Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bayan nan ba komai se cup na ruwanta da juice.

"Nawa kuma fah?" Ya tambayeta bayan jan ajin da ta gama yi masa daga bisani tace, "Ban girka ba" ba tare da ta kalli direction nasa ba.

"Mey na ce miki kafin na fita?"

"Ba zaka iya ba da barazanar siyo abinci? In ba shi ba toh na manta."

"Young lady let me make this clear to you muddin kina zaune a cikin gidan nan a k'ark'ashina kike kina ganewa ko? I won't allow it you disrespect me in my own house."

"Hilarious!" Tayi exclaiming tare da k'yalk'yalewa da dariyan daya mugun k'ular da Afzal "Sannu masu gida, nayi maka rashin kunyan me ka isa kayi? Iyaka kace zaka sakeni, please make it quick ko duka na zakayi? Yanzu kai bakaji kunya ba? Ka kalli tsabar cikin idanu na kace wai inyi maka girki? LOL ina gadara da ji da kai d'in ya tafi? Idan ban manta ba bakin da yace ayi mishi girki yau shi ya ta6a cewa baze iya cin abinda hannayena suka girka ba. Now I see you're not a man of your words" ta k'are tana zuba masa mumunan kallo da dara-daran idanunta. Da k'yar Afzal ya iya danne zuciyansa ya juya ya fice tare da bar mata gidan gabad'aya. Idan yace ze biyewa Nazeefah to k'arshenta zata sanya sa aikata abin kunya ne, amman ko ta guji randa zata turasa jikin bango.

Da harara ta bisa yayinda ya ficce tare da furta "Tafi nono fari" k'asa-k'asa.

A da yayi niyyan zuwa gida gun Ummi amman gudun abinda hakan ze iya haifarwa se kawai ya wuce gidansu Amal inda ya tarar da ita zaune kan tabarma tana bitan karatu. Sallama yayi a hankali sannan ya shiga.

"Wa'alaikumus Salam" ta amsa dai-dai lokacin data kai k'arshen aya jin murya kaman na yayanta . "Yaya!" Ta yi exclaiming cike da jin dad'i bayan ca ta tabbatar da cewa eh shi d'inne. Sede sam ba walwala a fuskarsa har izuwa lokacinda ya k'ariso ya zauna a kan benchin dake gefen taburman da take zaune.

  "Yaya ina yini?" Ta gaishesa tana mey ajiye Qur'anin da take karantawa a kan mazauninsa.

   "Yaya meya faru?" Ta kuma tambaya tana me k'are masa kallo.

  "Lily I'm hungry" ya sanar da ita tamkar wani yaro k'arami.

  "Yunwa kuma?" Ta nanata "Meya faru? Nazeefah bata gida ne?" Jin yayi shiru tayi saurin mik'ewa ta zarce kitchen Allah yaso yau shinkafa da wake da stew sukayi ba tuwo kaman na jiya ba. Da sauri-sauri tayi serving nasa ta d'auko masa d'aya daga cikin gorunan aldeb dake kula ta ajiye masa.

  "Gashi Allah sa ka iya cin abincin gidan namu" a nitse ya shiga cin abincin yayinda ta d'ebo mishi ruwa a cikin wata plastic jug. Komawa tayi ta zauna akan taburman had'e da k'ura masa ido tana me mamakin yadda yake cin abincin a hankali dukda cewa yuwa ta addabesa, hakan ba k'aramin burgeta yayi ba. Seda ya cinye tas ya kora da ragowan ruwansa da aldeb d'in sannan ya maido da kallonsa akanta inda idonsu ya had'e, murmushi ta sakar masa "In k'ara maka?"

"Me kika mayar dani, glutton?"

Murmushi kad'an tasa had'e da kawar da kanta "Thank you Lily" ya furta wanda hakan yasata maido da kallonta a garesa "Don't mention Yaya you deserve morethan this" murmushin ya miyar mata "ina Mami?" Ya tambaya.

  "Ta fita gidan biki."

  "Papi fah?"

  "Ya fita kasuwa."

  "Yau ma ked'ai ce a gida?"

  "Eh nima inason in gama bita na ne daman se in fita."

  "Se kuma nazo namiki ruining schedule ko?"

"Haba Yaya ko kad'an wallahi karka damu amman meya faru?"

  "Game deh?" Ya tambayeta.

  "Waya ta6a min kai? Waya hana min ka abinci?" Shirun da yayi tayi zaton ko Nazeefah ce, amman meye dalili?
  "Nazeefah ce?" Ta tambaya a hankali, kai zallah ya gyad'a mata.

  "Toh meyasa?"

  "I don't wanna talk about it Lily I'm sorry."

"It's okay na fahimce ka."

"All I know is hak'uri na ya kusa k'arewa."

  "Ayya Yaya se kana had'awa da hak'uri kasan mu mata rauni ne."

"Rainin hankalin Nazeefah ya soma yawa ne Lily, she is taking my patience for granted."

  "Se hak'uri Yaya wataran se labari kuma ai kaga Nazeefah yarinya ce idan ban manta ba kai ka fad'a mun cewa she's just 17 years old wasu abubuwan se kana overlooking amman ka sake hak'uri."

"Shikenan Lily ya wuce."

  
**** Akan ana gaba zama ya daidaita, tsakanin Afzal da Nazeefah sede abinda ya k'aru. Tun kan rashin kunyan da tayi masa ya daina shiga harkarta kwata-kwata kowa zaman kansa yake a gidan, har rana me kaman ta yau kuwa kwana be ta6a had'asu ba, girki de Nazeefah nayi duk da cewa ba kullum ba amman tanayi na dai-dai bakinta kad'ai, shima Afzal ko da wasa be sakeyi takan kulolinta ba. Gado ba gwaninta ba, munde san hali irin na Afzal idan yayi fushi da abu to ciresa yake gabad'aya daga ransa. Abincinsa yawancin a restaurant yake ci kokuwa gida gun Ummi and atimes gun su Amal.

Ana cikin haka ne su Nazeefah suka bud'e makaranta zasu koma second semester kenan. Wayyo ita dad'i kasheta, aga wa Afzal zena fita yana bari a gida yanzu, itama idan ta fita tun safe se shida zata na dawowa abinta. Da safe tsab yau ta tashi ta shirya abinta, bayan ta karya ta leqa parlour taga Afzal bai nan d'akinsa ta nufa ta kwankwasa k'ofa, bayan d'an lokaci ya taso ya bud'e da alama bacci yake don wani kakkafewan da idanunsa sukeyi. Sanye yake da guntun wando zalla wanda hakan ya bawa Nazeefah daman k'are wa k'irar jikinsa kallo. Wai wai wai zalla take furtawa a zuciyanta yayinda ta kasa d'aga idanunta daga kan well visble abs nasa, packs guda shidan nan duk sun bayyano. Ouu la la!

"Lafiya kinzo kinyi min tsaye bakin k'ofa?" Ya tambayeta yana me tsamo ta daga duniyar tunanin data wula. Da sauri ta kad'a kanta had'e da kawar da kai yayinda ta shiga jin haushin kanta yanzu shikenan Afzal ze soma jin kansa tunda ya kamata tana kallonsa ba ko kyaftawa haka shin meke damunta ne? Mstw! Mozewa tayi tace, "Zani school tunda kayi gwanintan d'aukoni daga gidan mahaifina ya zamo dole ka bani kud'in break bayan nan kuma inason yin full tank wa mota na."

Se yanzu Afzal ya bud'e idanunsa da kyau yake kuma k'are mata kallo yanzu da irin wannan shirin ne matar aure zata fita? Lalle yau ya sake tabbatawa Nazeefah batada hankali. Kallonta yake daga sama zuwa k'asa. Na farko d'aurin kanta ma ba me mutunci bane ina d'aurin nan na ture kaga tsiya? Shi ta buga a kanta k'eyar nan gabad'ai gashinta ne a waje data nannad'e, ga kuma kayan da take sanye da, wata matsatssiyar straight gown me tsagu a baya wanda yabi surar jikinta tun daga sama har k'asa gaba kuma k'aramar mayafin data d'auka wanda ya kasance small size na gyalen R&S da ta nannad'e sa gefen kafad'arta d'aya. Be ce da ita komai ba ya juya cikin d'akin ya nufi gun safe nasa had'e da sa password d'in. Bayan ya bud'u ya k'irgo kud'i ya dawo ya mik'a mata amsa tayi cike da walak'anci da tak'ama sekace ba wacce tazo tana tambayar abu ba. Da sauri ta shiga k'irgawa dubu shida ta tarar kafin ta kawo wata tunanin a ranta yace, "2k kud'in makarantar ki 4k kuma kiyi full tank da ita" yana kaiwa nan ya ja k'ofansa ya rufe ba tare da ya bata daman yin magana ba.

Mamaki ne ya mamaye Nazeefah don kuwa ko a mafarki bata ta6a kawowa a ranta cewa Afzal ze bata kud'in kashewa a rana har dubu biyu ba kode yana nufin har da na gobe ne? Amma ai da ya sanar da ita.
A gida ma gabad'aya dubu Mami ke bata dama-dama ma Daddy ne ke bata dubu biyu. Lallai kuwa auren nan ya d'an had'u ta wani fannin.

**** A makaranta...

Nazeefah ne zaune da k'awayenta suna cin abinci a restaurant. Nana ce ta ta6e baki tace, "Amarya kenan kinga wani fresh da kika k'ara kuwa? Gaskia angon nan namu na kula dake."

"Toh ba dolensa ba" ta amsa tana murmushi.

"Amman ya ganki yau da safe kuwa?"

"Sosai ma ai da shi ze kawo nima nace ya bari kawai yayi baccinsa, wani abu ne?"

"Babu ai naga wankan da kika d'aukan ne sekace ba matar aure ba."

"So kike kice wai mijina baya kishina?"

"Kusan hakan Babe kinga Hafiz (saurayinta da ake shirin yi masu aure) wallahi ko gyale ya haneni da sawa sena tabbata yayi tafiya nake sa abuna amman yana gari kam ban isa ba, d'an banzan kishi ne da shi." Sosai kalamun Nana suka tsaya wa Nazeefah a wuya, da biyu dama itama tayi wannan shed'anin shirin taji ko Afzal zeyi magana se gashi kamar yadda ya saba manna mata hakan yayi. Yo dama mutumin da ba sonka yake ba kam ai ba yadda za'ayi yayi kishin ka wai ma tukun meyasa ta damu? Da yayi kishinta da kar yayi duk uwa ubansu d'aya.

Dagewa tayi tace; "Ai da dad'ewa na fahimci Hafiz nakin nan d'an zamanin da ne yo me acikin sa gyale? Kuma kinga Baby na ya yarda dani yasan ko tsindir d'ina na fita bazan kula wani a waje ba kede ki binciki Hafiz naki gani nake kaman be yarda dake ba."

"Haka dey kikace anyways ga ankon nan fa kunsan abun ya matso" Nana tayi maganan had'e da shiga photos a wayanta don nuna wa k'awayen nata sample. Nazeefah ce ta soma kar6a tana gani "Na farkon lace ce 15k ita zaku sa a pre wedding dinner se atamfar kuma a kamu ita 5k ce, next material d'in kuma na dinner'n ango ne wanda za'ayi a Abuja shi 10k ne altogether is 30k kenan. Kar ku damu da siyan head ango ya d'au nauyin duka biyun tare da makeup wa 3 best friends d'ina."

"Awww kice mu soma booking makeup artist tun yanzu" cewar Nazeefah tana mik'a wa Adama wayar.

"Manyaaaa" Rumaysa tayi praising nata "Gaskiya na sha wutan lace d'innan bari zuwa anjima zan miki transferring kud'in."

"Ni kuma ko zuwa gobe ko jibi haka kunsan Ummi sunyi tafiya banida enough kud'i" cewar Hadiza.

"Nazeefah kefa?" Tambayar Nana.

"Ai ko a yanzu ma ina iya k'irgawa in baki tunanin barin Baby na nike for this Abuja dinner anya kuwa zan iya?"

"Su masu baby! Sha wannan iyayi sede kiyi ma su Rumaysa da basu da direction nikam kinga na kusa" take suka rushe da dariya.

"Alright zuwa anjima zan miki transferring."

Chan da yamma Nazeefah ta dawo gida, ruwa ta watsa ta nemi vest da wata wandon data d'an sauk'o k'asan guiwa da kad'an tasa sannan ta shafa mai a kanta ta kama a tsakiya ta fito. A parlour ta tarar da Afzal yana d'an wasu aikin office d'in, kamar yadda ta saba ba sallama bale gaisuwa ta k'arisa kansa tayi tsaye "Malam ina buk'atan kud'i k'awata zatayi aure kud'in anko 30k, d'inki 15 se kuma na gudumawa 20k."

Sai dai yadda kuka san kurma haka ya mata wajen ko d'aga kai ya kalleta ma beyi ba ran Nazeefah in yayi dubu be 6aci ba, a rayuwa ba abunda ta tsana kaman shariya.

"Mallam ya ina maka magana kana mai dani mahaukaciya?" Nan ma shirun yayi mata, gabansa ta shawo "Mallam magana fa nake" sede shiru by now zuciyan Nazeefah tafasa yake. Paper'n data ga yana typing content nasa a computer tasa hannu ta waske se a nan ya d'ago lumsassun idanunsa yana kallonta.

"Ban gane ina maka magana ba kana mayar dani yar iska, da ba don kayi gwaninta ba ka aureni you think zan tsaya ina tambayarka kud'i ne har ma ka tsaya kana nuna min isa da tak'ama? Wallahi Afzal kake ko wa ka sani ba'a tsiya ka d'auko ni ba, a gida ban ta6a neman abu k'ark'ashin iyayena ba na rasa saboda haka I see no reaso why zanna maka magana kana manna min. Ka bani abinda nake buk'ata wallahi idan ka bari raina ya 6aci naje gida na tambaya kaine da jin kunya ace mutum ko rik'e mace tal ya kasa." Tun d'azun jira take yayi magana amman yak'iyi banda idon da ya kafa mata kaman hoto, bayan ya gama sauraronta daga bisani kawai ya wafce paper'n nasa data d'auke had'e da mik'ewa. Laptop nasa ya d'aga ya shiga nufan d'akinsa yayinda take binsa a baya tana k'orafi da surutu tana habaici tana zaginsa.

"Ai da fili ka fito kace baka da kud'in da yafi maka ba wai ka tsaya kana nuna isa da tak'ama ba andeji kunya wallahi ace common kud'in da be taka kara ya karya ba ya gagari mutum" har anan be tanka taba, yana kaiwa d'akinsa ya shiga had'e da sa makulli ya rufe. Ganin suratai da buga k'ofan nasa da take ba shi zaisa ya taso ya bata kud'in ba don kanta ta wuce d'akinta.

Washegari tun 1 ta dawo gida ta dafa indomie taci sannan ta shirya tsaf ita gata me iyaye tunda miji ya hanata kud'i zata je ta amsa a gun su. Tana cikin shan ruwa sega Afzal ya dawo daga office ko meya faru kuma yau? Shi d'inda se yamma yake dawowa kode wata mantuwar yayi? Ta tambayi kanta.

"Yauwa Mallam ka dawo a dai-dai zani gidan mahaifina in tambayeshi kud'in daka hana mun, zan nuna maka rijiya ba gun wasan yaro bane keep your damn money" yana gama sauraronta ya shige d'akinsa file nasa daya mance ya d'auko sannan ya fito. Wato kuma yau don munafirci don zata gidansu shine har da sa babban mayafi ta lullu6e jikinta haka, lallai munafiki ya shiga uku a rayuwa Afzal yayi tunanin haka a ransa. Shi bema d'aurata a ka ba bale abubuwan da takeyi su damesa kamar yadda Amal ta fad'i yarinta ke damunta ga rashin wayo da tarbiyya.

Isarta gidansu keda wuya se lale masu gadi da masu aiki suke yi mata kasancewar ta d'au kusan sati biyu bata lek'o su ba. Ita da Khaleefah sekace ba karnukan da suka saba haushi ba harda hugging nasu ba k'arya sunyi kewar junansu. Parlour'n Daddy ta shiga inda ta tarar da shi da Mummy zaune. Waje ta nema a k'asa kaman mey hankalin k'arshe sannan ta gaishesu cike da girmamawa. Sosai suka ji dad'in ganinta cikin wannan kamilalliyar shirin, barin ma Daddy. Ina irin manyan gyalen nan na kashka shi ta lullu6e jikinta dashi tun daga kanta.

"Ina Afzal ko yau baku taho tare bane?" Ya tambayeta.

  "Wallahi aiki yayi masa yawa in ba haka ba daman tare zamu taho amman ko yana gisheku barin ma Mummy wai yaushe zaki sake kawo mana kwad'on dambun nan naki mey dad'i."
Murmusawa Mummy tayi cike da jin dad'i ita kam Alhamdulillah Allah ya bata sirki d'an arziki imagine zuwansu sau biyu nan se yayi ma Khaleefah kyautan kud'i itako na zani. "Kice masa kwanan nan in shaa Allah."

"Toh Mummy."

"Toh bari in barku tare zan d'an fita" Daddy ya sanar dasu.

"Daddy idan ba damuwa ina d'an buk'atan wani abu."

"Mene kenan Nazeefah akwai matsala ne?"

  "A'a" tayi saurin amsawa.

"Toh madallah ina jinki."

"Daddy k'awata ce daman zatayi aure" ta fara a nitse.

"Toh masha-Allah Allah ya sanya alheri."

"Ameen" both ita da Mummy suka amsa a tare.

"Toh Daddy kud'in anko nikeso dana gudumawa."

"Toh nawa ne?"

"Ankon 30k ne se kuma na d'inki 15k dana gudumawa dubu ashirin, Mummy ai zaki iya tuna k'awata data kawo min bedsheets na 40-40k d'innan guda biyu a bikina ko?"

"Tabbas Allah ya basu zaman lafiya."

"Yauwa toh daddy ita zata yi aure."

"Toh kin tambayi Afzal kud'in ne kokuwa?" ya tambayeta. Gabanta ne taji yayi mumunan fad'i me hakan ke nufi? Kame-kame ta shiga yi chan de ta amsa da "A'a" k'sa-k'asa.

"Toh ai shi ya kamata ki soma tambaya Nazeefah bani ba."

"Ban fahimce kaba Daddy" a bak'wance zancen ya isketa.

"Nauyin ki ya tashi daga kaina ya koma kan mijnki Afzal, duk abinda kike buk'ata shi zaki tambaya sai idan abin yafi k'arfinsa ne zan iya taimaka miki nan ma sena tambayi izininsa saboda kar a nuna masa rashin isa, ina fatan kin fahimce ni? So kije ki tambayesa tukuna se idan ya nuna baida hali dukda cewa ma nasan hakan baze faru ba amman idan abin ya juya hakan zan tambayesa izini ko nawa kikeso ni kuma na miki alk'awari zan baki."

"Allah sarki Daddy se naga kaman hakan yayi sauri I mean da auren mu wata nawa ne da zan soma tambayansa kud'i masu yawa haka banda na makarantar da yake bani. Daddy please ko na yau kawai ka bani yaso zuwa nan gaba mun sake sakewa da juna sena soma tambayarsa banson yayi mun mumunar fassara yayi tunanin kud'insa nakeso cin ko makamancin haka."

"Sam Afzal baze miki mumunar fahimta ba Nazeefah, Afzal yaro ne mey hankali da tunani."

"Sosai ma kuwa" Mummy ta sanya baki tana mey gyad'a kai. Ji Nazeefah ke wane tasa hannu a kai ta k'urma ihu yanzu bayan gorin iyayen data gama yiwa Afzal ne Daddy keson ta koma ta sake tambayansa? Chab! Yau tana cikin wani yanayi tasani ko sama da k'asa zata had'a Afzal ba bata kud'in nan zeyi ba, menene mafita?

"Daddy d-" ido Mummy tayi mata da wuri don haka tayi shiru "Toh ni bari in shirya zan d'an fita idan kin koma gida ki gaishe min da Afzal." Ba don tanaso ba ta amsa da "Toh Allah ya kare." Daddy na fita ta taso ta zauna kusa da Mummy.

"Mummy dan Allah ki taimaka min."

"Dame?"

"Mummy da kud'in please."

"Wai baki ji abinda Daddy'nku ya fad'a miki bane? Bawai ana hanaki kud'in bane Nazeefah ki gane mana ba a son nunawa Afzal d'in rashin isa ne, baze ji dad'i ba amman yanzu ki gwada tambayansa muji me zece."

"Ni banason in tambayesa."

"Dalili?" Mummy ta tambaya da mamaki.

"Haba mana Mummy kinde san halin Afzal."

"Kode naki ba? Tell me something kin tambayesa kud'in nan da rashin kunya da isa yak'i ya baki shine kikazo nan kina yi mana k'arya ko."

"Ni bance ba."

"Ja chan har ni zan haifeki ki tsaya kina min k'arya? Toh wallahi ki cigaba."

"Toh Mummy laifi na ne? Na tambayesa ya hanani me kikeson inyi?"

"K'arya kike wallahi, idan har a cikin girmamawa kika durk'usa kika tambayesa nasani tabbas ze baki kud'in nan tunda de Allah yayi yana da hali."

"Wallahi yayi kad'an in durk'usa a gabansa" ta furta ba tare da tasan yaushe ba.

"Innalillahi! Kika ce mey?" Mummy ta tambaye ta cike da mamaki. "Wato rashin kunya kike yi masa a gidan ko? Toh wallahi ki cigaba ranan da ya illata ki kece da asara."

"Mummy please ni in zaki bani kud'in toh in bazaki bani ba ni zan tafi."

"Ki tafi kar kuma ki sake dawowa maras kunya kawai a da nayi niyyan baki kud'in nan amman tunda haka ne na fasa. Sani ya rage miki ko kiyi humbling kanki ki basa hak'uri ki tambayesa cike da girmamawa ko kuma kije bikin k'awarki ba anko ba gudumawa kece k'awaye zasuyi gulma a bayan ido bani ba kin ganni nan k'awata ta haihu zani suna in kin tashi tafiya ki gaishe min da Afzal."

  "Mummy dan Allah karki min haka Mummy kiyi hak'uri."

"Afzal zaki baiwa hak'uri bani ba" tana kaiwa nan ta mik'e ko sake kallon Nazeefah dake ta kiran sunanta batayi ba ta wuce d'akinta. Haka idily Nazeefah ta cigaba da zama cikin parlourn totally out of what to do, gashi ba kud'in arziki bane acikin account nata sam be kai N50k ba. Haka duk su Rumaysa suka sata gaba a bikinta seda kud'in nata ya k'are tas. Mstww! Dan kanta taja motarta ta fice ta koma gida tun isarta take tunanin yadda zata 6ullowa al'amarin nan don a gaskiya bata jin zata iya yin abinda Mummy tace tayi. Ai ma zubar da aji ne, idan ta durk'usa a gaban Afzal ai seya fara jin kanshi ya aza ya kai ne alhalin ba kowa yake ba a idanunta gaskiya no way! Toh kode ta fasa zuwa bikin ne? Gab da lokacin bikin ta soma yi musu k'aryan laulayi na damunta. Kai amman fa k'arya ba kyau don komin yaya ne a k'arshe za'a kamata, haka kawai mutuncinta ya kwa6e. Wayyo Allah menene mafita?

Share maganar tayi har na tsawon kwana biyu, bayan sati d'aya Nana ta soma damunta da kira tana tambayarta ko lafiya ita da ta d'au Nazeefah ce zata soma siyan anko sekuma gashi. K'arya Nazeefah tayi mata cewa ta mance ne amman right away zatayi mata sending kud'in in shaa Allah da haka sukayi sallama. D'akin nata ta shiga zagayawa tana tunanin ya zata 6ullowa al'amarin sede ta kasa yanke hukuncin komi daga k'arshe de ta yanke hukuncin kirar aminiyarta ko zata iya ranta mata kud'i kafin nan.

"Babe wallahi banida kud'i nima da k'yar na samu na had'a kud'in ankon nan na bada d'inki haka ma yanzu bansan me zan kai mata as gudumawa ba wannan shegen saurayin nawa ne ya kod'a ni in gaya miki yace ze turo min kud'i shiru."

"Toh bestie yanzu what is the way out?"

"Hmm mafitar ki d'aya ce Bestie."

"Mey fah?"

"Humble yourself kawai ki tambayeshi da hankali banda rashin kunya."

"Haba bestie yanzu wannan itace shawara?"

"Idiot ai ba cewa nayi ki soma girmamasa ba amman yanzu ki gwada kigani maybe dalilin daya sa ya hanaki don kin tambayesa cike da rashin kunya ne kinde san maza da son a girmama su so ki gwada yin hakan muga ko ze baki."

"Kai Bestie anya?"

"Ki tsaya kina taurin kai karki sauk'e wannan girman kan muga inda ze kai ki wallahi kinsan aikinsu Adama k'iris suke jira suyi chaaa a kanki."

"Toh naji zanyi tunani."

"Yauwa se anjima Mama na kira na."

"Aha bye." Da haka sukayi sallama. Zama gu d'aya Nazeefah tayi tana nazari ta bisa a hankalin ne ko kuwa? Timing nasa tayi bayan sallan isha dai-dai lokacinda yake kallon sports ta fito ta leqa sa sekuwa gashi kallon yakeyi.
It's now or never ta tunasar da kanta tare da numfasa sannan ta k'arisa parlourn, pack na takeaway'n daya gama ci tasa hannu ta d'aga "Kagama ci zan iya fita dashi?" Ta tambayesa cike da kissa. Kallonta ya tsaya yi na d'an lokaci da tunani kala-kala na tafiya a kansa kode aljanu sun shige ta ne? Kai ya gyad'a mata a hankali nan ta d'aga ta kai kitchen tayi disposing a dawowanta harda d'auko masa ruwa ta tsiyaye a cup ta ajiye masa tare da durk'usawa a gefe shide Afzal banda binta da kallo da yake ya kasa yin komi.

"Afzal nace dama kayi hak'uri game da rashin kunyan dana maka ka bani kud'in ankon please." Da mamaki ya zaro lumaassun idanunsa waje sekuma yayi sauri ya kawar da kansa ba tare da yace mata komi ba.

"Afzal?" Ta kuma kiransa.
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment