Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

sirri yake nufin tana yad'awa idan akwai mutumi d'ayan da ta mar maganan aurenta itace Maamah kuma ta yarda da Maamah tasan Maamah baza ta ta6a ci mata amana ba. Kuka tayita sha wajen har zuwa lokacinda Safiyya ta gama abincin Afzal ta ajiye masa kan dining gun Amal ta k'arisa ta durk'usa.

"Aunty kiyi hak'uri dan Allah ga abincin Uncle yayi."

"Kije kice mishi ya fito."

"Da kaina?" Kai zalla ta gyad'a mata nan ta wuce bayan tayi mar sallama ta sanar dashi ta gama godiya yayi mata sannan ta dawo kan Amal tana cigaba da bata hak'uri kaman dagaske.

"Kije d'akinki Safiyya ba komai" haka Afzal yazo ya tarar da ita zaune a wajen, ko kallonta beyi ba ya k'arisa dining. Da k'yar ta tattara kanta ta koma d'aki Qur'ani kawai ta d'auka ta shiga karancewa shi kad'ai take jin ze iya rage mata wannan k'unci da bak'in cikin da takeji. Bayan Afzal ya gama cin abinci yazo shiga d'akin yaji sautin karatunta na tashi, na d'an lokaci ya tsaya ya saurareta sannan ya koma parlourn ya cigaba da zama be sake kewayowa d'akin ba se da ya tabbata tayi bacci wajajen sha d'aya kenan. Tsince akan gado tana bacci ya tarar da ita da alama karatu take bacci ne ya d'auketa don ga handouts nata baje a gabanta, Jallabiyan jikinsa ya tu6e sannan ya tattare handouts d'in ya ajiye a gefe ya gyara mata kwanciyan nata ya haura ya kwanta daga chan gefe shima had'e da kashe musu wuta.

Haka ya cigaba da d'aga mata kai yana shareta, washegari Amal tayi kuka har ta godewa Allah test da ta rubutan ma dukda cewan tayi karatu batazo ta gane mey ta rubuta ba saboda gabad'aya ba hankalinta a jikinta.

"Amal kiyi hak'uri haka kukan nan ba shida amfani" fuskanta daya kumbura tim ta d'ago daga kan benchi tana share hawayenta "Maamah a rayuwa ba abinda na tsana kuma yafi k'ona mun rai kaman banyi abu ba ace nayi fisabilillahi ko ke na ta6a sanar dake sirrin gida na ne in ba wannan karan da matsaloli suka yi mun yawa ba?" Kai Maamah ta kad'a mata a hankali cike da tausayi "Amma cemin yayi wai ba aiki na se buga waya wa mutane ina sanar dasu sirrin gida na harda wai ya d'au ina da hankali ashe babu duk na munafirci ne Yaya fa Maamah, Yaya yake kwatantani da wannan munanan kalamu" ta sake rushewa da wani kukan.

"Amal ki kira Mami ki sanar da ita kawai taya Ya Afzal ze miki haka ina laifin ma ya sanar dake laifin da kika yin amma haka kawai ya barki acikin duhu ai ba yi bane hakan."

"So kike ya gama tsanata idan na sanar da su Mami? Ban kira kowa bana yace ina kiran waya ina yad'a sirrin gida na bale har in kira Mami? Hmm ashe ina tona kabari na da kaina kenan."

"Toh ya zakiyi Amal? Ni anya kuwa ba kishiyarki bace take neman had'a kanki da Ya Afzal?"

"Nazeefah wai?"

"Sosai ma kiyi tunani mana mey yake nufi da yace miki ita take k'aryar? Nazeefah yake nufi."

"Da wuya idan itace I trust Nazeefah bata da wani mugun hali kuma kinga ita bama zuwa gida na take ba bale ace taga wani abun taje tayi mai gulma."

"Don't get too confident trusting her Amal wallahi halin mutum se Allah idan ba haka ba waze shiga tsakaninki da Ya Afzal haka?"

"Maamah ban sani ba amma zan cigaba da addu'a har se idan Allah ya amsa kuka na."

"Toh Allah taimakeki ya shige miki gaba Amal shi kuma Ya Afzal Allah sa ya gano gaskiya ya sani cewa idan mutum yayi laifi confronting nasa ake bawai a rik'e shi a zuci ana k'untata mai ba."

**
Washegari kasancewar Amal tana iya kai har yanma a school ta yi girkin rananta tun da safe kafin ta fita. Abinda Safiyya zatayi kawai tayi wa Afzal microwaving ne idan ya dawo daga office that is idan ze ci ma kenan tunda yanzu ya k'aura daga cin girkinta. Tun k'arfe sha biyu ya dawo gida yana shiga ciki yaga cup da snacks haka akan table sekace anyi bak'o sallama yayi Safiyya ta fito tayi mai sannu da zuwa.

"Auntinki na gida ne?"

"A'a ta fita school."

"Wannan fah?" Ya nuna cup d'in "Kinyi bak'uwa ne?"

"A'a Aunty ne ta shigo bada dad'ewa ba ita da wani."

"Excuse me?!" Yayi exclaiming had'e da zaro idanunsa waje.

"Yanzu suka bar nan."

"Ita da wa?"

"Ita da wani na miji suka shigo ta d'au wasu takardu suka d'an zauna se suka sake fita tace tayi mantuwa ne."

"Amal ta kawo na miji gidan nan?" Sam ya kasa amincewa da hakan.

"Ni na d'au ma ko d'an uwanta ne yadda suka zauna a kujera d'aya."

"A kujera d'aya!?" Ya sake tambaya idanun nan kaman zasu fad'o a k'asa dan mamaki. Dan yadda zuciyarsa ta shiga k'ona ko k'ala be sake cewa da Safiyyan ba take idanunsa suka kad'a sukayi ja. Cikin wani irin taku ya k'arisa d'akin nasu kawai ji Safiyya tayi ya buga k'ofan wane yana neman 6allesa, d'aki ta koma jiki na rawa ta kira Nazeefah.

"Aunty na aikata, kuma wallahi ya amince."

"Kai haba!"

"Bakiga yadda yake ta nishi ba kaman zaki."

"Kinyi dai-dai ai in shaa Allahu kwanan Amal a gidan nan ya kusa k'arewa aikinki na kyau."

Amal baiwar Allah da tun fitanta k'arfe sha d'aya se biyar ta dawo bata san meyake jirarta ba a gida. A galabaice driver ya dawo da ita tana shiga parlour ta tarar da Afzal zaune kan kujera ko d'aga ido beyi ba bale yasan mutum ya shigo gidan se harkan gabansa kawai yake itama bata yi mai magana ba sanin ko tayi ba amsata zeyi ba. Da mamaki ya bita da kallo wato ma ko magana baza tayi masa ba lallai rainin har ya kai haka? Bayan ta kawo masa k'ato gida ta dawo kuma bazata iya ce mai sannu ba, wuyanta ya kai yanka. Da abinda zata sak'a masa kenan duk kalan halaccin da yayi mata a rayuwa? Wajajen goma ya koma d'akin kwance akan gado ya tarar da ita a galabaice.

"Kibar min d'akin nan kije ki kwana wani wajen" yace da ita zallah.

Da mamaki ta tsaya kallonsa ashe Allah ze kawo ranan da zeyi mata gori akan abubuwan da yayi mata a rayuwa? Ko k'ala bata ce da shi ba ta d'au pillonta da waya ta bar masa d'akin bayanta yabi yayi locking k'ofar sannan ya dawo ya kwanta yana mamakin wannan sabon d'abi'artan wato ma tsabagen tasan halinta ta kuma san mey takeyi shiyasa ko a bakin zaninta bale ta tambayesa dalilin da ze hanata kwana masa a d'aki ba. Toh ta cigaba.

Ta d'ayan fannin kuka Amal ta kwana tana yi bata jin zata iya da wannan walak'anci mey yayi zafi da ze koreta daga d'aki? Saboda bata kawo ko tsinke gidan ba? Da k'yar bacci yazo ya d'auketa. Kasancewar tana da morning lectures washegari bayan Asuba tayi wanka sannan ta wuce d'akin nasu dan d'auko kayan da zata sa sallama tayi jin shiru seta bud'e k'ofan amma bata gansa a ciki ba don haka kawai ta yanke hukuncin yana bayi ne. Wajen wardrobe ta nufa ta shiga fiddo da kayan da zata sa tana cikin hakan Afzal ya fito daga bayi ko juyawa ta kallesa batayi ba harkan gabanta ta cigaba da yi daga wajen wardrobe ta k'arisa gun mirror ta tattara man shafawanta da turare da sauran abubuwan da zata buk'ata ta fice. Binta da kallo yayi shima bece da ita ko k'ala ba. Tana gama shirinta tayi ma driver magana ko tambayan Afzal kud'in makaranta batayi ba sallama kawai tayiwa Safiyya ta fice. Yau ma kaman jiya Afzal ya riga Amal dawowa and thesame thing cup ya tarar a kan centre table da plate na abinci daya tambayi Safiyya still ta basa amsa irin na jiya akan Amal ce ta shigo da wani basu jima da tafiya ba. Na matuk'a ransa ya 6aci yau kam baya jin ze iya d'aukan rashin hankalin nata abun ya ishesa zama yayi a parlourn yana jiran dawowanta chan bada dad'ewa ba ta iso yau ma a galabaice. Kanta ta sunkuyar lokacinda ta shiga parlourn har ta kai ga wucesa ya kira sunanta chak ta tsaya had'e da kewayowa.

"Wa kika kawo mun gidan d'azu?"

"Mey kake fad'i Yaya?

"I'm not repeating myself Amal wa kika kawo mun gida d'azu?"

"Wa zan shigo maka dashi gida Yaya? A iya zama na da kai na ta6a shigo maka da na miji gidan nan ne? Why don't you believe me Yaya? Na d'au ko da an fad'a maka hakan bazaka amince ba saboda a tunani na kafi kowa sanin hali na, a tunani na kafi kowa sanin abinda zan iya aikatawa da abinda bazan iya ba I'm so disappointed with you Yaya" ta tsaya ta numfasa yayinda hawaye yake ciko mata a ido "Ina soyayyar da kake ikirarin kana mun? Ashe za a iya fad'a maka magana akaina ka hau ka zauna akai ba tare da kayi bincike akai ba?"

"Stop acting like you're the Amal I used to know saboda gabad'aya kin canza, I can't trust you anymore Amal yau komin ya girman laifi yake aka ce mun kin aikata zan amince saboda I've lost my trust in you since the day kika fara d'iban sirrin gidan ki kina yad'a wa jama'a."

"Allah ma shaida ne ban ta6a kwasan abinda kake mun a gidan nan na fad'awa kowa ba not even Mami" ta amsa tana share hawayenta.

"Ki bud'e kunnenki ki saurareni da kyau ban yafe ba idan kika sake kawo mun wani k'ato cikin gidan nan."

"Yaya please idan wani abun nayi maka ka fito fili ka fad'a mun amma ka daina cemun nayi abinda ban aikata ba, yaushe na shigo gidan nan tun fita na bale har in shigo da wani?"

"Da ace ban shigo na tarar da ragowan snacks da drink da kikayi serving nasa bane se ki gaya mun maganan banza."

"Drink? Wallahi ni ban kawo wani gidan nan ba ka kira driver ka tambayeshi ko ya dawo dani gida tun fita na da safe in ba yanzu ba."

"You're not as smart as you think you're Amal and ki cigaba."

"See Yaya idan gajiya dani ne kayi kawai ka fad'a mun I'll understand you it's too early for this, taya banyi abu ba ina ji ina gani zaka na mun sharri da fari kace ina kire-kiren waya ina baza sirrin gida na a waje yanzu kuma zargi na ka fara? Har kana tunanin kai na ya waye da zan fara kawo maka maza a gida? Wallahi a da koda wasa aka cemun zaka yi mun abinda kakeyi mun yanzu bazan amince ba amma ka cigaba dama nasani dole wataran zaka goranta mun tun da har ka iya ka koreni daga d'akinka jiya." Bata jira jin mey zece ba ta wuce d'akin data koma a guje. Kuka ta shigayi daga haka har ta fara yin amai, bata tsaya ba seda ta harar da abincin cikinta tas har jiri na neman d'ibanta. Da rarrafe ta k'arisa d'akin ta kwanta ahaka har wahalallen bacci ya d'auketa. Next da ta tashi Safiyya ke ce mata Afzal ya riga ya tafi kai kawai ta gyad'a mata har ta tashi zata tafi seta kira ta.

"Na'am Aunty?"

"Mey kika cewa Ya Afzal jiya da bana gida?"

"Game da mey Aunty?"

"Kinsan mey nake nufi ai."

"Wallahi ban fahimce ki ba dan ni magana ma be had'ani da Uncle ba."

"Waya ce mishi na shigo da na miji gidan nan?"

"Na miji? Wallahi bani bace Aunty dan meyasa zan miki sharri? Wallahi bani bace."

"Shikenan tashi ki tafi." Chan bayan sallan Isha ta fito kitchen dan had'a custards ta sha sanadin wani irin yunwan da ya dameta. Tana tsaye a kitchen tana jiran ruwan ya tafasa Safiyya ta shigo zata dafa indomie.

"Ki d'au k'wai biyu ki soya" tace da ita.

"Toh Aunty nagode" jiki na rawa ta bud'e fride d'in ko ya akayi kawai d'aya ya ku6uce daga hannunta ya fad'i ya fashe.

"Subhanallahi! Ya akayi haka Safiyya?" Amal tayi saurin tambaya tana neman toshe hancinta.

"Aunty dan Allah kiyi hak'uri wallahi ban sa ya akayi ba bari in goge da wuri ina tissue" kafin ace mey k'arnin ya mamaye kitchen d'in gabad'aya gas d'in Amal ta kashe da wuri sannan ta juya sink ta shiga kwararo amai, amai tayita yi wane zata harar da hanjinta yayinda Safiyya ke bata hak'uri. Bakinta ta wanke Safiyya ta taimaka ta jata izuwa d'aki.

"Sannu Aunty kina buk'atan wani abun?" Kakkarwa take sosai ta kad'a mata kai "Ki had'a mun black tea kawai."

"Toh ina zuwa" nan da nan ta had'o ta kawo mata.

"Shikenan kina iya tafiya."

"Ba wani abinda kike buk'ata?"

"Babu kar ki damu."

"Allah sawwak'e."
Da k'yar Amal ta samu ta sha rabin tea d'in taji ta k'oshi zazza6i ne ya rufeta a lokaci guda ko makaranta ta kasa fita washegari ga shi jikin nata ya d'au zafi. Maamah ce da ta jita shiru ta kira dan tambayan ko lafiya.

"Wallahi zazza6i Maamah kaman zan mutu."

"Allah sarki shafakillahu habibty Allah baki lafiya."

"Ameen nagode."

"Na yi miki assignment d'in na mana submitting."

"Allah sarki Maamah kaman kinsan ina ta bi a raina wallahi nagode sosai Allah ya bar zumunci."

"Ameen munyi waya da Ya Abdul ma yace in gaisheki."

"Allah sarki ina amsawa."

"Ya Afzal fah? Be kaiki asibiti bane?"

"Ya koma gun Nazeefah tun jiya ai."

"Baki kira kin sanar da shi bakida lafiya bane?"

"Ko nayi mey zai mun? Kin manta ba wanda ya tsana kaman ni ne a duniyan nan yanzu?"

"Allah sarki Amal do you need anything? Wallahi Ya Afzal bai kyautawa."

"Ba komai Nazeefah wataran se labari nagode" ta amsa hawaye na tsiyaya mata daga ido.

"Gobe zan shigo in duba ki in shaa Allah ki huta kinji? I love you."

"I love you too sekinzo."

****
Se wajajen sha biyu Amal ta samu k'arfin jiki a gida ta yini ranan ba inda taje, chan Maghrib nayi kuma zazza6in ya sake tashi ga amai idan ta fara kaman zata harar da kayan cikinta sosai Safiyya ta tausaya mata take kuma k'ok'arin kula da ita. Har anan Afzal be san mey ake ciki ba kaman yadda be kira Amal ba haka itama bata kirasa ta sanar da shi batun rashin lafiyarta ba ko Mami bata kira ba.

Bayan Safiyya ta tattare plate d'in ta fita dashi Amal ta janyo wayanta ta shiga calender tana counting yau kwana uku kenan da missing period nata anya kuwa lafiya? Kode? Subhanallahi it can't be possible Allah yasa ba abinda take zargi bane inde haka ne ya zamo dole gobe taje asibiti ta tabbatar da koma mey amma fatanta Allah yasa ba abinda take zargi bane. Se sha d'aya ta fita washegari bayan da zazza6in nata yad'an sauk'a. A wani private clinic Driver ya sauk'eta inda ta k'arasa ta bud'e file tukun ta shiga ganin doctor tayi mata bayanin yadda takeji. Murmushi likitan tayi mata tace "Amma Amarya ce ke ko?" Kai Amal ta gyad'a mata cike da rashin fahimta.

"Shiyasa ai."

"Ban fahimce ki ba Dr Sadiya."

"Congratulations you're pregnant Mrs Abdallah."

"Pregnant?" Amal ta nanata cike da k'in yarda "Taya bakiyi mun gwaji ba bakiyi komi ba kice ina da ciki?" Murmushi ta saki kad'an "ni da aiki na kuma Mrs Abdallah ai ko ban miki gwaji ba idanunki kad'ai ma shaida ce kina d'auke da juna biyu."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" taji Amal ta furta.

"Lafiya?" Tayi saurin tambaya.

"Dan Allah kiyi mun tests d'in tukuna I can't be pregnant at least not when babu jituwa tsakani na da mijina, I can't be pregnant Dr please do something" ta fad'a cike da tashin hankali.

"Subhanallahi please calm down, taya zaki k'i kyauta daga Allah haka Mrs Abdallah?"

"Ba haka bane Dr matsaloli sunyi mun yawa and cikin nan will only add to it please help me."

"That's where you're wrong wannan ciki sede ya warware miki duk wani matsalan da keda mijinki kuke fuskanta, ki yarda dani mijinki na jin wannan news ze sauk'o daga kowani irin temper yake kai, kede ki godewa Allah kawai" ta sanar da ita ta na wani rubutu jikin wani paper "Ga wannan kije next room zasu yi miki scanning mu gano sati nawa ne duk abinda akwai zasu sanar dake kafin ki fara zuwa pre natals naki, congratulations once more." Jiki na k'yarma Amal ta amshi paper'n "Don't be afraid Mrs Abdallah in shaa Allahu juna biyun nan shi ze zame sanadin shirya tsakaninki da mijinki."

"Toh nagode Dr."

"Sey kuma ga wannan magunan basuda k'arfi in shaa Allah baza suyi komi wa cikin ba, zasu rage yawan jin jiri da kuma yawan yin amai da zazza6in duka, Allah inganta."

"Ameen Dr nagode se anjima." Next room ta shiga inda akayi mata scanning cikin. Kwata-kwata ma cikin sati uku ne sede maimakon Amal tayi murna tun dawowanta gida take aikin kuka gabad'aya ta rasa meke mata dad'i bata ma san wa zata fara kira ta sanar da shi wannan labari ba abu d'aya da ta sani shine Afzal ne mutumi na k'arshe da zata kira ta sanar da shi. Tunda ya fara zarginta yanzu ai da k'yar ma idan ze amince cikinsa ne a jikinta, ya zatayi? Wannan musiba da mey yayi kama??





RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨
[13/08, 09:39] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣

💦💦 🍃🍃🍃
*RANA D'AYA!*
💦💦 🍃🍃🍃
August, 2018
beeenovels.blogspot.com

_Written by Miemiebee👄_


*PAGE 3⃣4⃣*




Ko makaranta Amal ta kasa fita washegari saboda yadda jikin nata ya tsananta, gashi de ta fara shan maganin amma ba sauk'i. Kaman yadda Maamah ta d'au alk'awari haka tazo ta duba Amal da soft drinks nata, Safiyya ce ta amsa ta sa a fridge sannan ta kai ta d'aki inda Amal ke kwance akan gado ta duk'unk'une kanta acikin bargo se kakkarawa take. K'arya ne mutum ya ganta be tausaya mata ba.

"Subhanallahi Amal!" Maamah tayi exclaiming cike da tashin hankali. "Amal dan Allah karki mutu" take idanunta suka ciko da hawaye tsan-tsan tausayi.

"Amal mey kike yima kanki haka? Meyasa baki kira Mami ba? Meke damunki dan Allah?"

"Maamah calm down ki kwantar da hankalinki."

"Ya jikin naki? How are you feeling?"

"Da sauk'i zuwa anjima zazza6in ze sauk'a morning fever ne."

"Subhanallahi sannu ai baki fad'a mun zazza6in yayi tsanani haka ba what's wrong?"

"Maamah I'm pregnant" ta sanar da ita.

"You're what?!" Tayi exclaiming had'e da zaro ido waje.

"Maamah ina d'auke da cikin Yaya" ta jaddada mata yayinda ta rushe da kuka. Hugging nata Maamah tayi tana kukan tare da ita sun dad'e a haka sannan ta janye Amal a hankali tana mey share mata hawayenta.

"Amal I'm so happy for you, Allah ya inganta idan lokacin yayi ya raba lafiya."

"Ameen" ta amsa chan ciki-ciki.

"Ya Afzal ya sani?"

"Ke na fara fad'awa ko Mami ban kira na sanar da ita ba."

"Amal why? Ai Ya Afzal ya kamata ya fara sani ke bakisan wannan news shi ze zame sanadin shirya tsakaninku ba?"

"Shirya tsakanin mu?" Ta tambayeta had'e da sakar da murmushin takaici "Maamah things just got worst kin san mey Yaya yamun?" Kai Maamah tayi saurin kad'awa.

"Korana yayi daga d'akinsa shiyasa kika ganni anan bayan nan jiya yake ja mun Allah ya isa idan har na sake shigo masa da na miji gida Maamah zargi na Yaya yake, gani yake kaman duk zaman mu cin amanan sa nake."

"Innalillahi wa inna ilai raji'un the fuck is wrong with Ya Afzal? Ya yake abu kaman wanda baida ilimi? Ai yaci ace yasan abinda zaki iya aikatawa da abinda bazaki iya ba daga gun wani d'an jakar uban yaji wannan batu? Waya gaya mishi kina shigo da maza gidan nan?"

"Wallahi ban sani ba Maamah kinsan zurfin cikin Yaya bayi ta6a fitowa fili ya fad'awa mutum abu."

"Amal dan Allah ki tattara kayakinki kibar mai gidan nan haka wannan walak'anci dame yayi kama? Se kikace mishi mey dayace kibar masa d'akin nasa?"

"Mey kuwa zance masa? Pillow na kawai na ja na fice mey zance masa?"

"Hmm wallahi munafukar mey aikin ki d'innan nake zargi da ganin yadda fuskanta yake bak'i k'irin d'innan haka zuciyarta take in ba haka ba ina Ya Afzal zeji batun nan? Bawai zama yake a gida koda yaushe ba dole gaya mishi akeyi."

"Na gwada mata magana tace ba ita bace banida lafiya ban so jan maganan ba nace kawai shikenan."

"Wallahi itace kinji rantsuwa ba kaffara ina gaya miki Nazeefah ba kishiryar arziki bace wallahi aiki suke tare da 'yar nan dalilin daya sa tun farko ta kawo miki ita kenan. Wallahi aiki suke tare."

"Nazeefah kuma?"

"Don't be fooled by her kind gestures makashinka na nan tare da kai duk inda kake, kiyi tunani ita munafukar Safiyyan ce take kai wa Nazeefah rahoton komi a gidan nan ita kuma mak'irar seta ce ke ce kika kira kika sanar da ita."

"Maamah ni bana son abu da tashin hankali da tada magana idan ma aiki suke tare wataran dubunsu ze cika dukda cewan ban yarda da hakan ba I know Nazeefah baza ta ta6a yimun haka ba."

"Hmm Amal kenan ki bud'e idonki kisani yadda ka d'auki mutum ba haka yake d'aukanka ba ko a jinki kowa ne keda zuciya d'aya kamanki? Wallahi ba haka bane, balle wai har kice kin aminta da kishiyarki? Kishiyan da ba wacce take gaba dashi a fad'in duniya kaman ka? Ki bani izini inyi questioning mey aikin kin nan kawai."

"Maamah please ki barta bana son k'ananun magana" Maamah bata saurareta ba ta mik'e "Maamah dan Allah ki dawo" ficewa tayi ta dawo da Safiyya biye a bayanta "Bani wayanki" ta buk'aceta.

"Waya na kuma?"

"Eh wayanki."

"Lafiya?"

"Wani abun kike 6oyewa ne?"

"Wani irin magana kuma kike Aunty? Mey zan 6oye?"

"Good then pass me your phone" hannu ta mik'a mata tana jiran ta sanya mata shi aciki bayan Saffiya ta d'au lokaci ta sanya wayan cikin hannun Maamah cike da fargaba.

"Amal ya numban Nazeefan yake?"

"Maamah dan Allah
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment