Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

_"Eh shi."_

_Wallahi ban ta6a sanin bakida wayau ba se yau, ashe rashin wayon naki ya kai matakin da har zakiyi sha'awan aure a wancan matsiyacin gidan."_

_"Amma Umma ai nagari ake nema ko musuluni bece se mai kud'in bala'i ba bale ma fa yana karatu bazamu rasa na rufin asiri ba."_

_"Uwarki da karatun da kuma rufin asirin nace, chin kwalin degree d'in zakiyi kokuwa, kuma ni zaki gaya ma musulunci? Toh naji musulunci bece se me kud'i ba amma ai al'adar ki bata amince ki auri talaka ba."_

_"Umma amma-"_

_"Dakata idan kuma kina ganin ya akayi na auri Abbanki kike bayan bayida komai kisani Abban ki d'an uwa na ne, auran had'i akayi mana kuma nima muddin zaki amince ki auri wani nawa koda baida kud'i zan amince miki amma muddin bare zaki aura toh wallahi se mey na hannu kiji ki sani."_

_"Umma bana son Ya Faisal dan haka bazan aureshi ba" na sanar da ita cikin 6acin rai. Amsana ba k'aramin tunzirata yayi ba, kafin in hankara kawai naji ta rufe ni da d'an banzan duka ana cikin haka ne Abba ya dawo daga kasuwa ya kar6eni. "Haba Awatif! Meyayi zafi haka zakisa yarinya a gaba kina dukanta kaman ganga? Meya faru?"_

_"Yo ba gara gangan ba dama an san ba mutum neba bale yayi wayo, kuma ba ruwanka Malam wannan tsakani na da 'yata ne ehe! Bana son shisshigi."_

_"Shisshigi fa kikace? Ni da 'yata kice shisshigi?"_

_"Eh shisshigi ne mana kana na miji ina ruwanka da harkan daya shafemu." Abba be sake kulata ba ya juyo a gareni "Yayata ta kaina yi hak'uri" ya shiga bani hak'uri "Mey ya faru?" Bayanin komai na mishi Umma na tsaye tana hararata cike da takaici._

_"Haba Awatif! A ina akace se mey kud'i za'a aura? Tunda yarinyan nan tana son yaron nan kuma yana da shirin turo magabatansa me zey hana muyi mata abinda takeso?"_

_"Aww biye mata zakayi kai ma? Toh wallahi kunyi k'arya dukanku 'yar nan bazata auri matsiyaci ba se Faisal mu zuba daku mu gani" tana kaiwa nan ta janye hijabin ta daga kan igiya ta fice. Kuka na cigaba da yi a wajen Abba yana ban hak'uri._

_"Abba dan Allah ka bawa Umma hak'uri Abba bana son Ya Faisal bana sonsa."_

_"Yi hak'uri Jameelah zanyi mata magana in shaa Allahu zata sauk'o kinji? Kukan ya isa haka."_
_Haka nan Umma ta k'wace mun waya ta hanani waya da Khaleefah ko fita ta hanani in ba Islamiya ko boko ba kullum ina rufe kup a gida gashi duk yadda Abba ya so fahimtar da ita gaskiya hakan ya gagara saboda Umma ta kasance mace mey zafi ko Abba wani sa'in tana fin k'arfinsa daga k'arshe Abba yace sede in hak'ura inyi yadda takeso saboda yayi-yayi ya ganar da ita gaskiya amma tak'i fahimta niko nak'i amincewa da hakan, ranan paper'n mu na k'arshe bayan mun gama naje na samu Khaleefah na sanar da shi cewa Faisal ya kusa turo magabatansa da yayi ma iyayensa magana su riga sa turowa idan har akayi haka toh dole Umma ta yarda amma sai dai shima koda ya kai maganan gida iyayensa suka k'i amince mai acewansu ya bari seya gama makaranta tukun. Na sosai na shiga wani irin yanayi bani da wata sana'ar data fiye na kuka acikin gida. Ba waya gashi ko fita Umma bata bari na inyi kusan sati biyu kenan banji daga Khaleefah ba rana d'aya kwatsam kawai mukaji ana sallama, amsawan da Umma tayi sega Khaleefah. Da fari da bata gane waye shi ba ta kar6esa da fara'a ta k'arisa dashi ciki bayan ya zauna yayi mata bayanin kansa ya fayyace mata k'udurinsa akaina Umma ta ci mai mutunci tayi mai koran akuya a idona ta kuma nuna masa ni Faisal zan aura. Ranan na kasa bacci dole washegari da yamma na saci idonta naje duban Khaleefah. Wannan yini shine mafi munin yini a rayuwa na, ban ta6a tsammanin Khaleefah ze iya mun abinda ya mun ba, ashe abinda Umma tayi masa ya mugun ci masa rai dan haka yayi tunanin k'untata mata ta hanyan 6ata mun rayuwa, yana ganin idan ya cuceni kaman ya cuceta ne, a tunaninsa Umma na sona d'inda har idan abu ya shafeni zata shiga damuwa saidai ba haka bane. A yinin ranan ne Khaleefah ya mun fyad'e ba irin rok'o da hak'urin da ban basa ba amma haka seda ya aikata abinda yayi niyya ba ko d'igon imani tattare da shi had'e da taimakon abokansa k'waya biyu. Bayan faruwan abun ban sake sanin inda nake ba se bayan kwana biyu dana farka na tsinci kaina a gadon asibiti. Abba na fara tararwa nan take na shiga zubda hawaye yana bani hak'uri shigowan Umma ta shiga zagina na tana kira na da 'yar iska. Duk yadda Abba da likita suka so ganar da ita fiyad'e akayi mun tak'i amince tana ganin gaskiya amma ta take. Ba irin sunan da bata kirani da shi ba harda ja min Allah ya isa. Har aka sallameni daga asibitin kuma bata sake koda lek'oni ba, Abba ne ya zauna akaina har aka sallameni. Ranan da muka dawo gida Abba ya shirya zuwa tinkarar iyayen Khaleefah akan abinda d'ansu ya mun dan k'watan mun hak'k'i amma haka mahaifin Khaleefah ya bushe ido yace sam shi d'ansa be aikata wannan mumunan abu ba sharri kawai ake son yi masa. Shima Khaleefah koda aka kaimu gaban mey unguwa rantsuwa ya ringa yi shi ba abinda ya ta6a had'amu ko sani na ma beyi ba haka muna ji muna gani aka tauye mana hak'k'i. Faisal kuwa tun da yaji wannan magana ya d'auke k'afa daga gidan mu hakan yasa Umma ta sake tsanata, dama chan nasan ba sona yake har zuci ba, kyau da jiki na kawai yake bi. Bayan wata biyu da faruwan abun ne kwatsam rana d'aya na tashi da zazza6i da amai. Ko kallon kirki Umma batayi mun ba, ina cikin aiki a kitchen da rana kawai amai yabi kaina na fito na shiga kwararowa a tsakar gida ana cikin haka Umma ta dawo gida daga unguwa, salati ta shiga yi tana tafe hannu amma ko agaji bata taimaka mun da ba seda na gama na kishingid'a jikin bango sannan ta tako ta shiga dubata._
_"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ciki! Wayyo jama'a! Shikenan tayi cikin shege" ihu ta shiga yi tana kururuwa seda ta tara mana jama'a a gidan kafin ace mey magana ya zagaye gari akan cewa 'yar Malam Muhammad tayi ciki alokacin kuwa har Khaleefah ya koma makaranta, koda nazo na samu waya na kirasa layin nasa bai shiga ba shakka ya canza. Tun daga ranan da aka tabbata ina da ciki Umma ta sauya mun a gidan tokari na safe daban na yamma daban tamkar ba 'yar da ta tsuguna ta haifa ba haka ta tsaneni take kuma gaba dani. Sau dayawa nakan zauna in sha kuka ina kokonton anya kuwa Umma ce asalin mahaifiyata? Se daga baya Abba yake sanar dani dalilin daya sa ta tsane ni. Tun farko bata so ayi mun takwaran Baaba Jameela ba yar Abba wacce jininsu sam be had'u ba, sam babu jituwa a tsakaninsu tun ma kafin ta auri Abba, bayan auran nasu kuma se abun ya sake lalacewa tamkar annabi da kafiri haka suke ji da juna, toh tunda aka samun sunan Baaba Jameela Umma ta tsaneni. Shima Abba bawai yaso yasa sunan bane sedon mahaifiyarsa da dama akayi niyan yi mata takwaran tace ta yafe ayiwa Baaba Jameela kasancewar tunda tayi auri sama da shekara ashirin ko 6atan wata bata ta6a ba, dalilin da yasa aka sa min sunanta kenan._

_Ba yadda banyi da Abba ba da ya barni in zubar da cikin amma yak'i acewansa yin hakan haramun ne bayan nan kuma nima ina iya rasa raina ta dalilin hakan. Ko fita ban isa inyi ba haka ina ji ina gani na daina zuwa islamiyya bayan nayi nisa sosai a karatun, shima Abba kaman wasa duk inda yaje se an ringa binsa da kallo ana nuna sa da yatsa, harta kasuwa gun aikinsa. Umma ce kad'ai ke fita freely ta dawo gida bawani fargaba ko tashin hankali saboda ko zagi na ake seta tsaya ta sa baki ayi da ita. K'arshe de haka zaman garin Askira ya gagaremu amma Umma ko a bakin zaninta hasali itama ke yad'a wa mutane nayi cikin shege. Alokacin da Abba ya gir6e gonansa lokacin cikina na wata hud'u ya kawo shawaran mubar garin Askira idan ba haka ba ko nazo na haife cikin nawa ba bar min d'an za'ayi ba shi kuma abinda yake gudu kenan, baya son laifin Khaleefah ya shafeki Baby._

_Koda Abba ya sanar da Umma cewa zamu bar Askira ita tace ba inda zata tunda ba ita ta turani inyi abun kunya ba. Ganin Abba dagaske yake ko ba ita shi zeyi tafiyarsa yasa ta amince ta biyo mu. Gidan mu da komai da muka mallaka Abba ya siyar muka dawo nan Maiduguri bada sanin kowa ba dan ko Umma ma Abba be sanar da ita inda zamu ba kawai ganin kanta tayi anan cikin garin Maiduguri. Mun dawo bada dad'ewa Umma ta kamu da ciwon nono wato breast cancer, ina da shekara sha tara na haifeki Baby, bamu ta6a neman abu gun Abbanki mun rasa ba, komi yi mana yake, damuwa na tun kafin in furta yake yaye mun. Tamkar 'yar cikinsa haka ya d'aukeki yake kula da ke. Kina da shekara biyu mutuwa yayi halinsa ya tafi da Umma sede har ta mutu bata ta6a rik'eki a hannu ba. Tsanan duniya gabad'aya ta d'au ta aza mana ni da ke ko kallon arziki ban ta6a ganin tayi miki ba, batun Khaleefah kuwa har yau ban sake ji daga garesa ba. Sau dayawa manyan 'yan kasuwa masu aure harma da samari su kan nuna suna son su aureni amma tun kan abinda Khaleefah ya mun naji na tsani na miji a rayuwata shiyasa kika ga har yau ban sake yin aure ba, dan kuma gudun kar wataran yaran dana haifa su nuna miki banbancin 'yan uba, bana son abunda ze ta6a farin cikinki Baby, bana so"_ ta k'are cikin tsananin kuka.

Kuka sosai Amal take itama, Afzal ma na sosai jikinsa yayi sanyi yana mamakin rashin imani irin na Umma marigayiya da kuma wannan Khaleefah mahaifin Amal.

"Baby kiyi hak'uri na 6oye miki wannan sirri da nida Papinki mukayi dan Allah kiyi hak'uri."

"Kibar bani hak'uri Mami, ni ya kamata inyi hakan na rashin fahimtar ku da banyi ba keda Papi please forgive me." A hankali Mami ta rungumeta yayinda suka cigaba da kuka shima Afzal seda k'walla ya ciki masa a ido dan tausayi. Be dad'e ba aka sallamesu Afzal ya dawo da su gida chan dare da Mami tashigo kawo wa Amal abinci Amal ta tsayar da ita.

"Mami alfarma nake nema."

"Fad'i ko mey kikeso Baby."

"Mami ku raba aure na da Yaya."

"Subhanallahi meya faru Baby? Wani abun ya sake miki ne?"

"Mami sanin kanku ne kun cuci yaya tun farko da kuka san asali na be kamata ku had'a mu aure ba."

"Baby wani irin magana kuma kike? Ya kike magana sekace mun zalunce shi? An fa fad'a mishi gaskiya kuma a hakan yace yana sonki Abbanshi ma na wajen."

"Kina nufin Abba ma yasan asalina?" Kai Mami ta gyad'a mata a hankali.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta cike da tashin hankali yayin da hawaye ya shiga ciko mata a ido. "Bayan su se suwa kuka sake sanar dasu asalina?"

"Wallahi babu Baby daga su shikenan."

"Nide na fad'a muki kuyi ma Yaya magana kawai ya bani takarda na bazan iya cigaba da zama da shi ba, zaluncin ya isa haka."

"Baby dan Allah kibar magana haka, ya kike magana sekace laifinki ne kika kasance haka? Karfa ki manta wannan k'addararki ce haka Allah yaso ya ganki kuma ba wai yayi hakan dan baya sonki bane se don ya gwada k'arfin imanin ki."

"Na sani Mami shiyasa nake son Yaya ya sauwak'e mun, Yaya be kamanci shegiya kaman ni a matsayin matarsa ba-"

"Baby dan Allah kibar magana haka ki daina kwatanta kanki da wannan mumunar kalma" Mami tayi saurin katse ta yayinda ta saki murmushin takaici "Akwai k'arya ne acikin hakan Mami? Ko ba shegiyar bace ni?" A hankali Mami ta jata jikinta "Dan Allah ki bar fad'in haka, Baby tunda muna sonki mijin ki na sonki mey kuma kike nema? Wannan abu ya riga ya faru ba abinda zamu iyayi mu canza ko a tunaninki ni d'in dad'i nakeji na cewa bakida uba? Wallahi Baby na fiki takaici da zafin hakan shiyasa ni da Papinki muka d'au burin baki tarbiyya da ilimin boko da na islamiyya duka dan ki banbanta daga sauran 'yan matan da suka tsinci kansu acikin hali irin naki masu yawo akan layi suna barikanci saboda ganin da suke ba ta hanya madaidaiciya aka same su ba, Baby idan ba wai fad'a akayi ba bawanda ze miki kallon shegiya dan Allah ki daina fad'in haka" cikin kuka ta d'ago kanta daga jikin Mami tana share hawayenta "Godiya nake da ilimi da tarbiyyan da kuka bani Mami amma ban cancani miji kaman Yaya ba da yake da asali da mutunci da ma komai ba bayan ni inada akasin hakan, dan Allah ku mishi magana ku kuma basa hak'uri na zaman da mukayi tare."

"Baby cikinsa da kike d'auke da shi fa? Ya zakiyi da shi? So kike ki haifi d'an shima ba uba?"

"Sam Mami amma k'addara tariga fata cikin nan kuma zan raineshi, yadda Papi ya tayaki rainon cikina na tabbata ze tayani rainon wannan har zuwa lokacinda zan haifa in mayar masa da d'ansa."

"Kekuma fa Baby? Haka kikeson ki k'arisa rayuwarki cikin k'unci da takaici ba miji kaman ni?"

"Ya fiye akan in zauna da wanda nake ganin kaman ina cutansa ne Mami, wallahi gani nake Allah ma baze yafe mun ba."

"Subhanallahi bayan shi yace kar a fad'a miki gaskiyan al'amarin ko bayan da yaji komai? Da ace mune muka 6oye mai gaskiya da seya zama yadda kike fad'an amma fa da saninsa da kuma amincewansa kafin aka d'aura muku aure."

"It still doesn't matter Mami, Yaya deserves someone much better than me, he's way out of my league bazan iya cigaba da zaluntarsa ba." Duk yadda Mami taso fahimtar da Amal gaskiya hakan ya gagara ita sam hankalinta yak'i d'aukan maganar ita kawai Afzal ya sallameta, game da soyayyar da takeyi masa kuwa zata rok'i Alah ya cire mata shi daga zuciyarta du da cewan tasan hakan ba k'aramin abu bane. Da k'yar Mami tasamu kukan nata ya lafa ta sata taci abinci ta sha magunanta sannan tayi mata sallama ta janye k'ofar taje ta samu Papi take irga mai yadda su kayi da ita. Na matuk'a Papi ya tausaya wa Amal dama ranan da ya jina yana gudu kenan, ranan da zata gano gaskiya ta tsani kanta.

Tana mik'e akan gado tana kukan zuci wayanta dake kanta ya shiga ruri dubawan da za tayi taga Afzal ke kiranta ba shiri ta 6arke da kuka. Tunda take a rayuwarta bata ta6a tsanar kanta da kuma k'yamar kanta ba kaman yanzu, gabad'aya ji tayi batada mutunci bata da daraja, bata jin zata sake iya sa Afzal ko Abbansa a ido waya sani ma ko sun sanar da Ummi hala itama Ummin ta sanar da Nazeefah. Amma ko idan da har Nazeefah tasan asalinta ta tabbata da ta yi mata gori da shi. Shin meyasa Afzal be bari an fad'a mata gaskiya ba? Ai idan da ta san gaskiyan al'amarin tun fari da bazata soma auren sa ba ma. Haka tana gani wayan ya tsinke bata d'aga ba har a karo na biyu ma k'arshe kawai seya tura mata sak'o. Sa6anin yadda ta saba goge sak'onninsa anytime ya tura mata yau se tayi tunanin ta bud'e inda ta fara karancewa kaman haka;

_My Adorable Kitten please don't let what you found out earlier ruin you, you're still the beautiful, charming, elegant, intelligent, clever, and amazing Amal that I know, my wife and mother to my unborn kids. I love you regardless have a peaceful night rest, I'm missing you and our little one down here. Xx_ 😘

Tana gama karancewa ta shiga wani sabon kukan haka ta kwana tana yi se kusan Asuba bacci mey nauyi ya d'auketa. Wajajen goma ta tashi bayan tayi wanka Mami ta kawo mata breakafst nata taci sannan Papi yayi sallama cikin d'akin nata. Zama yayi ya mata nasiha sosai amma inaaa Amal ta riga tayi making up mind nata ita sam bazata komawa Afzal ba. Daga k'arshe Afzal d'in Papi ya kira ya sanar da shi halin da ake ciki yana tashi daga office ya biya gidan nasu. Ba yadda Papi beyi da Amal ba da ta fito daga d'akinta Afzal yazo wajenta amma tak'i ta rufe kanta a d'aki se kuka take. Na sosai zuciyan Afzal yake k'una gabad'aya ya rasa ina zesa kansa. Kwana uku ya jera yana zuwa duban Amal amma ko yaje baya samun su had'u gashi koya kirata bata d'agawa, messages nasa ma bata replying tamkar sabon mahaukaci haka Afzal ya koma. Su Papi ma sunyi mata magana har sun gaji amma tace sam bazata cigaba da zama da Afzal ba tana cutansa, acewarta zalunci ne ace yadda yake d'an halak ita ko ga ta inda aka sameta ace sunyi aure. Tun sha biyu ya baro office yau yaje ya samu Ummi a gida kallo d'aya tayi masa ta gano yana cikin matsala.

"Meya faru kuma Prince? Amal d'ince har yanzu bata sauk'o ba?"

"Ummi things just got worse."

"Subhanallahi kamar ya?"

"Ummi kiyi hak'uri na 6oye miki wannan sirri da nayi nasani ko ba dad'ewa da jimawa gaskiya ze fito shiyasa nake son sanar dake yanzu."

"Speak up already meya faru?"

"Ummi gab lokacin da na kusan auren Amal iyayenta suka bayyana mun da Abba wani 6oyayyan al'amari wanda na buk'aci Abba da kar ya sanar dake bawai dan ban yarda dake bane se don ina gudun kar hakan ya canza miki ra'ayi akan Amal."

"Ina jinka."

"Ummi Amal batada asali."

"Asali kaman ya kenan?"

"Amal ba ta halatacciyar hanya aka same ta ba."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un kana nufin Amal shegiya ce?"

"I'm sorry but yes."

"Kuma ka aureta Afzal? Baka da hankali ne?"

"Ummi ki tsaya ki saurareni mana bawai abinda kike tsammani bane, k'addarar fyad'e ne ya fad'o akan mahaifiyarta."

"Haka suka ce maka? Kuma ka yarda?"

"Yes Ummi saboda ba k'arya sukeyi ba idan da har k'arya ne da bazamu ta6a jin sirrin nan daga bakinsu ba amma fa Papi da kansa ya sanar da ni da Abba."

"Toh ai wayo suka maku saboda sun san ba a iya 6oye abin kunya ne."

"Ummi kibar cewa haka, just calm down and listen to me ita kanta Amal bata ta6a sanin gaskiyan ba se last week."

"Ita Amal d'in?"

"Yes nida Abba suka fara fad'awa akan daga nan se su sanar da ita amma na buk'aci da a cigaba da 6oye mata gaskiyan saboda nasan halinta muddin har ta gano gaskiya toh zata iya k'in amincewa ta aureni gashi yanzu ta gaano gaskiya tace ita sena sauwak'e mata tana cewa she don't deserve to be with me I deserve someone better."

"Ita Amal d'in? Ya akayi ta gane gaskiyan yanzu?"

"Shine ai nake kaiki, ranan da naje gidansu muke sulhu ne taji komai" labarin duk yadda sukayi ya kwashe ya bata, Ummi can't help but to remain shocked. Tausayin Amal ne ya kamata na matuk'a.

"Toh yanzu ya kenan? Zaku rabun?"

"Kema kinsan bazan iya rabuwa da Amal ba Ummi."

"Toh ya zakayi Afzal tunda iyayenta ma sunyi su ganar da ita sun gagara."

"Even stil Ummi I'll continue to try my best."

"Ko kana so inyi mata magana?"

"Nooo bana son tasan kin sani."

"Toh Allah baka ikon shawo kanta wallahi tabani tausayi matuk'a yarinya ga haddan Al~Qur'ani."

"Ummi bakiga yadda take kuka ba ranan da gaskiyan ya fito."

"Allah sarki Amal 'yar nan jarabawanta a duniya dayawa suke Allah de bata ikon cinyesu."

"Ameen Ummi."

"Ya batun Nazeefah fah? D'azu Mummy'nta ta kirani muka gaisa when do you plan on bringing her back?"

"Ummi muddin Amal bata dawo mun ba bazan iya dawo da Nazeefah ba."

"Zata dawo in shaa Allah Prince zan tayaka da addu'a."

"Thank you Ummi barin wuce gida in huta idan Abba ya dawo ki gaishesa."

"Bazaka jira lunch ba sauran kad'an fa."

"I'm not hungry Ummi thank you." Rakasa tayi har gun mota sannan ta dawo ciki.

Afzal be fasa zuwa duban Amal ba a rana na shida ne da yaje ya tarar da Mami kad'ai itama tana shirin fita, tana gama cin abinci ta basa hak'uri kan zata shiga nan mak'ota yin barka akan ya jira Papi shi ma ya kusa dawowa.

"Ayya ba komai Mami sekin dawo zan jirasa."

"Yauwa toh barin wuce." Bayan ta fice ya mik'e had'e da zaro wayansa daga aljihu sannan ya taka har izuwa bakin k'ofan d'akin Amal dai-dai gun ya tsaya ya shiga buga layin nata sede yana ji daga ciki yana ringing amma bata d'agawa.

A hankali ya gwada bud'e k'ofan sa6anin kullum ya tarar da k'ofar a bud'e da mamaki ya bud'e mik'e akan katifarta tana bacci ya tarar da ita a tunaninsa gabad'aya tana ganin call d'inne kawai tak'i d'agawa ashe bacci take even though yasan koda idonta biyu ma ba d'agawa zatayi ba. Cikin d'akin ya k'arisa ya tsuguna a gefenta. A hankali ya aza hannunsa akan cikinta yana shafawa a hankula.

"Kitten?" Ya kirata da k'aramin murya. "Kitten wake up it's me Afzal" ya sanar da ita kaman a mafarki take jin sautin muryansa, a hankali ta shiga bud'e idonta har ta sauk'esu akansa ba k'aramin razana tayi ba ganinsa da tayi akanta kad'an ya rage bata sa ihu ba.

"Shhhhh it's just me calm down" ya buk'aceta. Kanta ta kawar ba tare da tace da shi komai ba.

"Amal?" Ya kirata nan ma bata juya ba a hankali ya kewayo da fuskarta. "Babe please come back to me, dan Allah kiyi hak'uri mu koma gida I terribly miss you." Shiru ta mai ba tare da tace komai ba hakan yasa ya cigaba.
"Amal fushi kike dani har yanzu da bazaki mun magana ba? Please forgive me I'm sorry, I'm terribly sorry."

"Why did you do it?" Ta soma da tambayarsa tare da kewayowa.

"Did what Sweetheart?" Yayi saurin tambayarta.

"Mesa ka hana su Mami sanar dani gaskiya Yaya? Meyasa ka aureni bayan kasan yin hakan kaman ka zalunci kanka ne, sanin kanka ne iri na da bamuda asali bamu cancanc-" da sauri ya katseta ta hanyan aza hannunsa kan dry lips nata. "Please not a word Amal, I married you because ba laifinki bane da kika kasance haka, I married you because I love you Amal, I don't care koba ta halatacciyar hanya aka sameki ba and above all I married you because it's been destined you're going to be my wife and the mother to my kids Amal saboda akwai rabo a tsakaninmu" ya k'arashe maganan had'e da aza hannunsa akan cikinta. "Please come back home with me Baby please don't say no." By now kuka take sosai "I can't Yaya, I really can't" ta sanar dashi cikin tsananin kuka had'e da kawar da kanta.

"So dagaske ne da Papi yace kince
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment