Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

mik'e a kasalance, a corridor'n d'akinsu ya tarar da Amal tsaye wajen se kuka take shark'af-shark'af. Wani irin tsinkewa gabansa yayi bade taji duk abinda shida Ummi suka tattauna akai ba? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

"Amal?" Ya kira sunanta da hanzari ta juya mai baya ta k'arisa cikin d'akin bata kai ga rufe k'ofan ba ya hankad'e ya fad'a ciki. "Amal please stop crying" ya buk'aceta cikin sanyin murya yayinda yake k'ok'arin rik'o hannunta sede ta hanasa.

"Amal please enough ke baki san kukan nan rashin lafiya ze k'ara miki ba?"

"One of us have to go Yaya" ta fad'a tana mey share abinda yace mata.

"Amal-"

"Dole ka rabu da d'aya tsakani na da 'yar uwata koba haka ba?"

"Am-"

"Just answer me Yaya na riga naji komai."

"Yes Amal amma dan Allah ki kwantar da hankalinki."

"Tayaya? Tayaya kake tsammanin zan iya kwantar da hankalina Yaya bayan ina shirin rasa mijina mafi son komai a rayuwata? Mijina wanda na d'au mutuwa ce kad'ai zata iya raba mu? Mijina da na d'au shine mahaifin yaran da zan haifa? Wanda farin cikin rayuwana ya dangana a jikinsa? Ta ina hankali na yaga ta kwanciya Yaya? I'm about to lose you, I'm about to lose the love of my life, my soul, my spirit, and my everything!" Kawai ta fashe da wani irin kuka. Tsan-tsan tausayi Afzal be san a lokacinda hawaye suka ciko masa a ido ba, ashe itama Amal haka take sonsa kawai bata nunawa ne? Ashe tana iya shiga damuwa idan har rabuwa ya shiga tsakaninsu? Ya d'au shi kad'ai ze sha wuya a rashinta ashe itama rayuwanta na iya fad'awa gwagwarmaya a rashinsa wow!

"Amal please enough kibar kukan haka."

"Wa zaka d'auka acikinmu Yaya?"

"Amal please-"

"Just answer me Yaya" ta katsesa cike da tashin hankali "Just answer me please."

"I don't know Amal saboda I can't choose, kaman yadda bazan iya jure rasa ku duka ba haka ma bazan iya d'aukan d'aya in bar d'aya ba. I love you both, I really do."

"But one of us has to go, baka ji abinda Ummi tace bane?"

"I know I just... I just don't know ni kawai kibar kukan nan."

"Bazan ta6a iya daina kuka akanka ba Yaya because I love you, I love you so damn much shiyasa rabuwa da kai yake min zafi, gani nake kaman idan na rasaka nima ina iya rasa nawa ran" da sauri ya katseta "But Amal you're not going to lose me bance Nazeefah zan d'auka in bar kiba."

"I don't know Yaya, ban sani ba ko Nazeefah zaka d'auka akaina but I just want you to know that my everything revolves around you, I don't think bayan kai zan iya kwad'aita wa zuciyata son wani d'a na miji because my heart is with you Yaya, I can never stop loving you" ta k'are tana kuka. A nitse ya rik'o hannunta maras canular cikin nasa yana murzawa a hankali "And I can never stop loving you too Amal I'm not picking Nazeefah over you kema kin sani."

"But one of us has to go."

"Se kuma aka ce kece zaki tafi? Kin manta cewa zuciyana baya bugawa se ya ji ki a kusa dashi? Kin manta cewa without you I'm nothing? kin manta cewa ke kad'ai ce hasken da nake buk'ata a rayuwa na da kuma Iskan da nake buk'ata dan in rayu? Kin manta da duka hakan ne Amal?"

"Not for once did I forget any of these Yaya saidai a wannan hali da muka tsinci kanmu yanzu nake ganin soyayyar mu ma tayi kad'an ta ceto mu daga cikinsa."

"Meyasa kika ce haka Amal? I thought our love for one another was enough."

"I'm sorry Yaya but it isn't."

"Amal it is because I'll never leave your side, I came into your life to stay forever not just for some time because I love you, I love you Amal morethan anything you could ever imagine."

"And I love you too Yaya, morethan life itself. Your love is incomparable amma rabuwa ce ta zamo dole."

"Ba se mun rabu ba Amal dan Allah kibar cewa haka."

"Dole ne in fad'i haka Yaya, dole ne mu cire son zuciya muyi abinda ya kamata."

"Mey kike nufi?"

"Ina nufin Nazeefah. Nazeefah k'anwatace Yaya kuma komin yaya ina sonta komin mey tayi mun I'll always want the best for her. Kai kanka kasan irin son da Nazeefah keyi maka, ka kuma san cewa akan ka Nazeefah na iya yin komai, bazan so ace a matsayina na 'yar uwarta kuma yarta ba na shiga tsakaninta da masoyinta. I don't care ko ita bata feeling thesame way I feel towards her, ban damu ko tana so na ko bata sona ba, ban damu koda nice mak'iyar ta a duniyan nan ba as long as she's my sister I'll love her and want only the best for her, this is why I'm giving up on you for her."

"Amal kin kuwa san mey kike cewa?" Afzal da mamaki ya rufesa ya tambaya.

"Yes Yaya, ina sonka amma hakan ba wai na nufin zan cigaba da mallakanka bane, na yafe soyayyar ka wa k'anwata na hak'ura ni ka sauwak'e mun ku kucigaba da zama tare, seeing my sister happy is enough to make me happy."

"I can't Amal" ya amsata a raunane "Bazan iya rabuwa dake ba, bazan iya ba."

"Zaka iya Yaya, ni kaina nasan how hard life will be for me without you amma ba komai mukeso a duniya muke samu ba, wani sa'in dole muyi making sacrifices koda kuwa akan abunda muka fi so ne it is why I'm doing this. I love you but I have to let you go."

"No Amal dan Allah kibar cewa haka, you're not leaving me you're not."

"Yes I am Yaya, you have to let me go."

"No I can't I can't live without you."

"Idan baza ka iya rayuwa ba ni ba Nazeefah kuma fa? Mey zakayi da ita?"

"I don't know Amal, but I can't afford to lose you."

"Kaman yadda kake jin bazaka iya rabuwa dani ba itama Nazeefah haka take ji Yaya, haka take jin bazata iya rabuwa da kai ba. Ka fini sanin yadda take sonka let's do this for her kar mu bari sharrin laifin Daddy ya fad'a kanta."

"Ke kin amince ya fad'a a kanki kenan Amal? Keda Daddy yafi cutarki da mahaifiarki?"

"Yes Yaya na hak'ura hakan ya fad'a akaina saboda InnAllaha ma'as sabireen I'm sure Allah will listen to my silent cries and see me through."

"But I can't Amal, bazan iya jure ganinki cikin bak'in ciki da k'unci ba kullum. Kece aka sameki ta haramtacciyar hanya, kece kika girma ba uba, kece kikayi girma cikin talauci bayan kaman yadda Nazeefah tayi girma cikin kud'i da kulawa da jin dad'i kema kin cancanci hakan amma haka akayi depriving naki, bayan nan kece kikazo aure kina ji kina gani aka rabaki da masoyinki na asali aka sanya ki aurena na dole dukda bakiya so. For all your life you've never been happy-"

"But you made me happy Yaya" tayi saurin katse sa da murmushin takaici d'auke a fuskanta "zan iya cewa ranakun da na zauna da kai sune mafi farin ciki da murna a rayuwa na gabad'aya, the happy moments I've spent with you have erased every single bad day I've witnessed before and I'm morethan thankful to God, I cannot ask more for more. You gave me only the purest form of love, koda Papi ya sanar dakai asalina baka k'i ni ba, baka k'iyamace ni ba infact sema k'ara nuna mun so da kayi. You loved me as if your life depended on it, ka bani kulawan da bayan Mami da Papi ba wanda ya ta6a bani irinsa, your love was simply enough for me Yaya so karka damu dani, I'm morethan satisfied."

Be iya ya sake cewa komai ba kawai tuna kalaman Nazeefah yake da take cewa _No Daddy, bazan rabu da Ya Afzal ba idan ma akwai me rabuwa da Ya Afzal toh Amal ce not me_ shi kansa ya sani baza a ta6a had'a halatayyan Amal dana Nazeefah ba, they're two different people. Idan akwai kalma d'ayan da Nazeefah ta sani wanda Amal bata sani ba shine 'Son Kai' ko shi baze iya yin abinda Amal tayi ba yanzu. Janta yayi jikinsa kawai ya rungumeta yayinda ta kuma rushewa da wani kukan tsuma zuciya. Kukan ta cigaba da yi ajikinsa yayinda ya rik'e ta tsam a jikinsa, seda tayi mey isarta sannan ya d'agota ya shiga share mata hawayen nata inda ya jata bakin gadon ya kwantar da ita had'e da sa mata sabon ledan ruwan. "Rest okay?"

Kai zalla ta gyad'a masa be kai ga mik'ewa ba wayansa dake aljihu ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Nazeefah, ba tare da 6ata lokaci ba ya d'aga "Nazeefah?"

"Na'am Ya Rouhi ina kwana?"

"Lafiya ya kike? Ya su Mummy?"

"We're all good."

"Wani hotel kuke? I need to see you."

"Deribe Hotels" ta sanar dashi.

"I'll come pick you up okay? Tell Mummy ni nace zan zo in d'aukeki."

"I'll seka zo."

"Yauwa ba-bye." Nan ya katse tare da kewayowa kan Amal data k'ura masa ido. "Zanje gida gun su Mami domin sanar dasu halin da ake ciki okay? Daga nan inje in duba Nazeefah."

"Allah ya kare."

"Ameen I love you" ya sanar da ita had'e da sauk'e mata peck a goshi sannan ya mik'e ya fice bayan ya ja wa mey gadi kunne akan cewa komin yaya kada ya bar Amal ta fita. Daddy yayi ma waya yace yaje ya samesa a gidan Nazeefah sannan ya wuce Deribe hotels yaje ya d'auko Nazeefah inda suka nufi gidansu Amal. Nazeefah da bata san ina yake kai su ba se tambayan sa take ina ne nan, shi de iyaka ce mata yayi ze d'au wasu mutane ne shikenan. Ciki ya shiga suka gaisa da su Papi inda yake sanar dasu cewa Amal tayi 6ari bata da lafiya yazo ya d'aukesu ne suje su dubata. Cikin k'ank'anin lokaci suka shirya suka fito, sanin halin Nazeefah ba lallai ne ta yarda ta koma baya haka kawai ba se yayi mata k'aryan cewa Papi d'an uwansa ne Mami kuma matarsa ce don haka tayi hak'uri su zauna da matar a baya se shi ya zauna a gaba. Batayi gardama ba ta samu Mami suka zauna a baya bayan sun gaisa.

Sude su Papi ko da suka ga Afzal ya d'au wani hanya daban bana gidan Amal ba basuyi magana ba. Ahaka har suka isa gidan Nazeefah suka k'arisa ciki. Fitowan da zasuyi daga motan Nazeefah ta hangi Daddy dake zaune akan varenda akan d'aya daga cikin kujerun da aka ajiyesu a wajen.

"Ya Rouhi meyasa ka kawo ni bayan kasan Daddy na nan?"

"Enough Nazeefah we're here to sort out things."

"Not when Daddy is around take me back to Mummy."

"Ya isa Nazeefah I know this is not easy on you amma kiyi hak'uri magana kawai zamuyi shikenan."

"Ni bana so banida sauran abinda zance masa tunda ya had'ani kishi da 'yar uwata."

"Nazeefah please" Afzal yayi mata ido wanda hakan yasa tayi shiru.
Na sosai Mami da Papi suka shiga rud'ani domin a iya saninsu de kaman yadda Afzal ya gabatar musu da Nazeefah ce musu yayi ita matarsa ce toh mey take nufi da cewa mahaifinta ya had'ata kishi da 'yar uwarta? Shin Afzal d'in mata nawa ne garesa?

"Afzal lafiya dai ko?" Papi da ya kasa hak'ura ya tambaya cike da rud'ani.

"Yi hak'uri Papi mu shiga daga ciki Mami, Nazeefah let's go in." Har anan Papi da Mami basuga fuskan Daddy ba kasancewar bayan sa ne ke fuskantansu itama Nazeefah dan sanin da tayi masa yasa ta gane shine. Sun k'arisa corridorn kenan Afzal yayi gyaran murya inda Daddy ya juyo idanunsa wanda basu sauk'a a ko ina ba se akan na Papi da Mami. Daga kan kujeran amma sanda yaci tuntu6e kad'an ya rage kujeran be yasar dashi a k'asa ba yasamu ya tari kansa. A rikice ya mik'e tsaye yayinda idanunsa dana Mami suke a had'e har anan, ita kanta Mami dan mamaki ta kasa yin magana haka Papi ma se k'ura wa juna ido kawai suke. Daga bisani Daddy ya kira sunan Mami.

"Jamee?" Da mamaki Nazeefah ta tsaya kallonsa tana mey tambayan kanta ta inda akayi Daddy yasan 'yan uwan Afzal 'yan uwan ma ba dangin kusa ba. Tun ganinsu da tayi talakawa ta yanke hukuncin irin dangin nesa-nesa d'innan ne su.

"Khaleefah?" Mami ta ambaci sunansa baki na rawa. Yau shekaru nawa? Sama da ashirin, ashirin da biyu kenan. Ashe dey Allah ze sake had'asu. Ashe de zata sake sanya mutumin daya cuceta ya kuma 6ata mata rayuwa a ido. Nazeefah kam kanta ya gama d'aurewa yanzu se raba ido take.

"Afzal meke faruwa anan? Waye mutumin nan? Meyasa kuma ka kawo mu gidansa?" Papi ya kewayo yana kallon Afzal.

"Mu shiga daga ciki dan Allah zan sanar da ku komai."

"Papi mu koma" cewan Mami had'e da juyawa. "Ba cikin da zamu shiga."

Da hanzari Afzal ya sha gabanta "Please don't walk away Mami, please kar ki tafi."

"Na d'au cewa kayi Baby tayi 6ari bata da lafiya" Ido Nazeefah ta zaro waje cikin Amal ya zube? Shikenan bata da wata tsoro yanzu, dama cikin nan shine tsoronta, kar don cikin Afzal yace ze d'au Amal akanta. Amma yanzu da ya zube ta tabbata idan ma za6i aka basa acikinsu biyu inhar ma basu haramta masa ba kenan ta tabbata ita za a sanya sa na dole ya d'auka tunda itace uwar gida.

"Yes Mami and ba k'arya nake muku ba I intend to take you to her idan mun gama warware matsalar dake nan."

"Wace matsala kenan?" Papi ya tambaya.

"Papi wannan shine mahaifin Nazeefah matata."

"Mahaifin matarka?" Ya kuma tambaya.

"Eh Papi."

"Ka san mey kake fad'i kuwa Afzal?" Mami da ta kewayo ta jefa mar tambayar "kasan kuwa wannan azzalimin mutumin shine mahaifin Amal?"

"Eh Mami mahaifin Amal kuma mahaifin Nazeefah."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Papi yasa salati. "Jameela yaran nan 'yan uwa ne" yace da Mami da tuni idanunta suka ciko da hawaye.

Nazeefah kam se raba ido take yayinda abun ya tsaya mata a wuya, yanzu Daddy ya rasa da wa zeyi barikanci ma seda irin Mami?

"Mey nayi maka a rayuwa da ka za6i kayi ta k'untata mun haka Khaleefah?" Tace da Daddy da har yanzu be kuma cewa komai ba idonta na tsiyayar da hawaye. "Duk kalan zalunta ta da kayi ka lalata mun rayuwa hakan beyi maka ba seda ka dawo kan 'yata?" Anan kan Nazeefah ya sake shiga duhu aww wai dama ba karuwar Daddy bace? Tarketa Daddy yayi ya d'irka mata ciki? Oh Allah! Wannan abun kunya da mey yayi kama ace a gaban mijinta ana tuhumar mahaifinta da aikata zina. Ji tayi gabad'aya ya fita mata daga rai bata k'aunansa.

"Jamee-"

"Allah ya isa Khaleefah, Allah ya isa tsakani na da kai."

"Mami dan Allah kiyi hak'uri mu shiga ciki muyi magana" Afzal yace.

"Wani magana zamuyi Afzal? Ya kama ya had'a 'yan uwan jini kishi wani magana ne kuma za'a sake yi wanda yafi a sauwak'ewa yaran duka? A tunani na da gan-gan yayi hakan dan ya mayar mun da 'ya bazawara."

"Jameelah dan Allah kiyi hak'uri wallahi ban san cewa rabo ya shiga tsakanin mu ba-"

"Dakata Khaleefah" Papi ya katsesa "Bamu buk'aci jin komai daga bakinka ba, mu shiga Afzal muji abinda kake tafe dashi muje Jameela." Ba don Mami na so ba ta bi bayan Papi suka k'arisa ciki inda Afzal ya bayyana musu halin da ake ciki tun daga kan lokacin da aka bige Amal zuwa lokacinda Daddy yagano gaskiya dama komai, daga k'arshe kuma ya sanar dasu tambayan da sukayi wa malamai da kuma amsan da suka samu. Na sosai hankalin Nazeefah ya tashi, acewarta baza a bawa Afzal za6i ba ita za'a sanyasa ya d'auk'a na dole ashe ba haka abin yake ba. Ita kam ma bata yarda ba. Zata nemi wani Malami tayi mar tambaya ta tabbata za a samu sa6ani tsakanin amsan da Afzal ya samu. In ba haka ba ina zata sa ranta idan Afzal ya za6i Amal akanta? Yau nata ya k'are.

"Tabbas wannan abu da kunya yake da kuma zafi ace 'yan uba suna auran miji d'aya. Anan Allah yana nuna mana cewa komin yaya mutum yayi baze ta6a iya yi masa wayo ba kuma muddin kad'au alhak'in mutum baka nemi yafiya ba toh tun a duniya Allah ze fara kamaka ya nuna maka illan yin hakan. Saidai ina son ka kwantar da hankalinka Afzal kasani wannan k'addarar bata su Amal ce kad'ai ba no harda kai kaima. Ka kuma sani kai kake da za6i tsakaninsu, kuma duk wacce ka za6a bawanda ya isa ya tambayeka meyasa. In shaa Allahu duk nan zamuyi maka kyakkyawar fahimta mu baka goyin bayan da ya kamata Allah shige ma gaba" Papi yace.

"Ameen" Afzal ya amsa "Nagode Papi."

"Se yaushe kenan zamu sake ji daga gareka?" Mami ta tambaya.

"Wannan ba abu neba mey sauk'i Mami, ba abu neba da zan iya yinsa da kaina acikin k'ank'anin lokaci amma zan dey yi k'ok'ari inga ban ja lokaci ba."

"Gaskiya ya kamata saboda kowa yasan inda ya tsaya, ba yaran kad'ai ba harta mu manyan ma" Papi ya amsa.

"Tabbas Papi saidai ban san wa zan d'auka wa zan bari ba acikinsu don gudun yima d'ayarsu rashin adalci, shiyasa na yanke hukuncin yin istikhara duk za6in da Allah yayi mun shi zan bi dafatan idan nayi hakan both parties bazasu ga kaman anyi musu rashin adalci ba zasu kuma fahimceni."

"Ai zancen rashin adalci ma bai taso ba Babana, za6i naka ne ba wanda ya kai ya tilasta maka."

"Nagode sosai Papi idan ba abinda zaku sake fad'a semu wuce gida kuje ku duba Amal."

"Babu mu tafi" Mami ta amsa cike da hanzari.

"Papi dan Allah kayi hak'uri nasan abinda nayi muku is unforgivable nasan banida right na baku hak'uri amma dan Allah kuyi hak'uri ku saurareni wallahi tallahi ban san rabo ya shiga tsakani na da Jameelah ba, ban ta6a sanin Amal 'yata bace se lokacin da tayi hatsari. Meyasa zan so in had'a 'ya'yana biyu kishi? Dan Allah ku saurareni."

"Jameelah kina da abin cewa?" Papi ya juyo had'e da tambayan Mami.

"A'a Abba mu tafi" ta amsa tamkar bataji abinda Daddy ya fad'a ba. Nan suka mik'e duka "Ermm Ya Afzal can I have a word with you? Papi ku d'an yi hak'uri dan Allah" fad'in Nazeefah.

"Ba komai muna jiranku a waje." Hannun Afzal taja izuwa d'akinsu sannan ta rufe k'ofan.

"Ya Rouhi za6a zakayi tsakani na da Amal kenan yanzu?" Ta tambayesa a maraice.

"Nazeefah I have no other option inda ta nine da saidai in cigaba da zama daku duka because I love you both."

"Nasan Amal zaka d'auka akaina I know."

"Please don't talk like that."

"Ka k'aryata hakan ne? Ka k'aryata cewa ba Amal zaka za6a ka sauwak'e mun ba?"

"Nazeefah please-" yana yunk'urin ta6a hannunta ta ja da baya. "For all my life, I've loved you Ya Rouhi, banida burin da yafi inga na kasance tare da kai na sanya ka farin ciki. Duk wani abinda nayi da abaya wanda ya 6ata maka rai kasani nayi ne because I love you, saboda nafi son in mallakeka ni kad'ai. Dukda auren biyayya mukayi I'll still choose you to be my husband if I were to be given a second life. Lokacin da na fara jin dad'in aurena kawai ka auro mun Amal out of the blue. Amal da na tabbata kafi sonta acikin zuciyanka fiye dani saboda ita za6in zuciyarka ce nikuwa za6in mahaifinka ne."

"Nazeefah-"

"Ba seka k'aryata komai ba Ya Rouhi hakan ne kuma nima na sani. Kafi son Amal a kaina wai tayaya ma bazaka fi sonta ba bayan she's fertile wataran zata haifa maka yaran da kata mafarki kake so ni kuwa mey zan iya baka? Babu saboda ga dukkan alamu juya ce ni."

"Nazeefah enough please ke kanki kinsan ba haka bane, ke kanki kinsan ke ba juya bace."

"Then explain to me why shekarana sama da uku a gidanka amma ko 6atan wata ban ta6ayi ba."

"Saboda kowa da lokacinsa ne Nazeefah" ya sanar da ita a hankali yana mey d'ago hannayenta yana had'asu da nasa. "Saboda Amal ta rigaki conceiving doesn't mean ke bazaki ta6a iya d'aukan ciki ba. Ina kika mance da tarihin Annabi Ibrahim da matarsa Saratu? Shin kin mance a tsufansu suka haifi Annabi Isma'il? Haihuwa lokaci ne Nazeefah, saboda Amal ta rigaki doesn't mean you're sterile. I believe in you Nazeefah kuma ni koda ma bazaki iya haihuwa ba hakan baze dameni ba ai dama ba jayayya mukayi kafin mukayi aure cewa dole dole se kin haihu min ba."

"Then pick me over Amal, idan har kana nufin abubuwan da ka fad'a ka d'aukeni ka saki Amal." Da mamaki Afzal ya tsaya kallonta yayinda kalamun Amal suke dawo masa yadda ta cire son kai ta nuna lallai lallai ita ta hak'ura ya d'au Nazeefah akanta.

"Nazeefah shin bakiya tausaya wa 'yar uwarki ne ke?"

"Tausaya mata? Meyasa zan tausaya mata Ya Rouhi bayan tana shirin sace mun mahaifi da miji?"

"Amal bata da niyyan hakan kema kin sani Nazeefah, k'addara ce ta riga fata ba ita ta za6i mahaifinku ya zama d'aya ba, ba ita ta za6i mijinta ya kasance d'aya dake a matsayinki na 'yar uwarta ba, k'addara ce."

"Amal ba 'yar uwa ta bace Ya Rouhi duk wanda yake shirin rabani da kai ba d'an uwana bane. I love you Ya Afzal, kuma ba kai bana jin zan iya rayuwa. Nasani yadda nake sonka ba haka kake sona ba but for once please choose me over Amal. For once ka nuna min kana sona nima let me feel loved Ya Rouhi. It has always been Amal, komai Amal komai Amal let it be this time, let it be Nazeefah. Please choose me over her I love you Ya Rouhi so much."

"Nazeefah I love you too, kema kin san hakan."

"Then choose me ka d'aukeni ka saki Amal."

"But I'm not the one to decide Nazeefah. By Allah ko wuk'a aka sa min a wuya bazan iya za6an d'aya acikinki da Amal ba. It's not as easy as it seems."

"I know it's Amal you're going to pick dukda hakan I want you to know that I'll never stop loving you Ya Rouhi, koda ka d'au Amal akaina hakan bazesa in daina sonka ba saidai in tsani Amal na shiga tsakani na dai da tayi. I love you so much Ya Rouhi" ta k'are idanunta na cikowa da hawaye. Janta yayi jikinsa ya rungumeta tsam yayinda take k'ok'arin k'watan kanta.

"Just let me go Ya Rouhi" ta fad'a tare da k'watan kanta daga jikinsa, idanun nan sun kumburo sun kad'a sunyi ja "Muddin ka za6i Amal a kaina bazan ta6a
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment