Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

abin duniya ya shiga tsakaninsu, da haka kowa ya tashi ya koma inda ya fito suka bar takawa lafiya k'alau.

Wannan ganin shine na k'arshe da suka mishi da numfashi a tare da shi, domin kuwa waziri ne ya biya wasu yan daba guda biyu sukayi shiga irinta fadawan gidan aka shigo dasu gidan a motar dreba ta kai yara makaranta, wajen takawa suka shiga suka taushe mishi kai da pillow har saida ya daina numfashi, tunda asuba kuma aka farga da rasuwar takawar, liman daya zo masallaci da k'arfin gwiwar sanar dashi kowa ya amince, kuma bayan nan yayi istikhara kan lamarin, duk da ubangiji ya nuna mishi wani duhu a cikin abun amma kuma hasken dake ciki shi yafi yawa, dan haka ya zo da niyyar idan sun gama sallah ya fad'a mishi ya amince ko juma'ar da zata zo ma za'a iya d'aura auren ba damuwa.

*Abuja*

Tunda asuba da sukayi sallah sukayi karatu suke zaune falo cikin raha da k'aunar juna, Abbas ne ya kalli Raihan yace "Mama na wai har yanzu sakamakon na ku bai fito bane?"

Cikin sakin fuska tace "Dady yau zai fito, anjima kad'an zamu je mu dubo."

Kallon Abdul yayi yace "Abdul, anjima ka shirya zamu fita tare da kai a motarka."

Da girmamawa ya amsa da "Ok Dady, zuwa k'arfe nawa?"

Kallonshi Abbas yayi yasan ya tambaya ne dan ya shirya kafin lokacin, dan haka yace mishi " 08:00 pm."

Jinjina kai yayi yace "Ok Dady."

Cike da kunya Raihan ta kalle shi tace "Dady, alk'awarin mu?"

Da mamaki yace " Wane alk'awari kuma nayi mama na?"

Sanda kanta tayi k'asa cikin kunya tace "Dady u promise me zaka fitar damu abroad idan result d'in mu yayi kyau."

Murmushi yayi yace "To banda rigimar mama na ai result d'in bai fito ba, ki jira ya fito sai mu gani."

Cikin sangarta tace "Dady gaskiya mun fasa zuwa abroad d'in, mu *Niger* muke so mu tafi."

Murmushi yayi kafin yace wani abu Ammie dake zaune tace "Shawara mai kyau, kinga kenan lokaci yayi da zaku kaiwa auntynku ziyara."

Rauda ce da sauri tace "Wace auntynmu kuma?"

Hararanta Ammie tayi tace "Husna da zatayi aure niger ba dalilin auntynku dake aure a can bane ita ma harta samu miji a can."

Cikin yanayin na tuno Rauda tace "Ohhh hakane fa, ki ce aunty *Khairiya* ('yar Bakura yaya ga Husna), gaskiya indai hakane aunty Raihan zanje tare da ke nima na ga niger."

Cikin ruwan sanyi Raihan tace "Babu inda zaki bini yarinya, ki jira idan auren Husna ya tashi saiku tafi tare da Ammie."

Abbas ne yace "To ai ko ke baza ki ba sai auren ya tashi, in ya so daga basraba saiku wuce niger d'in."

Turo baki tayi tace "Amma dai Dady za'a baro ni can wurin aunty Khairiya ko?"

Mik'ewa yayi yana fad'in "U have a choice." Ganin ya nufi kitchen yasa Khalifa cewa "Dady kayi b'atan kai, nan fa madafa ce."

Juyowa yayi yace "Wajen matata zanje, dukanku nan kun manta da ita tana can tana faman girka mana abinda zamu ci."

Dariya Khalifa yayi ya d'ago mishi yatsa irin πŸ‘yace "Fatan alkairi Dady, amma fa banda fad'a kuma, kar ku zo ku rikice mana sai munje rabo."

Dariya Abbas yayi ya mishi dak'uwa yana fad'in "Hancin ubanka Imran."

Yana bud'a k'ofar kitchen d'in Harira ce ya fara hangowa suna ta kai da kawowa, wani bak'in ciki ne yaji ya taso mishi tare da tuna abubuwan da suka faru a baya, k'aramin tsaki yayi ya juya zai fita sai kuma Sameera ta juyo, murmushi ta sakar masa ta mik'awa Razeena had'in kabejin da tayi tace "Ki saka a fridge kafin a kammala sauran."

Karb'a tayi ita kuma ta juya wajenshi tana ci gaba da murmushi harta isa tana fad'in "Barka yallab'ai, har kun kammala karatun?"

Hannunta kawai ya kama ya nufi wajen cin abinci da ita, Harira na ganin haka cikin dubara ta aje aikinta ta bi bayansu, dan dama ana aikin banda hararan Sameera babu abinda take tana ayyanawa a ranta wai ita ce mai bayar da oda a duk fad'in gidan nan, lab'ewa tayi tana jin me suke fad'a, Abbas ne cikin rashin son magana yace "Sam, dan Allah me zai hana ki sallami yarinyar can? Idan taimakonta kike so kiyi why not ki bata kud'i tayi sa'a, amma dai ta bar gidan."

Da mamaki tace "Why? Me tayi kuma yanzu?"

K'ura mata ido yayi yace "Tambayata ma kike? Kinga, ina so ne nasan zaki iya sallamarta ko kuwa?"

D'an had'e fuska tayi ta turo d'an bakinta gaba tace "Please sir forget about Harira, mun riga da mun gama maganar nan fa, kuma fa ni bance kai zaka biyata kud'in albashinta ba, so dan Allah ka manta kawai."

Wani kallo ne ya mata baki bud'e sai yayi kamar zai girgiza kai sai kuma ya fasa, wai Sameera ce ke fad'a mishi ai ba shi zai biya mai aiki ba, sai lokacin ya girgiza kanshi tare da sakin mamakin dake kan fuskarshi yasa hannu ya shafi yalwataccen gemunshi yace "Ok, duk abinda kikayi d'aya ne, amma ki sani duk abinda zaije ya dawo babu ruwa na ni."

Da k'arfi ya fara takawa da nufin tafiya b'angaren shi, da sauri ta rik'e hannunshi a lokacin kuma Harira dake lab'e harta koma kitchen, kafeta yayi da ido fuska ba annuri, ita kam cikin kwarkwasa tace "Do something now, ka samu kayi wanka kafin ka fito na had'a maka break a part d'in ka, dan bana son yara ma su dameka."

Fizge hannunshi yayi yana fad'in "Sai me? Ina ruwanki idan sun dame nin?"

Juyawa yayi zai fice ta bishi da murmushi tana fad'in "Kayi wankan fa, yanzun nan zan kawo maka break d'in."

Juyowa yayi harda dafe k'ugu yace "Mayunwaci ne ni? Kinga yunwa a jikina ne?"

Gimtse dariyarta tayi ta girgiza mishi kai alamar a'a, saida ya sake juyawa tace "Allah dai ya huce zuciyar mijina."

Cak ya tsaya ba tare daya juyo ba, wato ta mayar dashi wani shagirigirbau, sake rik'e k'ugun shi yayi ya juyo yana kallon cikin idonta ya nunata da yatsa yace "Billahil-azeem idan ban b'arar dake ba ki ce d'an iska ne ni."

Tintsirewa tayi da dariya abinda ya k'ara bashi haushi kenan, da gudu ta nufi falo inda tasan Ammie na nan, da k'arfi ta shiga falon tana dariya tana juyawa taga ko ya taho, shi kuma a sukwane ya taho yana kawowa falon ya fara tafiya a hankali, Khalifa na ganinsu yace "Yeah, anzo gurin."

Duk da kujerar da Ammie ke zaune ta zaman mutum d'aya ce amma bai hana Sameera zaune a k'afafun Ammie ba ta d'ora kanta a k'irji kamar wata beby tana fad'in "Ammie kin ganshi ko."

Ammie kuma dan taya b'era b'ari saida ta fara shafa bayanta kafin ta harari Abbas dake kallon Sameera tace "Kai kuma meye haka da sanyin safiya zaka taso min 'ya gaba da gudu? Wallahi fa bana son abin nan da kake min, yarinya ko babu laifin bak'i bana fari saika dinga cutar min 'ya."

Abbas kallon ikon Allah yake, hakan yasa Sameera yi mishi gwalo tana dariya, Abba ne ya kallesu yace "Wallahi wata rana saita karya miki k'afafu, kuma a k'arshe yaro na za'a bari da kashin kud'i wajen neman magani."

Ammie ce tace "To idan bai kashe na shi kud'in ba ai muma muna da kud'in kashewar, sannan shi kud'i zai kashe auta ta kuma jinyata zatayi."

Saida Sameera ta sake cukuikuyeta tace "K'warai kuwa Ammie na."

Wata jar harara Abba ya jefa mata wacce tasa ta mik'ewa daga k'afafun Ammie bata shirya ba, dan har yanzu akwai wutar bala'i a jikin mahaifinta wacce ta ninka ta ta sau dubu, tsaf ta fahimci me hararan daya mata ke nufi, shiyasa ma ta mik'e tayi shiru, juyawa Abbas yayi zai bar falon yana fad'in "Allah ya shiryaki."

Muryar Abba ce ta dakatar dashi da yaji yace "Liman kuma? A wannan lokacin."

Juyowa yayi ya ga Abba ya mik'e ya nufi k'ofar fita yana d'aukar kiran da liman ya mishi, bayan sun gaisa ne Abbas yayi saurin tambayar lafiya? Dan haka kawai ba zai kirashi ba a wannan lokacin, cike da muryar jimami liman yace "Yallab'ai sai dai hak'uri, kamar yanda muka sani ne kowane mai rai lokacinshi yake jira, to a daren jiya Allahn daya bamu takawa ya fimu son shi ya kuma karb'i abinshi, sai hak'uri kawai."

Duk da Abba bai zubar da hawaye ba, domin kuwa mutuwar mahaifiyarsu da kuma ta mahaifiyar Sameera *(Khadija)* ne kad'ai ya zubar da hawaye, amma hakan ya girgiza shi sosai, cikin sanyi jiki da maimaita kalmar inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ya shigo falon, suna ta hayaniyarsu, wajen Ammie ya nufa inda Abbas ya bi bayanshi ya tsaya saboda ganin yanayinshi, saida ya kalli Sameera da Abbas da Ammie kafin yace "Ku shirya, tafiya basraba ya kama mu yanzun nan."

Sameera da gabanta ya fad'i ne tace " Abba, lafiya? Meya faru a basraba?"

Ko kallonta baiyi ba dan haka Ammie ta mik'e tace "Yallab'ai lafiya? Meya faru ne? Ko wani ne ya rasu?"

A hankali ya jinjina mata kai alamar eh, Abbas ne yayi saurin cewa "Abba waya rasu?"

Saida ya had'e yawun da suka bushe mishi a mak'oshi kafin ya kalleshi, kamar ba zaiyi magana ba saboda yanda ya kafeshi da ido, can kuma sai yace "D'an uwa na, d'an uwana da shi kad'ai ya rage min, *Musayyib* ne ya rasu daren jiya."

Yana fad'a ya juya a sukwane ya bar falon alamar yana son b'oye yanayinshi, Sameera da ko da aka fad'i haka ta tuna da kiran daya mata jiya bayan sallah isha'i yana sake mata nasiha data dinga hak'uri da rayuwa, bayan haka har suka tab'a hira yana fad'a mata ya nemawa d'an uwanta auren 'yar liman, sun jima suna waya amma yanzu ace babu shi, neman durk'ushewa tayi hakan yasa Abbas saurin tallabota ya rumgume a jikinshi, tana jinta a k'irjin shi saita fashe da kuka sosai tana cakumar rigarshi tana k'ara sautin kukan, Ammie da ba zata iya hanata kuka a wannan lokacin ba dan tasan yanda suke da kawunta, soyayyar da yake nuna mata ko mahaifinta baya nuna mata ita, fita tayi ita ma dan suyi shirin tafiyar, yaran na ganin haka suka mik'e kowa ya nufi d'akin shi zuciya cunkushe saboda ganin mahaifiyarsu na kuka, Raihan saida ta rik'o hannun Sameera cikin rawar murya tace "Dan Allah Ammie kiyi shiru ki daina kuka, takawa addu'arki yake buk'ata yanzun, shine soyayyar da zaki nuna masa."

D'akinta ta haura ita ma sai Abbas daya nufi da Sameera b'angaren shi yana rarrashi, ita kuma sai fad'a masa take jiya fa ya kirata sun jima suna magana, yanzu ace wai ya rasu, a ciwon komai da komai, yana shiga d'akin shi ya zaunar da ita bakin gado ya d'auki wayarshi, Bashir ya kira ya fad'a masa, Bashir da a lokacin ke zaune falo yana sauraren hayaniyar yara Imranatu kuma da Ma'awa da ke ta k'ok'arin shirya abun kari, kallonta yayi baiwar Allah tana cikin farin ciki, taya zai fara fad'a mata rasuwar mahaifinta, ajiyar zuciya ya sauke ya mik'e ya tunkareta, hannunta ya kama har zuwa d'akin kwanansu kafin ya fara mata da nasiha sannan ya rarrasheta, yana fad'a mata ita ma ta fashe da kuka ta fad'a saman k'afafun shi, haka dai ya lallab'a ya taimaka mata ta shirya dan Abbas yace yanzu zasu tafi, wajensu Bilkis da Naseer ma haka abun yake, inda Abbas bayan ya gama waya dasu ya kira captain Ali ya sanar dashi zasu tafi basraba.

Cikin k'ank'anin lokaci kowa ya gama shirinsa ya fito, Sameera kitchen ta nufa ta samu Razeena ta fad'a mata su kula da gida sosai, sannan tace wa Harira ta kula da yaran, a wannan lokacin da Sameera a cikin nutsuwa take data fahimci kallon da Harira ta mata na kin ma raina min hankali ne, haka suka fito sun kuma samu driver har ya zo d'aukar yaran zuwa islamiyya, saida suka ga tafiyar yaran kafin suma Abbas ya jasu a d'aya motar kuma Naseer ne, suna isa airport captain ya riga daya iso, ba b'ata lokaci suka shiga kowa ya kimtsa suka d'aga sai masarautar basraba.

Da saukarsu mota uku ce sarki Imran ya turo dan d'aukar su, masha Allah, unguwar cike take da mutane da ababen hawansu, rasuwa ce data jijjiga masauratar dama kewayenta gaba d'aya, jimamin da mutanen gidan ke ciki yasa tsohon sarki mahaifin Sameera da ma ita kanta Sameera da kuma yar sarki mai mutuwa Imranatu basu samu gaisuwa da irin wasasun da ake ba idan sun zo, k'arfe *08:30* motoci sukayi gudan layi mai tsayin gaske zuwa mak'abarta.

*Allah ka mana kyakyawan k'arshe.*

*Muje da sauri*: Abba ne ya bayar da umarnin ayi addu'ar uku har ta arba'in ma, domin kuwa irin mutanen da suka halarci jana'izar bai kamata ace sai sun sake dawowa ba, dan har masarautun dake kewayensu ma sun hallara, take aka had'a akayi addu'ar amma hakan baisa jama'a barin gidan sarautar ba, kamar da wasa sai gashi har anyi *kwana biyu* da rasuwar sarki mai murabus, a wannan kwanakin kuma uwar d'aki hankalinta ya tashi sosai, tunaninta ya karkata kan wane irin banzan mataki ne waziri ya d'auka akan mijinta? Me yasa bai fad'a mata irin wannan matakin zai d'auka ba? Da tayi gaggawar dakatar da shi, har yanzu tana so ta keb'e dashi dan suyi magana, amma rashin gaskiya yasa duk wani motsinta sai taga kamar wani yana kallonta, dole ta hak'ura da tunanin idan anyi uku kowa ya watse zata neme shi.

*Yau kwana uku*, Sameera dama jiya gidansu kawu Bakura ta kwana tare da mijinta, hakan yasa yanzun sukayi sammakon shigowa masarautar dan shirya komawa, tun farfajiyar gida bayi ke durk'usawa suna gaisheta tana amsawa, ita da Abbas b'angaren uwar d'aki suka nufa dan tunaninsu kowa na can, amma suna daf da kaiwa sai jakadiyar uwar d'aki *Lami* ta taho a sukwane ta sunkuya tana wasata tare da fad'a mata ana mata magana a falon mai rasuwa takawa, juya akalarsu sukayi zuwa can, suna shiga tare da sallama suka samu taron jama'a, uwar d'aki, mahaifinta da mahaifiyar Abbas, waziri da matarshi ga kuma liman da sarki Imran, gefe ma dai duk su Naseer ne da su Imranatu, wuri suka samu suka zauna kusa da juna, Abba ne yayi gyaran murya ya kalli liman yace "Liman jiya munyi wata magana da kai akan auren Imran da kuma yar wajenka, hakane?"

Cikin jinjina kai liman yace "Hakane."

Imran ya kalla yace "Imran, kasan da maganar nan ko kuwa?"

Cikin ladabi yace "Na sani Baffa."

Kallon mutanen dake d'akin yayi yace "A yammacin ranar da d'an uwana zai bar duniya sunyi magana da liman, bayan liman ya min bayani kuma na gamsu d'ari bisa d'ari, dan nasan ba zai fad'a min abinda ba haka ba, bayan liman kuma ya sake kiran *Falmata* ya sanar da ita an tsayar da maganar, hakan ya tabbatar min wannan shine burin d'an uwana na k'arshe, shiyasa na tara mu anan ina neman yardar kowa da had'in kai dan ina so na d'aura auren bayan sallah la'asar a yau d'in nan."

Liman ne yace "Yallab'ai wannan ai ba wata matsala bace, nima a yanzu bana da wani buri daya wuce na ga anyi auren nan, da alama burin takawa kenan na k'arshe."

Jinjina kai Abba yace ya kalli liman yace "Imran ka amince a d'aura auren nan yau?"

Cikin sanda kai k'asa yace "Bana da wata matsala Baffa, na so ace mahaifina yana raye zaiga wannan lokacin."

Abba ne yace "To Alhamdulillah, tunda kun amince sai kowa yaje ya fara shirin data kamace shi kafin la'asar."

Kamar saukar aradu sai kuwa matar waziri *Asabe* tace "Tab'dijam, lallai ma duniyar nan babu gaskiya, ace mutum lokacin da yana raye ba'a k'ago wannan labarin ba sai yanzu, humm."

Kowa kallonta yayi, waziri kuma k'uri yayi da ido yana kallon yanayin Abba, dan yasan in ranshi ya b'ace ba fa da ita zaiyi ba da shi mijinta zaiyi, tabbas Abba yaji maganar har cikin ranshi, dan k'arshen raina masa hankali ne matar tayi, da ace ba mace bace ko kuma a cikin family take da saiya kasheta da mari, amma daya saci kallon 'yar tashi yaga har ta fara hawa sai kawai a ranshi yace "Zan barki da wannan ita ce daidai ke, idan na tabbatar kin shiga hankalinki zai dakatar da tarzomar."

Abbas kuma hankalinshi na kan tashi yar rigimar, wani kallo data wa Asabe ne yasa shi rik'e hannunta yana murza yatsunta, gyara zama Sameera tayi da kyau tana kallonta da wani irin yanayi kafin tace "Ke kuma malama waya saka bakinki a cikin maganar family? Ku fa kawai kun zo nan ne fa a matsayin wanda zasu zama shaidu a cikin al'amarin."

Sake matsowa tayi gaban kujerar kamar zata fad'o k'asa tace "To wai ma me kike nufi da abinda kika fad'a? Kina nufin mahaifina da liman zasu zauna su k'irk'iri labarin k'arya ne a cikin mutanen da baku fi su kiraku da bayinsu ba? Ke yanzu inba rashin mutumci ba har zaki kalli wannan ki fad'a masa maganar nan, ko kinsan abinda kika fad'a zai iya jaza miki hukuncin kisa ta hanyar rataya?"

A kowane sakan ranta ne take ji yana k'ara b'acewa, dan ji take kamar fa matar ta kalli Abbanta ne tace mishi mak'aryaci, ga kuma Abbas dake ci gaba da matsar yatsunta alamar tayi shiru tayi hak'uri, kenan ma yasan da an b'ata mata rai, mik'ewa taje tayi da niyyar tace matar ta fita sai kawai Ammie tace "Kiyi hak'uri takwara, koma ki zauna."

Ko kallon Ammie ba tayi ba sai hararan matar take amma dai ba tace komai ba, hannunta Abbas ya kama ya jawo dan ta zauna amma tayi k'yam ta cije, liman ne yace "Hajia Fati kiyi hak'uri ki zauna muyi magana."

Hawaye ne taf a idonta ta nuna Asabe tace "Abba na fa take nufin mak'aryaci ne, Abban nawa."

K'aramin tsaki Abbas yayi ya mik'e tsaye ya had'e fuska ya kalleta yace "Malama fita anan, taron yara ne a gurin nan da zaki tayar mana da hankali."

Juyawa tayi ta kalleshi ido tsaye da nufin yi mishi tas, amma suna had'a ido saiya mata kallon da yasan dole ta shafa mishi lafiya, yau da gobe tasa Abbas karantar matarshi da kuma iya zama da ita, duk zuciyarta da masifarta tana shakkarshi, duk yanda bata barin takwana shi kam tana kwana har ma ta hantse bata rama ba, sai dai inya gaya mata abin ya mata zafi sosai to ta kanyi zazzab'i ko ciwon kai na tsananin bak'in ciki da takaici, wani lokacin kuma kan yara take hucewa duk abinda sukayi saita musu fad'a harta had'a da duka, yanzun ma tana ganin ba zata iya ramawa ba saita juya kan Asabe wacce ita ta jima da tsorata, tunkararta tayi da sauri da niyyar cakumota ta jefar a k'asa...


*Wato takwara har yanzu ba'a shiryu ba kenan a gane cewa an girma.*
05/06/2020 Γ  13:18 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_8_


Washe gari ma tunda asuba suka shirya dan tafiya sadakar uku, a tare aka fito dan tafiya, su Junaid a mota d'aya suke sai Ammar dake tashi motar shi kad'ai kamar maye, wasu motocin har sun fara fita sai kawai Ammar ya fito daga motar shi ya zo ya tsaya gaban k'ofar Junaid dake mazaunin matuk'i, kallonshi yayi ya sauke gilashi yana jiran yaji me zai ce mishi, shiru sukayi sai kallon kallo ake, hakan yasa Amar dake baya zaune yace mishi "Fita ka dawo nan, shi zai tuk'a."

Murya k'asa k'asa Junaid ya fito yana fad'in "Iko sai mai shi."

Yana komawa baya Ammar ya shiga ya figi motar suka fita daga gidan suma, sun d'auki titi ana tafiya cikin yan uwa, tafiya ake su dai ukun suna hira amma banda shi daya rufe kunnuwa da abin sauraro (Γ©couteur), cikin mintocin da basu kai awa ba sai gasu gidan roumji, kwanar da zaka shiga ta tabbatar da kai cikin garin sauran motocin suka shiga, amma me sai Ammar yayi tazarce zuwa titin tare da k'ara gudu, kallon kallo aka fara sai dai kowa ya kasa magana, Amar ne yayi k'arfin halin cewa "Ammar ina ga fa ka b'ata hanya."

Shiru yayi mishi sai ma k'ara birkaka giya da yayi, kallonshi Junaid yayi zaiyi magana Amar ya mishi alama daga nan kar yace komai ya kalleshi kawai, Jibril na ganin haka saiya tab'e baki ya k'ara gyara zama yace "Ai dai duk tsiyarshi ba siyar damu zaiyi ba ko? To fak'at."

Amar ne yace "Amma da dad'i musan inda zamuje."

Muryar Ammar suka tsinta yana fad'in "Budurwar taka tasan da zuwanka ne?"

Da mamaki Junaid ya juyo ya kalli yan uwa suma kallonshi suke, a hankali Ammar ya karkato kai zuwa ga kallon Junaid dan yasan dashi yake, kallonshi yayi shima yace "A'a bata sani ba, ita ai tana nan garin."

"Bata sani ba kuma shine zaka je har ka nemi aurenta? Baka tsoron ta d'auka ita ce rayuwarka hakan yasa ta rainaka."

Yanda yake maganar yasa Junaid ji kamar mahaifinshi colonel ne ke maganar, dan haka yayi shiru baice komai ba, tsaki Ammar d'in yayi yace "Ku tabbatar idan munje zamu dawo yau d'in nan, dan ba zan iya kwana wani gari ba haka kawai."

Tsuru tsuru sukayi da ido suna kallon juna, Jibril ne ya fad'a da k'arfi "Wai kana so kace yanzu can muka nufa?"

Yana sharara gudu yace "Hakane."

"Amma..." Kasa k'arasawa Jibril yayi sai Amar daya ce "Amma d'an uwa Hajia da su Abba ba zasu ji dad'i ba, kuma ya zamuyi doguwar tafiya irin wannan ba tare da mun sanar dasu ba?"

Ba tare daya kalleshi ba yace "To idan har yanzu nono ake baka na aje ka anan mana ka koma ka tsotsa."

Shi kanshi Amar saida ya murmusa kafin yace "Kafi kowa sanin dole zamusha fad'a wurin Hajia, haka ma Abba da Ummy."

Wata yar iskar dariya Ammar yayi ta gefen baki yace "Kuma kowa anan yasan waye za'a yiwa fad'an ba, ni ne, dan haka ban tsoron duk abinda zasu fad'a, na saba da jin hayaniyarsu a kai na dama."

Junaid da shi dai ya ma rasa farin ciki zaiyi zasuje neman auren masoyiyarshi? Ko kuma yaji ba dad'i saboda bala'in da zasu tarar a gida? Dan ya sani dole sai Hajia ta d'auki mataki a kansu musamman taji me suka tafi yi, hakan yasa ya kallesu yace "Amma dan Allah yan uwa mu bar tafiyar nan ta zama sirri, dan in Hajia taji ranmu zai b'ace, ni kuma bana so saboda ni wani abun ya faru daku marar dad'i."

Da wani kallo Ammar ya kalleshi yace "Sai me? Ta yanke duk hukuncin da zata yanke, ina da tabbas ba zata yanke mana hukuncin da zai cutar da mu ba saboda muna tare da shalelenta."

Ajiyar zuciya Amar ya sauke danya fahimci kamar abun na d'an damun Ammar d'in, wayarshi ya d'auka ya sake danna wa'azin da yake sauraro yana fad'in "Allah ne ya taimaki tsohuwar nan ba'a siyar da bindiga haka kawai, da tuni hankalin kowa ya kwanta a gidan nan idan na wurga mata alburushi a tsakiyar zuciya."

Junaid ne ya kalleshi yace "Kakar taka zaka kashe Ammar?"

Saida ya harareshi yace "Kakarku dai."

Amar ne cikin dariya yace "Ko ba komai fa ta haifi ubanka."

Nan ma juyowa yayi ya kalleshi yace "Ubanka dai ta haifa."

Tintsirewa sukayi da dariya, kallon Junaid yayi yace "Ina fatan dai kasan inda zamu je? Ba sai munje ba ka samu gillisuwa a tsakiyar garin da ba na ubanninmu ba."

Zaro ido Junaid yayi yace "Wallahi da gaskiyarka, ni duk cikin labarin da Iklima ta bani bata fad'a min sunan unguwarsu ba, amma bari na kirata saina tambaya."

Jibril ne daga baya yace "Yayi dai zakin soyayya, Allah dai ya kai damo ga harawa."

Juyowa Junaid yayi yana
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment