Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

auren nan just tell us."

"Bazan iya ba ku gafirceni." Na matuk'a kan kowa ya d'aure a wajen, ba wanda ya fahimci inda ya dosa gashi duk sun k'osa suji dalilin da yasa yake cewa auren ya haramta.

"Alhj dan Allah kayi magana, ka fa sani rik'e maganan nan ba shine mafita ba, we're your family komin yaya bazamu guje ka ba just tell us."

"Ya haramta na fad'a muku ya kuke so inyi? Kar ku biye ma Afzal. Tunda baze saki 'yar nan ba ku amince ku bini mu tattara mu bar k'asar nan shine kwanciyan hankalin mu gabad'aya."

"Tayaya Alhj? Mene wannan abu da kake k'in gaya mana? Toh inde haka ne ina Nazeefah? Ku sauk'o mu bi Afzal mu bar mai gidan idan tayi tsami maji."

"Hjy Surayya dan Allah karki tozartani a idon jama'a haka, kar ku tafi ku barni ku kad'ai gareni."

"Fine seka sanar danu wannan magana da kake 6oyewa kokuwa mu tafi."

"Ni koda zaku tafi ku amince a raba auren nan, na yarda ku tafin amma a raba auren yarannan tukuna."

"Haka kawai ba gaira ba dalili kake son a shiga tsakanin masoya biyu? Toh wallahi kayi k'arya Alhj."

"Sau nawa san gaya miki auren nan ya haramta?! Sau nawa!" Ya daka mata tsawa.

"Sau nawa nima zan gaya maka muddin banji dalili ba bazan yarda a raba auren nan ba?!" Itama ta mayar masa a tsawace.

"Ya haramta nace!"

"Mayar da aure ba fashi ku sauk'o mu tafi Nazeefah."

"Kar ku tafi ko ina, auran Afzal da Nazeefah ya haramta saboda Amal da Nazeefah 'yan uwa ne!" Ya sanar dasu a fusace ba tare da yasan yaushe ba.






RANA D'AYA!💖
#RD

Love... King Miemiebee👄✨




Miemiebee Novels

Monday, 10 September 2018
RANA D'AYA!
BY MIEMIEBEE
PAGE 42




"What??" Mummy tayi exclaiming cike da k'in yarda yayinda fuskokinsu duka ke d'auke da d'umbun mamaki barin ma Afzal da Nazeefah da suke jin lamarin kaman raha.

"Ku gafirceni Hjy Surayya amma aure tsakanin Afzal da Nazeefah ya haramta, dole ne ya sauwak'e mata saboda Amal yar ta ce."

"Innalillahi wa inna ilai-" Mummy bata kai ga idda salatin ba kawai suka ji k'aran fad'uwan abu a k'asa rigijib! Afzal kam dan mamaki bakin yin salatin ma ya rasa.
Atake duk suka maida hankalinsu game da k'aran inda suka ci karo da sumemmiyar jikin Nazeefah a k'asa. Kasancewar Khaleefah ne a kusa da ita seya rigasu fara yin kanta yana mey jijjigata amma ina ko motsi batayi ba shiri Afzal ya k'ariso ya d'agata yayi waje da ita se cikin motansa inda Khaleefah da Mummy suka zauna a baya da ita Daddy kuma a gaba. Nearby clinic Afzal yayi rushing inda akayi emergency room da Nazeefah. Tunda aka shiga da Nazeefah har Dr da nurses da suka duba ta suka fito kap acikinsu Afzal ba wanda Allah ya basa izinin sake yima Daddy wani tambaya as duk sun shiga cikin rud'ani. Jugum suka zauna daga lungu daban-daban kowa da abinda yake gudu masa a kai. Ita de Mummy har yanzu ta kasa aminta da komai haka ma Khaleefah amma banda Afzal da jikinsa ya soma basa tabbas Daddy ne mahaifin Amal in reference to labarin Mami da yaji. Duk yadda yaso k'aryata zancen Daddy ya kasa, yana da yak'inin cewa Daddy ne mahaifin Amal. Shin wani irin cakwakiya ne wannan? Taya za'ace yana auran wa da k'anwa? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

Da wani idon ze sake kallon Nazeefah ya kalli Amal? Shin yanzu dukansu biyu sun haramta masa kenan ko ya? Yau ina zaisa kansa idan ya wayi gari ba Amal ba Nazeefah? Wannan wace irin k'addara ce? Ko a tatsuniya be ta6a jin inda abu haka ya ta6a faruwa ba. Wayyo Allah shi. Ana cikin haka likitan daya duba Nazeefah ya fito ya sanar dasu kan ta farfad'o suna iya shiga ganinta. Mummy da Khaleefah suka soma shiga sannan Afzal, daga k'arshe kuma Daddy da ya tsaya daga bakin k'ofa tsabaragen kunyan da yake ji ko k'arisawa ciki ya kasa. Jikin Mummy Nazeefah ta fad'a tana kukan tsuma zuciya "Mummy please tell me it's a joke, Mummy it can't be Mummy please."

"Shhh ya isa haka" itama Mummy'n bata san lokacinda ta shiga zubda hawaye ba, ya rage Khaleefah kad'ai ke basu hak'uri. Duk anan kallonsu kawai Afzal yake bako uffan, yayi tsaye kaman gunki daga wani sashe. Daga bisani Mummy da Nazeefah kenrik'e a hannunta ta kewayo kan Daddy.

"Alhj meke faruwa? Shin kama san kuwa abinda kake fad'i?"

Nauyayyen ajiyan zuciya ya sauk'e sannan ya k'ariso cikin d'akin "Hjy Surayya ki gafirceni amma Amal kishiyar Nazeefah 'yata ce."

"Noo" Nazeefah ta shiga kad'a kai yayinda hawaye ke tsiyaya daga idanunta "Please don't do this Daddy I beg of you."

"I'm very very sorry Nazeefah-"

"Daddy ta yaya?" Tayi saurin katsesa "Taya Amal ta zamo 'yar uwata? How Daddy?" Ta tambayesa tana mey rushewa cikin tsananin kuka.

"It's a long story Nazeefah, fatana Allah yasa kin fahimci dalilin da yasa nake son ki rabu da Afzal ki kuma bani had'in kai."

"No Daddy, bazan rabu da Ya Afzal ba idan ma akwai me rabuwa da Ya Afzal toh Amal ce not me."

"Ya isa haka Nazeefah" Mummy ta dakatar da ita.

"No Mummy why will I be the one to pay for Daddy's mistake? Balle ma ban yarda cewa Amal 'yar uwata bace. Amal kishiyata ce she can never be my sister never!" Bori ta shiga yi wanda da k'yar Mummy ta samu ta lafa da ita. Hawaye na tsiyaya daga idanta ta d'ago kai tana kallon Daddy da jikinsa ya gama mutuwa ga kukan da iyalansa sukeyi har anan Afzal bece komai ba tsabagen state of shock da ya shiga, gani yake kaman a mafarki komi yake faruwa.

"Taya Amal ta zame yar Nazeefah Alhj? Ta yaya? I need answers."

"I'm terribly sorry Surayya."

"So kake kace mun kana da 'ya a waje?" Shiru yayi dan kunya ko amsawa ya kasa ga yadda Khaleefah ya kafa masa ido. Da irin wannan abin kunya da wani ido ze sake yima 'ya'yansa horo yanzu?
"Magana nake maka Alhj!" Ta tambayesa a fusace "I need answers we all need answers here!" Tayi demanding.

"Wallahi nima ban san da zaman Amal ba se lokacin da aka kad'eta."

"Baka san da zaman Amal ba?" Mummy ta tambayesa unbelievably. "Baka san da zaman Amal bafa kace? A ina aka ta6ayin haka?"

"Wallahi ban san da zaman Amal ba se kwanan nan."

"Taya ya zakace kana da 'ya amma baka san da zamanta ba Alhj? Until when zaka daina yi mun da 'ya'yana k'arya?"

"Wallahi ban san ciki ya shige jikin mahaifiyarta ba bayan faruwan abun."

"Yanzu ko kunya baka ji kake k'arya a gaban sirinkinka da 'ya'yanka Alhj? Wannan abu da me yayi kama? Ashe kana da 'ya a waje na aureka ban sani ba? Kuma kak'i ka sanar dani har yau? Ashe da ba don wannan cakwakiya ba haka zan cigaba da zama da kai kana mun k'arya kana zolayata? Why Alhj?"

"Surayya wallahi ba haka bane ni kaina recently na san cewa Amal 'yata cr, na so in sanar dake kuma amma tsoro nake, tsoron rana irin ta yau ki yarda dani Hjy Surayya."

"K'arya kakeyi wallahi k'arya kakeyi" ta fad'i tana kuka.

"Idan da nasan yaran nan 'yan uwa ne ajinki zan bari su auri Afzal ne dukansu biyu Surayya? Please believe me."

"Shine kuma yanzu dan rashin adalci kake son 'yata ta biya laifin da ka aikata? Toh kayi k'arya Alhj wallahi kayi k'arya."

"Hjy Surayya dan Allah kiyi hak'uri ki bani had'in kai a raba auren nan."

"Wallahi Allah ya isa nida 'ya'yana Allah ya isan mana." Har anan Afzal be ce komai ba. "Tashi Nazeefah tashi mu tafi." Hak'uri Daddy ya shiga bata amma ko ta kansa batayi ba yana yunk'urin ta6ata kuwa ta fisge jikinta "Koda wasa kar ka sake yink'urin ta6ani mu tafi Khaleefah" har bakin k'ofa Daddy ya bisu yana basu hak'uri amma ba wanda ya kewayo ya kallesa acikinsu. Bayan sun fice ya juyo kan Afzal.

"Afzal da-"

"No Daddy" yayi saurin katse sa had'e da ficewa daga d'akin yayi gun motansa be ratse ko ina ba se gida. Yana bud'e k'ofa sega Amal ta taso yi masa sannu da zuwa hannunta ya ja ya jefata jikinsa had'e da rungumeta tsam wane wani na shirin k'watan masa ita. Wani irin rikicaccen kuka yasa wanda ya mugun d'aurewa Amal kai.

"Subhanallahi Ya Omri why're you crying?" Se kuka kawai "Ya Omri please stop" kokawan d'agosa daga jikinta ta shiga yi amma ta kasa dan yadda ya damk'e ta. "Ya Omri cry nomore I'm here" bayanshi ta shiga bubbugawa a hankali tana basa hak'uri yayin da kukan nasa ya tsananta. Sun d'au tsawon lokaci a haka sannan na k'arfi da yaji Amal ta samu ta janyesa daga jikinsa yana mey k'ok'arin sake kankameta.

Kallo d'aya ta kaiwa idanunsa da suka kad'a sukayi ja nan take itama idan nata ya cika da hawaye ba shiri ta shiga tsiyayar da su tsan-tsan tausayi da k'auna. "Ya Omri what happened? Meyasa kake kuka haka?" Janta yayi ya sake rungumeta se chan ya saketa ya shiga share mata hawayenta har anan tambayansa take meya faru.

Hannunta biyu ya d'ago ya had'a da nasa yana murzawa a hankali yayinda ta k'ure masa ido tana shirin jin abinda ze fad'a mata. Bayan nishin da ya fisga ya kira sunanta "Amal?" Abinda ya jima beyi ba.

"Na'am Yaya?" ta amsa.

"Amal promise me."

"Promise you what Yaya?" Tayi saurin tambaya.

"Just promise me."

"I promise Yaya, everything for you."

"Thank you, thank you so much."

"Meya faru Yaya? Meyasa kake kuka haka? Batun Nazeefah ne?"

"Ko kad'an Amal, this is about you." Na sosai kanta ya d'aure "Ni kuma Yaya? meya faru?"

"Promise me again Amal, ki min alk'awari koda mey ya faru bazaki ta6a tafiya ki barni ba."

"Subhanallahi shin meya faru Yaya? Meyasa kake magana haka? Please talk to me."

"Just promise me Amal please."

"Yaya kafi kowa sani na bazan ta6a tafiya in barka ba because I love you, I love you so much."

"Thank you Lily" nan ya jata jikinsa ya sake rungumeta. Na matuk'a kanta ya sake d'aurewa shin meke faruwa? Hannu ta zagaye a bayansa hugging him back. "Amal I've found your biological father" ya sanar da ita a saitin kunnenta wani irin mumunan fad'i gabanta yayi ba shiri ta janye jikinta daga nasa. "Ka samu asalin mahaifina?" Ta tambayesa cike a k'in yarda. Kai zalla ya gyad'a mata yana me rik'o hannayenta cikin nasa.

"How? When? Where? " Ta jero mai tambayoyi nan take. Kafin ya amsa ta shiga k'aryatasa "No Yaya this can't be true, har a ina ka sansa bale idan ka gansa ka ganesa? You're mistaken Yaya koma waye ne mahaifin nawa nasan baya raye."

"No Lily, not at all mahaifinki yana raye."

"How? Taya kasan yana raye? Ya ma akayi ka sansa? Yaya please" kai take ta kad'awa cike da k'in yarda.

"Calm down Amal but that is not even the problem."

"Yaya what're you saying?" Seya bud'e baki ze sanar da ita seya kasa.
"Yaya please speak up what problem? Meyake faruwa?"

"Ki kwantar da hankalinki bana son abu ya samu lafiyan abinda ke cikinki."

"Yaya just tell me."

"Forget it, shikenan ma."
Hannunsa tayi saurin rik'owa kafin ya juya "Please tell me Yaya what is going on?"

"Kiyi min alk'awari bazaki yi reacting ba, komin yaya bazaki tada hankalinki ba za kuma kiyi wa bak'on lamarin nan kyakkyawan fahimta."

"Yaya ka fad'amun mana."

"I have to know, bana son zuciyanki ya tsinke abu ya sameki ko baby'nmu so promise me bazaki tada hankalinki ba."

"Okay I promise ka fad'a mun dan Allah" ta fad'a a k'ose.

"Amal you and Nazeefah are sisters" shiru kukeji a wajen ko motsawa Amal ta kasayi bale magana, k'ok'ari take ta fahimci inda ya dosa amma ta kasa. Daga bisani ta shiga kad'a kanta "Ni da Nazeefah?" Ta tambayesa.

"Yes Amal, Nazeefah k'anwarki ce" sulalewa k'asa tayi wanda da sauri Afzal ya tarota ya direta akan kujera yayinda idanunta suke shirin kafewa. Ruwa ya nema ya shiga yayyafa mata sede kaman sake kashe mata jiki yake tun yana iya ganin cikin idanun nata har ta rufesu. Ba shiri ya yasar da glass cup d'in inda yayi kaca-kaca a k'asa ya shiga bubbuga ta sede ina ko motsawa batayi. Dafe hannunsa da yace zeyi jikin kujeran kawai yaji abu kaman ruwa dubawanda zeyi ya tarar da jini wani irin rikicaccen ihu ya saki. "Amal? Amal? Please wake up Amal!" Se ihu yake yana kiran sunanta amma inaa ta riga ta jima da sumewa. Ba shiri ya kicicci6eta a hannu bema damu da jinin daze masa staining blue getzner'n dake jikinsa ba. A bayan mota ya sata ya shiga gaba se TH inda akayi emergency room da ita. Ko zama Afzal ya kasa gun se safa da marwah yake yana kuka kaman k'aramin yaro kowa yazo wucewa seya tsaya ya kallesa. Dan yadda ya rikice ko kiran Ummi ya sanar da ita halin da ake ciki ya kasa chan wata nurse ta jasa wani gu ya wanke hannunsa dake d'auke da jini har sannan ta tayasa goge kayansa sede jinin ya riga ya kama amma duk da hakan be damu ba. Bakin k'ofan nata ya koma ya tsaya yana jiran fitowan likitocin chan bada dad'ewa ba sega k'ofan ya bud'u. Ko daman yin magana be baiwa likitan ba ya shiga kwararo masa da tambayoyi.

"Calm down calm down" Likitan ya shiga kwantar masa da hankali sede is of no use saboda hankalinsa ya riga ya tashi.

"Please answer me how is my wife?"

"Your wife will be fine you don't have to worry nan da 'yan mintuna kad'an zata farfad'o."

"And my baby?" Reaction daya gani a fuskan likitan kad'ai yasa k'asusuwan guiwansa sakewa yayinda cikinsa ya d'au ruwa. Ba shiri ya shiga kad'a kai "Please speak up Dr how's the baby? Kun samu kun ceto cikin?"

"I'm very sorry Sir amma it was too late tun kafin ku iso nan cikin ya lalace an de wanke cikin yanzu anyi duk wani abinda ya kamata I'm very sorry zaka iya shiga ganinta." Motsi wannan Afzal ya kasayi a wajen tun ficewan likitan da nurses d'in se hawaye kawai yake zubarwa yayinda gobaran tsanan Daddy yake ruruwa mai a zuciya. Ma shin meya kaisa sanar da Amal cewa ita da Nazeefah sisters ne? Da ya san abinda yin hakan ze haifar da be soma ba. Yanzu shikenan sunyi ban kwana da baby'nsu kenan? Baby'n da har ya gama imaging yadda kamanninta ze kasance d'aya da na Amal tasa? Baby'n da ya gama picturing rayuwansu da ita? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un tabbas wannan rana a cike yake da masifa da k'unci. Guiwa na rawa ya dafe handle na k'ofan ya bud'e ya shiga ciki. Chak ya tsaya gun ya kasa k'arisawa tsan-tsan tausayi kawai, ta ina ze fara sanar da Amal cewa cikin nata ya lalace? Nooo baze iya ba. Jiki na rawa ya k'arisa ciki had'e da jan kujera ya zauna a gefenta. Kakkarwa hannunsa ke ya d'ago ya dafe nata da canular ke kai. "Amal I'm so sorry, I'm terribly sorry please wake up karki tafi ki barni you promised to stay by my side" kuka yake tamkar d'an yaro a gurin. Ba ma wai na zubewan cikin ba sena tsoro da yake zamansu na iya k'arewa shida Amal tunda dry gashi ita da Nazeefah 'yan uwa ne. Baze iya rayuwa ba ita ba.

Kukan ya cigaba da yi ba fashi har seda Amal ta shiga bud'e idanunta. Mik'awa yayi had'e da sumbatan goshinta "Thank you for staying alive with me Rania" ya sanar da ita hannunsa na acikin gashin kanta yana shafawa a hankali.

"Rania why aren't you saying anything?" Ya tambayeta bayan dogon shirun da tayi hannunta kawai yaga ta kai akan cikinta a hankali ya aza nasa akai shima.

"Is my baby still with me?" Ta tambayesa murya ciki-ciki. Rasa na cewa yayi kawai ya shiga yi mata murmushi saidai duk yadda yaso 6oye k'uncin da yake ciki ya kasa a hankali hawaye ya shiga ciko masa a ido.

"Ya zube ko?" Ta sake tambayansa itama idan nata na mey cikowa da hawaye. "Yaya please answer me idan zubewa yayi just tell me" ta k'are hawayen na tsiyaya daga idanunta.

"Amal I'm so sorry please forgive me."

"Ya zube?" Ta kuma tambayansa kai zalla ya gyad'a mata yayinda ta rushe da wani irin masifaffen kuka. Gadon ya haye da wuri ya jata jikinsa ya shiga bata hak'uri amma se bori takeyi da k'yar ya samu ya lafa da ita. Tana kwance a jikinsa ta kira sunansa.

"Yes?" Ya amsa patiently.

"Meyasa se ita? Why not me?"

"Because you're more precious Rania, saboda Allah ya tausaya mun yasan idan ya d'aukeki bazan iya rayuwa ba."

"Yaya na kasa amincewa da hakan, dan Allah ka gafirceni."

"Saboda mey Rania? Mey kikayi?"

"Na kasa rik'e amanan rik'on da ka bani Yaya I'm so sorry."

"Ko kad'an ba laifinki bane Rania idan har akwai wanda ze nemi tuna toh nine, da ban sanar dake gaskiya ba da cikinki be zube ba, da har yanzu baby tana tare damu."

"But for how long zaka ta 6oye mun gaskiya Yaya?"

"It doesn't matter now, ni kawai ki daina blaming kanki, dama haka Allah ya qaddara baby bazata rayu damu ba, fatan mu Allah yasa mey ceto ce."

"About what you said? Shin da gaske ne Nazeefah k'anwa tace?"

"Amal that doesn't matter now lafiyarki ne a gaban mu yanzu."

"No Yaya" ta d'ago kai a hankali tana kallonsa a raunane "It does matter, is Nazeefah my half sister? Shin dagaske ne Mahaifin mu d'aya ne da ita?"

"Amal I'm very sorry I never wished for things to turn out this way."

"Just answer me."

"Yes Amal, keda Nazeefah 'yan uwa ne."

"Ta yaya? Taya ma hakan ze zamo gaskiya?" Nan ya kwashe labarin duk yadda akayi ya bata Amal kam se kuka. Yanzu ma'ana kenan mutumin da ya taimake ta lokacin da Nazeefah tasa aka bigeta shine mahaifinta, mutumin da take ta fatan ina ma ace mahaifinta shine asalin mahaifinta? Meyasa taji ta tsanesa gabad'aya yanzu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un taya hakan ma ze zamo gaskiya? Tayaya ma ya gane ita 'yarsa ce? Ashe de ba tsakani da Allah ya taimaka mata ya kuma kula da ita ba lokacin, shin tayaya ma yasan ita 'yarsa ce? A iya labarin da Mami tayi mata ta nuna mata cewa shi mahaifin nata bema san an haifeta ba. How is this even possible?? She need answers. Kuka take Afzal yana bata hak'uri.

"Yaya baka gane bane Daddy baze ta6a zama mahaifina ba, baka fahimce sa bane."

"Please cut it out."

"No Yaya it can't be possible idan da Nazeefah k'anwa tace da naji hakan a jikina please stop saying she's my sister please."

"Amal saidai muyi hak'uri amma bazamu iya canza k'addarar Allah ba."

"Ya zamo dole mu hak'ura da juna kenan Yaya."

"Saboda mey Lily?" Ya tambayeta a raunane.

"Bazeyi mu cigaba da zama ahaka ba Yaya, bazeyi muna jini d'aya da Nazeefah mu cigaba da kasancewa matayenka ba, zama damu ya haramta maka."

"No Amal please don't talk like that dan Allah kibar cewa haka, I can't live without you kinfi kowa sanin hakan."

"I'm sorry Yaya amma gaskiya d'aya ce rabuwa ya zamo dole."

"No please Amal, dan Allah kibar cewa haka, kefa kika ce our love for each other is enough."

"Not in this case Yaya saboda we can't escape from the truth."

"But you promised never to leave me."

"I'm sorry I'm breaking that promise now."

"Please don't Amal there has to be a way."

"What way Yaya?"

"I don't know, zamuyi tambaya akai in shaa Allahu zasu san yadda zasuyi damu but please kibar cewa zaki tafi ki barni bazan iya rayuwa ba ke ba Amal I really can't."

"I'm really sorry Yaya I'm so sorry."

"I dont want you to be Amal, I want you to stay please kiyi mun alk'awari." Kai zalla ta iya gyad'a masa yayinda hawaye ke bin k'uncinta. Ita abun ma ya taru ya mata yawa ga miscarriage, gashi ita da k'anwarta suna auren miji d'aya. Wannan wace irin k'addara ce?

"Kayi ma likitan da ya dubani magana I want to be discharged."

"But Amal you're sick bakida k'arfi."

"Ina son in tafi gida."

"Wani gida d'aya? Har yanzu kina kan bakanki na tafiya? Please don't leave me Amal please don't."

"Just take me home Yaya."

"Promise me bazaki gudu gida gunsu Mami ma?" Kai zalla ta gyad'a masa amma abinda zuciyanta ke raya mata ba ta gudu ta koma gunsu Mami bane so take ta gudu ta shiga wani duniyan daban inda ba wanda yasan tarihinta. Cakwakiyan dake cikin rayuwanta ya isheta, abin kunyan yayi yawa. Haka Afzal yaje ya samu likita yace a sallamesu ba yadda likitan beyi dashi ba akan yabari koda zuwa gobe idan Amal ta d'an samu k'arfin jiki amma ina Amal tace ita sede yau za'a sallameta hakan kuwa akayi daga k'arshe. Magungunan da aka rubuta mata Afzal ya sai sannan suka koma gida inda Afzal ya d'auketa ya kaita ciki, a kan gado ya kwantar da ita sannan ya fad'a bayi yayi wanka ya sirka mata ruwan zafi bayan ya fito ya taimaka mata tayi wankan itama sannan ya shirya ta tsaf ya shirya kansa shima. Gabad'aya ya rasa nayi ga kukan da Amal take tayi masa tun d'azu da k'yar ya samu ta hak'ura ta daina. Wayansa ya d'aga ya kira Nazeefah amma layin a kashe yake cewa, na Mummy yayi trying nan ma switched off dama yasan za'ayi haka yasan Mummy zata kashe wayanta sannan tasa Nazeefah ma ta kashe nata don kar Daddy ya samu ya same su. Ummi ya kira next ya tambayeta ko tana gida inda ta jaddada masa eh. Key'n motansa kawai yaja ya k'arisa kan Amal da ke ta jan numfashi.

"Rania you're sick, enough already please kukan ya isa haka."

"Zaka fita ne?"

"Zanje gun Ummi zan dawo yanzun kinji? Akwai abinda kike buk'ata?"
Kai ta kad'a masa yayinda ya janye mata bargo ya rufeta da kyau, peck ya sauk'e mata akan goshi "Rest okay? I'll be right back I love you" nan ma kai ta gyad'a masa sannan ya fice. Bada dad'ewa ba Amal ta mik'e zaune, a sannu a sannu take takawa ta d'auko akwatinta., bata da k'arfin ko sisi ta shiga fiddo da kayakinta tana shiryasu cikin akwatin nata bayan ta gama had'a kayakin nata ta sanya hijabi ta d'au wayanta ta fito waje. Kaman Afzal yasan abinda take shirin yi yasa key ya rufe k'ofan ta waje. Mey gadi na ganin ta fito yayi sauri ya je ya sameta.

"Hjy lafiya?"

"Ka tayani jan akwatin waje dan Allah."

"Direba na gida ko in mishi magana ne?"

"A'a barshi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment