Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

"Excuse me" tace da shi tare da nufan dining dan d'aukan kiran, ba k'aranin har6wa zuciyanta yayi ba ganin Safiyya ke kira shin wai meke damun yarinyar nan ne haka? Rejecting call d'in tayi take nan Afzal ya sake buga mata har rawa jikinta yake ta kuma rejecting juyawan da zatayi taga Afzal gab a bayanta.

"Muje ka watsa ruwa ko? Bari in sirka maka ruwan." Kafin tace zata taka k'afa Afzal ya rik'o hannunta "Who's calling?" ya tambayeta.

"Ermm.. ermm Airtel ne Wallahi kasan su da kiran mutum anyhow." Wayan Safiyya ya d'aga ya sake dialing lambar nata nan ya shiga ruri kafin tace zata katse yasa hannu ya hanata "Ba Safiyya ke kira ba? Ki d'aga mana." Kakkarwa ta shiga yi a wajen bata san lokacinda ta sake wayarta a k'asa ba da ta hango wayan Safiyya rik'e a hannunsa. B'ari bakinta yake yayinda cikinta ya d'ura ruwa.

"Ya Rou-" wani irin zafaffan mari me rikitarwa ya zabga mata, wani irin rikicaccen ihu tasa bata hankara ba ya sake kai mata wani abinku da farin fata take fuskan nata yayi ja yatsun Afzal biyar suka bayyana akai.

"Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri" ta furta cikin wahala da tashin hankali har wani kurma-kurma ta fara jin kanta tsan-tsan zafin marin.

"I can't believe your guts Nazeefah, how could you? For all these while ashe wasa kike mun da hankali? Wace irin munafuka ce ke? Ma tukun mey Amal ta tare miki? Tell me mey Amal ta tare miki da kika za6i ki k'untata mata kisa in tsaneta ki shiga tsakanin mu haka? Baki tsaya anan ba har seda kika sa aka kad'eta? Are you forreal? So kike ta mutu?"

"Ya Afza-" wani marin ya sake kai mata dan yadda ko muryanta baya son saurara. Ihu Nazeefah tasa seda Hindu dake bacci ta fito daga d'aki a kid'ime ganin Afzal ne da kansa ta ja k'ofanta ta sa key.

"Mey ta tare miki nace?!" Hannunta ya damk'o yana yi mata wani irin rik'o tuni k'asusuwanta suka shiga yin k'ara "Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri kar ka karya mun hannu."

"Answer me then mey Amal ta tare miki?"

"Zan fad'a maka zan fad'a maka amma dan Allah ka sakeni wayyo Allah na" sassauta rik'on nasa yayi. "Speak up! Idan kika bari na sake tambayanki wallahi na lahira seya fiki jin dad'i, mey Amal ta tare miki nace?"




RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨




Miemiebee Novels

Wednesday, 15 August 2018
RANA D'AYA!
BY MIEMIEBEE
PAGE 36



Cikin tsananin kuka da azaba tace, "Mene Amal bata tare mun ba Ya Afzal? Komi ma Amal ta tare mun, tamkar katanga haka Amal ta shiga tsakani na da samun soyayyarka, yadda kake sonta ba haka kake sona ba, yadda kake jin zaka iya sadaukar da rayuwanka mata ba haka kake ji da ni ba, komi Amal komi Amal, ko shopping muka fita seka tambayi ina na Amal, wayanka duk hotunan Amal ne aciki, girki nasani Amal ta fini iyawa, tafi ni iya tarerayarka, ta fini iya nuna maka soyayya, ta fini kyau ta fini fasali, ta fini ilimin boko da na islamiya gabad'aya komi da nake tunani Amal ta fini da shi. Gashi da shigowanta gidan nan dududu bata fi wata uku ba amma har ta d'au cikinka ni shekarana uku da watanni na kasa yin hakan-"

"Amal na da ciki?" Ya katseta cike da k'in yarda.

Kuka take sosai ta gyad'a mai kai "Amal na d'auke da cikinka Ya Afzal bazan iya ba, ta ko ina Amal ta fini taya kake tsammanin zan iya yin kishi da ita. Ya Afzal I love you dan Allah karka ga laifi na wallahi son da nake yi maka ne ya janyo komai, akanka zan iya sa ayi ma mutum kallon me ta6in hankali ko ciwon aljanu, akan ka zan iya yin duk wani irin mak'ircin da kake tsammani, akan ka zan iya sa mutum ya zargi matarsa akan ka zan iya sa a bige mutum dan a illatamun shi, I love you Ya Afzal, akan soyayyarka kuma zan iya yin komai-" zuciya ne ya d'ibesa ya sake gaura mata wani marin, na hud'u kenan k'asa ta sauk'a yayinda ta shiga raira kuka.

"Kinsan Amal nada ciki kika sa aka kwa6eta saboda ki kashe ta ki kashe abinda ke cikinta Nazeefah?" Har yanzu ya kasa amincewa da hakan. "So it's all been you these while, duk kalan mak'iricin da kika shuk'a har kika fitar da Amal daga d'akinta be isheki ba no har sai kin sa a kwa6eta? Ashe haukan naki har ya kai stage d'in da zaki iya yin kisan kai? D'ana kikeson ki kashe? Kuma a haka kike cewa kina so na? You're insane Nazeefah, ki sani na tsaneki, na tsani duk wani mey k'aunar ki, I hate you Nazeefah."

"Ya Afzal dan Allah kar kace haka, Ya Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba, a shirye nake da in hallaka duk wanin da yake da shirin shiga tsakani na da kai Ya Af-" zuciya ne ya d'ibesa ya shiga yin ball da ita a wajen. Belt nasa ya zare ya shiga zaneta ta duk inda zanan ya sauk'a dama gashi vest ne kad'ai a jikinta da wandon rigan bacci iya guiwarta.

D'an banzan duka Afzal yayi mata sekace ya samu ganga ko jaki, dukan da tunda baabarta ta haife ta ba a ta6a yi mata irinsa ba seda yaga ta fara yin amai a wajen sannan ya barta se huci yake.

"Ki bud'e kunnuwan k'ashin nan naki ki saurareni da kyau Wallahi tallahi kin deji rantsuwa ba kaffara ko? Idan abun ya samu lafiyan Amal mey hanani kasheki a gidan nan se Allah Nazeefah, da hannu na zan kasheki nace a dai-dai ina kika sa aka bigeta?" Nazeefah ba bakin magana banda kuka ba abinda take iyayi ga yadda jikin nata ya tashi nan take, belt d'in ya sake zabga mata "Ba magana nakeyi maki ba?"

"Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri na tuba."

"Aww bazaki amsa ni ba?" Bata hankara ba ya sake zabga mata belt d'in Nazeefah se ihu take tana kuka tana neman agaji amma ba wanda ze iya taimaka mata, ba mai gadi Hindu kuwa uwar tsoro tuni ta rufe kanta a d'aki se hasbnullahu wa ni'imal wakeel take ta nanatawa. "Answer me! A ina kika sa aka kad'eta?"

"Wallahi a dai-dai bakin makaranta ne dan Allah kayi hak'uri na tuba Ya Afzal."

"No Nazeefah you're never sorry and I swear to you, na miki imani da Allahn da raina yake hannunsa you must pay for this, you must pay for everything you've put Amal go through I don't care if it costs you your life, sekin biya abinda kikayi wa Amal" yana kaiwa nan ya wuce kitchen ya kulle k'ofan da key ya zare sannan ya wuce d'akinsu ya tattara spare keys na gidan ya sanya a aljihunsa ya dawo ya d'aga wayanta ya fice ya kulle k'ofar ta waje yadda bata isa ta kira kowa ba bale tayi tunanin guduwa. A 360 yabar gidan nata ya wuce chan bakin unimaid ya shiga tambayan mutanen dake kusa batun hatsarin da akayi d'azu ina aka kai yarinyar dayawa suka ce basu sani ba da k'yar ya samu wani mai shagon da yace yana da tabbacin TH suka wuce tunda shine asibitin dake kusa da nan d'in. Be 6ata lokaci ba ya wuce TH d'in inda ya zarce emergency ward ya shiga neman d'akin da Amal take ciki.



******
"Se anje an siyo jini ba jini a blood bank and the patient is losing so much blood" cewan likitan dake aiki akan Amal ma wata nurse. "Kuje ku nemo jinin yanzu type O- (negative)" a guje ta fito inda suka ci karo da mutumin da ya kawo Amal da driver'nsa.

"Ya nurse? Ya jikin patient d'in?" Yayi saurin tambayarta.

"I'm sorry sir amma patient d'in ta rasa jini sosai wanda dole se anyi mata transfusion se gashi anje blood bank kuma babu type nata."

"Wace blood group ce?"

"O-" ta sanar da shi.

"O-?"

"Yes Sir."

"Idan ban manta ba nima blood group O ne."

"Sir O+ daban O- shima daban O+ ze iya receiving daga O+ kaman shi da kuma O- amma O- dole se O- kaga kuwa yanzu idan kai O+ ne bazeyi ka bawa patient d'in jini ba."

"I'm sure O- nake nima."

"Sir you have to be certain."

"Amma kun tabbata inda zakuje neman akwai blood group natan?"

"Gaskiya bamu da tabbacin hakan sir se munje mu duba tukuna."

"Toh ai duk 6ata lokaci ne wannan ina kuma ace anje chan d'in babu blood group natan? Ai mun koma baya."

"Hakane kuma Sir."

"And mey ze faru idan ba ayi mata transfusion d'in da wuri ba?"

"Based on tests da muka gudanar sakamako ya nuna tana d'auke da juna biyu toh muddin ba ayi supplying nata da jinin akan lokaci ba eventually zata iya rasa ranta da kuma abinda ke cikin nata."

"Muje ku gwada jinin nawa in irin nata ne se ku d'iba, bags nawa kuke buk'ata?"

"D'aya da rabi Sir."

"Let's go muje ku d'ibi nawa kusa mata da wuri kafin lokaci ya k'ure."

"Sir are you sure?"

"Let's go we don't have time" haka kawai wannan Alhj yaji wani irin strong connection tsakaninsa da Amal duk da cewan bey santa ba, amma jinta yake a kusa da zuciyarsa. Nan da nan akayi d'akin d'iban jini da shi amma da fari aka gwada blood type nasa inda yayi matching dana Amal, bayan nan aka kuma wani gwajin don tabbatar da cewa jinin nasa baya d'auke da wani cutan zamani. Anan aka zuge leda d'aya da rabi kamar yadda nurse d'in ta fad'a sannan akayi masa recommending magunan k'ara jini da zena sha dan ya maido masa da jinin nasa.

Godiya sosai mutanen asibitin suka tayi masa. Nan da nan akayi infusing wa Amal aka bata taimakaon gaggawa da ikon Allah kuma aka samu aka ceto cikin nata ba tare da wani abin ya samesa ba.
Har anan su Mami basu da labari saboda ko waya Amal bata fito dashi ba bale a lalumo layin wayansu aciki, saboda acewarta test kawai zatayi ta dawo gida se bata damu ta fito da wayan ba.

Har anan wannan Alhaji da ya ba wa Amal jinin jikinsa be tafi ba ya na nan yana jiran farfad'owanta. Tana farfad'owa nurses sukayi masa magana nan ya k'arisa cikin d'akin inda ya tarar da ita kwance akan gado da bandeji nad'e a kanta da k'afarta, da kuma wani a hannunta wanda aka nad'e mata shi tun daga wuya dan support da alama shima hannun ta samu matsala ne. Sosai ya tausaya mata barin ma da yaji tana da ciki.

"Ga wannan shine mutumin da ya baki jinin jikinsa har leda d'aya da rabin da aka sa miki kyauta se kiyi masa godiya" nurse d'in tace da Amal. A hankali Amal ta shiga juyo da kanta har ta kai akan wannan mutumi. Mutuwan tsaye mutumin yayi lokacinda k'wayoyin idanunsu suka had'e. Ita kanta Amal seda taji wani iri a jikinta, tabbas bata mance fuska amma seji take a jikinta kaman ta ta6a had'uwa da wannan mutumi amma kuma ta rasa a ina. Shi ma on the other side kallon Amal yake na sosai ba tare da ya koda kyafta ido ba, ji yayi kaman sun ta6a had'uwa a wani gun amma duk yadda yayi ya kasa tuna a ina, da ya cigaba da kallon cikin idonta kuwa se gani yake kaman kansa yake kalla aciki there's something about her eyes that reminds him so much of himself, he sees himself in her. Wani irin mumunan tsinkewa gabansa yayi yayinda rayuwansa na da ya fara taho masa.

"Nagode sosai Allah sak'a da alkhairi Baba" tace da shi kai yayi saurin kad'awa had'e da sakar da murmushin dole "Ba komai 'yata sannu Allah sawwak'e."

"Ameen" ta amsa da murya chan ciki-ciki.

"Ya sunanki?"

"Amal Abdallah" ta sanar da shi haka kawai yaji gabansa na fad'i jin sunan mahaifinta.

"Mahaifiyar ki fah?"

"Jameelah Muhammad" ido ya rufe na k'ank'anin lokaci yana k'ok'arin composing kansa. Baze ta6a mancewa da wannan suna ba, ko a ina yaji sunan nan yasan sunan Jameensa ce amma kuma ai ba ita kad'ai bace Jameelah Muhammad a duniya ba, ze iya yuwuwa wata Jameelah Muhammad d'in ce. Amma idan kuma itan ce fah? Can it be? Noo da sauri ya kad'a kansa yana d'auke wannan mumunan tunani it can't be possible it can never be.

Murmushi ya sakar wa Amal "Ko zaki bada lamban mahaifinki a kirasa?" Da biyu ya tambayeta hakan don jin mey zata ce idan har tace 'eh' ta basa that means ba shida alak'a da ita idan kuwa har tace ba na mahafinta se na mahaifiyarta that means zarginsa akanta ya tabbata kawai se yaji tace "Eh."

Wani irin ajiyan zuciya ya sauk'e had'e da yima Allah godiya tunda har tana da mahaifi toh ba abinda yake zargi bane barka. Nan da nan ya zaro wayansa daga aljihu Amal ta irga masa lamban Papi wanda ya kira take bayan sun gaisa ya sanar dashi abinda ke tafe da shi inda Papi yace yanzu haka ma suna hanyan zuwa asibitin ne mijinta ya riga ya kira ya sanar da su.

"Iyayenki suna hanyan tahowa sunce mijinki har ya kira ya sanar da su" yace da Amal. A lokaci guda zuciyan Amal ya buga to the mention of Afzal's name. Idan su Mami sunayi wa Allah kar su k'ariso nan da shi, bata k'aunan sake sanya sa a idanunta har k'arshen rayuwarta, baza ta ta6a mancewa da abinda yayi mata a rayuwa ba "Toh Amal barin je inyi settling bills naki in amso miki magunanki ko?"

"Baba da ka bari ai kayi mey wuyan wannan ko iyaye na zasuyi handling dan Allah kar ka damu."

"Ba komai 'yata kede Allah baki lafiya"

"Ameen nagode Allah sak'a da mafificin alkhairi." da haka ya samu ya fice inda ya tura driver'nsa ya biya komai aka amso magunan sannan aka mik'awa nurse ta kaiwa Amal.

"Nurse?" Amal ta kirata.

"Na'am kina buk'atan wani abu ne?"

"How about my baby? Cikin na nan ko ya zube?"

"Cikin ki na nan baiwar Allah, an samu an tsayar da bleeding d'in tun kamin ya isa cikin mahaifarki ya 6ata cikin." Wani hamdala Amal ta sake "Thank you, k'afa na da hannu fa? Targad'e ne ko kariya?"

"Targad'e ne duka biyu" Tasan zato zunubi ne amma tana da tabbacin Nazeefah is behind everything, na sosai ta duba kwalta kafin ta tsallake har yashe ne bata ga wannan mota mey uban gudu ba idan ba wai dama fakonta motan yake ba. Tana sake zargin Nazeefah ce behind this saboda duk yadda akayi taji batun tana da ciki ne daga bakin Safiyya shine take son rabata da abinda ke cikinta, k'arshe kuma idan har ba a bakin Nazeefah ko Safiyya ba ba yadda za'ayi Afzal yasan tayi hatsari.

"Don't mention" nurse d'in tace da ita tana me tsamota daga duniyan tunanin data wula "iyayenki sun sake yin waya anyi musu kwatancan d'akinki yanzun zasu shigo" kai zallah Amal ta gyad'a mata sannan ta maida kallonta ga jinin da ke kan shigewa jikinta ta canula. Mamakin halin alkhairi irin na mutumin nan kawai take, yadda be santa ba, be san wani nata ba, be san daga ina ta fito ba amma har ya d'ibi jinin jikinsa leda d'aya da abu ya bata gaskiya ne na Allah basu ta6a k'arewa toh Allah ya sak'a masa da mafificin alkhairi.

****
Dab su Papi sun zo shiga k'ofan ward nasu Amal suka tarar da Afzal tsaye bakin k'ofan da tashin hankali bayyane karara a fuskansa yana ganinsu ya nufe su "Papi-"

"Dakata Afzal" Papi ya tsayar da shi ta hanyan d'aga hannunsa "Bana buk'atan jin komai daga bakinka, ka kira mu ka sanar damu abinda ya samu Baby mungode Allah saka da alkhairi kana iya tafiya dan babu wata alak'a kuma tsakaninka da Amal yanzu."

"Papi dan Allah kar kayi mun haka dan Allah kar ka rabani da Amal I beg of you please."

"Miss" Papi ya kira wata nurse. "Dan Allah ku janye bawan Allah nan daga nan."

"Bawan Allah ba tun d'azu aka sallameka ba? Baka da appointment da kowa anan bazeyi ka shiga ba nan restricted area ne dan Allah kayi hak'uri ka tafi, yes Sir how can I help you?" Ta kewayo tana tambayan Papi bayan da ta gama da Afzal.
Nan Papi yayi mata bayanin komai lamban wayansa ta amsa ta zuba cikin computer'n dake gabanta yana gama scanning ya nuna wayan da sukayi last da phone desk. "Bismillah kuzo in shiga daku."

"Mami? Mami please don't don't do this please" Afzal yace da Mami lokacin da tazo shigewa ciki "Please karku hana ni ganin Amal" ko kallonsa Mami batayi ba bale tasan yanayi ciki akayi dasu akayi directing nasu zuwa d'akin da Amal take yayinda aka bar Afzal tsaye a waje.
Kuka wane d'an yaro Afzal ya shiga yi a wajen, yau ina ze sa kansa idan su Papi suka raba sa da Amal? Ya suke son ya rayu idan ba Amal a ganga da shi? Taya suke son ya fara neman tuba idan ko kallonta bazasu barsa yayi ba? Yau ina ze jefa kansa? Tabbas ya tafka babban sokanci na k'in saurara mata da yayi lokacin da take son yi masa bayani, tabbas ya tafka babban laifi na amincewa da maganan Safiyya akan na Amal da ta kasance matarsa, ta ina ze fara bata hak'uri? Ta ina ze fara nuna mata how deeply sorry he is and how badly he's regretted everything he's done to her? Tabbas ya tafka babban kuskure a rayuwansa na amincewa da duk maganan da aka fad'a masa ba tare da ya gudanar bincike akai ba. Tabbas duk mey irin hali irin nasa yana tattare asara, masifa da kuma nadama.

***
Tunda Alhajin yaji isowan iyayen Amal ya 6oye kawai se basa jikin sa yake Jameensa ze gani. Ba k'aramin tsinkewa zuciyansa yayi ba lokacin da yaga ana shiga da Mami da Papi cikin d'akin Amal.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai yake ta furtawa yayinda jikinsa yayi la'asar. Shekaru ashirin da biyu da suka wuce kawai yake tunawa, yau ina zai sa kansa idan gaskiya ta fito? Shikenan mutunci da girman da 'yan unguwa suke basa ze rushe, shikenan reputation na family'nsa ze rushe. Shin da wani idon ze sake kallon Hajiya Surayya? (Mummy'n su Nazeefah) meke shirin faruwa da shi? Shin yanzu Amal 'yarsa ce? Shin ciki ya shiga jikin Jamee bayan abinda ya faru a tsakaninsu? Wannan ne dalilin da yasa suka baro garin Askira? Duk da cewan blood group nasu da yazo d'aya ma babbar shaida ce akan cewa Amal 'yarsa hakan baisa ya amince ba. He needs to carry out a DNA test. Test d'in da ze tabbatar masa da cewan Amal jininsa ce ko kuwa a'a.

"Alhj yanzu PA'nka ya kirani batun meeting da kake da shi da deputy governor" Driver'nsa ya sanar da shi.

"Ohh haka zamu tafi ko?" Ya amsa yana k'ok'arin composing kansa.

"Eh Alhj" daga haka suka kama hanya suka fice har anan Afzal na zaune bakin k'ofan akan wani benchi inda ya had'a kai da guiwa. Seda Alhj'n nan ya wuce Afzal ya d'ago kansa bisa ji da yayi an bud'e k'ofar a cewansa ma Papi ne yazo shiga da shi sede yaga ficewan mutum, zama ya cigaba da yi a wajen yak'i tafiya

****
"Sannu Baby" cewan Mami.

"Ya kikeji? Ya jikin naki?" Papi ya tambayeta.

Kai ta gyad'a musu a hankali "Da sauk'i" ta amsa.

"Ya Nurse meya sameta?"

Ta samu internal bleeding sannan tayi losing blood sosai bisa ga fashewan da kanta yayi bayan nan kuma ta samu targad'e a k'afarta da hannu amma ba abinda ya samu lafiyan abinda ke cikinta." Da mamaki both Papi da Mami suka juyo suna kallon Amal da alaman tambaya bayyane karara a fuskokinsu.

"Ciki?" Mami ta tambayeta "Baby kina da ciki?" Shiru tayi bata amsa ta ba.

"Meyasa baki sanar damu ba Baby?" Papi ya tambaya nan ma shiru tayi "Kiyi magana kinji Mama na? Kar kiji komi."

"Papi, Mami kuyi hak'uri kar ku d'au na 6oye maku wannan al'amari saboda wani dalili ne k'wak'k'wara nayi hakan ne sabida gudun da nake kar kuce zaku miyar dani gidan Yaya saboda wannan lallura."

"Sam baza muyi miki haka ba Baby shin baki yarda dani bane dana ce miki se idan ke kika ce kina so zaki koma gidan Afzal zaki koma? Ki sani nida mahaifiyarki bazamu tilasta ki akan abinda bakiya so ba, sanin kanmu ne nan duka Afzal be kyauta miki ba so ki kwantar da hankalinki kinji? Allah ya inganta kuma."

"Ameen Papi thank you."

"Wata nawa ne?"

"Sati uku ne kacal Mami" ta sanar da ita.

"Allah inganta Mamana sannu Allah sawwak'e."

"Shin har ya aka bigeki Baby? Baki kalli hanya bane kafin ki tsallake kwaltan?" Mami ta tambayeta.

"Mami na kalla kinsan shi tsautsayi baya wuce ranan sa" haka kawai taji ta rufa wa Nazeefah asiri saboda tasan halin Papi muddin yaji Nazeefah na da hannu acikin wannan al'amari abu baze zo yayi kyau ba saboda ba Afzal kad'ai ba har su Ummi da Abba da ze shafa ita kuma abu da tashin hankali ne bata so. Tun da de Allah ya raba ta da su yanzu sede tace Allah miyar masu da anniyarsu.

"Ermm Nurse" Papi yayi ma nurse d'in magana.

"Yes sir?"

"Nace shin meyasa baku kai ta regular ward ba? Gani nayi nan VIP ne."

"Tabbas nan VIP ward ne."

"Toh ai kud'in zeyi yawa kuma kin dega ba k'arfi muke da shi ba."

"Kar ka damu da wannan sabida bawan Allahn da ya kawo 'yarka asibitin nan ya riga ya biya kud'in d'akinta har na sati sannan ya saye mata magunan da duk likita ya rubuta."

"Subhanallah! Wannan wani mutumi ne haka?"

"Bayan nan jinin nan da kake gani ma na jikinsa aka janye aka sawa 'yarku leda har d'aya da rabi."

"Blood type nasu yaso d'aya?"

"Tabbas duk O- suke."

"Alhamdulillah Alhamdulillah amma dan Allah waye mutumin nan? Nasan godiya kad'ai baze biya abinda yayi mana ba amma dole ne inyi masa godiya."

"Shigowanku ya tafi kuma bey ajiye mana wani identification card nasa ba yana biya ya tafi."

"Allah sarki Allah sak'a masa da alkhairi ya biya sa da gidan Al-jannah."

"Ameen" duka suka amsa "Tabbas na Allah basu k'arewa" fad'in Mami. "Amma Baby kinga mutumin ke?"

"Eh Mami har nan ya shigo nima na basa lamban Papi."

"Allah sarki baki san sa ba?

"Gaskiya ban san sa ba amma se gani nake kaman mun ta6a had'uwa da shi."

"Allah sarki Allah ya biya sa, zaki ji yunwa ai yanzu ko Baby?" Ta tamabayeta.

"A'a Mami."

"Kaman ya a'a Baby? Kin manta zaki sha magani ne bayan nan kuma kinsan dole seda cin abinci yanzu in ba haka ba abun cikinki baze samu lafiya da k'wari ba ko dan shi seki hak'ura kina cin abinci."

"Bari inje da kaina cikin restaurant anan in sai miki abincin" fad'in Papi.

"Toh Papi nagode."

"Allah ya baki lafiya shine babba uwata." A bakin k'ofan ward d'in ya sake had'uwa da Afzal da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment