Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanka yayi ya shirya cikin manyan kaya, maimakon ya fita saiya koma ya zauna yana jin kunyar fita, Sameera ma data ga har yara sun tafi makaranta amma bai fito ya karya ba yasa ta d'auki abun karin na shi ta shida part d'in shi, a falo ta ajiye a k'aramin center table ta nufi bed d'in shi, a hankali ta bubbuga amma shiru, sake bubbugawa tayi daga ciki yace "Please Sam ki barni dan Allah, na fad'a miki bana son takura."

Cikin muryar rarrashi tace "Dan Allah Abban Ameer ka bud'e min k'ofar nan, ka sani fa baka da wanda zaka fad'awa damuwarka sama dani, idan kuma ba zaka iya fad'a min ba to ka fad'awa Abba ko Ammie mana, amma kana gani gaba d'aya ka saka kowa damuwa, yara sun tafi islamiyya babu farin ciki saboda basu ga Dadynsu ba, Ammie tana tambaya ta lafiyarka k'alau? Bansan me zan ce musu ba."

Daga ciki ya amsa da "Ki fad'a musu bana jin dad'i ne kawai."

Sanin ba zai bud'e ba yasa tace "Shikenan, zanje na fad'awa Ammie komai ita idan ta zo nasan zaka bud'e, ba zan fad'awa Abba bane dan nasan idan ya zo zai karya k'ofar ne."

Da sauri ya taso yana fad'in "No Sam, please."

Jin yana bud'ewa yasa ta tsaya tana kallon k'ofar, yana bud'ewa sukayi ido hud'u da shi, damuwa ce karara kan fuskarshi, saidai ya k'i kallon fuskarta har yanzu, ajiyar zuciya ta sauke tace " Muje ka ci abinci gaya nan falo."

Juyawa yayi ya d'auko wayarshi da makullin mota sannan ya dawo, wucewa yayi kamar wani gunki harya zauna kan kujera, durk'usawa tayi gabanshi ta fara zuba mishi abincin, harta gama bai kalleta ba saida ta ajiye mishi gabanshi, cokalin ya d'auka zai fara ci amma sam baya da appΓ©tit, da k'yar ya daure ya rufe ido zai kai loma bakinshi wayarshi tayi k'ara, cike da rashin kuzari ya d'auki wayar ya duba, bak'uwar lamba ce dan haka ya k'i d'auka saida aka sake kira na biyu shi ma bai d'auka ba, amma dake Salma ta fad'awa Ma'arufa komai game da shi saita turo mishi text kamar haka _"Ka d'auki waya zamuyi magana ne, very importante."_

Bai wani damu ba dan in bai d'auki wayar ba dama text ake turo mishi, ana sake kira ya d'auka ya kara a kunne, muryar Ma'arufa ce a kunnenshi tana fad'in "...


*More comment plsss*
16/06/2020 Γ  13:22 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_16_

"Iya wani zunubi zuciyata ta aikata wanda ko a mafarki bai dace ace nayi ba bare kuma a zahiri."

Dafe k'irji Iya tayi tace "Ke 'yar nan! Me kika aikata haka? Allah yasa dai ba wani mummunan bai abu kikayi ba."

Alhaji da farko juyawa yayi tunda yaji tace sirri ne kuma bai kamata ace yaji ba, amma jin tace zunubi kuma saiya dakatar da shi, *zuciya* kuma *zunubi* murmushi yayi ya tsaya dan yasan duk inda zancen zaije ba zai wuce maganar soyayya ba, sai dai yana so yaji meyasa matashiyar ke tunanin zunubi zuciyarta ta aikata? Ko dai irin *wahalalliyar soyayyar* take? Soyayyar da babu sakamako mai kyau a cikinta saina wahala da dakon abinda baya anfanar da gangar jiki bare ita kanta zuciyar, dan haka ya tsaya dan jin matsalarta.

Kallonta tayi a marairaice tace "Iya mummunan abu ne kam, dan idan akaji zata min alawadai, wasu kuma zasu min dariya saboda ganin matsayina bai kai can ba, kuma nima nasan da haka Iya, jarabawa ce kawai wacce take neman tafi k'arfi na."

Cike da tsoro Iya ta dafata tace "Zeituna, a sanin dana miki ba kya da wasu miyagun halaye, amma maganganunki sun d'ugunzuma tunani na zuwa kwokwonto da son jin zunubin da kika aikata, fad'a min wane irin zunubi ne wannan."

Cikin zubo da hawaye tace "Iya na kamu da so, son wanda bai kamata ace na kamu da son shi ba, son mutumin da ba zai tab'a kallon ko da fuskata ba bare ya ji wani abu mai kama da so a zuciyarsa a game da ni, son mutumin da ko da ace 'ya ce ni mai gata yafi k'arfi na saboda wasu dalilai, Iya bansan ya zanyi ba dan Allah ki bani shawara?"

Cike da kulawa ta kalleta tace "Zeituna har yanzu a duhu kike saka ni, ki fito ki fad'a min matsalarki, kin manta na fad'a miki ke kamar 'ya ce a gurina?"

Gyad'a kai tayi alamar eh kafin Iya tace "Dan haka Zeituna karki sare, ke fa 'ya mace ce, kina da damar da zaki so kowa kuma kowa ma ya so ki, karki k'ask'antar da kanki har ki dinga ganin baki dace da samun soyayyar wani d'a namiji ba, ke nifa na yarda da yata wallahi, tsaye da kyau haka zaune da kyau, har waye zai ce ma baya sonki? Ai ki k'addara koma waye to shi yayi babban dace da har samu nasarar samun soyayyar ki, dan haka fad'a min naji waye shi?"

Cikin murmushin jin dad'i na yabon da Iya tayi mata ta kalleta sororo tace "Iya Abban Ammar ne, mijin aunty Sa'ada, lieutenant Hassan Gaga."

Har gaban Iya saida ya fad'i a wurin, zaro ido tayi lokaci d'aya kuma dan karta sanyaya mata gwiwa taji ba dad'i sai kuma ta wayance tace "Haba dai? Dama ai na fad'a miki koma wanene shi yayi dace ba ke ba, ke baki ga banbancin dake tsakaninku da shi bane?"

Da mamaki Zeituna ta kalleta tace "Wane irin banbanci Iya? Lieutenant fa nace miki na gidan nan, mahaifinsu Ammar."

Da yar harara ta bita irin ta yo shi d'in fa kafin tace "To sai me? Tabbas yana da kud'i da kuma ilimi, amma duk da haka akwai abinda ke ma kika fishi."

"Me kenan Iya? Cewar Zeituna da har yanzu take mamaki.

Murmushi Iya tayi tace "Kin fishi k'urucuya, Zeituna ke yarinya ce shi kuma tsoho, hakan zaisa ba zai iya juyawa soyayyarki baya ba."

Rufe ido Zeituna tayi irin wai kunyar nan tana fad'in "Kai Iya, Allah ba tsoho bane."

Waro ido Iya tayi tace "Iyeeh! Kaji min yarinyar zamani ko, to zan gani idan ba tsohon bane."

Had'e murmushin kan fuskarta tayi tace "Iya zan bar garin nan."

"Me? Barin gari? Meyayi zafi? Ke duk zafin soyayyar ne? Zeituna karki halaka kanki mana, ki bi komai a sannu kina kai kukanki wajen ubangiji, nima zan tayaki da addu'a." Duk iya tayi maganar ne tana kallonta.

Girgiza kai tayi tace "Iya ba wannan bane matsalar, matsalar kawu Mamu ce."

Nan ta kwashe komai ta fad'awa Iya wanda taji suna tattaunawa, kuka take sosai Iya na rarrashinta da cewa tayi hak'uri kar tayi saurin barin gari tunda babu inda zata je, sun jima nan zaune suna tattaunawa har Alhaji ya bar wurin cikin matuk'ar sanyin jiki, d'akin baccinshi ya shiga ya zauna kan kujerar da bata da maraba da gado yana tunani, hak'ik'a *so* wani abu da babu wanda ya bari, babu ruwanshi saiya shiga zuciyar babba komai girmansa ya kuma gaura shi a k'asa, haka kuma ya shiga zuciyar matashi komai k'uruciyarshi yayi maganin wautarshi da rashin hankalinshi, tunanin Zeituna da halin da take ciki ne ya tsaya masa a rai, kawun ta? Amma baya tsoron mahallicinsa? 'Yar d'an uwanka zaka nemi ka jefa rayuwata a harkar karuwanci? Da wannan tunanin Alhaji ya jima zaune ya kasa yin komai har saida ya samu tsayayya kuma gamsashiyar shawara sannan ya mik'e ya shiga wasu harkokin.

Da safe bayan sun karya Hajia tace lieutenant ya kira colonel ya sanar da shi gobe zasu je Goure neman auren Maryama, haka kuma ya kira gwamna ya sanar dashi an tsayar da auren 'yarsa Amna, yanda tace haka yayi hakan yasa colonel daya samu sararin aikin kiran da aka mishi ya d'auko mota ya kamo hanya tare da masu tsaronsa a biye da shi.

β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘

Tunda suka je asibiti ko aiki ya had'a su Ummy ta k'i yarda ko ido su had'a, ya fahimci hushi take dashi abinda ya tsana kenan a duniya, yawan sakawa Ummy na fushi dashi yasa yake k'ara jin haushin Hajia shima, har lokacin tashin shi yayi ya shirya ya fito, har zai wuce ta gaban d'akin inda ake kwantar majinyata saiya hangeta tana cirewa tsohuwar da yasa a kwantar da ita saboda tana neman agajin gaggawa, turo k'ofar yayi ya shiga babu sallama, juyowa Ummy tayi tana ganinshi ta d'auke kai, amma saboda dokar aiki da kuma ba kowa yasan d'a da uwa bane yasa cikin dakakkiyar murya a harshen fransanci tace "Docteur har ka fito? Na ga lokaci ya d'an ja kuwa."

Saida ya kalli robar ruwan ya kalli tsohuwar ya zauna bakin gadon kusa da tsohuwar yana kallon fuskarta yace "Kaka ya jikin naki?"

Kallonshi Ummy tayi, wato ba zai kulata ba dan ma ya samu ta mishi magana? K'wafa tayi a cikin zuciyarta ta juya da wani d'an kwano kwano kuma shi ba faranti ba a hannunta wanda ake zuba 'yan magunguna da allurai zata fita, ji tayi yace "Madame jira."

Tsayawa tayi ta had'e wani abu a mak'oshinta kafin ta juyo da fara'a a fuskarta, a lokacin kuma tsohuwar ta amsa mishi da "Jiki da sauk'i likita."

Fuskar dai a yabo ba fallasa yace "Ina fatan dai baki manta duk abubuwan dana fad'a miki ki kiyaye ba ko?"

Cikin murmushi tace "Ban mance ba likita."

Mik'ewa yayi ya dauk'i abun sauraron bugun numfashi ya dinga d'ora mata a k'irji, ajewa yayi akan farantin dake hannun Ummy ya d'auki abun awon hawan jini ya zura mata a hannu ya d'aure mata ya danna wani madanni, nan ma saida ya samu sakamakon da yake buk'ata kafin ya d'an duba idonta, katinta dake aje kusan kanta ya d'auka ya duba tare da wasu yan rubuce rubuce, takardar maganin daya bata tun farko ya sake nuna mata yace "Kaka ki tabbatar an siyo wannan magungunan fa."

Gyad'a mishi kai tayi tace "Yaron nawa ma yana zuwa yanzu zan bashi ya siyo."

Murmushi ya mata wanda ya ba Ummy mamaki, tana tsaye tana kallon shi ya d'an dafa kafad'ar ta yace " Da kyau kaka, Allah ya sawak'e ya kara afuwa."

Kallon Ummy yayi yace "Madame idan yaron nata ya zo ku tabbatar kun bashi ya siyo maganin, idan ya kawo ku nuna mishi yanda zatayi aiki da shi babu jinkiri, daga bisani sai ku sallame ta, amma zata dawo nan da sati biyu."

Ummy ita tasan kawai bura uba ce yake mata, amma haka ta daure tayi murmushi tace "Ok docteur, za ayi yanda ka ce."

Wani d'aure fuska yayi yace "Haka nake so."

Cikin takon k'arfi ya fita ya shiga motarshi, da kallo tsohuwar ta bishi tayi murmushi tace "Allah sarki likitan babu ruwanshi, Allah ya mishi albarka."

Kallonta Ummy tayi a ranta tace "Bala'i, tsohuwa dan baki san shi bane shiyasa kika ce haka."

β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘

Ana idar da sallah la'asar Hamna ta shirya cikin kayan makaranta da kuwa jakarta, saida ta sake jadaddawa Amna tsarinsu tunda ita ba zata tafi ba, a tsorace dai Amna tace "Dan Allah karki jima kiyi sauri ki dawo, kinsan fa in suka gane zan sha masifa a gurin Hajia."

"To naji dan Allah." Ta fad'a alamar matsuwa, fitowa sukayi falon Hajia na zaune, ganin kayan makaranta a jikinta yasa Hajia ta bita da kallo kawai bata hanata fita ba, Amna dake nesa da Hajia zaune tana kallo ne ta kalla tace "Ke kuma ba zaki je makarantar ba ne kome?"

Murya a tausashe tace "Hajia yau zamuyi hadda ne na alk'ur'ani, ni kuma kwana biyu kenan bana tab'a Alk'ur'ani shiyasa ba zan je ba."

Shiru tayi mata Hamna kuma na jinsu amma ta fice abinta, a motonta ta tafi ba jimawa ta isa gidansu k'awarta *Nafi*, tana zuwa ta cire kayan makarantar nan ta shiga tsarawa kanta kwalliya, sun d'auki lokaci suna shiryawa kafin suka gama suka d'auki hotuna, yamma lik'is suka hau moton dan zuwa wajen kamun k'awarsu da akeyi yau wanda gobe ne d'aurin auren, a cikin *hotel jangwarzo* ne dan haka basu wani jima ba suka iso.

β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘

Sai bayan sallah azahar ya dawo gidan bayan ya ci abincinshi a waje, dan rabon da yace ya ci abincin gidan nan harya manta, yana zuwa kayan jikinshi ya cire ya watsa ruwa ya kwanta, ba jimawa kuma bacci mai dad'i ya d'auke shi, kiran sallah ne ya farkar dashi dayake akwai babban masallaci wanda ya kasance na gidan ne dake kallon juna da gidan, a kasalance ya tashi yayi alwala ya tafi masallacin ya dawo, yana zuwa ya samu kira a wayarshi rutu-rutu, baiyi tunanin mayarwa ba ya nufi ban d'aki dan yin wanka, wani kiran ne ya sake shigowa wayarshi ya dawo ya d'auka yana tsaki, daga can b'angaren aka ce "Anyi walk'iya mun ganku, yanzu Ammar mu zakawa rashin mutumci?"

Saida ya zauna bakin gadon cikin muryar bacci yace "Idan kana son gani na ni ko ba ayi walk'iya ba zaka iya haskani da fitila, rashin mutumci kuma yanzu na fara darza muku shi, kafin nan fad'a min dalilin kiran nawa?"

*KB* da yasan halin kayanshi ne yace "D'an iska kana nan da halinka, indai za'a fad'a to sai ka fad'a kai ma."

Kamar bashi da lakka yace "Ai ni na wuce ka kirani d'an iska, sai dai d'an rai-rai (sahara), malam muryarka na damuna fad'a min meya faru."

Kb ne yace "Domin Allah Ammar tun yaushe muka fad'a maka da bikin *Abdullahi* ya taso? Tun shekaran jiya aka fara k'unshi amma bamu ga k'eyar ka ba, yanzu ma muna shirin tafiya wajen kamu ne nace bara na kiraka dan naga iskancin naka ba mai k'arewa bane."

Yana d'an tattausa wuyanshi ya lumshe ido yace "Ni ne zaku gayyata wani wai k'unshi? Kawai muyita yawo a rana wai zamu je d'aukar abinci kamar 'ya'yan da aka haifa lokacin hamada (yunwa), sannan yanzu kamun me zanje? Idan naje uban wa zan kama? Amaryar ko ango? Kaga malam nifa bana cikin wannan salon 'yan banzancin, ranar d'aurin aure naje na shafa fatiha dani."

Tab'e baki Kb yayi yace "Shikenan, idan baka zo ba ai nasan 'yer uwarka ta zo ita, dan duka k'unshin da akayi na ganta har ma tana kirana da yayanta, na d'auka ma kai ka fad'a mata ni abokinka ne."

Ba tare daya bud'e ido ba ya d'an saka hannu ya murzasu yace "Saboda ubanka ne shugaban k'asa saina zauna ina fad'awa mutane kai abokina ne? Ni na ma tab'a fad'a maka ina da yer uwa a duniyar nan?"

Jin dariyar da Kb keyi yasa ya kashe wayar ya mik'e ya shiga wankan shi, amma yana shiga sai zuciyarshi tace mishi "Wacece kenan?"

Tunani ya fara kan wacece a cikin yan matan, wani dogon tsaki yayi jin zuciyarshi ta mishi katsalandan da fad'in "Indai ba Hamna bace can su suka sani."

Tsakin da yayi yasa yace "To ina ruwanka inma ita ce? Can ta k'arata mana, wannan dama ai kullum cikin yawon biki da gidajen k'awaye take."

A haka ya fito daga wankan ya shirya cikin bleue riga da bak'in wando, yana d'aukar makulli da waa ya fito ya tunkari wurin aje motoci, amma sai ji yayi yana son yasan wacece a wurin taron, dawowa yayi ya shiga yar farfajiyar da zata sadaka da falon Hajia, tun anan ya ga Jamila tare da Zeinabu da kuma Soueiba da kaka Husseina, wucewa yayi yana fad'in "Barka."

Inda Jamila ta bishi da "Ina wuni yah Ammar."

Kamar bai ji me tace ba haka yasa kai falon, yana shiga kuma yayi daidai da fitowar Umaima da alama bata jima da dawowa daga aikin ba wanka ne tayi, ita ma bai sake bi ta kanta ba duk da tana fad'in "Ina wuni yah Ammar."

Saida ya wuce ta murgud'a baki tace "Surukantaka da irinka ai asara ce wallahi."

Hajia na zaune kan kujerar da kullum anan kake ganinta tana kallo da remote a hannunta tana canza tasha, kallon tvn yayi ya ga film ne na turanci tsagwaronsa amma ko ta kafe tvn da ido, murmushin jin haushi yayi ya wuce yana fad'in "Ki ba kanki lafiya, ke ba ji kike ba kuma ki tsura musu ido kamar mai ganewa."

Da kallon banda lokacin ka ta bishi tace "Uwarka nake jira ta zo ta fassara min."

Wayarshi dake hannunshi ya nuna mata yace "Na kira miki ita ne tayi sauri ta k'araso?"

K'wafa tayi dan tasan yanzun sai ranta ya b'ace a banza a wofi, ganin ya tunkari sama inda d'akin su Amna yake yasa ta d'aga murya tace "Kai me zaka je yi musu a d'aki? Jarabarce ta motsa ko? To fito daga nan kaji na fad'a maka, duk gaggawar ungozuma ai ta bari a haihu."

Wani murmushin shak'iyanci ya sake mata yace " To Hajajju mutan makka banda abinki jaraba ta motsa ai dole na samu inda zan d'ura ta, addu'arki kawai nake buk'ata ina zurawa na zura kan daidai ta yanda ba zan fito daga d'akin nan ba saina samo miki sabon shalele, ko ba komai kinga kya rabu da waccen gardin da kike kira shalele."

Hajia rasa amsar da zata bashi tayi sai kawai tace "Zan iya d'aga maka k'afa kan duk iskancin da zakayi a gidan nan, amma wallahi karka kuskura kayi gigin kawo min d'an gaba da fatiha, ba zan lamunci haka ba, kuma dama na jima da sanin cewa kana hassadar soyayyar da nakewa shalele, ka ka ci kanka wallahi."

K'ala baice mata ba ya k'arasa ya bud'a k'ofar d'akin kawai ya shiga ba tare da neman izini ba, Amna da fitowarta daga wanka kenan tana zaune bakin gado zata shafa mai, duk da towel d'in jikinta kakkaura ne kuma ya sauko har kan gwiwarta, amma tsananin tsoratar da tayi ba kad'an bace, yanda ya shigo d'akin take mamaki, a saninta dai anyiwa samarin gidan kashedi (interdit) da shiga d'akin yan matan haka kawai, suma kuma yan matan basa zuwa b'angaren su saida dalili, shi kanshi saida ya shigo d'in yaji yayi nadamar shigowa, dan kuwa mutanen k'asan nan da Hamna ta so tayarwa tunda safe sune yanzu Amna ta tayar daga kwanciyarsu, amma dayake masifa ce ta kawo shi sai yayi kamar bai wani damu ba ko yasa abun a kai, k'arasowa yayi ya rufe k'ofar ya tsaya gabanta, Amna data kasa tashi sunkuyar da kai tayi gabanta na bala'in bugawa da k'arfi, wata irin tsayuwar rashin d'a'a ce ya mata ta yanda da zai sunkuyo to fa kansu na iya had'uwa, tun daga nan ya tabbatarwa kanshi da Hamna ce dan wani lokacin baka iya tantance su duk da akwai d'an banbanci amma ba mai yawa ba, amma danya kamata sai yace "Ina Kankana."

Wani irin zabura da taji zuciyarta tayi yasa ta d'an dafe k'irjin ta ta rintse ido, cije hak'oranta tayi a ranta tace "Shikenan Hamna kinja min masifa ina zamana, da nasan shi zai nemeki wallahi da ban yarda da abinda kika fad'a min ba, ohh ni, *tawa ta same ni*."

Wani tsinannen rank'washi (k'ozo) ne daya sakar mata a kai har saida taji jinin al'adarta ya bulbulo da k'arfi, cikin d'aga murya yace "Ba dake nake magana ba, 'yar banza kai mai zubin mage, kina ji ina magana zaki min shiru." Dafe kai tayi ta fashe da kuka bilhakk'i tana fad'in "To yah Ammar ai..."

Shirun da tayi yasa yace " Ai me? Fad'i ina jinki ko na cire miki hanci yanzun nan."

Cikin kukan tare da d'aga murya dan ta samu mai kawo mata agaji tace "Ni ce fa."

Sunkuyawa yayi ya lek'a fuskarta hakan kuma yasa har saida numfashinsu ya gauraya, dayake ta gama wanke bakinta ne ta fito kuma ta d'auki turaren baki mai fitar da k'amshin ayaba yasa kamar ya cabki bakinta ya tsotsa, ita kuma d'an kawar da kanta tayi gefe, cikin wata irin murya yace "Ke ce kankana kike nufi?"

D'aga kai tayi da sauri alamar eh, jinjina kai yayi dake nufin ok zaki sha mamaki, mik'ewa yayi daga sunkuyon yasa hannu ya fara cire d'amarar k'ugunshi (bel, ceinture), a matuk'ar firgice ta kalleshi dan ganin me yale shirin yi, yana zage shi gaba d'aya ta zabura ta mik'e zata zuba a guje, hannunta ya rik'o tare da wurgata kan gadon ta fad'a kwaram, a lokacin ne kuma idonshi suka sauka kan jinin daya d'an fara b'ata zanin gadon, dan ko audigarta bata saka ba ta tsaya shafa mana, wani tarrr yayi da idonshi ya nuna mata wurin da yatsa yace

"Ita sarauniyar shan kankanar nasan dai aman ruwa takeπŸ™†β€β™€οΈ, ke kuma kenan na jini kike?"

Girgiza kai tayi ba tare data daina kukan nan ba, sake dungure mata kai yayi yace "Dan ubanki ki min shiru, magana ce fa kawai muke ban kai ga dukanki ba."

Tsaf ta had'iye kukan tana wik'i-wik'i da ido, d'orawa yayi da "Amna ni k'aramin yaro ne?"

Kai ta girgiza mishi da haka yace "To meyasa zakiyi tunanin raina min hankali? Shin kinsan tayaya d'azu nasan cewa kina fashin sallah?"

Ita dai da kai kawai take amsa mishi, ci gaba da cewa yayi "Shine har zaki nuna min kanki a matsayin kankana, kenan ni sakarai ne mahaukaci? Haka ranar ma tayi shiga irin taki taje min dan na bata wayarta, shine yanzu ma ta fita daga gidan da niyyar idan wani ya tambayeta kice ita ce anan ke kuma a can."

D'aga belt d'in yayi da niyyar tsorata ta kawai, amma Amna da tsoro ya mata waya sai tayi wuf da Ammar ta rirrik'e rigarshi ta d'ora kanta a k'irjin shi tana fad'in "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri."

_Ai ko malam ko uba zai dakeka kayi wuf da shi to ka gama dasu aradu, bare wani Ammar😏, nifa wannan karan bana yinka._

Sanyin da jikinshi yayi yasa shi sakin belt d'in bai shirya ba, lumshe ido yayi saboda tula tulan nonuwanta da suka zauna daram kan k'irjin shi, take yaji daga k'asa anyi wani ziiiiiii da yasa shi cewa "Ya salam."

Ba tare daya bud'a ido ba cikin kasalalliyar murya yace "Amna ya kike so dani? Na mutu?"

Jin wata tattausan murya da bata tab'a ji ba yasa ta d'ago kanta, da sauri ta matsa baya ta saki rigarshi a d'an tsora ce, k'asa tayi da kanta cikin muryar kukan shagwab'a tace "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri karka dake ni, wallahi ba laifi na bane, Hamna ce tace nayi inba haka ba wai saita ja min matsala wajen Hajia, kuma ni nasan zata iya saboda tana yin kamar ni wani lokacin tayi abu."

D'ago kai tayi ta kalleshi, duk da wani sabon yanayi ta gani a tare dashi, ya wani saki ido dabaki yana kallonta kamar ya fizgota jikinshi amma haka ta daure ta sake marairaicewa tace "Kayi hak'uri dan Allah, ba zan sake ba."

Belt d'in shi ya nuna mata da ido yace "Mik'o min."

Da sauri ta d'auka amma da zata mik'a mishi saida ta ja baya, karb'a yayi tana kallo harya mayar a k'ugunshi, cikin amon muryar data kasa fahimta yace "Ai nasan inda take, zanje can na sameta na yanka mata kazar wahala sannan na d'auko ta."

Juyawa yayi da sauri harya bud'e k'ofa kuma ya juyo ya kalleta yace "Wallahi na bada baya kika kuskura kika kira kankana kika fad'a mata ina zuwa, hummm."

Saida ya gyara tsayuwa yace "Kinsan me zan miki?" A hankali ta girgiza kai, ba yanayin wasa a fuskarshi yace "Wallahi zaune zanyi na b'ata lokaci wajen cire miki duk sinadaran dake jikinki, kin gane?"

D'aga kai tayi kawai almar eh amma ba tare data fahimci sinadaren da yake nufi ba, yana fita ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu da shine ake nufin nayi rayuwar aure? Amma tayaya?"

Yana fita baibi ta kan Hajia ba ya fice daga gidan ya nufi hotel d'in dan d'aukar Hamna...

*BΓ©bΓ© Abdul latif ba lafiya, addu'arku masoya*πŸ‘
17/06/2020 Γ  11:45 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*



Please Login or Register in order to submit comment