Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tarin albarka ba, yanzu haka tsegumin da al'uma keyi kenan da ma wasu masarautun ana cewa sarki ya karya doka ta hanyar zama da mace d'aya har na tsewon shekara goma sha biyar, shine muka ga ba zamuyi shiru ba al'umar gari su ci gaba da tsegumi akan masarautar nan ba tare da munyi yunk'urin dak'ile matsalar ba."

Shiru yayi kansa k'asa yana tunani akan abinda suka fad'a, tabbas gaskiya ne shi kanshi yana tunanin k'ara aure ko da zuciyarshi na son *Ameera* ne kad'ai, amma kuma ganin matsalar mata da ba'a rabasu da kishi musamman yanda suke k'azanta shi idan ance sun had'u gidan sarauta ko wani babban gida, shi shaida ne akan irin kishin da matan mahaifinshi keyi da mahaifiyarsu, duk da sun gamsu shine magajin sarki amma kuma suna bak'in ciki da hakan, kawunansu shi da yan uwanshi ba a had'e yake ba saboda yan ubanci, to wannan ne yake mishi shamaki da tunanin k'ara aure sai yaji yafi so yayi ta zama da Ameerarsa kuma sarauniyarsa, yana cikin tunanin abun fad'a musu liman yace "Ranka shi dad'e ba abu bane na ujila da muke buk'atar jin amsa daga bakinka yanzu yanzu, zamu koma mu, lokacin daka yanke shawara ma ji."

Waziri da sam maganar liman bata masa dad'i bane ya kalleshi, tsaki yayi a cikin zuciyarshi saboda takaici, shi fa burinshi yanzu bai wuce ace 'yarsa ta shigo gidan sarauta ba a matsayin matar sarki, kuma yayi sa'a *uwar d'aki* (mahaifiyar Imran) har yanzu bata son Ameera saboda ganin basu dace ba, shiyasa ma ta k'arfafa masa gwiwa kan su tuntub'e shi da maganar k'ara aure, ita ko ta mishi magana zai shawarci *takawa* (har yanzu suna kiran tsohon sarki da wannan sunan), kuma takawa zai bashi zab'i ne yayi idan yana so idan baya so ya bari, uwa uba kuma 'yar uwarshi Sameera kuma mai bashi shawara akan harkokin mulki dama na cikin gida, ita kanta zata zame musu matsala, dan hakane ya taho da liman dan su mishi magana saboda yana matuk'ar ganin girman liman saboda mutum ne da babu wanda yake shakka in banda ubangijinshi, zuwansu tare ne zaisa ya yarda da duk abinda suka fad'a ya kuma gamsu, muryar sarki ce ta dawo dashi daga duniyar tunani yana fad'in "Liman na yarda da bayaninku, amma duk da haka zanyi shawara, duk abinda na yanke zaku ji."

Da girmamawa liman ya amsa da "Allah ya shige mana gaba, Allah ya k'ara maka lafiya da nisan kwana."

Mik'ewa yayi yana fad'in "Mun barka lafiya ranka shi dad'e."

Mik'ewa waziri yayi yana bin bayan liman da harara, shi da ya so ayi komai a k'are yau d'in nan, amma gashi ya mishi shamaki da matsayin dake tunkaro shi, suna fita ya mik'e ya d'auki babbar alkyabarshi ya saka ba tare daya d'ora hular ta ba, cikin tako d'aid'ai ya tunkari k'ofar fita, yana isa k'ofar fadawa biyu ne tsaye suka sunkuya suna masa kirari, wucewa yayi suka take masa baya, duk da dare ya fara yi amma har yanzu ana kai da kawowa gidan, iya hangenka iya girman gidan, a haka ya isa b'angaren tsohon sarki wanda yanzu baya komai sai zaman gida da bawa mutanen gidan karatu, dan har yanzu jikinshi babu kyau tun rashin lafiyar daya kwanta sakamakon rashin sanin inda d'an uwanshi da yarshi suke, kamar yanda baya buk'atar k'yale k'yalen duniya hakan yasa ko mai gadin shiga k'ofar shi babu, Imran kuma dama kai tsaye yake shiga wajen mahaifin nashi, dan haka yanzu ma suna kawowa ya dakatar da fadawa shi kuma ya k'wank'wasa k'ofa, yaye labulen yayi dan tunda yaga k'ofar bud'e yasan zai iya shiga kai tsaye, zaune ya hango Musayyib ya tank'washe k'afafun shi da wani babban littafi a gabanshi yana karatu, yana ganinshi ya rufe littafin yana sakin murmushi da fad'in "Imaran kai ne yanzu? Zo zauna nan." Har Imran ya zauna shima yana murmushin, saida ya gama daidaita zama kamar yanda mahaifinshi yake kafin ya kalleshi yace "Ni ne Abba, Abba na karatu ake?"

Da murmushi ya amsa da "Kamar dai kullum."

"Allah ya k'ara maka lafiya Abba na, Allah ya k'ara maka nisan kwana."

Murmushi yayi sosai yace "Imaran, ko yanzu na mutu Alhamdulillah, na rabu da iyayena lafiya, nayi mulkin jama'a kuma na tabbatar ban bar hawaye a idon talakana ba sai wanda ubangiji bai bani ikon saninshi ba, ina zaune da ku lafiya, to ni kuwa me zan nema a wata doguwar rayuwar?"

Ba tare da murmushi ya bar fuskar Imran ba yace "Hakane Abba, ina fatan Allah yasa na kamalta mulki irin naka."

Shi ma da murmushin yace "Kana kamaltawa Imran, labari na zuwa min na duk abinda ke faruwa, sai dai fatan a gama lafiya a kuma tabbata a haka."

D'an kallonshi sarki yayi yace "Abba na magane ce dani a baki na, bansan ko kuna da lokacin da zan iya fad'a muku ba?"

"Imran ka d'auka lokacin nan nawa na kane, kai ba ma wannan ba kad'ai gaba d'aya lokacin daya rage min na sauran rayuwa ta."

Murmushi ya sake fad'ad'awa dan ko ba komai yana jin dad'in zamanshi tare da mahaifinshi, duk wata kalma da zata fito daga bakinshi mai dad'i ce, uwa uba ya kirashi da sunan Imaran, dan inba gabanshi ya zo ba baya jin wannan sunan, daga ranka shi dad'e sai mai martaba sai Allah ja zamaninka da sauransu, hakan yasa yake jin dad'i idan ya tuna a duniya akwai wanda ke kiranshi da Imran sak, dan ko mahaifiyarshi bata kiran sunanshi musamman daga lokacin da aka d'ora shi mulki zuwa yanzu, wani lokacin yana ji kamar tana sakaya sunanshi ne saboda ta tusawa abokan zamanta takaici, wani lokaci kuma kamar harda alfahari. Gyara zama yayi ya fara masa bayanin abinda su waziri suka fad'a mishi tare da cewa yana neman shawararshi.

Bud'ar bakin tsohon sarki cewa yayi "...

*Mu tara a shafi na gaba insha Allah, shin zai ce yayi aure ne ko kuma a'a? Wa ma za'a aura masa ne? Ya kuma zaman zai kasance?.*

โœ‹
29/05/2020 ร  11:19 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_6_

Kallonshi yayi yace "To, ban gane me kake nufi ba?"

"Yanzu zan fahimtar da kai Baba." Ya fad'a yana gyara zama sosai, ba tare da tsoron komai ba ko fargaba yace "Ni mutum ne daya yarda da tsafi, ina da wanda yake jib'antar al'amuran rayuwata (boka fa yake nufi), akwai wata babbar harka dana saka a gaba nake son ganin na cimma burina a kai, amma ya fad'a min komai zai tafi daidai da zaran na samu budurwa ina nemanta ta duburarta, ya kwatanta min kalar yarinyar dama fallasa min kamaninta, ina ganin yarinyar nan kuma na tabbatar ita ce, na fad'awa boka na kuma ya tabbatar min ita ce silar k'ara bunk'asar arzik'i na, amma komai zai tafi yanda ake so ne idan na fad'awa iyayenta komai da ita kanta yarinyar, dan ana buk'atar ku sani sannan ku amince d'ari bisa d'ari, wannan shine ya kawoni gareku, idan baku amince ba to ku sani kunyi asarar babbar dama, dan akan harkar nan a shirye nake dana kashe kud'i daga million d'aya har million hamsin, indai buk'ata zata biya."

Kawu Mamu da yana saurarenshi gumi ne ke keto mishi, a zuciyarshi addu'a yake su rabu lafiya dan ya fahimci k'aton matsafi ne, amma yana jin million ta fara magana saiya kalleshi da sauri ya goge zufar yace "Million hamsin fa kace d'an nan? Kuma zaka iya bada su?"

Wani shak'iyin murmushi yayi yace "Sosai ma, zan iya yin komai domin ganin na samu abinda nake so."

*Allah ka mana tsari da irin mutanen nan, kawu Mamu ma ba iyaye ne da zakayi alfahari dasu ba, ko ba 'yar daka haifa ba ace mutum ya fito gwaro gwaro ya fad'a maka k'udirinshi akan wani naka, ina ga sai inda k'arfin ka ya k'are, abun kamar a almara amma kuma ya faru, ana irin wannan tab'argaza me zai hana ubangiji yayi fushi damu har ya dinga jarabtarmu da masifu iri-iri, Allah mun tuba ba dan hallayenmu ba ka mana gafara, domin kuwa kai mai gafara da kuma jin-k'ai.*๐Ÿ‘

Cikin jin dad'i kawu Mamu yace "Wannan ai ba komai bane, dama ba ni na haifeta ba 'yar d'an uwa na ce, dan haka indai har zaka bayar da wannan kud'in to a shirye nake dana saka ta tayi maka duk abinda kake so, kuma dama ai yarinyar tana 'yan yawace yawacenta, kaga kuwa abun ba zai bata wahala ba."

Duk da hausar tashi da k'yar yake ganeta amma dai ya fuskanci abinda yake nufi, dan haka ya kalleshi yace "Ka amince kenan?"

Cikin sautinshi na fulatanci yace "K'warai kuwa Alhaji."

Jinjina kai yayi alamar gamsuwa tare da saka hannu cikin aljihu, wasu sababbin kud'i ya fito da su yan jaka goma goma ya dire mishi gabanshi yana fad'in "Ga wannan naka ne, ka fara rik'ewa kafin na sake dawowa."

Sake zura hannu yayi wani aljihun ya zaro wanda suka ninka waccen ya aje mishi yace "Wannan kuma a bawa yarinyar tayi buk'atunka, ta kuma tabbatar duk abinda zatayi zatayi shine dan gyaran jikinta saboda anfani na, ni zan tafi yanzu, zan dawo nan da sati d'aya lokacin nasan ta gama gyaran kanta."

Yana fad'a ya mik'e ya saka takalminshi, kawu Mamu da tuni hankalinshi ya tashi kud'in ya d'auka yana waiwayen bayanshi yana zubawa aljihu, ganin bai ma san me yake ciki ba yasa ya wuce kawai ya barshi, saida ya bud'e murfin motar ya juyo yace "Sunan yarinyar Zeituna ko(dan bokanshi ya fad'a mishi a daren jiya)?"

Cikin kid'imewa kawu Mamu yace "Eh Eh, sunanta kenan, Zeitu ba."

Shiga kawai yayi ya tayar ya wuce, kawu kuma cikin gidan ya shiga Jumma na ganinshi tace "Yanzu Baban *Jumare* a waje ka baro mana tabarmar salan wani ya d'auke?"

Da yatsa ya mata alama tayi shiru sannan ta biyoshi, bukkarshi suka shiga har saida ya sake labule kafin ya kalleta kamar marar gaskiya yace "Ke ba tabarma ba ki fad'i abinda kike so ma zan miki, zauna ki saurare ni kiji."

Zaunen tayi tana kallonshi da tambayoyi pal a ranta, nan fa ya kwashe komai ya fad'a, al'ajabi tare da jinjina rashin imanin mijinta ne suka rufeta, da mamaki ta kalleshi tace "Baban Jumare, yanzu kuma kai ka amince da nufin mutumin nan a kan 'yar d'an uwanka? Baka tsoron abinda mutane zasu fad'a? Sannan ba ka tunanin ma ko kasheta zasuyi? Haba ka duba lamarin nan mana."

Rufe ido yayi ya fara zazzaga mata bala'i wai 'yar d'an uwanshi ce ai, sannan kullum ita ke fad'a mishi Zeituna karuwanci take, to meye yanzu dan anzo har gida an nemi izininshi, ita dai hankalinta bai kwanta ba har saida yace "To wallahi idan ba zaki bani goyon baya ba sakinki zanyi, kinga dai yanzu ina da kud'i? Dan haka k'ara aure ba zai min wahala ba."

Sai lokacin kad'ai ta wayance ta nuna mishi ba komai kawai, kud'i ya tsakuro ya bata yace "Wannan kuje kusuwa ke da ita idan ta dawo ki siyo mata kaya masu kyau na kwalliya da ado, wannan kuma kema kya fara tab'awa." Ya fad'a yana d'auko jaka goma ya bata, ai sai taji kamar ya bata duniya, nan fa suka shiga bushasha da kud'i anata farin ciki.

*Misalin 08:07 na dare*

Tunda Hajia na gidan shiyasa yau Zeituna bata tsaya cikin gidan ba, tare da Iya suka fito kowa yayi hanyarshi, amma tana ganin Iya ta b'ace ma ganinta saita lab'e a cikin kwanar ta zauna anan, lieutenant kawai take so ta gani sannan ta wuce gida, duk motar da taji tayi oda a k'ofar gidan saita lek'o da sauri, amma sai taga wani ne daban ba shi ba, a k'alla ta d'auki minti kusan ashirin bai dawowa sai kawai ta yanke shawarar tafiya, dan bata so tayi dare irin na jiya na jawa kanta masifa, mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta kama hanya duk zuciyarta babu dad'i, da haka ta isa gida tana zuwa kuma mamaki kuma ya nemi halakata saboda Inna Jumma ce da kanta ta bata tuwo, inda kawu kuma har yake tambayarta ta k'oshi? Jumma ce tace "Tashi ki d'ibi ruwa kiyi wanka ki zo zaki rakani unguwa."

Da mamaki ta kalleta tace "Unguwa kuma Inna?"

"Eh." Tashi tayi tana mamakin canzawar mutanen, ta zauna tare da su na tsawon shekara goma sha biyu, amma abu makamancin wannan bai tab'a faruwa ba sai yau, to me suke nufi? Ta tambayi kanta, kar azo ko salwantar dake zasuyi ma dan su huta, wata zuciyar ta fad'a mata haka, da wannan wasi-wasi ta samu tayi wanka sai dai babu wani sabulu mai kyau, haka ta fito suka shirya suka fito, adaidaita suka samu ta kaisu kasuwa ta aje, kayan kanti ta siya mata saidai ba masu yawa ba, saboda tsadarsu yasa basu iya d'aukar dayawa ba, daga doguwar riga uku sai riga da siket biyu, kayan kwalliya ta siya mata aka had'a da sabulu da man goge baki da sabi takalma masu tsini, daga nan suka wuce gida Jumma na ji a ranta ita ma fa ta waye, alhalin duk kayan da ake siye babu wanda ake yayinshi yanzu duk tsofaffin yayi ne, amma a haka take ganin ita ma ta zama cikakkiyar yar birni.

Zeituna kasa bacci tayi da suka ce wannan kayanta ne, ta nemi tasan dalilinsu na canzawa amma kawu Mamu yace ai d'iyarshi ce ita ma, zai iya yi mata komai kamar yanda zai wa su Jumare, wanda a wannan lokacin Jumare dake kamar k'anwa ga Zeituna dan ta bata shekara uku haushi kamar zai kasheta, har d'aki ta samu Jumma tana kuka wai an yiwa Zeituna siyayya ita ba'a mata ba, nan ta bata hak'uri tace ita ma gobe zata amshi kud'i wurin babanta a siyo mata, da haka kad'ai tayi shiru ta koma d'akin su, haka tayita hattarar Zeituna tana zaginta tana harara tana mata cilli da kayan da aka siyo, saida kawu Mamu ya mata magana daga cikin bukkarshi yace zai ci uwata kad'ai ta shafa mata lafiya.

โžก๏ธโžก๏ธโžก๏ธโžก๏ธโžก๏ธโžก๏ธโžก๏ธ

Ko da Junaid ya zo gida shiryawa yayi ya sake fita, bai zame ko ina ba sai gidansu Maryama, yana zuwa kuma sun fita ba jimawa, amma yayi nasarar ganin Huda a k'ofar gida da madara tana sha, hannunta ya kama yace "Huda ko?"

Kai kawai ta d'aga mishi, murmushi yayi yace "Ina mamanki?"

Saida ta kalli hanyar dasu Maryama sukayi tace "Yanzu suka fita ita da tanti Iklima."

Nuna hanyar yayi yace "Kenan ta nan suka bi?"

"Eh." Ta fad'a tana sake d'aga mishi kai, mik'ewa yayi yasa hannu aljihu ya ciro jaka goma guda ya damk'a mata a hannu yace "Wannan kisha madara kinji ko."

Da sauri ta fizge hannunta ta sakar masa kud'in tace "A'a bana so, Mamata ta hanani karb'ar kud'in maza."

Da mamaki yace "To me yasa?"

Tana kallon idonshi tace "Tace wai ita zatayi aiki dan ta samo min komai da nake so."

Murmushi ya sakeyi ya k'ara mik'o mata kud'in yace "To ki karb'i wannan, ni bana cikin wanda ta hanaki karb'an kud'in su saboda ni mahaifinki ne."

Zaro ido tayi tace "Kaiii, ni fa bana da Baba, mutane ma ce min suke shegiya, kuma suna cewa mamata yar iska ce."

Jim yayi saboda rashin jin dad'in abinda ya fito daga bakin yarinyar, murmushin yak'e ya mata yace "To yanzu dai karb'i wannan, insha Allahu lokaci yayi da zaki ga mahaifinki kema."

Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, idan na amsa Mama zata toye min hannu na da wuta."

Lura da yayi ba zata karb'a ba yasa yace "To shikenan, yanzu fad'a min me kike so na siyo miki idan zan dawo."

Rufe baki tayi tsoro ya bayyana a tare da ita tace "Dan Allah karka fad'awa Mama na nayi hira da kai, ta hanani tsayawa da maza a waje."

Tana gama fad'a ta ruga a guje tayi cikin gidan, da kallo ya bita shi kuma yana mamakin yanda Maryama ke tsaye kan tarbiyyar 'yarta, amma kuma ita tana zubarwa da yarinyar mutumci, motarshi ta shiga ya nufi inda yasan zai ganta, bai kuwa sha wahala ba ya samu Iklima zaune bakin wani dakali a pacific tare da wani, fitowa yayi suka gaisa ya tambayeta ina Maryama? D'akin dake bayansu ta nuna mishi tace "Tana ciki, amma tana fitowa yanzu."

Kallon d'akin yayi yaji zuciyarshi na neman bugawa, ji yayi kamar ya tura k'ofar ya shiga, amma kuma tsoron abinda zai gani yasa ya kasa hakan, tsayuwarshi kuma ya jirata shi ma dai wani k'arin tension d'in ne, juyawa yayi ya bud'a mota zai shiga sai yaji an fito daga d'akin, juyowa yayi sai kuwa suka had'a ido, sam bata cikin yanayin farin ciki dan fuskarta a had'e take, bayanta wani matashin yaro ne ya fito da ba zai wuce shekara ashirin da d'aya zuwa da biyu ba, Maryama kuma a k'alla ba a k'asara ba tana da shekara ashirin da shida zuwa da bakwai, zai iya kiranta warin k'anwar shi Umaima, wani buhun haushi ne ya rufe shi ya tsaya yana kallonta harta k'araso kusa da Iklima, wannan matashin kam sai wasar baki yake ya bawa d'aya abokin na shi hannu yace "Saura kai, amma ba zan jira ka ba gaskiya."

Mik'ewa shi ma yayi ya shiga d'akin sai Iklima data juyo ta kalli Junaid tace "Yallab'ai Junaid sai anjima."

D'akin ta shiga yana kallo suka rufe, zaune Maryama tayi bakin dakalin ita ma dan jiran Iklima, shi kuma waccen matashin ya wuce Junaid ya bishi da kallo kamar ya shak'e shi, amma ya zaiyi duk abinda ya samu shamuwa watan bakwai ne ya ja mata, kallonta yake kamar zai had'e ta ita kuma ta had'e fuska tana danna wayarta, rufe murfin motar yayi ya tako ya zo gabanta, cikin wani yanayi yace "Yanzu dan Allah Maryama baki ji kunya ba?"

A hankali ta d'ago kai ta kalleshi tace "Kunya kuma? Ta me fa?"

Girgiza kai yayi yace "Maryama me waccen yaron zai miki? Idan dan kud'i kike siyar da mutumcinki na baki kud'i Maryama dan ki tsira daga rainin irin wannan yaran, idan kuma dan jin dad'i kike bud'a farjinki ga kowane d'a namiji, domin Allah me waccen zai iya yi miki? Me zai hana ki nemi cikakken namiji wanda zaki san ya shige ki har ma ya sakaki kukan dad'i ko na wahala, amma waccen da ko kaciyarshi bata gama warkewa ba tsiyar me zai tsinana miki? Ni fa da aure nake sonki, Maryama dan Allah ki taimaka ki aure ni ko na kwana d'aya ne, ni kuma zanyi k'ok'ari na ga na gamsar dake ta kowane fanni har ki yarda ki zauna dani, amma wannan abun kunya dame yayi kama, yaron da na tabbatar kud'in daya biyaki shi kanshi k'uru ce yayi ya baki su saboda shed'an na k'awata mishi yin zinar, mtssss."

Duk da ba cikin hargagi yake maganar ba amma ta tabbatar ranshi ne ya b'ace, mik'ewa tayi ita ma cikin b'acin rai da fitar da hawaye a idonta tasa hannunta ta fito da kud'i a rigar nononta ta warware su, jaka biyu ce nuna mishi tayi tana fad'in "Kaga abinda ya bani, wannan kuma zan ci abinci da su na tsawon kwana uku ni da 'yata, malam ka fita a harka ta mana, soyayya ce nace banayi ka shafa min lafiya mana, ko ana so dole ne?"

Sai kuma ta fashe da kuka ta koma ta zauna kamar an turata, cikin kuka ba tare data kalleshi ba take fad'in "Taya kake tunanin zan ji dad'in rayuwata? Taya kake tunanin ina farin ciki da abinda ke faruwa da ni? Waccen yaron fa bai fi sa'an k'ane na ba na biyu, amma yau ni ce na kwanta yaron can ya nemi yanda yake so, meye anfanin rayuwa ta Junaid? Me yasa iyayena zasuyi min haka? Me yasa wannan mutumin da ko sunanshi ban sani ba ya tafi ya bar ni da 'yarsa? Me ya kamata nayi yanzu? Junaid ka fahimci wani abu, duniya yanzu ba'a taimako dan Allah sai dan abinda zaka bayar ko za'a samu daga gareka, da irin hakane aka lalata min rayuwata, kuma da hakanne ma yanzu ake ci gaba da gurb'ata min rayuwar."

A hankali ya zauna akan dakalin cikin sanyin jiki ya kalleta yace "Maryama rayuwarki na da anfani, kuma tabbas yanzun rayuwarki a gurb'ace take, amma idan har kin so canzawa kuma kika bani dama wallahi zaki dawo sabuwar mace kamar babu abinda ya tab'a faruwa dake, dan Allah Maryama ki amince da soyayya da nake miki, wallahi babu nufin cutarwa ko sharri a zuciyata, ni zan zama miji na gari a gareki, sannan zan zama uba da za ayi alfahari da shi ga 'yarki Huda, ki amince ki bani linzamin ragamar rayuwarki, zan d'aukeki na kaiki cikin ahalina kuma farin cikina, kema zaki zama d'aya daga cikin dangina."

Shiru tayi sai yar shashek'ar kuka da take tana tunanin abinyi, tabbas tun zuwanta garin nan a cikin manya manyan mutanen da take jin labarinsu a gari akwai ahalin Gaga, wanda suke ji da iko, matsayi, da kuma naira, ahali ne daya tara yan boko sosai kuma bokon ta musu rana, matsalarta d'aya shine tana jin tsoron shiga cikin babban dangin irin wannan saboda abinda ka iya zuwa ya dawo, tana cikin wannan tunanin Iklima suka fito suma, saurayin wucewa yayi inda Iklima ta kallesu tace "Mari kina nan dama? Ai na d'auka kin tafi da naga mutumin na ki ya zo."

Mik'ewa tayi tana k'ara share hawaye tace "Mu tafi kawai."

Wucewa tayi ita kuma zata wuce Junaid yace "Iklima dan Allah zan iya sanin labarin Maryama? Dan na fahimci abun na damunta kuma kamar tana yi ne ba da son ranta ba."

Rik'e hab'a tayi tace "๐Ÿค” Ni! Rufa min asiri, wallahi ba zan iya fad'a maka komai ba a game da ita har saita bani izini."

Kallonta yayi yace "Bima'ana dai kinsai komai?"

"K'warai kuwa na sani."

Saida ya kalli Maryama dake tafiya ko d'an kwali babu a kai sai riga da siket d'in ta na atamfa ko waiwaye babu yace "To dan Allah inhar ke masoyiyarta ce ta gaskiya ki fad'a min asalin Maryam, ma'ana garinsu, iyayenta, inda da inda suke zaune, idan kika min haka kin gama biyana a rayuwa, ni kuma zan tabbatar na gyara rayuwar k'awar ki da yardar Allah."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ina k'aunar Mari, kuma ina sonta da shiriya kamar yanda nake so wa kaina, ni labari na bai kai na ta muni ba, dan ni na fito ne da son raina, hasalima ina gari d'aya da iyayena, amma ita na ta labarin akwai tausayi ciki, kuma sau da dama ina cewa ta sake komawa gida, watak'ila mahaifiyarta ta yafe mata, amma sam bata saurare na saboda tayi hushi ita, dan haka zan fad'a maka komai daya shafeta ko da hakan na nufin zamu samu matsala, nasan daga baya zata fahimce ni kuma ta yafe min."

*Bara muji tarihin Mari.*

Nuna mishi dakalin tayi tace su zauna, bayan sun zauna ta saita nutsuwarta tace "Maryama 'yar asalin garin *Gourรฉ* ce dake yankin *Diffa*, tana rayuwa kamar kowa ita ma tare da iyayenta, ita kad'ai suka haifa a duniya, dan haka suke matuk'ar sonta musamman mahaifinta, tana samun duk wani abu da take so a duniyar nan, mahaifinta na nuna mata gata duk da cewa ba mai k'arfi bane, tana karatunta na islamiyya da boko, suna tsaka da rayuwarsu cikin farin ciki wata rana mahaifinta yayi had'ari da moto, munanan raunikan daya samu ne suka jaza mishi kwanciya jinya na tsawon shekara biyu kwance a gida, k'afafun shi basa takuwa haka ma ko zama baya iya wa sai kwanci, wannan rashin lafiyar tashi ita ta jijjiga Mari da mahaifiyarta, ta kai ta kawo sun cinye duk wani abu da suke da shi, yan uwa kuma babu mai k'arfin da zai iya d'auke

Please Login or Register in order to submit comment