Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

k'are.

D'akin ta ya nufa inda ya tsince ta zaune bakin gado tana karatu da mamaki ta tsaya tana kallonsa ba tare da tace komai ba. Takawa cikin d'akin yayi ya k'wace handout natan kafin tace zatayi magana yaja hannunta ya mik'ar da ita ya shiga janta waje.

"Yaya what're you doing? Ka sakeni let me go" ko sauraranta beyi ba seda ya kaita tsakan d'akin nasu. Wardrobe ya nufa ya zaro takardan har anan kallonsa Amal take yayinda zuciyanta yake bugun d'ari-d'ari dan yadda ta tsure a tunaninta gabad'aya dukanta yake shirin yi. Takardan ya bud'e a idonta "rubutun waye wannan?" ya tambayeta?

"Rubutu na" ta amsa a takaice.

Sa mata yayi acikin hannu "here read it" d'agawa tayi ta shiga karantawa layi uku ta karance ta shiga kad'a kanta yayinda idanunta suka ciko dam da hawaye amma Allah ya isa tsakaninta da Safiyya da Nazeefah. Tun a asibiti ta gano Nazeefah ba sonta take har cikin zuci ba, tun anan ta gano Nazeefah ba da zuciya d'aya ta d'auketa ba. Tun anan ta gano Nazeefah is behind everything that has been happening to her barin ma yadda ta dage ta rink'a nunawa Ummi cewa lallai-lallai ita ce ta sa zuciyan Afzal ya buga. Ta sani ba wanda zeyi mata wannan d'anyen aikin se su, Maamah batayi k'arya ba da tace suna aiki tare idan ba haka ba tayaya Nazeefah zata san takai Afzal asibiti idan ba wai kirarta Safiyya tayi ta sanar da ita ba.

"Wallahi Yaya bani na rubuta ba" ta sanar da shi cike da tashin hankali.

"Ba ke kika rubuta ba?"

"Yaya wallahi bani bace wallahi bani na rubuta ba" rantsuwa ta shiga yi yayinda hawaye ya fara tsiyaya daga idonta.

"Can you even listen to yourself Amal? Aljani kike son kice ya rubuta ko mey? Ko kin k'aryata wannan ba rubutun ki bane?"

"Yaya you have to believe me wallahi bani ce na rubuta ba bazan ta6a yin abu haka ba" ta sanar da shi cikin tsan-tsan kuka ransa ne ya gama 6aci gabad'aya besan a lokacinda ya damk'ota ya shiga jijik'ata ba "Why do you have to keep on lying to my face Amal? Why!?" Ya tsawata mata kakkarwa take sosai yayinda hawaye ya shanye mata murya "I love you Amal, I love you morethan anything in this world amma da abinda zaki sak'a mun kenan? Duk kalan halaccin da nayi miki a rayuwa you think I deserve this from you? Har ni zakice jikinki kawai nakeso ba zuciyarki ba? Ni Amal? In ba da mukayi aure ba ko hannunki na ta6a sha'awan rik'ewa ne?"

"Ya- Yaya please believe me" ta ce dashi muryanta na d'aukewa "Wallahi bani na rubut-"

"Damn it Amal!" Ya katse ta. "You're such a horrible liar, idan ba ke ba toh waye? Waye yake da irin sigar rubutunki bayan kanki? Answer me!" Ya sake daka mata wani tsawan da gabad'aya yasa jikinta rawa fiye da na da. Ita tsoronta ma kar gabanta ya cigaba da fad'i abu ya samu d'an cikin nata ne tunda de bawai cikin babba bane abu kad'an yana iya zubar dashi.

"Wallahi bani bace-"

"When will you stop lying to my face? When Amal?" tureta yayi kad'an ya rage bata sha k'asa ba "Stop lying to me already just admit it, confess all your crimes a shirye nake in yafe miki mu fara sabon rayuwa all over again Amal just admit it."

Cikin tsananin kuka tace, "I have nothing to admit Yaya saboda bani bace wallahi ba ni na rubuta wannan abu ba."

"You're still not telling me the truth."

"You have to believe me wallahi ba k'arya nake yi maka ba-"

"You're lying! Just admit it, admit it already."

"Yaya I have nothing to admit ya, taya kake tsammanin zan amince da laifin da bani na aikata ba? Wallahi bani bace wallahi bani na zauna na rubuta wannan abu ba, kana tsammanin har zan rubuta mumunan abu haka kuma se in ajiye a inda nasan idonka ze kai?"

"Fvck it!" Yayi growling yayinda yake wani irin nishi kaman zaki. "Amma rubutun waye ne?"

"Yay-"

"Just fvcking answer me!" Ya katseta cike da rashin hak'uri.

"Rubutu na ne amm-"

"Shhh!" Ya katse ta "Abinda nakeso inji kenan" hannu ya mik'a ya amshe paper'n "You've really hurt me Amal, you've hurt me so badly, kin karya zuciyan da take mutuwar sonki kin yasar, bazan ta6a mancewa da wannan abu da kikayi mun ba I might forgive you someday amma bazan ta6a mancewa dashi ba."

Cikin sautin kuka ta kira sunansa "Yaya-"

"Just get out" ya sanar da ita a hankali.

"Yaya dan Allah ka saur-"

"I said get out!" Ya daka mata tsawa a raunane ta tsaya tana kallonsa sannan ta shiga takawa a sanyaye ta bar mai d'akin. Tana isa d'akinta ta baje akan gado ta shiga raira kuka. Kuka take wane zata cire ranta har seda ta fara jin k'warnafi. Bayi ta fad'a ta shiga kwararo amai kaman ba gobe seda ta harar da duk wani abunda yake cikinta sannan ta lalla6a ta fito. Yanzu ta tabbata da abinda Maamah ta jima tana fad'a mata. For all these while Safiyya amanarta ta rink'a ci ita ta ringa zuba mata gishiri da borkono a girki, ita ta rink'a kwasan abinda Afzal ya keyi mata tana kaiwa Nazeefah, ita ce ta fad'a masa tana kawo maza gida, ita ta kira Nazeefah ta sanar da ita suna asibiti bayan da ta ajiye masa wannan takarda ya karanta. Wow!

Meyasa ta kasa gane gaskiya tun farko? Meyasa bata gane Safiyya ce behind everything ba? Tabbas ta tafka sokanci gaskia ne da Maamah tace mata yadda ka d'auki nutum da zuciya d'aya yanzu shi ba haka ya d'aukeka ba. Ko da wasa bata ta6a kawowa a ranta cewan Safiyya zatayi mata abinda tayi ba. Bature beyi k'arya ba da yace "Trust No One" tabbas da tun farko bata ajiyeta kusa da zuciyarta ba da tun kafin abu ya ta6ar6are haka zata gano gaskiya. Tsakaninta da Nazeefah kuma sede tace Allah, Allah kad'ai ze sak'a mata yabi mata hak'k'inta. Chan ta mik'e taje ta samu Safiyya a d'akinta.

"Sannu Aunty ya jikin naki?"

"Safiyya a iya zama na dake ban ta6a cutar dake ba, ban ta6a tokararki ba, ban ta6a tauye miki hak'k'in kiba a matsayin k'anwa ta ta jini na d'aukeki da zuciya d'aya shiyasa har yanzu na kasa gane dalilin da zaisa kiyi mun abinda kikayi mun." Cike da d'aurewan k'wak'walwa Safiyya ta tsaya kallon Amal yayinda cikinta ya d'au ruwa lokaci guda bade Amal ta ganota ba? Yau kashinta ya bushe ta shiga uku ta lalace.

"Mey na miki da kika za6i ki k'untata mun acikin gida na ki hana ni sakat? Mey na miki da kika za6i ki shiga tsakani na da mijina kisa har ya fara zargina akan ina ci masa amana? Mey na ta6a yi miki Safiyya? Amma ba komai ki kira uwar d'akinki ki sanar da ita cewan ta kwantar da hankalinta saboda burinta na rabani da Ya Afzal ya cika koda Yaya be sakeni ba ni zan tattara kayakina in bar gidan nan tunda kun riga kun juyar mishi da kai kunsa yana mun kallon munafuka, mak'aryaciya, annanimiya wace bata da aiki sena gulma. Ba gidan kukeso ba? Zan tattara kayakina in bar muku ita" bata jira jin mey Safiyya zata ce ba ta juya ta fice. Bayi Safiyya ta shiga a guje ta juye fitsarin da ya matseta a lokaci d'aya sannan ta fito ta d'au wayarta dan kiran Nazeefah se kakkarwa take yayinda jikinta yayi la'asar da irin kalamun da Amal ta fad'a mata sede sam layin Nazeefah yak'i shiga.

****
Babban akwatinta ta janyo daga d'akin da ta tarasu aciki ta nufi d'akinsu da Afzal sallama tayi sannan ta shiga ko kallan Afzal dake mik'e akan gado batayi ba ta zarce direct wajen wardrobe, da mamaki ya mik'e zaune yana kallonta sede bece da ita ko uffan ba. Kayakinta yaga ta shiga tattarewa na matuk'a ta basa mamaki shin mey take shirin yi? Tafiya? Tafiya zatayi ba tare da ya bata takarda ba? Ido ya cigaba da zuba mata yana ganin iya gudun ruwanta. Kayakinta ta cigaba da tattarewa tana had'awa tana gamawa da fannin kayakin ta zarce gaban mirror ta d'ibi mayukan shafawanta da turare da makamancin haka sannan taja akwatin ta fice har anan Afzal beyi mata magana ba. Handouts nata da littafafai da sauran muhimman abubuwan da zata buk'ata ta tarasu cikin wani akwati daban shima.

Na sosai Afzal ya kasa kunne yana jiran jin k'aran engine na mota inda ze tabbatar da tafiya Amal zatayi kokuwa kawai ta tare kayakinta ne ta k'aura izuwa d'akin da ta koma gabad'aya. Washegari da sassafe ko karyawa Amal batayi ba taja akwatinta ta fice. Ko da driver yace ze kaita inda zata hanasa tayi napep ta tsara a waje bayan d'an takawan da tayi ta wuce gida. Har bakin k'ofa ya sauk'eta sannan ta sauk'e kayakinta ta sallamesa ta k'arisa ciki.

Papi ta tarar a tsakar gida yana zaune yayinda suke hira da Mami dake kitchen tana shirya musu abun karin kumallo. "Baby!" Ya kirata da mamaki yana bin jakukkunan hannunta da kallo "Ya haka? Meya faru?" Ya jero mata tambayoyi. Ba shiri Mami dake kitchen ta sauk'e tukunyarta ta fito tana kallon abin al'ajabi. Ba k'aramin tsinkewa zuciyanta yayi ba ganin Amal da akwati haka, Allah de yasa ba abinda take zargi bane. Da sauri sukayi kanta suna tambayarta meya faru. Sede wane 'yi kuka' suka ce mata dan yadda ta rushe da wani irin masifaffen kuka, a rikice Mami ta jata jiki ta shiga hugging nata tana bubbuga bayanta yayinda Papi yaja akwatunan nata suka k'arisa ciki. Dan kukan da takeyi Papi ya rok'i Mami da tabar ta da tambayoyin haka ta bari se idan ta huta tukuna. Dan haka suka fita daga d'akin suka barta, kukan ta cigaba dayi har izuwa lokacin da wani wahalallen bacci ya d'auketa.

****
Wajajen tara da rabi Afzal ya tashi daga bacci bayan yayi wanka ya sanya shirt da shorts ya fito inda ya tarar da Safiyya na goge-goge. Cikinsu duka ba wanda yasan da tafiyan Amal banda mey gadi da driver. A cewan Safiyya har Amal ta irga wa Afzal halin da ake ciki ne don haka tayi surrender ta tsaya chak gu d'aya tana jiran sauk'an mari a fuska kawai setaji ya tambayeta "Ba gaisuwa ne?"

"Yi hak'uri ina kwana Uncle wallahi hankalina ya tafi wani gun ne" Ta gaishesa "Lafiya" ya amsa "Kiyi mun frying chips da two eggs."

"Toh barin kammala aikin nan" instead ya wuce d'akinsa se yayi tunanin lek'a na Amal inda ya tarar da d'akin empty, shiga yayi ya zauna yana jiran fitowarta dan a tunaninsa gabad'aya ta shiga bayi yin wanka ne sam be kawo a ransa wai har Amal ta tafi ba. A cewansa tunda bata tafi jiya ba that means ba yaji zatayi ba kawai ta tattare kayakinta ne ta dawo dasu nan gabad'aya. Sede da ya duba gaban dressing mirror ya tarar dashi empty ko vaseline babu. Tirk'ashi! Ba shiri ya mik'e yayi knocking bisa k'ofan bayin, jin shiru seya bud'e ya lek'a ciki inda ya tarar da bayin empty a guje ya fito yana tambayar Safiyya ko ina Amal taje sede kaman yadda baida masaniya itama hakan ne. Waje ya fita yana tambayan mey gadi ko yaga fitan Amal.

"Tabbas naga fitanta Ranka shi dad'e nima na bud'e mata k'ofar."

"Ina taje? Ita kad'anta ta fita ko kuwa da akwati?"

"Akwati har biyu."

"Damn it! Meyasa baka hanata fitan ba kokuwa ka kirani ka gaya mun? Shin baka san aikinka bane? Mstww!" ciki ya dawo ya d'aga wayansa har ya danna kan contact na Amal don kiranta se kuma ya fasa yayi sauri ya katse wato shi be yi zuciya ya ce ya saketa ba be kuma ce ta tafi gida ba itace take da zuciyan yin hakan? Ita gata tana da gun zuwa wato, da kyau ta kyauta taje duk inda zata je.

*****
Wajajen goma da rabi Amal ta tashi inda ta fara duban wayanta saidai da mamaki taga ko message Afzal be tura mata ba bale ya kirata, lallai yau ta gane waye Afzal. Wannan walak'anci da mey yayi kama? Ace yana kallonta tana shirya kayakinta amma ko yayi mata magana bale yayi tunanin hanata. Yanzu kuma da ya tashi yaga bata gidan meya kamata yayi? Lallai yau tasan inda ya ajiyeta, yau tasan matsayinta a zuciyansa, yau ta tabbata Yaya baya sonta.

Masa me kyau Papi ya aika aka siyo mata ta karya da shi tasha magunanta alai sannan Mami ta shigo suka gaisa.
"Bakida lafiya ne?" Mami ta tambayeta tana bin magunan dake gabanta da kallo.

"Eh Mami ban ji dad'i sosai ba kwana biyu."

"Allah sarki, Allah sawwak'e."

"Ameen."

"Ya baki ci masan ba sosai duka fa naki ne mu tun d'azun muka karya."

"A'a Mami na k'oshi na d'an ci ai anjima ma ina da test."

"Kai haba?"

"Wallahi around 1 haka."

"Toh Allah ya bada sa'a Papinki na buk'atan ganinki." Hijabinta ta sanya ta mik'e a sanyaye tabi bayan Mami bayan sun k'arisa d'akin nasa suka nemi waje suka zauna daga angles na d'akin. Gaisuwa suka fara yi bayan nan Papi yake tambayarta meke faruwa.

"Papi komai ma ya faru, ba abinda be faru ba ni kawai kar ku sake turani gidan Yaya dan Allah" seta rushe da kuka.

"Subhanallahi ya isa haka kinji? Ba wanda yace ze sake mai daki gidansa fad'a mun meya faru."

"Nazeefah ba kishiyar arziki bace after all, yadda na d'auketa da zuciya d'aya ba hakan ta d'aukeni ba, ashe duk shiri ne bawai har cikin zuciyarta bane tana so na, son munafurci take yi mun...." nan ta kwashe labarin duk yadda akayi tun daga kan lokacin da Safiyya ta fara zuba mata gishiri da borkono a girki zuwa kan lokacin da Afzal ya fara shasshareta zuwa kan lokacinda tayi masa magana yace tana kire-kiren waya tana baza sirrin gidanta a waje, zuwa kan lokacin da Safiyya tace ta fara kawo maza gida har izuwa na takardan da suka sa wa Afzal cikin kaya bata 6oye masu komai ba illa labarin cikin da take d'auke da shi.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai Papi yake ta nanatawa da mamaki bayyane karara a fuskansa itakam Mami se tafe hannu kawai takeyi dan mamaki ko salatin ma ta kasa ambata.

"Kikace a idon shi kika tattare kayakin ki beyi miki magana ba?" Mami ta tambaya.

"Wallahi a idonshi Mami" ta amsa tana share hawayenta.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ta sa salati.

"Har yanzu kuma be kira ki ba?" Papi ya tambaya.

"Be kirani ba."

"Kuma nima be kirani ba ko ya kiraki Jameela?"

"Sam" ta amsa tana kad'a kai.

"Tabbas Afzal zeyi nadama, ashe har za a fad'a mishi magana akanki ya hau ya zauna akai ba tare da ya tsananta bincike ba? Ashe har zega ayan tambaya akan tarbiyyan dana baki a gidan nan Baby? Har ke yake tsammanin zaki ci masa amana sabida 'yar aikinki ta ce hakan? Baze tsaya ya tambayeki yayi bincike ba?"

"Wallahi Afzal butulu ne" cewan Mami "Ko a mafarki aka ce mun zeyi haka wa Baby bazan yarda ba, wannan sigan walak'anci da mey yayi kama? Ai ko a bishiya ya 6alloki be kamata yayi miki haka ba ni fa ba abinda ya fi ci mun rai kaman da ya koraki daga d'akinsa. Wannan wani irin gori ne?" Ta tambaya cike da tsiwa.

"Ya isa haka Jameela ki kwantar da hankalinki uwata ta shi kije ki huta ai ba makaranta yau ko?"

"Akwai ina da test."

"Kinyi karatu?"

"Eh jiya nayi yanzu ma zan d'an ta6a kafin lokaci yayi."

"Toh uwata Allah bada sa'a kinji? Ina son ki kwantar da hankalinki ki cire Afzal daga zuciyarki. Nasani abinda yayi miki da zafi amma hak'uri ya zama dole mamana, dan shi baza ki bari ki cutar da kanki ba, in shaa Allahu shi yake tattare da asara ba ke ba gashi ai da kika cigaba da hak'uri kina kai kukanki wa Allah, Allah ya bayyano miki da komai kuma batun cewa za mu miyar dake gidansa k'arya ne, baki komawa har se idan ke kika ce hakan bazan mayar masa dake ba koda yazo yin bikon ki Baby zan nuna masa cewa ba wanda ya kai ya walak'anta mun ke muddin ina raye so ki kwantar da hankalinki kinji? Ki cigaba da karatu Allah yayi miki albarka."

"Ameen Papi nagode."

"Tashi Mamana" da haka ta mik'e ta fice zuwa d'akinta ta cigaba da karatu. "Amma Afzal be kyauta ba wallahi" cewan Mami bayan ficewan Amal.

"Dama na sani wataran se ya gorantawa Baby shiyasa ban goyi bayan ka sanar dashi asalinta ba tun farko."

"A gaskiya nima Afzal ya bani kunya yadda ba bincike ba komai ya yanke hukunci."

"Ai walak'anci ne ba komai ba wallahi kuma kasan meya fi 6atan rai? Yadda tana tattare kayakinta a gabansa amma ko k'ala be ce ba irin bata da gata bata da gun zuwa d'innan kokuwa duk inda taje zata sake dawowa da k'afarta."

"Ya isa Jameela ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu ba shi ba Baby."

"Ahtoh dan wannan rashin mutunci ne a fili saboda bata da uba yake ganin ze iya walak'anta ta toh wallahi yayi k'arya Baby nada gatanta."

"Ki sauk'ar da muryanki kar Baby ta jiki dan Allah magana ya riga ya k'are muddin ba Baby ce tace zata koma gidan sa ba toh ba shi ba ita cin fuskan ya isa haka."


***Sha biyu nayi ta shiga shiri sallama tayi wa Mami sannan ta fice, tana gama test nata sukayi sallama da Maamah. Dama yawancin ana samun napep na jiddari (unguwansu) acikin makaranta se yau kuma Allah yayi babu dan haka ta taka har wajen gate ta shiga nema. Tazo tsallake titi kawai kaman daga sama wani mota mey d'ankaren gudu ya d'auketa ya wuce ko kewayowa beyi ba. Nan mutane suka duk'ufa sukayi kan Amal da tuni ta sume a wajen yayinda kanta yake bulbulan jini. Mota aka shiga nema wanda zeyi gaggawan kaita asibiti ana cikin haka sega wani babban motan daya fito daga cikin makarantar ya faka a dai-dai inda abun ya faru. Daga ciki babban mutum da ake ja yace da driver'n sa "Iliya sauk'a kaje ka taimaka musu mu kai yarinyar asibiti." Nan da nan aka d'auki sumemmiyar jikin Amal aka sata cikin motan inda suka wuce TH.

****
K'ofan ta rufe ta fad'a bayi a guje sannan ta d'aga wayan. "Hello Aunty?"

"Safiyya mission complete yau burina ya cika, na fidda Amal daga gidan Ya Afzal maganan da nake miki yanzu har mutanen nawa sun bigeta in shaa Allah se cikin ya zube."

"Aunty meyasa kika sa aka bigeta? Kin fidda ta daga gidan nan bey isheki ba har sai kinsa an bugeta? Seda na ce miki ya isa haka amma kika k'i ji wallahi abunda mukayi wa Aunty yayi yawa ni nayi nadaman fara aikin nan da ke."

"Mey kike cewa Safiyya? Bayan burin mu ya cika kike wannan banzan maganar? Kin manta da mak'udan kud'ad'en da na miki alk'awari ne?"

"Ban fad'a miki bane amma Aunty ta riga ta gane mu, ta gane muna aiki tare, kap abinda muka aikata ta irga mun jiya kafin tabar gidan nan."

"Sai mey? Ba ta riga ta bar gidan ba?"

"Aunty duk da haka da bakisa an bigeta ba wallahi Aunty bata cancanci abubuwan da mukayi mata ba."

"Kiji ni Safiyya wallahi idan kika kuskura kika 6ata mun aiki na sena tabbata na lahira ya fiki jin dad'i hello Safiyya? Safiyya? Hello?" Tuni Safiyya ta katse wayan. Tun tafiyan Amal yau ta kasa samun sukuni, sosai kalamun Amal suka ta6a ta suka sa duk ta tsani kanta. Bud'e k'ofan da tace bari tayi taga Afzal tsaye bakin k'ofan bayin yana wani irin nishi wane zaki ga yadda idanunsa suka kad'a sukayi ja zir, wai shin har yaushe ya shigo bata ji sa ba? Innalillahi ashe batayi locking k'ofar ba duk dan sauri ta d'auki call d'in Nazeefah kafin ya tsinke. Kafin ta hankara kawai taji ya fincikota da hannunta seda ya fiddo ta daga bayin.
Tsulewa tayi ta shiga yin kakkarwa yayinda idanunta suka ciko dam da hawaye.

"Da wa kike waya?" Ya tambayeta cikin wani irin salon da ya mugun sanyata jin fitsari. Kai zalla take iya kad'awa "Nace da wa kike waya?!" Ya daka mata wani irin tsawan da tuni ya sa ta shiga sake fitsarin da take ji tsabaragen tsoro.
"Uncle dan Allah kay-"

"Shut up you fool! nace da wa kike waya?" hannu ya mik'a ya fisge wayan nata tare da shiga call logs last numban da tayi waya da shi yayi dialing bada dad'ewa ba Nazeefah ta d'aga "Hello Safiyya? Hello Safiyya?" Wani irin rawa jikin Afzal ya fara lokacin da yaji sautin muryan Nazeefah acikin wayan. Kashe wayan yayi daga sama kawai Safiyya taji sauk'an mari a fuskanta tass! wani irin rikicaccen ihu tasa yayinda ta soma ganin stars suna bin kanta. Be bari tayi overcoming zafin marin ba ya k'ara mata d'aya kumatunta duka ta rik'e tana kuka.

"Abinda ta turoki gidan nan kiyi kenan ko? Ki shiga tsakani na da Amal is that it?"

"Uncle dan Alla-"

"Shut it!" Ya daka mata tsawa "wa kuka tura a kad'e?" Kai zalla take kad'a masa yayinda ta gama tsurewa "Nace wa kuka tura a kad'e?" Nan ma shiru "You fool I'm talking you" fincikota yayi had'e da kai mata wani marin again a rikice tace, "Aunty wallahi Aunty a ka kad'e ni bani bace."

"What?" Yayi exclaiming cike da k'in yarda. "Kun sa a bige Amal? Bakuda hankali ne?" Turata yayi har jikin bango sannan ya shak'ure mata wuya take idanun Safiyya suka kad'a yayinda ta shiga yin tari kad'an ya rage Afzal be kasheta ba sannan ya saketa nan ta sauk'a k'asa tana wani irin tari.

"A ina kuka sa aka bigeta?" Shiru tayi se kuka kawai take wani ball yayi da ita da k'afa "Nace a ina kuka sa aka bigeta?" Cikin tsananin kuka tace "Wallahi ban sani ba tunda Aunty tace zata sa a bigeta nace kar tayi amma tak'i jina" wani ball d'in ya sakeyi da ita "K'arya kikeyi nace k'arya kikeyi a ina kuka sa aka bigeta?"

"Uncle wallahi ba k'arya nakeyi ba tace de daga makaranta za a bi Aunty amma wallahi ban san a dai-dai ina bane dan Allah ka yarda dani."

"Wallahi tallahi kin de ji rantsuwa ba kaffara ko? Muddin wani abun ya samu Amal ki sani da hannu na zan kasheki" yana kaiwa nan ya fice daga d'akin makulli yasa ta waje sannan ya k'arisa d'akinsa ya d'au key'n motansa ya fice be tsaya ko ina ba se gidan Nazeefah. Tana zaune akan dining tana cin abinci kawai taga shigowan Afzal kaman diran yesu.

"Ya Rouhi?" Ta kira sunansa had'e da mik'ewa dan yi mai sannu da zuwa. Peck ta mishi placing a gefen kumatu "Ya Rouhi mey ka shigo yi? Ba se gobe zaka shigo ba?" Ko amsata ya kasa yi yayinda zuciyarsa ke raya masa kawai ya had'a kanta da jikin bango ya shak'ure mata wuya se idan ta daina numfashi tukun ya saketa danne zuciyan nasa yayi sannan daga gefe yayi dialing lambarta ta wayan Safiyya.

DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment