Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ta rasu muka je ta'aziya" tayi mai k'arya saidai take waien ya gano k'arya take. Kukanta baya wuce akan Abdul, tunanin hakan ba k'aramin k'ona masa zuciya yayi ba. Danne zuciyan nasa yayi ya mata ta'aziyya, hira sama-sama sukayi bayan sun gama ci ya d'an zagaya da ita cikin school sannan ya mayar da ita lecture hall nasu ya koma office.

Nazeefah na kitchen tana had'a girkin yamma taji ringing na wayanta akan dining table. Da wuri ta fito ta d'auka ganin k'awarta Khadijah ke kira.

"Halo Khadijah?"

"Na'am Nazeefah ya kike?"

"K'alau."

Shiru yau baki fito school ba."

"Wallahi cramps ne ya rik'e ni d'azu amma da sauk'i yanzun."

"Ayyah Allah k'ara sauk'i toh."

"Ameen yane toh?"

"Nace ba wani mota ne kam mijinki yake hawa?"

"AMG C43 lafiya?"

"Chab! Wallahi shine! 'Yan mata shine!" Ta sanar da k'awayenta dake gefenta.

"Shine wa?" Nazeefah ta tambaya curiously.

"Babe mijinki muka ga tare da wata some minutes ago nan cikin unimaid garden." Wani irin mumunan fad'i gaban Nazeefah yayi.

"Afzal d'in?" Ta tambaya cike da k'in yarda.

"Wallahi shine shi da wata suka zo suka ci abinci suka fice duk a idonmu."

"Kai k'arya ne ban yarda ba, bade Afzal ba sede ko me kama da shi."

"Ki tsaya achan, ana fad'a miki abu kina musu wallahi shi muka ga ni bansan ma mey ya hanani d'aukansu a waya ba da na tura miki an kashe musun."

"Khadeejah, Afzal fa kikace? Afzal kika gani da wata?"

"Tabbas."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Nashiga uku na lalace! Tun ba yau ba nake zarginsa ashe de gaskiya ne, amma ko! Yanzu rashin kunyansa har ya kai yana d'aukan 'yan mata yana kaisu cin abinci a idanun jama'ah?"

"Hmm ai na miji ba d'an goyo bane Nazeefah komin dad'inki da shi seya cimiki amana."

"Oh Allah nagode sena shigo gobe."

"Allah kaimu." Tana ajiye wayan ta shiga sintiri a dining space d'in har miya ya soma k'onewa bata sani ba. A takaice girkin ranan sam ba hankali a jikinta tayi. Koda Afzal ya dawo bata mai maganan ba duda cewan ji take kaman ta rufesa da duka don zafin kishi. Lafiya k'alau tayi welcoming nasa bayan sallan Maghrib suna zaune a dining zasu fara cin abinci Afzal ya lura da kallon da Nazeefah ke tayi masa kusan tun dawowansa daga office.

"Nazeefah are you sure you're okay? " ya tambayeta. Kai tayi saurin gyad'a mai had'e da kawar da kanta. Nan da nan tayi serving nasu spoon d'aya Afzal ya kai baki ya harar da abincin waje.

"Subhanallahi!" Yayi exclaiming.

"Lafiya?" Tayi saurin tambaya.

"Ai na fad'a dama ba lafiya ba shin meke faruwa? Kinji uban gishirin dake cikin abincin nan kuwa? Bayan nan ga warin k'una what's really going on? Jikin naki ne har yanzu? Ai da kin bar girkin" Ji take tamkar ta d'aukesa da mari dan haushi. Bak'in cikin da yakeji yanzu kad'an ne dangane da wanda ya cusa mata.

"Mey kajeyi a makaranta yau?" Ta tambayesa. Sosai tambayan nata ya basa tsoro taya ma tasan ya shiga school yau bayan bata fita ba? Allah ya taimakesa bawai munafukan k'awayenta bane suka gansa tare da Amal suka kirata suka yi mata gulma. Shima tun farko mey ya kaisa cin abinci a cikin school? Ai don Nazeefah bata fita school ba that doesn't mean k'awayenta ma basu fita ba, yayi sakarci. Tabbas su suka had'a komai.

"Kayi shiru" ta sake da cewa.

"Naje ganin friend d'ina dake lecturing achan ne" ya shirya mata k'arya dukda cewa yasan ba zama zatayi akai ba. Kallon da takeyi masa zalla ma amsa ne game da tambayan da yake yi wa kansa.

"Wani abu ne?" Ya tambaya da kallon ya soma yi masa yawa.

"Babu kawai dama ance mun anganka a school ne yau."

"Ohhh like I told you naje ganin friend d'ina ne" ya amsa saidai yasan k'arya take masa, kaman yadda shima yayi mata k'aryar. Tabbas an gansa da Amal ne aka kira aka gaya mata.

"Ya cikin naki ya daina ciwo?" Ya tambayeta yana neman canza topic d'in gudun kar fad'a ya 6arke musu.

"Da sauk'i" ta amsa sama-sama.


***
Tun kan wayan da Amal tayi da Abdul se gabad'aya halinta ya sake sauyawa ya koma na da, no matter how hard she tried ta kasa mancewa da shi, da tunaninsa take tashi da kuma shi take yini. Shima ta 6angarensa hakan ne. Kullum cikin tunaninta yake ba makawa.

Haka zata yini d'aki tana kuka. Kwana biyu kenan bata fita school ba ta fake da cewa wai period cramps ke damunta. Shiko Afzal da zaran yaji bataje school ba yasan batun Abdul ne. Hak'urinsa ya k'are, bai jin ze iya jure hakan again he wants Amal to be his alone gashi a gida be san ta ina ze fara sanar da Nazeefah cewan yana shirin k'ara aure ba tabbas yasan baza ta ta6a amincewa da hakan ba, a cikin d'an k'ank'anin lokaci ya gano irin zazzafan kishin da take da shi. Lallai se yayi taka tsan-tsan da d'aukan Amal a mota anyhow tunda yanzu har an soma kawo mata gulma gida.

Washegari ya shirya tsaf abinsa ya je gida gun Abba. Bayan sun gaisa yake ce mai shi yana son a tura gaisuwa gidansu Amal a shirye yake ya k'ara aure. Sosai Abba ya taya sa murna had'e da masa nasiha sosai akan yin adalci inda daga k'arshe kuma yake tambayansa ko ya sanar da Nazeefah batun auren ko kuwa tukuna.

"A'a tukuna amman ina da niyya nafison idan ku manya kun gama komai sena sameta in fad'a mata abinda ake ciki, kar taga kaman ba neman aure nake ba kawai ina flirting ne a waje."

"Kana da point kam amma kana ganin k'in sanar da ita har se idan an sa rana ko makamancin hakan shine dai-dai?"

"I suppose it is Abba" ya amsa sa.

"Toh shikenan Allah shige ma gaba zanyi magana da kawunanka cikin satin da za'a shiga se muje gidansu Amal d'in."

"Toh Abba nagode sosai Allah saka da alkhairi."

"Ba komai Allah yayi ma albarka."

"Ameen bari in lek'a Ummi."

"Ai bata gida baka sani bane?"

"Wallahi no dake ina shigowa site naka na zarce."

"Ayya ai ta fita suna wai."

"Toh ba matsala ni zan wuce." Da haka sukayi sallama. Gidansu Amal direct ya wuce yayi mata waya kan ta fito gashi nan bakin k'ofa. Hijabinta ta ja ta sanya ta feshe jikinta da turare sannan ta fice taje ta samesa inda suka gaisa. Bayan nan ya kira sunanta a nitse.

"Na'am" ta amsa.

"Nace ba izun naki nawa ne yanzun? It's been long ban ji kina mun zancen islamiyya ba Lily."

"I'm sorry kasan jami'a da islamiyyan ne se a hankali idan ba hutu akayi ba bana samun time na karatun kaman yadda nakeso."

"Hakane kam, kina ma k'ok'ari ai am very proud of you tunda kika fara karatu baki samu carry over ba."

"Thank you Yaya."

"So izib nawa kika had'a so far?"

"Saura goman k'asa in gama had'awa gabad'aya kuma dama chan tun da na ta6ayin biyar d'in k'asan a takaice de izu biyar ya rage mun idan na zauna nayi tilawa."

"Masha Allah so ina da Hafizah as a wife to be kenan?" Kai ta gyad'a masa a hankali cike da kunya. "Zaki iya tuna alk'awarin dana d'aukan miki anytime kika gama haddanki?"

"Eh toh not vividly amma de kace akwai special kyautan da zaka mun idan na had'a."

"Very good Umarah nakeson mu tafi tare."

"Saudi?" Ta tambayesa cike da k'in yarda.

"Eh Lily Saudi."

"Yaya are you serious?" Ashe de Allah ze nuna mata ranan da zata kai wa d'akinsa ziyara. Oh Alhamdulillah!

"I'm damn serious, I would want us two to go together."

"Toh Allah nuna mana I really can't wait."

"Ameen but kinsan bazeyi muyi tafiya mu biyu kad'ai ba ko? Tunda ni ba muharraminki bane."

Dank'ari se yanzu hankalinta ya buga ta kuma fahimci inda ya dosa a takaice de so yake yace mata aurensu ya kusa. Oh Allah ita bawai auren neba matsalarta, tunanin yadda zata fara zaman aure da Afzal take wai ma zancen kishiya a gefe. Mutumin da duk rayuwarta ta d'aukesa a matsayin yayanta kuma rana d'aya seta fara kallonsa a matsayin mijinta? How is that even possible?




RANA D'AYA!
#RD

Love... king Miemiebee👄✨

[13/08, 09:31] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣

💦💦 🍃🍃🍃
*RANA D'AYA!*
💦💦 🍃🍃🍃
July, 2018
beeenovels.blogspot.com

_Written by Miemiebee👄_


*PAGE 2⃣3⃣*

"Lily kinyi shiru" ya fad'a yana kallonta.

Kanta tayi saurin kawarwa tare da ambatan sunansa a hankali se kuma tayi shiru.

"Lily I'm sorry but I can't wait any longer, I've waited for so long to be with you and to make you mine and now is the perfect time, please kar kice a'a nasan kina iya had'a haddan naki acikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa. Idan har kika samu kika had'a kinga se ayi bikin sauk'an naki dana auran mu at once bayan nan kuma se mu wuce Saudi for our honeymoon, don't say no please."

Excuse ta shiga nema amma gabad'aya ta rasa ta mey zata ce masa. Bata san mey ba amma anytime Afzal yakeyi mata zancen aure gabanta yake tsinkewa yana fad'i, har wani tsoro-tsoronsa ma takeji. K'arshe de ta samu ta 6ullowa zancen ta hanyan sak'alo sunan Nazeefah. "Toh Yaya Nazeefah fah? Ita baza mu tafi da ita ba?"

"Lily I want you to believe in me, ki sani cewa zanyi iya k'ok'arina don ganin nayi adalci tsakaninki da 'yar uwarki. Nasan auran mey mata a zamanin yanzu isn't something easy but I need you to believe in me, ni da Nazeefah cikin kwanakin nan zamu tafi in shaa Allah so that idan munzo tafiya dake bazata ga kaman anyi mata rashin adalci ba. But kafin mu tafi da ita I need your approval please ki amince zaki aureni, I've spoken with Abba already a shirye yake suzo su sami su Papi ayi maganan, amincewan ki kawai nake nema Lily."

"Yaya I do believe in you, tsoro na d'aya ne" ta sanar da shi a nitse.

"What is it? Tell me" ya amsa take.

"Nazeefah, Yaya tsoron zama da kishiya nake bansan mey Nazeefah zata iya aikatawa ba, ban san irin kishin da take da shi ba, bansan ko zata amince dani kokuwa a'a ba, banason in zame d'aya daga cikin jeri matan da kishiyoyinsu suke yi musu illa kaman yadda banida niyyan cutar da ita bazan so nima ta cutar dani ba."

"You're safe with me Lily, I'll do everything in my power to keep you save and kar kiyi tunanin Naeefah is that evil nasani kishi kam dole ne but she'll never hurt you, I'll make sure of that and besides banida niyyan had'aku gida d'aya, unguwa ma ba had'aku zanyi ba ni kawai ki amince."

"Toh shikenan Yaya na amince da k'udurinka, kana iya turo su Abba but I have one favor to ask."

"Ask me anything Lily."

"Please kayi hak'uri semun kammala first semester d'in yaso se ayi auren cikin hutu, bana son hidiman bikin ya raba mun hankali."

"I'll do only as you wish Lily se abari idan kin kammalan ba second semester kuke ba?"

"Eh" ta amsa had'e da gyad'a kai.

"Allah taimaka toh."

"Ameen."

"So will you agree to marry me?"

"Yaya ba nace eh ba."

"I want to hear it again, Lily am head over hills for you, please tell me again will you marry me?"

"Yes Yaya" ta amsa cike da kunya ko kallon gefensa ta kasa bale cikin idansa.

"Thank you Lily ji nake kaman duk duniya ba wanda ya kaini farin ciki, Lily a yau kin cika mun buri da kuma mafarki. I've been looking forward to this day and now I shall be looking forward to the day I'll make you mine, the day you'll start answering my name and the day I can call you my wife. Lily you don't have to worry because I've promised to take care of you, to love and protect you with my life, I've promised to never leave your side. In shaa Allah bazakiyi nadaman aurena ba."

"I know Yaya Allah and I'm very grateful Allah ya baka ikon yin adalci tsakani na da Nazeefah."

"Ameen Lily kinsan wani abu?"
Kai tayi saurin kad'awa da nufin a'a .

"Guess!"

"But I can't ka fad'a mun kawai."

"I love you" ya sanar da ita. Har cikin ranta taji nauyin kalamun nasa yayinda kunya me tsanani ya rufeta fuskanta ta shiga karewa. "Kin san wani abu again?" Nan ma kai zalla ta iya kad'awa.

"I love you" ya kuma sanar da ita. By now kam Amal ji take kaman zata lume k'asa don kunya, bata san mey ba amma kunyansa takeji kunyan ma me tsananin tsiya bata tsammanin zata ta6a iya sakewa dashi. Wani sa'in tana missing relationship nasu na da dasuke a matsayin Yaya da Lily zallah ba wani abun ba.

"Can't I get an 'I love you' back?" Ya tanbayeta tare da had'e girarsa.

"Yaya..." se kuma tayi shiru.

"Lily I know you're not comfortable with me, nasan kina tsananin jin kunya na and I respect that alot but please give me the chance to love and make you happy."

"Yaya I'm already yours ka daina damun kanka haka."

"I feel honored then" ya amsa "Can I ask of a favor?"

"Ina sauraronka."

"Can you please tell me you love me too? I need to hear these words so badly."

"Yaya-"

"Lily I know it you don't love me-" ya katseta.

"Yaya ya kake magana haka?" Itama tayi saurin katse sa.

"Na sani Lily, nasani har yanzu Abdul ne a zuciyarki kuma shi kikeso and bawai ina kishi da hakan bane kokuwa ina jin haushi, nasan zafin rabuwa da masoyi nasan ze d'au lokaci kafin ki iya mancewa dashi ki bud'e mun zuciyarki. I just want you to know that no matter what I'll stand by your side. I'll provide support and love you regardless, I'll be here Lily even if you don't need me."

"But Yaya I need you also-"

"Shhh!" ya katse ta "And also bana son kiyi tunanin cewa banida godiya ne nake tinziraki haka ina gaggawa, ki sani it's just because I love you so damn much. Bayan nan I'm very grateful for all the sacrifices you've made to save my life, I'll forever remain grateful to you Lily I just need to hear these words koda kuwa you don't mean them just tell me."

"Yaya I-" seta bud'e baki zata sanar da shi kalamun seta kasa ji tayi bakinta yayi nauyi, banda sunansa ba abinda take iya furtawa.

"Please try" ya rok'eta. Sede ina duk yadda taso sanar dashi hakan abun ya gagara se gani take kaman Ya Abdul na tsaye a gefen windon yana kallonta.

"I'm sorry then" yace k'arshe feeling so sad.

"Yaya ni ya kamata in baka hak'uri dan Allah kayi hak'uri Wallahi I'm trying, I really want to forget about Ya Abdul abun ne yafi k'arfina please forgive me" ta sanar da shi cikin sautin kuka.

"Its okay Lily ba se kinyi kuka ba, forgive me but ba laifi na bane don hak'uri na ya gaza, you're just like a drug, so addicting. Ji nake kaman in ban same ki ba ina iya rasa rayuwana."

"Yaya dan Allah kabar magana haka I'll always and forever be yours, kasa a ranka na riga na zama taka bana son inji kana maganan rasa rayuwanka, ya kakeson in rayu in ba kai?" Tunda suka fara hirar se yanzu ne ta juyo tana kallonsa idonta cike da k'walla.

"Forgive me, but bakiya sona ya kikeson inyi idan ba mutuwa ba?"

"Yaya I care about you, I care about your existence morethan anything dan Allah kabar cewa haka."

"Anything for My Lily."

"Thank you" ta amsa had'e da sakar masa k'aramin murmushi tana share hawayen nata. Murmushin shima ya miyar mata yayinda ta shiga duban lokaci a cikin wayanta. "Maghrib ya kusa ko?" Ya tambayeta. Kai ta gyad'a a hankali "Ya kamata mu soma yin niyyah."

"Sure" ya amsa tare da mik'a hannunsa ta back seat ya janyo wata leda. "Here wannan naki ne."

"Yaya baka gajiya da bani gifts ne kam kullum?"

"Bazan ta6a gajiya da farinta miki ba Lily."

"Amma Yaya-"

"Not a word please" ya katseta. Bata k'ara musu ba ta mik'a hannu ta amsa had'e da yimai godiya. Seda taga ficewansa ta k'arisa ciki. D'akinta ta nufa inda ta zazzage kayakin gabad'aya designer turaruka ne da man shafawa aciki seda su gel da sauran kayan shafe-shafe. Oh! Idan ta tuna da irin kashe kashen kud'in da Afzal yakeyi akanta setaji kaman ta samu Ummi tace ayi mishi fad'a ya daina. Bata son a sanadinta ya samu kariyar arziki ko makamancin hakan gashi ya dage kullum idan zezo se yayi mata gaggarumun shopping.

***A nitse Afzal ya k'arisa gida sede tun da ya hau kan hanya yake tunanin kalamun Amal da kuma yadda ta kasa furta masa kalaman da kunnensa suke kwad'ayin ji. Be san kuma mey zey sakeyi Amal ta bud'e masa zuciyarta ba ta koyi sonsa, he misses her alot. He misses her smiles and laughter, everything about her he mise. Duk abinda yasan ya kamata yayi ya yi amma ina har yau ta kasa sakewa da shi. Yana isa gida Nazeefah ta taso tayi masa sannu da zuwa jawo hannunta kawai yayi ya rungumeta feeling so lonely.

Ta kai kusan minti d'aya tsaye ko motsi babu sannan a kid'ime ta zagaye hannayenta a bayansa hugging him back cike da rashin fahimta. "Afzal is everything okay with you?" Ta tambayesa a hankali har anan be saketa ba yayinda kuma ya kasa amsa ta. "Afzal?" Se anan ya raba jikin nasu.

"Nazeefah I feel so alone, shin bayan su Ummi akwai mey sona kuwa?"

"Wani irin magana kuma kake haka? Meya faru?"

"Just answer me, akwai?"

"Akwai mana Afzal, and ina d'aya daga cikinsu. I love you Afzal no matter what, kar ka ta6a tsammanin bakada masoya bayan su Ummi. I'm here and I love you kaji?"
Kai ya gyad'a a hankali "Thank you Nazeefah."

"You shouldn't mention food is ready taho muje inyi serving naka ko seka dawo daga masallaci? Naga Maghrib ya kusa" Ta tambayesa. Bata kai da juyawa ba ya rik'o hannunta kafin ta fahimci abinda yake shirin yi kawai taji moist lips nasa akan nata, mutuwan tsaye tayi a wajen yayinda ta kasa koda kyafta ido. A hankali taji large arms nasa yana rufe bayanta yayinda yake matso da ita kusa da shi, deepening the kiss in the process. Wani irin electrification taji yana bin jikinta yayinda taji numfashinta na neman d'auke mata, bata san a lokacin da ta shiga mayar masa da martani ba. A hankali a hankali suke tafiya manne da juna har seda Afzal ya turata jikin bango. Mutum na iya cewa sun mance da duniyan da suke ciki don zafin kiss kawai, gabad'aya sun fita daga hayyacinsu. Chan Afzal ya saketa a hankali yana k'ok'arin kama numfashinsa kaman yadda itama takeyi, goshinta ta sauk'e dai-dai saitin ha6arsa yayinda wani irin zazzafan sonsa yake shiga jikinta. Ji take gabad'aya duniya ba wanda ya kaita murna, ashe de Allah ze k'addaro mata da wannan rana? Oh she can't get over how sweet, soft and moist his lips were, bata k'i ya sake kissing nata over and over again ba.

"I'm sorry" taji ya furta a hankali yayin da minty breath nasa yake fifita hancinta. Shi kansa ya rasa gane meke faruwa.

"It's okay" ta mayar masa har anan ba wanda ya motsa acikinsu.

"I'm sorry" ya sake fad'a had'e da sauk'e hannayensa da suke rik'e da kunkuminta "I'm really sorry ban san meke shirin faruwa da ni ba please forgive me" kafin tace wani abun ya wuceta da hanzari inda ya zarce d'akinsa. Key ya sa had'e da manna bayansa jikin k'ofan. Idonsa ya rufe gam amma ya kasa daina tunanin kiss da sukayi sharing da Nazeefah shin meke faruwa? Gabad'aya ji yayi Amal yake kissing, mey soyayyar Amal ke shirin yi masa? Taya zeyi kissing Nazeefah ya d'au Amal yake kissing? Anya kuwa soyayarta ba shi ze halaka sa ba? Yanzu da wani ido ze sake kallon Nazeefah? Oh Allah! Yau yana cikin wani yanayi. Sallan Maghrib da be fita ba kenan ranan wane sabuwan amarya haka ya la6e a d'akin. Tun Nazeefah na jiransa da ya fito suci abinci har bacci yayi gaba da ita zaune akan dining d'in. Chan wajajen goma ya lek'o waje a sanadin yunwan daya fafarosa. Sid'ak-sid'ak yake tafiya wai kar tajiyo motsinsa ta fito, ba k'aramin tsinkewa zuciyansa yayi ba ganinta da yayi zaune akan dining ta kafa kanta akan dining table d'in. A farko niyyan juyawa ya koma d'akinsa yayi tunda de bata gansa ba amma kuma ya fasa sanadin kukan da cikinsa yayi don yunwa. Matse idonsa yayi ya k'arisa wajen had'e da yin gyaran murya se kuma yaga bata motsa ba.

"Nazeefah?" Ya kira sunanta nan ma shiru lek'a fuskanta da zeyi kawai ya tarar bacci takeyi. Allah sarki bade bacci ne ya d'auketa anan ba tun tana jiransa ya fito suci abincin tare? Shin ta ma yi sallah kuwa? A hankali ya shiga tada ita har ta bud'e idonta.

"Kinyi sallah?" Ya soma da tambayarta. Kai zalla ta gyad'a masa yayinda idanunta suke neman kafewa.

"Abinci fa kinci?"

"Ba tun d'azu ina jiranka ka fito muci ba kak'i."

"Ba wai nak'i bane Nazeefah..." se kuma yayi shiru a bisa rashin sanin abinda ze sake cewa.

"Are you ashamed because you kissed me? Are you Afzal?" Ta tambayesa da mamaki.

"Ko kad'an ba haka bane."

"Toh yaya ne? Afzal I know you don't love me but I'll never surrender, zan cigaba da hak'uri ina farinta maka har izuwa ranan da Allah ze sa a ranka kaji zaka iya yafe mun abubuwan da nayi maka da a baya, I really am sorry" ta k'are maganan idanunta na
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment