Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ne ze bika tabbas yaga hakan yanzu. Yanzu da ace aikin alkhairi yayi a baya sede 'ya'yansa suci riban hakan, amma daya shuk'a tsiya ba shi kad'ai ba harta yaransa seda hakan ya shafa.

****
Nazeefah bata fasa turawa Afzal sak'o tana neman tubansa ba safe ba dare tun tana kiransa baya d'agawa har ta hak'ura ta daina yau kwanan ta biyu kenan gabad'aya ta fita daga kamanninta dama ba k'iba bane da ita akan raman nata ta sake ramewa ba aikinta se kuka da tunani kullum, gashi ko makaranta ta shiga bin ta da kallo ake Rumaysa duk ta bazata a gari mijinta ya kaita cell sekace ba ita ta d'aurata akan gur6arcacciyar hanyar ba.

***
Afzal na zaune a office amma hankalinsa gabad'aya akan Amal tasa yake kullum haka yake yini da tunaninta ya kuma tashi da shi gashi tun ranan be sake sanyata a ido ba, koya kirata bata d'agawa sak'o ma ya tura mata bata replying nasa, whatsapp messages ma ko reading batayi he can't explain how much he's missing her. So yake ya sake ganinta kafin a sallameta daga asibitin dan yaji daga bakin nurse d'in cewa yau za a sallameta jira yake lokacin lunch yayi yaje ya dubata wanda kafin nan ya d'au wayansa ya kira Ummi jin shiru tun ranan da sukayi magana har yau bata sake nemansa ba. Seda wayan ya kusa tsinkewa ta d'aga bayan sun gaisa yake tambayarta ko sunyi magana da Abba, bata 6oye masa komai ba ta fad'a masa yadda sukayi da Abba yadda ya nuna komin yaya shi bazesa hannu cikin wannan al'amari ba na sosai zuciyan Afzal ya karye.

"Halo Afzal are you still on the line?"

"Yes Ummi" ya amsa cikin wani irin salo ko daga jin muryarsa Ummi tasan zuciyarsa ta mace.

"Don't lose hope Afzal ka cigaba da addu'a nima bazan fasa bawa Abbanka hak'uri ba in shaa Allahu ze sauk'i aje ayi maka bikon Amal kaji? Amal zata dawo a agreka da izinin Allah."

"Ta yaya Ummi? Ko jiya naje na samu Papi amm he's not willing to talk to me in the case of Amal it's worse ko magana bata yimun Ummi I'm slowly dying I can't do without her."

"Ka kwantar da hankalinka Afzal."

"Ta ina hankalin nawa ze kwanta Ummi ina shirin rasa Amal? I'm definitely going to die."

"Subhanallahi wai bazaka bar magana haka ba? Bazaka mutu ma kuma in shaa Allah Amal zata dawo a gareka kar ka gaji da bata da iyayenta hak'uri nima zan taimaka maka zan samu Mami inyi mata magana."

"Thank you Ummi, I know I can always count on you thank you so much Allah sak'a miki."

"Ameen ka kwantar da hankalinka kaji?" Kai ya gyad'a tamkar tana gabansa "Se mun sake waya zan kuma cigaba da bawa Abban ka hak'uri nasan ze sauk'o even though ba yanzu ba amma definitely he'll."

"Thank you so much Ummi" da haka sukayi sallama. Azahar nayi bayan ya idar da sallah yaci abinci ya wuce TH sede yana isa ya tarar da sad news na cewa an riga an sallami su Amal har sun koma gida, tamkar yayi kuka haka yaji dama yaso yayi wa driver'nta magana yazo ya d'aukesu ya kaisu gida, a cewansa gabad'aya se yamma zasu tafi ashe ba haka neba. Be gaji ba washegari da yamma bayan ya taso daga office ko gida be je ba ya zarce gidan su Amal sallama yayi Mami ta amsa sannan yasa kai ya shiga ya nemi gu ya tsuguna. "Bismillah hau kan tabarman mana ka zauna" Papi yace da shi.

"A'a Papi nan ma yayi nagode. Ina yini?"
Gaishesu yayi duka cike da ladabi da biyayya inda suka amsa ba yabo ba fallasa har hakan yaso d'aurewa Afzal kai a tunaninsa gabad'aya zasu koresa yau idan ya shigo sekuma ya tarar da sa6anin hakan.

"Papi ya jikin Amal?" Ya tambaya afterwards.

"Da sauk'i Alhamdulillah."

"Jiya naje asibiti na tarar har an sallameku kun dawo gida dama driver naso turawa ya dawo daku gida."

"Ayyah karka damu mungode."

"Papi bazan gaji da baku hak'uri ba dan Allah kuyi hak'uri ku dawo mun da Amal, nasan nayi kuskure amma kuyi hak'uri ba yadda banyi da Abba ba ya sa baki ya tayani baku hak'uri amma yak'i saboda shi kansa fushi yake dani akan abinda nayi wa Amal, dan Allah kuyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."

"Tabbas d'an Adam ajizi ne amma a gaskiya bazan 6oye maka ba Afzal abinda kayi wa Baby ya ci mun tuwo a kwanu. Ban ta6a tsammanin hakan daga gareka ba Baba na, atunani na ko a bayan raina zaka kula min da Baby ka rik'e min ita amana se gashi tun a ido na ka soma walak'anta ta kodan gani kake bata da uba bata da gata?"

"Wallahi Papi ba haka bane, sanin kanmu ne nan duka Amal tafi k'arfin a walak'anta ta kuyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."

"Tafi k'arfin a walak'anta ta amma harda korinta daga d'akinta Afzal? Saboda ko tsinke bata kai gidan ba?" Mami da tayi shiru tun d'azu ta tsoma baki.

"Mami Wallahi ba don haka bane sharrin shaid'an ne amma in shaa Allahu hakan baze sake faruwa ba."

"Tabbas saboda Amal baza ta sake komawa gidanka ba, haka tace kuma ina biye da ita d'ari bisa d'ari."

"Mami dan Allah kar kiyi magana haka Mami keda ya kamata ki tayani shawo kanta kuma kike cewa haka? Mami kin fi kowa sanin yadda nake son Amal kin fi kowa sanin yadda rashin ta a kusa dani yake babban hatsari da tashin hankali a gareni dan Allah kar kiyi mun haka."

"Ina sane da hakan Afzal, shiyasa kai na ya d'aure na rasa gane dalilin daya sa kayi mata abinda kayi ko dan gani kake bata halacacciyar hanya aka sameta ba dan haka bata da wani k'ima da daraja? Kake ganin kaman alfarma kake mata saboda ka aureta hakane Afzal?? A jinka idan da anyi shawara da ita zata so ta kasance hakan ne? Ko a jinka ni d'in inda nasan sharrin dake jira na a yinin ranan zanje in sami azzalumin mutumin daya cuceni d'in ne?" Ta k'are maganan idonta na cikowa da hawaye, dama rana mey irin ta yau take gudu shiyasa bata goyi bayan Papi ya sanar da Afzal asalin Amal ba tun farko, ai ga irinta nan yanzu tun ba ayi nisa ba ya soma walak'anta ta.

"Subhanallahi Mami dan Allah kar kice haka, Mami please don't ever talk like that ni wallahi in ba da kika d'auko maganan ba ma yanzu gabad'aya na manta da ita wallahi ban ta6a goranta wa Amal akan asalinta ba idan k'arya nake muku ku kira ta ku tambayeta wallahi bazan ta6a yin haka ba please forgive me if you felt that way I'm terribly sorry."

"Ya isa Jameelah yi hak'uri ki koma ciki ni da Afzal zamuyi magana karki d'aga muryanki Baby ta jiyoki yi hak'uri ki koma ciki" batayi musu ba ta mik'e ta shige d'aki inda Papi da Afzal suka cigaba da tattaunawa.

"Shin meya faru Afzal? Naji 6angaren labarin daga gun Amal kaima zan so inji naka 6angaren."

"Papi kunfi kowa sanin yadda nake son Amal, wallahi sharrin abokiyar zamanta ne, ita tayi manipulating mind d'ina ta shiga tsakani na da Amal, Papi komi na saiwa Amal harta tsinke idan na koma gun 'yar uwar nata senaji a bakinta taya zan san wai ta had'a baki ne da 'yar aikin Amal tana kai mata rahoton duk abunda ke gudana a cikin gidan namu?" bayanin komai dalla-dalla yayi wa Papi.

"Tanan kam kayi gaskiya ko ni ne zan fi yarda da Nazeefah akan ita Baby saboda wannan shaida k'wwak'k'wara amma batun shigo da maza cikin gidanka fah? Ka ko san Allah ya haramta auren da zargi ya shiga? Ashe har Allah ze kawo ranan da zaka yi kokonton tarbiyyan dana bawa Amal?"

"Wallahi Papi ni ban ta6a zargin Amal ba, itace bata fahimce ni ba dan ko da 'yar aikinta ta gaya mun cewa sau biyu tana shigo da maza cikin gidan tunani na gabad'aya akan course mates nata ya k'are ba wai kwartaye ba, wallahi sam ni hankali na be kai ga chan ba saboda nasan da wata irin mata nake zaune. Kuma ko da na tashi yi mata magana ce mata nayi kar ta sake shigo mun da coursemates nata cikin gida ba wani abun ba, itace tayi mun mumunar fahimta dan haka nake sake baku hak'uri, kuyi hak'uri."

"Na fahimce ka, amma batun kana ganinta take had'a kayakinta baka hanata ba baka kuma yi mata magana ba ba fa shin hakane?"

"Wallahi Papi ban zata wai shirin yaji takeyi ba, dama tunda muka soma samun matsala na turata d'ayan d'akin kowani safiya takan shigo d'akin namu ta shirya toh ko da naga tana shirya kayakin nata senayi tsammanin ko zata tare chan gabad'aya ne washegari kawai na tashi na tarar bata gidan wallahi ban san lokacinda ta tafi ba."

"Idan har haka ne meyasa baka nemeta ba bayan faruwan hakan? Da ace a ranan kazo bikonta ka deji rantsuwa ko? Wallahil azeem komin ya girman kuskuren da aikata yake zansa maka Amal a mota ka koma da ita gida saboda ka nuna tanada muhimmanci kenan amma bakayi hakan ba Afzal, ni kake tunanin zan kiraka ince maka naga Amal ta taho gida lafiya?" Kai ya kad'a a hankali cike da nadama "Abinda ya 6ata mun rai kenan, banzan da kayi da ita kak'i ka neme ta kak'i ka neme ni ko mahaifiyarta, anan ka nuna baka damu da ita ba, anan ka nuna ita ba kowa bace kasan komin jimawa da dad'ewa zamu sata a mota mu miyar maka da ita mu baka hak'uri tunda de gidanka yafi gidan iyayenta gata ko ba haka ba?"

"Subhanallahi dan Allah Papi kayi hak'uri wallahi ni ba hakan a zuciya na nasan nayi kuskure kamata yayi in kira Amal idan banyi hakan ba kuma in kiraka ko Mami, amma d'an Adam ajizi ne kuyi hak'uri ku gafirceni in shaa Allah hakan baze sake faruwa ba wallahi fushinku a gareni babban tashin hankali ne especially in the case of Mami bana son ku d'au bana son Amal wallahi ina sonta, I really do love her kuma se inda k'arfi na yak'are zan cigaba da baku hak'uri har se Allah ya huci zuk'atan ku."

"Ni ba fushi da kai nake ba Afzal nayi maka hakan ne dan ka gane kuskurenka ka kuma san k'ima da darajar Baby bayan nan kuma don in tabbatar da kalan soyayyar da kakeyi mata kuma na tabbatar da hakan yanzu don idan da wani ne da tuni yayi zuciya kodan irin abinda nida Maminta muka rink'ayi maka a asibiti amma haka baka fasa zuwa ba kullum dukda tokarin da muke maka. Hakan ya nuna mun dagaske ne komi ya faru bisa kuskure ne amma kana son Baby kuma ina alfahari da hakan sosai Afzal tabbas se mey sonka ne ze so wani naka akan Baby kuma na tabbatar da cewa kai masoyin mu ne na hak'ik'a."

"Godiya nake Papi, ba k'aramin farin ciki kalamunka suka sanyani ba kuma hak'urin nan shi zan cigaba da baka da Mami kuyi hak'uri duk sharrin shaid'an ne."

"Shikenan Babana ya wuce Allah yasa mu dace."

"Ameen Papi godiya nake, Allah saka da alkhairi."

"Ameen."

"Shin yanzu zan iya dawo da Amal d'akinta? Dan Allah kar kace a'a Papi, alk'awari na d'auka bazan sake k'untata mata ko yi mata ba dai-dai ba bi iznillahi."

"Na yarda da kai Afzal amma nima ba daga ni bane, bazan iya tilasta wa Baby akan cewa lallai-lallai se ta koma maka ba iyaka inyi k'ok'ari in shawo maka kanta."

"A hakan ma godiya nake Papi, Allah sak'a da alkhairi yabar zumunci."

"Ameen ba komai ana tare ai."

"Kuma dan Allah ka sake bawa Mami hak'uri ni wallahi sam ba hakan a raina."

"Karka damu."

"A kuma gaishe mun Amal da jiki nasan koba don tana bacci ba bazata amince ta fito mu gaisa ba."

"Zan gaisheta in shaa Allah."

"Godiya nake barin koma yamma nayi" hannu ya zira a aljihu ya zaro envelope daya tanadar da 20k aciki ya mik'awa Papi akan a sai wa Amal abinda take buk'ata sede sam Papi yak'i amsa daga k'arshe ajiyewa kawai yayi ya mar sallama ya fice. Mik'ewa Papi yayi ya d'au kud'in dan kai wa Amal a d'aki dukda cewan yasan bacci takeyi. Bud'e k'ofan da yayi ya tarar da ita tsaye dai-dai wajen ta jik'e jak'ab da hawaye. Salati yasa ba shiri bade taji dukkan abubuwan da suka tattauna akai ba? Bade taji labarin asalinta ba?

"Baby?" Ya kirata cikin mucacciyar murya, d'ago kan da tayi zata kallesa kawai ta zame k'asa a sume.
"Baby?" Kumatun ta ya shiga tapping amma ba response. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Jameelah! Jameelah! D'au waya ki kira Afzal beyi nisa ba Baby ta sume."
Da gudu Mami ta fito ta fad'a d'akin Amal inda tasa ihu had'e da k'arasawa da salati "Abba meya faru? Na shiga uku!"

"Ki d'au waya ki kira Afzal" da hanzari ta d'auko wayanta ta sanar da Afzal halin da ake ciki akan ya juyo, yana isowa ya d'au Amal ya kaita mota inda Papi ya zauna a gidan gaba Mami kuma a baya tana rik'e da Amal. Emergency ward akayi da Amal lokacin da suka isa asibitin.

Cikinsu duka uku ba wanda ya iya ya zauna se safa da marwah sukeyi a waiting room d'in, Mami se kuka. "Abba meya sameta?" Ta tambayi Papi.

"Ban sani ba Jameelah tsoro na d'aya Allah yasa bata jiyo abinda muka tauna akai ba, ina zaton taji komai saboda tsaye a bakin k'ofan d'akinta na tarar da ita tana kuka lokacin da na bud'e k'ofar."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mami tasa salati "Yau na shiga uku Abba ya zanyi dan Allah? Mey zancewa Baby yanzu? Shikenan abinda nake gudu ya faru."

"Ya isa haka Jameela ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu Baby zatayi miki kyakkyawan fahimta."
Bada dad'ewa ba likitocin da suka duba Amal suka fito nan su Papi suka duk'ufa suna tambayansu ya jikin nata.

"In shaa Allahu ba wani abu serious bane kawai a bisa fad'in da tayin ne ta kusan fama ciwon nata amma Alhamdulillah achan Allah ya tsayar babu internal bleeding ba komai, ta ma riga ta farfad'o kuna iya shiga ganinta." Hamdala dukansu uku suka sauk'e a wajen sannan suka duk'ufa cikin d'akin, Amal na ganinsu ta shiga zubar da hawaye.

Hak'uri Papi ya shiga bata Mami kam banda hawayen da take zubarwa ta kasa yin komai.

"Kukan ya isa haka Mamana ko ta halal aka sameki ko kuwa ta haram kaf nan bamu damu da hakan ba saboda ba abinda ya isa ya canza matsayin ki a idanun mu da kuma yadda muke sonki a zuk'atan mu Baby, kece Amal nan da muka sani muke kuma so har yanzu."

"No Papi" ta amsasa tana kad'a kai "Bakuwa sona idan da har kuna sona da bazaku min k'aryan asali na ba har na tsawon shekara ashirin da d'aya, I can't believe you and Mami could do this to me."

"Baby dan Allah kar kiyi haka sanin kanki ne ni da Maminki ba wanda muke so sama dake."

"That's not true Papi how could you do this to me? Har ku sanar da Yaya asalina amma ni ku hanani sanin gaskiya? No one deserves to know the truth above of me no one Papi" ta sanar da shi had'e da rushewa da wani kukan.

"Baby dan Allah kiyi hak'uri" Mami tasa baki "Wallahi ni da Papinki mun so sanar dake gaskiya lokacin aurenki amma Afzal ya hana saboda baya son hakan ya jefa ki cikin wani hali."
Mamaki sosai kalamun Mami suka sanya Amal, har Afzal ne yace kar a sanar da ita gaskiya kuma akan wannan dalili? Wow! She's speechless ita kanta tasan batada masoyi sama da shi bayan su Mami shiyasa har yau ta ke mamakin kanta na kasa yafe masa kuskuren da yayi mata. Kai ta d'ago a hankali ta sauk'e idanunta akansa murmushi ya sakar mata kafin tayi sauri ta kawar da kanta.

"Meya faru Mami? For all my life you made me believed inada Abba akan cewa mutuwa ce tayi mana yankan k'auna ashe ba haka bane, ko a mafarki aka cemun keda Papi zaku yi mun k'arya haka bazan ta6a yarda ba, why do you have to lie to me Papi? Why Mami?" Kuka take sosai duk ta basu tausayi a wajen.

"Baby kiyi hak'uri" Papi yace da ita "Bawai mun 6oye miki gaskiya bane don son kai kokuwa makamancin haka munyi hakan ne saboda muna sonki."

"Papi ba haka so yake ba, idan da har kuna so na bazaku ta6a 6oye mun wannan muhimmiyar maganar ba."

"Ya isa kukan haka Mamana ya isa dan Allah karki k'ara wani ciwon ma kanki." Kewayowa tayi kan Mami. "What happened Mami? Meya faru? Na tabbata bazaki cuceni haka kawai ba seda k'wak'k'warar dalili, na tabbata koma waye ne mahaifin nawa shi ya cuceki."

"Tabbas 'yata, sanin kanki ne ba wanda nake so sama da ke a fad'in duniyan nan kuma idan da har Allah na shawara da bawa kafin ya k'addaro masa da k'addara da na hana afkuwan wannan mumunar k'addara, kin fi kowa sanin bazan ta6a sha'awar kawo ki duniyan nan ba uba ba Baby ko dan nayi miki tsari daga tokarin 'yan unguwa da kuma yara 'yan uwanki. Sai dai kaman yadda Allah ya fad'a a Qur'ani _fa inna ma'al usri yusrah_ kowani wuya da musiba na tattare da sauk'i. Acikin ikonsa da sassauci se ya kawo mun sauk'i ta hanyan bani uba mey tausayi kaman Papinki, ubanda ze iya sadaukar da rayuwansa dan farin cikin 'yarsa, uban da yayi playing role na mahaifinki a rashin asalin mahaifinki Baby, ba abinda zance da Papinki sede Allah ya sak'a masa da mafificin alkhairi ya basa gidan Aljannah. Tabbas k'addarata mumunar k'addara ce wanda bazan yi fatan irinsa wa mutum ba koda kuwa mutumin ya kasance mak'iyi na" ta tsaya ta numfasa nan Afzal ya mik'e "I'm sorry let me excuse you" yace dasu duka.

"A'a Afzal" Mami tayi saurin tsayar da shi "Ka riga ka zamo na gida tamkar d'an cikina kuma nakeji da kai, kaman yadda Baby zata ji wannan labari kai ma zanso ka zauna kaji komai" ta buk'acesa sede du da hakan Afzal beji ya cigaba da zama a d'akin ba gani yake kaman ya musu invading privacy.

"Karka ji komai Baba na ka zauna" Papi ya jaddada masa lokacinda k'wayan idonsu ya had'e numfasa yayi sannan ya dawo ya zauna inda Mami ta fara daga inda ta tsaya...




RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨





Miemiebee Novels

Saturday, 25 August 2018
RANA D'AYA!
BY MIEMIEBEE
PAGE 39

_Barkan mu da Sallah darlings, da fatan kowa tayi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ameen.😘 Ina kuke 'yan gida na *MIEMIEBEE NOVELS?* wannan pejin naku ne, thank you for all the love, support and care, Allah cigaba da had'a kawunanmu yabar zumunci, I love y'all fisabilillah❤️💕






_Labari na ya fara ne lokacinda na had'u da Abdallah wanda ake kira da Khaleefah, lokacin ina matakin form 5 (ss2) da karatu a Government Girls College dake garin Askira inda muke da zama a da kafin muka dawo nan. Umma (mahaifiyata) ta kasance mey buri akaina kasancewar ni kad'ai Allah ya azurta ta da, tunda ta haifeni har ta koma ga mahaliccinta ko 6atan wata bata sake ba. A dalilin haka ta d'au burin duniya ta sauk'e akai na, na cewa se mey kud'i ko d'an wane zan aura. Lokacin da samari suka fara lek'o kai suna nemana se Umma ta hanani kula kowanne daga cikinsu acewarta se mey kud'i. Duk yadda Abba yaso ya ganar da ita cewan shi fa miji na gari ake nema ba se mey d'ankaren kud'i kaman yadda take buri ba hakan ya gagara, acewarta taya 'yar shuwa kaman ni zan fara auren d'an talaka. Dan inyi ladabi a gareta se na hak'ura ban kula kowa duk wanda yazo guna da sunan zance se in ce masa ni an riga anyi mun miji ana cikin haka ne na had'u da Khaleefah watarana a hanyana na dawowa daga Islamiyya. Acikin duk manema na ba wanda ya ta6amun ya kuma burgeni ya kwanta mun a rai kaman Khaleefah, duk yadda naso sharesa lokacin da ya fara mun magana hakan ya gagara kawai na tsinci kaina ina mishi fara'a, har gida ya rakani ranan na basa lamba na a karo na farko da ya tambaya. Khaleefah saurayi ne kyakkyawa san kowa k'in wanda ya rasa, lokacin da muka had'u yana matakin part 2 ne a karatu a wata jami'a a chan k'asar waje inda ya samu scholarship. Khaleefah ba d'an babban gida bane amma saurayi ne mey zafin nema saboda tun a lokacin yana d'an sana'a haka, kafin ya koma makaranta soyayya me k'arfi ya shiga tsakanin mu amma ban ta6a nunawa Umma ba sanin bazata ta6a amincewa dashi ba. Ko da yazo ya koma makaranta hakan bey hana mu cigaba da gudanar da soyayyar mu ba, ze kirani mu wuni muna waya nima ranan da nasamu kud'i kuma nakan sa kati in kirasa muyi hira. Ana cikin haka ne d'an Alhj Iro Chairman na Askira ranan da suka zo makarantar mu kawo ziyara ya ganni yace yana sona ni kuwa ban basa fuska ba nace masa ina da wanda nakeso dukda haka be saurareni ba seda yazo har gida ya samu Abba ya sanar da shi k'udirinsa akaina da kuma abinda na fad'a masa na cewa ina da tsayayye. Umma naji ta hau ni da surutu akan bata yarda in kula kowa ba se Faisal d'an Alhj Iro. Niko a lokacin ba wanda na tsana kamansa, daren ranan na kira Khaleefah na irga mai halin da ake ciki inda ya rok'eni da in kwantar da hankalina idan ya dawo next hutu zeyi ma Abbansa magana ya turo magabatansa. Na sosai na tsaya da addu'a dan kar Faisal yayi gaggawan turo magabatansa cikin ikon Allah se har wani hutun ya sake zagayowa Faisal be turo ba. Lokacin ina matakin ss3 da karatu har mun soma rubuta WAEC._
_RANA D'AYA ina cikin waya da Khaleefah Umma ta jiyoni, fisge wayan tayi ta jawoni tsakar gida tun daga d'aki sannan ta shiga duka na tana huci._
_"Ban ce ba ruwanki da wani d'a na miji a gidan nan ba se Faisal?"_

_"Umma dan Allah kiyi hak'uri" na shiga bata hak'uri cikin tsananin kuka._

_"Rufa mun baki maras kunya kawai ce miki akayi ban san mey nake bane da nace se Faisal zaki aura? Ana neman miki sauk'i da jin dad'i anan gaba kina shashashanci."_

_"Umma dan Allah kiyi hak'uri wallahi bana son Ya Faisal ni Ya Khaleefah nakeso."_
_Zazzafan mari ta sauk'e mun a fuska. "Ina fad'a kina fad'a? Mey za'ayi da talaka da talauci idan ba Allah ya d'aura ma mutum ba? In ba rashin wayo irin naki ba ma taya a matsayin ki na 'yar shuwa zaki hau auran talaka? Kin ci sa'a har d'an chairman yace yana sonki amma kike sokancin nan? Naira na kiranki kina cewa baki so? Jakar ina ce ke? Wallahi idan har kinga kin auri Khaleefah yake kowa toh a bayan raina ne. Ma tukun waye shi? D'an gidan waye ne?"_

_"Umma kiyi hak'uri."_

_"Tambaya nake miki waye shi nace?"_

_"D'an gidan Malam Ilu ne."_

_"Wani Malam Ilu? Na bakin titi?"_


DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment