Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

da fad'in "A'a dakata haka malama, ya isa kinji ko, addu'ar ki ba zata sani jin haushi ba domin kuwa ke Allah ya fara tsinewa kafin mu, dan haka ai ba wani abun kunya bane, hakan ma shine zai tabbatar da mun gada kenan ga uwa ga uba, sannan naji dad'in sunan da kika kiramu da shi na shegu, wannan shine asalin sunanmu dama, amma daga yau karki k'ara mana katsalandan a rayuwarmu kamar yanda a lokacin da muke yara muna kallonki kina rayuwarki babu wanda ya saka miki ido, ina fatan kin fahimta."

Juyawa tayi ta shiga d'akin Salma na fad'in "Dan ubanki ai ni duk iskanci na banyi da wanda yake d'an uwana ba, har nayi yawon bariki na gama ban tab'a nema da wanda ya sanni ko na sanshi ba, amma kuma fa? Ciki d'aya fa kuka fito, ni ce nan na haifeku."

Ma'aruf ne ya tab'e baki yayi yace "And so what dan ke kika haife mu, naga dai abun kunya ba kanmu ne aka fara ba bare ace zai k'are a kanmu, ke tab'argazar da kikayi ma waye zaiyi irinta a duniyar nan, shine har zaki wani mana fad'a sai kace hallitarmu ki kayi."

K'wafa yayi yana shirin shiga d'akin ta dakata da kukanta tace "Amma ai duk iskanci na ni ban tab'a iskanci da wanda ke d'an uwana ba ko da na nesa ne bare kuma shak'ik'i, kawai ku dai ku ce taku tsinuwarce tafi tawa."

"To sai me? Idan har mu tsinannu ne ke fa? ke da kike cin amanar mijinki da amininshi, kika haifi yara har biyu a gidanshi da sunan nashi yaran dan kawai ki ci gadonshi, yanzu ba gashi nan ba wa gari ya waya? Ba kud'in, ba farin ciki, ba jin dad'i."

Salma kam kallon Ma'arufa kawai take dake fad'a mata magana son ranta, Ma'aruf ne ya d'ora da "Kula ba k'afa ba, sannan duk fitsararmu bamu tab'a neman jinsinmu ba, amma ke fa? Kinyi tarayya da 'yan uwanki mata ma saboda lalacewa, a haka har zaki mana wani wa'azi."

Cikin kuka ta dafe k'irji tace "Ina uwarku kuke fad'a min duk abinda ya zo bakinku? Wallahi kunyi asara."

Ma'arufa ce tace "Hum! Wannan kuma ke ta shafa."

Ma'aruf ne yace "Kwad'ayi ai mabud'in wahala ne dama, yanzu gashi baki samu komai ba sai wahala da kike, abinda zaki ci ma gagararki yake yi, shi kuma Abbas yana can da matarshi da yaransu cikin farin ciki sun ma manta da wata hallita wai ita Salma kamar dai yanda suka manta da wannan rub'abb'en margayi Abban."

Cikin jin haushi da takaicin ambatar sunan Sameera tace "Amma ai har yanzu Abbas bai sake ni ba, tunda abinda ya faru ya faru bamu sake had'a ido ba, dan haka ni nasan bai sake ni ba har yanzu."

Wata dariya Ma'arufa tayi tace "Kaji matar nan da hauka, to tsufanki ne ke nuna miki har yanzu ke matarshi ce? Domin Allah ke yanzu ko mata sun k'are a duniya me zaiyi da ke."

Ma'aruf ne yace "Inhar gaske ne ma bai sake ki ba to ina inada tabbacin bai sake ki bane saboda yana so sai kun had'u ido da ido, dan nasan sakin da zai miki sai ya kai dubu biyar."

Dariya suka dinga yi mata har Ma'aruf ya saka rigarshi ya nufi k'ofar fita, ta gaban Salma ya bi inda take zaune k'ofar shigowar saboda abinda ta riska, ledar garin kwakwinta da sugar ya kalla yace "Gurguwa gari zaki sha? Bari idan na fita zan siyo miki kifi ki d'an ci dan nasan anjima ba'a had'u da abu mai lami ba."

Ma'aruf data zauna kan turmi ce tace "To ina za ta ga abu mai lamin, ai ta gama cinye nata rabon tun gidan waccen mutumin."

Ko da ya fita Salma ta yunk'ura da sandarta ta zauna kan tabarmarta, kallon Ma'arufa tayi tace "D'auko min kofi da cokali a d'aki."

Shiru Ma'arufa tayi kamar ba taji ta ba har saida tayi niyya ta mik'e ta d'auko mata, kawo mata tayi daga tsaye ta jefo kofin ta koma ta zauna, nan ta gyara kwakin tana ci tana kallon Ma'arufa cike da takaicin wayar da take jin tana yi da saurayi wacce batsa tafi yawa, saida tayi maganin yunwar dake damunta kad'ai nutsuwarta ta dawo jikinta, a hankali maganganun yaranta suka dinga dawo mata, sai kawai taji bata buk'atar tsayawa da yak'in daga nan, gashi tun ranar da *Tahir* ya harbe mata k'afa ta gama jinya ta dawo k'auyen nan bata sake ganin Abbas ba, tasan ba zai iya ci gaba da zama da ita ba, sai dai kuma bata san a wane matsayi take ba tunda bakinshi da bakinta bai had'u ba har yanzu, ga kuma tunanin Sameera wacce ta raina amma yanzu ta tabbatar ita ce sarauniyar gidan Abbas kuma sarauniyar zuciyarshi, da wannan tunanin ta riski wunin ranar, har saida zuciyarta ta sake durmiyata kan wani zunubin kuma, sai dai wannan karan ba ita za ta yi fad'an ba, tunda tana da yara kamar Ma'aruf da Ma'arufa, tana da yak'inin cewa su Abbas ba zasu iya shaida su ba tunda sun girma duk sun canza daga yanda suka san su, sai bayan magriba Ma'aruf ya shigo gidan da ledoji a hannu.

D'aya leda ya mik'awa Salma yace "Alk'awarin dana miki ne, ki ci kema kiji dad'i."

Sauran ledar kuma kujera yar tsugunno ya janyo ya zauna gaban Ma'arufa ya bud'e yace su ci, kallonshi Salma tayi ta kalli ledar taga gasassar zabuwa ce da kuma balangu, sai lemu mai sanyi guda biyu alamar dai shi da ita, aje ledarta tayi gefe d'aya tana kallonsu suna ci tace "Ku saurare ni da kyau muyi magana."

Ma'aruf ne kad'ai ya iya ma kallonta kuma take ya ci gaba da cin abincinshi, cikin d'aga murya tace "Da ku fa nake magana kuna jina ku min banza."

Ma'arufa ce tace "To wai ba kunne ne ke ji ba, ki fad'a mana amma ki tabbatar serious magana zaki fad'a."

"Akan Abbas ne." Ta fad'a tana kallonsu dukansu, kallonta sukayi suka ce "Kamar ya Abbas, meye faru?"

Ba alamar wasa tare da ita tace "Ku yanzu kuna son ku k'arar da rayuwarku a haka kamar ni? Ni a wahalce ku a wahalce, abincin ma sai nayi bara na samu ke kuma sai kin sayar da matancinki, kuna ganin wannan ita ce rayuwar daya kamata mu ci gaba da yi? Ku tuna fa kuna yara irin gata da soyayyar da Abbas ya nuna muku, amma haka ya rabu da ku yanzu gashi kuna cikin wahala, shin ba kwa jin kuna son kuyi wani abu a game da haka?"

"Kamar me fa?" Cewar Ma'aruf kafin ya d'ora da "Duniya na da tabbacin mu ba 'ya'yansa bane bare mu ce muna da gadonshi, ke baki kyautata masa ba bare muce zai kallemu da mutumci ko dan zaman tare da akayi, duk da dai mutum ne mai son taimako musamman matasa, amma bana jin zai iya taimakonmu saboda abinda kika masa."

Kallonsu tayi da shu'umin murmushi tace "In tambayeku mana? Shin ya zakuji ace yau kun wayi gari kun samu million ashirin ashirin naku na kanku?"

Ma'arufa ce ta saki wata k'ara tace "Wooo! Ai wallahi Hajia kud'in nan suka shigo zaki sha mamakin irin rayuwar da zanyi."

Ma'aruf kam cewa "Ai gurguwa wannan kud'in suna zuwa ni da zama nigeria kuma sai dai in nayi sha'awa kawai insa a nuna min ita ta babban majigin allon kallona dake mak'ale a gadona na alfarma."

Cike da makirci Salma tace "Dan haka kuwa zaku samu wannan kud'in cikin sauk'i inhar kukayi abinda zan fad'a muku yanzun nan, ku zaku huta, ni ma kuma zan huta."

Ai da sauri suka gyara zama suna fuskantarta suka ce "Muna jinki Hajia."

Dalla dalla Salma ta musu na abinda take son su aiwatar duk da kuwa had'arin shi da kuma muninshi, su kuma dayake magana ce ta kud'i sam basu duba komai ba musamman Ma'arufa wacce ita ce zata fi shiga had'ari tare da rasa wani abu na ta, amma a wajen su wannan ba damuwa bane idan da kud'i, saida ta gama kitsa musu Ma'aruf ya bushe da dariya yace "Kai gurguwar nan har yanzu ashe kanki da sauran wuta, ai shirin nan yayi d'ari bisa d'ari wallahi."

Ma'arufa ce ta wani girgiza gaba har saida k'irjin ta suka motsa tace "Alaji yaka ganni gaban *oga Samuel* da millon ashirin a account d'ina? Kaga a ranar zan samu 'yancina kuma zai zama kawar bawa na."

"Gaskiya kam, duba kiga yau kafin ya barmu mu taho shege kamar wani ubanmu, harda jaddada mana yake kar mu wuce gobe."

Salma ce tace "Waye kuma Samuel? Kwartonki ne ko?"

Cikin nuna rashin damuwa tace "Um um, wanda muke zaune a gidan shi ne, tunda ya bud'a ido ya ga nice hasken gidanshi ni ke kawo mi shi manyan costumer yake nanik'e min, baya so ina nisa dashi ko nan da can, kuma dama lokacin da muka je gidan ba kud'in d'aki ne damu ba, shiyasa saiya bamu d'aki a cewa shekara zan biya shi, duk da yanzu yasan ina tare da mutanen da zasu iya biya min kud'in, amma baya so na bar gidan ne shiyasa baya karb'ar kud'in har yanzu, kuma yayi hakane saboda wanda suke zuwa gurina suna masa alfarma sosai a siyasance, a ikonce da kuma arzik'ance, sannan ga kyautar da suke mishi ta fitar hankali."

Tab'e baki Salma tayi tace "Inhar kukayi abinda nace to ba Samuel ba, har wad'anda ke neman naki zaki iya had'a kafad'a da su."

Ma'aruf ne yace "Ai ki kwantar da hankalinki, kamar anyi angama ne, goben nan muna komawa zamu fara shirye shiryen komai yanda ya dace."

"Da kyau." Cewar Salma tana murmushi, haka sukayi kwanan farin ciki da tunanin samun kud'i kamar wanda suka bayar ajiya, haka gari ya waye bayan Ma'aruf ya samo musu abin kari sun gama suka shirya komawa inda suka fito, abun mamaki saiga Ma'arufa ta dunk'ulo har dubu uku ta bawa Salma ta rik'e kafin su sake dawowa, Ma'aruf kuma ya bata k'aramar wayarshi saboda su dinga kirantatana sanin abinda ke faruwa cikin gaggawa, haka suka d'auki hanyar komawa zaria kafin su wuce abuja.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Zaune yake a farfajiyar gida akan kujera yayi shiru sai dai idonshi jawur suke da wani hoto a hannunshi yana kallo, ba zai iya tantace abinda yake ji ba a game da wacce ke cikin hoton, sai dai ko ba komai yasan har yanzu yana matuk'ar sonta, amma abinda ta mishi na k'ona masa rai sosai, haka kuma wata zuciya na tuna mishi da cewa ba laifin ta bane, laifin ta d'aya shine b'oye mishi da tayi harta aureshi da cikin wani a jikinta, yana wannan halin ne k'annan shi dake bi mishi ya shigo gidan kuma kai tsaye wajen ya nufa, tsaye yayi yana kallonshi ganin hawaye na neman zubo mishi yasa yayi gyaran murya, da sauri *Abbacar* ya kalleshi tare da sanya hoton aljihun gaban rigarshi yana k'ak'aro murmushi yace " *Saleem* kai ne? Yaushe ka shigo? Ai banji shigowarka ba."

Murmushi yayi ya rumgume hannayen shi yace "To dama ina zaka ji bayan *Zeenat* ta tafi da gaba d'aya nutsuwaka."

Murmushi ya sake yi da bai kai ciki ba yace "Hmmm."

Sunkuyawa yayi ya dafa cinyarshi yace "Yaya Abbacar wai sai yaushe wannan tunanin zai k'are ne? Baka tunanin kana shiga hakk'in iyalinka dayawa? Yanzu da ace *Sayyada* ce ta fito ta sameka da hoton tsohuwar matarka wacce ta cutar da kai ta ruguza mana farin cikinmu tayi d'aid'ai da rayuwarka, me kake tsammanin zata ji a ranta?"

Murmushi dai ya sakeyi yace "Hoton Zeenat ne fa ba ita d'in ba, kuma ita kanta Sayyada ai tasan da ina kallon hoton ina kuma tuna baya."

Cikin kulawa Saleem yace "Yaya Abbacar, na fahimci har yanzu kana son Zeenat a zuciyarka, amma kuma kana jin zafin abinda ta aikata maka ko?"

Girgiza kai yayi yace "Ko d'aya Saleem, kawai dai ina tuna rayuwar baya ne."

Murmushi rainin hankali yayi yace "Karka raina min wayo mana yaya, nasan abinda kake ji a ranka mana inhar zan kwatantashi da kaina."

Kawar da kai yayi yace "Ko kad'an Saleem babu haka a raina, sai ma addu'a da nake binta da ita Allah ya mata rahama."

Tsaye ya mik'e yana kallonshi yace "Kenan kana so ka ce sam baka jin zafin cin amanar da Zeenat ta maka? Kenan ko ka tuna cewa aminin yayanta ne ya lalata ta sannan ya mata ciki wanda ta zo da shi gidanka baka jin komai?"

Tapi ya dinga yi yana dariya yana fad'in "Amma gaskiya kayi k'ok'ari yaya, kaga kuwa idan da ni ne haka ta faru dani da tuni zuciyata ta buga, dan ni ba zan iya zaunawa a duniyar nan ba ina tunanin matar da ta shigo da cikin wani k'ato gida na ba, to taya ma haka zata faru? Matata ta sunna na haskota a ido na tare..."

" Stop it Saleem, ya isa."

A hankali Saleem ya kalli yayanshi da tuni hawayen nan dake mak'alewa suka fito, rufr idonshi yayi zuciyarshi na bugawa da k'arfi yana ji kamar ya mangare Saleem d'in, a hankali ya bud'e ido ya sauke a kanshi ba tare da yace komai ba ya mik'e daga kujerar, kasancewar har yanzu yana da yar matsala wajen tafiya saboda tun lokacin da yayi paralysé yasa bai iya tafiya da kyau, cikin jan k'afa d'aya ya shiga cikin falo ya bar Saleem nan, da kallo ya bishi harya b'ace kafin ya rik'e k'ugu, har k'asan zuciyarshi yana jin zafin ganin d'an uwanshi a wannan halin, halin da ba kowa yayi sanadiyar shigarshi ba sai mace, tabbas Zeenat ta cutar da su sosai, domin kuwa a dalilinta ne har yanzu yayanshi baya iya tafiya daidai, a sanadin abinda ya faru dashi ne yasa mahaifiyarsu data rage musu kwantawa jinya wacce dama take tare da hawan jini, suna ji suna gani ta mutu da bak'in cikin abinda Zeenat d'in ta musu, yanzu gashi shi kanshi Abbacar d'in baya da aiki sai tunanin ta da zubar da hawaye, shi kad'ai ne yake gani yaji dad'i tunda babban magajin nasu yana Gombe acan yake harkokinshi tare da iyalinshi, sai in ya zo duba su kawai ko kuma su sunje.

D'auke hannayenshi yayi d'aga k'ugu yana d'an cije leb'e da wani irin yanayi a tare da shi mai wuyar fassarawa, ko cikin gidan bai shiga ba ya sake shiga motar shi ya bar gidan, duk da dai yasan Abbas shima kuma ya sanshi, amma hakan ba shine zaisa ya fasa abinda yayi niyya ba, domin kuwa duk da abinda ya faru sam su Abbas basu raba alak'arsu da Zeenat ba, ko ba komai dai yar kawunshi ce wacce ita ma ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar shi.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Da dare suna zaune dukansu kamar yanda suka saba kullum bayan sun gama cin abinci, hira suke sosai ana dariya sai dai yaran tsakaninsu suke hira haka ma manyan, ana haka Sameta ta kalli Abbas da suka fi kusa tace "Sir, ina da magana fa da kai."

Ameer dake ta mak'ale mishi a wuya yana ci gaba da wasa da shi yace "Ina jinki, amma kafin nan sau dubu nawa na fad'a mi ki bana son sunan nan?"

Turo baki tayi tace "To ai idan na fad'i sunan ne saina dinga tunawa da baya, lokacin da bana iya kallon idonka kullum kaina k'asa ina fad'a, good morning sir, good evening sir, sir your food is ready, sorry..."

Bata k'arasa ba ya dakatar da ita yace "Heee, ya isa to naji, fad'a min abinda zaki fad'a min, idan ba haka ba zaki sa Ammie ta ji kina tuna baya yanzu zata fara mita akan bautar da ke da akayi a baya."

Dariya tayi tace "Kai kuma shine baka so ko a tuna baya? Saboda kasan baka da gaskiya."

Saida ya sumbaci bakin Ameer yace "Indai ba fad'a kike so muyi ba a daren nan to ki fad'i abinda zaki fad'a."

Tab'e baki tayi tace "Tunda na tuna baya kuma ai kaima kasan dole muyi fad'a, dan kasani dai ba tsoro nake ji ba."

Sai lokacin ya kalli k'wayar idonta cikin k'ara k'asa da murya yace "Na gano ki munafuka kawai, wato neman hanyar fad'a kike dan na biye miki muyi bala'i a daren nan, dan kinsan a k'arshe kowa zai kwana d'akin shi ne ko kuma ki kawo mana Ameer a tsakiyarmu ko, to ba zanyi hushi ba kuma ba zanyi masifar ba can kiji da abarki."

Tashin su Naseer da iyalensu ne yasa suka kallesu Abbas na fad'in "Ya dai malamai naga kun mik'e?"

Bashir ne yace "Yaya wallahi bacci muke ji, zamu je mu kwanta ne saida safenku."

Hararanshi yayi yace "Ku d'in ne zaku kwanta tunun yanzu?"

Wani kallo Sameera ta masa tace "Yallab'ai, miji da matarshi yace bacci yake ji, meye na ka a ciki dan Allah?"

Bilkisu ce tace "Yafi so muyi ta zama anan ke kuma saboda gobe da ace ya makara bai tashi ba yace surutun mu ne ya hanashi bacci."

Kallonta yayi yace "To ba surutun naku ke hanani baccin ba? Musamman ke da wannan mai..."

Ya fad'a yana nuna Sameera wacce ta tilasta mishi yin shiru saboda kallon data masa, fuska a had'e tace "Ka k'arasa mana kai nake sauraro."

"Shikenan kawai abar maganar." Ya fad'a yana sunkuyar da kai, mayar da kallonta tayi garesu sukayi ban kwana kusan duka yaran saida suka zo suka bata hannu suna fad'in saida safe, su Abba ma tashi sukayi suka musu saida safe, Abbas ne cikin shafar kai ya mik'e ya tari gaban Ammie da Ameer yace "Ammie na ce ko zaku tafi da Ameer wajenku ne yau dai kam ya tayaki hira har kiyi bacci."

Wani kallo ta masa tace "Ban gane ba? Ni na fad'a maka ina son ya tayani baccin? Me zaisa ba zai kwana tare da yan uwanshi ba kamar kullum?"

"Eh to Ammie, da yake wai naga kamar baku tashi bacci bane yanzu." Yana fad'in hakane dan yasan Ameer da rigima zai iya cewa a wajensu zai kwana, ko kuma idan suka samu sab'ani da uwarshi tace anan zai kwana tare da su, shi kuma yau kam yanda yake jinshi babu abinda zai hanashi sukuwa idan har ya samu filin nan.

Kallon Ameer tayi wanda keta latsar wayar Abbas bai ko san sunayi ba tace " Wannan sarkin had'iyar ne zan tafi dashi ya kwana wuri na, ai kafin gari ya waye duk ya cinye min katakon dake d'aki na."

Su Raudat da suma suke shirin tashi ne suka bushe da dariya, sai Raihan da murmushi kawai tayi wanda ya bayyanar da hak'oranta, Abba ne ya kamo hannu Ameer d'in yana fad'in "Yanzu takwaran nawa ne kike fad'a ma wannan maganar? Lallai ma matar nan kin samu wuri dayawa, aboki muje d'aki na ka kwana kaji ko."

Abbas ne yace "Kuma fa Abba madarar ma da yake tashi yasha cikin dare yanzu ya daina, tunda yayi yawu kunga ai baya zauna wuri d'aya ba."

Ammie ce ta tab'e baki tace "Ai ina d'aga mishi k'afa ne ma saboda yana da sunan na ka, amma badan haka ba ai daya gane kurenshi."

Kamar daga sama Khalifa yace "Wai ke da duka mazanki sai kinyi fad'a ne? To idan kika b'ata mana dukanmu ya zakiyi kenan?"

Da yatsa Ammie ta nuna shi tace "Kai rufe min baki a wurin nan, ina shirin bacci ne zaka sani cacar baki, kai idan za'a kwana a hantse ba gajiya zakayi ba, parrot kawai."

Hararan ta Khalifa yayi yace "Zan kama ki ne tsohuwa."

Nuna Abbas tayi tace "Kaga tsohon nan bani ba."

Kallonta Abbas yayi yace "Ammie maganar mata ce fa, ai da Ammienshi kika kira tsohuwar ko."

Wani kallo ta masa tace "Kai yanzu waccen ta maka kama da tsohuwa a ganinka? Ko dai ba kya duban madubi ne?"

Abba ne yace "Kai kuwa ina zata kira 'yar gwal da tsohuwa, ai sai kai data raina kuma da bata haifa ba, amma ai abin a fili yake kowa yasan waye tsoho a cikinku."

Sun jima tsaye wuri d'aya suna wannan gardamar da cacar bakin kafin kowa ya nufi makwancinshi, da k'yar Abbas ya karb'i wayarshi a hannun Ameer wanda yace da ita zai tafi ya kwana, saida Sameera ta shirya cikin kayan bacci ta nufi fita dan zuwa d'akin Abbas, a k'ofa suka had'u wanda ya kasa jira yake ganin kamar ba zata zo ba, yana shigowa ya rufe d'akin ya rage hasken wutar d'akin, rumgume juna sukayi a cikin kunne ya rad'a mata "Kinsan da nayi kewarki?"

"Uhmmm." Ta fad'a cikin mak'oshi, cikin salo ta fara tsotsar bakinshi har tayi nasarar kama harshenshi, salon da take masa yasa ya fara jin kamar bashi ba, ana cikin haka ta raba bakinsu ta zura harshenta a kunnenshi ta fara wasa da shi a ciki, wata sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da k'ara k'amk'ameta, daga nan komai ya canza abun ya girmama zuwa kan gado.

*Bayan awa biyu* dukansu bacci ne ke son d'aukar su, cikin taushin murya Abbas yace "My Meera ina son haihuwa dayawa har cikin zuciyata, shin kina ganin nan gaba zaki iya haifo min yara shida? Kinga idan aka had'a da wanda muke da sai su zama goma sha biyu cif."

Zunbur ta tashi zaune tana kallonshi tace "Da gaske kake yallab'ai? Amma fa ni na d'auka zamu barsu ne daga guda shidan, kaga nima na huta ai."

Lumshe ido yayi ba tare daya tashi zaune ba yace "Wallahi iya gaskiyata nake fad'a miki, ina so naga kin haifa min yara dayawa, amma idan ba zaki iya ba saina..."

Kafeshi tayi da ido tace "Sai kayi me? Ka k'ara aure kake nufi?"

Bud'e ido yayi a kanta yace "Eh mana, tunda ke ba zaki iya ba."

Gyara zama tayi ta d'auki pillow ta soma dukanshi dashi tana fad'in "Je kayi auren dan Allah ga wurin nan, wallahi kana aure zan koma basraba da zama, ba zan k'ara saka kaina a had'ari ba saboda kai tunda kuskurenka ne."

Da k'yar yayi sa'ar rik'o ta ya had'a da jikinshi sosai ya sake lumshe ido yana murmushi, ita kam k'ok'arin raba jikinta da nashi take amma ya matseta sosai, masifa take tana fad'in "Rabu dani malam ka tashi ka koma d'akin ka, 'ya'yan ne ba zan haifa ba kaje kayi auren, naga ma ko Salma ai zaka iya dawowa da ita ta haifa maka yaran tunda har yanzu baka saketa ba, humm, wallahi kana bani mamaki mutumin nan, na ce ka saketa ka ce kayi tun tuni, na tambayeka saki nawa ka mata amma ka gagara fad'a min, nasan ma baka saketa ba saboda kana sonta har yanzu, watak'ila ma kana zagayawa wajenta ban sa..."

Da k'arfi ya matseta sosai ya danna bakinta a nashi yana mata wata mahaukaciyar tsutsa, shiru tayi tana saurarenshi saida ya saketa da kanshi kafin ya kalleta da idonshi kamar zaiyi bacci yace "Mai sunan mamana surutunki ya fiki yawa, idan kika fara bala'i ba kya tsayawa ko numfashi ki sauke."

Zata yunk'ura ta tashi ya sake matseta yana shafa gashinta yana fad'in "Shiiiii, yi bacci kinji ko, yi baccin abinka."

Kamar zatayi kuka tace "Amma fa na fad'a maka tun tuni cewa zamuyi magana."

Cikin magagin baccin dake fizgarshi yace "Ki bari da safe zamuyi maganar kinji."

"Maganar fa na da mahimmanci."

Shiru ya mata baice komai ba hakan kuma yasa ta tashi zaune tace "Uhum wato ba ma ka da lokacina ko, to gaskiya ban yarda ba tashi muyi maganar, dan idan nace sai gobe to wuri ya k'ure."

Yanda take jijjigashi ne yasa ya bud'e ido ya sauka daga kan gadon ya nunata da yatsa yace " Allah badan ina tsoron hushin Ammie ba dana tsula miki d'an karan duka a daren nan, wai Sameta yaushe ne zakiyi hankali ke? Har abada ace ba zaki bar mijinki ya huta ba kamar wata..."

Bai k'arasa ba ya juya ya bar d'akin, dan dama maganganun daya fad'a mata ya fad'a ne dan karta bishi d'akin shi saboda ya santa da zuciya, shiyasa ya tak'aita daga nan, yana shiga d'akin shi ya kwanta amma saiya kasa bacci, dan basa raba shinfid'a inba rigima sukayi ba ko sunyi fad'a, tunanin halin da take yanzu yakeyi kafin daga bisani ya fara tunanin Salma, tabbas ya saki Salma tun ma ranar daya gane da sihiri ya aureta, sai dai bai fad'a ma kowa ba inba Abba ba, amma da ana saki billion daya ma salma, da wannan tunanin bacci ya d'auke shi.

Sameera ma haushin maganganun daya fad'a mata ne suka sakata yin kwanciyarta tana huci, ta kuma san safiya nayi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment