Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

tayi wanda ke tsaye yana kallon ikon Allah kafin ta kalli sauran kishiyoyinta, tab'e baki tayi sannan ta kalli Imran tace "Ina so ka auri 'yar waziri."

Da sauri Imran ya k'ura mata ido yana kallo, liman ya kalla ya kalli Abba dake tsaye har yanzu, kallon waziri yayi tare da matarshi da ya ga ita tuni harta washe hak'ora, a cikin ranshi kawai ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allahumma ajirni fi musibati, wak-lufli khairan minha."

Kallonta yayi yaga ta kafeshi da ido, babu yanda zaiyi haka yace "Na amince Umma, Allah yasa hakan ya zama alkairi a gare ni."

Sai lokacin ta nutsu ta zauna tana kallonshi tace "Kaga kenan sai a d'aura auren tare ko?"

A hankali ya kalli Abba da kamar ka k'yarta mishi ashana ya kama da wuta, d'auke kanshi yayi daga kallonshi saboda tsoro da kwarjini ya kalli liman, cikin girmamawa yace "Ku gafarce ni Liman, idan babu damuwa ko za'a iya d'aga auren nan har nan da sati d'aya, dan bana so daga rasuwar takawa ace nayi aure kuma har mata biyu a lokaci d'aya."

Da fara'a liman yace "Babu komai mai martaba, wannan ma shawara ce mai kyau, sannan sati kamar gobe ne idan da rai da lafiya, Allah dai ya nuna mana yasa alkairi."

Haushi ne yasa Abba barin falon rai b'ace inda Ammie ta bi bayanshi, harsu Imranatu da su Naseer ma bin bayansu sukayi, Abbas ma cikin kamala ya fita tare da Imran d'in inda suka k'ara tattaunawa akan lamarin, daga nan shima gidan kakannin na su ya nufo wanda suka rasu shekaru da suka wuce yanzu sai yan uwan mahaifiyarsu ne a gidan da iyalensu, tun a k'ofar gidan ya had'u da Abba da su Bashir cirko cirko suna kallon Abba daya jefa jakarshi a mota, da mamaki Abbas ya kalli Ammie da ita ma take kallonshi jiki a sanyaye yace "Ammie lafiya? Ba dai tafiyar ce ba?"

Cikin k'asa k'asa da murya tace "Nima tun d'azu abinda nake tambaya akai kenan ya min shiru."

Abba daya rufe boot d'in mota zai shiga mazaunin matuki ne yace "Duk mai tafiya ya zo mu tafi, wanda ba zashi ba kuma saiya zauna."

Aabbas ne yayi saurin cewa "Abba ka barshi to zan tuk'a mu zuwa airport d'in, bara na kira Sameera."

Da sauri ya shiga kai tsaye kuma d'akin da suke sauka ya wuce, kwance ya sameta akan gado, shi farko ma mamaki ta bashi daya ganta wai tana kuka, amma da yaji harda shashek'ar kuka take wai ita an mata magana sai ta ma bashi haushi, daga k'ofar d'akin yace "Malama ki taso mu tafi idan kin gama kukan to."

Shiru tayi kamar ba tasan ma dashi a wurin ba, cikin dakakkiyar murya yace "Nace ki taso mu tafi ko, Abba ne a waje ke jiranmu fa, kinsan kuwa a kan ki ba zan yarda na sake b'ata masa rai ba."

Ai kamar jira take sai ta d'ago cikin kuka ido sun mata jawur tace "Sai ka tafi mana, kasan ba zaka b'ata masa rai a kaina ba meyasa ma ka zo inda nake, ku tafi ku barni babu inda zanje ni."

Ko takalmi bai cire ba ya shigo d'akin ya d'auki gyalenta dake kan gadon ya rik'e d'aya hannun kuma ya kama damtse ya jata, tuburewa tayi tana fad'in "Wallahi ka sake ni, ka rabu dani na fad'a maka babu inda zanje fa."

Har sun fito fili gidan taga da gaske janta yake sai kawai ta kalli hannun nashi ta sunkuya ta gartsa masa cizo *(karo na biyu kenan😁)*, Abbas da saukar hak'oran kawai yaji baisan sanda ya saketa ba yace "Ashhhhh."

Kallon hannun yayi har jini ya kwanta abinka ga farar fata, a fusace ya kalleta da niyyar zabgeta da mari ma'ana tarihi ya sake maimaita kansa, sai kawai ta zabga da gudu ta koma d'akin ta mayar da k'ofa ta rufe, cikin k'arajin murya take fad'in "Na ce ba zanje ba, ka rabu dani mana ko ana dole ne?"

Dafe k'ugu yayi ya sauke ajiyar zuciya, a ranshi yake ayyana gaskiya badan suna cikin mutane ba, to fa daya b'alla k'ofar nan yau saiya tab'a lafiyar jikinta, dan har yanzu tana wasu abubuwan ne saboda tab'arar da ita da Ammie keyi, amma ba dan haka ba ai abinda tayi yanzu ko Raihan tayi shi saika mata tsinannen duka bare ita uwarta, wata uwar oda da Abba yayi daga waje yasa Abbas zabura ya juya ya kalli k'ofar, sake dawo da kallonshi yayi ya ga k'ofar a rufe, matsawa yayi jikin k'ofar yace "Zan tafi, idan kinga dama ki tabbata a nan, amma ki sani cizona da kikayi bashi kika d'auka kuma zan rama."

Daga cikin d'akin tace "Ka rama mana, ko kashe ni zakayi ba zanji ciwo ba indai har zaku tafi ku barni, dan wallahi saina ci uwar matar nan ko kuma na k'ona garin nan."

Wata zuciyar ta fad'a mishi hushi ba naka bane tunda kasan halin kayanka, a hankali ya saisaita nutsuwarshi ya d'an had'a kanshi da k'ofar d'akin yace "please Sam kar kiyi abinda bai dace ba, dan Allah na rok'e ki, kinji."

Cikin kukan daya tabbatar daga zuciyarta yake tace "Ba zan iya ba Abban Ameer, matar nan fa mahaifina ta kalla ta fad'a mishi mak'aryaci, kana ganin na zama 'yar halak idan har na rabu da ita?"

Wata odar ya sake ji wacce ta sashi sake fad'in "Meera ki bud'e k'ofar nan ki fito mu tafi, Abba yana jiranmu kuma kinsan shi ma ranshi a b'ace yake."

Ba tare data daina kukan ba tace " Ba zan biku ba Abban Ameer, kawai ku tafi ku barni anan."

Yasan tunda ta fara ba zata sauko da wuri ba, gashi kuma har ga Allah shi ma baida niyyar sake kwana anan saboda akwai muhimmin zaman da zaiyi a daren yau d'in, dan haka yace "Shikenan zan tafi na barki anan, amma ki min alk'awarin ba zakiyi fad'a da matar nan ba."

Shiru tayi sai kukan da take rerawa har yanzu, a hankali ya sake cewa "Please, do it for me, karki manta cewa ni mijinki ne, sannan kin min alk'awarin yin duk abinda zai faranta min raina."

Har yanzu shiru babu alamar zatayi magana, dan haka ya juya ya fita yana sake tattare gyalenta dake hannunshi, yana zuwa Abba bai bari ya amshi tuk'in ba, saida suka fara tafiya Ammie ta tambaya ina autarta? Yana fad'a mata tace ba zata taho ba ta kalli dake tuk'i kamar zaiyi ihu tace "Dan Allah ka aje ni na koma wajenta, gobe saimu dawo tare da ita."

Wani wawan birki ya taka daya sa su tsorata, sauke jajayen idonshi yayi a kanta wanda yasa gabanta dukan dubu uku uku, da sauri tayi k'asa da kanta hakan yasa Abba cewa "Ki zab'a to, idan har na ajeki anan sai dai kuyita zama ke da ita, tunda abun na ku iskanci ne."

Tun daga lokacin babu wanda ya sake magana a cikin su har suka isa airport suka shiga jirgi suka sake d'agawa, a haka suka kai gida tafiyar babu dad'i ko kad'an.

*Bayan tafiyarsu*

Tun bayan tafiyarsu da kwana biyu Ma'arufa da Ma'aruf suka zo Abuja a motar abokin Ma'aruf, shi da kanshi ya zo har k'ofar gidan wajen mai gadi yake tambayar ko yallab'ai yana nan? Kasancewar abubuwan da suka faru yasa Abbas d'aukar ma'aikata wanda suka san aikinsu yasa mai gadin cewa "Lafiya kake neman Alhaji?"

K'aryar da yayi cewa shi yaron yallab'ai ne yasa mai gadin cewa "To ka kira shi mana kaji inda yake."

Cikin son lauyewa yace "Eh kuma fa hakane." Daga haka ya juya ya bar k'ofar gidan, amma rashin sanin inda zai samu bayani akan Abbas na gari ko bayanan yasa ya fara sintiri a unguwar dan sanin ta yanda zasu fara, yana ganin lokacin da aka fita da yara idan zasu tafi school kuma yana ganin lokacin dawowarsu, haka kuma yana ganin shigar Saleem gidan wanda a wannan lokacin ke yawan sintiri gidan duk dan son samun kusanci da Raihan, idan zai zo haka yake kashe ma su Khalifa kud'i sosai sannan ya kawo musu da sunan tsaraba, faran faran yake nuna musu a fuska yayin da k'udirinshi kuma mummuna ne, kuma duk wani motsinshi Fadila ita ma a hankalce take da shi, sai dai har yanzu Raihan ta k'i yarda su keb'e daga ita sai shi bare harya fad'a mata wani abu da zai sa ta fahimta, a hakane washe gari kwana uku sai ga motar su Abbas sun dawo daga basraba wanda hakan ya wa Ma'aruf dad'i kuma ya hanzarta zuwa ya d'auko Ma'arufa a gidan da suka sauka.

Yaran sunyi farin cikin dawowar iyayensu da kakaninsu, amma basu ji dad'i ba da aka ce musu mahaifiyarsu bata taho ba, bayan sallah magriba Abbas ya shira tare da Abdul suka fita a motarshi, duk da yana sauri ya dawo dan akwai taron da zai shiga da compagninshi na motoci k'arfe *09:00* am saboda wasu manyan bak'in da suka zo bai hanasu tafiya a hankali ba suna hira, cikin minti ashirin suka isa asibitin kud'i wacce d'aya daga cikin yaran *ABBASIYA* ne mamallakinta, bayan sunyi parking ne Abbas ne ya kalli Abdul yace "Ka jirani ina zuwa."

Cikin mamaki da fargaban abinda ya kawosu asibiti Abdul yace "Dady lafiya ko? Waye ba lafiya? Kai ne?"

Murmushi ya masa yace "Bani bane, kuma kowa lafiyarsa k'alau, kawai dai na zo ganin wani ne a ciki."

Saida ya sauke b'oyayyar ajiyar zuciya yace "Ok Dady, a fito lafiya."

Jinjina kai yayi ya fita daga motar ya shiga ciki Abdul na kallonshi harya b'ace mishi, bayan ya shiga ne yake fad'awa *Dr Kabir* sun zo tare da yaron da za mishi gwajin jini, kuma kamar yanda ya fad'a baya so yasan da an deb'i jininshi ne dan ayi wani abu da shi, saida ya sake tabbatar mishi da babu matsala, saida yayi kira a waya ba jimawa ya datse kiran kafin suka fito tare, Abdul na ganinsu ya fito daga mota cikin girmamawa ya gaishe da Dr Kabir, amsawa yayi cikin raha kafin Abbas ya kalli Dr Kabir yace "Muje na gani ko?"

Da girmamawa yace "Yes sir, zamu iya tafiya."

Wani b'angare na musamman suka nufa inda Abbas yace Abdul ya zo su tafi, suna cikin tafiya wani mutum ya fito daga cikin gurin da zasu shiga, saidai mutumin a matuk'ar firgice yake wanda zaka ita gani k'arara, suna kusa da juna shi da Abdul sai kawai yayi saurin dafe hannunshi tare da sakin 'yar k'ara, da sauri Abbas ya rik'e shi yana kallonshi yana fad'in "Son lafiya? Meya faru?"

Murmushin yak'e yayi yace "Nothing Dady, wani abu ne naji ya soke ni a hannu na." Ya fad'a yana d'aga hannunshi tare da kallon wurin, da sauri dr Kabir ya matso yana fad'in "Oh my goodness, yana zubar da jini fa."

Juyawa Abbas yayi ya kalli mutumin da yayi kamar baisan tsiyar da suke ba saboda tafiyarshi kawai yake, da nuna reaction d'in takaici yace "Kabir waye wannan? Ina kuka samu mahaukata irin haka?"

Cikin jimami dr Kabir yace "Sorry sir, maybe ko ya karb'i result d'in shi ne kuma sakamakon ciki ne ya d'aga mishi hankali, ko kuma dai wani ne babu lafiya ana neman jini ba'a samu a lab d'in mu ba."

Kama hannun Abdul yayi suka shiga ciki da niyyar ya duba shi, suna shiga ya zaunar dashi akan kujera, wata yar roba ya d'auko mai haske wacce tsayinta ba zai wuce d'an yatsa manuniya ba ya tara jinin, Abdul na kallo baiyi tunanin komai ba, saida ya gama ya shafa mishi magani a wurin tare da rufe mishi ciwon dan dama komai a tsare take ba wani babban ciwo bane, fitowa sukayi duk da haka saida ya bashi magani dan kawar da duk wani zargi yace yasha saboda kar yayi zazzab'i ko hannun yayi kumburi, a haka suka d'auko hanyar dawowa gida, wannan karan Abbas ne ya tuk'a motar har suka iso layinsu.

Kamar yanda Salma ta fad'a musu haka suka aiwatar da komai, Ma'arufa na ganin motar Abbas ta danno cikin layin ta taho a guje ta shiga gaban motar har saida ta bugeta kuma taji zafi, take ta fad'i a wurin tayi kamar ta suma amma tana jin duk abinda zai faru, jakar kayan dake hannunta ce ta fad'i gefe, inda d'an kwalinta kuma ya rufe mata fuska, cikin tashin hankali Abbas ya fito tare da Abdul suna salati da sallalami, suna zuwa gaban budurwar da ke kwance suka ganta kamar babu rai, amma kuma babu alamar rauni a jikinta ko d'aya, a hankali Abdul ya sunkuya yana kiran " Baiwar Allah, baiwar Allah kinji ciwo ne?"

Jin shiru yasa Abbas d'agowa ya kalli Abdul sukayi ido hud'u yace "Ko dai ta mutu ne?"

Ido waje Abdul yace "Ban sani ba Dady, mu kaita asibiti to."

Da sauri ya d'ago ya juya ya ga babu alamar mutane a wurin dan unguwar silent ce, dan haka ya tak'ark'are zai kamata yace wa Abdul "Help me mu sata mota."

Da sauri suka kamata suka nufi mota da ita zasu saka ta gidan baya, k'aramin kallabinta ya fad'i k'asa fuskarta ta bayyana, dammm! Abbas yaji gabanshi ya fad'i saboda kallon fuskarta da yayi, har suka sakata a ciki Abdul ya d'auko jakarta Abbas bai daina kallonta ba, tabbas babu kama a fuska, amma dai yana jin kamar zai tuna wani abu a game da yarinyar, wani yanayi yake ji da bai iya fad'in takamaimai abinda yake ji ba lokaci gida, har Abdul ya saka jakarta bayan inda take zaune ya rufe Abbas na tsaye, Abdul ne yace "Dady ko ka santa ne?"

Da d'an sauri ya kalleshi, maimaita tambayar yayi a ranshi *ko na santa?* to a ina? Ya tambayi kanshi, cikin sanyin jiki da rashin kuzari ya rufe motar hakan yasa Ma'arufa farkawa, a zabure, saida ta juya da k'arfi ta ganta a mota sai kawai ta fashe da kuka da k'ok'arin bud'e motar tana fad'in "Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ku rabu dani karku cutar dani, dan Allah kuyi hak'uri kunji ku sauke ni anan, zan koma gidanmu ma."

Jin ta bud'e motar yasa su zagayawa wajenta da sauri suna son suji akan su wa take magana, fitowa tayi amma saboda iya shege saita durk'ushe alamar k'afar ta ba zata taku ba, Abbas ne yace "Kinga baiwar Allah, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, babu abinda zamu miki, asibiti ne zamu kaiki kinji."

Sake mik'ewa tayi tana kuka tace "A'a wallahi bana so, dan Allah ku barni na tafi kafin su riskeni a hanyata, wannan ba komai bane a wajena, nasha wahalar da tafi wannan ma kuma ban mutu ba."

Zata taka k'afar ta sake cijewa ta d'yangasa ta da k'yar tana cije baki, lura da hakan da Abbas yayi yasa yace "Saurare ni baiwar Allah, da alama k'afar ki ta bugu sosai, ki zo mu kaiki asibiti daga nan saiki fad'a mana inda zaki je sai mu kaiki."

Kamar gaske cikin kuka mai ban tausayi tace "A'a ba zanje ba, dan Allah ku barni na tafiya ta, na so ace had'arin nan da mukayi da ku ya zama silar mutuwa ta, amma gashi har ita kanta mutuwar ma bata son d'auka ta, ya Allah! Sai yaushe ne wannan azabar zata yaye?"

Yanda take magana da kuma yanda take rera kukan yasa jikinsu duk yin sanyin, a hankali Abbas yace "Baiwar Allah yanzu ina zaki je?"

Girgiza kai tayi tace "Ban sani ba."

Abdul ne yace "To ina ne gidanku?"

Kallonshi tayi cikin share hawaye tace "Da nisa, ni ba 'yar garin nan bace."

Abdul ne ya sake cewa "Kuma kin tabbatar baki san inda zaki je ba?"

Cikin kuka tace "Kwana na hud'u a garin nan ina yawo bansan inda zan nufa ba."

Abbas ne yace "To amma baki kowa anan ne?"

"Bana da." Ta fad'a a tausashe, da mamaki yace "Amma kinsan baki da kowa me yasa kika zo nan?"

"Bani ce na zo ba, k'addara ce ta kawo ni nan."

Ajiyar zuciya Abbas ya sauke yana tunanin abinyi, ya d'an jima a haka har Ma'arufa ta jawo jakarta tace "Sai anjimanku."

Ta fara tafiya da k'yar tana d'yangasa k'afa Abbas yace "Dakata baiwar Allah." Tsayawa tayi ta juyo shi kuma yace "Idan ba damuwa ki zo muje gidana, saina kira dr ya duba ki tunda kin k'i yarda muje asibiti."

Shiru tayi tana jin wani farin ciki na shigarta na samun nasara, dan a yanda suka shirya dama shiga gidan ne zai musu wahala, amma tana shiga babu abinda zai tsayar da ita aikin daya kaita kawai zata fara, jin shirun yayi yawa hakan yasa Abdul cewa "Ki zo muje kinji, kar kiji tsoro, Abbanmu mutumin kirki ne, ki d'auka daga yanzu har zuwa lokacin da zaki bar fadarshi zaki kasance cikin aminci ne."

Jim ta sake yi alamar tsoro kafin tace "Na yarda zan biku, Allah yasa va zaku cutar dani ba kamar yanda wanda na zo domin shi garin nan ya nemi cutar dani."

Tabbas akwai labari mai ban tausayi a cikin rayuwarta, amma kuma ba yanzu ne lokacin da zasu sani ba, dan haka ta taho ta shiga da k'yar kafin suma suka shiga suka tayar, bata fi tafiyar minti biyu ba suka tsaya k'ofar gidan, horn yayi mai gadi ya bud'e mishi k'ofa tare da musu barka da zuwa, suna ratsawa suka shiga Ma'arufa ta saki baki tana kallon gidan, cab'! Ashe dama wannan masarautar ya gina ya shiga shi da iyalinshi? Gaskiya gurguwar nan ta cuce mu da bata bari wannan ya zama ubanmu ba, da wannan tunanin da take taji motar ta tsaya sun fita, fitowa tayi ita ma inda tabi bayansu tana sake k'are ma gidan kallo, kai kasan maganar ma ace an kashe kud'i a wurin b'ata yawun baki ne, dan ko a k'asashen waje ka gida wannan gida dole asan ka tara masu gidan rana, ji tayi kamar zata fad'i a daidai lokacin da ta taka k'afarta a teress d'in falon, ga wani masifaffen sanyi da k'amshi daya daketa, a lokacin suna kan dinning suna cin abinci dan haka suka zarce can, a tak'aice dai ta samu tarba sosai a gurin kowa da kuma sakin fuska banda Abba wanda har yanzu ranshi a b'ace yake, abincin ma ya fito ci ne saboda yaran karsu damu da damuwarshi tunda haka aka saba, nan Ma'arufa ta zauna aka yi serving d'in ta ita ma tana ji kamar tace wayyo ta wayyo kanta, abincin dare d'aya amma kai kace wata walima ce tasa aka shirya, nan suka ci abinci aka gama sai cewa tayi zata tafi, duk yanda suka so da ita ta bari a kira likita ta k'i, aka suka hak'ura Ammie tace bai kamata ta tafi ba tunda dare yayi kuma tace bata san kowa ba, a haka Ma'arufa ta samu yanda take so ma'ana masauki a gidan.

D'aki ne dake k'asa kuma babu tazara tsakaninshi dana Sameera, babu abinda babu a ciki dan Sameera ce ke kula da shi saboda saukar bak'i idan sun zo daga basraba, duk da wani lokaci idan ta b'atawa Abbas rai yana cewa kishiya zai mata kuma ya sakata a d'akin, amma sai tace ai babu mai k'arar kwanan da zata yarda ta shigo mata gida, ko shi saita k'ona shi da ranshi idan yayi wasa, to fa anan Ma'arufa ta sauka ta samu tayi wanka ta canza kaya, kafin ta kwanta Ammie ta turo Raudat da magani wai ta shafa a k'afar ta ko taji dama dama, har Raudat zata fita Ma'arufa tace "Ya sunanki?"

Juyowa tayi da fara'a tace "Raudat."

Murmushi ta mata kafin tace "Zo zauna muyi hira lil sis."

Dawowa tayi ta zauna tana kallonta ita kuma tace "Ina Ummynku take ne? Ko kuma mahaifiyarku ta rasu kamar ni? Dan na fahimci wacce kuke kira da Ammie kamar granny d'in ku ce ko?"

Bud'ar bakin Raudat sai cewa tayi "...

*Sub'ul da baka.*

πŸ‘
12/06/2020 Γ  11:49 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ’ž _*MASOYA NA*_πŸ’•


_Bismillahir rahamanir rahim_

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_9_


Tunda Allah ya halliceta take zaune shekara goma sha bakwai a matsayin matarsa bata tab'a sanin cewa baya k'aunar ta ba irin yau, to mana baya k'aunar ta, dan rashin imanin daya darza mata ko dabba kayiwa haka kasan sai dai a d'auki gawarta, tabbas tasan akwai fyad'e a duniya, domin kuwa ita ta hanyar fyad'en ma ya rabata da nata budurcin, amma sanin azabar dake tattare da haka bata sani ba kam sai yau, babu inda bata jin yana mata zafi a jikinta, kama daga labb'anta wanda har cizasu yake tsabar mugunta zuwa kan k'irjin ta daya dinga lindasu kamar yana wankin kayan da suka shekara ba wanki, k'asanta kam ko magana ma ba ayi, duk da uwa ce ita ta haihu amma gyara da kular da take bawa wurin yasa yake zam-zam, to a yau dai kam ta tabbatar ya gama wangaleta ta yanda ko d'inketa akayi ba zata sake birgeshi ba bare ya moreta, cikin wannan hali da take taji ya kasheta da wani tattausan mari wanda ita a wurinta wata azabar ce ya biyota da ita, mik'ewa yayi ya fad'a ban d'akin ta ya tsarkake kanshi, yana fitowa ma jakar daya jefar ya d'auka ya d'ora akan gado ya bud'e ya d'auki kayanshi ya saka, sai lokacin ya kunna hasken d'akin ya kalleta.

Sam baiyi dariya ba saboda baya so ta samu damar sauke mishi tijara, amma yasan yau kam mai rabasu sai Allah, ko bata zage shi ba saita dake shi, har zuciyarshi yasan tana buk'atar taimako, amma danya d'an fara bata tsoro idan yace tayi sau d'aya ba sai ya maimaita ba yasa ya k'are mata kallo ya fita a d'akin, tana ganin haka ta tattara k'arfinta ta mik'e zaune da k'yar, kallon kanta tayi ta madubin dake gefenta tace "Ni zai yi wa haka? Lallai ma mutumin nan."

Misalin *09:00* na dare suna zaune dukansu kan dinning table, sanye take da doguwar rigar material mai kyau da tsada bleue light da d'an kwalinta, babu komai a fuskarta data shafa idan ka cire mai da lips a bakinta, tana hango Ammie zaune ta sake sangarta tafiyarta cikin shagwab'a ta k'arasa ta rumgumeta ta baya ta fashe da kukan sangarta, da sauri Ammie ta fara tambayarta "Auta ta lafiya? Waya tab'a min ke?"

Abbas da tunda ta fito yake kallonta, maganar gaskiya kallo d'aya ya mata ya ga har tayi wata ramar k'arfi da yaji, hatta tafiyarta ma ta kasa daidaituwa da kyau duk jikinta ya saki, wani haushi ne ya tokare masa mak'oshi yaji kamar ya mareta, shin bata lura da bak'uwar dake wurin bane? Idan ma bata ganta ba ai tasan Abdul na wurin yaron dake shirin zama sirikinta, kasa amsawa tayi yayin da yaran duk suka k'ura mata ido har da Ma'arufa dake mamakin karuwanci Sameera, Ammie ce ta gyara zamanta kan kujerar da nufin zaunar da Sameera kan k'afafun ta, amma suna had'a ido da Abba taga kallon da yake ma Sameera tasan duk yanda za ayi zai iya d'aukar wuk'a yace zai gagara mata, dan haka ta mik'e tsaye tace "Auta zo muje d'aki na ki fad'a min meya sameki, naga duk kin canza kamar ba ke ba."

Hannunta Ammie ta kama zasu fice sai idonta ya sauka kan bak'uwar su, yanzun ma kamar ganin ta da ita na farko sai taji gabanta ya fad'i tare da jin haushin yarinyar, wani tunani ne ya d'arsu a zuciyarta take a wurin, shin idan fa k'addara tasa yarinyar ta aurar mata miji? Kanta ta bawa amsa ta hanyar fad'in "Ai kuwa babu abinda zai hanaki k'ona gidan nan kamar yanda kike fad'a masa."

Da haka suka tafi part d'in su Ammie suka zauna falo, cikin rarrashi Ammie tace "Auta fad'a min meya miki?"

Turo baki tayi gaba ta
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment