Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Saturday ba aikin office se suka yini a gida abinsu, da safe sukayi breakfast tare, yau bayan kokon Amal har ta iya taci soyayyan k'wai da fries. Bayan breakfast ta rok'i Afzal da ya kaita salon ta wanke kanta. Shirayawa sukayi tsaf suka fice sede suka tarar da shagon a rufe, dawowansu Afzal yace ze wanke mata da kansa.

"Ya Omri yaushe ka iya wanke kai?" Ta tambayesa da mamaki.

"Da ke kike wanke min nawa?"

"Toh ai naka ba gashin kirki bane akai."

"Kede kam kizo mana kiga."

"A'a nikam gaskiya na yafe haka kurum ka jagwalgwala mun kai?"

"Rania I'm serious ki tsaya kiga in be wanku da kyau ba sekiyi complaining" wardrobe nata ya nufa ya d'auko mata vest da shorts "hungo sanya su."

"Amshi mana Rania kinga fa La'asr ya kusa" amsan tayi ta tu6e ta sanyasu ya jata bathroom d'in. Daga bakin tub d'in ya ajiye mata kujera ta zauna akai ta mik'a kanta ciki inda gashin nata ya sauk'a har k'asan tun d'in. Tsoro yawan gashin nata ya basa shi kansa yama rasa daga ina ze fara wankewan, maganin mey kaud'i kenan.

"Toh Ya Omri ka fara mana" tayi maganan had'e da tattare gashin nata ta d'ago kai tana kallonsa yayin da yake tsaye a kanta.

"Toh ki mayar da kan naki mana ai nasani" ya fad'a confidently sannan ya zauna daga gefenta a bakin tub d'in. Hand shower ya bud'e ya jik'a gashin nata da shi jak'ab sannan ya tsiyaya shampoo akai ya shiga massaging kan a hankali dan dad'i har wani bacci-bacci Amal ta soma ji a gurin. Wanke mata gashin yayi mey kyau shi kansa be tsamman ze iya ba bayan ya wanke ya d'aure mata head towel suka fito ta zauna gaban mirror sannan ta kunce towel d'in tana tsiyaye ruwan.

"Ya Omri zaka iya taimaka mun da jakan hand driers d'ina?" Ta tambayesa politely.

"A ina?"

"A k'asan wardrobe d'ina." Wajen ya nufa ya d'auko ya mik'a mata sannan ya cigaba da tsaye akanta yana ganin yadda take busar da gashin, na d'an lokaci shima ya gane yadda akeyi. Hannunta ya rik'e yana mey dakatar da ita. Da mamaki ta d'ago kai tana kallonsa "Kawo inyi miki."

"Ya Omri ai kayi mey wuyan zan iya yin wannan da kaina karka damu."

"No Rania kawo in miki" murmushi ta sakar masa sannan ya amsa ya shiga busar mata da gashin yana tajewa kaman yadda yaga tana yi har seda gashin ya bushe garau sannan ya jawo mai ya shiga shafa mata bayan nan yayi combing mey kyau sannan ya kama mata shi a tsakar kai sakwa-sakwa.

"Amazing Ya Omri you're just incredible."

"Yayi kyau?"

"Alot, thank you so much."

"Don't mention so you owe me big yanzu."

"Meyasa?"

"Nima wataran se kinyi mun aski." Dariya tasa na sosai "Ashe kuwa zaka ga disappointment har nice zanyi maka aski? Ashe wani ya kusa ya fara yawo da hula."

"Lool" dariyan yake shima '"Yar k'auye ko rik'e clipper ma bata iya ba hala."

"Toh akwai na miji ne a gidan mu da har zan koyan?"

"Ni d'in akwai mace ce a gidan mu har na koyi wanke kan?"

"Ai wanke kai da sauk'i yake akan yin aski barin ma irin naku na 'yan gayu da se an gyara saje, gaban kan ma a cire wani shape, spare me please ni bazan iya ba."

Dariya sosai ta basa amma ya cize, "Toh shikenan zan je Uni sex Salon (salon da maza ke zuwa mata ke zuwa) na Racheal tayi mun askin tunda ita ta iya."

"Gun mace zaka je?" Ta kewayo tana tambayansa da mamaki yayinda kishi ya bayyana karara a fuskanta.

"Toh ba kince ke baki iya ba."

"Toh ka je d'in zunubin ai ku biyu za a rubuta muku banda ni" ta sanar da shi had'e da juya mai baki sannan ta cigaba da harkan gabanta. Murmushin gefe ya saki nan da nan ya canza kayan jikinsa yasa wani bak'in half jamfan da ya mugun amsansa ya feffeshe jikinsa da turare ya zuba accessories nasa sannan ya d'au jakan askinsa ganin fa dagske yake ze fita Amal ta k'urma ihu kafin ya kai ga bakin k'ofan ta sa key ta k'wace.

"Matar Afzal ki bani guri in wuce."

"Wallahi bazaka fita ba."

"Harda rantsuwa?"

"Eh wallahi bazaka fita ba."

"Toh ni da gida na?"

"Eh naji amma bazaka fita ba."

"Askin ke zakiyi mun ne?"

"Ai gashin kama be yi wani tsawo ba fitina ne kawai."

"Nide matsa min."

"Seka rantse gun na miji zakaje tukuna."

"Why?"

"Taya wata mace zata ta6amun kai? Wallahi Nazeefah kad'ai na yarda ta ta6a ka."

"Really?" Ya tambayeta yana dariya.

"Sosai ma kuwa, bayan nan ga 'yan mata cike kullum a shogon so kake su yi mun snatching d'inka?"

"Toh laifin waye? Ba ke kika ce baki iya ba."

"Toh zan koya" dariya sosai ta basa amma ya moze. "Ni matsa min."

"Zan koya Allah zan koya amma kar kaje shagon Racheal dan Allah."

"Yaushe zaki koyan toh?"

"Ya Omri ai kasan ba a dare d'aya zan iya koya ba but zan sa kai."

"Promise?"

"I promise" ta amsa tana gyad'a kai dad'i sosai yaji ya jata jikinsa had'e da zagaye hannayensa a 'yar kunkuminta "Ashe kina sona haka dama?"

"Eh mana" ta amsa tana turo k'aramin bakinta. Bata hankara ba kawai taji yayi owning lips nata a hankali yake turata har suka fad'a kan gado ya shiga yi maya wasanni. Da k'yar ta iya k'watan kanta "Ya Omri yanzu na wanke kaina Allah bazan iya sake jure jik'asa ba."

"Karki damu zanyi miki drying."

"A'a Ya Omri da Allah kayi hak'uri ka bari" ko sauraranta beyi ba ya tu6e vest d'in daga jikinta. "Ya Omri stop wallahi zanyi maka ihu."

"Kiyi d'in se muga mey k'watan ki" haka ya cigaba da sarrafa ta har seda ya kashe mata jiki lissss ya biya buk'atansa.

a_An hour later..._

Amal ce kwance jikin Afzal yana shafa dogon sumarta yayinda wayansa dake kan side drawer ya shiga ruri. "D'an mik'i mun wayana Rania" ba gardama ta juya ta d'ago "Wake kira?" Ya tambayeta.

"Nazeefah" ta amsa had'e da mik'a masa, niyyan basa waje tayi har ta janyo vest nata zata sa seya rik'e hannunta ya sake kwantar da ita a jikinsa tare da zagaye hannunsa a bayanta sannan yayi receiving call d'in.

"Halo Ya Rouhi?"

"Na'am Rabba'atul Bait ya kike?"

"Lafiya ya gida ya Amal?"

"Alhamdulillah lafiyanta."

"Jikin nata da sauk'i?"

"Eh Alhamdulillah."

"Su Daddy sun dawo d'azu."

"Oh haba?"

"Eh."

"Sun dawo lafiya?"

"Lafiya k'alau yaushe zaka zo ka d'aukeni Ya Rouhi?"

"Tunda yau suka dawo mu bari mana gobe? Su huta yau ko?"

"Ya Rouhi anya kuwa you miss me?"

"You know right I do Rabba'atul Bait ki shirya kayakin ki yau kinji? First thing gobe zanzo in d'aukeki."

"Toh shikenan sekazo I love you."

"I love you too" yace sannan ya katse.

"Rania?" Ya kirata kai ta d'ago a hankali tana kallonsa. "I'm sorry kinji?"

"Why? What for?"

"For everything I said to Nazeefah that made you felt jealous."

"Karka damu Ya Omri, tunda nima kana fad'a mun daddad'un kalamu haka dan mey zanji haushi sabida ka fad'awa 'yar uwata? Wannan kishi dole ne amma bawai hakan na nufin naji haushi bane, so karka damu kaji?" Dad'i sosai kalamunta suka sanya sa ya sake rungumeta tsam ajikinsa "I love you soo veryy much Rania."

"So gobe zaka je ka d'auko ta?"

"Yes in shaa Allah har gida tace zata zo ta baki hak'uri."

"Allah kaimu toh."

"Ameen."

"I'll miss you for the 2-2days da zaka na yi mata."

"I'll miss you terribly too Darling" ya sanar da ita had'e da placing mata light kiss a goshi "Tashi muyi wanka toh muyi sallah kinga ana neman hud'u se muje muci abinci ba?"

"Sure Ya Omri."

"Karde har kin mance?"

"Dame fah?"

"Seriously Rania?"

"Yi hak'uri ka tuna mun na d'an sha'afa ne."

"Wato kin ma manta yau zamu fita first baby shopping namu ko?"

"Ya Omri beyi sauri ba?"

"Haka kullum kike cewa ai a hankali a hankali zamuna ragewa please don't say no, I'm so excited."

"Alright toh."

"Kin yarda zamu je?"

"Anything for my Omri." Nan da nan sukayi wanka sukayi sallah sannan suka shirya suka wuce shopping. Siyayya sukayi sosai, Afzal na kwasan kayan baby girl Amal na yin na baby boy se dariya masu shagon suke musu amma ko a jikinsu. Se after 6 suka dawo gida da goshin maghriba.

****

GIDAN ALHJ ABDALLAH.




RANA D'AYA!
#RD 💖

Love... King Miemiebee👄✨



Miemiebee Novels

Friday, 7 September 2018
RANA D'AYA!
BY MIEMIEBEE
PAGE 41




_Assalamu Alaikum readers, I would like to show my deepest appreciation to each and every one of you that took a minute or so out of their precious times and asked, prayed or checked up on me. I really am grateful and feeling much better Allah yabar zumunci ameen. 😘 Before proceeding on, I would like to dedicate and give this chapter to SADNAS marubuciyar •miemiebee a wanki garori• and her amiable group members, thank you so much for the love and support wannan chapter'n naku ne! Xoxo 😘❤️_



Cike da jin dad'i da rawan jiki ta d'auko akwatin ta ajiye kan gado sannan ta shiga fiddo da kayakinta daga wardrobe tana jerasu aciki, taci rabin aikin Mummy tayi knocking bisa k'ofan d'akin. "Come in" ta amsa sannan ta bud'e ta shiga.

"Ya da shirya akwati haka ina zuwa?" Ta soma da tambaya.

"Mummy Ya Afzal yace gobe zezo ya mayar dani d'akina" ta sanar da ita cike da jin dad'i.

"Kai haba!" Mummy ta tambayeta unbelievably tana mey tayata murna.

"Wallahi ai tun last two weeks yaso mayar dani amman bakwa nan yace in hak'ura sekun dawo."

"Allah sarki Afzal, toh Alhamdulillah yayi kyau sosai Allah kaimu."

"Ameen Mummy" ta amsa delightedly.

"Kiga duk kalan rashin hankalin da kika tafka hakan be hanasa yafe miki ba har yake shirin mayar dake d'akinki. Sekiyi ma kanki fad'a Nazeefah ki kiyaye 6ata masa rai, kuyi zaman lafiya da 'yar uwarki ba abinda hakan ze ragar miki."

"Hakane Mummy in shaa Allahu komai ya wuce har gida zanje in samu Amal in bata hak'uri."

"Masha Allah, Allah baku zaman lafiya duka."

"Ameen Mummy."

"Toh kinata hanzari haka ko gobe bazaki had'a kayakin bane?"

"Toh Mummy in kuma da safe zezo fah? Ai gara nayi na gama yanzu tunda ba abinda nakeyi."

"Toh ki sauk'o muci abinci dinner is ready."

"A'a nikam zan sauk'o daga baya sena gama had'a kayakin nawa tukuna."

"Toh barin sanar da Daddy'nku."

"Yauwa do please thank you" nan Mummy ta fice ta ja mata k'ofar. Bayan sun gama cin abincin tayi gyaran murya, "Alhj?" Ta kira Daddy.

"Na'am Hjy Surayya."

"Errm batun Nazeefah ne daman, Afzal yace gobe zezo ya mayar da ita d'akinta." Dummm! Zuciyan Daddy ya buga ko motsi ya kasa yi.

"Alhj lafiya?" Mummy data karanci yanayin da ya fad'a nan take tayi saurin tambaya.

"Lafiya ba komai."

"Nace Afzal ze zo bikon Nazeefah gobe."

"Bazata koma masa ba" ya fad'a zalla. Da mamaki Mummy ta tsaya kallonsa "Dalili Alhj?"

"Nace bazata koma ba zuwa zeyi ya bata takardanta zamansu ya k'are."

Mummy ta kasa amincewa da abinda kunnuwanta ke jiye mata da mamaki tace "Alhj ka ko san me kake fad'i? Har mun samu yaron nan ze mayar da ita d'akinta kake cewa bazata koma ba? Ko kai zaman 'yarnan a gidan nan haka na maka dad'i ne? Ko so kake ka mayar da 'yar taka bazawara?"

"Nide na fad'a miki kije ki sameta kice mata ba inda zata" yana kaiwa nan ya mik'e ya nufi d'akinsa. Kai Mummy ta kewayo tana kallon Khaleefah da shima ya tsaya kallonta da d'umbun mamaki d'auke a fuskokinsu. Daga bisani ta mik'e ta je ta samu Nazeefah a d'aki, lokacin har ta gama had'a kayakin nata tana cikin tattare jakukkunanta da takalma.

"Nazeefah wani abun ya had'aki da Daddy'nku ne?" Mummy ta tambayeta bayan ta zauna bakin gado.

"A'a wani abu ne?"

"Gashi ina mishi maganan gobe Afzal zezo ya d'aukeki yana cewa ba inda zaki."

"Ba inda zani kuma?" Nazeefah tayi exclaiming cike da k'in yarda.

"Haka yace wai zamanki da Afzal ya k'are."

"Dalili? Ya Afzal yayi mishi wani abu ne?" Ta tambaya a rud'e.

"Anya kuwa? D'au waya ki kirasa muji" ba makawa ta janyo wayanta ta shiga kiran Afzal sede yayi ta ruri har ya tsinke be d'aga ba kasancewar ya riga ya kwanta. Three missed calls ta masa be d'aga ba ta hak'ura.

"Mummy he ain't picking up."

"Kode yayi bacci ne?"

"Might be amma meyasa Daddy ze hana Ya Afzal mayar dani d'akina?"

"Shine nima ban sani ba Nazeefah."

"Mummy dan Allah kiyi mishi magana Mummy bana son abinda ze rabani da Ya Afzal please dan Allah Daddy ya rufa mun asiri."

"Karki damu zanyi masa magana ki kwantar da hankalinki nake ga sun d'an samu sa6ani ne."

"Please do Mummy."

"I'll je kici abinci kinga dare nayi."

"Ni bana jin yunwa."

"Toh kiyi sallah ki kwanta seda safe" da haka Mummy taja mata k'ofar ta fice taje ta samu Daddy dake mik'e akan gado ya zura wa ceiling ido. Sallama tayi amma ko amsawa beyi ba don yadda hankalinsa sam baya jikinsa.

"Alhj?" Ta kirasa bayan ta zauna a gefensa nan ma shiru k'arshe seda ta d'an ta6asa sannan ya dawo hankalinsa. "Alhj dan Allah ka tashi muyi magana."

"Wace magana ce zamuyi? Na gaya miki 'yar nan bazata koma gidan Afzal ba ko baki ji bane?"

"Naji Alhj amma-"

"Amma mey?" ya katseta a fusace "Ni da 'yata kike son nuna mun iko akanta? Bazata koma ba bazata koma ba."

"Bawai haka bane Alhj a tunani na koda sa6ani kuka samu da shi Afzal d'in be kamata ka hana sa miyar da yarinyar nan d'akinta ba tunda tana sonsa yana sonta-"

"Surayya dan Allah nace kiyi min shiru" ya katseta cike da rashin hak'uri "Idan kuma shirun ne bazaki iya ba ina iya bar miki d'akin."

"Allah huci zuciyanka gobe zamuyi magana" Daddy be sake ce mata komai ba. Abinda ya kama daga kan shi harma Mummy da ita Nazeefar bawanda ya iya samun baccin kirki ranan barin ma Daddy da yake ganin asirin sa ya kusa tonuwa besan da wani idon ze sake kallon iyalansa ba.

****
Kiran Afzal ne ya tada Nazeefah daga bacci washegari ba shiri ta d'aga wayan.

"Good morning Baby" ya fad'a a karo na farko.

"Ya Rouhi" ta kirasa cike da tashin hankali.

"Yes is everything okay?" Yayi saurin tambaya.

"Ya Rouhi wani abu ya had'aka da Daddy ne?"

"Nop why?"

"Ya Rouhi cewa yayi wai bazaka miyar dani d'akina ba."

"What?!" Yayi exclaiming had'e da dropping cup na tea da yake sha.

"Ya Rouhi please do something I don't want to be separated from you."

"Karki damu I'm on way now" daga haka ya katse wayan ya fad'a d'aki ya d'au key'n motansa. "Rania?" yayi knocking bakin k'ofan bayin.

"Yes Ya Omri?" Ta amsa daga ciki.

"Zan fita ina zuwa."

"Toh seka dawo" be 6ata lokaci ba ya fice.

****
Mik'ewa tayi ta fad'a bayi tayi brushing ta canza kayan jikinta sannan ta sauk'o k'asa dan karyawa. Hayaniyan data jiyo ta gun d'akin Daddy yasa ta k'arisa gurin inda ta tarar da Mummy da Daddy se faman fad'a sukeyi.

"Haka kawai bazan zuba ido ka mayar min da 'ya bazawara ba wallahi Afzal zezo kuma ze tafi da yarinyar nan" Mummy ta fad'a cike da tsiwa kaman ba ita ba.

"Idan ke kike iko da Nazeefar se mu gani" Daddy ya mayar mata.

"Daddy dan Allah kayi hak'uri" Nazeefah da idanunta suka ciko tim da hawaye ta tsoma baki "Daddy dan Allah karka rabani da Ya Afzal Daddy idan wani abun ya maka I'm sorry on his behalf please don't separate us two."

"Kiyi hak'uri Nazeefah amma rabuwa da Afzal ya zama dole" kuka ta shiga yi na hak'ik'a "Daddy dan Allah kar ka min haka dan Allah kayi hak'uri I'm so sorry" har cikin zuciyansa Daddy yaji ba dad'i ashe akan 'yarsa Allah ze rama wa Jameelah abinda yayi mata, why not akanshi? Meyasa se akan 'yarsa? Ashe anan Allah na nuna masa kamar yadda alheri yake d'anko shima sharri haka ne muddin baka shuk'a me kyau ba toh 'ya'yanka ma bazasu ga mey kyau ba.

"Ki barsa" Mummy tace da ita tana mey janta jiki "Afzal d'in ai zezo se ya hanaki binsa muga" tana kaiwa nan taja Nazeefah d'akinta ta shiga lalashinta amma inaa Nazeefah se kuka. Ba'a dad'e ba sega Afzal ya taho yana isa ya kira Nazeefah inda ta tura Khaleefah ya shigo da shi zuwa parlourn Daddy sannan ya shiga daga ciki yayi ma Mummy magana. Mayafi ta yafa ta fito da Nazeefah biye a bayanta. Bayan sun gaisa take tambayarsa ko abu ya had'asa da Daddy.

"Wallahi ba komai Mummy kema kinsan bazan so abinda ze shiga tsakani na da Daddy ba kodan Nazeefah."

"Hakane Afzal yanzu abinda nakeso da kai ka d'au Nazeefah ku tafi karka sauraresa."

"Nace baze tafi da ita ba" suka jiyo muryan Daddy kaman daga sama nan take duk suka kewayo suna kallonsa.

Har k'asa Afzal ya sauk'a ya gaishesa amma ko amsawa beyi ba "Ka rubuta mata takardanta yanzun nan bazata bika ko ina ba."

"Daddy ban fahimce ka ba."

"Sakin ta nake so kayi yanzun anan" ya jaddada masa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya sa salati "Daddy idan wani abun nayi maka kayi hak'uri amma karka rabani da Nazeefah dan Allah."

"Baka ji me nace bane?"

"Daddy naji dan Allah kayi hak'uri."

"Ai ni na rok'eka da ka aureta daman tun farko yanzu kuma ina rok'onka da ka sawwak'e mata zaman ku ya k'are."

"But Daddy I love Nazeefah, ina sonta bana kuma son in rabu da ita."

"Zaman ku ya k'are nace Afzal ka sakar min 'ya."

"Wai Alhj meke damunka ne? Haka kawai kake shirin shiga tsakanin yaran nan a ina aka ta6a yin hakan?"

"Hjy Surayya banyi magana dake ba saboda haka ba ruwanki."

"Niko nake da ruwa acikin zancen nan taya zaka sa na dole miji ya rabu da matarsa?"

"Afzal ka rubutawa yarinyar nan takardanta nace" yace kaman wanda beji abinda Mummy ta fad'a ba.

"Daddy dan Allah kayi hak'uri" Nazeefah ta rok'esa cikin tsan-tsan kuka saidai ko kallonta beyi ba. "Idan kuma ranka ya 6aci ne game da dawo dani gida da Ya Afzal yayi kayi hak'uri amma bashida laifi, nice nayi mar laifi a matsayinsa na mey mata biyu kuma dole ya kwatanta yin adalci tsakani na da 'yar uwata. Tunda ni nasa Amal tayi yaji na raba ta da gidanta nima dole a rabani da nawa. Amma ka duba yanzu da Amal ta dawo ba gashi yana son ya miyar dani d'akina ba? Kuma seka hana hakan Daddy? Please don't." Na sosai maganganun Nazeefah suka shige jikin Daddy suna masu samun mazauni a birnin zuciyansa. Ba shi kad'ai ba kowa seda kalamun nata suka ta6a sa a gurin amma haka na dole Daddy yayi banza da ita. "Afzal ba magana nake ma ba?"

"Daddy I'm terribly sorry idan mayar da Nazeefah gida da nayi na kwanakin nan ne ya 6ata maka rai kamar yadda Nazeefah ta fad'a. I had no option but please don't be mad, I'm sorry and I do love Nazeefah."

"Ka rubuta mata takardanta nace-"

"Baze rubuta ba Alhj nace baze rubuta ba" Mummy da ranta in yayi dubu be 6aci ba ta katse sa.

"Afzal baka jina ne?"

"Daddy ina ji" ya amsa na dole.

"Ka rubuta mata takardanta nace." Kuka Nazeefah ke sosai tace, "Please don't do this Daddy, please."

"Me kake jira ne har yanzu Afzal?" Daddy yayi kaman be jita ba "Biro ne ko takarda baka da ita? Khaleefah wuce d'akinka ka d'auko mar."

"Daddy kayi hak'uri amma ka sani bazan iya rubutawa Nazeefah takardan saki haka kawai ba please understand me."

"Daddy kayi hak'uri mana" Khaleefah da ya zuba musu ido tun d'azun ya fad'a.

"Daddy please don't do this" Nazeefah ta kar6esa, "Please don't Daddy, Afzal is sorry kayi hak'uri ka barni in tafi dashi."

"Nazeefah kiyi hak'uri amma gaba kad'an zaki gane am doing this for your own good."

"Which good Daddy? Kana shirin raba ni da mijina wanda yake sona nake kuma sonsa kake cewa you're doing this for me? How? Mummy how is this going to be of help to me?" Ta jiyo cikin tsananin kuka tana kallon Mummy data janyota jiki.

"Zaman ki da Afzal ya haramta Nazeefah bazeyi ki cigaba da zama da shi ba dan haka ya zamanto dole ya sakeki ya sauwak'e miki."

"Kaman ya zamansu ya haramta Alhj? Wani abun sukayi ne da zakace zamansu ya haramta?" Mummy tayi saurin tambayarsa "Dan na d'an wata ya korota gida kuma akan gaskiyansa se kace zamansu ya haramta? A ina ne idan mace tayi laifi akace miji baze hukunta ta ba? Tell me!" Tayi demanding.

"Nide na fad'i nawa zamansu ya haramta don haka ya k'are, Khaleefah yi maza ka d'auko mar paper da biro kar ka bari in nanata kaina."

"Khaleefah zauna ba inda zaka" Mummy ta dakatar da Khaleefah daya zabura.

"Daddy I'm sorry amma bazan iya rubutawa Nazeefah takardanta ba" Afzal ya fad'a had'e da mik'ewa "I'll get going ina zuwa amma."

"Afzal! Afzal!" Kiransa Daddy yake amma ko kewayowa beyi ba. Gidansu ya wuce direct unfortunately Abba bayi nan yayi tafiya Ummi kad'ai ya tarar. Irga mata halin da ake ciki yayi inda ta sha mamaki na sosai.

"Toh yanzu ya zamuyi? Amma meya samu Alhj Abdallah haka?"

"Wallahi Ummi I don't know and he seem so serious about it."

"Subhanallahi meya buga masa kai toh? Kode koran Nazeefah gida da kayi d'inne ya 6ata mar rai haka?"

"Amma ai ba koran walak'anci nayi mata ba Ummi besides Nazeefah was at fault dole in hukunta ta kodan inyi ma Amal adalci."

"Tabbas Prince kuma nima bawai nace kayi laifi bane am just surprised gashi Abbanka baya nan."

"Se yaushe ze dawo?"

"Yau yace."

"Toh kafin nan kije ki samu Daddy kiyi mishi magana please."

"Ni kuma Prince?" Ta dafe k'irji.

"Eh Ummi I don't want to lose Nazeefah please go" ya fad'a cikin tsananin tashin hankali.

"Prince ta ina zanje in fara yi wa Alhj Abdallah magana a matsayinsa na sirki na? Ai beyi fasali ba kade bari Abban naka ya dawo zuwa anjima."

"Ummi please" ya rok'eta abin tausayi.

"I'm sorry Prince but I can't" kafad'ansa ta dafe "Abbanka ze dawo anjima I'll be the one to explain everything to him kayi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment