Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai tace "Na sani da ace wani daga waje na ya ci zarafinta, wallahi sai inda k'arfina ya k'are wajen bi mata hakk'inta, da nayi anfani da mahukuntan dake gidan nan da kud'i da muk'amin mahaifinta wajen ganin na kai ko d'an uban waye k'asa, amma daya zama d'ana ne saina kasa yin komai na lullub'eta tare da laifin ina ta hura mata wuta, banda fargaba idan aurenta ya tashi, na yarda da kaina da gyaran dana koya iyaye da kakanni, dole zata banbanta tsakaninta da budurwa, shiyasa kullum fatana Allah ya fito mata da miji tayi aure."

Kallonta duka suke sai kuma ya juya ya kalli Shureim dake tsaye gaban madubin Hajia yana kallon kwalaben turaren da suka d'auki hankalinshi saboda kyawunsu, kamo hannayenta yayi ya rumgume cikin muryar alhini yace "Yanzu Ummy wannan dalilin ne yasa kike ta nesanta ni dashi dama? Shiyasa ba kya so kiga muna kusantar juna sai kin raba mu?"

Kallonshi tayi tace "Kayi hak'uri Ammar, nasan yanda soyayyar jini d'aya take, duk yanda zan nisanta ku a cikin dubu zaku iya gane junanku, kawai dai ina nesanta ku ne bana son kuyi saurin gane junanku."

Sakin yaron yayi ya rumgumeta kamar zaiyi kuka yana fad'in "A da tunani na shine baki sona, idan kina hantarata da zagi na sai naga kamar baki damu dani bane, amma yau na gane babu wanda kike so sama dani Ummy, duk wannan kasadar saboda ni ne kika d'auketa, nagode Ummy, dan Allah ki yafe min komai dana mike."

K'ulli ta sakar mishi a baya tana fad'in "Shashashan banza, taya wai zaka ce bana son ka bayan a cikina na haife ka."

D'ago kai yayi yace "Hauka na ne ke nuna min haka Ummy."

Rank'washin shi tayi a kai tana murmushi tace "Kai fa na daban ne yarona, tashin hankalin da ka so min yanzu shine nayi gudu tun tuni yasa ban fad'a maka ba, nasan in ka sani zaka shelanta ne kowa yaji."

Dariya yayi yana sosa inda ta rank'washeshi yace "Kamar kin sani kuwa Ummy."

Wani kallo ta masa tace "Au! Kamar ma na sani ne? Wa ya fini saninka a duniyar nan."

Hajia dake dariya tana kallonsu ne tace "To ku bani hankalinku nan."

Juyawa sukayi suka kalleta cikin nutsuwa, saida ta kallesu tace "Maganar nan ba zata tsaya iya nan ba, dole akwai wad'anda zamu fad'a ma su san halin da ake ciki."

Kallon juna sukayi suka sake kallon a tare da mamaki Ummy tace "Hajia su wa kenan?"

Cikin kallon basira tace "Hassan, dole ya sani ko da bama so, da kuma Husseina wacce yanzu ni kaina nake girmamata, ita kwatankwacin Alhaji ce da baya nan a gidan nan, dan haka ita ma zata sani, sai kuma Amna amma bansan ku me zakuyi tunani a game da ita ba?"

Tashin hankalin Ummy da ma Hajia ce kuma gashi ta tsallake cikin sauk'i, dan haka yanzu ita bata damu ba duk wanda ma zai ji ya ji a shirye take, cikin ladabi tace "To Hajia ke me kike gani?"

Saida ta gyara zama tace "A gani na ni dai a fad'a mata, ba dan komai ba sai dan halin rayuwa."

Da sauri Ammar yace "A'a Hajia, kar a fad'a mata gaskiya ina jin tsoro."

A tare suka kalleshi da mamaki, Ummy ce tace "Tsoro? Ammar kai d'in? Lallai."

Hajia ce tayi murmushi tace "Ashe dai har abun ya zo inji me tsoron wanka, Ammar kai ne baka so a fad'i gaskiya, har kake cewa kana jin tsoro, tsoron ma matar aurenka."

Kallonta yayi yace "Hajia ko yanzu wallahi a shirye nake dana fad'awa duk duniya waye Shureim, ita dai ce kawai bana son ta sani."

"Saboda me to?" Cewar Ummy tana kallonshi.

Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Saboda tana d'aya daga cikin mata ukun dake kassara tunani na, tana d'aya daga cikin wanda tunanin al'amarinsu ma kad'ai yake firgita min nutsuwa ta, tana d'aya daga cikin sanyin idanu na, d'aya ce daga cikin ukun da bana son ganin tashin hankalinsu."

Kallon Ummy yayi yace "Taya zan so nutsuwarta ta bar gangar jikinta kan abinda na aikata, kwanciyar hankali na ce ita, taya zan so taji abinda nake da tabbacin zai gusar da hankalinta, idan kuma haka ta faru ni wa zai nemo min nawa hankalin, mallakina ce kuma babban rabon dana gada a gidan duniyar nan, idan zan misaltata da gona to bansan adadin girman ekar dake cikinta ba, daga ni har yarana ita ce duniyar mu."

Ummy da taji hawaye sun cika idonta ne tace "Bansan ya zata ji idan aka fad'a mata ba?"

Murmushi yayi yace "Ummy kunsan a ina naji kuwa?"

Girgiza kai tayi tana kallonshi har ya d'ora da "Ita ce ta fad'a min."

Hajia ce tayi saurin cewa "Ita wa?"

"Amna mana." Ya fad'a yana kallonta, zaro ido duka sukayi sai kuma Ummy tace "Amna? To ita a ina taji? Amma kuma banji tashin hankali ba?"

Murmushi ya sake yi yace "Ummy yarinyar nan tayi a rayuwa wallahi, ita ta fad'a min da kanta, amma abun tsoratarwa ta d'auki abun kamar tatsuniya, abun ma dariya yake bata sabodaa ganinta abu ne da ba zai tab'a faruwa ba, sannan tana da yarda akai na da kuma yar uwarta d'ari bisa d'ari."

Da mamaki tace "Amma a ina Amna taji maganar nan?"

Ammar ne yace "A wurin Amie k'awarsu."

Da wani mamakin tace "Amie kuma? A ina Amie taji to? Babu fa wanda yasan da maganar nan."

D'aga kafad'a yayi irin ohon nan yace "Ki tambayi *uwar Shureim*."

Wani galala Ummy ta kalleshi a ranta tace "Kaji wani wai uwar Shureim, to wannan ya ma bari har a gama fad'a ma wanda ya dacen kafin ya fara kiranta da wannan sunan?"

A fili kuma cewa tayi "A gaskiya bana tunanin zata fad'a mata, amma kuma abun da mamaki sosai."

Bud'ar bakinshi cewa yayi "Ummy karki ba kanki wahala wajen sanin yanda akayi taji, kawai share zancen."

Hajia ce tace "Kunga, hak'uri zamuyi mu daure a fad'a mata, kamar yanda na fad'a muku ko saboda halin rayuwa, abinda nake so ku fahimta shine idan yanzu bata sani ba a k'arshe kuma ta ji a wani wurin aka tabbatar mata da gaskiya, to fa ba zata ji dad'i ba kuma mummunan abunda ba ayi tsammaninshi ba zai iya faruwa."

Jinjina kai yayi yace "Gaskiya ne, na yarda a fad'a mata amma ba yanzu ba gaskiya."

Ummy ce tace "Eh gaskiya kam, bai kamata ba dama a fad'a mata yanzu, saboda har yanzu ni dai jikin nan naya yana bani tsoro."

Hajia ce tace "Shikenan yanda kuka ce, a jira ta samu lafiya sai a sanar da ita."

Ammar ne ya mik'e tsaye ya kama hannun Shureim yace "Zan fita mu dawo."

Da murmushi Ummy tace "A dawo lafiya."

Da kallo suka bisu har suka fice, Ummy ma godiya ta ma Hajia ta fita tana jin kamar ta taka rawa tsabar farin cikin da take ciki. Wani ikon Allah suna fita farfajiyar zasuyi wajen ajiyar motoci suka had'e da ita ta dawo daga wajen kitso, cikin murna ta bud'e hannayenta zata d'auki Shureim, baya yayi da shi yana kallon fuskarta, kallonshi tayi fuska a had'e tace "Shureim zo nan."

Wani murmushi ya mata, bayan tsawon lokaci rabon da bakinsu ya had'u yau sai gashi dalilin Shureim yace mata "Fita zamuyi."

Bata kula da abinda ya fad'a mata ba ta zura hannu zata jawo shi, k'ara baya yayi dashi yana kallonta shi ma fuska a had'e yace "Na ce fita zamuyi dashi yanzu, ko kuma ban isa bane?"

Wani kallon rashin mutumci ta masa tace "To miye na tambaya ta bayan gashi ka bawa kanka amsa."

Kai tsaye take nufin bai isa ba kenan, matsowa yayi kusanta sosai har numfashinsu ya fara gauraya ya kalli k'wayar idonta kamar yanda take kallon na shi babu rusunawa yace "Wallahi *kinci albarkacin yaron nan dake tskaninmu*, ba dan haka ba da saina na zubar miki da k'ananan aljanunki, marar kunya kawai da baki iya girmama mutane ba."

Zaro idon da tayi alamar ya akayi haka yasa shi saurin katse mata lissafi da cewa "Eh, na sani, sai kuma yaya yanzu? Shashasha kawai."

Wucewa yayi har ya fara tafiya sai kuma ya tsaya ya juyo, duk da bata juyo ba saida yayi murmushi yace "Zaki iya tuna na tab'a fad'a miki sau d'aya nake aika d'an sak'o na kuma ya isa inda nake da muradin yaje? Ki kama kanki yarinya ko kuma..."

Wucewa yayi rik'e da hannun Shureim ya barta tsaye, saida taji sun tayar da mota tayi saurin wucewa ciki kamar zata tashi sama, bata kula ba tayi karo da Ummy dake niyyar zuwa b'angaren Amna, suna had'a ido ta kama hannunta da k'arfi ta jawota suka k'arasa fitowa daga falon, saida ta juya ta ga babu kowa tace "Ummy, waya sanar dashi maganar nan?"

Dariya Ummy tayi ganin tsoron dake fuskarta duk ta furgice tace "Kwantar da hankalinki to? Ni ai ke zan tambaya wa kika fad'awa har ya fad'a ma Amie maganar nan?"

"Me? Amie kuma?"

Cikin mamaki tace "Ummy ni ban tab'a maganar nan da kowa ba."

"To ya akayi Amie taji har ta fad'awa Amna?"

Gaba d'aya idonta ta k'walalo waje ta dafe k'irjinta dake bugawa da k'arfi, dafata Ummy tayi tace "Kwantar da hankalinki mana."

Girgiza kai tayi tace "Ummy Amna fa kika ce? Taji wannan maganar? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Ummy na shiga uku na lalace, Amna da shegiyar zuciya."

Murmushi ta mata tace "Yanzu dai ki fara nutsuwa tukuna sai kiji abinda ya faru."

Cikin saurin maganar da bata san ta iya shi ba tace "Ummy ina maganar nutsuwa kuma kawai ki fad'a min komai."

A hankali Ummy tace "Shi ya fara samu na da maganar yace Amna ce ta fad'a masa, ita ma kuma wai Amie ce ta fad'a mata, amma fa ita ta d'auki maganar da wasa, muna cikin maganar kuma Hajia ta fahimci akwai matsala ta ja mu d'akinta."

Shirun da tayi ya ba Hamna damar d'ora hannayenta saman kanta tace "Na shiga ni Hamna, na mutu shikenan, Ummy sai me ya faru?"

D'orawa tayi da "Magana mukayi ta fahimtar juna, Hamna idan kika ga yanda Hajia ta fahimce ni har ta bamu shawara wallahi zakiyi mamaki."

Da sauri ta rik'o hannayenta tana fad'in "Ummy kina nufin ba tayi fad'a ba?"

Girgiza kai tayi tace "Ko kad'an in fad'a miki."

Kamar zata fashe da kuka tace "Amma kuma Ummy Amna fa? Ina tsoron ranar da zata ji da abinda zata iya yi wallahi."

Cikin taushin murya tace "Insha Allah ita ma zata fahimce mu fiye ma da Hajia, abinda kike tunanin tayi ba zai tab'a faruwa ba, Amna tana da hak'uri sosai."

"Amma kuma tana da zuciya Ummy." Ta fad'a tana sako siraran hawaye, hannu tasa ta shafe mata tace "Dan Allah karki d'aga hankalinki Hamna, ki nutsu ki shiga ki samu kiyi wanka ki ci abinci, karki yarda wani ya gane kina cikin damuwa, muyi addu'a yanzu Allah ya bata lafiya, ke baki ji abinda ta fad'a ba kwana uku da suka wuce, kallon mahaukaciya ma take wa Amie fa."

Jinjina kai tayi tace "Shikenan Ummy." Shigewa tayi ciki Ummy ma ta nufi b'angaren Amna.

Ko da taje ta samu an ba wa Amna maganin zazzab'i tasha, d'aki suka ce taje ta kwanta ta huta da kwaramniyar nan, da shigarta d'aki baifi minti sha biyar ba Hamna ta shiga dubata, kwance ta same sai rawar d'ari take, ko da ta tab'a jikinta taji zafi sosai kamar garwashin wuta, idonta sunyi jawur da su kamar ba nata ba, Ummy ta fito ta fad'a ma suka shiga tare, ko da ta ga jikinta tace kawai su kaita asibiti, ba b'ata lokaci Hamna ta jasu dan Ammar ya riga da yayi nesa da gida, acan ya samesu har san jona mata k'arin ruwa. Tsananin zafin jikin baya raguwa sai sama yake, cikin d'an lokaci k'ank'ani ta canza ta fice a hayyacinta, da fari an k'ara mata ruwa sai aka nemi jini ma aka k'ara mata.

Allah da ikonsa kafin gari ya waye ba zaka tab'a kallon Amna kace ita ce ba, ta gigice ta canza duk ta disashe ta zama abar tausayi, gashi tayi kamar ta kumbura a jikinta, zuwa wayewar gari saida aka saka mata wani tiyo dake kai mata ruwa, a hannayenta k'arin ruwa da jini, n'aurar taimaka mata wajen numfashi abubuwan kamar ba a jikin mutum ba.

*Sai daren ranar* kad'ai likitoci suka d'an samu kan matsalar, Ammar ne zaune gaban likitan ya k'ura masa ido inda zuciyarsa ke dukan uku uku, ya kasa had'a yawu ko alama sai tattarasu yake yana son turasu mak'ogoronshi amma sun k'i wucewa, likitan ne ya mayar da hankalinshi kanshi cikin nutsuwa yace "Docteur ya kukayi sakaci haka da marar lafiya? abu ne dake matuk'ar wuya samun irin haka a lokaci d'aya, kuma da an ankara da wuri da an cire mata d'aya a barta da d'ayar, yanzu gashi lokaci ya k'ure mana sosai."

Ammar dake kallon bakinshi kamar kurman dake fahimtar yaren leb'e ne yace "Ban cika fahimtar ka ba fa, ka min gwari gwari zan fahimta."

Saida ya dan furzar da iska ya kalli tsakiyar idonshi yace "Duka sun lalace, k'wadarta."

Da sauri ya dafe kanshi da hannu biyu, sosai yake matse kanshi yana so yaji ya daina sara masa amma abun ya ci tura, da k'yar ya d'aga kai ya kalle shi yace "Ta yaya? Duka biyun zasu lalace lokaci d'aya? Ta yaya dan Allah? Me ye abunyi yanzu?"

Cikin rashin karsashi yace "Mu kan mu abun ya bamu mamaki, dan abune da bai cika faruwa ba gaskiya..."

Katseshi yayi da cewa "Me ye abunyi yanzu?"

Cikin girgiza kai yace "A gaskiya yanayin jikinta ma ba zai bayar da damar da za'a fara mata dialyse ba, dan kaga tana jin jiki sosai kuma kowane dialyse zatayi perdre d'in 10 kg, dan haka ina ga mu..."

Da k'arfi ya mik'e tsaye yana fad'in "Dan haka ayi me? A barta ta mutu kenan? Haka kake so ka ce?"

Girgiza kai yayi yace "Non docteur, amm..."

Cikin daka masa tsawa yace "Kaga fad'a min mafita kawai, ina so ka fad'a min abinda zanyi matata ta samu lafiya, bana son ganinta a halin da take cikin nan."

Shi dai yana so su rabu lafiya dashi sai kawai ya rubuta masa magaunguna yace ya siyo, da gudu ya fita kamar wanda yasha giya dan har yanzu kanshi mugun sara masa yake.

*Kwanansu* biyu a asibiti, abubuwa sun k'ara dagulewa, tun safiyar yau da Ammar ya shigo d'akin ta fara masa nasiha ya rage zuciya ya dinga hak'uri ya kula da yara waye waye, sai kawai zuciyarsa ta karye ya fita daga d'akin, Allah ya sani har zuciyarshi yana son Amna kuma yana son zama da ita, amma baisan wacce k'addara ce ke shirin raba shi da ita ba, baisan ilimin dake cikin rashin lafiyarta ba, tunda ya fita ya zauna cikin masallacin asibitin bai sake tashi daga nan ba, yanda ya ga safiya a cikin shi haka ya riski rana da dare.

Al'amarin bai sake tashin hankalin kowa ba saida ta nemi a kawo mata yaranta, daga kwance haka take shafar kawunansu tana musu murmushi, Ameera da tafi kowanensu shak'uwa da ita ce ta kwanta kan jikinta tana kuka, Ameer ne ya jayeta daga jikinta yana fad'in "Ke baki gani bata da lafiya."

Fizge hannunta tayi ta sake kwantawa kan jikinta, Ummy dake tsaye kusansu ne ta kalli Hamna dake tsaye ita ta kawosu tana hawaye, hannun Ameera ta kama cikin muryar kuka tace "Beby na zo mu je ko? Zaki sha ice cream?"

Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um."

Saida ta share hawayenta ta sake kamota tace "Muje kinji har da madara zan siya miki."

Duk da bata saki jikinta ba haka ta bi Hamna zasu fita, cikin muryar da bata fito sosai ba Amna tacej "Yer uwa."

Juyowa tayi tana kallonta ta tako a hankali ta zo ta tsaya, hannu ta mik'a mata ita ma ta zuro mata na ta hannun ta rik'e gam, murmushi ta saki mai kyawun gaske tace "Karki manta dani kinji, ki ci gaba da min addu'a, ke da yah Ammar zaku kula min da yarana, nasan da haka ban da matsala, karki rabu dasu duk wuya, yah Ammar zai shiga damuwar rashi na, ki...kkk...kw..."

Ganin ta kasa fad'ar kalmar kuma ita kuka ya ci k'arfinta yasa ta fizge hannunta da k'arfi ta tashi a guje ta fita, bata tsaya ba saida ta kai k'ofar asibitin ta durk'ushe nan tana kuka da iya k'arfinta.

Ko da ta fita Amna ta kalli inda Hajia take ta mata alamar ta zo, matsowa Hajia tayi tana kuka ta rik'e hannunta tace "Amna dan Allah kiyi ta addu'a, insha Allahu zaki tashi kinji."

Sakin hannun Hajia tayi ta kalli inda Hadiza ke tsaye wacce ta zo da taji jikin ya k'i kyau, ita ma alamar ta zo ta mata ta rik'e hannunta, magana take yi amma bata jin komai, a hankali ta durk'usa ta kai kunnenta kusan bakinta, cikin sanyin muryar da bata fita tace "Mama, ki yafe min, ki yafe min, Abba ma ya yafe min, yah Ammar, ki kira min yah Ammar na rok'i gafararshi, dan Allah ki ce masa ya zo ina son ganinshi, Mama, Mama, Mama, sau uku na kira sunanki ko? Dan Allah ki ce Hamna ta zauna tare da yah Ammar da kuma yara na, zata iya kula dasu kamar yanda nake yi, dan Allah Mama, kinji, kinji ko."

D'agowa tayi tace "Na ji Amna, kiyi ta kalmar shahada a bakinki, bari na kira miki Ammar d'in."

Tashi tayi da sauri ta fita, amma tana fitowa ita ma ta tsaya cikin wani d'aki da babu kowa ta shiga rera kuka, ta d'auki kusan minti ashirin tana kuka kafin ta fita ta same shi zaune ya had'a kai da gwiwa, da sauri tace "Ammar, ka zo dan Allah Amna tana son ganinka."

Tasowa yayi daga cikin masallacin ya matso kusanta cikin layi na galabaita yace "Mama dan Allah ku rabu da ita, zafin ciwo ne ke damunta kawai."

"A'a Ammar, ka zo kawai tunda tace tana buk'atar ganinka."

Cike da kasala yace "Shikenan muje."

Juyawa tayi ya saka takalminsa ya bi bayanta, ji yake gabanshi na tsananta fad'uwa, ko da suka isa d'akin suka ji ana ta kalmar shahada da kabbara, babbar kalmar data daki zuciyarsa ita ce ta"Allah yasa anyi sa'ar tafiya."

Suna shiga tare suka ganta ruf, da d'aya d'aya ya shiga kallon mutanen d'akin, yanayin kowa da furucin bakunansu ya tabbatar masa da abinda zuciyarsa ke raya masa, wani tartsatsi yaji daga kanshi har zuwa k'afarshi, kamar wani ne ya turashi sai ganinshi sukayi ya fad'i warwasss...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร  00:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_64_


Da sauri Ummy tayi kanshi ta durk'usa tana duba shi, mik'ewa tayi da sauri zata fita daga d'akin saiga Amar da Jibril sun shigo da sallama, da sauri ta kallesu tace "Yawwa ku kama shi dan Allah, ina zuwa."

Fita tayi daga d'akins
su kuma suka tallabe shi suka fito dashi, a wani d'akin aka kwantar da shi Ummy duk ta rikice sai wasu likitocin ne suka diba shi suka saka masa ruwa.

*Allah mai girma*, jinjiga, girgiza, d'imuwa da zautuwa babu wanda baiyi ba, Amna dai ta tafi gidanta na gaskiya cikin sa'a, duk wanda ke d'akin a lokacin ya shida tayi kalmar shahada a matsayin kalmarta ta k'arshe a duniya, an ci kuka har an gode Allah kamar babu gobe, wasu suna son suyi dauriya amma da an kalli yaranta uwa uba Ameera sai a saka wani sabon kuka.

Hamna na zaune kan dakalin dake fuskantar cikin asibitin su Zeituna suka fito jiki a mace kowa na ta sharar hawaye, da mamaki ta taso ta tare su cikin dakusashiyar murya tace "Aunty kuma ta saka ku kuka ko? Ni bansan me yasa take haka ba, amma yanzu ya jikin nata?"

Kallon juna sukayi sai Hajia da tace "Jikin Amna yayi sauk'i Hamna."

Murmushi tayi tace "Taji sauk'i kenan Hajia?"

Sake kallon juna sukayi suka mata shiru, kallon kowane take da alamar tambaya tace "Lafiya? Wani abu ya faru ne?"

Zeinabu ce tayi k'arfin halin cewa "Hamna ciwon Amna dai ya k'are daga yau."

Kallonta take kamar irin bata gane komai a abinda take fad'a, suma duk ido suka tsura mata suga me zai faru, kusan minti d'aya tayi a haka kafin ta fara jinjina kanta, lokacin data motsa sassan jikinta ne kad'ai ta fahimci wasu sabbin hawaye masu zafi dake gangaro mata, nuna kanta tayi da yatsa kamar mai koyon magana tace "Am...na, ye..r uwata, me ya sameta?"

Hajia ce ta dafata cikin ban baki tace "Sai hak'uri Hamna, haka Allah ya so, addu'a zaki mata kinji."

Wani k'arfi ne taji ya zo mata ta tunkari d'akin da gudu, babu wanda yayi yunk'urin binta a guje sai k'wala mata kiran da suka shiga yi, a lokacin Amar da Jibril sun fito sai cikin ma'aikatan asibitin dake binsu a baya zasu tafi da gawar morgue, yanda suka ji suna k'wala mata kira gashi sunyi karo da ita a k'ofar shiga yasa Jibril k'arfin halin rik'o hannunta, da k'arfin bala'i tasa d'aya hannun ta turashi baya har yayi tangal tangal sai kuma ya tsaya cak, ta, cikin ankarewa da mazantaka Amar ya rik'ota gaba d'aya, dan inba haka yayi ba zata zille masa, k'ok'arin kubcewa ta shiga yi da wani mugun kuka da iya k'arfinta, saida ya rintse idonshi gam ya had'e yawu yayi salati ga annabi sannan yayi k'unar bak'in waken d'ora kanta a k'irjinshi amma jikinta bai had'u da na shi ba, hanya suka basu suka je wucewa da gawar, kukan kura tayi ta rik'e gadon tana shirin bud'e zanin rufar dake jikinta, wannan karan kam k'arfi yasa mata yana son b'anb'are hannunta daga jikin gadon, zubewa tayi zaune ta rik'e gadon gam tana kuka tana fad'in "Wallahi bata mutu, bata mutu ba yer uwata ku sake dubata da kyau, Amna ki tashi dan Allah karsu rufe ki kinji."

A lokacin su Hajia suka shigo suma suka fara rik'eta, da tsiya aka rabata da gadon aka turashi aka fita, daga zaunen nan tabi gadon da kallo tana zuwa k'ugunta har ta fuskanci k'ofar fitar, kuka take sosai sai Amar daya sulale ya bar wurin yana mai tausaya mata, take yaji wasu k'walla a idonshi shima daya tuna idan fa shine yau aka ce ya rasa nashi rabin jikin Ammar?.

Duk k'ok'arinsu na son su lailayeta zuwa mota su tafi gida sun kasa, sunyi juyin duniya ta k'i basu had'in kai, gashi sun dai babu mai iya d'aukarta, mai iyawa mutum d'aya ne kuma shima baisan a inda yake ba yanzu, hatta lieutenant da ya zo cikin mutuwar jiki bai iya cewa komai ba kallonsu kawai yake suna jata, zuwa Labaran ne kad'ai ya kwakwafeta ya lallab'ata ta tashi suka tafi gida.

Hamna kowa yafi tausayinta, tayi kuka kamar ita ma zata mutu, muryarta ta disashe idonta da fuskarta sun kumbura sumtum, ta k'i ci ta k'i sha sai kuka kawai, tana uwar d'akin Amna zaune rumgume da Ameera wacce yanzu ita kad'ai take yarda da ita. Hadiza da Ummy an rasa ina uwar Amna a cikinsu, dukansu sunyi juriya wajen tak'aita mata kuka,

Tunda aka kwantar dashi bai sake sanin me ke faruwa ba saida ya kwana ya hantse, tunda ya bud'a ido ya kafe wuri d'aya yana kallo, tashi yayi zaune ya sauko da k'afafunshi, kanshi na kallon k'asa yana tariyar abinda ya faru, a hankali yaji siraren hawaye na fita a idonshi, cikin zuciyarsa yake fad'in "Ta tafi? Da gaske ta tafi? Ya zanyi? Me yasa zata tafi a wannan lokacin?"

K'ofar da yaji an bud'e yasa shi d'ago kai amma bai kalli me shigowa ba, har saida suka k'araso suka tsaya kanshi suna kallonshi, a hankali Junaid yace "Ammar ya jikin na ka?"

Cikin girgiza kai yace "Ni ma ban sani ba?"

Amar ne ya zauna kan gadon yana kallonshi yace "D'an uwa, kayi hak'uri kaji, dama duk..."

Katseshi yayi da cewa "Ina

Please Login or Register in order to submit comment