Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ya tona mata asiri Jameela?"

"Abba banda ni da kai fa ba wanda yasan 6oyayyan al'amarin nan a tunani na ba amfanin sanar da iyayen Afzal wannan batu, mu rufa wa kanmu asiri kaman yadda Allah yake rufa mana banga amfanin tozarta kanmu wa mutane haka ba."

"Ya kike magana haka Jameela? Shin bakisan duk auran da aka ginata akan k'arya bata d'aurewa ba?"

"Na sani Abba amma gani nake kaman mutuncin mu ne ze zube barin ma naka dana Baby, wallahi da wuya mutanen nan su sake d'aukan Amal da k'ima da daraja ba."

"A'a Jameela, ba wani zancen abin kunya ko kuwa zancen zubewan mutunci anan, ba wanda yafi k'arfin jarabawa da k'addara. Gaskiya kuma ko bamu fad'eta ba wataran zata fito da kanta don haka gara mu fad'a musu komai da bakin mu akan suzo su gano gaskiya wataran, a gani na hakan ne zai zubar mana da mutunci da daraja a idonsu."

"Amma Abba yau shekara nawa? Kusan ashirin amma banda mu ba wanda yasan wannan labari, tunda muka baro Askira ba tashin hankalin da ya sake binmu kana ganin ya dace mu sake jefa kanmu acikin wani rud'anin?"

"Ki kwantar da hankalinki Jameela in shaa Allah ba rud'anin da ze biyo bayan yin abinda ya dace."

"Toh shikenan tunda kace haka se a sanar dasu d'in dama ni kawai ina gudun tokarin da za'a zo ana yi wa Baby ne."

"Har wa ya isa yayi mata tokarin? Ai ba lalle ne akace se sun aureta ba idan sunga bazasu iya auranta a haka ba walillahil hamd dama tun farko su sukace suna so ba tallar su akayi mata ba, amma kam ba dani za a a gina aure akan k'arya ba. Abinda ka raina kake ganin ba komai ba shi zezo ya zame maka babban matsala nan gaba. Ke zaki gani kaman ba komai bane yanzu koda ba'a sanar dasu ba amma rananda k'wai ya fashe se mutum ya raina ka yaga kaman ka ci mai amana ne ka zaluncesa saboda haka yanzu ne lokacin da ya dace da a sanar dasu gaskiyan al'amarin idan sunga su bazasu iya had'a zuri'a da ita ba shikenan Allah ze kawo mata wani, hannun mutum baya ru6ewa ya yasar."

"Tsakani na da Khalifah sede Allah ya isa, Khalifah ya cuceni a rayuwa bansan da wani idon zan sake kallon Baby ba idan har ta jiyo gaskiyan labarinta, Khalifah ya cuceni ya cuceni!" Ta rushe da kuka.

"Yanzu kuka kike saboda Baby ta shigo ta tsince ki ahakan ko mey? Kisani Baby baza ta ta6a yi miki mumunan fahimta ba, sanin kowa ne Khalifah ne ya cuceki bawai ke kika cuci kanki ba. Ya auna tunaninki ne da k'arancin shekarunki yayi riba da hakan, shiyasa kika ga koda 'yan unguwa da dangi suke tsangwamar ki nayi tsaye na kareki, koda wasa ban ta6a baki laifin abinda ya faru ba kuma bazan ta6a ba Jameela ni nasan kalan tarbiyyan dana baki."

"Abba banida kaman ka, bazan ta6a iya biyanka kalan halaccin da kayi mun ba a rayuwa fatana kawai Allah ya sak'a maka da gidan aljannah."

"Ameen share hawayen naki haka ki shirya abinci wa bak'in namu munyi waya da Abban Afzal d'in yace suna tahowa."

"Toh shikenan Abba" da haka ta fice instead ta wuce kitchen seta nufi d'akin Amal inda ta tarar da ita kwance kan katifarta. Tana jin k'aran k'ofa ta 6oye wayarta da take ta faman kallon hotunan Ya Abdul k'ark'ashin pillow.

"Bade bacci kike ba?" Ta soma da tambayarta.

"A'a nagama tilawa ne nace bari in d'an huta."

"Oh dama nazo ne muyi wata magana" A nan Amal ta mik'e ta zauna tana mey baiwa Mami full concentration nata "Ina jinki."

"Baby kiyi hak'uri ki yafe mun" ta sanar da ita. Cike da rud'ani Amal ta tsaya tana kallonta "Mami hak'urin mey kuma kike bani? Ai baki yi mun komai ba."

"Ko da wasa kar kice haka 'yata, laifin da na miki har yau ba wanda yayi maki irinsa, Baby na cuceki a rayuwa, nayi miki k'arya gabad'aya rayuwarki, k'aryan da ban san ta ina zan soma wanke kaina ba amma dan Allah ki gafirceni kisani ba haka hali na yake ba, k'addara ce ta riga fata."

"Mami ban fahimceki ba dan Allah meke faruwa?"

"With time zaki fahimci komai Baby ni gafararki kawai nake nema."

"Mami baki yi mun komai ba ni don haka nakeson ki daina tambaya na yafiya, you have nothing to be sorry for" k'arisawa tayi tare da hugging nata. "I love you so very mucu Mami no matter what."

"Allah yayi miki albarka Baby, ya cigaba da kare mun ke ya sanya miki albarka acikin dukkan al'amuranki."

"Ameen Mami please don't cry" a hankali ta saketa ta shiga share mata hawayenta sannan suka wuce kitchen d'in tare suka shiga had'a kan girkin.

Bayan La'asr Afzal da Abbansa suka duro gidansu Amal. Bayan taransu da su Papi sukayi Mami ta sa Amal fito musu da drinks da aka tanadar musu don Abba ya ganta. Daga baya-baya ta tsuguna ta gaishe sa cike da ladabi da biyayya kanta sauk'e a k'asa bayan nan ta gaishe da Afzal sannan ta k'arisa ta ajiye tray d'in daga gabansu sannan ta tsiyaye musu juice d'in a cup each.

'A gaskiya Afzal ya iya za6i' abinda Abba keta furtawa a ransa kenan haka kawai Amal ta shige masa zuciya. Kaman yadda Afzal yake son mace kamila mey kunya shima mahaifin nasa haka ne, kamun kai, fasali da kunyan Amal ba k'aramun burgesa yayi ba, fatansa Allah basu zuri'a d'ayyiba.

Bayan Papi ya sanar da su Abba date da Amal ta za6a su Abba suka amince right away, bayanin komi dalla-dalla Papi yayi musu akan cewa ta za6i February d'inne saboda by then ta samu hutu a makaranta kuma da ikon Allah ta samu ta had'a haddan Al~Qur'anin da takeyi. Abba couldn't ask for more akan fasali da kamilancin nan kuma ga hafizancin Al~Qur'ani madallah nan take yafara shawaran kyautan da ze bata ranan sauk'an nata. Bayan Mami ta mik'e ta basu waje, Papi yayi gyaran murya ya fara kaman haka, "Godiya ya tabbata ga Allah yadda komi yake tafiya lami lafiya."

"Tabbas, mune da godiya Mallam Muh'd Allah sak'a muku da alkhairi ya ji k'an mahaifa."

"Ameen ameen saidai wani hanzari ba gudu ba."

"Toh toh ina sauraranka."

"Batun Amal ne, a gaskiya ni mutum ne mey fad'in gaskiya a ko da yaushe komin d'acinta komin kuma ya take."

"Tabbas haka wannan yake ni kaina na fahimci hakan a d'an cikin kwanakin nan da muke tare."

"Madallah, kasan shi gaskiya komin d'acinsa fad'inta yafi barinta da tayi tsami."

"Tabbas Mallam Muh'd."

"Ban san ya kai da Afzal zaku kar6i wannan labari ba amma ya zama dole a matsayina na wanda Amal take hannunsa in sanar daku duk wani abinda na sani game da ita baze yuwu don son abun duniya ko makamancin hakan inyi muku k'arya in tauye muku hak'k'i ba saboda son zuciya da gudun abin kunya."
Na matuk'a both Afzal da Abbansa suka shiga cikin rud'ani amma ba wanda ya iya bud'a bakinsa ya tambayi meke faruwa, shiru sukayi suna jiran jin k'arshen labarin.

"Shi aure abu ne babba wanda ko addininmu ma ya nuna mana fa'idarsa shiyasa bana wasa da sha'aninsa, idan aure yayi kyau toh zuri'ah ma zatayi kyau idan ko ta 6aci zumunci da komai ya lalace kenan. D'aya daga cikin ababen da yake rusa d'aurewan aure kuwa shine ginata akan k'arya."

"Wannan haka yake Mallam Muh'd" Afzal de ido ya zubawa Papi yayinda hak'urinsa ya gaza don jin k'arshen wannan labari.

"Shiyasa nace tun kafin magana yayi nisa gara in sanar daku wannan al'amarin dake 6oye a gareku. "

"Ina jinka Mallam Muh'd."

"Sanin kanku ne ba nine mahaifin Amal ba, Kakanta nake amma a hannu na ta girma."

"Wannan haka yake Mallam Muh'd."

"Afzal nasani ko ban tambaye ka ba ze iya yuwuwa Amal ta ta6a maka magana batun mahaifinta akan ya rasu, hakane?"

"Hakane Papi da jimawa ma kuwa, a kullum addu'an mu na tattare da shi Allah ya jik'ansa ya sa mutuwa hutu ce a garesa."

"Ameen" Abba ya amsa.

"Gaskiyan al'amarin shine banida yak'inin hakan. Kaman yadda bazan iya cewa eh gashi Abban Amal ya mutu ba haka zalika bazan iya cewa yana raye ba, masani se Allah."

"Sorry?" Afzal da kansa ya d'aure yayi saurin tambaya. "Kana nufin baku san inda ya shiga ba kawai kukayi assuming ya rasu?"

"Haka nake nufi Babana. Daga ni har Mamin nata bamu da masaniya akan inda bawan Allan nan yake."

"Subhanallahi! Allah ya fito dashi a duk inda yake toh" Abba ya fad'a yayinda Afzal ya amsa da "ameen."

"Ina son ku sani cewa ba a haifi Amal da uba ba, Amal bata da uba" kat kuma seya yi shiru. Yadda kuka san anyi mutuwa neither Afzal nor Abba spoke up. Shiru kukeji a wajen yayayinda fuskokinsu ke d'auke da d'imbun mamaki da neman k'arin bayani barin ma Afzal.

"No this can't be possible" Afzal ya shiga k'aryata zancen daga bisani "No I'm not believing this, taya zakace an haifi Amal ba uba bayan ita da bakinta tace mun ya rasu ne please Abba tell him this's not possible" yayi stating a kid'ime. A lokaci guda ya fita daga hayyacinsa. Taya batin kowa ace Amal tasa ce bata da uba? Wai mey ma hakan ke nufi? So ake ace mai Amal tasa shegiya ce? Bayan duk kamala, kamun kai, addini da hankalinta? No! Baze ta6a yarda da hakan ba.

"Afzal kayi hak'uri nasan ni mey laifi ne, yaci ace tun farko na sanar da kai da mahaifinka gaskiyan al'amarin ba se na bari har magana ta kai ga matakin aure ba amma kuma Allah be bani ikon yin hakan ba se yau, ka sani ko da wasa ban so zolayar ka ba. In da kuwa hakane da bazan ta6a sanar daku wannan al'amari ba dukda muhimmancinta se idan ranan da dubu ya cika saboda haka nake sake baku hak'uri idan har duk tsawon lokacin nan kunga kaman na 6ata muku lokaci ne ku gafirceni. Gaskiya de d'aya ce kuma na fad'eta ba a haifi Amal da uba ba tunda mahaifin nata ya samu abinda yake nema daga gun mahaifiyarta bamu sake ji daga garesa ba har yau. Yanzu haka Amal bata san da wannan magana ba saboda ba wanda ya ta6a sanar da ita gaskiyan labarin ta."

Shiru ne ya d'au wajen, daga bisani Afzal ya shiga magana "Mey hakan ke nufi kenan Papi?" ya tambayesa cikin rud'ani "Kana nufin zaku rabani da Amal kenan?" Har anan Abba bece komai ba.

"Ba wai haka nake nufi ba Afzal shawara ya rage naka da na iyayenka kaman yadda bazan iya tilasta maku auren Amal ba haka bazan iya hana ku ba ni duk abinda kukace shi za'ayi kawai bana son agina aure ne akan k'arya."

"Kaman ya Papi? Wani irin magana kake haka? Dan an haifi Amal ba uba shikenan se na k'ita? Laifin ta ne? Ya kake magana haka Papi?"

"Ba wai abinda nake nufi ba kenan Afzal ka fahimceni, kade san irin zamanin da muke ciki a yanzu, yadda ake tsangwan yaran da suka tsinci kansu a cikin hali irin na Amal. Ni kuma muddin ina raye bazan bari aci zarafinta ba. Amsan ku nake jira idan kunga baza ku iya had'a zuri'a da ita a hakan ba toh kar kuji komai ku sanar dani haka Allah ya k'addara."

"Tabbas kayi gaskiya Mallam Muh'd sam ba k'arya acikin abinda ka fad'a ko d'aya kuma ina gode maka na bud'e mana cikinka da kayi har ka sanar damu wannan sirri me uban nauyi. Ina son ka sani cewa sirrinka is safe with us, ba wanda ze kuma yaji wannan magana bale har hakan ya jawo wa Amal matsala a rayuwarta. Ya zama dole in yabawa halinka, a gaskiya samun irinku a zamanin yanzu se an tona. Sai dai ina son ka sani cewa this will not change a fact, kasani baza mu bari wannan labari ya dawo mana da hannun agogo baya ba kokuwa yasa a fasa abinda aka fara. Muddin Afzal yana son Amal kuma yana son ya aureta ko a hakan ni da mahaifiyarsa bamu da matsala saboda ba laifin Amal bane don an haifeta ba uba baza kuma a k'i ta don hakan ba so Afzal" nan ya juyo yana kallonsa "Mey zaka ce game da wannan al'amari? Kasani abinda kakeso shi zanyi maka."

"Abba bansan na mey kake tambayan baki na ba, I love Amal and ko a yaya take zan aureta I don't care ko ta rasa ganinta kokuwa ji. Ko da gurguwa ta koma zan aureta a hakan saboda zuciyarta nakeso ba looks nata ko asalinta ba. I love her and I'll marry her regardless." Sosai Papi yaji dad'in kalamun Afzal da Abbansa tabbas sun cika mutanen k'warai sun kuma nuna wa Amal so tsakani da Allah.

"Toh Mallam Muh'd kade ji, saboda haka nake son ka kwantar da hankalinka ka sani wannan aure kaman an riga an d'aura ne da izinin Allah."

"Toh madallah Allah sanya albarka aciki ya nuna mana ranan."

"Ameen ya Allah" Abba ya amsa.

"Papi ina da alfarma please" Afzal yace.

"Ina jinka Babana."

"Kace Amal bata da masaniya game da al'amarin nan ko?"

"Bayan ku da nake sanar ma wannan labari da mahaifiyarta ba wanda yake da masaniya ga al'amarin nan kuma nakega se 'yan unguwan da suke nan lokacin da abun ya faru a garin Askira."

"Papi please kada a ta6a sanar da Amal wannan magana."

"Ko meyasa kace haka Afzal?" Ya tambayesa cike da son k'arin bayani.

"Bana son hakan yasa ta tsani kanta ta fara guje wa mutane ciki harda ni, please kar a fad'a mata komai this should remain as a secret between us kamin alk'awari kai da Mami baza ku ta6a fad'a mata komai game da maganan nan ba. I want her to remain the Amal that she is, with equal right like everyone possesses."

"Afzal-"

"Please Papi, Abba dan Allah ka rok'eshi da kar su sanar da Amal komai wallahi nasan halinta kad'an ne daga cikin aikinta bayan taji labarin nan tace ta fasa auren saboda tunaninta bata zeyi bata kai ta auri d'an halak ba, I love her this way and I wouldn't wanna be separated from her."

"Toh Mallam Muh'd kade ji alfarman da Afzal yake nema inda hali kada a sanar da Amal d'in kaman yadda ya buk'ata dan Allah."

"Alhj Amin nifa duk abinda kukace shi za'ayi saboda kun nuna mun halacci kun nuna wa Amal d'ina soyayyan da bayan nida mahaifiyarta bana tsammanin akwai wanda ze sake kwatanta mata irinsa idan har kuna ganin fad'a mata wannan magana ze iya jawo matsala se a fasa Allah tabbatar mana da alkhairi."

"Ameen nagode" Afzal ya fad'a "Thank you so much Abba thank you Papi."

"Ba komai d'an albarka Allah cigaba da yi ma albarka."

"Ameen Papi thank you."

"So zamu koma Afzal bismillah jeka fiddo da kayakin toshin."

"Wasu kayakin toshi kuma Alhj Amin?"

"Yadda de al'ada ta kawo d'an akwatuna uku ne da naka guda d'ai dana mahaifiyarta itama."

"Shikenan mu kuma aikin mu komai aka kawo hab mun kar6a?"

"D'aya daga cikin riban haifan 'ya mace kenan. 'Ya'ya mata arziki ne."

"Hakane kam amma namun yayi yawa ne."

"Toh wannan kuma sede kayi musu da al'ada dan ni shi nake bi tashi Prince ga makullin motar." Afzal da kansa ya shigo da akwatunan da suke guda biyar in number seda kit guda d'aya making it six. Godiya sosai Papi yayi sannan ya rakasu har bakin k'ofa. A hanyan su na komawa gida Afzal ya rok'a Abba da komin yaya karya sanar da Ummi wannan 6oyayyan al'amari ya buk'acesa da maganan da ya zauna a mtsayin sirri a tsakaninsu su biyu kad'ai. Abba beyi jayayya da hakan ba, shi de addu'ansa d'aya ne yadda Afzal ke son Amal da yadda itama ta sadaukar da soyayyarta masa Allah sa soyayyan nasu ya d'aure.

Bayan dawowan Papi ciki ya kira Mami inda yake nuna mata kayakin da su Afzal suka sauk'e yake kuma sanar da ita alfarman da Afzal ya rok'a.

"Toh Alhamdulillah sede nayi kaud'i na sanar da Baby nifa."

"Kin sanar da ita mey? Yaushe?" Ya tambaya cike da k'in yarda. "Da izinin wa?"

"Bawai na fad'a mata ainihin labarin ba neman tubanta kawai nayi da ta yafemun idan labari ya isketa."

"Toh da sauk'i dan Afzal yace baya son a sanar da ita komai."

"Allah sarki yaron nan ya cika d'an halas wallahi, tsakani da Allah yakeson Amal Allah yasa son ya d'aure har bayan auransu."

"Ameen kira Baby'n ku shiga da kayakin ta duba barin shiga da nawa nima."

"Sun amince da ranar da muka d'aukan ko sun buk'aci ayi canji beyi musu ba?"

"A'a sun nuna komai ya musu yanzu de rana kawai ake jira."

"Toh madallah Baby!" Ta k'olla mata kira.

"Na'am" ta amsa daga ciki.

"Fito mu shiga da kayakin gashi har akwatuna uku kika samu na toshi."


***** 8:12pm
Nazeefah ce a kitchen tana dafa musu indomie ita da Afzal yayinda yake zaune a kan gado a d'aki yana had'a kan ragowan aikin da ya rage masa a office sega wayansa ya shiga ruri dubanwan da zeyi yaga Amal ke kira wai! Wata sabuwa, baze ma iya tuna rabon da ta kirasa ba. Be 6ata lokaci ba yayi picking, "Se yau aka tuna dani kenan."

"Ai kullum kana cikin raina Yaya makaranta ne bayi bari na."

"Toh ya kike?"

"Lafiya k'alau ya aiki? Ya gida? Ya Nazeefah?"

"Alhamdulillah komai k'alau ya school?"

"School se godiya."

"Madallah Allah taimaka toh."

"Ameen Yaya da wahala haka kuma?"

"Wani wahala ne kuma Lily nifa bana son godiyan nan naki."

"Kayi hak'uri amma godiya ya zama dole Yaya, mungode sosai Allah saka da alkhairi ya k'ara bud'i please ka tayani yiwa Ummi godiya."

"In shaa Allah Lily."

"Toh goodnight kar in shiga hak'k'in Nazeefah."

"Toh Lily goodight, I love you" daga nan ta katse. Mayar da wayan yayi ya ajiye yana me tunanin abinda Papi ya fad'a masa. Sede ya kasa yarda da hakan har yanzu gani yake kaman mafarki ne, shi Amal kawai yake tausayawa yasani komin jimawa wataran gaskiya ze fito he can't imagine the kind of pain Amal will go through idan ta gano gaskiyan labarin asalinta shide ya d'au alk'awari no matter what baze ta6a goranta mata da komai ba he'll love her until his last breath.

***
A kwana a tashi kaman gobe ne ga mey rai a haka har su Amal suka kammala exams nasu na first semester daga nan ta mayar da hankalinta sosai ga karatun Qur'aninta dan son samu ta had'a kafin auran nasu, dududu saura watanni biyu ne bikin.

Ta fannin Afzal da Nazeefah kuwa sun gama shiri tsaf a yau jirginsu na zuwa Saudi ya tashi amma kafin nan seda suka bi gida sukayi sallama da kowa. Kaman yadda ya d'au wa Amal alk'awari, suna isa Jiddah yayi texting nata akan cewa sun isa lafiya.

Nazeefah dan farin ciki fa ji take kaman ma duniyan bazata iya d'aukanta ba. Lafiya k'alau suke zama ita da Afzal duk wani abinda tasan yana iya 6ata masa rai batayi, yi tayi bari ta bari. Ba k'aramin jin dad'in zama da ita Afzal yake ba, ba tashin hankali ba komai se zallan soyayya da kwanciyan hanakli. Haka nan tun sauk'ansu a Saudi kusan kullum se sun fita sunyi shopping sun fita yawo, sede wayon Afzal duk abinda ya sai wa Amal baya barin Nazeefah ta gani, ko da wasa be ta6a kawo abu d'aya daya saya wa Amal a hotel room nasu ba. Wani balarabe mey hankali ya samu wanda yake ajiye kayakin nasa a wajensa. Yau satinsu d'aya kenan amma tun kiran Afzal da Amal tayi don yi mai sannu da zuwa bata sake kiransa ba shima kuma da gan-gan be sake yi ta kanta ba, Allah ma yayi Nazeefah na d'auke masa kewa da idan yayi wasa se wani attack d'in ya sakd kamasa. Sosai yake missing nata amma yayi making mind nasa muddin ita bata kirasa ba toh shima baze sake kirarta ba har se idan sun dawo Nigeria lafiya.

Nazeefah na wanka a bayi kasancewan zasu fita unguwa kawai sega call na Amal dan mamaki yama kasa d'agawa seda call d'in ya kusa tsinkewa tukun.

"I'll call you back" ya sanar da ita had'e da katsewa. Mik'ewa yayi ya fice inda ya sauk'a k'asa sannan ya kirata. Bayan sun gaisa yake ce mata "Se yau aka tuno dani kenan ai na d'au bazaki kira ba."

"Shine kak'i kira kaima wato ko?"

"Gani nayi kaman ina damunki ne Lily not as before kwata-kwata yanzu baki kirana ko na kiraki ma Allah-Allah kike mu gama wayan ki huta ko ba haka ba?"

"Se gashi na baka kunya na kiraka kuwa."

"Waya sani ko Mami ce ta sanya ki na dole kaman ma ina jin muryarta k'asa-k'asa."

"Kai Yaya banda sharri de ya Nazeefah?"

"Lafiyarta k'alau tana wanka ma muna shiri zamu fita."

"Toh yayi kyau a dawo lafiya se anjima."

"Wait!" ya katse ta.

"Yes?"

"Baki fad'a mun mey kikeso ba fa, ko bakiya son tsaraban Yaya?"

"Ina so mana."

"Then tell me then mey kikeso, name anything."

"Anything?" Ta tambayesa tana nazari. Sosai yake jin dad'in hiransu na yau. Watarana Amal ta sake tana hira dashi koda shike yasan ba har cikin ranta take hakan ba kawai de tanayi ne but even still he can't help but to feel happy.

"Anything Lily" ya jaddada mata.

"Ni tsarabar kanka kawai nakeso, ka taho mun da kanka cikin k'oshin lafiya."

"Shikenan abinda kikeso?"

"Yes Yaya" ta tabbatar masa.

"Toh karki damu dal acikin leda zan kawo miki kaina."

"Wani dal acikin leda kuma? Zan de yi maneji da kai ko ka manta kai ba saurayi bane yanzu?"

"Aww abun kuma gori ya koma?" Dariya tasa ta cikin wayan shima besan lokacinda ya jonata suka cigaba da dariyan ba. Ba k'arya acikin soyayyan da yake yi mata, ita ta daban ce, he'll choose spending time together with her than anything in this world. Shi kansa ya san son da yakeyi mata bayida k'arshe kaman yadda bayida farko. Da alama Allah ya soma amsa masa add'o'in da yata sauk'ewa akan Amal ne a gaban ka'aba shiyasa ta soma sakewa da shi haka.

"A hakan kuma zaki aureni ba."

"Don't get too confident ina iya nemo d'an saurayi na in aura."

"Nine nan de d'an saurayin naki karma ki 6ata lokacinki."

"Toh Yaya kar na cinye wa uwar gidanmu lokaci je ka tayata shiri se anjima ko? Mami tace in gaishe ka."

"Toh ina amsawa thanks for calling baby I love you." Wani irin bak'on yanayi ta tsinci kanta da yakirata da 'baby' dukda cewan sunanta ne na gida amma setaji wani iri kodan tana da tabbacin da wata manufar ya fad'a ne?

"You take care" da haka sukayi sallama. Afzal
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment