Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

suna tare da Amal. Bayan lectures ya k'are yau Amal ta shiga sauri don kar ta rasa keke napep kasancewar mai napep nata bai ji dad'i ba ta sanar da Afzal yazo ya d'auketa kuma tana ganin duk sasa aiki ne gara kawai ta tafi da kanta.

"Ya naga kaman kina hanzari yau lafiya?" Maamah data karanchi saurin da Amal keyi ta tambaya.

"Wallahi me napep d'ina ba lafiya gashi kinga yamma yayi banason in rasa abu hawa."

"Toh ki bari mana idan Yaya na yazo d'aukana se muyi dropping naki ba a Jiddari kike ba? Kinga mu muna Polo layin duk d'aya ne."

"How kind of you, but na gode karki damu I can manage."

"No please Amal I insist dan Allah kibari mu sauk'eki yau."

"Maamah da kin bari kawai I don't want to he a burden."

"C'mon karki damu kode tsoron Yayan nawa kike tun kafin ki gansa?"

"Kusan hakan" ta amsata tana jin kunya.

"Karki damu Yaya baida matsala muje mu zauna akan slabs d'incan yanzu ze zo" ba gardama suka k'arisa suka zauna bada dad'ewa ba sega 406 na yayan Maamah ya iso, k'arisawa tayi ta mishi bayanin situation d'in gladly yace ta kira Amal d'in suyi dropping nata. Gidan baya Amal ta shiga ta zauna had'e da gaishesa kanta a sauk'e, shiko tun da ta taso yake kallonta haka kawai ta mishi kyau dukda cewar bawai wani makeup take sanye dashi ba. Throughout the drive yake satan kallon Amal ta mirror har Maamah ta gane, ba yadda Amal batayi dashi ba ya sauk'eta a bakin junction zata k'arisa ciki da kanta amman yak'i sam wai se ya kaita har k'ofar gidansu hakan kuwa akayi, godiya tayi musu sosai da suka sauk'eta. Bata kaiga shiga gida ba se ga call na Afzal, bayan ta d'aga yake tambayarta ko tana school ne har yanzu shi sam baida labarin rashin lafiyan driver'n nata se yanzu da ya kira mutumin don jin koya sauk'e Amal.

"A'a yanzun na iso gida ko shiga ciki ma banyi ba."

"Mesa baki kirani nazo na d'auke kiba?"

"Yaya I'm sorry amman naga kaman duk saka wahala ne tunda zan iya tahowa da kaina."

"Ba fata ba amman idan aka sace min kefah?"

Dariya kad'an ta saki "Haba Yaya sekace yarinya, bale ma brother'n friend d'ina ne ya kawo ni sun rage min hanya." Alokaci guda kawai yaji ransa ya 6aci yayinda wani irin zazzafan kishi ya mamaye masa zuciya. "Motan wani kika shiga?" Ya tambaya cike da 6acin rai da tsiwan daya mugun firgitar da Amal, sosai ta razana game da tsawan da ya daka mata.

"Yaya wan k'awata nefah" ta furta a hankali cike da tsoro.

"Meaning? Don wan k'awarki ne se akace ki shiga motanshi? Inda kuma bakinsu a had'e da k'awar naki suka yi miki wani abu fah? Ke bakisan ba a yarda da mutum so easily bane yanzu?" Ya k'ura ta.

"Yaya I'm sorr-" katse wayan ma yayi gabad'aya a kanta. Da mamaki ta sauk'e wayan daga kunnenta tana mamakin yadda ransa ya 6aci lokaci guda haka, tana iya rantsewa bata ta6- jin 6acin ransa ba se yau. Yau ta shiga uku ta 6ata wa Yayanta rai ita da tasan ransa ze 6aci haka dama bata sanar dashi gaskiyan lamarin ba kokuwa da bata amince ta shiga motan wan k'awar nata ba. Yanzu ta ina zata fara bashi hak'uri????



RANA D'AYA
#RD

Love... King Miemiebee👄✨
[13/08, 00:34] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣

💦💦 🍃🍃🍃
*RANA D'AYA!*
💦💦 🍃🍃🍃
June, 2018
beeenovels.blogspot.com

_Written by Miemiebee👄_


*PAGE 1⃣3⃣*



Da mamaki ta k'arasa ciki ta watsa ruwa taci abinci, dab bayan sallan Maghrib ta gwada kiran Afzal sede kamar yadda ta k'udurta a ranta haka mutuminku yak'i d'aukan wayan, sau biyu take kiransa ta regular line nasa amman yak'i d'agawa, private line nasa ta kira next. nan ma yak'i d'agawa dagangan dan kuwa wayan na a gefensa yana mik'e kan gado sede ya kalla ya cigaba da zura wa ceiling ido. Sak'o ta tura masa ta text message tana basa hak'uri nan ma yak'i reply bayan ya karanta. Duk da haka bata kariya ba, ta bisa whatsapp ta tura masa messages bil adad tana basa hak'uri tana kuka duk seya karanta ya kuma k'i reply abinda yafi ci mata rai kenan. Taya har ze karanta amman baze bata reply ba? Yau ina zata sa kanta? Assignments nata data d'ibo zatayi ma taji baza ta iya ba tsan-tsan tashin hankali.

Dab tazo kwanciya wajajen k'arfe goma na dare ta sake kiran lamban nasa sai da still Afzal yak'i d'agawa, ganin ba mahalicci se Allah kawai ta tofe addu'o'inta ta kwanta abinta duk da cewan ba baccin take ji ba, gabad'aya hankalinta yana kan halin da Afzal ke ciki. Ita da tasan hakan ze biyo baya wallahi da bata shiga motan Ya Abdul d'in bama tun farko.

Washegari lectures nata na safe na k'arewa tama driver'nta waya ya dawo da ita gida. Aldeb da zo6o me dad'in gaske ta d'au lokacinta ta had'a ta zuba masa a silver flasks nasa sannan ta tanadar wa Papi da Mami nasu a gefe. Wanka ta sakeyi ta canza kaya tasa matching color hijab ta feffeshe da turare sannan driver ya sauk'eta a office nasu Afzal. Tun da ta ga motansa a fake hankalinta ya d'an kwanta. Tana isa bakin office nasan a sama tayi knocking inda ya amsa da "Come in" a hankali ta bud'e ta shiga. Sosai mutuminku yayi murna da kuma mamakin ganinta amman ya dake a gun yana wani mozewa, kansa ya kawar tamkar ba mutum neba ya shigo office d'in had'e da cigaba da aikin dake gabansa. Ajiyar zuciya ta sauk'e ta k'arisa ciki ta zauna kan kujerar da ta saba zama a kai kullum tare da yin shiru.

Ganin be da niyyan yi mata magana na kusan tsawon minti biyu kawai se ta gaishesa "Yaya good afternoon" Yadda kuka san da kurma take magana haka yayi mata, ko kai be d'aga ba balle ya kalleta se rubuce-rubucen sa kawai yake.

"Yaya gaisuwan nawa ma bazaka amsa ba?" Ta tambayesa cikin kamala a hankali tamkar wacce take shirin yin kuka. "Yaya so kake ne ciwon zuciya ya kamani in mutu? Dan Allah kayi hak'uri" har anan be ce mata komi ba.
"Yaya I'm sorry, I'm so sorry" ta fad'a had'e da rik'e kunnuwanta yayinda idanunta suka soma cikowa da hawaye.

"Yaya yanzu se nayi kukan zaka mun magana?" Yanzu kam har hawayen sun soma d'iga sede har anan Afzal yak'i koda d'aga kai ne ya kalleta.

"Toh shikenan" tayi maganan tana share hawayenta "Bari in koma inda na fito tunda ko d'aga kai bazaka iyayi ba ka kalleni" ta ja hanci "Ga Aldeb da zo6o nan na kawo maka, I'm still saying sorry" tana kaiwa nan ta mik'e, bata kai ga taka k'afarta ba Afzal ya mik'a hannu ya rik'e hijabinta, chak ta tsaya gun ba tare da tace komi ba se faman kukanta take a hankali.

"Don't go" yace da ita a hankali dad'i sosai taji amman ta fake itama "Ni ka sake mun hijabi."

"Nace ki tsaya" ya nanata cikin tattausar murya. Juyowa tayi tana kallonsa yayinda hawaye ke d'igowa sama-sama daga idanunta. "Bayan tun jiya ina baka hak'uri kak'i kulani bale ka hak'ura ni ka sakeni inyi tafiya ta dama tun ba yau ba na gano ba ka sona."

"I'm sorry toh zauna kin ji?" Ya ce da ita a hankali.

"Nifa tafiya ta zanyi ka sakeni kurum."

"Lily nace ki zauna."

"Toh haka akeyi ne?" Ta tambayesa had'e da turo d'an bakinta. "Ko baccin kirki na kasa yi jiya, I called and texted you severally sarai kana gani kak'i responding d'ina, Wallahi if only ka san yadda hankali na ya..." ba se kawai ta rushe mishi da kuka ba. Yana tayi shiru tayi shiru kar ta tara masa jama'a amman inaa tak'i jinsa, se kukarta take harda me sauti. A haka ne har PA'n Afzal ta lek'o take tambayan ko lafiya. "Lafiya Blessing don't mind her kukan banza take" yace da PA'n sannan ya samu ta ja musu k'ofan ta fice.

"Yanzu Lily ni ke miki magana amman bakiya ji? In ce miki kiyi shiru kik'i yi? Se kin tara mun duka mutanen office d'in tukuna zaki ji dad'i?" Itama yadda kuka san bada ita yake ba, se aikin kukanta take harma tana k'ara sautin, gaban hijabinta ko lis ta jik'asa da hawaye. "Toh kiyi hak'uri, yi hak'uri kibar kukan haka" ya soma pampering nata yana bata hak'uri.

"O'o ba tun jiya nake baka hak'uri ba kak'i ji na."

"Toh ba ya wuce ba?"

"Ni seka cemin ka hak'ura tukuna" ta fad'a tana zum6uro baki yayinda ta 6oye kusan rabin fuskarta k'ark'ashin hijabinta.

"I'll think about it keep quiet first."

"O'o ni seka ce ka hak'ura" ta sake sa wani kukan sanin sarai ya tsani hayaniya.

"My Goodness!" Ya furta cike da tashin hankali yana susa temple nasa. "Da gan-gan kike ko?"

"Ni se kace ka hak'ura" ta kuma sa wani kukan.

"Fine! Naji na hak'ura shikenan kiyi shiru."

"Ka hak'ura dagaske? Bazaka sake ignoring calls d'ina ba?" Se anan ta ciro fuskan nata gabad'ai tana kallonsa. Ba k'aramin dariya ba reaction na fuskarta yasanya sa da k'yar ya had'iye dariyan ya gyad'a mata kai "Bazan sake ba" ya sanar da ita.
Se anan taji sanyi a ranta ta shiga share hawayenta, hannu ya cusa a aljihunsa ya ciro hanky ya mik'a mata. Ba gardama ta amsa ta share hawayen nata dashi bayan da ta gama ta mayar mishi ya amsa ya mayar cikin aljihunsa.

"Wato taurin kan nan namu na nan har yanzu ko?"

"Wani taurin kai kuma Yaya?" Ta tambayesa tamkar bata fahimci abinda yake nufi ba.

"Baki na nawa ina ce miki kiyi shiru amman ki k'i yi?"

"Toh ba kaine ba, inata baka hak'uri amman kaki hak'ura."

"Toh ai kece kika janyo."

"Kawai don na shiga motan wan k'awata? Believe me da nasan hakan ze 6ata maka rai wallahi bazan soma ba."

"Na ji and I'm sorry for making you worried and restless jiya but on a serious note bana son in sake jin kin shiga motan wani Lily, komin ya situation d'in yake kuwa, duk randa driver'n ki bashida lafiya call me up and let me know if I'm too busy to come pick you up zan tura driver'n office kona gida yaje ya d'auko ki banason in sake jin kin shiga motan wani, kinji?"

"Na'am Yaya, in shaa Allah anyi na farko anyi na k'arshe."

"Masha Allah that's my Lily."

"Amma Yaya, Maamah is my very good friend bana tsammanin har zata iya cutar dani. I trust her."

"Ni bance miki Maaman ne ban yarda da ita ba wan nata ne ban yarda dashi ba."

"Toh amma-"

"Lily enough, nide na fad'a miki in ba wai fad'a kikeso muyi ba toh karki sake shiga motanshi ko na wani banda nawa kinji?"

"Naji Yaya" ta amsa tana mamakin iko irin na Afzal lallai wannan da ace yana da k'anne da sun taso da discipline don ba k'arya yayi kalan yayun dake jibgan k'annensu idan suka tafka rashin hankali.

"Ya lectures toh?" Yayi maganan yana janyo cup a saman fridge nasa don tsiyaye Aldeb d'in. "Kawo in tsiyaya maka" tayi maganan tana k'ok'arin amsan cup d'in "Lectures Alhamdulillah amma ba dad'i mutun kullum 7 ya fita sekace d'an secondary school."

"Lol toh me maraban ki da 'yan secondary school d'in?"

"Yaya wallahi akwai difference."

"Toh big girl naji" yayi maganan yana amsan cup d'in "Thank you" yace da ita.

"You're welcome" chan tace, "Ba kace yayi dad'i ba" tare da had'e gira.

"Ina santi ze bar ni in fad'a? Rabonki da ki kawo mun Aldeb har na manta."

"Forgive me Yaya daga yanzu kam zanyi k'ok'ari koda once in a week ne ina kawo maka."

"Keda kike school yanzu? Don't bother."

"When it comes to my Yaya komin yaya ne se an mishi abinda yakeso so kar ka damu."

"Hakane?" Ya tambaya yana me jin dad'in amsan data basa.

"Sosai ma kuwa."

"Toh shikenan thank you."

"You're welcome, I guess I can go now, kaima ka samu ka kammala aikin dake gabanka, zani gida inje inci abinci yunwa nakeji."

"Let's eat out it's almost lunch time" yayi maganan yana duban agogonsa. Ba musu ta jirasa ya d'an k'imtsa kan table nasan sannan suka wuce restor suka ci abinci, bayan sun gama ci ya sauk'eta a gida sannan ya komo office.

****
A kwana a tashi be ragar da komi ba se gashi yau su Amal suna rubuta first semester exams nasu. A gida kuwa ta fannin Nazeefah da Afzal suna nan kaman kayan wanki ba cigaban komi, don koda tace wa Mummy kan zata fara yiwa Afzal girki koda wasa bata ta6ayi ba, ko tace zatayi se wata ra'ayin ta hanata ta hura mata kai kan cewa ai yanzu da zaran ta fara yi masa girki ze ga kaman sonsa take tana son su shirya kar tayi, itako seta biye wa ra'ayin. Amma se de bataji Afzal na waya da Amal ba, se zuciyarta tayi mata k'ona, zama take ta gabzi kukanta ta godewa Allah a hakan kuma ta tsaya tana cewa ita ba son Afzal take ba.

****
Amal da Maamah ne ke zaune akan slabs suna karatun paper'nsu na gobe Maamah ta fara janta da hira.

"Friendy?" Ta kirata.

"Na'am" Amal ta amsa cike da fara'a.

"Har yanzu fa baki bani amsa ba wallahi Ya Abdul ya tak'ura min."

"Nikam kibar zancen can Maamah muyi karatu" Janye handout d'in Maamah tayi. "Ha'a! Ya da haka?" Amal ta tambaya tana k'ura mata ido.

"Wallahi yau kam sekin bani amsa haba mana friendy yanzu kodan k'awancan dake tsakaninmu ma baza ki bawa Ya Abdul dama ba? Wallahi he's a very cool and gentleman if you get to know him, baida matsala sam."

"Na sani Maamah bazaki gane bane."

"Mey ne bazan gane d'inba? Kede kawai kice kin k'i min Ya Abdul kuma shikenan na gode ni kika k'i ba shi ba wallahi."

"Wallahi ba haka bane don Allah karkiyi magana haka."

"Ya kikeson inyi toh? Yaya na fa kikayi rejecting tun yaushe nake k'ok'arin shawo kanki amman ko lambarki kin hana in basa wallahi ko baccin arziki Ya Abdul bai samu kwana biyun nan as kullum tunanin ki yake tun kan ranan daya rage miki hanya har izuwa shekaran jiya da ya kaimu Unimaid garden."

"Ji k'arya wai ko bacci baya iyayi a d'akinsa kike kwana ne da zaki san hakan?"

"Eh yimin wayo ki canza topic d'in" Maamah ta fad'a tana juya mata ido.

"Lol yi hak'uri toh."

"Nide ba hak'urin da zanyi sekin amince in bawa Ya Abdul numbanki."

"Ke dad'i na dake naci wallahi kibari mana mu gama karatun tukuna gobe ne fa exams d'in."

"Friendy seconds nawa ne ze d'auke ki kice 'ki bashi' kawai? Wallahi rashin mutunci ba kyau."

"Nikam kode biyanki Ya Abdul yayi ne? Dagewan naki fa yayi yawa."

"Wallahi sam ba haka bane, you're just the perfect girl for him wallahi tun da nasan Ya Abdul 'yan mata biyu ya ta6a yi ta farkon har sun fara zancen aure Allah yayi mata rasuwa se kuma ta biyun sunyi nisa itama yazo ya gane tana son abokinsa se suka rabu daga baya tayi-tayi ta dawo mishi amman ina he's already heartbroken."

"Allah sarki Allah ya jik'an ran musulmi."

"Ameen" ta amsa, "Kuma kinga kusan wata shida kenan da faruwan hakan ban sake jin yana neman wata ba se daya kafa idanunsa akanki Wallahi he's intentions to you are clear."

"Na ji kuma na gamsu Maamah kawai ina ganin this's not the right time for me to be in a relationship ne kiga part one fa kawai nake I have almost 5 years to go Ya Abdul baze iya jira na ba."

"Wallahi ze iya, he is willing to wait till forever for you."

"Hmm" ta numfasa.

"Kode kam Yayan nawa be miki bane? Yayi muni dayawa ko?"

"Haba ai kema kinsan yana da kyau wallahi gashi chocolate skinned, ga saje ga ido kaman naki a nan."

"Yana da kyau kenan?"

"Eh mana" ta amsa without knowing when "I mean ni ba ruwana ki rufa min asiri kiban handout d'ina" ta shiga canza zancen.

"Amal pleasee ki amince pleasee wallahi ko na basa lamban naki baze kiraki ba se mun gama exams shi da bakinsa ya cemun haka."

"Toh naji ba se kin cinye ni ba ki bashi shikenan?"

"Yeyyyyy!!" tasa ihu had'e da hugging d'in Amal wane wacce ke neman suffocating nata.

"Toh nikam sakeni haka mu k'arisa karatun nan kinga har Azahar ya doso." Handout natan ta mayar mata suka cigaba da karatu suna iddawa sukaje sukayi sallah sannan kowacce tayi hanyan gida. Kamar yadda Ya Abdul ya d'au alk'awari, seda su Amal suka kammala exams bayan kwana biyu ya buga mata waya, lokacin tana zaune tsakar gida tana bita wayan ya shigo. Ganin new number yasa bata d'aga da wuri ba seda ya kusan tsinkewa. Shiru tayi da ta d'agan chan daga d'ayan 6angaren taji bak'on murya nayi mata sallama. Cikin sark'ak'k'iyar muryarta me sanyi ta amsa da "Wa'alaikumus salam wa rahmatullah."

"Amal ya kike?" Sama-sama suka gaisa dake har yanzu bata fahimci wake magana ba. "Baki gane muryan bako har yanzu?"

"Eh wallahi I'm sorry."

"Abdul Rahman ne" ya sanar da ita.

"Abdul Rahman daga ina kenan?"

Murmusawa yayi kad'an sannan yace, "Ya Abdul toh" se yanzu ta fahimta ashe de Abdul Rahman ne complete name nasa, wow. "Laa! Ya Abdul ina yini?"

"Bayan wuyan da kika bani har kin manta dani ko?"

"Haba Ya Abdul ina na isa."

"Gashi kuwa."

"A'a wallahi kullum da Ya Abdul Maamah ke addressing naka bata ta6a ambaton full name naka ba kaga ko bazeyi in gane wanene ba at first thought" ta mar bayani a hankali.

"You're right so ya hutu?"

"Hutu Alhamdulillah ya aiki?"

"Lafiya k'alau kun gama exams ko?"

"Eh wallahi."

"Toh Allah ya bada sa'a."

"Ameen thank you."

"I thought I should call and check up on you."

"Ayyah to nagode sosai a gaishe da gida."

"Zasuji take care" a haka sukayi sallama. "Phew!" Ta numfasa had'e da ajiye wayan a gefe sannan ta cigaba da karatunta. Tun daga ranan Ya Abdul ke kiran Amal suna gaisawa, kar kuma kuyi tsammanin irin kira barkatai ba fasali d'innan ne, no a sati befi suyi waya sau biyu ba idan yayi yawa shine sau uku ko hud'u. A hankali shak'uwa ya fara shiga tsakaninsu ba abinda ke burge Amal a gun Ya Abdul kaman yadda yake yawan sanyata dariya, sede basuyi waya ba koda ranta a 6ace ne seya faranta mata da kalamun sanya dariyansa, he's so jovial Maamah batayi k'arya ba da tace bashida matsala. A satin da zasu koma makaranta ne yayi insisting se ya zo sun had'u mutumiyarku da shegen tsoro kam ba se ta shiga yi masa corner-corner ba. Yau tace zata islamiyya, gobe tace zata raka Mami gidan suna ko makamancin haka daga k'arshe de ya gane tsoro take ta ke6e dashi shi kad'ai kuma bega laifinta ba hasali ma yaba mata yayi sosai hakan na nufin tasan abinda takeyi ne. Don haka ya tambayeta idan ze taho da Maamah zata amince ta fito? Tuni ta amince. Hakan ko suka shirya ranar Laraba da yamma se gashi da Maamah sun k'ariso gidansu, har ciki Maamah ta shiga suka gaisa dasu Mami sannan suka fito da Amal inda Amal ta zauna a gidan gaba ita kuma ta koma baya. Bayan gaisuwa suka sha hira sosai dukansu ukun cikin motan, se dariya Ya Abdul yake sanya su barin ma Amal dake dariya harda k'walla, kusan k'arfe shida Ya Abdul yace ya kamata su tafi, don dad'in hira Amal ji take kaman kada su tafi. Dab tazo sauk'a daga motan kenan ya mik'a mata wata leda, ta kar6a ita kuwa tak'i ba yadda beyi ba amman tak'i, daga k'arshe seda ya baiwa Maamah ta shigar mata dashi ciki har cikin d'akinta.

**** Bayan ta dawo ciki ta wuce d'akinta ta fito da ledar, zazzagewan da zatayi ta tarar da chocolates turum, ba wanda babu aciki da wanda Afzal ya koya mata ci da wanda se yau ma ta ta6a ganinsu, abu de yayi kyau. Haka nan ta 6oye abinta cikin akwati tana ci a hankali a hankali. Bayan sallan Isha ta kira Ya Abdul tayi masa godiya inda suka sake ta6a hira kad'an sannan sukayi sallama. Ganin goma be cika ba ta yi tunanin kiran Afzal da alama aiki yayi zafi ne ko nemanta bayya yi kwana biyu, daman yayi tafiya zuwa Lagos for a meeting, yau k'imanin kwana biyu zuwa uku kenan. Tana kiransa on the first ring ya d'aga, "Yaya kayi wuyan gani" ta soma cewa.

"Wallahi Lily, I've been so busy ko time na wayan ma bani dashi."

"Allah sarki ya kake ya aikin?"

"Alhamdulillah ya gida dasu Mami?"

"Lafiyansu k'alau d'azu take cewa kwana biyu bata ji motsinka ba nace ai kayi tafiya, she's sending her warm greetings so as Papi."

"Toh ayya ina amsawa."

"Yaya I miss you yaushe zaka dawo?"

"Saturday in shaa Allah."

"Toh Allah kaimu barin barka haka nasan a gaje kake."

"Alright Lily thank you have a peaceful night rest."

"You too, seda safe" da haka sukayi sallama.

****
Nazeefah ce zaune gaban Tv ta sa channel na Zee world tana kallon wata indian series se faman buga tsaki take, ga takaicin rainin wayon da ake tayi a series d'in ga na rashin Afzal kwana biyun da tayi bata sanyasa a ido ba bata kuma ji muryansa ba, ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, se a yanzun take sake jaddada cewa lallai-lallai ta fad'a kogin sonsa. Seta d'au wayarta zata kirasa seta kashe ta fasa, tayi hakan sau fiye da a k'irga. Daga k'arshe de ta dage ta kira har ya shiga yana ringing, se cewa kanta take ai don ya sanar dani zeyi tafiya ne yasa zan kirasa, da ace tafiyansa kawai ya kama yayi wallahi ko ta kansa bazan yi ba bale har in kirasa.

Ya kusan tsinkewa ya d'aga kasancewar har ya fara bacci. Shiru tayi bayan da ya d'agan kaman yadda shima yayi shiru
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment