Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

hak'uri kaji? I'm sorry" kai zalla ya iya gyad'a mata.

"Ka karya ko tukuna?"

"Na karya" ya amsa.

"Toh ka kwantar da hankalinka, muyi fatan Allah dawo da Abbanka lafiya."

***
Wajajen sha biyu Amal da ta ji shiru daga Afzal ta d'au waya ta kirasa lokacin har bacci ya fara d'aukansa zaune a kan kujera a parlour, ba makawa ya d'aga inda ta soma da "Halo Ya Omri?"

"Na'am Rania."

"Ina ka shige? Shiru tun d'azu."

"Rania akwai matsala" ya sanar da ita.

"Subhanallahi ina dey kana lafiya ba abinda ya same ka ko?"

"Not at all."

"Alhamdulillah" ta saki ajiyar zuciya "toh meya faru?"

"Rania sena dawo gida kawai I'm on my way."

"Toh Allah dawo da kai lafiya I love you."

"I love you too" ya amsa sannan ya katse. Duban agogo yayi yaga pass 12 "Ummi!" Ya shiga kiranta chan sega ta tashigo. "Lafiya? Naji kana kirana."

"Ummi se yaushe Abba ze shigo?"

"Zuwa anjima yace Prince bansan yaushe flight nasun ze tashi ba."

"Ummi I don't want to lose Nazeefah please do somethibg."

"In shaa Allahu ba abinda ze faru kai de ka kwantar da hankalinka kaji?"

"Zan wuce gida idan Abba ya shigo seki kirani."

"Toh shikenan Allah ya kare." Be kai ga tada engine na motar sa ba sega Nazeefah na kiransa. Nan take ya amsa "Halo Nazeefah?"

"Ya Afzal..." ta kirasa kawai seta rushe da kuka.

"Ohh dear!" Ya ambata had'e da murza temple nasa "Rabba'atul Bait please kibar kukan haka ba shida amfani."

"Ya Rouhi tayaya ne bazan yi kuka ba bayan Daddy yana shirin rabani da kai?"

"I'm not going to let that happen kinji? Abba is on his way idan ya dawo zezo ya samu Daddy yayi mishi magana in shaa Allahu ze sauk'o ya amince in dawo dake d'akinki okay?"

"But Ya Rouhi he seem so serious wallahi se rok'onshi muke tayi amma ko sauraron mu beyi I'm scared."

"Don't be sweetheart in shaa Allahu mutuwa ce kad'ai zata raba mu dan bazan ta6a aikata abinda Daddy ke cewa inyi ba because I love you okay?"

"I love you too Ya Rouhi promise me komin yaya bazaka rubuta mun takarda na ba."

"I promise darling" ya sanar da ita.

"Thank you Ya Rouhi."

"Yanzu share hawayenki kibar kukan haka toh sena shigo anjima."

"Okay take care" daga nan ya katse ya sa key ya wuce gida inda Amal ta taresa. Bayan ta kawo masa ruwa yasha take tambayar sa meke faruwa nan ya labarta mata komai inda itama tayi mamaki na sosai sannan ta shiga kwantar masa da hankali.

***
Se wajajen hud'u jirginsu Abba ya sauk'a driver yaje ya d'auko sa daga airport. Ruwa ya watsa sannan suka ci abinci da Ummi inda take basa labarin halin da ake ciki. Kansa ne ya mugun d'aure akan mey Alhj Abdallah zece a sakan masa 'ya? Shin meya faru? Nan da nan ya kira Afzal a waya yake tambayarsa kode wani abun ne ya had'asa da Daddy amma Afzal ya nuna sam ba komai banda mayar da Nazeefah gida da yayi akan laifin da ta aikata. Take a lokacin Abba yaje ya samu Daddy saidai Daddy na kan bakansa har yanzu shi a sakar mishi da 'ya ba yadda Abba beyi da shi ba, ba kalan hak'urin da be basa ba amma ya dage ina shi a sakar mishi da 'ya kawai irrespective of abotakan dake tsakaninsu. Na matuk'a ran Abba ya 6aci be ta6a tsammanin haka daga gun amininsa ba, ai ko da ma ace laifi Afzal yayi masa be kamata yayi haka ba.

"Na d'au zamuyi magana man-to-man mu fahimci juna da kai Alhj Abdallah a matsayinka na amini na ashe ba haka bane."

"Kayi hak'uri Alhaji Amin ko ni ban so abubuwa su kasance haka ba amma ya zama dole in raba auren yaran nan ne badan son ra'ayi na ba nima."

"Sai don mey toh? Idan wani abun ne ka sanar dani mana kar fa kamanta aminin ka ne ni."

"Ina sane da hakan Alhj Amin amma kayi hak'uri bazan iya sanar da kai dalili na ba ni kawai asa Afzal ya sawak'e wa 'yata."

"Kaine mahaifin Nazeefah kuma se yadda kace za'ayi amma a tunani na zaka sanar dani koma meye dalilin, in shaa Allahu zanyi maka kyakkyawar fahimta."

"Kayi hak'uri Alhj Amin komin yaya naso sanar dakai bazan iya ba shiyasa nake sake baka hak'uri kayi hak'uri."

"Shikenan tunda abinda kake so kenan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi."

"Ameen nagode da fahimta ta da kayi ina fatan hakan baze 6ata tsakanin mu ba?"

"In shaa Allahu ka gaishe da Madam." Har bakin gate Daddy ya rakasa sannan ya koma ciki Abba ya k'arisa gida. Tun daga bakin k'ofa Ummi ta soma tambayarsa yaya.

"Yace shi a sauwak'e wa 'yarsa" ya sanar da ita.

"Innalillahi! Toh Alhj ya zamuyi? Prince fa? Wallahi yana son yarinyar nan ina gudun kar hakan ya jefa sa cikin wani halin."

"Toh mahaifinta yace ga abinda yake so mun isa muce a'a ne?"

"Eh mana ai wannan bayi bane wallahi taya haka kawai ba k'wak'k'waran dalili se don an kora 'yarsa gida akan laifin data aikata ze shiga tsakanin masoya biyu yace se an rabasu, rabawan ma wanda ba komawa?"

"Toh ya zamuyi Hjy Mariam?"

"Muko muke da abinyi wallahi mu kai k'ararsa kotu na tabbata bazasu goye masa baya ba."

"Mey yayi zafi har da zuwa kotu Hjy Mariam? Shi prince d'in bashida mata a gida ne? Kokuwa Nazeefar ce k'arshen halittu?"

"Ko d'aya Alhj amma ai zaka duba halin da d'an nan ze iya fad'awa cikine. Yaran nan yana son yarinyar nan haka kawai kuma a rabasu wallahi babban hatsari ne ga rayuwansa harma da ita d'in."

"Ina sane da dukkan hakan Hky Mariam kuma idan da akwai wani hanyar da zanbi da na bi dan in dawo masa da matarsa amma gar-da-gar Alhj Abdallah yace shi a sakan masa 'ya baya son jin komai mey kikeso inyi? Zancen kai k'ara kotu kuma ma be tashi ba idan dey mata ne Allah ya haliccesu dayawa ko a gobe yakeso yakan k'ara wani auren."

"Hakane kam amma Alhj Abdallah bai kyauta ba ai ko dan abotakan dake tsakaninku ma be kamata yayi haka ba."

"Zuwa gobe zan kira Afzal yazo anan ya rubuta mata takardanta a kai musu mu rabu dasu lafiya."

"Oh! Duniya, toh shikenan Allah ya kaimu bari in k'arisa site d'ina."

"Alright."

*****
"Ya Omri ka kwantar da hankalinka haka, everything is going to be alright."
A raunane ya d'ago lumsassun idanunsa ya kafa mata.
"Rania I'm sorry" ya furta a hankali sam ba a son ransa bane ya nuna tsan-tsan damuwa akan Nazeefah a gaban Amal haka amma ba yanda ya iya ne abun ne yafi k'arfinsa.

"Why?" Ta tambayesa cike da rashin fahimta.

"For showing concern over Nazeefah like this nasan be kamata in nuna tsan-tsan damuwa akanta a gabanki haka ba but I just can't help it, kaman yadda nake sonki haka nake son ta itama. Kuma kaman yadda bazan so abu ya shiga tsakanin mu dake ba ba ita ma haka ne Rania. I can't afford to lose her, I just can't" ya fad'a cikin raunannen murya.

Baza tayi k'arya ba da fari taji haushi da kuma kishin yadda ya shiga matuk'an damuwa akan Nazeefah amma sanin yadda zafin rabuwa da masoyi yake musamman ma na dole irin wannan se taga ba laifinsa bane, ta tabbata idan da itane a position na Nazeefah zeyi haka ko fiye da hakan ma, toh kishin mey zatayi? Matsowa kusa dashi tayi sannan a hankali ta kwantar da kansa a k'irjinta tana mey shafe gashin kan nasa a hankali "Don't be sorry Ya Omri, na fahimci yanayin da kake ciki and I'm here for you, feel free to cry in my arms I love you so much." Hannayensa ya zagaye a 'yar kunkuminta yayinda hawaye ya shiga tsiyaya daga idanunsa sun dad'e a haka har seda wahalallen bacci ya d'aukesa. Cike da dabara ta kwantar dashi kan gadon ta gyara mai kwanciya sannan tayi zamanta a gefe tana mamakin dalilin da zaisa Daddy ya aikata abinda yayi.

Chan wajajen Isha sega kiran Ummi da hanzari Amal ta mik'a wa Afzal kiran inda ya d'aga. "Ummi?"

"Na'am Prince."

"Ummi ina kika jefa wayarki ina ta kira switched off?"

"Wallahi bak'i nayi d'azun suna ta game daga nan suka kashe min wayar suka yasar a lungu se yanzu na samu."

"Ohh na d'au wani abu nema ya sameki ya Abba? Ya dawo?"

"Eh ya dawo" ta amsa a sanyaye.

"Yaje ya ma Daddy magana?"

"Eh ya mishi."

"And???"

"Prince-" se kuma tayi shiru.

"Please speak up Ummi" ya fad'a cikin tsananin fargaba.

"An yi mishi magana amma he's not willing to back out Prince yace lalle-lalle se ka sakar masa da 'ya."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya saki salati "No Ummi."

"I'm truly sorry Prince amma abinda yace kenan gobe da La'asr Abbanka na buk'atan presence naka. Seda safe ka gaishe da Amal" tana kaiwa nan ta katse wayar. Ko sauk'e wayar daga kunnensa Afzal ya kasa Amal ce ta tako daga gaban dressing mirror ta amshe wayan had'e da mik'ar da shi ta rungumesa tsam a jikinta tana basa hak'uri. Kaman d'an yaro ya zage yana kuka a jikinta ba makawa. A dalilin mey Daddy zeyi masa haka? No he can't stand by it, baze iya jure rabuwa da Rabba'atul Bait tasa haka kawai ba sabida selfish interest na mahaifinta. Tunda yana sonta tana sonsa toh in shaa Allah ba abinda ya isa ya rabasu he don't care koda maganan zata kai kotu. A shirye yake da yayi filing case akan Daddy, ya tabbata kotu zata dawo masa da matarsa.

****
Washegari da safe suka shirya tsaf da Amal yayi dropping nata a school. Wajajen sha d'aya Nazeefah ta kirasa bayan sun gaisa ta buk'acesa da ya taho school a waje kaza yazo ya sameta. Be 6ata lokaci ba ya fice be tsaya ko ina ba se inda tace su had'un. Yana sauk'a daga motan ta ruga a guje taje tayi hugging nasa tana kuka har na fitan hankali. Rungumarta yayi tsam a jikinsa shima yayinda yake danne hawayen dake k'ok'arin ku6uce mar. Sun dad'e a haka sannan a hankali ya shiga raba jikinsa daga nata sede ina se sake matsesa Nazeefah ke da k'yar ya samu ya d'agota ya shiga share mata hawaye yana bata hak'uri yayinda take ta kad'a mar kai.

"It's okay calm down I'm here."

"It's not okay Ya Rouhi it's not" ta sanar dashi cikin tsananin kuka.

"Look at me" ya buk'aceta "Look at me okay?" Cikin sanyi ta d'ago jajayen idanunta ta kafa mai. "Nothing in this world will ever seperate me from you except for death okay?"

"How Ya Rouhi? Tayaya? Abba ma ya mishi magana jiya yak'i ya sauraresa se kai ne ze saurareka?"

"I know it's not possible just trust me."

"I really want to but I'm scared, tsoro nakeji Ya Rouhi."

"Kar fa ki manta nike da ikon rubuta takardan nan ko ba haka ba?" Kai ta gyad'a yayinda ya cigaba "Idan ban rubuta ba kuma Daddy be isa ya miki wani aure akan igiyan aure na ba ko ba haka ba?" Nan ma kan ta kuma gyad'awa "Excellent ni kuma ko da kasheni za'ayi sama da k'asa su had'u bazan rubuta miki takardan nan ba Nazeefah I'll never do it."

"I know Ya Rouhi amma kuma ko da hakan Daddy baze ta6a barina in koma a gareka ba ya gwammace in cigaba da zama a gida da igiyan auranka akaina daya amince ka miyar dani d'aki na."

"I'm coming to beg him again later today idan har be amince ba zan kai k'ara kotu Rabba'atul Bait akan ki a shirye nake da inyi breaking rules and even worse saboda bana son rabuwa dake, da a rabani dake gara na rasa komi nawa dana malakka I love you Nazeefah, I love you so very much." Kuka ne yaci k'arfinta ba shiri ta fad'a jikinsa tana kuka shima ba don ya danne hawayen ba da tuni ya jonata sunyi kukan tare. A hankali ya rabata daga jikinsa ya rik'o 'yar fuskanta cikin hannunsa yana mey share mata hawayen nata "Your home will forever be here with me Darling" ya sanar da ita be hankara ba yaji tayi owning lips nasa kissing him so dearly. Kasancewar wajen ba mutane shima se be 6ata lokaci ba ya shiga sumbatarta in a soft demanding way. Sun dad'e a haka sannan yayi breaking kiss d'in daga bisani yayinda suka shiga mayar da numfashi.

"Don't cry anymore okay?"

"Okay" ta amsa tana gyad'a kai fuskarta ya d'ago yadda take kalon setin idanunsa "I won't rest har se idan na dawo dake d'akinki Nazeefah you have my words."

"I trust you Ya Rouhi and I love you so dearly."

"I love you too Darling."

"Ka koma haka nan nima I have a class to attend."

"Alright se na shigo anjima da yamma okay?"

"Okay Allah kaimu."*******

_3:47pm_

Yana cikin tattare kayakinsa da shirin kulle office sega wayansa ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Amal ke kira. Be 6ata lokaci ba ya d'aga "Hello Rania?"

"How're you Ya Omri?"

"Alhamdulillah what about you?"

"Lafiya k'alau."

"And my baby?"

"Itama lafiya."

"Yau kika galabaitar mun da ita ko?"

"Toh so kake inyi ta zaman gida ina tara wa kaina carrovers?"

"A'a Mummy'n Baby yi hak'uri kunci abinci?"

"Eh na dafa indomie."

"Akwai wani abinda kike buk'ata?"

"A'a I'm just missing you yaushe zaka dawo?"

"Abba requested to see me so daga chan zan wuce gida okay?"

"Batun Nazeefah koh?"

"Yes."

"Everything will work out fine in shaa Allah."

"Thank you baby I love you."

"I love you too seka dawo."

"Sleep until then sena zo in tada ke." Da murmushi kwance fal a fuskarta ta amsa "Toh shikenan take care" nan ta katse. Be kai ga ajiye wayan nasa ba sega kiran Abba na shiga be hankara ba ya d'aga inda suka gaisa.

"Ermm nace Umminka ta sanar da kai cewa ina buk'atan ganinka ko?"

"Eh Abba I'm on my way."

"Alright Allah ya kare."

"Ameen" da haka ya katse ya gama tattare kayakin nasa ya fice. Direct gida ya wuce inda ya samu Abba da Ummi zaune a parlour suna jiransa. Ba tare da 6ata lokaci ba Abba ya sanar da Afzal gaskiyan al'amarin inda yayi mar nasiha sosai akan cewa ba komi mutum yake so yake samu a duniya ba dole wataran se an k'ara da hak'uri amma ina Afzal tamkar kurma haka ya zame a wajen maganganun Abba kawai suna shiga ta kunnensa suna fita ta d'ayan ne shi bega abinda ze rabasa da Nazeefah ba bayan mutuwa.

"Saboda haka ga takarda nan da biro ka rubuta mata takardanta kuma saki ba d'aya ba, ba biyu ba yake nema saki uku yake so."

"No Abba" ya sanar dashi ciki rud'ani "I can't do this."

"I know Afzal amma ya zame maka dole ba muke iko da Nazeefah."

"Abba baka gane bane? Bazan iya rubutawa Nazeefah takarda ba I can't."

"Prince kayi hak'uri" fad'in Ummi.

"No Ummi I can't zan je in samesa inyi masa magana in shaa Allah ze sauk'o."

"Umminka bata sanar da kai cewa da kaina naje na samesa bane? Alhj Abdallah ya riga yayi making up mind nasa ba abinda zakayi da zaisa ya sauk'o."

"I'll still try my luck Abba idan kuma be hak'ura ba then I have no choice dole in kai maganan nan kotu dan idan ba mutuwa ba banga abinda ze rabani da matata ba."

"Nima haka nace mu kai k'aranshi kotu tunda de ba zaluntar yarinyar nan kakeyi ba kotu zata tsaya maka ta dawo maka da matarka."

"A'a Hjy Mariam seda na fad'a miki ki yasar da maganan nan kink'i akan mey zamu kai maganan nan har kotu? Nazeefar itace autar mata ko mey?"

"Ba itace k'arshen halitta ba Abba amma bazan iya rabuwa da ita haka kawai saboda selfish interest na Daddy ba."

"Afzal kar ka manta Nazeefah 'yarsa ce kuma bamu keda iko da ita ba."

"No Abba, Nazeefah matata ce kuma nafi Daddy iko da ita shiyasa nake rok'onka da ka bani dama inje in samesa inyi masa magana."

"Afzal wai kam mey kakeyi haka? Akan rashin mutuncin da Alhj Abdallah yayi maka ya kuma yi wa mahaifinka ai yaci ace ka fita daga harkansa da 'yartasa gabad'aya. Ka sani suke da asara ba mu ba, idan aure kake so ka k'ara ko a yau ka kawo mace gidan nan zan aura maka ita, infact ko uku kakeso ka k'ara zanyi maka komai balle ma kai da kake da mace a gida? Mene Nazeefah za tayi maka wanda Amal baza ta iya yi ma ba? C'mon man up."

"Abba ba haka bane, baza ka ta6a ganewa ba Nazeefah and Amal are two different people dan Allah ka bani dama inje in sake basa hak'uri in shaa Allah he'll come around."

"Alhj kayi hak'uri ka barshi yaje d'in hala rabonsa ya ratse" Ummi ta fad'a.

"Shikenan kaje amma ni ba ruwana na riga na fad'a maka abinda ya kamata."

"Nagode" yace zalla had'e da mik'ewa "Ni zan koma duk abinda akwai I'll let you know." Da haka ya fice dai-dai gaban gidansu Nazeefah yayi parking ya k'arasa ciki.

"Ka kawo takardan nata ne?" Daddy ya tambayesa bayan gaisuwan da sukayi.

"Daddy ba abinda ya kawo ni ba kenan dan bazan ta6a iya rubutawa Nazeefah takarda ba haka kawai. Hak'uri nazo baka, dan Allah kayi hak'uri."

"Shin mahaifinka be sanar dakai abinda nace masa bane?"

"He did Daddy amma bazan iya ba, wallahi ina son Nazeefah kuma bana k'aunan rabuwa da ita idan wani laifin nayi kayi hak'uri-"

"Dakata Afzal!" Daddy yayi saurin katsesa "Idan ba so kake ranka ya 6aci ba ka bani takardan 'yata zaman aure ne nace bazaku k'ara ba."

"Shikenan Afzal ka mik'e ka tafi zamuyi magana" Mummy dake la6e tun d'azu jikin garu tace.

"Mummy dan Allah ki basa hak'uri wallahi bazan iya rabuwa da Nazeefah ba."

"Na gane Afzal just go zamuyi magana." Ba dan yana so ba ya mik'e ya fice. Acikin mota ya zauna ya shar6i kuka kaman ba gobe.

Daddy da yaga dagaske Afzal yake baze iya rabuwa da Nazeefah ba ya shiga nazari, yasani koda kotu ya kai k'ara da k'yar su biye masa sabida bashida wata k'wak'k'warar dalili, da ace Nazeefar ne bata son auren da rabasa bazeyi wuya ba amma yasan komin yaya Nazeefah bazata ta6a amincewa ta rabu da Afzal ba. Ya zeyi toh?

Chan bayan sallan Isha Mummy na zaune a d'akin Nazeefah tana ta faman bata hak'uri Daddy yayi knocking bisa k'ofan ya shiga.

"Ermm Hjy Surayya ki tattaro min passports naku."

"Passports? Kayi mey dasu?"

"Kede kam ki tattaro mun mana ina ruwanki?"

"So kake ka d'ibe mu kaje ka jibge mu a wani k'asan saboda selfish intrest naka?"

"Ba abinda na tambaya ba kenan ki bani passports naku."

"Bazan bada ba."

"Nazeefah ina passports naku?"

"Daddy dan Allah kayi hak'uri Daddy meyayi zafi kake shirin kaimu wani k'asan? A dalilin mey?"

"Saboda bana son abinda ze sake had'aki da Afzal."

"Daddy da igiyan auren Ya Afzal akaina kake son inyi tafiya ba tare da izininsa ba?"

"Sau nawa zan fad'a miki Afzal ba mijinki bane? Zaman ku ya haramta."

"Ya haramta kaman yaya wai? Idan wani abun ne ka fito fili mana ka sanar damu Alhj meye amfanin wannan 6oye-6oyen da kakeyi?" Mummy ta tambayesa.

"Ina jiran passports naku muddin Afzal baze sauwak'e wa 'yar nan ba toh barin k'asar nan ya zama dole."

"Daddy makaranta na fah? Khaleefah ma fa?" Nazeefah dake kuka ta tambayesa sede ko ta kanta beyi ba ya ja k'ofan ya fice. Fad'i tayi jikin Mummy tana kuka. "Wallahi wallahi kinji ko? Ba inda zamu. Iyayin Daddy'n naku ya soma isa na Allah kaimu gobe k'ara zan kai kotu akan mey dan na zuba masa ido ze tsaya yana yin son ransa a cikin gidan nan? Ki kwantar da hankalinki Allah kaimu goben.".****

Chan wajajen goma Nazeefah ta d'au waya ta kira Afzal, ringing d'aya biyu ya d'aga.

"Hello Rabba'atul Bait?"

"Ya Rouhi please help me Ya Rouhi bana son in rasaka."

"Wani abu ya sake faruwa ne?"

"Ya Rouhi Daddy na shirin relocating namu out of Nigeria gabad'aya."

"What?!"

"Wai muddin bazaka bani takarda na ba zamu bar k'asar, d'azun yazo ya tattare passports namu Ya Rouhi please help me out."

"Shhhh its okay don't cry ina Mummy?"

"Mummy tace zata kai k'aransa kotu."

"Ki kwantar da hankalinki kinji? Sena shigo gobe kibar kukan haka."

"Please come."

"I'll, you should get some rest I love you."

"I love you too" ta amsa sannan ya katse. Safa da marwah ya shiga yi a parloun yana nazari sannan chan yaje ya samu Amal a d'aki suka kwanta.

Washegari bayan sallan Azahar Afzal ya taho gidansu Nazeefah ba irin hak'urin da be bawa Daddy ba amma ina ko sauraronsa Daddy baiyi ana cikin haka Mummy dake sauraronsu tun d'azu ta sanya baki.
"Toh tunda de haka ne Afzal ni na baka dama kaje kayi filing case a kotu se muga idan kotun zata basa goyin baya ya raba wannan aure." Wani irin har6awa zuciyan Daddy yayi tabbas idan ya bari maganan nan yakai kotu toh asirinsa ze toni kenan. Ya zeyi?

"Ni kike shirin kaiwa kotu Hjy Surayya?"

"You give me no option Alhj. Idan wani abun ne kake 6oye mana tell us we're your family zamuyi maka kyakkyawn fahimta amma zancen canza mana gari be tashi ba."

Kai ya shiga girgizawa "No Hjy Surayya bazaku ta6a fahimta taba, ba don ni ba dan Allah kuyi hak'uri a raba auren nan."

"Trust me Alhj zamu fahimceka just tell us" a hankali ta shiga yi mai magana cike da kissa amma inaa Daddy ya kasa bud'e baki yayi magana se kad'a kai kawai yake.

"Toh inde haka ne mu ma bazamu amince mu bika koma ina ba kuma mayar da yarinyar nan d'akinta ba fashi."

"Afzal ka rubuta wa 'yar nan takardanta nace auren ku ya haramta!"

"A dalilin mey ya haramtan?" Itama Mummy ta mayar masa cike da tsiwa. Dai-dai lokacin Nazeefah da Khaleefah suke sauk'owa daga sama. A bakin stairs d'in suka tsaya suna sauraron iyayensu.

"Ya haramta nace kuyi wa Allah ku raba auren nan."

"Mey sukayi da zaka haramta musu aure? A dalilin mey?"

"Ya haramta Hjy Surayya ki yarda da ni."

"Na yarda da kai Alhj, just tell us ka gaya mana dalilin da yasa ya haramtan, muddin kaine da gaskiya na maka alk'awarin tayaka raba
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment