Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ganta cikin zanin rufa ta rufe, suna kwantawa ya k'amk'ameta sosai suka lullub'a cikin zanin nan yana ta ci gaba da wasa da jikinta, ba wuya bacci ya d'auketa shi kuma yana ganin haka ya tashi ya je d'akinshi ya sako doguwar riga ya dawo, sallah ya kabbara bai kuma jima da farawa sai aka fara kiran sallah asuba, saida yaje masallaci yayi sallah ya zo da niyyar tashinta, yana shigowa ya ganta ta fito tayi alwala ita ma.

Tunda sanyi safiya sosai mota uku ce ta rako Hajia zuwa gida, duk gidan na wasar baki na ganinta wanda bai kai ciki ba, kowa yaje ya kwashi gaisuwa da yi mata sannu, sai da rana ta fito sosai sannan ta fito waje, kaf saida ta zagaye gidan tana duba abinda aka b'ata dan anga bata nan, haka ta dawo falonta nan ma ta ga komai yana yanda yake sannan ta zauna, lokacin ne Maryama ta shigo gaisheta tare da Huda a bayanta, Hajia na ganinta ta sake d'aure fuska, har suka k'araso bata daina mata wani banzan kallo ba, ita ma cikin rashin kunya a tsaye ta kalleta tace "Anzo lafiya?"

Wani kallon kin ma rainani ta mata tace "Ban fad'a miki bana son ganin wannan shegiyar 'yarta ki a falona ba?"

Fuska a had'e tace "Shegiya kuma? 'Yar tawa?"

"Eh 'yar taki, ko kin manta hanyar da kika sameta ne?"

Saida tayi wata tsayuwar rashin mutumci kafin tace "A gaskiya Hajia bana so ana kira min 'ya da shegiya, idan ba haka ba fa akwai matsala."

Gyara zama Hajia tayi zatayi magana sai Zeinabu dake nesa dasu tace "Ke Maryama, yanzu Hajia zaki wa rashin kunya, wai ke wace irin fitsararra ce ne?"

Kallon Zeinabu tayi tace "Ki shinshina kiji mana, kunga nifa gaskiya ba zan d'auki wannan wulak'ancin ba, haka kawai daga shigowa gaisheki sai ku hau mutane da jaraba."

Zeituna da fitowarta kenan daga madafa ne tace "Maryama, shin bai ci ace kin girmama mutanen nan ba duba da matsayinsu a gurinki."

Husseina dake zaune kan d'aya daga cikin kujerun teburin cin abinci ce tace "Ke Maryama ya isa haka, wuce ki koma d'akinki bana son hayaniya."

A hassale ta kalli Zeituna tace "Wane matsayi? Wane matsayi garesu gare ni? To idan ni na tuna su ki tambayesu suna tunawa da hakane? Sam basa kallona da mutumci saboda karuwa ce ni, to ai kunsan da haka kuma kuka barshi ya aureni."

Daga zaunen nan Hajia tace "Yayi marar kunya, to dama wa zaiyi tsammanin ki girmama shi a gidan nan duba daga inda kika fito, sannan ki sani wallahi da Junaid ya bi ta tawa da ko a hanya ya ganki saiya tofar da yawu, dan haka yanzun nan ki fitar min a falo tare da shegiyar 'yar nan ta ki."

Cikin jin zafin maganar Maryama tace "Shegiya? To kuji da kyau Nurul Huda ba shegiya bace, ita ma nan gidan ubanta ne kamar yanda kowane yaro ko ganin gidan ubansa ne nan, wallahi ko aure na da Junaid ya k'are ni zan bar gidan nan amma banda ita."

Wani kallon marar hankali suka bita dashi dukansu kafin Hajia tace "Au! Wai dama rashin hankalin naki har ya kai haka? To yaushe yayi adaptΓ©nta a matsayin 'yarsa? Kina da hujjar anyi haka?"

Ita ma wani murmushin baku da hankali ta musu tace "Ba ina nufin gidan uban bogi ba, uba mahaifi nake nufi wanda ya haifeta, wanda ta fito ta tsatsonshi."

Sallama Junaid yayi wanda ya shiga can bai sameta ba ya shigo nan, da sauri Hajia tace "Yawwa k'araso, zo ka fad'a mana yaushe wannan aljanar yarinyar ta zama 'yarka?"

Murmushi tayi tace "Zaku jijjiga idan kuka ji ubanta na asali a gidan nan."

Sororo Zeinabu tayi, tunaninta d'aya shine Huda yar Junaid ce, kenan hakan na nufin *tarihi ya maimaita kansa*? Junaid kuma da baisan kan maganar ba kallon Maryama yayi yace "Bani na haifeta ba Hajia, kawai dai ina matsayin ubanta ne."

Murmushi tayi ta kalli Maryama tace "To kinji meya fad'a? Dan haka ki sani ko da zai mayar da 'yarki a matsayin 'yarsa dole saina yarda da hakan kafin yasa hannu a takardar sheda."

Zeinabu ta fara kallo kafin Hajia tace "Ina so daga yau kar a sake kira min 'ya shegiya alhalin tana gidan ubanta, idan ba haka ba wallahi duk saina tono shegun gidan nan in ya so ayi duk wacce za ayi, Junaid dama na aureshi ne dan shi ya matsa sosai, ko da na bar gidanshi ba zanji zafi ba, dan har yanzu sana'ata na nan na jirana na d'ora daga inda na tsaya."

"To sai me? Ki koma kasuwancinki mana ni kuma a randa kuka rabu dashi a ranan zan d'aura masa aure da wata, dan in tabbatar miki ke banza ce wallahi." Cewar Hajia a hassale ita ma, tab'e baki tayi tace "Amma ki sani ba zai so zab'inki ba kamar yanda ya so ni."

Juyawa tayi ta fita, shi Junaid kawai mamaki yake, ashe dama haka take? Lallai zuciya bata mana adalci da take samu son wanda basu dace damu ba, ya juya zai bita Hajia tayi tsaki tace "Malohon banza, yarinya k'arama ta tsaya tana fad'a min magana a matsayina na uwar ubanka amma kana saurarenta, ai ko da ni baka sona ba za iya mayar mata da martani ba saboda ni kayi dan uwarka ma."

Saida ta kawar da kai tace "Hum! Shiyasa ake cewa kowane kare da ranar sa, yau da Ammar ne matarshi ta tsaya tana fad'a mana magana, wallahi ko 'yar sarkin Istanbul ce ita saiya zabgeta da mari sai dai a d'aureshi ko a kashe shi."

K'ala baice mata ba yayi tafiyarshi haka ma Zeinabu barin falon tayi, yana fita d'aki ya sameta zaune sai cika take, cikin fad'a yace "Mari ashe baki da mutumci? Uwar tawa da kakata kika gurzawa wannan rashin mutumcin? To wallahi ya zama na k'arshe, inba haka ba zan miki abinda zakiyi mamaki, dan ba zaki mayar dani sakarai ba."

Ya juya zai fita ta mik'e tace "To indai hakane ka fad'a musu kar wanda ya sake kiranta da shegiya, nan gidan ubanta ne ita ma, kuma a shirye nake da na bar gidan nan amma ita tana nan duk da bata da gadon ubanta."

Murmushin ko dai bata da hankali ya mata yace "Mari ban miki musu ba cewa ina kallon Huda kamar 'yar dana haifa, amma ba hakan zaisa ki ce nine uban ta ba."

Ita ma murmushin ta masa tace "Karka damu Junaid, da sannu zaka san waye ubanta indai har kakar can taka tana sarar kiranta shegiya."

Bai kula da abinda ta fad'a ba kawai ya bar gidan, *da yamma* kuma Jibril ke samun labarin abinda ya faru wajen Husseina, hankalinshi ya tashi sosai, dan haka daya shiga b'angarensu saiya fara wucewa b'angaren ta, Huda dake zaune k'ofar shiga tana wasa yace ta kira mishi ita, bayan ta fito ne rai b'ace yace "Maryamaashe baki da hankali? Akan me zaki musu rashin kunya saboda kawai kina ganin kina da wani sirri a hannunki, to dan Allah in kin cika babbar karuwa kije ki fad'a, ki fad'a sai me? Huda 'yata ce kuma na yarda zan karb'eta, amma kisan wani d'aya shine nima gado nayi, kinsan ko a wurin wa?"

Wani kallo take binshi da shi kamar bata fahimtar abinda yake fad'a, murmushi yayi yace "A gurin kakana mana, ko kuma nace kakanmu ni dake wato malam Rabi'u."

Saida ya had'e fuska ya nuna ta yace "Idan kika bar min Huda anan to ki sani Labaran ma zai koma wajen nashi uban, tunda abun babu mutumci."

Sama da k'asa ya bita da harara ya nufi hanyar b'angarenshi yana fad'in "Yar iska kai duk ki d'aga hankalin mutane, to kaina farau shiga gonar da bata hallata gareka ba."

Da kallo ta bishi, malam Rabi'u, kuma Labaran? Yana nufin malam ne ya haifi mahaifinshi? Kai ia ba zai yiwu ba? Malam daya tsani zina, dalilin da yasa kenan bata nemi taimakonshi ba sanda tayi ciki, dan tasan zai iya kasheta ma da duka, sai yanzu a nuna mata babban mutum kuma uba ace d'anshi ne, to ta yaya? Da wannan tunanin ta koma ciki ba tare data gamsu da abinda ya fad'a ba.

Yamma lik'is Amna ta shigo b'angaren Hajia, kai tsaye wajen Husseina ta nufa, har d'aki ta sameta tace "Hajia dan Allah ba kiyi ajiyar yakuwa ba?"

Dariya ta mata tace "Uwar kwad'ayi, akwai amma busassa ce tana madafa."

"Yawwa, ina zuwa." Ta fad'a tana nufa madafa, tana zuwa ta samu Zeituna suna aiki, ko da ta fad'a mata abinda ta zo yi tace "A'a koma duniyar Ammar, ki bari zan d'ora miki ita a wuta."

Saida ta rumgumeta ciki da shagwab'a tace "Nagode uwarmu, Allah ya barki ke da ubanmu."

Da murmushi kawai ta bita ta fita, tana fita ta d'ora mata, kafin ta tafasa ta gyara kayan had'inta, Amna kuma jin an fara kiran sallah yasa tayi alwala a d'akin Husseina tayi sallah, tana idarwa ta cire hijabi ta mik'e da niyyar zuwa ta gyara, sai ga Zeituna ta shigo da wata roba mai kyau ta mik'a mata tace "To aci lafiya duniyar Ammar."

Dariya tayi tace "Kai aunty Zeituna kin dai rik'e wannan sunan ke ma."

"Kamar yanda kike rik'e sunan uwata ba." Ta fad'a da dariya, bud'a robar tayi tace "Lahh! Aunty Zeituna yanzu gyara min kikayi?"

"Mun gama aiki ne da madafar za'a rufe sai kawai na k'arasa miki." Tana fad'a ta juya tana fad'in "Na tafi nayi sallah nima."

"Nagode aunty Zeituna."

Murmushi kawai tayi ta fita, ta zauna ta d'iba ta kai bakinta, wani masifar dad'i taji kamar zata tsinka harshenta ko yawu zasu dalolo mata, hannu tasa zata k'ara kaiwa Ammar ya shigo da sallama d'akin Husseina, Husseina data sallame ce ta amsa tare da Amna, yana k'arasa shigowa ta bud'e mishi hannu d'aya alamar ya rumgumeta, sunkuyowa yayi ya rumgumeta tare da manna mata suma a baki yana kallon kwanon hannunta, Husseina ya kalla yace "Hajajju anwuni lafiya?"

"Lafiya lau, har an sauko?" Ta fad'a da raha, bai iya amsa mata ba sai Amna da yace ma "Menene kike ci da yasa kika baro can?"

Shagwab'e fuska tayi tace "Duniyata yakuwa?"

Zaro ido yayi yace "Ya me?"

Baki sake ta sake cewa "Yakuwa."

Da k'arfi yasa hannu ya fizge robar yace "Ubaki ma, Allah baki cinta sai kace wata mayya, kina da k'aramin cikin ne zaki ci wannan abun."

Cikin kuka ta tara mishi hannu tace "Dan Allah yah Ammar taimaka ka ban kar yawuna su k'are."

"Sun jima basu k'afe ba, Allah ba zan baki ba."

Kallon Husseina tayi tace "Dan Allah Hajia ki ce ya bani, ina so na ci."

Da sauri ya fito da waya daga aljihu kawai ya d'ora a kunne ya juya zai fita yana fad'in "Hello, Hello, kai bana jinka."

Tsaf ya fice dan kar Husseina ma tayi magana, dariya ta mata tace "Kin gani ko, dan haka ki hak'ura kawai."

Girgiza kai tayi tace "Je ne peux pas wallay, bari na same shi."

Dariya ta mata tace "To kije, kinga idan da rabon kisha mari sai ki dawo kina kuka."

Tsayawa tayi daga d'aukar hijabin tace "Kuma fa hakane? Ba zai dakeni ba Hajia ai yanzu ya daina."

Saka hijabin tayi ta fita da sauri ta nufi b'angarensu, tana zuwa ta same shi zaune sai k'ara kallon yakuwar yake yana b'ata fuska, yana jin shigowarta ya d'aga kai ya sauke mata idonshi da suka bayar da yanayin k'araso na ci ubanki, cak ta tsaya tana kallonshi da tsoro tana d'an cukuikuye hijabinta, hannu ya tara mata tare da nuna mata cinyarshi yace "...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.N.A]* β˜†πŸ–ŠοΈ


_Bismillahir rahamanir rahim_

_46_


"Zo zauna nan."

Saida ta k'ara yin kalar shagwab'a sosai kafin ta fara takowa a hankali tana nufoshi, k'ank'ance idonshi yayi yana mamakin k'arfin halinta, tasan fa idan ta zo me zai mata, tasan saiya mintsineta ko ya mata wata muguntar, amma duk da haka ta taho kuma a madadin ta koma ko ta nemi wajen b'uya, baisan lokacin da murmushi ya sub'uce masa ba, tabbas k'arfin hali da jarumtarta sun birge shi, ta nuna mishi zata iya hak'uri da shi duk abinda zai mata, kafin ta k'araso sai kawai ya ji babu buk'atar ya mata abinda yayi niyyar yi. Cike da tsoron nan ta zauna akan cinyarshi ta rufe fuskarta ko da ya kan iya kawo mata mari ko ja mata hanci ya matse shi, a hankali ya janye hannayenta yace "Kalleni mana, tsoro kike ji?"

Girgiza kai tayi ba tare data bud'e ba, yana kallonta shima yace "To in dai hakane kalleni."

Bud'ewa tayi ta kalli fuskarshi amma ba cikin idonshi ba, aje robar hannunshi yayi kan k'aramin teburin yana kallonta yace "Fad'a min duniyata me kike so?"

Robar hannunta ta nuna mishi tare da turo leb'enta na k'asa gaba na sama kuma ta shigar da shi ciki sosai, kallon robar yayi sannan ya kalleta yace "Amna bana son irin wannan ciye ciyen fa, da zogale ce ma tafi anfani a jiki, ki bari gobe da safe na miki alk'awarin zan samo miki zogale kinji."

Yanda tayi da fuskarta yasa shi sumbatar kumatunta dan tayi fayau da ita tayi kyau sosai, shafa kumatun yayi yace "Kiyi hak'uri kinji, ai kin yafe min ko?"

Cikin shagwab'a wai ita ga auta ta kama hannunshi dake kan fuskarta tasa babbar yatsarshi baki tana tsutsa, murmushi yayi yana d'an girgiza kai yace "Autar Tanti kenan, rigamar dai ta motsa ko? To fad'a min me zan miki da zaisa ki hak'ura."

Cike da sangarta tace "Ni kawai ka ban na ci wannan, shi nake so na ci, kuma ai ba laifina bane na beby ne."

Cikin muryar dake isar mata da sak'on kiyi hankali fa yace "Amnaaa." Da sauri tace "To kawai ka siyo min kankana."

Rugugugu! Sautin da gabanshi ya bayar kenan sanda ta ambacin sunan kankana, nisa dashi da tayi da kuma samun Amna sunyi tasiri sosai wajen mantar dashi ita, amma kuma bai kamata ace ya manta da ita ko dan abinda ya aikata mata, to amma ya zaiyi? Dole ya manta da ita tunda dai babu komai tsakaninsu, ciki ne dama yake zargin tana da kuma da akwai ciki da yanzu ya bayyana kowa yaji, dan baya tunanin Ummy zata iya yin abinda tayi yanzun, jin ta sake saka hannunshi a baki tana tsutsa yasa shi dawowa hayyacinshi, murmushin yak'e ya mata yace "To bari nayi wanka sai mu tafi tare."

D'agata yayi daga jikinshi ya nufi hanyar d'akin kwananshi, tsayawa yayi ya juyo yace "Amma ke da baki shan kankana?"

"Haka kawai nake sonta yanzu." D'akin ya nufa yana fad'in "Kinyi waya da kankanar asalin?"

Cikin d'aga murya tace "Eh, tana lafiya."

Bayan isha'i suka fita, haka kawai suka dinga yawo suna zaga gari, sun jima sosai kafin ya mata siyayyar kayan ciye ciye suka dawo gida, tana fitowa daga cikin mota ta d'an matse cikinta tace "Wash."

Kallonta yayi sanda yake fitowa yace " Ya dai?"

Duk da abune da take wayan ji amma hakan baisa ta iya fad'a masa ba sai kawai tace "Ba komai, cikina ne ya d'an juya."

Tsaye yayi har ta zagayo wurinshi ya kama hannunta yace "Ki kula fa Amna, karki ja min asara ki sani sabon aiki."

Dariya kawai tayi suka nufi b'angarensu, saida ya tabbatar ta nutsu harta kwanta sannan ya zo ya ga Abba suka tattauna kafin daga bisani sukayi sallama.

*Washe gari* da safe kusan duk familyn ne a falon kowa da wanda ya zo ya gaisar, Ammar ma suna kusa da Zeituna zaune shi da Amna, da k'yar Junaid ya matsa mata ta zo gaishe da mutanen ba dan ta so ba, shiyasa ma ko da ta shigo ko sallama ba tayi ba, tana kallo yana gaishe da kowa amma banda ita, ganin hakan yasa Ammar k'ura mata ido, ko shi dai ai yana gaishe da kowa da girmamawa, amma tsabar rashin kunya ita ba sallama kuma ba gaishe da mutane, ba fa zai d'auka ba, wannan iskancin ba za'a yi shi dashi ba. Junaid na juyowa inda yake dan su gaisa ya kula da kallon da yake mata, cikin dubara ya d'an ja gyalenta suka koma gefe, juyawa tayi zata fita Junaid ya bita da kallo, Ammar daya kula da kowa na wurin ya bita da kallo amma babu mai k'arfin halin da zaiyi magana yasa shi kallon Junaid yace "Matarka raina mutane ne tayi?"

Ido a tsaitsaye ya kalleshi fatanshi kawai su rabu lafiya, ita kuma juyowa tayi tana mishi wanni kallo tace "Kamar ya?"

Saida ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yace "Naga kamar kinfi k'arfin ki gaishe da mutane, me kike ji dashi to?"

Cike da rainin tace "Ina da wani abu d'aya a rayuwata, duk ta yanda aka zo min haka nake zuwa nima, an nuna min ba'a k'aunata a gidan nan, shiyasa nima ban nuna ina k'aunar kowa ba."

Idonta ya kalla yace "Amma ai kinsan girmama mutum ko? Sannan nan ba gidanki bane ko na mijinki, dolenki ki girmama duk wanda kika gani a ciki inhar kina da mutumci."

Murmushi ta masa ta rumgume hannaye a k'irji tace " Idan kuma bana da mutumcin fa?"

Mik'ewar da yayi tsaye yana d'an nad'e hannun rigarshi yasa Zeituna mik'ewa tana kallonshi tace "Dan Allah rabu da ita kaji, bata gajiya da rigima da kowa."

Kallon Zeituna yayi yace "Um um uwa barni, ina so ne na fad'a mata da yaren da zata fahimta, duk rigimar da take muku ai dan bata samu daidai da ita bane, ni ba ita zan tsawatar ma ba mijin nata zan dallawa mari a gabanta ta gani, hakan zaisa ta shiga taitayinta."

Kallon Junaid yayi rai a b'ace yace "Yo ba dan ma ya d'auki mutane 'yan iska ba har wacece wannan yarinyar da zata zauna tana mana fitsara, yaushe ta shigo gidan naka har ta fara baka kulawar da kake ganin ta isa ta taka iyayenka kuma ta zauna lafiya, to in kai ka zama fanko wallahi ni akan iyayena babu yar iskar data nemi ta raina min su kuma na kalleta, dan ubanta kuma ta jaraba ta gani idan ban fizgo hanjin yarinya ba ta baki, to miye a cikin ido banda ruwa."

"Da kyau Ammar, nagode, ka tabka rashin mutumcinka yau Hajia Zeeya'atu na bayanka, tunda shi gindinta ya mishi shamaki da zuciya."

Kowa saida ya kalli Hajia da tayi maganar nan, Amna sagale ta kalle ta wacce ta tsargu da abinda ya fad'a take jin kamar da ita yake tunda dai ita ce matarshi, Ammar kuma a ranshi yace "Tunda rashin mutumci ne kenan kin d'aure min gindi? To na fasa."

Maryama ce tace "To sai me? Ka mari mijina a gabana ka gani, wallahi da nima saina tsinke matarka da mari kuma a gabanka naga me zai faru."

Juyawa yayi ya kalli Amna dake zaune ya tintsire da dariya ya nuna Amna yace "Ke wannan? Jar bala'i! Wallahi kuwa da kinja yau kowa ya kwana da yunwa, ke ki bar bala'i yayi kwana kinji, bana fad'a da mace ni sai maza mazan ma wanda suka k'osa, idan kuma kika cikani sai dai nasa 'yar aljannata ta d'aukar min ke ta cilla a garu."

Cikin taushin murya Amar yace "Dan Allah d'an uwa ka rabu da ita."

Kallon Maryama yayi ita ma yace "Gaskiya baki kyauta ba, banyi tsammanin haka daga gareki ba."

Zaune Ammar yayi yana kallon Amar yana fad'in "To dama me kake tsammani? Baka ga kakan nan nata ba mai masifar fad'a kamar Hajiar gidanmu."

Amar da suke kallon juna ne ya mishi alama da ido cewa Hajiar fa na kallonka, duk da ya fahimci me yake nufi sai kawai ya gyara zamanshi ya ci uwar fuska kamar bashi ba, Husseina kad'ai ta iya fito da dariyarta amma sauran duk sun gimtse ta su, Hajia da kamar ta fashe ce tace "Shiyasa ba ma tab'a zama lafiya ni da kai, ba dai nice mai masifar fad'a ba? Zaka gani, akwai ranar da zaka nemi kaji ma fad'an nawa amma na maka nisa."

Kallonta yayi fuska a had'e yace "Haba Hajiata, raha ce fa kawai, ke kinsan dani dake bata b'acewa, fad'an ki ai ni jinshi nake kamar kukan tsintsaye matuk'ar dad'i a kunne."

Maryama dai basu ma san lokacin data fita ba tare da Junaid, yau ma fad'a sukayi sosai saboda yaji zafin abinda Ammar ya mishi, kuma yasan gaskiya ya fad'a mishi shiyasa ma bai biye mishi ba, amma fa daya mare shi da sai dai cikinsu d'aya ya kashe wani, yanzun ma k'ara fad'a mishi tayi dan sam zaman gidan nan nashi ya fice mata a rai, bata damu ta bar gidan ba tunda kowa na gidan baida mutumci a cewarta.

*Misalin 09:00* na safe Tanti Hadiza ta zo gidan, babban falon ta fara shiga cike da fargaban kalaman da zata ji daga Hajia, a lokacin tana d'akin Alhaji dan haka ta samu tarba mai kyau daga su Zeinabu da Soueiba da kuma Zeituna da bata tab'a ganinta ba ido da ido sai yau, a falon suke suna ta hira ta yaushe rabo inda suka cika mata gabanta da abun sha da ci, fitowar Hajia yasa duk wannan farin cikin ya b'ace kowa ta kama jikinta, duk da ta gane wacece amma bata wani kulata ba ta kalli Zeituna tace "Zaman me kuke anan? Ina ce aiki kuke a madafa."

"Eh Hajia." Ta fad'a tana mik'ewa ta nufi madafar, su Zeinabu ma mik'ewa sukayi inda Hadiza ke mamaki da maganar zuci cewa "Har yanzu bata canza ashe, yaushe matar nan zata daina bautar da matan 'ya'yanta? Allah ya kyauta."

Daga tsaye take k'are mata kallo sama da k'asa, murmushin gefen labb'a ta mata ta kawar da kai daga kallonta tana danna wayar hannunta tace "Wani ko a cikin kaskon mai ka saka shi haka zaka ciro shi a tsiyace, ank'i d'ana ba, amma sanyin ac da abincin gidanshi kad'ai ya isa ya gyara maka jiki."

Nufa tayi kan kujerarta ta zauna k'afa d'aya kan d'aya tace "Ina manta wani abu fa, wasu haka suke zuwa duniya a wahalce kuma su koma babu nasara."

Ita ma murmushin tayi wanda bai fito da hak'oranta ba ta mik'e tana kallonta tace "Ina kwana Hajia."

K'ala ba tace mata ba dan haka ta juya zata fita sai kuma ta kalleta tace "Ba wai zama a cikin daula bane ke nuna kayi nasarar zuwanka duniya, ni a gurina nasarar da soyayyata ma tayi ma nasara ce, wasu basa da sa'ar zama da wanda suke so, ni kuma yanzu haka ina cikin farin cikin da na tabbatar sauran matan gidan nan basa cikinshi, idan kuma k'arya na fad'a ki tambayi kowace kiji zata fad'a miki indai har gaskiya zasu fad'i."

Cikin ladabi ta sake kallonta tace "Kiyi hak'uri abisa abinda ya faru, ganin Amna na zo wacce kullum ke min k'orafin ban zo naga gidanta ba, kuma tace gidan jikin wannan yake shiyasa na lek'o mu gaisa kar nima na watsar daku kamar yanda kukayi, ko ba komai ina da 'ya'ya a gidan nan."

Fita kawai tayi ta barta, tana ganin gidan tasan shine dan haka kawai ta shiga, sallama ta dinga rafkawa har Jamila da Amna suka lek'o su da su kafi kusa, dukansu rumgumeta sukayi da farin ciki, Amna har kuka tayi na ganin mahaifiyarta, haka suka shiga ciki ta zuba mata kayan tab'awa inda suka bud'e shafin hira, a k'alla awanta uku kafin ta tashi suka shiga wajen Umaimah da Maryama suka gaisa, data fito zata tafi a lokacin Amna ke cewa "Mama ki jira yah Ammar yanzu zaki ganshi tunda na fad'a mishi kin zo, ba zaiji dad'i ba idan ya samu kin tafiyarki."

Dariya ta mata tace "To ni dashi kusan kullum ba muna had'uwa ba, kowace juma'a fa sai yaje madarunfa."

Zaro ido tayi tace "Mama kowace juma'a? Amma shine bai tab'a fad'a min ba."

Dariya tayi zatayi magana sai gashi ya shigo da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment