Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

waye kuma Ya Abdul?"

"Wan k'awata ne..." nan de ta mar bayanin komi ba abinda ta ragar masa.

"Toh Amal naji bayanunki amman ke a tunaninki me zay sa Afzal miki fushi haka?"

"Wallahi ban sani ba Ya Sultan na zauna nayi tunanin nayi tunanin amman ina na rasa k'wak'k'warar dalili sede tun lokacin da ya hanani shiga motan wani bayan nasa nasan ya damu da lafiyata ce sosai kuma baya son inayin abu ban sanar dashi ba" ta sanar da shi.

"Haka ne kam k'warai, so ke a ganinki yanzu da ace keda bakinki kika sanar dashi cewa gashi wani yace yana sonki shi Afzal d'in baze ji haushi ba?"

"Eh Ya Sultan a gani na rashin sanar dashi da banyin bane ya haifar da komi, kuma wallahi ina da niyyan hakan kuma koda ace Yaya ya bud'i baki yace mun kar in amince da k'udurin shi Ya Abdul d'in in bari se karatu na yayi nisa tukun wallahi zan ji maganansa saboda tamkar wana na jini haka na d'auki Yaya nake kuma jinsa a jikina, duk abinda yace inyi muddin be sa6awa addini ba zan yisa, I respect him alot saboda son da yake nuna min bayan iyayena ban tsammanin akwai wanda ze nuna mun irinsa."

"Toh Amal yanzu ya kenan? Bazan 6oye miki ba Afzal yana fushi dake sosai."

"Wallahi nasani shiyasa nake neman taimakonka ka tayani basa hak'uri don Allah wallahi idan cewa yayi na dena kula Ya Abdul zan dena, zan iya yafe soyayyan kowa saboda farin cikin Yaya I care about him alot."

"Toh shikenan Amal I'll do all I can in shaa Allah Afzal ze sauk'o zanyi masa magana."

"Toh Ya Sultan thank you so much dan Allah duk abinda akwai ka taimaka ka kirani ka sanar dani."

"Here write down your number for me" yayi maganan yana mik'a mata wata jotter nan da nan ta rubuta mai tana masa godiya. Ya rakata tace sam kar ya damu zata k'arasa da kanta. Bayan ta fice ya zaro wayansa daya 6oye k'ark'shin wani littafi had'e da stopping recorder d'in. Wow ashe tun d'azun recording hirarsu da Amal yakeyi. A tunaninsa idan har Afzal ya saurari hirar nasu, ya kuma gaskata kalamun nan daga bakin Amal hakan ze iya sanya sa sanar da ita Amal d'in abinda ke zuciyarsa don haka washegari ya kira Afzal akan suje suci abinci tare. Suna tsakan ci ne Sultan ya d'auko topic na Amal.

"Jiya Amal ta shigo min ai" dum Afzal yaji gabansa ya fad'i, sosai fuskansa ya bayyana mamakin da ya sha amman ya basar pretending like everything is cool.

"Oh haba? Ya take?"

"Ba lafiya ba" ya amsa shi ba corner-corner.

"Why? Meya sameta?"

"Haba Triple A drop the act already."

"Sorry but I don't get you" yayi maganan had'e da d'age gira d'aya yana sipping drink nasa.

"Dan Allah ka dena wannan zurfin cikin wallahi ina gudun maka ranar da ciwon zuciya zata kama ka."

"Why? Meya kawo wannan magana kuma?"

"Mesa kake bawa 'yar yarinyan nan wahala haka? Shin baka tausaya mata ne? Wallahi ba haka so yake ba."

"Excuse me?" Yayi maganan cike da rashin fahimta.

"Sarai kasan me nake nufi until when do you plan to stop torturing her life like this? Har yaushe Triple A? Kai fa na miji ne, idan kai a matsayinka na miji ka kasa tunkararta ka sanar da ita abinda ke zuciyarka taya ita a matsayinta na mace yarinya ma at that kake tunanin zata iya gano hakan da kanta, iyye?"

"Ni ban fahimce ka ba."

"Wow!" Sosai Sultan ya sha mamakin abokin nasa, be ta6a sanin zurfin cikin Afzal ya kai ga haka ba se yau. "You can deny me for as long as you want amman bazaka iya k'aryata cewa kana son Amal ba, bazaka iya k'aryata cewa akanta ne ka samu wannan munafikin ciwon dake hannunkan ba kuma akanta ne ka fasa wayanka har seda ka sake siyan sabo ba."

"Look I'm not ready for this, idan kasan don haka ka kirani nan toh save it bana son sauraron ko kalma d'aya am leaving" wallet nasa ya ciro ya k'irga bill na abincin nasu ya ajiye akan table sannan ya mi'ke ya shiga tattara abubuwansa be kai ga takawa ba Sultan yayi playing audio'n da yayi recording jiya na hirarsa da Amal. Jin muryar Amal chak Afzal ya tsaya be sake motsi a wajen ba seda audio'n ta k'are.

Haushin kansa ya shiga ji na kasa sanar da Amal abinda ke cikin zuciyansa, na bawa zuciyarta daman son wani d'a na miji ba shi ba and k'arshe na sanya ta cikin damuwa haka. Ji yayi kaman ya wuce gidansu yanzun ya sanar da ita gaskiyan al'amarin ya tabbata kamar yadda ta fad'a idan da har ze bud'e baki yace yana sonta zata yafe soyayyar Abdul Rahman masa amman inaa baze iya ba, baze ta6a iyawa ba. Mutuncin da Amal ke basa baze ta6a basa daman ya furta mata kalamun so ba, baya son hakan ya zama sanadin da zesa Amal ta guje sa gara suta turawa a hakan.

"Ina had'a ka da Allah ka d'au mataki Triple A yarinyar nan bata ma san kana sonta ba nayi imani da Allah da ta sani wallahi bazata bawa shi Abdul d'in dama ba bale har su yi nisa haka."

"Ni Afzal ban ta6a bud'e baki na ce maka ina son Amal ba kuma idan har baka son muyi kaca-kaca da kai bazaka je ka samu yarinyan nan ka fad'a mata cewan ina sonta ba tunda baka ji daga bakina ba. Idan kuwa har kayi hakan toh Allah ya isa ni ban yafe ba-"

"Haba Afzal!" Sultan ya katse sa "Mey haka kakeyi? Mey yayi zafi haka har kake neman had'ani da Allah? Wallahi ko makaho ne yasan kana son Amal kuma muddin ka cigaba da wannan banzar d'abi'ar taka ba abin mamaki bane idan ciwon zuciya tazo ta kama ka, kamar kuma yadda kana ji kana gani Abdul d'innan ze auri 'yar nan a idonka ba yadda ka i-"

"Enough Sultan!" Afzal da zuciyarsa ta fara tafarfasa ya katse sa cike da tsiwa "Ya isa haka don kana matsayin amini na doesn't mean you have the right to speak to me like this. Ban damu da wanda Amal take so ba, ban damu da wanda zata aura ba kamar yadda ta fad'a maka nima haka zan sake jaddada maka I'm just hurt saboda bata sanar dani wani yace yana sonta ba a matsayi na na wanda take kira yayanta, wanda ke d'aukan nauyin karatunta da sauran ababe. Bata yimin adalci ba ace har sun daidaita da wani bata sanar dani ba bayan nan I have nothing more against her so please bana son in sake jin kana cewa ina son yarinyar nan, nide na fad'a maka" Yana kaiwa nan ya fice ya nufi motansa, tunda ya soma tuk'i kalamun Amal suke masa raha a kunne duk yadda yaso kawar da hankalinsa daga hakan ya gagara k'arshe seda ya afka hatsari ya bige wani me sai da mangaro kafin ya ce ze taka burki inaa har ya buge mutumin sede Allah ya takaita abun mutumin fad'i kawai yayi be ji ciwo ba wheel barrown nashi ne ya fad'i komi na kai yayi k'asa. Da wuri ya sauk'a yayi kan mutumin kaman yadda mutanen kusa suka yi kansu suma, nan de ya basa hak'uri ya biyasa asaran da ya janyo masa. Office ya k'arasa ya kammala aikin da ya rage sannan yayi gida ya watsa ruwa ya kwanta. Sede abin ya gagara ya kasa daina tunanin Amal, kalamanta se yawo suke masa a kai lokaci d'aya tausayinta ya kama sa.

Wayansa ya janyo yayi searching contact nata tare da unblocking sannan ya kirata a karo na farko ta d'aga "Yaya?" Ta kirasa da mamaki ba tare da ta basa daman yin sallama ba.

"Na'am Lily" ya amsa pretending as if everything is cool.

"Yaya you called!" Tayi exclaiming cike da farin ciki da k'in yarda.

"Yes Lily ya kike?"

"Yaya I'm sorry, I'm so sorry dan Allah kayi hak'uri."

"Ya wuce kinji?"

"No Yaya nasan abinda nayi maka ba dai-dai bane amman kayi hak'uri it shall never happen again please forgive me."

"It's okay, stop apologizing already ya wuce."

"I missed you so much Yaya dan Allah karka sake hukuntani haka wallahi hukuncin yamin tsauri, Yaya duk abinda nayi ba dai-dai ba kana da ikon min fad'a har zana idan ta kama zakayi mun amman ignoring d'ina haka is not a solution please."

"I'm sorry too Lily, I just didn't know how to react, my Lily is in love and I didn't know sede kawai ingani da ido na."

"Wallahi ina da niyyan fad'a maka Yaya Allah ne kawai be bani iko ba amman kayi hak'uri."

"So do you love him?" Ya tambayeta shiru tayi ta kasa amsawa "Lily?"

"Na'am Yaya?"

"Answer me."

"Yaya..." se kuma tayi shiru "Yaya in ganin mu tare ne baka so ina iya sanar da shi in bashi hak'uri."

"Not at all Lily ai farin cikink shine nawa besides ban ma san shi ba bale ince bana son shi so tell me about him."

"Sunan shi Abdul Rahman he's 28 years old yana aiki a INEC office."

"Masha Allah so do you love him?"

"Yes Yaya I do" ta amsa chan k'asa-k'asa wani irin k'una zuciyan Afzal yayi da jin hakan daga bakinta danne zuciyansa kawai yayi yace, "Masha Allah ki ja mishi kunne fa kice mishi Yayanki yace kar ya kuskura yayi toying da feelings naki dan ko idan yayi na lahira ma seya fisa jin dad'i."

Dariya tasa sosai "Kai Yaya nasan ai bazaka bari wani abun ya sameni ba besides Ya Abdul ma baze aikata abinda zesa a hukunta sa haka ba."

"I like that spirit, so abu d'aya nakeso dake Lily ki mayar da hankalinki da karatunki kinji? Karki bari Abdul ya d'auke miki hankali kin ji?"

"Na ji Yaya in shaa Allahu thank you."

"Toh barin yi shirin sallah ko?"

"Toh Yaya Allah ya kare goodnight." Sauk'e wayan yayi daga kunnensa a hankali yayin da zuciyar sa keyi masa wani irin rad'ad'i. Ta riga ta fad'a tana son Abdul in har Abdul ne farin cikinta toh shi kuma aikinsa ne a matsayinsa na yayanta yayi farin ciki da hakan. Meyasa yake jin haushi toh? Meyasa zuciyarsa take yi masa k'una haka? Yana son Amal, ya juma yana sonta, yana d'aya daga cikin burinsa na kullum ya mallaketa ya mai da ita nasa. Jira kawai idan lokacin yazo ya sanar da ita abinda ke cikin zuciyansa.

Da da jimawa yayi hakan amman baya son abinda ze raba mata hankali daga karatu se gashi nan wani daga chan yazo ya hargitsa masa plans nasa gabad'aya ya karya mishi zuciya, ya tarwatsar masa da mafarkin maida Amal amaryarsa, k'arshe kuma ya d'auke masa farin cikin rayuwarsa. Sosai idanunsa suka kad'a suka yi jaa zur idan ya tuna da dukka wannan ababe, k'iris ya rage beyi kuka ba. Masallacin daya kasa zuwa kenan k'arshe a d'aki ya idar da sallan ya mik'e kan gado har bacci yayi awon gaba dashi.

***
Haka tafiya ta cigaba, gabad'aya Afzal ya rasa walwalar rayuwarsa kullum cikin k'unci da bak'in ciki yake. Amal ce me kirarsa kullum idan bata kira ba sede su zauna ahakan. Sau dayawa takan zuwa office nasa seya ce wa PA'nsa tace baya nan. Ita de Amal ta rasa dalilin duk wannan d'abi'u se Afzal ya d'au sati biyu be kawo mata ziyara kuma koda yazo d'inma baya iya sakewa da ita suyi hira kamar yadda suka saba, sau dayawa takan zauna tayi tunanin ko wani abun tayi masa amman ina ta duba ta duba ta rasa dalili. Ita da Ya Abdul nata kuwa se abinda ya k'au, tun bata barin ya d'auketa ita kad'ai a mota ta soma yarda da amincewa da shi. Zezo ya d'auketa su wuce gun shak'atawa idan ya tashi maido da ita gida kuwa ya cika mata leda da chocolates da ice creams.

Ta fannin Nazeefah ma sede abinda ya k'aru a kullum k'ara son Afzal take tun tana k'ok'arin 6oye masa abin ya gagara har ya kaiga shi Afzal d'in ya gane yanzu. Yau ma kaman jiya da ta tashi yin girki da shi tayi yana dawowa daga office tayi masa sannu da zuwa ya amsa sannan take ce masa food is ready. Banza yayi da ita seda ta bisa har d'aki "Afzal nace nayi girkin da kai fah."

"Thank you a k'oshe nake."

"Haka jiya ma kace, shikenan ni na rink'a girki kenan kullum kana cemin a k'oshe kake? Until when ne zaka dawo gidan nan da yunwa kaci abincin?"

"Please! Save whatever this is kin dega daga office nake ko? I need to rest."

"Toh wallahi ni kuma bazan yarda ba akan me zanna maka girki kak'i ciki?"

"Ni na rok'eki kimin girki ne? Weren't you the one that said da kiyi min girki gara kinyi hauka?"

"Toh kuma shikenan seka d'auka ka zauna akai? Ko kai zaman nan haka na maka dad'i I'm willing to change and start over this again why can't you?"

"Because I don't love you Nazeefah kin gane ko? Ko mey kikayi you'll never impress me kin riga kin fita min a rai just let me be karki bari in sauk'e haushin da be shafe kiba akanki" yana kaiwa nan ya wuce bayi ya barta tsaye a gun. Hawaye kawai taji yana bin k'uncinta da k'yar ta iya tattara kanta tayi d'akinta ta shiga zuba kuka. Tun Mummy da Rumaysa suna ce mata tayi hankali tayi hankali kafin lokaci ya k'ureta tak'i ji gashi nan yau gar da gar Afzal ya bud'a baki ya ce mata ta fita masa a rai kuma ta tabbata ba komai bane ya janyo hakan illa rashin hankalin da tayita tafkawa, ina ma ace zata iya jan lokaci baya ta daidaita komi ba k'arya acikin zancen nan again tana son Afzal tana son shi kuma zatayi duk abinda ya kama don karkato da hankalinsa ya dawo a gareta.

Washegari da safe bim wajajen k'arfe sha d'aya ta shirya tsaf ta kira Afzal ta tambayesa izini sannan ta wuce gidansu Ummi dukda cewan bata sanar dashi inda zata. Maraba Ummi tayi mata suka zauna a parlour suka gaisa tasa su Esther suka kawo mata cookies da drinks.

"Kwana biyu kin k'i mu Nazeefah shima mijin naki ya kwan biyu be lek'o ba."

"Allah sarki Ummi wallahi kinsan harkan makaranta yanzu ma dan mun samu hutu ne."

"Wai bade har kun k'are part two din ba?"

"Eh wallahi Ummi se three kuma yanzu."

"Masha Allahu karatun naku na tafiya gaskiya Allah sanya albarka aciki."

"Ameen ameen Ummi nagode dama alfarma nazo nema ne."

"Toh 'yata ina jinki."

"Game da Afzal ne."

"Toh kuma bade wani abun bane ya faru ko? Ina sauraronki."

"Ummi hak'uri nakeson ki basa."

"Meya faru kunyi fad'a ne?"

"Ki basa hak'uri ya soma cin girki na don Allah, Ummi bazan 6oye miki ba tun auran mu ba wata jituwa a tsakaninmu as dukan mu bawai muna so auran bane mun yisq ne don ladabi da biyayya ga iyayenmu."

"Wannan haka take 'yata."

"Toh Ummi bazan 6oye miki ba wallahi ko girki ban ta6a yiwa Afzal ba, rayuwansa yake daban a gidan nima haka, kullum daga office se parlour se d'akinsa yake zama nima daga school se parlour se d'akina amman abun ya isheni yanzu na zauna nayi wa kaina fad'a I want to give us a chance nace zan fara yi masa girki kuma na faran sede ko nayi baya ci Ummi wallahi ina son Afzal amman ko na second d'aya baya ma kallo na balle yasan ina cikin damuwa, be damu dani ba jiya har cemin yayi baze ta6a sona ba na riga na fita masa a rai and I don't blame him saboda ni ne na janyo komi da kaina amman na tuba yanzu Ummi I promise to be a good wife to him but ya k'i bani dama, bansan ya zanyi ba wallahi ina son sa."

Iya mamaki Ummi ta sha bata tsamman gaban dake tsakaninsun ya kai har ga haka ba ita da take jiran jika amman ace haka ai wannan da alama ko had'a kwanciya basu ta6a yi ba, lallai kam akwai k'ura sede kuma ta gamsu da tuban Nazeefah. Idan ba so na hak'ik'a takeyi wa Afzal ba ba yadda za'ayi tana mace ace bata ji kunyan idon surkarta ba har tayi admitting kurakuren ta haka.

"Ummi dan Allah ki basa hak'uri ko ze soma cin abinci na ya dena had'a min rai haka kullum."

"Naji matsalar ki Nazeefah sede abu d'aya nikeson tambaya."

"Ina jinki Ummi."

"Ina fatan a iya zamanku baki ta6a goranta mai da wani abun ba?" Shiru tayi tana nazari chan tace "Wallahi nayi na masa akan girki."

"Ai kin 6ata komi kenan gorin da kikayi masan ne yasa har yau ya kasa cin girkin ki."

"Ummi amman ai idan kika basa hak'uri zai sauk'o."

"Zanyi iya k'ok'arina but I can't guarantee you hakan. Afzal halin mahaifin shi ya biyo se kuma har kaman nasa ma na son fin na mahaifin nasa. Kinga koni nan idan mukayi fad'a dashi se idan nazo na basa hak'uri yake sake amincewa yaci girkina kiyi imagining ke matarsa da har kikayi masa gori. Ina son ki sani cewa komin yaya fad'a ta 6arke muku da Afzal koda wasa karki kuskura ki goranta masa da wani abun dan shi idan yayi fushi da abu yayi ne har abada se wani ikon Allahn."

"Innalillahi Ummi kina nufin yanzu Afzal baze ta6a cin girki na ba kenan?"

"Bana fatan hakan, in shaa Allah zan kirasa muhi magana duk abinda akwai zan kiraki in sanar dake."

"Amman Ummi nagode sosai please don't let Mummy know of this pleaase."

"Karki damu 'yata in shaa Allah maganan nan a tsakanin mu ne."

"Thank you so much I shall get going."

"Bazaki bari kiyi Azahar ba tukun?" Tayi maganan tana duban lokaci.

"Zanje inyi girki kinsan yau juma'ah 2 Afzal ke dawowa gida."

"Toh Mama na Allah miki albarka bari in raka ki." Tana raka Nazeefah ta dawo ta d'au wayarta ta kira Afzal a karo na farko ya d'auka.

"Halo Ummi?"

"Na'am Prince d'ina."

"My Ummi ya kike? Ya Abba?"

"Lafiya k'alau ya aiki?"

"Alhamdulillah nace zaka iya biyowa nan idan ka tashi daga office yau?"

"Sure wani abu ne?"

"Kai de seka zo kawai."

"Toh shikenan ina idar da sallan Juma'ah zan zo."

"Yauwa Baby na Allah kawo ka lafiya yayi maka albarka."

"Ameen Ummi take care bye" da haka sukayi sallama. Kaman yadda ya fad'a mata hakan yayi yana tasowa daga Juma'ah ya d'au hanyan gida, a hanya Amal ta kirasa, connecting yayi da car Bluetooth nasa sannan ya amsa suka gaisa take yi masa barka da Juma'ah. Yana isa gida ya fara wucewa site na Abba suka gaisa sannan ya k'arisa na Ummi.

Bayan gaisuwa Ummi tayi gyaran murya, "Dama ba komai bane yasa nace kazo illa batun matarka Nazeefah."

"Toh kuma meya faru Ummi?"

"D'azu ai tana nan." Se anan ya gane ashe nan tazo da ta kira take tambayansa izini.

"Lafia dai ko?"

"Ai ka fini sani, kai de bazaka ta6a barin wannan zurfin cikin naka ba ko?"

"Mey tazo tace miki?"

"Komi ma ta fad'a ba abinda ba ta sanar dani ba ai dama sau dayawa nayi suspecting zaman auren nan naku ashe haka kuka ta turawa har na tsawon shekara d'aya Prince? Wallahi I'm very disappointed in you idan ita Nazeefar yarinya ce bata da hankali ai kai seka nuna mata kana dashi amman ba wai ka tsaya kana biye mata ba kuna tafka wawanci ba, yanzu meye ribar ka? Yaci ace ka ajiye d'a a zaman ka yanzu haka wallahi."

"Ummi don't just jump into conclusions wallahi Allah ma sheda ne nayi hak'uri da Nazeefah iyakan hak'uri, ba me iyayin hak'urin da nayi da ita ni kawai bana son 6ata ta a idonki ne kikaga ko kin tambayeni ya gida nake miki k'aryan cewa lafiya k'alau."

"Kalleni Prince" ta buk'acesa, ba gardama ya dawo da kallonsa a gareta "Zanyi maka wata tambaya kuma I want only a sincere answer."

"Ina jinki" ya amsa bayan tsawon lokacin daya d'auka.

"Yadda kasan zaka mutu tsakaninka da Allah ka ta6a bawa yarinyar nan hak'k'inta na aure a matsayinta na matar ka?" Shiru yayi yana mamakin bade abubuwan da Nazeefah tazo ta irga wa Ummi ba kenan cewa ko hak'k'inta be ta6a bata ba, lallai kuwa!

"A dalilin mey zan had'a kwanciya da ita Ummi? Kinsan mey tace ne? Da kunne na najita tana cewa k'awarta da ta bani kanta gara 'yan iska akan layi sunyi mata fyad'e kina ganin ya dace in raya sunnan manzo da ita?"

"Innalillahi! Nazeefar de?"

"Ummi k'arya zan miki ne? Wallahi da kunne na naji kefa baki san rashin hakalin da yarinyan nan take ba kuma wallahi albarkacin Abba take ci dan yanzu da zaran na saketa ko nayi mata wani abun kaman wa Abba nayiwa hakan ze iya 6ata tsakaninsa da amininsa ko ba haka ba?"

"Hakane Prince kuma na yabawa hak'urin ka amman seka duba kuma yanzu da ta gano kuranta take son ku fara sabon rayuwa, kamata yayi kayi hak'uri ka bata dama. Wallahi da bakinta anan take cemin tana sonka dan Allah in baka hak'uri."

"Ni to bana sonta" ya fad'a mata gar.

"Wani irin magana ne haka Prince? Matarka ce fa! Haka kakeson ka cigaba da rayuwanka? Shin kai baka kwad'ayin ganin jininka ne?"

"Inaso mana amman bada Nazeefah ba."

"Prince dan Allah kar kayi magana haka kamar yadda ka tsani yarinyan nan fa itama haka ta tsaneka da fari amman mey? Data bud'e zuciyarta maka ba gashi soyayyarka ta shiga ba kaima fa zaka iya dan Allah kar kace a'a."

"Ummi kin de sanni, kin fi kowa sani na idan abu yafita min a rai ya fita kenan har abada, a da kafin in auri Nazeefah ban tsane ta ba kaman yadda na tsaneta yanzu. Zaman da mukayi da ita ya sake sa na tsaneta yarinyan can bata da hankali, bata da tunani, ba ta da fasalin komi, ba yadda za'ayi ta zame uwa ga 'ya'yana no way!" Ya jaddada mata.

"Prince dan Allah ka dena magana haka, ka cigaba toh wallahi baza ka san lokacinda ze iske mahaifinka ba. Ka yayyafa wa zuciyanka ruwan sanyi kayi hak'uri ka bata dama ta sauk'e nauyinta a kanka a matsayinta na matarka."

"Ni ta bari kawai na yafe mata haka zamu cigaba da zama har zuwa lokacin da Allah ze raba mu."

"Wato kafi k'arfin in gaya maka magana kuma kaji ko Prince?"

"Ummi please kar kiyi magana haka sanin kanki ne banida kaman ki ans I always heed to you."

"Then listen to me ka bawa Nazeefah dama."

"Ummi zuciyana na mace d'aya ne kuma wata chan ta riga ta sace ta tafi dashi ba komai anan" yayi nuni da inda zuciyarsa ke. "Kinga ko ba yadda za'ayi in fara son Nazeefah."

"Babban magana! Bade shirin aure kake yi ba?"


DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment