Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

take sha, ita da jakarta kawai ya d'auka yasa a boot ya fizgi mota ya bar gidan gonar.

Harira da har fitsari ya kusa sub'uce mata a wando saida taga fitarshi ta fito, idonta akan wayar tasa hannu ta d'auka, dama kuma Ma'arufa ba tsaro take sawa a wayar ba, tana ja sama taga ta bud'e kuma abun mamaki akan wannan banzan video ne wanda ita taga zahirinshi ma, tsaki tayi ta sunkuya zata aje wayar sai kuma tayi cak kamar an tsikareta, tsaye tayi tana kallon wuri d'aya tana tunani, wani murmushi tayi jin wani tunani daya zo mata, sai kawai tasa wayar a jakarta ta juya dan barin gidan.

Ko da Ammie ta fad'awa Sameera d'aurin auren Raihan da wani tayi fad'a har bakinta ya fara kumfa, tana ganin kawai yana neman maraba da ita ne shiyasa ya had'ata da wanda bai san halayenshi ba, kuma wai yace gobe Alhaji Khamis zai tafi da ita Maradi, jibi kuma an gama mata visarta saita wuce Maroc, saida Abba tace tayi wa mutane shiru kad'ai taja baki tayi shiru tana gunguni.

Tafiya yayi kamar zai bar gari duk inda ya gani sai yaga kamar za'a kama shi, kuma har wannan lokacin yana tunanin anya kuwa abinda zakayi daidai ne? Da k'yar ya isa wata doguwar hanya da babu mutane sosai, nan kawai zuciyarshi ta yanke mishi ya ajeta bakin titi ko ta samu taimako a mata sutura daga wasu bayin Allah, haka kuwa yayi saida ya tabbatar babu kowa ya fito da ita ya aje tare da jakarta da d'an kwalinta kafin ya juya ya bar wurin zuciyarshi cunkushe jikinshi na rawa na rashin saboda da tsintar kai cikin gagarumin tashin hankali, daga nan gida ya nufa da tunani iri iri.

*Basraba*

Gidan sarauta gaba d'aya ya hargitse da hidima na walima da aka shirya, sosai aka ci aka sha kafin yamma tayi aka fara shirin tarban amare kamar yanda uwar d'aki ta buk'ata, yamma tayi rana tayi sanyi gidan ya k'ara yamutsewa ta ko ina saboda bak'i da suka fara shigowa da amaren, nan hadimai da bayi suka fara kai da kawowa suna nuna musu masaukinsu, haka aka dinga shiga da amaren suna gaishe da uwar d'aki da kuma sauran matan da kuma uwar gidansu gimbiya Ameera kafin aka wuce dasu nasu masaukin.

*A gurguje*

Da dare bayan jakadu sun shirya Jawahir wacce ita ta fara isowa gidan kafin Safiyya, hakan kuma na nufin ita ce gaba da Safiyya yau ita ke da sarki, sarki ma da kanshi ya tarasu su ukun ya nuna musu mahimmanci da darajar uwar gidanshi, sannan ya nuna musu yana son zaman lafiya da kuma had'a kansu, yana gamawa ya sallami kowace ya koma bed d'in shi.

Uwar d'aki da kanta ta turo jakadiyarta ta taimakawa sauran bayin aka shirya Jawahir cikin shiga ta alfarma kafin ta kamota har falon sarki tayi wa sarki magana sannan ta koma, izinin shiga ya mata bed d'in, cikin nutsuwa da jin kunya ta shiga kanta k'asa, kan gado ya nuna mata ta zauna shima ya zauna kusanta yana kallonta, ba laifi kam kyakyawa ce ga kuma kunya, saidai akwai k'ananan shekaru gareta da gani, ganin ta k'i d'agowa ta kalleshi yasa ya kalli hannayenta da suka sha lalle, sake kallonta yayi yace "Jawahir."

Har zata d'ago kanta kuma saita tuna yana daf da ita dan haka ta k'i d'agowa ta amsa da "Na'a."

Murmushi yayi dan ta birgeshi data kasa kallonshi hakan yasa ya mik'e ya kama hannunta yace "Muje muyi alwala muyi sallah."

Mik'ewa tayi tabi bayanshi har toilet, saida ta d'aga ido ta kalli toilet d'in ganin ban d'aki kamar d'akin kwanan wani, tare sukayi alwala suka fito sukayi sallah, bayan sun kammala ne ya mata tambayoyi kan addininta musamman yanda zatayi wankan tsarki da kuma yanda take sallahrta, abun mamaki shine amsa wasu tambayoyin da tayi ba daidai ba, bai wani nuna mata k'yama ko wani abu ba sai kawai ya bar abun a ranshi da d'aura niyyar d'ora mata a hankali harta fahimta, a nutse ya kalleta yace "Kina buk'atar wani abu ne da zaki ci?"

Kai ta girgiza alamar a'a, mik'ewa yayi tana kallo yayi shirin baccinshi tana zaune, ba zato ba tsammani taji ya kamo hannunta ya zaunar akan gadon ya koma ya kashe hasken d'akin sannan ya dawo, kwantar da ita yayi kamar wata beby ya kwanta gefenta, a hankali cikin nutsuwa da dabara ya samu ya lallab'a ta har ta zama cikakkiyar mace a wannan daren.

Kamar yanda mahaifanta suka rad'a mata tun kafin auren hakane ta kasance, a lokacin daya shiga ban d'aki dan tsarkake jikinshi cike da k'arfin halin duk da bata iya wa haka ta mik'e ta ta saka kayanta tayi sauri ta yaye wannan zanin gadon ta tura k'ark'ashin gado sannan ta zauna bakin gadon, yana fitowa ya kalleta da mamaki ya k'araso yana fad'in "Jawahir, ya zaki takura kanki haka? Kije kiyi wanka kinji."

Cike da dagiya ta murmusa kanta k'asa tace "Ba komai, dama zan canza zanin ne kuma bansan a ina zan samu ba, shiyasa..."

Maganar ta tace ta sark'e haka kawai dan haka ya kamata ya nufi toilet da ita yana fad'in "Ki barshi kawai, ni zan canza wani da kaina, yanzu ki samu ki kula da kanki kinji ko."

Yana fitowa ya fara k'ok'arin canza zanin, yana da niyyar idan ta fito ya tambayeta ina waccen zanin? Dan kar azo ta fita da shi sai kowa ya ga meya faru tunda akwai k'uruciya a tare da ita, amma jimawar da tayi tana kula da kanta da kuma kunyar fitowa yasa har bacci ya fara ridarshi saboda akwai gajiya a tare dashi, tana fitowa kuma jawota kawai yayi suka kwanta yana rumgume da ita a k'irjin shi kamar yar tsana.

*Abuja*

Cikin tsanani rud'u ya shigo gidan ya kuma zarce bed d'in shi, kile k'ofar yayi inda ya cire kayanshi ya shiga wanka, haka ya zauna ruwa na sauka a kanshi yana kuka kamar yaro k'arami, sam wunin ranar bai ma san ya akayi shi ba bare kuma yasan yanda ya gudanar da nashi, sanda Sameera ta ankara da motarshi taje d'akin dan suyi magana amma bai bud'e mata ba, haushi ne yasa ta baro k'ofar da niyyar ba zata sake komawa ba sai in ya fito dan kanshi, sam kamar ba gidan da aka d'aura aure ba, a haka har dare yayi yan mutanen da kenan ma suka watse, da dare kusan kowa ya kwanta amma banda Sameera dake tare da Raihan ana ta gyaran jiki, haka ma Abbas da abun duniya ya isheshi yake tunanin halin daya samu kanshi cikin d'an lokaci, sai kuma Harira data samu lambar Abbas d'in wurin Abdul raheem tana kwance kan k'aramin gadonta zata kira shi.

Yana kwance yana kallon sama kiran Harira ya doki kunnuwanshi, har ga Allah saida gabanshi ya fad'i kuma ya zabura ya tashi zaune, dan yanzu fa ya zama marar gaskiya ne kowane kira d'aukar shi yake wata matsalar ce, k'ara shiga damuwa yayi ganin bak'uwar lamba, amma wannan karan sai yayi saurin d'auka saboda maganin matsalar bai tsaya b'ata lokaci ba, shine ya fara cewa "Wake magana?"

Harira na jin muryarshi saida gabanta ita ma ya fad'i kafin ta daure tace "Harira ce."

Da d'an k'arfi yace "What! Harira kuma? Wacece hakanan kuma?"

Murmushi tayi tace "Harira dai yar k'auye mai aiki gidanka, na kira ne muyi magana idan kana da lokaci?"

"Bana da to." Ya fad'a a harzuk'e, dariya tayi dan tasan maganar yayi ne cikin jin haushi sannan tace "Dama wayar siyarwa ce gareni mai matuk'ar tsada wacce nake ganin da kai kad'ai zata dace, amma tunda kace baka da lokaci shikenan, saida safe, amma karka manta da abinda masu iya magana ke fad'a, *ko a k'ark'ashin k'asa ka shiga ka aikata abu to ka sani akwai ranar da zai fito*, bare kuma kai da a bayyane kayi komai naka ma, ka sani yanzu bana ganinka da wani sauran mutumci, tun ranar da nayi mugun gani, yallab'ai Abbas da karuwa a cikin gidanshi ba kunya ba tsoron Allah, tirr."

D'orawa tayi da "Ban tab'a tunanin zaka iya aikata zina ba, amma sai gashi naga ka aikata har kisan kai ma, hakan fa na nuna rashin imaninka yayi yawa."

Abbas da rigarshi tayi sharkaf da gumi yaji kanshi ya fara juyawa jikinshi ya fara kyarma ba tsayawa komai yace "Ke kuma nawa kike so?"

Wata dariyar jin dad'i tayi tace "Da idona naga duka ta'asar da kayi, a yanzu haka kuma ina rik'e da wayar yarinyar daka kashe mai d'auke da vidΓ©on caskalenku, ni ba kud'i nake so sab'anin hankalinka ne, idan har kayi abinda nake so ni kuma zan rufa maka asiri har abada."

"Ki fad'a min kawai me kike so da gaggawa? Sannan ki min alk'awarin zaki bani wayar nan idan har nayi abinda kike so."

Saida ta gyara kwanciyarta kafin tace "Ina so ka aure ni, da ka amince ni kuma zan baka wayar tare da duka idanu na da sukaga abinda kayi."

Sauka yayi daga kan gadon yace " In aureki? Ke a wa? Ke tsaya kiji, halin da nake ciki fa bai haukatar da ni ba ta yanda zan iya had'a kaina dake ba bare kuma har na had'a ki da matata, dan haka ki canza wata buk'atar amma ba wannan ba."

Zaune tayi tace "Kana nufin ba zakayi na kenan?"

Kai tsaye yace "Eh, haka nake nufi."

Cike da gadara tace "Ai kuwa zuwa safiyar gobe mummunan sak'on nan zai sauka idon matarta ka."

Yasan barazana ce dan haka yace "And so what? Ki nuna mata mana, kin d'auka mahaukaciya irinki? Wallahi kina nuna mata ba zaki bar gabanta ba har sai kin rasa k'afa ko hannu ko kuma ki rasa fatar jikinki."

Jim tayi dan kuwa tasan gaskiya ya fad'a, to ai ita zata fad'awa wani wacece Sameera ba wai wani ya fad'a mata ba, dan haka tayi murmushi tace "Shikenan tunda haka kace, ni kuma zan nuna maka bana maganar banza."

Cikin jin haushi yace "Shikenan mu zuba mu gani."

Yana fad'a ya kashe wayar, dafe k'ugu yayi ya shiga zarya yana tunanin ta ina ita kuma ta shigo labarin? Ya akayi ta sani ko? Rasa amsa da jin haushi yasa shi buga wayar a bango take ta tarwatse, ganin haka yasa shi fad'awa kan gadon yana dafe da kanshi da hannaye biyu kamar ya kwamtsa ihu da iya k'arfin shi, tabbas yayi bacci amma baisan wane irin bacci bane, domin kuwa abubuwa ne fal a kanshi wanda yasa yake ji kamar ma a zahiri ne idonshi biyu.

*Washe gari*
Ko da Sameera suka tashi ta d'ora gyaran da suka tsaya jiya, da taimakon su Bilkisu aka had'awa Raihan kayan jikinta musamman kayan bacci wanda ake siyo mata duk jiya, wani abun kam saidai suyi godiyar Allah, ba dan akwai dalar ba antara ta cirewa kawai ake a account da sun d'ora hannu a kai, kasancewar Alhaji Khamis babban mutum ne yace amaryar kawai suke buk'ata, hakan yasa Sameera dan kar a raina mata 'ya ta kashe mata kud'i kamar ba gobe ta fannin sutura wacce zata saka a gani dai, sark'ok'i ma na milyoyin kud'i aka siya mata ga kuma bala'in gyaran da suka saka aka aiko musu daga mai duguri da kuma sokoto, haka ma daga Niger saida aka kawo musu sak'o duk na gyaran jiki a safiyar yau da yake harka da kud'i, misalin *09:00* motoci uku ne suka paka cikin gidan Alhaji Khamis ya turosu su d'auki amarya da masu rakiyarta, sai lokacin kad'ai Abbas ya fito daga d'aki cikin doguwar riga kana ganinshi kaga damuwa, su Ammie da Abba ne da kuma Sameera suka mata nasiha sosai, daga bisani kuma k'annan ta kuka Uka dinga yi na rabuwa da yar uwa wacce aurenta ba zasu shaida komai ba, Raudat taso taje amma haka Abbas ya murje ido yace ai mutum biyu kad'ai zasu rakiyarta, Imranatu da Bilkisu da suka shirya tafiya da kuma Ammie suna ji suna gani sai Bilkisu ta hak'ura su biyu kad'ai, kuka Raihan keyi kamar ranta zai fita , sai duk ta jita kamar wata marar gata, haka suka d'auki hanya bayan hawaye da Sameera ta zubar ita ma.

Suna tsaye har suka ga fitarsu, Abbas juyawa yayi ya koma ciki Sameera ma juyawa tayi ta koma d'aki cike da jimamin yar ta, zata zauna kan gado sai kuma ta tsaya tana kallon bak'uwar wayar da bata san da ita ba, d'auka tayi tana k'are mata kallo tana jujjuyata, a saninta dai babu mai ita a mutanen data sani, gashi kuma ba taro akayi ba gidan bare tace wani ya manta, tunanin da tayi ne yasa taja sama sai taga ta bud'e da nufin ko zata samu wata shaida da zata nuna wayar wace, amma bud'awar ita tasa zuciyarta kusan daina aiki yayin da ta nemi numfashinta ta rasa, rawar da k'afafun ta keyi yasa ta durk'ushewa ta saki wayar, banda rawa babu abinda jikinta keyi sai hawayen da suka fara zarya a idonta, idonta sun kafe wuri d'aya kan wayar data fad'i gabanta, tana son d'auke idonta amma abun ya gagara, bud'a baki tayi tana wani irin numfashi da shashek'a duk lokaci d'aya, kai take girgizawa alamar a'a amma kuma ganin abun take yana k'aruwa, wani kukan kura tayi ta mik'e tsaye tare da wayar da gudun tsiya kamar wata yar shekara sha shida ta fita daga d'akin ko kad'an ba zaka rabata da mahaukaciya sabon kamu ba, part d'in shi ta nufa tana zuwa ta kama murfin k'ofar d'akin shi cikin sa'a ta bud'e, tana jin ta bud'e tayi wata fitinanniyar kururuwa tare da cire d'an kwalinta ta shiga d'akin, Abbas da kwantawarshi kenan jin wannan abu yasa shi tashi zaune yana kallon mai shigowa, ganinta a birkice yasan ba lafiya ba dan haka ya yunk'ura da sauri ya mik'e zai tarbeta, ai kamar mai tab'in hankali haka ta...


πŸ‘πŸ‘πŸ‘
26/06/2020 Γ  19:39 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_23_


Da dare ana ta kai da kawowa na hidimar bikin lieutenant inda aka fara gyara kayan cefanai na girkin gobe sai jiniya da odar motoci kamar zasu fasa unguwar, jim kad'an hayaniya ta fara gauraya gidan sanda mutane ke shigowa, mutanen gidan ne suka fara kimtsawa suna umartar yara da su koma sama, saida mutanen suka fara shigowa falon kad'ai aka fahimci ashe duk dangi ne na wajen Suley da kuma wasu daga cikin dangin Soueiba da mutanen arzik'i, duk girman falon nan sai gashi cike da mutane dan mace tafi talatin wanda suka zo kawo kaya, hakan kuma ya faru ne saboda maganar da Hajia ta fad'awa Husseina shiyasa take so ta bata mamaki.

Wata kyakyawar fuskar na gani sak Husseina sai dai wannan tafi d'an tsufa, amma fa ita ma tana cikin shiga ta alfarma da kuma dattako, su Zeinabu da Sa'ada ne suka matsa kusanta suka duk'a suna gaishe ta, cike da fara'a da sakin fuska ta amsa musu kafin ta kallesu a nutse tace "Ina su Ammar ne da Junaid? Yaran nan ko kad'an basa zuwa inda mutane suke sai dai in an zo inda suke."

Murmushi Sa'ada tayi tace "Kiyi hak'uri Hajia, kinsan ayyukansu ne sai a hankali."

Murmushi tayi ita ma tace "To, haka kuka ce dai, yanzu ina Hajiar take? Kayan jikanyarta muka kawo mata."

Zeinabu ce tayi saurin mik'ewa tana fad'in "Suna ciki, bara na musu magana."

Sa'ada ce tace "A'a ki barshi, ni zanje."

Mik'ewa tayi ta nufi d'akin Hajia, ba jimawa ta fito suka ci gaba da kawowa bak'i ruwa da jus jus wasu ko sanyi babu saboda basu sanar da zuwan nasu ba, minti ashirin Hajia ta d'auka kafin ta fito, fitowarta tasa kowa ya mayar da hankalinshi kan uwar yan uku, masha Allah, shine abinda wasu ke fad'a yayin da wasu ke mamakin rashin tsufan matar, wata arniyar shadda ce tasa yayin da ta watso wasu sark'a da yan kunnai da zobuna da awarwaro na zinariya, ba dan komai ba sai dan ta bayar da tsoro, dan hayaniyar da taji tasan ba zasu yarda su mata wannan gayyar ba babu wani dalili, wani d'aurin d'an kwali ne ta kashe mai sauk'in gaske wanda yasa manyan kitsonta sauka har gadon bayanta, kwalli ne kad'ai a idonta amma tayi kyau sosai sai d'aukar ido take ga jar fatar nan tayi wani shek'i, kamar d'awisu haka ta tako har ta zo kujerarta ta zauna tana shan k'amshi da k'arewa mutanen kallon hadarin kaji kallon mai bisa ruwa.

Wannan Izzar ta ta da kwarjini yasa wasu daga cikin matan ma suka manta da matsayinsu suka fara gaisheta, tabbas suna jin muryarta na amsawa amma basu ganin labb'anta na motsawa, nan dai *Hassana* (yar uwar Husseina) ta umarci a shigo da kayan, mace uku ce ta mik'e suka d'auko akwatinan masu bakwai bakwai a ciki har kala uku, da kuma d'aurin goro har guda biyu, har gaban Hajia suka diresu tana kallon akwatinan, wani matashin saurayi ne ya shigo da wani dallelen moton har falon ya aje shi inda babu mutane a ledarshi, Hassana ce ta kalli Hajia tace "To alhamdulillah, kayan Jibril ne muka kawo na Jamila, ga akwatina, ga moton da yace a kawowa amaryarsa dan ci gaba da zuwa makaranta, sai kuma..."

Ta fad'a tana saka hannu cikin jakarta ta fito da kud'i ta d'ora saman d'aya daga cikin akwatinan tace "Sai wannan, million biyu ne, sadakinta kuma sai ranar d'aurin aure."

Ko ba komai bajintar tasu ta birge Hajia, amma saita dake ta kalli Hassana wacce ita ma ba shiri suke ba tace "Ba laifi, amma yasan da cewa buzuwa zai aura ta b'angare na, ba zai birge ni ba har sai yayiduk wani abinda akeyi idan za'a auri buzuwa."

Wani murmushin gefen labb'a Hassana tayi tace "Wannan ba matsala bane, sai dai zaifi kyau ki fad'a mana yanda al'adun suke dan mu sani, duk da shima dai akwai abinda dole amaryar tayi kasancewarshi babarbare."

Wata hamshak'iyar dariya Hajia ta saki wacce ni dai tunda na fara rubutun nan banji inda tayi dariya ba, kallon Hassana tayi tace "Babarbare? Ta ina? B'angaren uwa?"

Murmushi tayi kafin ta kawar da kanta tace "Ba zan tsawwala muku ba, ina so kawai naga anyi guitar (jita) a daren d'aurin aurensu, za ayi shiga irinta buzaye ko kuwa mutum baya so, sannan ba wai Jibril ba kad'ai, har sauran angayen dole kowane ya kawo min kyautar rak'umi wanda ya amsa sunan rak'umi bayan tarewarsu da matansu, hakan kuwa shine zai sake nuna darajar yaran da kuma d'aga martabarsu."

Wani kallo Husseina dake gefe ta mata tace "Amma ai na d'auka wannan al'adar ana cikata ne idan aka samu yarinyar da mutuncinta?"

Murmushi Hajia tayi ta kalleta tace "Kina tsammanin duk yanda nake saka ido kan 'ya'ya da jikokina za'a iya samunsu da rashin kamun kai, ai wannan ba abu bane da za'a same shi a zuri'ata ba."

Murmushi Husseina tayi ta sassauta muryarta tace "Ke ina taki kyautar?"

Hassana ce ta kalleta sannan ta kalli Hajia tace "Ba damuwa, zamuyi duk abinda kika ce, ai Jamila da Jibril yan uwan juna ne, ko kyauta zai iya siya mata jajayen rak'uma bare kuma ya karb'i budurcinta."

Suna kammalawa sukayi sallama inda Hajia ta bud'a jakar hannunta k'arama ta bawa Sa'ada kud'i har jaka d'ari biyu tace ta basu tukuici kamar yanda akeyi, su kansu k'in amsar tukuicin sukayi suka ce ai yayi yawa, da k'yar Sa'ada ta matsa musu suka karb'a suka bar gidan kowa da abun fad'a a baki.

Suna tafiya Ummy ta zarce b'angaren samarin ta shiga da sallama, Amar Jibril da Junaid da kuma Ammar ta samu zaune a falon, gaishe ta sukayi dukansu banda Ammar da hankalinshi ke kan tv, zaune tayi tana kallon Jibril tace "Bak'i har sun tafi, munga kaya masha Allah, Allah ya sanya alkairi?"

Da murmushi ya amsa da "Ameen aunty."

Kallon Amar tayi tace "Saura ku, na ku sai yaushe?"

Amar ne yace "Ummy gobe mu ma zamu kawo."

Dukansu ta kalla tace "Sai kun shirya da kyau, dan Hajia tace za'a gudanar da wasu daga cikin al'adunsu na buzaye, musamman ma ku."

Ta fada da nuna su Ammar ta ci gaba da cewa "Tunda kunga ni kaina buzuwa ce, dan haka dole zata fi karkata abun ta b'angaren ku."

Amar ne yace "Ba damuwa bane Ummy, matsalar ni dai wannan k'aton rawanin ne bana tunanin zan iya d'aurawa."

Dariya tayi tace "Da kaina zan d'aura maka, tunda saika d'aura shine zaka fito a buzun."

Mik'ewa tayi tace "Saida safenku, ku kwanta da wuri kunsan gobe ne fa auren ubanku."

Sai lokacin Ammar ya kalleta ta wutsiyar ido ya kuma d'auke kan shi, fita tayi inda Ammar ya mik'e zai shiga d'aki, Amar ne yace "Ka tabbatar ka tashi da wuri fa, dan Abba yace ni da kai ne zamu take masa baya muna karb'ar bak'i."

Juyowa yayi ya kalleshi k'ala baice ba ya shige ciki ya barsu, Jibril ne ya gyara zama yace "Yau fa mutanen sun motsa."

Murmushi Amar yayi yace "Allah dai ya kyauta."

"Ameen." Cewar Junaid.

A nesa da k'ofar gidan ya paka mota ya tsaya inda kawu Mamu ya shiga dan kiran Zeituna, ba laifi gidan ya kaure da cacaniya alamar dai biki za ayi gobe, tuni dama ansa Zeituna ta shirya cikin wani kalar d'inki na atamfa wanda ba dan ta sanya hijab ba sai a mata dariya, dan kaf dangin babu mai wayewa ta zamani haka ita ma, dan ba k'awaye gareta ba bare tasan abu mai kyau ko marar kyau, lalle da kitso ma tayi sa'a a unguwar aka samu wanda suka iya suka mata, wata doguwar jagira aka ja mata tare da shafa mata jan jan-baki, fitowa tayi tana hard'e k'afafu saboda tsoron abinda zata tarar, tana isa ta inda yake ta tsaya kanta k'asa, tunda ta taho lieutenant ke hangenta yana raya abubuwa da dama, tana tsayawa ya sauke gilashin murya a d'an kausashe yace "Sai ki shigo ko, kinga ni ba yaro bane bare na fito na tsaya kowa na kallo na."

Gabanta ne ya tsananta fad'uwa ta zagaya ta kama k'ofar ta shiga, da k'yar ta janyo k'ofar ta rufe ta sake mayar da kanta k'asa tana wasa da yatsunta daga cikin hijabi, kamar yace ke ta zuba a guje take ji, wai yau gata a mota da Abban Ammar ana shirin d'aura musu aure gobe, jin shirun ne yasa ta tsargu ba tare data d'ago ba tace "Ina wuni."

Ajiyar zuciya ya sauke dan dama yana jiran tayi magana ne, kallonta yayi yace "Lafiya lau, ya hidima?"

Shiru tayi kamar ba taji ba, kallonta yayi kamar ya shareta sai kuma yace "Tun yaushe kike so na? Kuma kina ganin hukuncin da Alhaji ya yanke bai tauyeki ba? Har zuciyarki zaki iya zama da ni?"

Zeituna dake jin tambayoyinshi kamar saukar guduma a kanta tasan ba zata iya amsawa ba, sai kawai ta fashe da kuka tasa hannu ta toshe baki, sororo yayi yana kallonta da mamakin kukan na meye? Wani abu ya fad'a daya b'ata mata rai? Ko kuma sangarta ce tana so ya fara rawar k'afa yana rarrashinta? Ai ko abinda ba zai yiwu ba kenan, fuska ba annuri yace "Meye na kuka kuma? Na fad'i wani abu ne? Ko kuma dai takuraki akayi?"

Girgiza kai tayi hakan yasa yace "Shin akwai wani abu da kike buk'ata ne?"

Nan ma girgiza kai tayi hakan yasa ya kawar da kansa yace "To ni zan tafi, saida safe ko?"

Ji tayi wani kukan ya taho mata wanda yasa tayi saurin bud'e k'ofar ta fito,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment