Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

tana shafa gashin kansa a hankali "Kaman yadda ban iya wankan baby ba kaima na tabbata baka iya ba idan ba Mami wa ze nayi wa Nihal?"

"Toh ba se ki koya ba, in fact ni zan ma koya."

"Wa d'in wallahi baza ka iya ba."

"Toh ke ki koya mana Baby?"

"Ni wallahi tsoro nake gani nake kaman zan karyata idan na rik'eta ba kaya a jiki."

"God help me is just that I miss you Rania."

"Me too Ya Omri" ta amsa had'e da kwantar da kanta a gefen na Nihal a k'irjinsa.

"She's so beautiful" ta furta tana wasa da 'yar hannunta.

"Just like you" ya amsa had'e da zagaye hannunsa a bayanta. "Kinsan wani abu?"

"Tell me."

"Kinsan kin mun wayo ko?"

"Da nayi meh?"

"Da Nihal take kama dake ke kad'ai mana, ina laifin ko ido nane ta d'an d'auka."

"Toh yi na ne Ya Omri? If it was my way ai sede tayi kama da kai tunda de kafi ni kyau."

"Inji waye na fiki? Besides I was only joking, darling you're the most beautiful being I've ever known amma de ina son second child d'ina yayi kama dani kisan yadda zakiyi."

"Wa ya fad'a maka ma zan sake haihuwa? Daga Nihal se Nihal."

"Chab lalle ma! A dalilin mey?"

"Da nace ka shigo labour room ina k'i kayi?" Tayi maganan tana k'ok'arin mik'ewa.

"Sweetheart ba haka bane" yayi saurin fad'a yana k'ok'arin dakatar da ita.

"Toh yaya ne? Ni ban ta6a jin inda mata ta kira miji labor room yak'i shiga ba."

"Shine kikayi zuciya?"

"Toh bazan yi ba?"

"Baby ba haka bane I was so scared bana son jin kukanki."

"But I needed you in there sweetheart."

"I'm sorry okay? Next time in shaa Allah tare dani zaki shiga."

"Ba wani next time d'innan daga kan Nihal na gama haihuwa na se inde zaka auro wata."

"Ba watan da zan auro ked'in de zaki haifo mun masu kama dani har goma."

"Sannu toh kad'au haihuwan wasa ne?" Cike da dabara ya sake miyar da ita jikinsa "Yi hak'uri baby na yi hak'uri kinji?"

"Naji toh."

"Then kiss me."

"Dalili?"

"Dama nasan ni kad'ai ke kewarki?"

"Kaga bani Nihal in tafi nasan Mummy har ta gaji da jirana."
Mik'ewa yayi ya zauna "you must kiss me first."

"Or else?"

"Or else bazan bada Nihal ba."

"lol ba se inje in fad'a musu ka hana ni ba."

"Toh kije d'in" ganin ta mik'e dagaske yayi sauri ya cafke hannunta wanda hakan ya sata fad'i kan gadon. Nihal ya ajiye a gefe yayi sauri ya haye kanta yana mata dariyan mugunta.

"Yaya mey haka? Ka d'agani wallahi banida lafiya." Wani killer'n murmushin dake tafiyar mata da imani ya saki "Let your dream boy kiss and take your sickness away baby."

"Nikam ka d'agani Nihal dan Allah ki fara kuka."

"Ai ita 'yar arziki ce ba kaman ki ba."

"Au nice 'yar tsiya?"

"Ni ban ce haka ba" ya amsa yana dariya.

"Wallahi Yaya nasan maganin ka, nikam d'agani" bata hankara ba kawai taji sauk'an lips nasa akan nata. Kissing nata ya shiga yi a hankali yana mey tafiyar mata da imani. A sannu a sannu yake kashe mata duk wani sassa a jikinta, Amal bata san lokacinda ta shiga mayar masa da martani ba a garin haka har d'aurinta ya kunce. Knock da suka jiyo daga bakin k'ofan ne ya dawo dasu daga duniyan da suka fad'a a rikice Amal ta ture Afzal daga kanta ta mik'e zaune tana k'ok'arin mayar da d'an kwalinta. "Baby??" Suka jiyo muryan Mami.

"Ermm na'am Mami" ta amsa cike da tashin hankali.

"Kar6o Nihal d'inne har yanzu?"

"Ermm ermm na bata nono ne."

"Ohh toh kiyi sauri Mummy na jiranki."

"Toh Mami gani nan zuwa." Juyowa tayi ta danna wa Afzal dake ta faman kallonta harara yana wani lasan le6ensa, daga bisani kawai ta kai masa pillow fuska. "God help me! Ni kuma mey nayi?" Ya tambaya yana mata dariyan mugunta.

"Ma tambaya na kake ko? Fisabilillahi wani irin abun kunya ne wannan Yaya?"

"Da nayi mey? Talking as if you didn't enjoy it too."

"Aww ma haka zaka ce? Zaka gani" kafin tace zata mik'e yayi sauri ya rik'eta "Shikenan ke Rania abu kad'an zuciya."

"Ni sakeni in d'au 'yata mu tafi."

"'Yarki ko 'yar mu? Now that aside yi hak'uri Yaya is sorry."

"Naji sakeni."

"Kiyi hak'uri mana toh I said I'm sorry."

"Nace naji."

"Toh smile" murmushi cike da tsangwama ta sakar masa yayinda ya saketa ta d'au Nihal dake kwance a gefe, har bakin k'ofan yayi mata rakiya had'e placing gentle kiss a kan goshinta "See you around, I love you."

"I love you too" ta sanar dashi sannan ta k'arasa wajen su Mummy. Bada dad'ewa ba Maamah, da sauran k'awayenta suka zo yi mata barka. Da Azahar Ummi da Abba suka kawo abinci inda Abba ya sawa Nihal albarka, sun kusan tafiya Papi da Daddy suka shigo suma. Wajajen 2:30 Nazeefah tayi wa Mummy waya kan sun iso dai-dai wannan lokaci Daddy suke shirin komawa da Papi dan haka suka ke6e inda take sanar da shi shigowan Nazeefah. Mamaki na sosai Daddy ya sha take suka wuce airpot suka d'aukota. Kuka sosai Nazeefah ta tsaya yi da suka had'u se faman neman tubansu take har suka isa gida. Bayan ta watsa ruwa ta sauk'o ta sami Mummy inda tayi serving nata abinci.

Abincin take ci amma gabad'aya babu hankalinta a tattare da ita.

"Nazeefah lafiya?" Mummy da ta karance ta na d'an lokaci ta tambaya.

"Ermm babu" ta k'irk'iro murmushin dole, miyan yayi dad'i I've missed your cookings."

"Thank you, fad'i tunanin mey kike?"

"Babu fa kawai naga gidan ne ya canza site na waye wancan? Amaryar Daddy?"

"Eh na 'yar uwata ce mahaifiyar Amal kuma amaryar Daddy'nku."

"Oh" ta amsa sama-sama sounding not surprised. "Meyasa Daddy ya had'aku? Kuma harda mahaifinta suka dawo?"

"Eh we're one big happy family down here, kuma ni na kawo shawaran a had'a mu."

"Happy?" Ta nanata cike da rainin hankali.

"Nazeefah baki tambayi ya Amal 'yar uwarki take ba?"

"Mey had'i na da ita? Please not this time Mummy."

"Haba Nazeefah na d'au kin dawo saboda kin gano kuranki ne kina son ki gyara tafiyarki ko ba haka ba?"

"Wani kuskure Mummy? Mey na aikata? I'm not back because of that so called Amal I'm back because I've missed you and unless kina so acikin sati in koma in da na taho zaki daina mun maganan Amal bana son jin maganan da ya shafeta."

"Uh well tunda kince haka dama ina son sanar dake cewan ta haihu ne jiya ta samu 'yarta kuma tayi miki takwara." Chak ta tsaya da hannunta da take k'ok'arin kai loman tuwo. "What???" Ta tambaya out of disbelief.

"You heard me right Amal ta haihu ta yi miki takwara."

"Ni tayi wa takwara?" Ta kuma tambaya had'e da sakar da wani dariyan rainin hankali "You're always good at telling jokes Mummy but not this time around."

"Yaushe na zama playmate naki da zan na cracking jokes da ke Nazeefah? Amal ta haihu kuma tayi miki takwaraamma ita da Afzal sunyi deciing zasu na kiran 'yar da Nihal."

"Mummy kinsan mey kike fad'i kuwa?"

"Tabbas na sani kinga" tayi maganan had'e da d'ago wayanta kan pictures na Nihal ta kai had'e da mik'a mata "here swipe left ga yarinyar nan." Hannu na k'yarma Nazeefah ta amshi wayan ta shiga kalla da fari ma taso k'aryata komai sekuma taga irin tsan-tsan kaman da baby'n keyi da Amal nan ta sake tabbata da cewa eh 'yarta ce amma kuma se tayi mata takwara? Me ta ta6a yi mata mey kyau a duniya da har zesa tayi mata takwara? Shin Amal bata sane da irin k'iyayyar da tayi mata ne? Shin bata san cewa bayan shaid'an da fir'auna se ita tafi tsana fiye da kowa a duniya ba? Wow! Bata hankara ba kawai taji hawaye na tsiyaya daga d'ayan idonta wanda tayi saurin sa hannu ta goge had'e da mik'a wa Mummy wayanta sannan ta mik'e.

"Ya haka lafiya?" Munmy tayi saurin tambaya. Wanke hannunta tayi cikin bowl ta goge da towel ta shiga tafiya ko amsa Mummy batayi ba, tana kaiwa d'akinta ta fad'a ciki ta nufi kan gado inda ta kwanta. Kuka ta shiga yi kaman ba gobe tana mey tsanar kanta na d'aukan tsana da k'iyayyan duniya da tayi ta aza akan 'yar uwarta wanda suka kasance jini d'aya da ita. Ji tayi kaman ta kashe kanta dan irin munanan ababen cutarwan da ta ringa yi wa Amal baiwar Allah. Shin masu halayya irin na Amal guda nawa suke a duniya irin tamu ta yanzu? Ace duk irin sharratayyan da bita dashi amma ita ta sak'a mata da alkhairi haka har ta d'auki sunanta ta sanya wa 'yarta ta fari bayan ga mahaifiyarta dana mijinta a raye? Subhanallah ita kanta baza ta iya yafewa kanta abubuwan da tayi wa Amal ba bale ta soma neman yafiyanta. Gaskiya ne ta cuci kanta a rayuwa, da tun farko ta gane cewa idan abu rabon mutum ne ko ta yaya zai samu idan kuwa akasin hakan ne toh ko ta yaya ya buga baze ta6a samun abun ba koda ya samu ma abun baze yi lasting mishi ba. Da tun farko ta rungumi k'addaran cewa ita da Afzal are not meant to be da batayi hurting one and only sistee nata ba.

Tana cikin tsakiyan kuka Mummy ta bud'e k'ofan ta shiga da hanzari ta shiga share hawayenta.

"Nazeefah?" Mummy ta kirata had'e da dafe kafad'arta.
"Kukan mey kike haka? Tashi ki zauna muyi magana." Ba gardama ta mik'e zaune cikin tsananin kuka tace, "Mummy I've hurt Amal so much, ta ina zan fara bata hak'uri? She really did not deserve everything I put her go through Mummy nayi nadaman abubuwan da nayi mata."

"Inde Amal ce na tabbata ta jima da yafe miki komai Nazeefah tunda de har ta d'au sunanki ta sanya wa 'yarta bayan ga mahaifiyarta a raye, inspite of everything Amal still loves you Nazeefah."

"Abinda yafi ci mun rai kenan Mummy, meyasa zatayi mun takwara? Meyasa baza ta tsane ni ba kaman yadda na nuna na tsane ta? Meyasa bazata sak'a mun sharrin da nayi mata da sharri ba? Why is she making me feel like a bad guy?"

"She only did what's right to reunite you guys."

"Mummy I feel like a total crap ji nake kaman in kashe kaina Amal ta fini ta duk inda nake tunani" ta fad'a tana kuka sosai.

"Kar kice haka Nazeefah, life is a competition but we're not competitions amongst ourselves, yadda kike ganin Amal ta fiki da wani abun itama haka take ganin kin fita ta wani fannin, you guys are sisters Nazeefah you learn from each other okay?" Fad'awa jikin Mummy tayi tana mey cigaba da kuka yayinda Mummy ke lalashinta.

**** Washegari...
"Har kin shirya ne?" Mummy ta tambayi Nazeefah dake sauk'owa daga kan stairs.

"Eh Mummy good morning."

"Morning breakfast naki na kan dining."

"Thank you Mummy ina Daddy?"

"Ya fita office just a while ago."

"Ohh kakan Amal fah?"

"Yana nan zaki je gaishesa ne?" Kai ta gyad'a a hankali, dad'i sosai Mummy taji "sunansa Papi ba Kakan Amal ba kinji?"

"Naji."

"Muje in raka ki toh."

***
Bayan sunyi sallama Papi ya tashi ya bud'e musu k'ofa, a parlour suka zauna inda Nazeefah ta sauk'a har k'asa ta gaishesa. "Ina kwana Papi?" Na sosai Papi yaji dad'i ya amsa da fara'a "Tashi mamana, tashi ki zauna ya karatu? Ya k'are ko da saura?"

"Ya k'are Papi sauran graduation ne kawai."

"Toh madallah Allah sanya alkhairi."

"Ameen Amal tazo ta samu 'yarta kuma."

"Eh mun samu takwararki."

"Haka Mummy tace, toh Allah ya raya ya d'ayyiba."

"Ameen ameen."

"Dama nace barin gaisheka kafin in wuce chan gida in duba Amal kuma in baka hak'uri game da duk wani rashin hankalin da na tafka da a baya, please forgive me."

"Ba komai 'yata nagode Allah sak'a da alkhairi ya miki albarka komai ya riga ya wuce kinji?"

"Ameen Papi, thank you so much."

"Toh Abba bari mu koma" fad'in Mummy har bakin k'ofa ya rakasu sannan ya dawo ciki. Nazeefah na gama breakfast ta jira Mummy ta shirya suka fice. Tun da suka isa gidan gabanta ke fad'i shin idan sun had'u da Afzal zatayi mishi magana ne ko kuwa?

"Mummy I can't do this" ta fad'a kafin su shiga ciki.

"Sure you can Nazeefah karki ji komai okay??" Kai zallah ta iya ta gyad'a sukayi sallama suka shiga.

"Ha'a Mummy sannu da zuwa" cewan Afzal dake zaune a parlour da Nihal rik'e a hannunsa yana mey k'ok'arin tashi. Mik'ewan da yace zeyi sukayi ido hud'u da Nazeefah ba k'aramin fad'i gabansa yayi ba for a second ya d'au ma ko hallucinating nata yake.

"Nazeefah?" Ya ambata bayan tsawon lokacin da suka d'auka suna kallon juna da sauri ta kawar da kanta daga kallonsa had'e da gaishesa "Ina yini Ya Afzal?"

"Nazeefah yaushe kika dawo? Bismillah ku shigo" waje suka nema suka zauna ita da Mummy yayinda ya cigaba da rik'e Nihal.

"Jiya-jiya ta shigo" Mummy ta amsa.

"Oh ayyah ya karatu? Ya k'are ko da saura?"

"Ya k'are Amal ta sauk'a lafiya?"

"Lafiya k'alau Alhamdulillah an samu takwararki" ya amsa had'e da mik'ewa dan kai mata baby'n, a garin mik'a mata ita hannunsa ya goga nata kad'an. Mutuwan tsaye yayi waien yayinda itama tayi freezing inda take zaune, ji tayi duk wani rayuwan da sukayi da a baya suna dawo mata, ta d'au by now tayi moving on, ta d'au koda ta sake sanya sa acikin k'wayoyin idanunta baza ta sake ji mishi wani abu ba ashe ba haka bane, har yau akwai ragowan soyayyarsa a cikin zuciyarta.

"Masha Allah she's soo big" ta fad'a tana k'ok'arin 6oye bak'on lamarin daya ziyarce ta. "And soo beautiful ga shi kamanninsu d'aya da Amal."

"Wane an raba kara" cewan Mummy. Bayan Nazeefah ta d'an rik'eta ta mik'awa Mummy sannan tayi gyaran murya. "Ya Afzal nasan komi ya riga ya wuce amma dan Allah ka yafe mun duk wani abinda nayi maka da wanda na sani da wanda bana sane da shi I'm really sorry."

"Nazeefah there's no need to, mun riga mun zamo abu d'aya yanzu, Allah ya yafe mana gabad'aya Amal will be so thrilled to see you bari inyi mata magana." Knocking yayi bayan an amsa ya shiga a gaban dressing mirror ya sameta zaune tana taje sumarta.

"Ya Omri?"

"Ina Mami?"

"Wanka" ta amsa.

"Come there's something you need to see."

"Menene? Meya faru?" Lokaci guda hankalinta ya tashi a cewarta wani abu ne ya samu Nihal.

"Kede kizo."

"Yaya please speak up menene ya faru? Nihal ce?"

"Just come" cike da fargaba ta mik'e tabi bayansa suna shiga parlour ya matsa gefe wanda hakan ya bata daman sanya Nazeefah a ido. Da fari ma k'in amincewa tayi, ta d'au ko wasa idanunta suke yi mata.

"Nazeefah?" Ta kira ta cike da k'in yarda.

"My sister" Nazeefah ta amsa idanunta suna masu cikowa da hawaye.

"Nazeefah kece??" Itama ba shiri idanun nata suka ciko da hawaye.

"Yes Amal ni ce" da gudu ta ruga taje tayi hugging nata inda suka fashe da kuka dukansu biyu. Mummy dake rik'e da Nihal itama bata san lokacinda idonta ya cika da k'walla ba.

"Amal I'm so sorry please forgive me." A hankali Amal ta janyeta daga jikinta sannan ta shiga share mata hawayen ta, "ki daina neman tuba na Nazeefah, har cikin raina na yafe miki komai duniya wa lahira kukan ya isa haka." Sake rungumeta Nazeefah tayi tana mey sake tsanar kanta na duk wani cutarwan da tayi wa 'ya uwarta.

"Amal ban san da wani bakin zan yi miki godiya ba" cewan Nazeefah bayan sun nemi waje sun zauna a gefen Mummy. "Amal you named your first daughter after me, duk kalan mugunta da bak'in halin da na miki hakan be hanaki aikata abinda kika fasa ba, da Mummy tace mun kin yi mun takwara na kasa amincewa sabida kasa gane wace irin mutum ce ke da nayi, instead ki sak'a mun da sharri kaman yadda nayita cutar da ke se kika gwammaci ki sak'a mun da alkhairi, alkhairin da ba kowa ne ze iya yin irinsa ba, Amal I hate myself for ever hurting you please forgive me."

"Nazeefah komi ya riga ya wuce and I can't tell you how happy I am right now that you're back with us, addu'ata kullum bata fin Allah ya dawo mana dake cikin k'oshin lafiya and here you're in good health and shape Alhamdulillah."

"Amal thank you so much, thank you."

"Don't mention Nazeefah kuma dan Allah kibar kukan haka ya isa."

"Allah ya raya mana Nihal gani nake kaman mafarki har yanzu wai kin yi mun takwara, 'yar uwata guda tayi mun takwra it feels like a dream." Murmushi mey k'ayatarwa Amal ta sakar wa Nazeefah "Ya karatu ya k'are?"

"Eh saura graduation."

"Ayyah congratulations Allah sanya alkhairi."

"Ameen, Naki fah?"

"Final year zan shiga nima."

"Masha Allah Allah sanya alkhairi ina Mami?"

"Tana wanka nakega ta fito yanzu."

"Muje ki raka ni in gaisheta."

Da murmushi kwance a fuskanta ta mik'e "Oya tashi muje toh." Afzal ya kasa daina murmushi, all he's ever wanted is to see his Amal happy and ya san ba abinda ze kai mata shiryawa da Nazeefah dad'i se gashi yau Allah ya shirya tsakaninsu, he can't ask for more.

Har cikin d'aki gun Mami Amal ta kaita inda suka gaisa sannan Nazeefah ta nemi tubanta na duk wani abinda tayi wa Amal wanda ta san yayi wa Mami zafi, a wajen duk sukayi reconciling. Kusan Azahar Mummy tace zata koma dan yin girki Nazeefah kam tace sam bata tafiya, se hira suke da Amal ta rik'e takwararta a hannu. Chan da zatayi sallah ta mik'a ta wa Amal dan yin alwala, tana cikin yin sallah ne wayanta dake gefen Amal ya shiga ruri lek'awa tayi dan ganin wake kira acewanta ma ko Mummy ce se gani tayi Baby❤️💕🔐 na flashing akan screen d'in da hoton wani kyakkyawan bawan Allah yana nan d'an bak'i da shi attatched to it. Murmushi ta sakar ta cigaba da rik'e Nihal har izuwa lokacinda Nazeefar ta idar.

"Wa ya kira?" Ta soma da tambayanta.

"Baby" Amal ta amsa.

"Oh!" Ta furta tana sunkuyar da kai.

"Baza ki kira shi bane?"

"Ba matsala ko anjima zan kira shi."

"Wai kunya na kikeji ne? Kinga baza ki shanya mun in law ba haka kawai, d'au waya ki kira shi kice mishi sallah kike, gashi" Mik'a mata wayan tayi sannan ta cigaba da shayar da Nihal.
Kaman yadda Amal ta bui'aceta tayi ta kira sa back inda ya d'aga a first ring.
"Halo Babe?"

"Belle how're you?"

"I'm fine Babe? Ya kake?"

"I also, just that I miss you." So take tace she misses him too amma kunyan Amal take ji "Ermm Babe kasan wani abu? I will call you later okay? Se anjima" bata jira jin me zece ba ta katse. "Iyyeee so tell me who is the handsome looking dude?"

"Kai Amal kede kiyi focusing a abinda kikeyi kafin kisa nono ya bi mun kan takwarata."

"Baki amsani ba waye shi?"

"Wani ne."

"Your man?" Gira ta d'age mata as yes. "Wow ina kuka had'u? A UK?" Nan ma giran ta sake d'agewa.

"Awwn am so happy for you sister tell me about him mana."

"Nak'i."

"Pleaseeeeee."

"Sa'anki d'aya saboda Nihal."

"Haha naji ina sauraronki."

"Sunan sa Ahmad A UK muka had'u naje yin masters d'ina whereas shi kuma PHD. He's a Nigerian, yana zama a abuja yana da aure da yara biyu."

"Wow I'm really impressed in ba wai kin fad'a ba mutum baze ta6a cewa yana da aure ba."

"I know right ko ni da ya cemun yana da aure ban yarda ba, ashe wai harda yara biyu, ko da shike auren wuri yayi when he was 22, he had his first son at 24 and his second daughter at 27 he's now 34 years old."

"Impressive Nazeefah I'm so happy for you wallahi su Mummy sun sani?"

"Not yet ke na fara sanarda ina son se ya gama karatunsa ya dawo se in yi introducing nashi to the family."

"Hakan yayi Nazeefah wallahi nayi miki murna sosai ya uwar gidan ta shi? Ya had'aku ko tukuna?"

"Ya had'amu, ai be jima bama suka je mishi hutu suka komo bari kiga pictures da muka d'auka da ya fita damu outing ranan" tayi maganan tana latsa wayanta "Here you go" amsa Amal tayi ta shiga viewing tana swiping "Goodness he's got such a beautiful family wallahi, da ke da uwar gidan ban san waye gaba a kyau ba gaskiya gata itama very young."

"Yes she's 28 years old amma kika ganta wane tana early twenties nata."

"Bata da wata matsala ko?"

"Sam wallahi yadda kika san kanki haka take tamkar 'yar uwarta haka ta d'aukeni."

"Such is life Allah ya baku zaman lafiya mey d'aurewa ya sunan yaran nasa?"

"Fawwas da Fauzah."

"Masha Allah I'm sooo happy for you sis."

"Thank you Maman takwara."

****
Ba Nazeefah ce tabar gidan ba se bayan sallan isha. Haka kusan kullum tana gidan Amal, kafin suna kuwa ta samu ta had'a akwati mey set uku wa Amal biyu na baby d'aya nata. Amal ta samu kyautuka sosai sede ace masha Allah. Seda Mami tayi mata arba'in sannan ta koma gida.

Nihal na da watanni uku Amal ta soma shiga school so anytime zata fita school se ta biya gida ta kai wa su Nazeefah raino. Atimes kuma wa Ummi. Da Khaleefah ya dawo hutu kuwa se su had'u suyita fad'a akan Nihal cewa sam d'aya baze ta6a ta ba. Yarinya san kowa k'in wanda ya tasa, ga fara'a ga murmushi, gata very plumpy, gashin kan nan tabarkallah. Haka nan rayuwa ta cigaba da kasance musu cikin kwanciyan hankali da so da k'auna. Na sosai Afzal yake ji da Nihal sau dayawa yakan riga Amal dawowa gida daga office da ya tashi seya biya gidansu Mummy ya amshi 'yarsa su dawo gida ya mata wanka yayi rainonta kafin Rania'nsa ta dawo.
Amal could not ask for more, this is indeed a dream she's living. A perfect daughter, a perfect husband and a perfect family.


_7 months later..._

Ababe da dama sun gudana, da izinin Allah su Amal sukayi graduating bata da spill ko d'aya, ta d'ayan fannin ma Nazeefah har taje UK ita da Mummy anyi musu graduation nasu sun dawo. Shima
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment