Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

sorry please forgive me."

"I've forgiven you Rabba'atul Bait nazo ne don in jaddada miki ina shirin dawo dake d'akinki, zaki dawo?"

"Ya Rouhi zaka mayar dani gida?" Ta tambayesa cike da k'in yarda.

"Yes Rabba'atul Bait you're going back to your home."

"Ya Rouhi!" Ta ambata hawaye na ciko mata a ido yayinda ta fad'a jikinsa tana kuka, zagaye hannunsa yayi a bayanta yana calming nata "Ya Rouhi dan Allah kayi hak'uri na d'au alk'awari bazan kuma abinda na aikata ba please forgive me" a hankali ya d'agota yana share mata hawayen nata "Na fad'a miki I've forgiven cry nomore."

"Thank you so much."

"Baki tambayi ya jikin Amal ba." Alokaci d'aya yaga yanayinta ya sauya.

"Nazeefah na d'au kinyi nadaman abinda kika yi wa Amal koba haka ba?"

"Ya Rouhi nayi."

"Then why this reaction? In har Amal tana da niyyan yafe miki meyasa ke bazaki iya neman tubanta ba? Kinsan ko akwai hak'k'inta akanki? Kuma muddin baki nemi tubanta ba ta yafe miki Allah baze ta6a barin ki ba?"

"Ya Rouhi nayi nadaman abinda nayi mata, wallahi nayi."

"Then ki bata hak'uri I want you to call her and apologize." Shiru tayi bata ce komai ba tana tunanin ta inda zata fara kiran Amal ta bata hak'uri, wani irin k'ask'antarwa ne Afzal yake shirin yi mata haka?

"Bazaki iya ba?" Ya tambayeta yana mey tsamo ta daga tunanin da takeyi.

"Ya Rouhi ba haka bane" ta mai k'arya.

"Nazeefah yaushe ne zaki gane cewa Amal 'yar uwarki ce ba abokiyar gabanki ba? Yadda kike ganin ina son ta kema fa hakan nake sonki, in kuma kina ganin kaman nafi son ta ne then you're right saboda Amal na mun abinda zuciya na keso. Bata k'untata mun, bata sani surutu, kuma tana sonki saboda tasan ina sonki. Ta sani idan taso wani nawa kaman ni taso amma ke fah? You don't love her single bit. Why Nazeefah? Do you even love me at all? I doubt so because if you really do zaki so abinda nake so kema ki so Amal."

"Ya Rouhi dan Allah kar kace haka sanin kanka ne ina sonka, I do love you above of everything."

"No Nazeefah, idan da har kina so na da zaki so Amal ki guji aikata abinda ze 6ata mun rai but no, you keep on hurting Amal which is technically like hurting me, ita kuma zuciya mey kyautata mata take so ko baki san da haka ba?"

"Na sani" ta ambata kanta a duke.

"Good saboda haka nake son ki soma kyautata wa Amal, kin fini sanin yadda Amal ta d'aukeki da zuciya d'aya, kinfi kowa sanin cewa Amal bazata ta6a aikata kwatankwacin abinda kikayi mata ba saboda tasan idan ta ta6aki kaman ta ta6a ni ne why can't you do thesame? Yadda kike jin ni mijinki ne itama fa haka takeji you both have equal rights on me, I love you Nazeefah, I really do love you and bana son abinda ze sake shiga tsakaninmu but idan kika cigaba da wannan halin naki zakisa ki fita mun a rai kuma bana son hakan ya faru because I don't want to hate you Nazeefah please change your ways. Kece fa uwar gidana komin yaya matsayin ki daban yake dana Amal a zuciya na da kuma ma a idon jama'a, be kamata ace ke kike yin wannan rashin hankali ba kamata yayi ace Amal ce keyi kina mata wa'azi, ke bakisan da wannan abinda kikeyi ba Amal zata iya k'wace miki martabarki?"

"Ya Rouhi I'm sorry."

"Don't be Nazeefah, I just want you to change ki sauya d'abi'un nan kiso 'yar uwarki muyi zaman lafiya dukan mu please. Idan har kina sona zakiyi mun abinda nakeso."

"Naji Ya Rouhi in shaa Allah kuma zan canza, ko mey kakeso I'll do it."

"Ki tuba ki bawa Amal hak'uri, that's all I want."

"Ya Rouhi sena bata hak'uri ne? Ai na tuba."

"Toh bakiya son in dawo dake gida?"

"Ina so."

"Then kiyi hak'uri ki sauk'e girman kan nan ki bata hak'uri I kow it's not easy but do it for me okay?" Ya k'are had'e da d'aga hannunta ya rik'e acikin nasa.

"Naji zan bata."

"And promise me bazaki sakeyin abinda zeyi hurting Amal ba, promise me ko na mayar dake bazaki sake tada wa kowa hankali a gidan ba, zaki bawa Amal dama kuyi zaman lafiya." Hannunta ta aza akan nasa dake rik'e da d'ayan nata "I promise Ya Rouhi in shaa Allahu bazaka sake jin kaina dana Amal ba."

"Thank you Nazeefah thank you so much."

"Ni ce da godiya Ya Rouhi."

"So yaushe zaki kirata?"

"Bana son muyi magana ta waya nafison inje in sameta har gida in nemi tubanta."

"Masha Allah."

"Yaushe zaka mayar dani gida toh?"

"Yaushe su Daddy zasu dawo?"

"Next week."

"Suna dawowa zan zo in d'aukeki Rabba'atul Bait kinsan be kamata haka kawai in d'aukeki ba tare da sanin su ba."

"Hakane kam toh in yi mishi magana ta waya?"

"Still hakan beyi fasali ba kibari su dawo d'in ai nan da next week kaman gobe ne."

"I know Ya Rouhi is just that I miss you."

"I miss you even more darling" ya rik'o fuskanta "And I can't wait to have you back." Murmushi ta sakar masa sannan ya mik'a a hankali yayi kissing lips nata na lokaci kad'an. "I should get going."

"Tun yanzu Ya Rouhi?"

"I need to get back to work."

"Zaka gun Amal de."

"That is after I close from work."

"Toh tashi in raka ka" har gun motansa ta kaisa inda ya d'auko wani pack k'arami daga cikin motan ya mik'a mata "This is for you."

"For me?" Ta tambaya had'e da amsa.

"Open it" ya umarceta. Ba gardama ta bud'e wani Silver bracelet ne me bala'in kyau ta tarar aciki "Ya Rouhi this's so beautiful."

"Do you like it?"

"Alot, thank you so much Ya Rouhi."

"Alright ki koma ciki se mun sake waya." Da haka sukayi sallama ya koma office.

****
_9:36pm_
"Gobe zamuje muyi first baby scan namu ba? Ko bazaki iya zuwa ba?" Afzal dake kwance akan cinyan Amal a parlour ya tambayeta. Hannunta dake cikin gashin kansa tana wasa dashi ta cire "Mey ze hana Ya Omri? Allah kaimu."

"Ameen, d'azu naje gidan su Nazeefah."

"Oh how's she?"

"She's fine."

"Yaushe zaka maidota d'akinta?"

"Zuwa next week su Daddy sunyi tafiya so sai sun dawo "

"Allah kaimu:"

"Ameen" ya amsa had'e da d'ago kansa "I wish Nazeefah will be like you Rania."

"Meyasa kace haka?"

"Inda zata rage zafin kishinta ta sauk'o kaman ki ai kinga da mun samu zaman lafiya a gidan nan."

"Why?"

"Because bakida kishi Rania."

"Haka kake gani?" Ta tambayesa da murmushi kad'an.

"Yes Rania ban ta6a ganin kishinki ba."

"Saboda ina 6oye wa ne gudun sanyaka cikin damuwa kaman yadda kake ciki yanzu."

"Kina nufin kema kina kishi anytime na ambaci sunan Nazeefah?"

"Tabbas Ya Omri kawai dan ina 6oyewa ne ita kuma Nazeefah bata iya 6oye kishinta shiyasa kake ganin haka. If not ina matuk'an kishinka Ya Omri nakega fiye da yadda Nazeefah ma keyi, ma tukun tayaya ne ba zanyi kishinka ba bayan ina sonka?"

"Wow! So for all these while ranki na 6aci kema idan na kira sunanta?" Kai ta gyad'a masa "Amma bawai hakan na nufin na tsaneta bane saboda yadda nake jin inada iko da kai itama haka ne, we're both your wives Ya Omri and we love you."

"Rania you're just different in a unique way, Allah sa Nazeefah tayi koyi da halinki."

"Ameen" ta amsa tare da sakar da hamma.

"Baby na tana saki bacci ko?"

"Se kuma aka cemaka baby girl ce?"

"Toh mey ne da? Ai mace ce kyakkyawa kamar ki."

"A'a na miji ne, handsome kaman ka."

"Mu zuba mu gani."

"Eh mu zuba d'in, nida abu ke jikina kawani ce min na mace ce? Na miji ne let that sink."

"Wow ni kuma da nayi ajiyan kikeson kice bansan mey na ajiye ba?"

"Eh baka sani ba."

"Shikenan time will tell ba se munyi musu ba" cike da dabara ya mik'ar da ita kan kujerar had'e da aza kansa dai-dai saitin cikin nata kaman mey son sauraron abu "I wish I can listen to its heartbeat Rania."

"Not only will you listen to its heartbeat Ya Omri, one day zaka rik'e sa hannu" ta sanar dashi tana shafa kan nasa a hankali.

"Allah nuna mana wannan rana."

"Ameen" ta amsa.

"I can't wait have a replica of you calling me Daddy Rania, I really can't." Dad'i sosai taji ta sakar mar da murmushi "Thank you so much Babe."

"Godiyan mey kuma kake mun Ya Omri?"

"For everything Rania, for trying to give me a family Allah ya cigaba da miki albarka."

"Ameen Ya Omri everything for you yauwa d'azu ma Ummi ta kirani."

"Ayyah ya take?"

"Lafiya k'alau ashe ka fad'a mata I'm pregnant."

"A tunaninki zan iya yin shiru ne? Bank'i a buga a newspaper cewa kina da ciki ba Rania, you made me so proud and happy" hira suka ta6a sannan chan sukaje suka kwanta.

***
Lafiya k'alau suka cigaba da zama abinsu ba tashin hankali bale fad'a se zallan so da tsan-tsan k'auna amma kuma sey me? Kwana biyu zazza6in safe da na yamman nan ke son sake dawowa Amal, gabad'aya yabi yasata a gaba, kullum cikin amai take abin tausayi harta zube. Kaman kar Afzal ya fita office yau yakeji dan yadda jikin nata ya sake yin tsanani shi ya d'au sun riga sun wuce nan yanzu ashe rashin lafiyan mey tafiya ya dawo ne. Misalin k'arfe goma Maamah tazo dubanta. Ga laulayi ga targad'e a hannu da k'afan da be gama warkewa ba har yanzu.

"Sannu cikin nan na baki wuya Bestie."

"Thank you, anata lectures bani ko?"

"Gashi next week muna da tests har uku na Mallam Auwal biyu da na Malama Binta."

"Na shiga uku Maamah ko notes bani dashi gashi Malam Auwal baya bada handouts sede wani ikon Allahn kam in ba haka ba nasan inada carry overs wannan semester."

"Karki damu na miki photocopying nawa notes d'in na Malama Binta kuma gashi na sai miki" tayi maganan had'e da zaro su daga jakarta tana ajiyewa akan side drawer.

"Maamah bansan ya zanyi in ba keba, thank you so much Allah yabar zumunci."

"Ameen ba komai kede kawai ki samu time kiyi karatu in fever'n ya sauk'a. Ya Ya Afzal?"

"Ya fita office da k'yar wai ze zauna ya kula dani."

"Ayya meyasa kika hanasa?"

"Toh ba amfani Maamah zuwa sha d'aya haka zazza6in ze sauk'a."

"Ayyah ai ni na d'au kin rabu da zazza6in ashe da saura."

"Wallahi ko nima na d'au ya k'are kawai shekaran jiya ya fara mun kaman wasa fa se amai, komi naci hararwa nake."

"Sannu wata nawa ne yanzu?"

"D'aya fa da sati uku."

"Allah sauwak'e toh in shaa Allah kina fita daga first trimester naki shikenan."

"Ameen Maamah."

"Na gaya wa Ya Abdul fa."

"Mey d'in?" Amal ta tambayeta had'e da zaro ido.

"Batun kina da ciki mana."

"Innalillahi!" Ta dafe goshinta "Baki da hankali ne Maamah?"

"Toh mey? Ba abun farin ciki bane?"

"God help me wallahi baki had'u ba taya zaki fara sanar da Ya Abdul ina da ciki dan Allah? Mstw se yace mey?"

"Ya taya ki murna of course yace in gaisheki."

"Mstw wallahi ke banza ce wani sa'in ya yake toh? Se yaushe ze dawo?"

"Waya san masa ne kullum na tambayesa yace da saura da alama ya samu wata achan ne take d'ebe masa kewanmu."

"Allaha yasa toh wallahi da sena fi kowa yi masa murna."

"Wallahi ko, ameen deh." Hira Maamah ta tayata da se wajajen uku ta tafi sanin Afzal ya kusa dawowa. Saidai har shida Afzal yau shiru dan haka Amal ta d'au waya ta kirasa don jin ko lafiya, saidai da ya shiga seya katse yin hakan sau biyu se tayi tunanin ko yana meeting ne bada dad'ewa ba kuwa sega sak'onsa.

_Sorry for not informing you, I'm in a meeting be home in a moment I love you._

Murmushi ta sakar ta furta "Allah dawo daki lafiya." Sannan ta mayar da wayan ta ajiye.

Wajajen takwas Afzal ya dawo gida lokacin jikin Amal ya sake tashi se kakkarwa take k'ark'ashin bargo. Jakansa kawai ya ajiye ya nufi kanta yana shafa fuskanta a hankali "How're you feeling Rania?"

"Sannu da dawowa" kad'ai ta iya fad'a masa.

"Kinci abinci?" Ya sake tambayarta inda ta kad'a masa kai.

"Rania why? Bakiji abinda Dr yace miki ba jiya?"

"Ya Omri ko naci hararwa zanyi yana tayar mun da zuciya."

"I'm sorry kinji? Ko black tea ne ki dage ki sha bari in had'a miki."

"Please no bana so."

"Toh se mey? Bazeyi ki kwana akan yunwa ba Rania please."

"Koko nake so, idan nasha bana hararwa shi Mami ke bani lokacin da nike gida."

"Kokon dana sani kunun kamu?" Ya tambayeta da mamaki inda ta gyad'a masa kai.

"Toh Rania ina zan samu kamu? Ko da akwai ma ban iya had'awa ba kuma kinga dare yayi ba inda zan iya samu bale in siya miki."

"Don't worry zan sha ruwa kawai in kwanta gobe seka saya mun."

"Rania don't you get it? Bazan iya barinki ki kwana akan yunwa ba."

"I'm sorry" tace da shi idanunta na kakkafewa. Wayansa ya zaro daga aljihunsa "Wa zaka kira?" Tayi saurin tambayarsa.

"Ummi to ask ko zata iya had'a miki se in amso tunda gida ba nisa daga nan."

"Ya Omri ba seka sa Ummi aiki ba" saidai be saurareta ba ya kira Ummin bayan ta d'aga sun gaisa yake tambayarta ko akwai kamu a gida.

"Eh lafiya?"

"Ummi ban fad'a miki ba ko? Jikin Amal ya tashi."

"Subhanallahi bade laulayin ba?"

"Shi Wallahi gashi ko mey taci hararwa take se koko kad'ai kuma babu a nan gida shi'e nake tunanin ko zakisa su Esther su had'a mata yi hak'uri dan Allah."

"Kai kuma mey na wani bada hak'uri? Ai Amal 'yata ce bari in had'a mata yanzun ni da kaina driver ya kawo muku."

"Ko nima zan iya zuwa in kar6o kawai a had'a mata d'in."

"No ka zauna ka kula da ita tunda ga driver."

"Alright thank you Ummi."

"Kayi mata sannu bari in yi sauri in had'a mata" nan da nan ta wuce kitchen ta had'a kokon da kanta ta cika masu a wani k'aton flask yadda har gobe Amal zata iya sha sannan ta had'a musu da d'anye incase zata kad'a in ta samu k'arfin jiki. Zama yayi akanta yana ta yi mata sannu ko kayan jikinsa ya kasa cirewa kunun na isowa ya d'iba a cup yasa sugar kad'an yadda baze tayar mata da zuciya ba ya koma d'akin sannan ya kishingid'ar da ita jikin gadon ya shiga bata, na sosai yayi mamakin yadda tasha kokon sosai gashi ko hararwa batayi ba sa6anin duk wani abinda takai baki.
Ai ko idan haka ne ya zama dole ya koyi dama kokon dan yana yi mata. Bayan ta shanye ya buk'aceta da ta watsa ruwa zata fi jin dad'in jikinta amma tak'i, ba yadda beyi ba tak'i wai yau Amal tasa me son wanka wane kifi ce ake had'a ta da Allah tayi wanka take k'i? Tun jiya rabonta da yin wanka haka k'arshe se da ya d'iba ruwan d'umi a bowl da tsumma ya mammatse mata jikin nata da shi sannan ya samu ya sata tayi bacci. Nan shima yaci abinci ya k'arisa aikin daya rage masa daga office ya fad'a bayi ya watsa ruwa yana cikin fesa turare wayansa ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Nazeefah ke kira be 6ata lokaci ba ya d'aga inda suka gaisa.

"Su Daddy sun dawo ne?"

"A'a se next week kuma wai."

"Lafiya dai ko?"

"Lafiya kawai chan d'in ya musu dad'i ne."

"Ayyah se mun k'ara hak'uri sun dawo kenan ko Rabba'atul Bait?"

"Ya Rouhi ni kawai kazo ka d'aukeni."

"Bazeyi ba Rabba'atul Bait ki k'ara hak'uri kinji? Allah dawo dasu lafiya."

"Ameen ya jikin Amal?"

"Gashi nan Alhamdulillah deh."

"Allah sawwak'e toh."

"Ameen thank you."

"I miss you Ya Rouhi."

"I miss you even more darling it's late you should sleep by now."

"Goodnight toh."

"Sleep like a baby" nan ya katse ya gama abinda yakeyi yaje ya samu Amal suka kwanta. Duk yadda yaso kwantar da ita a jikinsa ya kasa sabida yadda jikin nata ya d'au wani irin zafi, sekace ba yanzu ya gama matse mata shi da ruwa ba.

Haka Amal ta cigaba da fama da zazza6in, da rana kad'ai take samu tayi karatu, ranan da zasuyi test d'in Afzal da kansa ya kai ta makarantar yayi magana da securities akayi cutting line aka shiga da ita ta gudanar da E-test suka komo gida. Haka duka sauran tests d'inma jiranta yake seta gama su taho gida tare. Kokon nan kuma shi kad'ai take sha ba tare da ta harar ba, da safe Afzal kafin ya fita office yake dama mata yasa a flask yadda da ta tashi sede tasha. Acikin sati Amal ta rame sosai tayi duhu sede jikin da sauk'i sosai yanzu zazza6in ya tafi se k'warnafi ko turare inba na wuta ko khumrah ba bataso, muddin tana d'aki Afzal be isa ya fesa turare ba se taji amai. Gashi sam bata son wanka yanzu, kwana biyu yau tak'i yin wanka matse mata jiki ma da Afzal yakeyi yau ta hanasa yi wai bata so. Alwala idan tayi na Azahar da shi takeyin La'asar wani sa'in har Maghrib. Shi de Afzal yanzu yake sake tabbatar da zancen cewa ciki nasa wasu matan k'aramin hauka.

"Rania yi hak'uri kiyi wankan kinji? Ni da kaina ma zan miki yi hak'uri." Ko tankasa batayi ba taja bargo ta rufe kanta, sauk'e bargon yayi "Yi hak'uri kinji? Karfa zama da dottin nan yayi miki illa."

"Wai wallahi inda kaine acikin halin nan ko alwala ma baza ka iya yi ba ka barni kurum in wari nake maka kaje d'ayan d'akin ka kwanta." Dariya sosai ta basa, mutumin da banda k'amshin turaren wuta ba abinda ke tashi daga jikinsa ne wai ze ce yana wari shi kawai gudun abinda zama da dattin ze iya haifar mata yake ba don wai tana wari ba.

"Yi hak'uri Rania beyi zafi haka ba."

"Toh ka barni in kwanta."

"Toh shikenan seda safe Allah k'ara sauk'i."

"Ameen" ta amsa tana rufe idonta sauk'an lips nasa taji a fuskanta "I love you."

"Ina da dotti ka manta ne?"

"I'll still kiss you Rania yi bacci kinji? Get well soon" Murmushi ta sakar masa sannan a hankali bacci ya d'auketa.

***
Da kwana hud'u Nazeefah ta kira Afzal akan su Daddy sun dawo, dad'i kenan he can't wait ya dawo da ita gida ta bawa Amal hak'uri su fara shiri, it's what he's ever asked for. Yana zaune a office yana aiki around 2:30 wayansa yayi beeping alaman shigowan sak'o. Message yagani daga Amal from snapchat da hanzari ya bud'e wayan ya bud'e, hotonta yagani wanda yake da tabbacin yau ta d'auka. Tana sanye da wani dogon rigan roba armless ba ko d'igon kwaliya amma tayi bala'in kyau da gashinta kame a tsakiyan kanta jelan na lilo. Be 6ata lokaci ba yayi replying nata;

_Triple A๐Ÿ’ฆ;_ Iyyeehh๐Ÿ˜๐Ÿ˜ yau baby na yabar min Rania tayi wanka kenan._
Bada dad'ewa ba sega reply nata.

_His Rania๐Ÿ‘‘; ๐Ÿ™ˆ na cika ka da wari two days ko?_

_Triple A๐Ÿ’ฆ; dama shuwa suna wari ne? Ai ban sani ba don ni kullum na matso kusa dake k'amshin turaren wuta da khumra nake ji._

_His Rania๐Ÿ‘‘; ๐Ÿ˜ฉ Ya Omri you're so sweeet_

_Triple A๐Ÿ’ฆ; ๐Ÿ˜๐Ÿ’• Ya jikin naki toh? Da sauk'i?_

_His Rania๐Ÿ‘‘; Alhamdulillah bakace nayi kyau ba๐Ÿ˜ฉ๐Ÿ˜ฉ_

_Triple A๐Ÿ’ฆ; Haba 'yar shuwata kema ai kinsan kinyi kyau ๐Ÿ˜๐Ÿ˜, send me more._

_His Rania๐Ÿ‘‘: O'o ai baka ce mun nayi kyau ba seda na rok'a๐Ÿ˜•_

_Triple A๐Ÿ’ฆ; Rania please๐Ÿ˜ฉ๐Ÿ˜ฉ๐Ÿ˜ญ Ya Omri is sorry._
Seda ta gama waina sa sannan ta d'au sabi ta tura masa inda yata yaba kyanta, na sosai yaso posting hoton amma tuna Nazeefah kan iya gani seya fasa, baya son abinda ze sake had'a kansu.

Sa6anin kullum yana isa gida Amal ta taresa yau harda hugging nasa.

"Yau turare na baya wari?" Ya tambayeta dan kuwa sede be matso kusa da ita ba seta toshe hancinta wai turarensa wari yake mata. Kai ta gyad'a tana masa murmsuhi "Welcome back Ya Omri."

"Jiki da sauk'i kenan."

"Alhamdulillah."

"You look so takeaway Rania."

"Thank you Ya Omri."

"Toh ya baby na? Kin bata abinci?"

"Mun sha kokon daka had'a mana kafin ka fita office har sau biyu."

"Mashaa Allahu, ya rage ko a k'ara had'a wani?"

"Ka bari seka huta besides na fara aiki mafa da hannun nawa kaga" ta d'ago hannun nata mey targad'e tana juyawa a idonsa. "Alhamdulillah, My Rania is such a strong woman Allah k'ara miki lafiya Sweetheart."

"Ameen Ya Omri mu k'arisa ciki" rage kayan jikinsa yayi ya ragar da shorts zallah sannan ya haura gado ya sameta inda take mik'i da handout rik'e a hannunta tana karantawa. Tamkar d'an yaro ya haye jikinta ya kwanta had'e da saita kansa dai-dai saitin k'irjinta da suka ciko tim. "Ya Omri zafi suke min kad'an gyara" tayi saurin sanar dashi.

"Ze daina Rania" yace da ita yana sake cusa kan nasa cikin k'irjin nata "Bacci nakeji na gaji daga aiki" murmushi ta sakar kad'an sannan ta zagaye hannunta a bayansa tana mey cigaba da karantunta, daga haka har itama baccin yayi awon gaba da ita. Da goshin Maghrib Afzal ya farka a hankali ya raba jikinsa daga nata ya fad'a bayi yayi alwala sannan ya tada ita itama.

Bayan da ya dawo daga sallan Isha ya had'a mata kokonta shi kuma ya had'a quarker oats yasha daga nan suka koma d'aki sukayi wankan su tare kaman yadda suka saba. Sede tun da suka kwanta Afzal keta tak'ura mata, itako tak'i barinsa chimma abinda yake da niyya se wani shusshuresa take shiko kaman maye ya kasa hak'ura.

"Ya Omri mana kana fa da office gobe."

"Rania yanzu duk hak'urin nan da nayi baki gani ba? I need you today hak'uri na ya k'are."

"Ni banida lafiya" ta amsa tana tattare bargon a jikinta.

"Na sani ai Allah k'ara miki lafiyan amma yi hak'uri ki barni kinji?"

"Ni gaskiya sena samu sauk'i."

"Haba My Rania yi hak'uri kinji? Kad'an kawai shikenan."

"Yimin wayo de" ta amsa tana cire hannunsa daya samu ya sak'ala cikin rigarta.

"Yi hak'uri kad'an nace I promise a hankali zan yi miki" rok'arta ya cigaba dayi har seda ya samu ya shawo kanta haka har suka gamsar da junansu. Tana rik'e a hannunsa bacci yayi gaba da ita. Shi kansa baze iya describing yadda yake son Amal yake kuma jinta a ransa ba, all he knows is that bayida irinta.

Kasancewar washegari
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment