Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kawai ka tayani kaja mun kayan nawa waje." Amsan akwatin yayi sun kai dab bakin k'ofan suka iske a rufe ta waje.

"Ya lafiya?" Amal da har jiri ya soma d'ibanta ta tambaya.

"Hjy kaman Alhj ya rufe k'ofan ta waje."

"Ya rufe k'ofa kaman ya? Bakada makulli ne?"

"Ya amsa kafin ya fita" ya amsa a takaice.

"Bakinku d'aya ko?"

"Wallahi Hjy ni Alhj be sanar dani komai ba face cewa da yayi in basa makulli na."

"Ka bud'e min k'ofan nan."

"Hjy wallahi ba makulli a hannu na."

"Ka d'auko key ka bud'e mun k'ofan dan Allah ka bud'-" tana cikin magana kawai ta sulale k'asa saboda jiri. "Hjy!" Mey gadi ya sa ihu nan driver dake ciki ya fito mey ze gani jikin Amal kwance a k'asa.

"Adamu meya faru? Mey kayi mata?"

"Wallahi ban yi mata komai ba dan Allah ka nemo waya ka kira Alhj bai jima da fita ba." Nan da nan Driver ya shiga neman Afzal a waya lokacin har Afzal ya isa gida an bud'e masa gate sauran kawai ya shiga sega kiran Driver ba 6ata lokaci ya d'aga "Alhj ka dawo gida akwai matsala, Hjy ta sume." Ko amsa sa beyi ba yayi reverse, tuk'i yake kaman a sama yake tafiya. Nan danan ya iso gida yayi parking bakin k'ofa ya k'arisa ciki. Har anan su Adamu mey gadi basu ta6a Amal ba gudun da suke kar yin hakan ya haifar da wani matsala.

"Kan Amal ya k'arisa da sauri yana tapping fuskanta. Ashe ba sumewa tayi ba jiri ne ya d'ibeta. Be 6ata lokaci ba ya cicci6eta yayi d'aki da ita inda ya sauk'eta kan gado. Lamban abokinsa ya kira da ya turo masa family doctor'nsa bayan nan ya koma kan Amal.

"Lily meyasa bakiya jin magana ne? Seda na fad'a miki ba inda zaki amma kika k'i ji? Ina kike so kije?"

"Yaya zaman mu ya haramta" kad'ai ta iya ce masa cikin wahalallen murya.

"You're not the one to decide Amal, so kike ki kashe kanki ne? Dan Allah karki sake yin haka stay here until you get better."

"Just take me home Yaya."

"Amal this is your home please."

"No Yaya."

"Ya isa haka just keep quiet bakida lafiya in kika samu sauk'i zamuyi magana." Zama ya cigaba da yi akanta har seda likitan ya k'araso ya dubata inda ya d'aura mata ruwa yakuma jaddada wa Afzal cewa kar ayi wasa da magunanta sannan kuma tana cin abinci sosai bayan nan ya koyawa Afzal yadda ze sake sa mata ruwa idan ledan da aka had'a d'in ya k'are. Har waje Afzal ya rakasa ya sallamesa sannan ya taho ciki ya koma kan Amal. Hannu ya aza akan goshinta yana shafa kan gashin da ya sauk'o har kan wajen a hankali, "Yaya what of Nazeefah? Ka sake ji daga gareta?"

"Rania please, ki bar zancen Nazeefah forget about everything lafiyanki ne a gaban mu yanzu kinji?" Ba dan tana so ba ta gyad'a mar kai.

"Nasan kina jin yunwa mey kikeso kici?"

"Bana jin yunwa Yaya I lost my baby."

"I know Rania and I'm sorry in shaa Allahu me ceto ne."

"Yaya I lost my baby" kawai ta rushe da kuka. Hak'uri ya shiga bata amma takasa hak'ura, da k'yar ya samu ya shawo kanta kukan nata ya lafa "Yaya baka tunanin cikin nan ya zube ne saboda k'arshen zaman mu yazo? Acikin sauk'i zamu iya rabuwa da juna tunda babu rabo a tsakanin mu yanzu, Allah na sonmu ne shiyasa yasa cikin nan ya zube saboda guje mana abin kunya da yake, dan Allah ka kaini gida."

"Rania har se zuwa yaushe ne zaki gane cewa kece ruhi na idan bake kuma bazan iya rayuwa ba?"

"Yaya I'm sorry amma ba abinda zamu iyayi, k'addarace rubucacciya dole mu rabu da juna."

"Ina son da kike ikirarin kina yi mun Amal? Ashe har Allah ze kawo rananda zaki k'wad'aici rabuwa da ni? Ashe Allah ze kawo rananda zaki tafi ki barni?"

"Yaya ba haka bane, kai kanka shaida ne game da irin soyayyar da nakeyi maka but that still isn't enough, taya zan cigaba da had'a miji d'aya da k'anwata? Shin akwai abu mafi muni irin wannan? Yaya idan har Nazeefah k'anwata ce da wani idon kake son in sake kallonta? Yaya wannan wani irin abin kunya ne?"

"I'm aware of all that Amal kuma idan har da akwai wanda zefi jin kunya acikin mu duka nan toh nine, ya Rabbi I married two sisters and slept with both of them ni nafi kowa abun kunya but I still don't care as long as you're willing to stay with me."

"How Yaya? Wani 6angaren zaman mu ya haramta ne ka kasa fahimta har yanzu? Baze yiwu ba ni kawai ka kaini gida."

"I don't care Amal!" Ya sanar da ita a tsawace ba tare da yasani ba. A sanadin haka ta firgita se kuma be ji dad'i ba, hannunta ya d'aga ya rik'e acikin nasa "Look I'm sorry but please ki daina cewa auran mu ya haramta Amal I beg you please." Hawaye na gangara daga idanta ta gyad'a masa kai "In had'a miki kunun ki kisha?" Nan ma kan ta kuma gyad'a masa "Kafin nan ka kira Mami ka sanar da ita banida lafiya."

"Is this what you really want Rania? Ko so kike idan ta taho ki sanar da ita gaskiyan al'amarin dake faruwa saboda ta d'aukeki ta tafi dake?"

"Yaya-" katseta yayi da wuri "Please Amal don't leave me, abinda yake faruwa already ya riga ya mun yawa, I just found out I'm marrying two sisters, after that kin samu miscarriage, mun rasa future'n mu, I don't know ko addini na ze haramta min ku duka ko ze bani za6i in d'auki d'aya, I'm so confused akan hakan kuma kike son ki sake tafiya ki barni? Shin ya kike son in rayu Amal? Dan Allah ba don ni ba koda bana nan kar ki d'au waya ki kira Mami I beg of you."

Na matuk'a ya bata tausayi, tasani tashin hankalin da take ciki kad'an ne a ganga da nasa amma saboda san zuciya se su take abinda Allah yace suyi zaman haramun? Tana sonsa, son da bata tunanin zata ta6a daina iya yi amma rabuwa ne ya zama dole. Ba don tana so ba sedon yadda ya bata tausayi ta gyad'a masa kai "I'm sorry."

"I dont want you to be Rania, kawai kiyi mun alk'awari bazaki kira Mami ko Papi ba, idan lokacin yazo ni da kaina zan kirasu in sanar dasu komai da kaina I just need time to sort out things. Promise me okay?"

"I promise" ta amsa tana gyad'a masa kai. Peck ya sauk'e mata a kumatu sannan ya fice nan da nan ya had'a kunun ya kawo ya bata da kansa da ikon Allah kuma tasha sosai sannan ya 6allo mata magunanta ta had'iye ya sake miyar da ita ya kwantar da ita. Be bar wajen ba seda ya tabbata baccinta yayi nisa. Duban agogo yayi yaga Maghrib har ya wuce nan da nan ya idar ya shige mota ya fice gida bayan kunnen da ya ja wa mey gadi cewa komin yaya kar ya bar Amal ta fita ga k'ofa ya bar musu a bud'e saboda fita masallaci.

Sannu da zuwa Ummi dake ta jiransa tun d'azu tayi mai sannan ya samu gu ya zauna a gefenta sede kallo d'aya tayi masa ta fuskanci yana cikin damuwa ga fuskansa daya nuna cewa yayi kuka.

"Prince lafiya?"

"Ummi Alhj Abdallah ba mutumin kirki bane."

"Ai dama sanda Abbanka ya fad'a maka ka sauwak'e wa 'yarsa kawai a rabu dasu lafiya kak'i ji, shin yanzun mey yayi maka? 'Yan unguwa ya tara suka ma duka ko mey?"

"Idan da dukan nema ai da da sauk'i."

"Meyayi ma toh?"

"Ummi Nazeefah and Amal 'ya'yansa ne they're half sisters."

"What?"

"Alhj Abdallah ne mahaifin Amal, Matana 'yan uba ne Ummi shine mahaifinsu duka."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shin Afzal ka san mey kake fad'i ma kuwa? 'Yan uwa fa kace?"

"Ummi dan Allah ki taimakeni Ummi bazan iya rayuwa ba Amal ba."

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel kace mey? Amal 'yar Alhj Abdallah ce? Yau na shiga uku na lalace Prince! Ya akayi hakan ya faru? Ta ina Amal ta zama d'iyarsa?"

"Bana baki labarin Mami ba? Yadda akayi ta samu cikin Amal?"

"Tabbas."

"Toh mahaifin Amal d'inne Alhj Abdallah shine yayi ma Mami aika-aika ya gudu basu sake ji daga garesa ba."

"Yau wannan wace irin rayuwace? Wace irin mumunar k'addara ce wannan? Innalillahi yanzu Alhj Abdallah yasan yaran nan 'yan uwa ne amma be ta6a yin magana ba se yanzu?"

"Cewa yayi shima recently yayi finding out gaskiya."

"K'arya yakeyi idan ba haka ba har ya akayi yasan Amal d'in 'yarsa ce." Labarin komi ya kwashe ya bata Ummi kam se salati kawai take ta kasa yarda da komi da Afzal ya fad'a se gani take kaman mafarki ne. Ta ina zasu fara 6ullo ma wannan al'amari yanzu?

"Yanzu Amal ta sani?"

"Nayi kuskuren fad'a mata as a result ta samu miscarriage Ummi mun rasa baby'n namu."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wai shin meke faruwa ne yau? Cikin Amal ya zube fa kace?"

"Ya zube Ummi yanzu haka tana kwance a gida likita yazo ya dubata ya sa mata ruwa akan hakan kuma take cewa zata koma gida, Ummi Amal na shirin tafiya ta barni ya zanyi da raina ba d'a ba Amal ba Nazeefah haukacewa kukeson inyi ne?" Ba shiri ya rushe da kuka. Hak'uri Ummi ta shiga basa yayinda kanta yagama d'aukan zafi itama, ta rasa ta ina zata fara 6ullo ma wagga al'amari ba abinda yafi k'ona mata rai kaman lalacewar cikin nan na Amal, amma kam Alhj Abdallah anyi mutumin banza. Ace duk zamanshin nan yana da 'ya a waje?

"Ya isa haka Afzal crying is never a solution ka jira idan Abbanka ya dawo musan nayi."

"I can't wait for that long Ummi, Amal bata da lafiya she needs to be taken care of zan koma gida."

"Afzal kayi hak'uri amma dole Amal ta koma gida."

"Kema kin goyi bayan ta tafi kenan Ummi? Please don't ku tausaya mun."

"Bawai ina nufin ta tafi har abada bane Afzal, ina nufin taje gida na d'an lokacin nan ta samu kulawa mey kyau daga gun Mami saboda kaima ba hankali a jikinka yanzu bale ka iya kula da ita kai kanka kana neman kulawa."

"Ummi I can take care of her, zan kula da ita ni kawai kibar zancen mayar da ita gida please."

"Toh Prince amma dey kasani koda bata koma yanzu ba zata koma wataran ko?"

"Mey kike nufi Ummi?"

"Afzal har ka manta da cewa ya da k'anwa kake aura ne? A ina aka ta6ayin hakan? A ganina kaman yadda Amal ta sanar da kai hakan ne aure tsakaninka da dukansu ya haramta."

"No Ummi please there has to be a way, zamu nemi Malami muyi tambaya in shaa Allahu ze san yadda zeyi damu."

"Prince don't get your hopes high."

""But Ummi I can't lose both of my wives ko za6i akace inyi bazan iya ba bale kuma in rasasu duka. A tunani na idan suda kansu suka amince zasu cigaba da zama as kishiyoyi regardless they're siblings se mu cigaba da zaman mu tunda a zamanin da ma ana had'a 'ya'yan Annabi Adam da Hauwa'u aure."

"Ya kake magana haka Prince? Kai yanzu baka ji kunya ba da gaskiya ya fito? An san ba laifinka bane amma ai da kunya Prince, wa da k'anwa ne fa. Kar ka bari son zuciya ya rufe maka ido ka aikata haramun, tun wani zamanin aka daina had'a jini d'aya aure? Kuma a tunaninka su d'in zasu amince au cigaba da zama tare ne yanzu bayan gaskiya ya fito? Wallahi a'a zafin kishi ma baze bar su ba."

"Ummi ya zanyi toh? Wallahi muddin kuka bari aka rabani da Amal toh nima kuyi shirin rasani because I can't do without her."

"Nazeefah kuma fah?"





RANA D'AYA!đź’–
#RD

Love... King Miemiebee👄✨




Miemiebee Novels

Sunday, 16 September 2018
RANA D'AYA!
BY MIEMIEBEE
PAGE 43



"Ya Salaam! I don't know! I really don't know Ummi amma bazan iya jure rashinsu duka ba because I love them both ko za6i akace inyi bazan iya ba."

"Rabuwa da d'ayansu ko dukansu ya zama dole Prince kai kanka ka sani."

"Bazan iya ba Ummi gara ni in mutu da in rasa d'aya daga cikinsu."
Nauyayyen ajiyan zuciya ta sauk'e yayinda take tausaya wa d'an nata tabbas yana cikin tsaka mey wuya "Yanzu ka kwantar da hankalinka ka koma gida d'in kaje ka samu Amal tunda bata jin dad'i gobe in shaa Allahu zan shigo."

"Allah kaimu" ya amsa.

"Yauwa nace su Mami fa ka sanar dasu?"

"Banyi ba tukuna but I'll."

"Ya kamata."

"Ummi tsoro nake kar suce zasu rabani da Amal."

"Baza suyi hakan ba in shaa Allah, kaide ka kwantar da hankalinka ka kuma sa a ranka cewa komin meya faru shine mafi alkhairi a gareka."

"Thank you Ummi bari in koma."

"Muje in raka ka."

"A'a ba amfani yi zaman ki" nan ya fice ya nufi motansa inda ya zauna ciki yana tunani, gabad'aya ya rasa mey ke masa dad'i. Wayansa ya zaro daga aljihu ya sake trying layin Nazeefah luckily seya shiga sede yana soma ringing aka katse cike da hanzari ya sake gwadawa wanda nan ma aka kuma katsewa. Kansa ne ya d'aure yana cikin nazari sega sak'o nan ta tura mai;

_I'm sorry I can't pick up your call, don't worry we're all fine._
Take yayi replying nata da;
_Alhamdulillah then, where are you at?_
Cikin minti d'aya reply nata ya iso
_Mummy ta kama mana d'aki a hotel zamuyi magana gobe goodnight._

Ajiyan zuciya ya sauk'e atleast they're safe, ko bey tambaya ba yasan Mummy ce ta hanata sanar dashi inda suke saboda gudun kar Daddy yayi saurin ganosu. Oh Allah!
Key yasa ya kunna motan ya dawo gida. Har anan bacci Amal ke, kayan jikinsa ya rage sannan ya duba ledan ruwan nata yaga da ragowa, gadon ya haye ya sameta inda ya kwanta a gefenta had'e da aza kanta a k'irjinsa wanda a sanadin hakan ta farka.

"Shhh go back to sleep it's just me" ya sanar da ita yana shafa bayanta a hakan har ta sake komawa baccin. Shi kam se tuna abinda Ummi ta fad'a masa yake _Rabuwa da d'ayansu ko dukansu ya zama dole Prince kai kanka ka sani._

Wajajen tara da rabi ya farka bayan yayi alwala yayi sallah ya zarce kitchen ya kad'a wa Amal kununta sannan ya dawo ya shiga tayar da ita. Taimaka mata yayi ta wanke bakinta sannan ya bata kunun da kansa bayan nan ya 6allo mata magunanta ta had'iye.

"Wa zaka kira?" Amal data k'ura masa ido ta tambaya ganin ya d'ago wayansa.

"Ummi, tace in kin tashi in had'aku ta gaisheki da jiki" bata sake cewa komai ba har se lokacinda Afzal ya had'asu suka gaisa. "Mami fa yaushe zaka kira su?"

"Zan kira su Amal amma ba yanzu ba."

"Se yaushe Yaya?"

"Meyasa kika k'osa in kirasu Lily? Didn't we talked about this?"

"Yaya I'm sorry I jus-"

"Ya isa please you're sick don't stress yourself. Zaki watsa ruwa?" Kai ta kad'a masa zalla sannan ya mik'e ya ciro mata kayan baccinta ya taimaka mata tasa. Bayan ta kwanta ya d'aura mata sabon ledan drip d'in sannan suka kwanta. Washegari kaman yadda Ummi tayi alk'awari tazo ta gidansu da breakfast mey kyau da kuma kunun Amal da ta dama mata cikin flask. Har cikin d'aki ta shigo suka gaisa da Amal sannan suka dawo parlour ita da Afzal.

"Na sanar da Abbanka halin da ake ciki jiya."

"Meyace?"

"He was also shocked and disappointed at his friend mun kuma samu mun tambayi Malamai har biyu mun kuma samu amsa iri d'ai daga garesu."

"Mey suka ce Ummi? Zan iya ajiye su duka?"

"Kai ma kasan hakan ba mey yiwuwa bane Prince."

"Innalillahi! Then mey suka ce? In rabu dasu duka?"

"Sunce ya zamo dole ka d'au d'aya ka saki d'aya."

"What? So kuke in za6i d'aya daga cikin Amal da Nazeefah?"

"Yes Afzal."

"Ta yaya Ummi? Taya kukeson in d'au d'aya in saki d'aya? Shin idan nayi hakan nayi adalc kenan?"

"Abinda yazo a shari'ance kenan, so sakan d'ayan su ya zamo dole idan har zakayi abinda addininka yace."

"No Ummi there has to be another way. Bazan iya za6an d'aya daga cikinsu ba I love them both yaushe ne zaku fahimci hakan? Is like choosing between air and lungs I can't because I need both to survive."

"Ya zama dole ka d'au d'aya acikinsu Afzal."

"No Ummi I can't!"

"Yes you have to, dubi nan" wayanta ta bud'e ta shiga kan sak'on da malaman suka turo musu bayan tambayan da sukayi inda ya shiga karancewa tun daga farko kaman haka;

arfrur
8442: Is it permissible to marry two sisters from one father at the same time?
A man has 2 wives and from each wife he has 1 daughter. Is it permitted for someone to marry the 2 daughters at one time (who of course have the same father but different mothers)? I am aware that it is not permitted to be married to 2 blood sisters at the same time, but is the case mentioned above slightly different?
Published Date: 2000-05-01
Praise be to Allaah.

It is not permissible to marry them at the same time, because they are sisters, regardless of whether they share the same father and mother, or they have only one parent in common, because of the aayah (interpretation of the meaning):

“Forbidden to you (for marriage) are: … two sisters in wedlock at the same time, except for what has already passed” [al-Nisaa’ 4:23]

It was reported from Abu Hurayrah that the Messenger of Allaah (peace and blessings of Allaah be upon him) forbade marrying a woman then her paternal aunt, or a paternal aunt then her brother’s daughter, a woman then her maternal aunt, or a maternal aunt then her sister’s daughter, or an older sister then the younger sister, or a younger sister then the older sister.” (Narrated by al-Tirmidhi, no. 1045; Abu Dawood, no. 1768. Al-Tirmidhi said, it is hasan saheeh).

Fayrooz al-Daylami said: I came to the Prophet (peace and blessings of Allaah be upon him) and said: O Messenger of Allaah, I have become Muslim and I am married to two sisters. The Messenger of Allaah (peace and blessings of Allaah be upon him) said: “Choose whichever of them you want [i.e., and divorce the other].” (Narrated by al-Tirmidhi, 1048; Abu Dawood, 1915, et al.)

_A hausance_
[Shin ya halatta namiji ya auri mata biyu wadanda suka kasance ubansu daya a lokaci daya?]

[Mutum ne ya kasance yana da mata biyu kuma daga kowacce mace yana da d'ya guda d'aya da ita. Shin ya halatta namiji ya auri yaran nan da suke uba d'aya a lokaci guda? ( wad'anda suka kasance ubansu guda amma kowacce da mahaifiyarta)?

Bai halatta namiji ya auri mata guda biyu da suka kasance yan'uwan juna ba maana yan'uwa na jini da ya kasance ubansu guda]
[Sai dai idan case din da aka ambata yasha banban da wannan ne?]

[Allah ne mafi sani]

[Ya haramta ga namiji ya auri mata biyu da suka kasance yan'uwan juna na jini koda kuwa uwa kawai suka had'a ko uba kawai suka had'a ko kuma uwarsu d'aya ubansu d'aya saboda fad'ar Allah madaukakin sarki a cikin Al-Qur'ani mai girma.]

[An haramta maku (game da aure) ka auri mata biyu yan'uwan juna na jini a lokaci guda, sai dai abinda ya riga ya wuce na baya.
(Suratun Nisaa'ee 4:23)]

[An kar6o daga Abu Hurayrah daga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace; an haramta ma namiji ya auri mace Sannan ya auri gwaggonta ta dangin uba, ko ya auri Gwaggon mace ta dangin uba sannan ya auri d'iyar k'ani/wanta.]

[Ko ya auri mace Sannan ya auri k'anwar innarta ta dangin uwa ko ya auri k'anwar inna sannan ya auri d'iyar K'anwa/yarta.]
[Ko ya auri Yaya Sannan ya dawo ya auri K'anwa.]
[(Al-Tirmidh N01045 da Abu Dawood N0 1678 ne suka ruwaito shi. Al-Tirmidh yace hadith ne mai kyau ingantacce)]

[Fayrooz Al-Dalaylami yace" Nazo wajen manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi sai nace "ya manzon Allah na musulunta amma kuma ina auren mata guda biyu yan'uwan juna na jini ( a lokacin daya auresu yana kafiri ne baisan hukuncin yin hakan ba) sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace; "ka za6i wadda tayi maka a cikinsu sai ka saki dayar"]

[Abu Dawood N0 1915, Al-Tirmidth 1048 da sauransu suka ruwaito shi.]

"Kaga anan tunda kaima a bisa rashin sani ka auri Nazeefah tukun kazo ka auri Amal, se Malamai sukayi amfani da wannan hadisi sukace kai ma zaka d'au d'aya ne ka saki d'aya tunda ba ba tare da sani ba ka auresu ba, da ace da gan-gan kayi hakan saboda son kai se ya zammana duka biyu sun haramta maka. Amma tunda ba da sani bane se aka baka za6i, kaga fa ba'a ce lalle se ka saki Amal ka zauna da Nazeefah ba saboda Nazeefah ce uwar gida, kuma ba'a ce lalle seka saki Nazeefah ka zauna da Amal ba saboda Amal ce babba. Za6i suka baka kaman yadda Annabin Rahama ya bawa wancan mutumin shima." Ummi ta sake yimar bayani.
Shiru yayi zaune a wajen yayinda zuciyansa yake yi masa wani irin k'una, ina ma ace ba a ta6a k'addaro masa da rana irin ta yau ba? Ina ma ace shi kam mutuwa kawai zeyi ya zamanto ba seya za6i Amal ko Nazeefah yabar d'aya daga cikinsu ba. Shin yanzu idan ya saki Amal yabar Nazeefah yayi wa Amal adalci kenan? Kokuwa idan ya saki Nazeefah yabar Amal yayi wa Nazeefah adalci? Wa ze d'auka wa kuma ze bari a cikinsu?

"I can't do this Ummi dan Allah karku tilasta mun" ya sanar da ita daga bisani.

"Kayi hak'uri Prince kowa yasan da zafi da ciwo amma dole ne muyi amfani da abinda shari'a ya kawo mana saboda gudun 6acin ran Ubangijin mu kuma kasani fa inna ma'al usri yusrah, kowani musiba na tare da sauk'i. Take for instance yanzu ace duka Amal da Nazeefan ne suka haramta maka ya zakayi? Amma seka duba privilege da addininka yayi maka na halatta maka d'aya acikinsu kayi godiya wa mahaliccinka."

"Hakane Ummi But wa zan d'auka wa zan bari?"

"This is not my decision to make Afzal, ka zauna kayi tunani in shaa Allahu zaka samu amsa ga wannan tambaya, idan kuwa hakan ya gagara se kayi istikhara, babu sharri acikin za6in Allah duk wacce tafi kwanciya maka a rai itace za6in ka seka ajiyeta ka sauwak'e wa d'ayar, ba wanda zeyi maka mumunar fahimta. Batun iyayen Amal kuma ka tabbata ka kirasu yau kokuwa kaje ka samesu ka sanar dasu halin da ake ciki hak'k'insu ne su sani, Allah shige ma gaba."

"Ameen" ya amsa da k'yar bakinsa yana rawa.

"Ni bari in koma se anjima" bayan ficewanta Afzal da kowani ga6a da sassan da suke jikinsa sun mutu sunyi lis ya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment