Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

yafe maka ba Ya Rouhi, I can never forgive you for causing me this so much pain" tana kaiwa nan ta bud'e k'ofan ta fice yayinda Afzal yake ta kiran sunanta. Daddy taje ta sama a parlour tace ya kaita gun Mummy. Jiki na rawa ya mik'e suka fice dama so yake yasan inda suke.

Afzal kam kansa ya gama d'aurewa, gabad'aya tausayin Nazeefah yabi ya mamayesa shi kansa yasan bey kyauta mata ba idan har ya saketa. Shi kamsa shaida ne gamey da irin son da take nuna masa. Toh Amal fa? Ya zeyi da ita itama? Haka nan ya fito sam babu walwala tattare da shi yaja su Papi suka wuce gida inda suka duba Amal.
"Mami nida N-" tuna Afzal ya mata kashed'i se tayi shiru.

"Na riga na sani Baby, Afzal ya sanar damu komai" Mami ita sanar da ita. "Allah na tare de ke kinji? Karki tada hankalinki Allah k'ara lafiya."

"Ameen" so take ta ce mata ita zata bisu gida amma dan ganin idon Afzal se tayi shiru, yana ficewa kuwa ta sanar dasu tana son ta bi su.

"Kema kinsan hakan ba me yiwuwa bane Baby. Bamu keda iko akanki ba, baze yiwu kina matarshi mu tafi dake haka kawai ba tare da izininsa ba. Ki k'ara hak'uri nan da d'an lokaci zamu san ajin da muke ciki." Lokaci kad'an su Mami suka k'ara sannan Afzal ya mayar dasu gida. A hanyansa na dawowa ya kira layin Nazeefah sede har ya tsinke bata d'aga ba. Ba kuma wai bata kusa da wayan bane d'agawan ne baza tayi ba.

****
Koda Daddy ya sauk'e ta bakin hotel nasun yak'i tafiya se rok'an ta yake da ta kira Mummy yana son ya ganta yayi mata magana. Itama dake a cike take shi, seta k'i gani take shine silan komai. Da tun farko be tarke 'yar mutane yayi mata ciki ba da duk hakan be faru ba. Ita se yanzu take sake gane dalilin da yasa yayi mata auren wuri ashe tsoro yake kar yadda ya lalata 'yar mutane shima a lalata masa ita. Se gashi da Allah ya tashi kamasa ya kamasa ta inda baya tsammani. Haka nan tak'i k'ira masa Mummy tayi shigewarta ciki. Mami kam koda taji abinda ake ciki bata sa ran Afzal ze d'au Nazeefah akan Amal ba sabida kaman yadda Nazeefah ta gaya haka d'in yake, idan ba ikon Allah ba da wuya ya d'au za6in mahaifinsa akan za6in zuciyarsa. Hak'uri tayita bawa Nazeefah yayinda take sake tsanan Daddy na jefa mata rayuwan 'ya acikin k'unci. Nazeefah yini tayi ranan tana kuka gashi ko Afzal ya kira bata d'agawa.

Cikin dare Afzal ya tashi ya gudanar da raka'a biyu yana mey neman kariya da haske daga Allah. Washegari ya cigaba da kiran Nazeefah amma haka tana gani bazata d'aga ba. Har hotel d'in yaje ya kira Mummy yana rok'anta da ta turo Nazeefah yana son yi mata magana amma haka 'yar nan tak'i fitowa. Ta 6angaren Daddy kuwa shima ya tak'ura wa Afzal da kire-kire yana rok'ansa da ya basa address nasu Mami dan yaje ya bada hak'uri amma Afzal yak'i akan cewa in bada izinin Papi ba baze kaisa gidan ba.

Amal kuwa da ikon Allah take samun waraka, na sosai jikinta ya warware. Tamkar bak'in juna haka Afzal da Amal suka zame wa juna. Kamar yadda bata shiga harkansa shima haka baya shiga nata, in ba wai abinda ya zama dole ba se su yini basuyi ma juna magana ba. Deep down inside their hearts kuwa ba k'aramin missing how open and free they're to each other suke ba. Na kwana biyun nan acikin d'ayan d'akin yake yini se bacci yake kawosa d'akin nasu.

Istikharan kwana uku yayi sannan ya iya ya amince da sakamakon daya samu saidai ya kasa d'aukan mataki a kai bale ya gudanar da abinda ya kamata. Rufe kansa yayi a d'aki yinin ranan yayita kuka tamkar ba d'a na miji ba. Baze iya jure rabuwa da ita, besan ya rayuwarsa zata kasance ba ita a kusa da shi ba. Jin shiru Ummi da yayi mata alk'awarin a yau ze sanar da ita sakamakon da ya samu ta d'au waya ta kirasa domin ji daga garesa. Kaman wanda bade d'au wayan ba ya d'aga a last ring d'in.

"Halo Prince?" Ta soma da cewa.

"Na'am Ummi?"

"Prince ya shiru? Tun d'azun nida Abbanka muke jiran kiranka lafiya dai ko?"

"Lafiya ya jikin Amal?"

"Alhamdulillah da sauk'i."

"Ya naji muryanka k'asa-k'asa haka?"

"Babu."

"Bade kuka kake ba Afzal? Meya faru?"

"Ummi I can't do this" ya sanar da ita tsakaninsa da Allah. "Wallahi bazan iya ba."

"Meya faru? Ka gama istikharan ne?
Hello Afzal?" Ta sake da cewa bayan shirun da yayi. "Afzal?"

"Na'am" ya amsa murya ciki-ciki.

"Ya sakamakon? Wace zaka d'auka? Wace tafi kwanciya maka a rai?"

"Ummi I can't bazan iya sakanta ba she's been through alot bana son yin hakan ya zame kaman na zalunce ta."

"Wacece? Amal ce?

"Ummi ina tausayawa rayuwar da zata fad'a bayan mun rabu bazan iya rabuwa da ita ba."

"Ka sanar dani mana Afzal? Amal ce?"




RANA D'AYA!💖
#RD

Love... King Miemiebee👄✨



Miemiebee Novels

Thursday, 20 September 2018
RANA D'AYA!
BY MIEMIEBEE
PAGE 44



"Ummi no, ba ita bace."

"Then wacece, Nazeefah?"

"Eh Nazeefah, Nazeefah ce Ummi."

"Ni yanzu ka rud'a min kai, Nazeefah ce tafi kwanciya maka a rai kokuwa ita zaka saka?"

"Ummi hankalina yafi kwanciya da Amal."

"Toh Alhamdulillah in shaa Allah hakan shi yafi alkhairi."

"Ummi Nazeefah kuma fah? Shikenan yanzu semu rabu?"

"Toh ya zamuyi Prince? Rabuwa da ita ya zamo dole se inde zaka bijire wa za6in da Allah yayi maka ka saki Amal wanda nima ba barinka zan ba tunda har Allah ya riga yayi ma za6i."

"I know Ummi kuma nima komin yaya bazan ta6a iya rabuwa da Amal ba but Nazeefah kuma fa? Na tabbata baza ta ta6a yafe mun ba, zan iya cewa soyayya na ne kad'ai ya bata wuya a rayuwa. Lokacinda ta soma jin dad'in aurena kuma na kama na k'ara aure nayi mata kishiya. Ban ta6a kyautata mata ba Ummi and now da abunda zan sak'a mata kenan bayan duk wannan wuya da ta sha? I need to treat her right one more time please ki taimakeni Ummi."

"Hak'urin nan de shi zan cigaba da baka Prince, nasan da wuya Nazeefah ta kar6i bak'on lamarin nan da hannu bibbiyu kaman yadda ka fad'a amma as time progresses zata gano cewa za6in Allah shine mafi alkhairi a gareku gabad'aya kuma ba kullum bane muke samun abinda muke so. Don yanzu koda ka bijirewa za6in da Allah yayi ma ka saki Amal kabar Nazeefah, ba alkhairin da ze biyo bayan hakan se ma sharri. Se ka ga ma rabon ya zame mata ajali, kuma zancen wai baka ta6a kyautata wa Nazeefah ba kaima kasan k'arya ne. Duk kulawan da ya kamata ace mace na samu daga gun mijinta kayi mata kuma itama ta sani, so just calm down and do what's right Allah na tare da kai."

"Thank you Ummi" da haka ya katse wayan yayinda kalamun Nazeefah suke ta yi masa yawo akai. Ji yayi gabad'aya baze iya sauwak'e mata ba. Dama seda ta fad'a mishi cewa tasan Amal ze d'auka akanta saboda baya sonta se Amal se gashi kuma Amal d'in ze d'auka yanzu. Sede ba don baya son ta bane kaman yadda ta fad'a se don Amal ce za6in da Allah yayi masa kaman yadda itama Yayi mata lokacin da zata aureshi. Tsoronsa d'aya kar wannan za6i ya sake 6ata tsakanin wannan 'yan uwa. Dan kaman yadda Nazeefah ta sanar da shi ya tabbata muddin idan taji Amal ya bari ya saketa seta tsani Amal fiye da yadda ta tsaneta yanzu. Oh Allah shin ya zeyi yanzu? Idan da ace ze iya rabuwa da dukansu biyu da yayi dan hakan shi zefi wa kowa kwanciyan hankali. Gara duka su rasa sa da ya d'au d'aya yabar d'aya amma yaya ya iya? Zuciyarsa bazata iya jure masa rashinsu duka ba barin ma Amal tasa da yake ganin idan har ya rasata baze iya sake samun mace mey kyawun halatayya irin tata ba. She's just different.

Mik'ewa yayi a hankali yabar d'akin ya nufi nasu inda Amal ke kwance a kan gado se tunani take. Har ya k'arisa kan gadon bataji shigowansa ba. Seda ya kira sunanta tukuna.

"Rania?" Da mamaki cike da tsoro ta mik'e zaune tana kallonsa. Bazata iya tuna when last ya kirata da wannan suna ba, probably tun da ya gano cewa ita da Nazeefah 'yan uwa ne. Ganin bata da niyyan amsasa seya mik'a mata hannunsa da nufin ta sa nata a ciki. Bayan dogon nazarin da tayi daga k'arshe seta mik'a hannunta ta sanya cikin nasa inda ya mik'ar da ita tsaye akan k'afafunta. Na matuk'a kanta ya d'aure yayinda zuciyarta ta shiga bugun tara-tara barin ma da Afzal ya rungumeta a jikinsa.

Shikenan ya tabbata ita zata tafi. Se bata kawai jikinta yake itace ze saka, tasani zamanta da shi ya k'are, ta sani Nazeefah ce tafi kwanciya masa a rai, ta sani Nazeefah ce za6in da Allah yayi mata. Tabbas tayi musu murna sedai kuma tayi k'arya idan tace bata ji zafin hakan ba because she loves him. No matter how hard she tried not to show how terrified she felt takasa saboda yadda take jin zafin rabuwa da shi. Kawai ji tayi hawaye na gangaro mata daga ido dai-dai wannan lokaci Afzal ya d'agota daga jikinsa da k'yar dan yadda ta kankamesa. Cike da mamaki ya tsaya kallon yadda take kuka sannan daga bisani ya shiga share mata hawayen nata "Please don't cry Rania."

"I should really start packing my clothes" ta sanar dashi tana mey hana k'wayoyin idanunta had'uwa da nasa. "I'm really happy for you two Yaya, Allah ya baku zaman lafiya mey d'aurewa."

"Mey kike cewa haka Rania? Zaman lafiya tsakani na da waye?"

"Da Nazeefah."

Murmushi ya saki kad'an "Meyasa kika ce haka? Why not you?"

"Saboda bani ce za6in da Allah yayi maka ba Yaya. I know I'll be the one to leave and even though nima hakan ne ze fiye mun kwanciyan hankali I just can't deny the fact that I still love you so very much and I'll miss you so damn much."

"But you don't have to miss me Rania because you're not going anywhere, this is your home anan kuma zaki cigaba da zama ba inda zaki."

"No ba sekayi hakan ba Yaya, zanje in samu Mami a gida, chan d'in ze fiye mun kwanciyan hankali yaso ko haya ne se kasa a nan d'in." Dariya sosai ta basa wanda ya kasa dannewa yayinda ta tsaya kallonsa cike da mamaki da takaici. Mey yake nufi da hakan?

"Rania listen to me, ba inda zakije nan ne gidanki kuma d'akin mijinki okay?"

"D'akin mijina? Nazeefah kuma fa? Karka bijire wa za6in Allah saboda son zuciya Yaya. Idan kuma tsoron abinda Papi da Mami zasuce kake then ka kwantar da hankalinka kasani duk zasuyi maka kyakkyawar fahimta kaman yadda nima nayi maka. We all know you love me Yaya, please don't bother yourself."

"Tsaya, kafin muyi aure mey kikayi? Kinyi Istikhara right?" Kai ta gyad'a masa a hankali cike da rashin fahimta sannan ya cigaba "Kuma bayan da kika gudanar se waye Allah ya za6a miki?"

"Kai Yaya" ta amsa a takaice.

"Kina ganin it is possible ace ni kuma nayi Istikharan yanzu se wata ta daban ta zame za6in da Allah zeyi mun bayan ke kuma ni Ya za6a miki?"

"But Yaya-"

"Ki sani Rania ko sau dubu mutum yayi Istikhara za6in Allah d'aya ne sedai idan shi yaso bijire wa hakan. Kaman yadda kikayi naki istikharan Allah ya za6a maki ni, nima haka ya za6a min ke yanzu. We two are meant to be Rania in shaa Allahu mutuwa ce kad'ai zata shiga tsakani na dake. Rania I love you so much kuma Allah kad'ai ne sheda game da irin son da nake yi miki, shi kad'ai yasan idan bake bazan iya rayuwa ba, shi kad'ai yasan muddin na rasaki bazan ta6a iya samun kamilar mace mey kyawawan d'abi'u da halatayya irin naki ba shiyasa ya za6an min ke ya sake bani daman da zan soki in kuma kula dake har ila k'arshen rayuwa na. I can't do without you Rania and I can't ask God for more da ya sake bani daman kasancewa mijinki, forgive me for all the times I've wronged you Rania, I'm terribly sorry please forgive me."

Kuka Amal ke sosai yayinda ta kasa amincewa da abubuwan daya fad'a mata. Se gani take kaman a mafarki komai ke faruwa tabbas itama bazata iya rayuwa idan ba shi ba. Gani take kaman duk yadda yake jin yana sonta ita tafi sonsa, don dai kawai ita bata nunawa ne. Daga k'arshe kuma bazata iya yima Allah godiya ba da ya sake bata daman kasancewa matarsa, sai dai kuma bazata iya duba irin rayuwan k'unci da tashin hankalin da Nazeefah zata fad'a ba a rashin Afzal. Se gani kawai take inda itace Afzal yace ze sauwak'e wa. Tasan duk kalan rashin tawakkalinta tana bayan Nazeefah. Tasan Nazeefah na iya yin k'aramin hauka akan wannan dalili, she knows this is not going to be easy on her shiyasa take tausaya mata sosai.

"Rania?" Ya kirata bayan shirun da tayi, jikinsa kawai ta fad' yayinda ta shiga yin kuka na sosai. "Bakayi mun komai ba Yaya don haka ka daina tambaya na yafiya I love you so very much." Ba k'aramin dad'i kalamanta suka sanyasa ba, matseta tsam ya sakeyi a jikinsa tamkar ana shirin k'watan masa ita yayinda wani irin sonta yake sake shiga zuciyansa. Sun dad'e a haka sannan daga bisani ya janyeta daga jikinsa sede har anan hawaye Amal ke.

"Please don't cry Rania."

"I wish I could stop Ya Omri."

"But there's no need to."

"There's every need to cry Ya Omri."

"Saboda ban barki kin tafi gida kaman yadda kikeso ba kike wannan kuka Rania? Saboda Allah ya za6an min ke? Ashe ba haka kika so ba, I thought you said you love me" Kai ta gyad'a mishi take tana murmushin takaici.

"Then meyasa kike kukan? A tunani na this is supposed to be the most happiest moment for us both."

"Yes it is Yaya kuma hawayen nan da kake gani, hawayen farin ciki ne gani nake kaman a mafarki komai ke faruwa, I can't believe that we're still going to remain married to each other after hope has been gone."

"I feel thesame way Rania, but tun farko tun kafin in gudanar da Istikharan nan nasan komin yaya akayi ni dake bamu rabuwa."

"Ko meyasa kace haka?" Tayi saurin tambayansa cike da mamaki.

"Saboda Istikharan da kikayi kafin mukayi aure Rania, idan da har ace akwai sharri a auran mu da Allah baze za6a miki ni akan Abdul daya kasance masoyinki ba. Idan har na rabu dake kinga kenan babu amfanin istikharan da kikayi. Ko ce miki akayi shi istikhara temporal decision ne na d'an lokaci? Hankali na ya tashi ne gabad'aya saboda Nazeefah. Ina matuk'an tausayawa halin da zata shiga idan har ta gano cewa I chose you over her, shiyasa nayi coming up da plan na cewa zanyi Istikhara kinga idan har nayi ita da iyayenta bazasuyi mun mumunar fahimta ba, zasuga za6in Allah nabi ba wai na zuciya na ba. Sedai kuma yanzu bayan dana gudanar da hakan nakega still Nazeefah bazata amince ta kar6i wannan bak'on lamarin da hannu bibbiyu ba. Nasan komin tayaya bazata ta6a fahimtar cewa Allah ne ya had'ani dake ba, bazata ta6a gane cewa ba komi mutum yake so a duniyan nan yake samu ba, gani take komai laifinki ne Rania and that is what hurts me the more knowing who you really are. Bana son a sanadin hakan ta sake tsanarki, ita gani take komai laifinki ne, ke kika janyo bayan ba haka bane. I wish Nazeefah could see this kind and selfless side of you. Har yau kalaman ki na yinin ranan da na sanar dake cewa Nazefah k'anwarki ce suna kaina. Har yau na kasa mancewa dasu kuma bazan ta6a mancewa da su ba. Yadda kika cire son kai kikace kin yafe ni wa Nazeefah even though kina so na bawai bakiya sona ba se don cewa da Annabi yayi "La yu'minu ahadukum hatta yuhibbu li akhihi ma yuhibbu li nafsihi" [imanin d'ayanku baya cika har seya so wa d'an uwansa abinda ya so wa kansa] I get that you love me but you're willing to let your sister have me and ba kowa keda irin imanin nan naki ba Rania ko ni nan bazan iya aikata abinda kikayi ba ranan saboda haka kuma naji respect naki ya k'aru a idona yayinda sonki ya sake k'aruwa a zuciya na."

Murmushin jin dad'i ta sakar masa tana mey share hawayenta "Ka sani ko da nace maka hawayen nan na jin dad'i ne k'arya nayi because zuciyata tausayawa Nazeefah take, I can't imagine the kind of hell she'll go through Yaya don haka har nakejin kaman mu hak'ura da juna sedai kuma bazamu iya yin jayayya da za6in Allah ba."

"Hakane Rania, let just pray for her in shaa Allah as time progresses zata fahimci komai ta kuma nemi gafararki ayi zaman lafiya gabad'aya."

"Da kuwa ba abinda zefi mun hakan farin ciki da jin dad'i Yaya. Inspite of how Nazeefah disperses me wallahi I still love her kuma zan cigaba da sonta ina yi mata uzuri har zuwa lokacinda zata gane gaskiya."

"Allah yayi miki albarka Amal ya baki yaran da zasu kula dake ranan da buk'atan hakan ya taso Rania, I'll forever love, cherish and adore you."

"Ameen Ya Omri I love you too."

"Let's eat out ai zaki iya fita ko?"

"Why not? Bari in shirya."

***
Washegari...

Dai-dai gaban gidansu Nazeefah yayi parking sannan ya zaro wayansa ya kira Daddy a karo na farko ya d'aga.

"Halo Afzal ka iso ne?"

"Eh Daddy."

"Toh bismillah mana ka shigo." Harga Allah beyi niyan shiga ciki ba amma yaya ya iya? Gyara packing nasa yayi ya k'arisa ciki inda ya samesa a parlour ya gaishesa. Bayan sun gaisa ya zaro takardan daya ninke daga aljihunsa ya mik'awa Daddy "Kaman yadda nayi muku alk'awari cewa zanyi Istikhara, duk kuma wacce Allah ya za6ar mun ita zan d'au in sauwak'e wa d'ayan. Toh game da sakamakon dana samu bayan na gudanar da Istikharan na yanke wannan hukunci ba don son kai ko son zuciya ko makamancin haka ba, da fatan kai da iyalanka zakuyi mun kyakkyawar fahimta. Ga takarda nan na sakin Nazeefah, dafatan ze isa gareta zaka kuma bata hak'uri a madadi na ni zan wuce."

"Dakata Afzal kar kayi saurin tafiya. Kayi hak'uri ka bani dama in baka hak'uri na jefaka da iyalinka cikin wannan rud'ani da tashin hankali da nayi. Kuma ka sani wannan hukunci daka yanke shine dai-dai koda ma ace bakayi istikhara ba bazan bari ka saki Amal ba saboda abinda nayi mata da mahaifiyarta kad'ai ya ishesu takaici da jarabawa. Dole nima in gir6e abinda na shuk'a. Da fari na d'au zan iya yi wa Allah wayo, na d'au idan har na aurar da Nazeefah shikenan bani da wani tsoro kuma ashe ba haka abun yake ba, ashe ita zina bashi ce idan har ka cita dole komin ta yaya ne ka biya. Kuma muddin ba a kaina ze ramawa Jameela abinda nayi mata ba dole se akan wanda nakeso. Dukda cewan Amal da Nazeefah 'ya'yana ne amma kaman yadda zanfi jin zafin sakin nan akan Nazeefah ba haka zanji ba idan da akan Amal ne saboda babu shak'uwan nan na uba da 'ya a tsakani na da ita. Allah ya za6an maka Amal ne saboda ya koya mun da 'yata darasi kuma saboda itama koda sau d'aya ne taji dad'in rayuwa. Ka sani wannan hukunci da ka yanke dai-dai ne kuma zanyi k'ok'ari in fahimtar da iyalai na, Allah ya baku zaman lafiya mey d'aurewa da Amal ya albarkaci rayuwanku in shaa Allah zan isar wa Nazeefah sak'onka."

"Nagode sosai Daddy."

"Ba komai, se kuma batun Jameela bazan gaji da rok'an kanka ba da kayi mun kwatance injeni gidansu in nemi tubarsu, idan ban samu sun yafe mun ba alhak'insu ya cigaba da bi na kenan, ka tausaya mun da iyalai na please Afzal."

"In shaa Allah zanyi ma Papi magana karka damu."

"Toh nagode sena ji daga gareka."

"Ba komai ni zan wuce" ya fad'a had'e da mik'ewa "Ka gaishe da Amal ina da niyyan shigowa inzo in dubata nima in nemi tubarta amma ina son in d'an bata lokaci saboda nasan yadda zata ji ta tsaneni yanzu."

"Zataji Daddy se anjima" yana kaiwa nan ya fice ya koma office har a yau idan ya gwada kiran layin Nazeefah bata d'agawa. Ba komai yasa yake son ya kirata ba se don so da yake ya bata hak'uri, baya son taga kaman baya sonta ne, har yau har gobe ze cigaba da sonta saboda akwai gur6in da ita kad'ai ce ta mamaye a zuciyansa. Ita ce macen da ya fara sani a rayuwansa, itace macen da ya fara sumbata itace macen da ya fara sharing wani abu nashi da ita. Shin har ze iya mancewa da ita a rayuwansa? He don't think so.

****
Daddy be samu ya kaiwa Nazeefah takardan nata a ranan ba se a washegari. Bayan ya dawo daga sallan Azahar ya d'au wayansa ya kira Mummy sedai kaman yadda ta saba ignoring call nasa hakan ma tayi yau don haka ya tura mata sak'o.

_Hjy Surayya kiyi hak'uri ki d'au wayan nan muyi magana. This is not about me it's about our daughter Nazeefah, thank you._
Sak'on ya shiga bada dad'ewa ba Mummy ta karanta se contemplating take ta kirasa taji lafiya ne ko ta bari. Chan k'arshe de ta kira wanda ya d'aga a karo na farko. Bata basa daman yin magana ba tace, "Meya samu Nazeefan?"

"Hjy Surayya wannan ba maganan waya bane gani nan tahowa yanzu."

"Karka 6ata lokacinka bana nan na fita."

"We both know k'arya kikeyi zanzo yanzu please" bata sake ce meshi komai ba ta katse wayan. Cikin mintuna da basu kai ashirin da biyar ba sega shi nan ya iso. Waya yayi mata akan ta fito nan da nan ta sanya hijabinta ta fice.

Ba yadda Daddy beyi ba da su k'arisa koda reception ne su zauna suyi magana tak'i, tace ita idan har baze fad'i abinda yake tafe dashi ba zata koma ciki. Toh suje cikin mota su zauna nan ma tak'i. Yasan sam bey kyauta mata ba amma ba wai yayi hakan dan ya raina ta bane ko makamancin hakan, shi tsoron sanar da ita yake gudun kada ta gujesa kaman yadda takeyi yanzu.

Hannu yasa a aljihunsa ya fito da takardan had'e da mik'a mata.

"Mey wannan?" ta tambaya ba tare da nuna yunk'urin amsa ba.

"Kedai bud'e ki gani." Kaman wacce bazata kar6a ba ta amsa ta bud'e had'e da karancewa.

_A ranan Laraba, goma ga watan Juneru shekara dubu biyu da goma sha takwas na saki matata Nazeefah, saki d'aya, biyu, uku saboda haramta mana zama da shari'a tayi a sanadin ta na kasancewa 'yar uwar matata Amal na jini._


DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment