Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_18_


"Ni sunana Alhaji Suleymane Gaga, wannan kuma babban d'ana kenan mai sunan mahaifina, *Hassan*, amma ina kiranshi da babba, a gidana 'yer d'an uwanka Zeituna take aiki, kuma mun zo ne akan maganarta yanzu haka."

Kallonsu yayi dukansu kafin yace "Alhaji kace manyan bak'i ne ku? Ai duk garin nan babu wanda baisan da zamanku ba, Gaga, Gaga, ai suna ne daya zaga ko ina a fad'in garin nan dama kewayenshi, sai dai kuma kun saka zuciyata cikin rud'u jin kunce kun zo akan maganar Zeituna, dan Allah idan laifi tayi ku dubi Allah ku yafe mana, karku ce zakuyi shara'a damu ko kuma ku rufe ni, ita da tayi laifin can ku hukuntata saboda yar banzar yarinya ce bata jin magana."

Lieutenant da bai fahimci komai ba kallon mamaki yake wa tsohon (dan kuwa ba zaka kirashi da dattijo ba), ance yar d'an uwanka, amma ka ce ita a hukunta ta kai a rabu da ka, to wane irin rik'o kake wa yarinyar? Alhaji ne yayi murmushi wanda shi jin haka bai dame shi ba idan aka kwatanta da abinda yake shirin aikatawa, cikin lumana yace "Ko d'aya, babu laifin data aikata, mun dai zo neman aurenta ne idan har za'a bamu."

Zabura yayi yana fad'in "Me? Aurenta? Zeitunar? Ku kuwa me kuka gani a jikinta da har zaku zo neman aurenta alhalin kuna manyan mutane haka kuma masu kud'i, wai ko dai ba Gagan da nake ji ana fad'a ba har a redio mai masana'antu da dama?"

Wani murmushin dattako yayi yace "Ni ne da kaina, idan kuma kana son k'arin haske saina maka dalla dalla yanda zaka fahimta."

Shi fa a saninshi yayanshi duk masu mulki da iko ne, ni kam ina zance ya min dalla dalla nasan ko da sojan cikinsu zai had'a ni, dan haka kawu Mamu yace "A'a Alhaji, ina dai mamaki ne, amma to wa yake son Zeituna da har ka zo neman mishi aurenta?"

Jim Alhaji yayi ya d'an sauke wata sanyayyar ajiyar zuciya ya kalli lieutenant dake kallon bakin Alhaji yaji wa zai nemawa auren wannan k'azamar yarinyar, kallon kawu Mamu Alhaji yayi ya nuna lieutenant yace " *babban d'ana* Hassan."

A tsorace lieutenant yace "Me? Ni kuma?"

Wani kallon karka mayar da ni k'aramin mutum Alhaji ya mishi kafin ya kalli kawu Mamu dake shima yake kallon lieutenant yace "Karka damu, bai d'auka abinda zan fad'a ba kenan."

Kawu Mamu kuma shi sam shekaru ko yayan mutumin ba shine a gabanshi indai har zai samu kud'i, to amma matsalar su aure ne ya kawosu bare yayi tsammanin samun kud'i dayawa daga garesu da suka zarce na Jano, dan haka kawai sai yace "A gaskiya Alhaji ba zai yiwu ba, domin kuwa Zeituna na mata miji, aure zan mata."

Murmushi Alhaji yayi yana mishi kallon babu abinda ban sani ba yace "Na sani, amma a labarin dana samu mutumin da zaka had'a ta dashi ba mutumin kirki bane, shiyasa ma na gabatar da d'ana dan shine ya dace da ita, tana son shi, shi ma kuma yana sonta, sab'anin waccen had'in da zakayi babu soyayya a cikinshi."

Kawu Mamu da wannan karan kwarjinin Alhaji ne ya hana shi kallon idonshi, zufa ya ji ta fara tsatsafo mishi saboda tsoro da fad'uwar da gabanshi keyi, ganin yayi shiru yasa Alhaji cewa "Karka damu, ka fad'a mana duk abinda waccen ya biya ni zan ninka maka shi, sannan ka tsaga wa Zeituna sadakinta, a take anan zan biyashi."

Da k'arfi ya kalleshi yana d'an nazartarshi, wata zuciyar ce ta nuna mishi karya saki reshe ya kama ganye, inda wata zuciyar ke nuna mishi ai ba k'ananan mutane bane, dan haka kamar sub'utar baki sai kuwa yace "Da gaske zaku biya ko nawa ne?"

Lieutenant da yaji wata tambayar sakarci kallonshi yayi yace "A cikin mu nan akwai k'aramin yaro ne da za'a zauna ana maka karya? Ka fad'a kaga aiki da cikawa mana."

Saida gaban kawu Mamu ya fad'i dan yanda ya mishi magana babu alamar arzik'i a ciki, Alhaji ya kalli yace "Shin zaku iya biyan waccen mutumin kud'in shi jaka d'ai-d'aya har jaka d'ari biyu?"

Alhaji ne ya kalli lieutenant wanda ya d'auka ko shi zai biya kud'in, hannu yasa aljihu da niyyar fito da kud'in daya d'auko saboda baisan ina zasu zo ba Alhaji ya dakatar da shi ta hanyar fito da kud'i daga aljihunshi ya aje gaban kawu Mamu yana fad'in "Wannan jaka d'ari biyar ne, ka biya mutumin kud'in shi da duk wani abu da kasan ya wa yarinyar ko kuma kai, saura sadakinta?"

Kawu Mamu jikinshi ne ya fara rawa hannayenshi na kakkarwa wajen d'aukar kud'in, mamaki yake ace masu kud'i basu d'auki kud'i a bakin komai ba, wai har riga rigan fito da kud'in suke ma, kenan kowanensu ya bawa jaka d'ari biyar baya? Ya d'auki kud'in yana ta zanzarin ya saka aljihu yaji Alhaji yace "Ka yanka mata sadaki mu biya."

Kallonshi yayi duk ya rud'e yace "Alhaji ko nawa ma ku kawo, ai ku manyan mutane ne, Zeituna ta zama taku halak malak."

Murmushi Alhaji yayi yace "Ka fad'a min sadakinta kawai na biya, domin kuwa akwai sharud'an da nake son gindaya maka bayan hakan daga yanzu har zuwa lokacin da amarya zata zama k'ark'sashin ikon d'ana."

Da sauri lieutenant ya kalle shi, wai da gaske Alhaji yake aure zai mishi? To shi kuma meyasa duk yaran gidan nan sai shi Alhaji ya zab'a? Me zaiyi da wani aure yanzu? Auren kuma ma da budurwa wacce bata wuce sa'ar 'ya'yan dana rik'e a hannu na ba (Hamna, Amna)? Meyasa Alhaji zaiyi haka ba tare da shawara ta ba? Auren farko na mahaifiya, aure na biyu kuma na mahaifi, d'an kawar da kallonshi yayi a zuciyarshi ya furta "Ya Allah."

Kawu Mamu ne yace "Alhaji zaka iya biyan sadakin Zeituna?"

Kallonshi yayi yace "Saurara kaji, idan ka zana sadakinta ba wai yana nufin kai zakayi komai ba, mijinta nan da kanshi ne zai mata kayan d'aki da lefe da duk wani abunda ake wa kowace 'ya 'yar gata, dan haka sadakinta da zaka fad'a yanzu inhar zaka bi kamar yanda addini ya tsara ne, to fa zaka bawa yarinya kayanta ta mora kamar yanda ita ce da zaman auren ba kai ba, idan kuma zakayi yanda muka saba ne a al'adance, to shine zaka cinye ba tare da yarinyar ta gani ba, amma duk da haka karka manta wani abu, Zeituna zata shiga gidan da million dubu ma tafi k'arfin ta bare tsirarun kud'in sadakinta."

A wannan karan kam yanda yaga shi kanshi Alhaji yayi magana sai al'amarin ya fara bashi tsoro, dan haka cikin rawar baki yace "Kawai ku bada jaka d'ari ma."

Wani murmushi Alhaji yayi na takaicin abinda kawu Mamu ya fad'a, dan shi ya zo ne ya nuna mishi gaba da gabanta, ya so ya yanko kud'in da shi a ganinshi ya fad'i k'arshen kud'i shi kuma saiya ninka mishi, ba dan komai ba sai dan yasan darajar 'yar da kuma bin dokokin da zai gindaya masa, hannu yasa aljihu duka rigarshi ya fito da kud'i da suka fi na d'azu, aje mishi yayi gabanshi yace "Ka rik'e wannan sadakin Zeituna nena biya lakadan ba ajalan ba, ka saka mana ranar da zaka d'aura aure mu zo mu d'auki surukata, tsinke bana buk'ata daga gareka."

Kawu Mamu fashewa yayi da kuka yana kallon kud'in yace "Alhaji, yanzu wannan kud'in nawa haka? Wannan ai ba zan iya irgasu ba, kona fara ba zan gama ba sai na kai shekara guda."

Murmushi Alhaji yayi yace "Million d'aya da rabi ne, a hakan ma dan ka fad'i kad'an ne, na so na biya sadakin da zai zautar da kai ko ka shiga hankalinka, ka gane cewa 'ya'ya da Allah yake bamu ba dan mu wulak'antar da rayuwarsu bane musamman akan kud'i."

Sam kawu Mamu hankalinshi bai kai ga tunanin abinda Alhaji ya fad'a masa ba, Alhaji ne yace "Yaushe ka saka ranar d'aurin auren?"

Lieutenant ne ya mishi kallon mahaifina ka ceceni mana, kamar zaka gurgunta rayuwata ne fa, Alhaji kuma bai kula shi ba sai kawu da yace "Kawai ku zab'i ranar data muku sai a d'aura auren."

Alhaji kuma dake son gaggawar d'auke Zeituna daga hannunshi ne yace "Idan na ce maka ranar juma'ar nan ban takura ka ba?"

Kallonshi kawu Mamu yayi ya d'an fara lissafi kafin yace "Nan da kwana uku kenan?"

Kai ya jinjina mishi dan haka yace "Ai kawai babu wata damuwa, babu takura ko kad'an, gobe ma da kaina zanje duk rugagenmu na sanar da sauran dangi dan su zo a shafa da su."

Alhaji ne yace "Abu biyu zuwa uku nake son fad'a maka, daga yanzu har zuwa lokacin da Zeituna zata bar gidan nan ban yarda ta sake zuwa aiki ba, sannan daga yanzu bana so aiki ko na gidanka ne tayi komai k'ank'antar shi, sannan kada ta zama cikin takura ko matsi har lokacin da za'a d'aura auren nan, idan ka kiyaye wannan sai mu zauna lafiya da kai, ina fatan ka fahimta?"

Mik'ewa Alhaji yayi lieutenant ma haka suka nufi mota kawu Mamu na fad'in ai za'a kiyaye, da haka suka shiga mota suka sake d'aukar hanyar komawa gida, sai lokacin ne Alhaji ya kalli lieutenant yace "Babba, nasan kana cike da mamakin abinda na aikata ko, kuma kana son sanin dalilin da yasa na aikata hakan, yarinyar nan tana cikin wani hali a gidan kawun nan nata, sam ba mutumin kirki bane tunda har zai iya karb'ar kud'i a hannun wani mutum ba dan ya aureta ba sai dan ya dinga lalata da ita ta duburarta, uk'ubar da suke saka yarinyar ma kad'ai bai isa ba shine harda neman ruguza rayuwarta, dalilin haka ta fara tunanin barin garin nan ko zata ji dad'i a ranta, domin kuwa ta kamu da son wani da bai ma san tana yi ba, ni kuma ina jin haka shiyasa nayi gaggawar d'aukar mataki tun kafin ta shiga uwa duniya."

Jinjina kai lieutenant yayi yace "Kayi daidai Abba, amma maimakon ka had'a ta dani ai da wanda take so d'in ka had'a ta da shi, zata fi farin ciki a hakan amma bani ba, Abba na mata tsufa dayawa, ina da matata da yarana, bana da tunani ko niyyar k'ara aure, yarinyar! Abba a duba k'uruciyarta, kada a tauye ta saboda bata da gata."

Kallonshi Alhaji yayi yace "Dan kana da mata da yara sai akace ba zaka k'ara aure ba? Ko kuma dan kai babu burin yin hakan a ranka sai kuma ubangiji ya barka haka? Duk kunbi kun d'orawa kanku rayuwar turawa saboda kawai kunsha boko kun k'oshi, Allah ya hore muku abinda zaku zauna da mace hud'u amma kuna mak'ale a mata d'aya d'aya, to ban lamunta , wannan karan k'addararka ta zo maka da sake k'ara aure bayan ka fara girma, kuma ta hanuna wannan k'addarar ta jefo auren naka, kayi na farko saboda uwarka, yanzu zakayi na biyu saboda ni ubanka, idan kuma ban isa ba na gani, wallahi ba kai ba har uwarku da kuka ga ina zubawa ido wannan karan sai mu samu matsala da ita akan auren nan."

Lieutenant da gabanshi ke dukan uku uku yake takaicin musawa mahaifin nashi wanda sanadiyar haka yau gashi yana kallon fad'an shi da abune mai matuk'ar wuya ganin hakan tare da shi, cikin girmamawa yace "Dan Allah Abba kayi hak'uri ka gafarce ni, wallahi bana da tunanin bijirewa buk'atar ka, kawai yarinyar ce na duba, amma kayi hak'uri insha Allah ba zan baka kunya ba."

Shiru Alhaji yayi ya kawar da kanshi suka ci gaba da tafiya, saida suka kusa daf da gidan ya juyo a nutse yace "Shin ka ma san yarinyar nan wa take so? Kasan waye ta jima tana dakon soyayyarshi a zuciyarta?"

Kai ya girgiza shi kuma yace "Kai ne, kai ne wanda take so, kai ne kad'ai mutumin da zata iya zaman aure dashi tayi farin ciki, da kunne na naji tana fad'in haka wanda maganar daga zuciyarta take fitowa, babba kayi hak'uri idan na takura ka, sannan ka min biyayya ta hanyar nuna wa yarinyar nan soyayya da gata, zan so ace ta manta da maraicinta, ku har yanzu baku san meye maraici ba, baku d'and'an d'acin dake cikin maraici ba dan haka ba zaku fahimta ba har sai ranar da kuka wayi gari kuka ga bama raye a doron duniya, amma ina baka tabbaci akan yarinyar nan zakayi alfaharin wannan had'in dana maka." Jinjina kai yayi alamar gamsuwa a haka suka ci gaba da tafiya sannu sannu har suka iso gidan.

*Tunda* Jibril ya je mayanka bai dawo ba saida tik'ek'en sa wanda Huda ta zayyana masa kamaninshi, a babbar mota aka saka shi wacce samanta ke bud'e shi kuma yana gaba dan jagorantarsu, suna zuwa har k'ofar gidan ya samu yaro ya aika yace a kira Mari, ta so fitowa da Huda amma tana can yau ta samu kayan mak'ulashe ko takan uwar bata bi ba, tana fitowa ta ganshi suka sake ido hud'u hud'u, rumgume hannayenta tayi a k'irji ta kalli san dake bayansu ta kalle shi tace "Sai gashi bayan shekara bakwai mun sake had'uwa, bawan Allah mena maka a rayuwa daka tarwatsa min tawa rayuwar? Laifin me na aikata maka daka zab'i hukunta ni ta hanyar raba ni da iyaye na? Kuskuren mane aikata a kanka daka gwammaci ka rama ta hanyar yi min ciki na haifi yarinyar da ake kiranta da shegiya? Meyasa? Ko fa saninka banyi ba a waccen ranar, amma ka kasa tuna komai ka zalince ni sannan ka tafiyarka ka barni da abun kunya, kai wane irin marar imani ne?"

Tunda ta fara magana yayi k'asa da kanshi yana k'ok'arin b'oye hawayenshi, saida ta gama ya kalle ta yace "Kiyi hak'uri Ma..."

Bata bari ya k'arasa ba ta gaure shi da Mari a gaban mutanen dake jiranshi ya fad'a musu yanda zasuyi da san nan, ko dafe kunci baiyi ba bai kuma nuna abun ya dame shi ba, dan yasan ya cancanci fiye da haka ma a wurin ta, cikin shak'ewar muryar da tasha kuka tace "Kai har kana da bakin da zaka bud'a ka bani hak'uri? To bari kaji da kyau, wallahi ba son auren d'an uwanka nake ba, amma zan aure shi saboda kai sannan na shiga da 'yata gidan ubanta, abinda zan fad'a maka kawai shine kada ka yarda wani ko wata ace za'a gorantawa 'yata cewa ita agola ce ko shegiya, wallahi duk wanda ya fad'i haka saina tona maka asiri, wannan shine dama, ka b'ace daga k'ofar gidan nan."

Zata wuce ya tare gabanta yace "Dan Allah Mari ki saurare ni."

Kallon da take masa kamar zata ci namansa d'anye dan haka yace "Ki dake ni mana idan hakan zai saki ki huce laifin dana miki, amma ina rok'onki ki bani dama na fara cikawa 'yata burinta ta hanyar yanka mata waccen sa a sake zana mata suna, ina so masu mata gorin ba'a yanka mata ragon suna ba su san 'yar gata ce ita ma."

Wani kallon mamaki ta masa tace "Gata? Yar gata fa kace? Shin kasan wahalar da nasha da ita kanta Huda?"

Had'e hannayenshi yayi yace "Dan Allah fa nace Mari, na rok'eki ki amince na faranta mata rai."

Tab'e baki tayi tace "Ka amince da abinda na fad'a maka cewa ban yarda kowa ya zagar min 'ya ba? Sannan ka yarda zan je da ita gidanku ba'a matsayin agola ba?"

Da sauri yace "Na amince Mari, babu ma wanda zai goranta mata."

Sake tab'e baki tayi tace "Shikenan, sai kayi abinda ya dace."

Juyawa tayi ta shiga ciki shi kuma yace yaran su d'an jira kad'an, yana rufe baki kuma sai kiran sallah la'asar, dan haka sukayi alwala suka shiga masallaci, ana idar da sallah yace akwai zanen suna na Huda wanda ba ayi ba a baya, nan fa aka sake rad'in suna kowa ya sake shaidawa ya bayar da kud'i aka siyo carton d'in alawa aka raba, wannan gabjejen San aka kayar aka yanka shi, daga nan shi kuma yace ya gama nashi burinshi yaga an zubar da jinin dama, nan fa nama aka dinga wadak'a da shi sai gashi har masu goranta mata sun manta suna wawasar nama ana sadaka, Iklima kam a tsakar gidan su habaici da zagi babu irin wanda bata aikawa matan gidan ba banda Mamar Husna, ana tsaka da haka motar da zata d'auki su Mari ta zo, ai kuwa Iklima tace k'afar ta k'afar Mari, tare suka d'auki hanya da Huda sai fatan sauka lafiya.

*Bayan* fitarsu Alhaji ba jimawa Ammar ya shigo gidan har falon Hajia, wannan karan Ummy ce zaune da yan biyunta sun sakata tsakiya, amma daga wacce faranti ke kan k'afafun ta tana ta gwaigwayar kankana ma zaka fahimta, Hamna na gashinshi ta zabura ta aje farantin zata haura d'akin su, da k'arfi Ummy ta jawota ta zaunar da ita tace "Haukan banza, sau nawa zan ce miki ke ba yarinya bace ki daina sarar gudun nan."

Ganin yayi tsaye yana mata wani kallo yasa Ummy had'e rai tace "Kai kuma lafiya? Meye ka wani tsaya mana a gaba haka?"

Kallon Amna yayi yace "D'auki kisha." Girgiza kai tayi alamar toh ta sunkuya ta d'auki farantin da yer uwarta ta aje tasa kankanar gaba ta fara sha ba dan ranta na so ba, dan ita ko warinta bata cika so ba amma haka ta ke sha, Ummy ce ta kalleta tace "Ke da baki shan kankana shine zaki sha ki takura kanki, mtsss wallahi abun haushi baya k'are muku."

Kallon Ummy yayi ya kalli kankana dake bayanta sai k'ara b'oyewa take ya matso, hannu ya kai zai kama kunnenta Ummy ta buge hannun tana fad'in "Wallahi ubanka zan ci idan ka tab'a min 'ya, wai kanka d'aya kuwa."

Sake had'e rai yayi cikin jin zafin zagin data masa yace "Ki bari ki ga me zanyi, tarbiyar da kuka kasa mata ce zanyi mata."

Da k'arfi tace "Tarbiyya? Kai tarbiyyar ce da kai da har zaka wa wani? Dallah malam fitar min anan wurin kafin ranka ya b'ace."

K'asa yayi da hannunshi kamar zai kama kunnen Hamna hakan yasa Ummy yin k'asa da sauri da niyyar rik'e hannun, cikin azama ya saka d'aya hannu ta sama ya kama kunnenta ya murd'e, wata uwar k'ara ta saki a kunnen Ummy ta fashe da kuka tana k'amk'ame ta, k'ok'arin yakice hannun ta fara yi amma ina ta kasa, shi kuma Hamna data bud'e bakin nan yayi nasarar buga mata hannu dole tayi shiru ta rufe bakin da hannaye yana fad'in "Wallahi kashedi na k'arshe zan miki, idan kika yarda kika sake fita daga gidan nan babu hijabi sai na ci k'undun ubanki, kuma wallahi tun a inda na had'u dake zan fara bugaki har cikin gidan nan, tunda dai ba kya jin magana ke, munafuka kawai."

Sakinta yayi ya juya ya bar d'akin Ummy ta bishi da bala'i amma ko a jikinshi, da fitarshi kuma sai ga colonel ya iso har cikin gidan yan rakiyarshi suka shiga, saida zai shiga d'aki ya dakatar da su ya shigo ciki, saida ya gaisa da mutane sosai da yara kafin ya shiga dan yin wanka.

Ya gama wanka ya saka dogon wando da singlet zai saka riga Zeinabu sarkin tsegumi tace "Amma dai kasan duk cikin sabgar nan da za ayi mu akafi cuta ko?"

Da mamaki ya juyo ya kalleta ya dakata da saka rigar yace "Me? Cuta fa kika ce? Cutar me aka mana?"

Zaune tayi bakin gado tana fad'in "To kayi tunani mana ka gani, mu fa yara uku zamu aurar lokaci d'aya, kuma biyu daga ciki mata ne, ka kuma san auren mata yafi na maza kashin kud'i, kaga kywa ai zamu shiga uku."

Kallon anya kuwa matar nan nada hankali ya mata? Dan shi dai inba hauka ke damunta ba baiga abun mita ba anan, da mamaki yace "Zeinabu yaushe kuma gidan nan muka fara rayuwar tsiya da talauci? Yanzu ke duk a lamarin nan kud'in da zaki kashe ne matsalarki? Ba wai farin ciki da 'ya'yanki zasuyi aure ba, meyasa kike hakane? Ke nama ji zamu kashe kud'in, babu kud'in ne na kashewa? Ko kuma ke aka ce ki fito dasu ki kashe bare ki wa mutane iya shege, sannan meyasa bakiyi tunanin d'an uwana ba da kuma matarshi Sa'ada? Su fa duka yayansu maza ne wanda su zasu kai, ke kuma d'an ki d'aya ne zai kai biyu kuma mata zasu kawo miki abun arzik'i, mtssss, wallahi Zeinabu matsalarki tayi yawa."

Mik'ewa tayi jin k'orafinta yau ma bai karb'u ba ta nufi k'ofar fita tana magana k'asa k'asa da fad'in "Aikin banza, ai nasan dama ba tunani gareka ba bare ka hango abinda na hango mana, indai har zamuyi yanda akeyi ne ai mazan idan sun kawo mana sai mun kusa ninka musu abinda suka kawo a cikin gara."

Tana daf da kaiwa k'ofar taja tsaki tare da murgud'a mishi baki, da k'arfi ya juyo dan tabbatar da gaske ne abinda yaji wai, ita ma sai bayan tsakin ya fito ta fahimci bala'in data jawowa kanta, ai da wani irin k'arfi yayo kanta zai cabkota amma hukuncin ubanjigi saita zame ta juya da gudu ta fad'a ban d'aki duk da k'ok'arin shi na son cabkota, tana shiga da iya k'arfinta ta maido k'ofar ta rufe daidai yana kawowa, kile tasa ta rufe gam shi kuma ya shiga bubbuga k'ofar yana fad'in "Zeinabu ni? Ni kike wa tsaki! Zeinabu yaushe kika raina ni haka? Allah ki bud'e k'ofar nan ko na karyata."

Wata irin jijjiga ya wa k'ofar da yasa ta fara motsi da k'arfi kamar zata karye, Zeinabu kam ciki ya d'uri ruwa sosai, tasan inhar ya bud'e to saiya karyata kam, yana cikin jijjiga k'ofar da k'arfi Sa'ada da tun farkon fara bubbuga k'ofar shi taji dan tana falon zaune ta kira Junaid tace ya zo, yana zuwa d'akin ya bud'a ya shigo da sauri ya tunkaroshi ya rik'e shi yana fad'in "Yi hak'uri dan Allah Abba, kayi hak'uri, muje ka rabu da ita."

Wani kallo ya ma Junaid ido jawur ya fizge ya shak'i wuyan rigarshi yana fad'in "Dan ubanka waya kawo ka? Me ma ya shigo da kai? Ka zo ne ka shigar ma uwarka? To yau saina kasheta a gidan nan, nace saina kasheta idan ya so nima a kashe ni."

Yanzu kam Junaid ya fahimci uwar tashi ta kwanto musu kura, turashi yayi ya kaiwa bango karo ya sake kama murfin k'ofar ya jijjiga da k'arfi, cikin d'aga murya yace "Shikenan, ai kin k'i bud'ewa ko, to bari kiga yanda zanyi da k'ofar."

Da sauri ya juya kayanshi daya shigo dasu ya fitar 'yar k'aramar bindigar dake jikin kayan ya zaro ya nufo k'ofar, Junaid na ganin haka ya shiga gaban k'ofar yana sake bashi hak'uri amma saiya ture shi gefe, ganin abun yafi k'arfin shi yasa shi fitowa yayi daidai da fitowar Hajia, da sauri yace "Hajia dan Allah ki zo kafin Abba ya kashe Umma, wallahi ranshi ya b'ace."

Da azama ta tako ta shigo d'akin tana fad'in "Kisan kai? Karfa yaran nan ya ja mana masifa a gida."

Tana shigowa daidai colonel yasa k'afa da k'arfi ya bangaje k'ofar, Zeinabu na jin ya bud'e ta dafe kanta da hannaye ta k'ame wuri d'aya ta rintse ido jin fitsari na zubo mata daga tsaye, shi ma kuma yana ganinta gabanshi ya saita bindigarshi ya nuna mata yana fad'in "Me na fad'a miki? Bance miki ki bud'e ba kafin na shigo da kaina, to yau zzzz..." Bai k'arasa ba Hajia ta shiga tsakaninsu tace "Ka kashe ni Hussein kafin ka kasheta, tunda so kake ka jawo mana abun kunya."

Ganin Hajia gabanshi ya sa shi kaucewa cikin hassala ya buga bindigar a bango ya saketa ta fad'i shi ma kuma ya kaiwa bangon duka da hannunshi, a hankali Hajia ta dafa kafad'ar shi ta shafa, shiru yayi bai juyo ba hakan yasa ta kama hannunshi suka fita zuwa falo, Junaid kuma kallon mahaifiyarshi yayi cikin ladabi yace "Umma dan Allah ki rage duk
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment