Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

maida hannun nata "I'm sorry" tayi apologizing.

"Su Ummi suna waje bari inyi musu magana su shigo" kansa taga ya kawar gabad'aya dan ko kallon ta baya sha'awan yi ko a mafarki akace masa Amal zatayi masa haka baze yarda ba kuma ba abinda yafi tsana kaman wannan munafikin halin hawainiyan nata, zatayi abu kuma ta zagayo kaman batayi komi ba tana proving innocence. Ko a ina yaci karo da rubutun chan yasan nata ne.

"Yaya har yanzu fushi kake dani? Yaya wallahi ban aikata ko d'aya daga cikin abubuwan da kake tokarina dasu ba Yaya sanin kanka ne ina sonka kuma bazan ta6a yin abinda ze 6ata maka rai ko zubar maka da mutunci ba you have to believe me."

"Ki kira mun Ummi da Nazeefah" yace da ita zalla ba tare da ya kalleta ba hawayenta ta share sannan ta mik'e "Allah baka lafiya" ko ta kanta beyi ba har ta fice

"Ya Afzal ya farfad'o Ummi."

"Ya farfad'o?" Ummi ta tambaya had'e da mik'ewa. Haushi Nazeefah taji wato seda Amal ta shiga ne ya ga daman tashi akan duk uban kalaman soyayyan da tayita fad'a masa? Duk su kwantar da hankalinsu soon enough ze saki Amal d'in.

"Yana buk'atan ganinki da Nazeefah."

"Alhamdulillah! Alhamdulillah" ta mik'a godiyar wa Allah.

"Abba fah?" Amal ta tambaya.

"Ya koma" Nazeefah ta amsa. Tana ganin shigewansu ta kira Safiyya suka koma gida tunda baya buk'atan ta na mey zata cigaba da zama?

"Prince!" Ummi ta kira sunansa had'e da hugging nasa "Prince dan Allah kayi a hankali wallahi likitanka na jiye maka."

"Ummi please it's okay I'll be fine."

"Welcome back Ya Afzal" Nazeefah dake tsaye akansa ta fad'a mai.

"Thank you Rabba'atul Bait" ya amsa yana mata murmushi.

"Prince meya faru? Mey Amal tayi maka?"

"Amal kuma?"

"Ka fara da zurfin cikin nan naka ko? Nazeefah ba ke kikace Amal ce bata kyautata masa ba?" Ido ya d'ago yana kallon Nazeefah da cikinta ya d'au ruwa tuni ta shiga rarraba ido.

"Haka nace miki?"

"Ya Afzal naga.. ermm... Toh ai sanin kanmu ne duka nan Amal ce sanadin ciwon naka Ya Afzal ko ba kai ka fad'a mun ba?"

"Se kuma nace miki Amal ce bata kyautata mun?"

"Toh waye ne?" Ummi ta tambayesa "Wayene idan ba Amal d'in ba?" Shiru yayi bece komai ba dan haka Ummi tayi tunanin ko bayi son yayi maganan a gaban Nazeefah ne. "Ermm nace mey kakeso kaci Prince Nazeefah ta girka ta kawo maka? Girkin waye ne acikinku?" Ta tambayi Nazeefah.

"Girkin Amal ne amma ba damuwa zan girka in kawo masa mey kakeso Ya Afzal?"

"Boiled potatoes da egg sauce" ya sanar da ita.

"Toh bari inje zan dawo yanzu in shaa Allah." Tana ficewa Ummi ta dawo da kallonta akan Afzal "Toh Nazeefar ta tafi gaya mun meke faruwa?"

"Ummi babu" mari me zafi ta kai masa akan cinya. "Ummi please! Kin fa san hannunki da zafi."

"Ina tambayanka abu kana kallon cikin idona kana mun k'arya? Nace meya faru? Wallahi ka kuskura kayi mun k'arya toh ni da kai."

"Ummi misunderstanding muka samu."

"Fad'a kukayi?" Kai ya gyad'a mata "Amma mun shirya shigowantan nan."

"Ka tabbata?"

"Eh Ummi."

"Ba senayi mata magana ba?"

"Babu amfani komi ya wuce."

"Toh koma meye ne de ka daina bin komi da zuciya haka kasan yadda zuciyar taka take da rauni please Prince Abbanka ma na nan ai d'azun ya tafi."

"Allah sarki ku daina tada hankalinku please I'll be fine."

"Zaka kwana ko zaka koma gida a yau?"

"Kwana kuma? Na samu sauk'i se in kwana a asibiti? Nazeefah na kawo mun abinci naci zan koma gida."

"Kana buk'atan wani abu toh?"

"A'a zaki iya tafiya Ummi thank you so much."

"Don't mention my boy Allah baka lafiya ko?" Kai ya gyad'a tare da amsawa yanayi mata murmushi. "Bari inyi ma Amal magana tazo ta tayaka zama kafin nan." Da mamaki ta nemi Amal bayan fitanta ta rasa ta dawowa ciki tayi tace, "Ban ganta ba fa, kode ta tafi ne?"

"Ohh ban fad'a miki ba ko? Na ce ta koma kinsan itama kwana biyu bata ji dad'i ba zazza6i ya sata a gaba."

"Haba! Shiyasa na ga ta rame Allah sarki Allah shi bata lafiya."

"Ameen Ummi." Zama ya cigaba dayi cikin d'akin har zuwa lokacinda Nazeefah ta kawo masa abincin ita da kanta ta basa bayan da ya gama tayi ma likitin nasa magana akayi discharging nasu. Kasancewar kwanan Amal ne har cikin gida Nazeefah ta kaisa sannan ta juya ta wuce nata gidan. Sannu da zuwa Safiyya tayi masa lokacinda ya shigo ciki.

"Ina Amal?" Ya tambayeta.

"Tana d'akinta" k'arisawa d'akinsa yayi ya zaro takardan d'azun had'e da ninkewa ya adana. Wayansa ya d'aga dan kiran Sultan inda ya tarar da missed call na Abba nan take ya kirasa back suka gaisa Abba yake mishi jaje. Suna k'are wayan ya kira Sultan.

"Maza yane?"

"Ba lafiya ba yanzu haka daga asibiti nake."

"Subhanallahi meya faru ciwon naka ne?"

"Yes and alot has happened Sultan ka shigo gobe kaji?"

"Toh sannu ya Amal ko gun Nazeefah kake?"

"Ni seka shigo kawai" tun daga amsan sa Sultan ya gane akwai matsala "Allah kaimu goben toh."

"Ameen" Afzal ya amsa had'e da katse wayan. Zama ya cigaba dayi a d'akin chan bayan sallan Maghrib Amal tayi sallama cikin d'akin nasa shiru yayi yak'i amsawa dan haka ta bud'e k'ofan ta shiga kansa yayi saurin kawarwa.

"Yaya-"

"Get out Amal bana k'aunan sake ganinki a cikin d'akin nan in shaa Allahu burin ki ya kusan cika kiban lokaci kad'an."

"Yaya mey kake nufi? Wani buri?"

"Just get out Amal in kuma fitan ne bazaki iya ba ina iya bar miki gidan gabad'aya."

"Allah huci zuciyanka" tace mishi zalla ta juya ta fice d'akinta ta koma inda ta kwanta kan gado ta shiga kuka sosai.

Washegari kaman yadda Sultan ya mar alk'awari haka yazarce gidan nasu daga office da Amal suka fara had'uwa lokacin tana zaune a dining tana cin abinci sannu da zuwa tayi masa tasa Safiyya ta kawo masa drink da snacks.

"Kinyi wuyan gani amarya."

"Ji Ya Sultan nice amaryar?"

"Amaryar amini na ma kuwa ke baki san yadda nake ji dake ba ko?"

"Uhm haka de kace amma ka barni da makaranta yana ta bani wuya."

"Karde shiya ramar dake haka? Har kun fara tests ne?"

"Ai mu kullum cikin tests muke Ya Sultan se a hankali."

"Allah sarki ba three kike ba yanzu? Kinyi mey wuyan ai Allah sa albarka."

"Ameen Ya Sultan yasu Umma?"

"Lafiyansu k'alau Afzal fa yana gida?"

"Eh ba motansa na waje ba?"

"Na sani koya fita strolling ya jikin nasa?"

"Toh Alhamdulillah de bari inyi mishi magana" nan ta mik'e ta nufi d'akin nasa sallama tayi amma be amsa ba dan haka ta bud'e ta shiga akan gado ta tsincesa yana bacci k'arisawa tayi had'e da tapping nasa a k'afa a hankali.

"Yaya? Yaya ka tashi Ya Sultan yazo" a hankali ya shiga bud'e idonsa har ya bud'e su duka ganin ita ne yayi saurin kawar da kansa "Bance kar in sake ganin ki acikin d'akin nan ba?"

"I'm sorry Ya Sultan ne yazo ya turo in kira ka" da haka ta juya ta fice. Brushing yayi ya wanke fuskansa sannan ya sanya shiry akan gajeren wandonsa ya fito ya sami Sultan. Bayan sun gaisa ya ce mishi su k'arisa ciki.

"Meya samu nan d'in? Ko so kake mu koro Amal waje ita da gidanta?"

"Bata d'akin come in" be sake musu ba ya mik'e suka k'arisa d'akin. Note na Amal ya d'au ya wulla wa Sultan akan cinya "Wannan fah?" Sultan yayi saurin tambaya.

"Ka bud'e kayi observing handwriting dake ciki" yadda aka ce da shi haka yayi bayan ya karance rubutun ya d'ago kai "Ehen?"

"Here take a look at this handwriting" yayi maganan yana zaro takardan d'azun daga inda ya 6oye "Handwriting na mutum d'aya ne ko kuwa?"

"Of course na mutum d'aya ne mana" Sultan ya amsa bayan yayi comparing handwriting d'in.

"Thank you ka zauna da kyau ka karanta content d'in." Hankali ya miyar kai ya shiga karancewa yayinda mamaki ya mamaye mai fuska da zuciya.

"Waya rubuta wannan maza?"

"Ka duba sunan dake jikin littafin" Afzal ya umarcesa.

"You don't mean this!" ya furta bayan daya duba yaga sunan Amal rubuce a bangon littafin.

"Yanzu zaka ga laifina idan na yanka mata ko wani irin hukunci?"

"Ban fahimce ka ba Triple A kana nufin Amal ce ta rubuta wannan?" Ya tambaya da d'umbun mamaki.

"Baka iya karatu bane?"

"I'm just confused Triple A, Amal de? Har Amal ce zata rubuta wannan abu? Kode kafin kuyi aure ne?"

"Kana ganin sabon paper sabon rubutu kana zancen kafin muyi aure?"

"Amma meya faru? Meyayi zafi da har Amal zata rubuta wannan abu a matsayinta na matarka?"

"Gata chan a chan d'akin kana iya zuwa ka tambayeta."

"Wow!" Ya numfasa totally speechless.

"Maza ban san meyake damun Amal ba yarinyar nan ta sauya gabad'aya ta koma wani abun daban banda munafurci da had'a kaina da Nazeefah ba abinda takeyi ko tsinke na sai mata seta buga waya wa Nazeefah ta fad'a mata knowing right ba duka abinda nakeyi mata nakeyi wa Nazeefah ba sedan kawai ta 6ata ni idon Nazeefah tasa Nazeefah tayi mun kallon maras adalci hakan be isheta ba har course mates nata maza ta fara kawo mun cikin gidan nan suna zama a kujera d'aya."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wacce Amal tukuna? Amal Amal naka da na sani?"

"Ita de Amal ta cikin gidan nan."

"Maza are you sure of what you're saying? Amal ce har zata shigo maka da gardawa cikin gidan nan?"

"In kira maka mey aikinta ne ka tambayeta?"

"Subhanallahi meya sameta?"

"Waya san mata ne?"

"Mey kake nufi kenan yanzu kana nufin kana zargin Amal kenan? Kana zargin tana ci maka amana?"

"Nooo not at all nasan Amal baza ta ta6a cin amanan aurena ba, ko tunanin yin hakan ma baza tayi ba I know that."

"Toh mey kake nufi da tana shigo maka da maza gida?"

"Yes ta daina shigo mun da coursemates nata saboda ba'a san abinda shaid'an ze iya raya musu ba wataran koba d'abi'arta bane wataran shi gardin ze iya kwad'aitar mata da hakan ko ba ka gane abinda nake nufi ba?"

"Sosai na fahimce ka amma Afzal I'm still shocked Amal da muka sani ce ta sauya haka take yin ababen nan da ka irgo? Innocent Amal taka?? Na tabbata haka kawai Amal bazata sauya halayanta ba sede idan kai kayi pushing nata don't you forget that for every reaction there's an action."

"Mey zanyi mata maza? Kafi kowa sanin irin son da nake yiwa yarinyar nan, Wallahi Amal bata ta6a neman abu a guna ta rasa ba komi ina yi mata da iyayenta amma ka kalli da abinda zata sak'a mun kuma abinda yafi bani haushi shine k'aryata komi da takeyi har yanzu ita bata amince da laifukanta ba bale ta nemi tuba mu sasanta tsakanin mu ni bazan iya ba, I can't do this anymore I'm tired of her sick behavior."

"Mey kake shirin yi?"

"Ba Abdul kowa take so ba? Seta je ta samesa."

"Wani irin magana kake haka Afzal? Da igiyan auranka akanta kake son taje ta auri wani?"

"Sawwak'e mata zanyi."

"Mey?? Kana da hankali kuwa Afzal? Wani irin zafin kishi ne da kai haka?"

"Toh mey kakeso inyi? Ba gara na sawwak'e mata ba taje ta samu shi wanda take son? Bazan iya zama da ita ba knowing zuciyarta na tare da wani gara na rasata gabad'aya dan idan har na cigaba da zama da ita toh zan cigaba da kallonta da abin ne wanda zuciya ta baza ta iya d'auka ba wataran sede ta har6a tabar aiki."

"Idan ka sawwak'e mata ta koma gun Abdul kai kuma fah?"

"Na sani sena fita shan wuya bayan rabuwan nan amma ka gaya mun mey riban ajiyeta a wajena idan zuciyarta na tare da wani daban Sultan? I love Amal kuma har duniya ta nad'e bazan fasa sonta ba but this is not reason enough to keep her with me tunda gashi da hannunta ta rubuta bata sona tayi nadaman aurena. Kaji fa har cewa take wai dama tun fari tasan jikinta kawai nake so yanzu da na samu abinda nake nema gashi ina walak'anta ta. Ni fa Maza? Ni d'in da ko hannunta ban ta6a sha'awan rik'ewa ba... excuse me" tari ya shiga yi yayinda zuciyansa ya fara tashi yana yi masa k'una tsan-tsan takaici da bak'in ciki da 6acin rai.

"Dan Allah kayi a hankali ba senun sake kaika asibiti ba it's okay ya isa."

Gyaran murya yayi ya cigaba "So I think it'll be better idan na barta taje ta samu shi wanda take so d'in ta huta kowa ma ya huta."

"Kai kuma fa Triple A? Ya zakayi da rayuwanka idan kuka rabu? Shin ka manta rayuwanka gabad'aya yana revolving ne a jikin na Amal? Shin ka manta idan ba soyayyarta zuciyarka bazata iya aiki ba? Shin ka manta idan ba ita a kusa da kai rayuwarka tana cikin gwagwarmaya? Ina ka mance da dukkan hakan Afzal har kake tunanin sawwak'ewa Amal? Besides ni ban yarda ma innocent Amal d'in da na sani zata iya aikata wannan munanan abubuwan da kake tokarinta da su ba. She's too innocent to do all these I know Amal kuma na yarda da ita."





RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨


Miemiebee Novels

Monday, 13 August 2018
RANA D'AYA!
BY MIEMIEBEE
PAGE 35




"Ka san Amal kuma ka yarda da ita? Lmao" wani kalan dariyan rainin hankali ya saki "So kake kace ka fini sanin halin matata ko mey Maza?"

"I dunno but I guess yes saboda komin yaya nasan Amal bazata ta6a aikata wannan aika-aika ba."

"Mak'aryaci ne ni kenan? K'arya nakeyi maka? Is that it?"

"Ba haka nake nufi ba Triple A amma da hankalinta kam Amal bazata ta6a aikata hakan ba, it's either she's possessed or something baka tunanin hakan?"

"You mean you deny ba ita tayi wannan rubutu ba?"

"Ba wai nace ba ita tayi bane it's crystal clear rubutun tane amma waya sani ko wani mental illness ne yake damunta wanda idan ya tashi yake sanyata yin abubuwan nan daka irgo saboda a gaskiya bana tsammanin kan Amal ya waye d'inda har zatayi wannan abubuwa. Triple A kayi tunani mana kai fa da kanka kake yabawa da irin kyawun halatayyar ta."

"Mental illness? Gani kake kaman tana da ta6in hankali? Just so you know har asibitin mahaukata na kaita aka kuma duba ta and you know what likitan yace ba abinda yake damunta idan kuma tunanin aljanu kake nan ma na kaita gun Malami anyi mata ruk'iya shima yace bata tattare da komai lafiyarta k'alau so stop giving me lame excuses."

"Wow! But what's really wrong? Ka sameta kayi mata magana? Kayi confronting nata? Maybe akwai wani 6oyayyan al'amari."

"Mey zance mata? Besides kasan ni ba d'abi'ata bane yima mutum magana idan yamun laifi idan shi hankalinsa be basa hakan ba ya nemi tuba ba sede a cigaba da zama hakan."

"Kana nufin tunda abubuwan nan suka soma faruwa baka ta6a yiwa Amal magana ba?" Ya tambayesa da mamaki gaskiya ne mey hali baya canzawa ko shi yana iya tuna lokacinda suka kusan shafe term d'aya (k'imanin watanni uku) a makaranta shi da Afzal lokacinda suke boarding house basu magana a sanadin wasu maganganun da abokansu suka je suka shiryawa Afzal cewan Sultan ne ya fad'a. Shiko Afzal ba bincike ba komai kawai ya hau kan magana ya zauna akai. Kyat kawai Sultan yaga Afzal ya dai na yimai magana da k'yar suka zo suka daidaita tsakaninsu. Tun daga wannan rana ya karanci halin Afzal ko meye mutum yayi masa bayi ta6a tinkarar mutumin da maganar sede yayita kallon meshi da abun har zuwa lokacin da mutumin zey gano yayi kuskure ya nemi tuba. Bayan nan Afzal ya kasance d'aya daga cikin jerin mutanen da basu tsananta bincike game da duk wani abinda aka fad'a musu wanda hakan yake babban hatsari. Su komai aka same su aka fad'a musu d'auka suke su zauna akai ba bincike ba komai wanda sam hakan be dace ba musamman ma ga magidanci kamansa mey mata biyu. Tabbas yasan a banza Afzal yake hukunta Amal baiwar Allan da bata ma san mey tayi ba yanzu. Ashe dalilin da yasa ta zube tayi duhu kenan bak'in ciki ne da tashin hankali ba stress na makaranta kaman yadda tace ba. Allah sarki.

"Maza that's so unfair hukuncin nan da ka yanke yayi wa Amal tsauri dayawa kuma wallahi bazan 6oye maka ba ba haka ake ajiye gida ba, ba haka ake handling mata biyu ba. Afzal da dayanzu ba d'aya bane, yaci ace ka zubar da mumunan d'abi'ar nan naka na kallon mutum da laifi ka fara tunkararsa da laifin da yayi maka kaji mey zece, kuma be dace a matsayinka na mey mata biyu ace dan uwar gidan ka ta fad'a maka abu kawai ka hau ka zauna akai ba kamata yayi ka tsananta bincike ka zaunar da Amal kuyi magana kaji nata 6angaren labarin itama na tabbata akwai ababen da Nazeefah takeyi mata wanda bata jin dad'insu amma ta za6i ta had'iye wa kanta dan karta had'a kanku haba maza! Wallahi sam baka kyauta wa Amal ba."

"Naji nasan bana tsananta bincike kuma bana confronting mutum idan ya mun laifi amma wallahi akan Amal na fara yin hakan bayan da Nazeefah ta irga mun komai nayi mata magana."

"And mey tace?"

"K'aryata komi tayi abinda ya fi bani haushi kenan, tayaya Nazeefah zata na sanin abubuwan da suke gudana a cikin gidan nan idan ba wai kirarta ake ana sanar da ita ba? Ai abinda zaka duba kenan."

"Wow! Ko ze iya yiwuwa hakan ne?"

"Hakan kaman ya?"

"Akan ba ita bace bata aikata abinda kake tuhumarta dashi d'in ba."

"Are you kidding me? Ka zauna kayi tunani Sultan ko tsinke na saya mata a gidan nan se naji labarin a bakin Nazeefah how on earth Nazeefah zata san abinda ke gudana acikin gidan nan idan ba wai kirarta ake ana fad'a mata ba? Ko so kake kace tana da CCTV ne?"

"No bawai haka nake nufi ba."

"Then tell me, tell me how exactly would Nazeefah know of everything da nakeyi wa Amal?"

"You have a point amma still da kayi mata uzuri sanin kanka ne Amal yarinya ce, halan yarinta ke damunta ka sameta kayi mata magana kaja mata kunne I'm sure zata saurareka ta kuma daina."

"Yarinta ko rashin tunani? Wallahi da gan-gan takeyin komai, and you seem to be forgetting her actual age, Amal is 21 years old Sultan she's nomore a child."

"Naji nan Amal bata kyauta ba tayi laifi, amma batun shigo da course mates nata maza cikin gidan nan fa? Ka ga hakan da idonka ne?"

"A'a amma ai 'yar aikinta ne ta fad'a mun."

'"Yar aikinta?" Yayi questioning nasa unbelievably '"Yar aikinta fa kace maza?"

"Yes ba ita take gida ba kullum ai tana sane da shigowa da fitan kowa."

"Amma Maza ka bani kunya, ban ta6a sanin kana da k'arancin tunani haka ba se yau ashe baka fasa halinka ba har yanzu wai tayaya ma zaka fara amincewa da abinda baka ji ba bale ka gani? Wallahi zato zunubi ne."

"Ce maka akayi zato nakeyi? Clearly 'yar aikinta tace sau biyu take ganin Amal na shigo da course mates nata har ragowan snacks da drink data basu ma na dawo gida na tarar ranan what else do you expect me to believe?"

"Ka tambayi me gadinka ne? Ka tsaya kayi wa ita Amal d'in magana kaji labarin daga bakinta? You have to listen to both sides before taking a decision Afzal dole ne ka zubar da wannan halin naka kafin lokaci ya k'ure kazo kana nadama, tabbas duk wanda baya tsananta bincike yana tattare da babban hatsari bana son kazo kayi nadama daga k'arshe."

"Kana tunanin Safiyya zatayi ma Amal sharri ne? Meye ribarta idan tayi hakan?"

"Kai kuma kana tunanin Amal zatayi maka k'arya ne da tace maka ita bata shigo da na miji gidan nan ba? Wai taya ma zaka fara amincewa da maganan mey aikinka akan na matarka ne Afzal? A ina aka ta6a yin hakan?"

"A gaskiya ka bani kunya maza yadda kana ganin gaskiya kake takewa."

"Ma tukun a ina ka tsinci wannan paper?"

"Cikin kayakina."

"Lmao cikin kayakinka? Wallahi ka bani kunya Afzal, it's so unfortunate that you're my friend. Har kana tunanin Amal zata rubuta wannan abu takuma sake ajiye maka shi acikin wardrobe inda ze fi sauk'in ka gani? A tunani na sede ta 6oye ba ta ajiye a inda zaka gani ba. Wallahi Allah this's a trap."

"Har wani marasa aikin ne ze zauna yayi wannan aiki? Kuma har ya iya yayi irin rubutunta sak?"

"The world isn't a safe place and there are toxic people everywhere so zan baka shawara ka zauna ka bi diddigin lamarin nan idan ma da hali ka zaunar da Amal d'in da Nazeefar da mey aikin nata da mey gadin naku duk gabad'aya kayi musu tambayoyi ka kuma saurari both parties am very sure zaka sha mamaki da sakamakon da zaka samu" yana kaiwa nan ya mik'e "wannan kuma" yayi nuni da takardan hannunsan.
"Duk da cewa rubutun Amal ne karara ajiki hakan baisa na yarda itace ta zauna ta rubuta ba kuma koda ma ita d'ince zan iya cewa tana da daman yin hakan tunda gashi a fili kake nuna mata rashin k'auna da adalci ta hanyan yanke hukunci ba tare da ka saurareta ba zan iya cewa abubuwan da kakeyi mata su suka tunzira ta har ta zauna tayo wannan rubutu, kai baka san the more kake k'untata mata the more kake sa take tunanin masoyinta Abdul take kuma kewon sa ba? Ko ka manta yadda kukayi auren nan ne Afzal? Yarinyar nan fa ba wani sonka take ba, lami lafiya suke soyayyansu da saurayinta suna building dreams nasu ka shiga tsakanin su haka dan ta ceto ranka ta sadaukar da farin cikinta da abin alfaharin zuciyarta. Kana ganin ta cancanci wannan walak'ancin da kakeyi mata? The earlier the better Triple A it's time for you to make things right idan kuma har bakayi ba toh ni zanyi da kaina" yana kaiwa nan ya ajiye takardan ya fice.

Mugun d'aurewa kan Afzal yayi gabad'aya ya rasa meke masa dad'i what if duk abubuwan da suka faru set up ne kaman yadda Sultan ya fad'an amma ai kuma wannan rubutu is real ko a mafarki aka nuna masa rubutun nan yasan na Amal ne. Amma kuma idan har ita ta rubuta ai baza ta ajiye a open place inda ze gani ba sede ta nemi wani 6oyayyan wajen ta ajiye, ya Allah what's really happening? Yini yayi gabad'aya ranan yana tunani ya kasa samun sukuni wajajen tara hak'urinsa ya k'are. Maybe is about time ya tunkari Amal suyita ta
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment