamu Alaikum" ta soma da cewa.

"Wa'alaikumus salam" aka amsa daga d'ayan 6angaren.

"Nazeefah?" Ta ambata had'e da sauk'e wayan tana mey duban lamban da kyau. "Nazeefah is that you?"

"Yes Mummy ina kwana."

"Wani layi nake ganin kaman Nigerian number? Kin dawo Nigeria ne?"

"Eh Mummy ina Abuja yanzu haka, zuwa anjima zan shigo in shaa Allah flight d'ina by 2 ne."

"Toh Alhamdulillah Alhamdulillahi sannu da dawowa Nazeefah sekin shigo."

"Ya Daddy?"

"Lafiyashi k'alau me kike so in dafa miki?"

"Anything will do Mummy."

"Don't you miss my Eghusi?"

"I really do Mummy amma bana son saki aiki ne."

"Karki damu Allah kawo ku lafiya."

"Ameen Mummy se mun sake waya."

"Erm Naz-" sede har Nazeefah ta katse wayan. Dama so take ta sanar da ita cewa Amal ta haihu kuma tayi mata takwara but then seta ga it'll even be better idan Nazeefan ta shigo tukuna. She has a feeling everything is going to work out yanzu tunda yanzu ba tare da kowa ya mata fad'a ba ta duba taga ya kamata ta dawo gida. Ohh she can't wait ita da Amal su fara shiri. Nan da nan ta kammala girkin ta kai musu nasu dining, ta kai wa Papi da sauran masu aiki nasu sannan tasa nasu Amal kuma a flask ta shirya komi tsaf sannan ta shiga bayi tayi wanka ta shirya. Har ta gama karyawa Daddy na bacci seda tazo fita ne ta tada shi "Alhj ni zan wuce yaso ko daga baya seka shigo."

"Ina zakije da safen nan haka?" Ya tambaya yana k'ok'arin bud'e idonshi.

"Gidan Amal zan kai musu breakfast."

"Ba munyi zamu fita tare ba? Ina Abba?"

"Ya na nan na kai mishi breakfast shima yana kwance yaso anjima seku taho tare naga baccin naka yayi nisa ne Alhj kaman stress yayi maka yawa."

'"Yata ce fa ta haihu."

"Shiyasa ai zaka iya zuwa duk lokacin da yayi maka, nasani 'yarka zatayi maka uzuri now go back to sleep idan ka tashi breakfast naka na jiranka akan dining ni na tafi."

"Toh ki gaishesu."

"Zasuji ba-bye." Acikin mintina k'alilan driver ya sauk'eta gidansu Amal inda ya shiga da baskets d'in ciki. Kasancewar ba kowa zaune a parlourn seta wuce ciki, ta inda ta jiyo hayaniya ta dosa had'e da yin sallama bakin k'ofan kamin ta bud'e.

"Yanzu k'ara ruwan sanyi kikayi akan wanda na sirka miki Baby?"

"Assalamu Alaikum" Mummy ta sake yin sallama wanda se a nan sukayi noticing presence nata suka kewayo bakin k'ofan. "Ha'a 'yar uwa yaushe kika shigo? Bismillah bismillah sannu da zuwa."

"Ya nake ta jin hayaniya haka?"

"Ina kwana Mummy?" Amal dake d'aure da towel ta gaisheta tana mey k'ok'arin sauk'a k'asa.

"A'a 'yata yi a hankali kinsan k'asan ki ciwo ne ba sekin durk'usa ba hakan ma yayi, ina kwana ya jiki?"

"Alhamdulillah da sauki'i ya daddy?"

"Lafiyanshi k'alau na barosa yana bacci akan cewa anjima shi da Abba zasu shigo, ya jikata?"

"Ayyah haka yace mun jiya Allah kawo su lafiya."

"Ina Nihal tamu?"

"Tana gun Yaya a d'ayan d'akin."

"Har anyi mata wanka ne? Sannu da k'ok'ari 'yar uwa."

"Sannu 'yar uwa ai da ma baza kizo ki same mu haka ba sede kizo kiga kowa yayi wanka tsaf amma wannan yarinyar" tayi maganan tana nuna Amal da yatsa "Nakega sede ke ko Ummi ne zaku tayata zaman jegon dan ni kam ta raina ni bata ko shakka na." Mummy na dariya ta tambayi meya faru inda Mami ta shiga irga mata, "yanzu haka ruwan dana sirka mata bayan nace kar ta k'ara na sanyi akai ta kama ta k'ara."

"Toh Amal ai seda ruwa mey d'umi ake wankan ko so kike jikin ki yayi tsami ya rub'e shi ruwan zafin ai magani ne kar fa ki manta jikin naki du ciwo ne yanzu."

"Mummy wallahi baki ji d'umin ruwan ba har fa hayak'i yake."

"Rufa mun baki sangaltacciya kawai."

"A'a 'yar uwa ke kuwa ya zakiyi ma maman Nihal haka? Kinga maman Nihal yi hak'uri ki shiga bayin kiyi wanka bari in sirka miki da kaina nawa baze kai na Mami zafi ba." Haka da k'yar suka samu Amal tayi wankan ta fito itama Mami ta shiga suka karya sannan Amal taje amso Nihal daga gun Afzal wa Mummy had'e da kai masa breakfast nasa. Sallama tayi bakin k'ofan bayan da ya amsa ta bud'e ta shiga. Tsince akan gado ta samesa da gajeren wando ajikinsa yayinda ya kwantar da Nihal akan k'irjinsa tayi tsit sekace ba ita ta fitinesu ta hanasu barci ba daren jiya.

"Toh kuma kinyi tsaye a wajen bazaki k'araso bane ko inzo in kar6e ki?" Yace da ita.

"Not at all Ya Omri I just can't believe my eyes, like you two are the most cutest beings I've ever seen."

"Look at you cute thing come in." Murmushi ta sakar mishi sannan ta mayar da k'ofan ta k'arisa ciki ta ajiye abincin kan bed side drawer sannan ta zauna daga gefensa. "Good morning Ya Omri" ta gaishesa tare da kissing lips nashi a lokaci guda.

"Morning my sunshine" ya amsa "You're looking spectacular se kace ba ke kika haihu ba jiya ba, such a strong girl."

"Kai Ya Omri" ta amsa tana murmushi.

"I'm damn serious kinyi kyau and above all you smell sooo good."

"Thank you Love kai kam dan k'azanta ko wankan ma bakayi ba anyways you're still smelling good."

"Aww dan ina mana raino kike so ki zageni?" Ya tambaya da d'aurarren fuska.

"Haba Sweetheart I was only kidding jazakallah kaji? Ya Nihal? Tayi bacci?" A hankali ya lek'a fuskan had'e da gyad'a mata kai "Sekace ba ita ta cika mu da kuka ba jiya."

"Toh baku yi mata abinda take so ba ai dole."

"Kaman ya ba ayi mata abinda take so ba Ya Omri? Ita wai kar in cire maman daga bakinta, a ina aka ta6ayin haka?"

"Oho de se kiyi hak'uri after all dama nata ne."

"Toh kawota in kaita wa Mummy she's so eager to see her."

"Oh ayyah, ehemm before I forget, wai Mami yaushe zat tafi?"

"Yaushe tazo ko yaushe zata tafi kake tambaya?" Ta sa dariya.

"Babe wallahi jiya da k'yar nayi bacci I miss your legs wrapped around me."

"Same here Ya Omri, I miss sleeping on your broad chest amma ya muka iya? Se na fita daga arba'in Mami zata tafi."

"What!! Wasa kike amma ko?"

"Ka zauna anan."

"Rania wallahi bazan iya ba gaskiya, if only you have an idea how I suffered yesterday alone."

"Toh Baby ya zamuyi?" Ta tambayesa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment