Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makullin mota a hannu, da farin ciki da ladabi suka gaisa kafin yace "Tanti har kin fito ne? Amma ai baki jima ba."

Da murmushi tace "Haba dai ina laifi ai na jima anan, zan wuce can gida ne wajensu Inna zuwa bayan sallah la'asar kuma saina koma."

"Amma kun gaisa da mutanen ciki kuwa?" Saida tayi dariya ta kalleshi tace "Mun gaisa, harda kakarka ma."

Dariya yayi shima yace "Ashe kunsha hira." Dariya tayi kafin ta kalli Amna tace "Ki koma ciki ni zan tafi, sai kuma na sake dawowa ganinki ko auta."

Cikin shagwab'a ta kwantar da kanta a kafad'arta tace "Mama yaushe zaki dawo?"

Kallon Ammar tayi da tunanin abinda zata fad'a mata sai kawai yace "Sai kin haihu mana zata dawo."

Kunya ce tasa Amna k'ara sunkuyar da kanta tana murmushi, Tanti kuma a ranta tace "D'ana kenan, anyi halin ba ."

Ammar ne yace "Muje tanti saina ajeku." Kallonshi tayi tace "A'a haba daka barshi ma, watak'ila akwai abinda kake wannan shirmammar ta taso ka."

"Ku zo muje kawai, ai babu abinda yafi mana ku." Ya fad'a yana nufa hanyar fita, rik'eta Amna tayi sosai wai babu inda zata je, abu da gaske sai kuwa tasa kuka ita sai dai ta tafi da ita, ita ma rumgumeta tayi tana fad'in "Saurare ni auta, kina ji na da kyau?"

Kai ta d'aga alamar eh, cikin fitar da kowace kalma take fad'a mata "Kiyi hak'uri ki koma d'akinki ki zauna, na miki alk'awarin zan sake dawowa ba da jimawa ba, wannan kukan yasa dama tun farko ban zo ba, amma idan kikayi shiru yanzu to zan sake dawowa kuma na taho miki da abinda kika fi so, zuwa lokacin nasan Hamna ta dawo kinga ita ma na ganta."

Turo baki tayi tana d'aga kafad'a da fad'in "Um um, um im, ban yarda ba ni gaskiya, kuma Hamna ma wa yasan ranar dawowarta."

"Au ba zaki hak'ura ba kenan?" Cikin turo baki tace "Na k'iya."

"Shikenan to nasan maganinki." Ta fad'a tana kallon inda Ammar ke tsaye, cikin d'aure fuska tace "Yarona zo ka min maganinta tunda bata jin rarrashi."

Takowa ya fara yi da k'arfi yana fad'in "Ai kuwa tanti bari kiga yanda zanyi da 'yar banza." Takalmanshi ya ciro yana shirin wurga mata da gudu ta koma d'aki tana rusa kuka, dariya suka saka mata inda tanti tace "Ai maganinki kenan, da kin kwantar da hankalinki da munyi sallama cikin farin ciki."

Suna nufa k'ofa Ammar yace "Tanti karki damu, insha Allahu zan kawo miki ita tayi sati d'aya, dan yanzu ta fara kumburo min baki kenan har illa masha allahu indai ba ganinki ta sake yi ba."

Dariya tayi tace "Auta ce ku barta tayi rigimarta, amma zaka iya barinta tayi sati d'aya ko?"

Kallonta yayi sai yaga ita ma kallonshi take kallo mai nuna na fa sanka ba zaka iya ba, sunkuyar da kai kawai yayi yana murmushin jin dad'in yanda ta san shi sosai tare da fatan ina ma mahaifiyarshi ce ta mishi wannan fahimtar, fita sukayi inda ya kaita gidansu dan ta gaisa da yan uwanta.

Kamar yanda ya fad'a kam ya cika alk'awari, ba tare daya fad'a mata ba kawai yace ta shirya, sai kawai ganin tayi sun d'auki hanyar garin, tunda ta ga haka ta fara murna tana jin dad'i sosai, da suka je saida ya wuni kafin ya juyo ya barota, murna a gurin Amna ba magana yau zata kwana tare da ummanta, ba ita kad'ai ba ita kanta tanti tayi farin ciki sosai, da dare da sukayi waya da Hamna ta fad'a mata gata nan ita kanta sai taji kamar tayi hira, anan take tambayarta me yasa yanzu ta b'oye lambarta in aka kirata sai dai ya nuna numΓ©ro unkwnon sannan me yasa bata Whastup? Haka kawai shine abinda ta fad'a mata, a wajensu Hamna ma da Ummy komai yana tafiyar musu daidai, sai dai basa cikin kwanciyar hankali, kullum Hamna tana fad'a ma Ummy idan fa asiri ya tonu tana jin tsoron abinda zai faru, ita ma kuma ta sani akwai gagarumar matsala, amma a ganinta lokaci ya k'ure musu.

Tanti Hadiza ta ga abinda yafi k'arfinta, bata san yaushe kuma a wane lokaci Amna ta zama marar kunya ba, dan tunda ta zo idan yau bai zo ba gobe zai zo, a gabanta saita rumgume shi ko ta sumbace shi, idan suka shiga d'akinta duk da babu abinda ke shiga tsakaninsu, amma irin yanda yake jin dariyarsu da maganganu k'asa k'asa abin nasa kanta girma, idan kuma dare yayi suna waya wani abun idan ta fad'a saita kalleta da mamaki, shiyasa yanzu daya shigo gidan ita kuma saita shiga mak'ota ko kuma ta shige d'akin mijinta ita ma, a haka ta kammala sati d'ayan nan suka koma gida.

Lieutenant ya fara mata k'orafi kan rashin dawowarta kan lokacin data fad'a mishi, amma sai take fad'a mishi basu gama bane ya k'ara hak'uri, har saida Hajia ta fara fad'a wanda Ummy tace kamar wak'a take jin fad'an nata, tunda dai har ta riga data tafi to anyi mai wuyar, a haka har lokaci ya k'ara kwararawa.

*Bayan Wata Biyar*

*France*: tunda ta shiga watan ta dama aka basu lokacin da za'a kawota kafin ta fara nak'uda, dan haka k'arfe *11: 54* suka shiga da ita d'akin haihuwa, Ummy bata san tana kuka ba saida wata banasariya ta dafa ta tace mata ta dinga mata addu'a zata haihu lafiya, tunaninta a lokacin shine idan fa aka samu matsala ya zatayi? Alwala ta d'auro ta shiga fad'awa Allah kukanta, bata matsa daga kan sallayar ba misalin *12:38* aka sanar da ita haihuwar Hamna lafiya, yaron bai dameta ba sai mahaifiyar da take tambayar ya take? Lafiya lau ita ma aka fad'a mata, saida tayi sujadar godiya ga ubangiji kafin ta shiga ganinta, murmushin daya sub'uce mata ne yasa Hamna dake kwance kallonta tace "Ummy lafiya?"

Dake tsaye inda take kusan gadon jaririn ta sake dariya taja hancin yaron tace "Ya rantse saiya zo duniya, gashi dai ya zo yanzu kuma *BADAK'ALAR* zata fara musamman mahaukacin ubansa yasan dashi."

Jim ta d'anyi saboda haushin Ammar data sake ji, har ga Allah tana b'oyewa ne dan kar Ummy taji ba dad'i, da k'yar ta kalleta tace "Kin fad'awa Abba ne?"

Girgiza kai tayi tace "Hamna ba zan sanar dashi yanzu ba, kema kin sani ina fad'a masa zai biyo jirgi ya taho, ni kuma ina so mu fara tafiya gida na d'an shirya ki da kuma ni saina kira na fad'a musu."

Shiru tayi kawai dan bacci ke son d'aukarta, saida aka k'ara tabbatar da lafiyarta da bebyn sannan aka sallamesu bayan an bata magungunan da zasu taimaka mata, suna zuwa gidan da suke Ummy ta zama mai haihuwar tare da anfani da duk abinda zai kawo mata ruwan nono wanda dama ta tanede shi saboda ranar, sai lokacin ta kira gidan ta sanar dasu, lieutenant yayi murna sosai da kuma fad'an rashin dawowa har haihuwa ta risketa tana nesa dasu, ya fad'a mata zasu zo tare da Hajia dan ba zai yarda ta taho yanzu ba, saita nuna masa ba komai kawai idan sukayi ko sati biyu zata dawo, tunda Zeituna ma gaf take da haihuwa bai kamata ya taho ya barota ba, da haka ya gamsu ya zauna sai hotunan yaro da suka game gidan da familyn cikin d'an lokaci.

*Gaga's house* da dare suna tafiya a hankali a cikin unguwar ya ga duk tayi sanyi sosai ba yanda ya saba ganinta, jawota yayi jikinshi yace "Lafiya? Me kike tunani?"

Saida ta d'ora hannunta kan k'irjinshi tana takawa a hankali tace "Hamna nake tunani, tunda na tashi yau nake tunaninta ina ji kamar wani abu na faruwa da ita, ta canza sosai amma kuma bata son yin doguwar magana da ni, bansan me yake damunta ba."

Shafata yayi yace "Karki damu kinji, watak'ila bata jin dad'in zaman gidan nan ne shiyasa, amma idan kina so saina kaiki ki ganta amma fa bayan kin haihu."

Murmushi tayi tace "Nagode."

Wayarshi tayi k'ara yana dubawa ya ga kiran Amar, yana d'auka Amar tsabar farin ciki da kuma tsokana yace "Kai yaro kana ina? Ka zo gida fa Ummy ta haihu."

Gabanshi kawai yaji ya fad'i ba tare da sanin dalili ba, amma saboda jaraba sai yace "Amar ni ne yaron? Ni ne dai yaro ko? To ka bari na dawo gidan zaka maimaita haka da bakinka."

Amar ne yace "Naji dai, yanzu ka duba WhatsApp d'inka na tura maka hoton bebyn, anan dai gida kowa ya damemu da cewa wai yafi kama da kai, ni kuma a ganina ai dani da kai duk d'aya ne."

Murmushi Ammar yayi yace "Hakane, amma ai na fika manyan ido, na fika dogon hanci, kai kawai gaskiya suka fad'a na fika kyau."

Yana fad'a kuma ya kashe wayar ya shiga WhatsApp, dannawa yayi foton ya fara alamar bud'ewa, fad'uwar da gabansa ya sakeyi yasa shi d'auke idonshi daga kan yaron, a hankali ya sake kallonshi idonshi bud'e kamar ba yaron da aka haifa yau ba, sanye da kayan sanyi masu hula safar k'afa data hannu, hancinshi tubarkallah zungurere. A hankali yake jin abun na shigarshi kamar sihiri, ba zai iya tantancewa ba k'auna ce ko soyayya, amma dai k'anan nashi ya shiga ranshi daga kallo d'aya, murmushi yayi ya jawo Amna yace "Kinga Ummy ta haihu."

Da sauri ta k'ura idonta tana fad'in "Na gani." Tana ganin yaron cikin farin ciki tace "Wow mai kama da jarumi na."

Kallon idonshi tayi tace "Kamar kayi kaki ka tofar wallahi."

Kallonta yayi, haka kawai yaji ya tsargu sai kawai ya share yace "Haka zaki haifo naki kema sak ni."

Ko da suka dawo gida sun samu anata wannan murna, lokacin Zeituna ma ita kawai tasan me take ji ana dai ganinta, saida dare yayi ta fara nak'uda sosai, likitar su Ammar aka kaita da gaggawa, ta jima tana nak'uda ta galabaita sosai, ana kiran sallah asuba ta haifo jaririyarta ita ma mai kama da ita gashi har saman goshinta luf luf, amma ana buk'atar k'ara mata jini dan ta rasa shi, lieutenant ne yace a duba nashi, har an duba za'a d'iba Ammar yace a d'ibi na shi, lieutenant yace "Ai akwai buk'atar a fara dubawa idan yayi daidai."

Murmushi ya masa yace "Ni fa jininka ne, ina da masaniya akan jininka da nawa Abba, amma in baka yarda a dararawa matarka ba sai an duba ni to a duba."

Dariya kawai lieutenant yayi, duk da haka da aka shiga ciki saida yasa aka gwada jinin sannan aka diba aka saka mata, tubarkallah masha Allah, a cikin kwana d'aya an samu k'aruwar yara biyu *Fatima Zahra* da kuma *Shureim*, fatan Allah ya raya.


*Bayan sati biyu*...

*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_47_


*Bayan sati biyu* yau Junaid ya tafi makaranta yana cikin koyarwa aka ce ana sallama da shi, yana fitowa yayi mamaki sosai ganin *Sani* tare da *Salma* a tare dashi, k'arasawa yayi suka gaisa ita ma ta gaishe shi, da mamaki yace "Tonton lafiya dai ko?"

Saida ya kalli Salma ya mata alamar ta basu wuri kafin ya gyara tsayuwa yace "Lafiya ba lafiya ba Junaid, wata alfarma na zo nema a wajenka."

_*Anzo wajen, Sani dai d'an Innusa ne yayan Alhaji, wanda yace baya buk'atar taimako ko alfarmar Alhaji Suley, dalilinshi yasa Hajia dagewa ta ga yaranta sun zama masu muk'ami a gwamnatacce, meya faru yau da har aka zo neman alfarma a wajen ahalin Suley?*_

Junaid ne yace "Tonton wace irin alfarma kuma? Ai daka kirani a waya sai naje har gidan ma."

Murmushin jin dad'i yayi yace "A'a ba sai ta kai ga haka ba, dama akan maganar makarantar yer uwarka Salma ne?"

Saida ya kalli inda take tsaye da uniforme d'inta yace "Wani abu ne ya faru?"

Cike da damuwa yace "Kasan dai yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi hali ba, tana tare da k'awaye ne da basa jin magana wanda yasa sukayi rashin kunya wa malaminsu, hakan yasa aka koresu tare da tab'a musu conduite (bansan me zan kirashi da turanci ba), yanzu tsawon sati d'aya kenan muna ta bibiya da bayar da hak'uri dan a gyara ta koma, amma abun ya ci tura wallahi, shine sai jiya malamin yace idan akwai wani babba ko malamin da muka sani mu mishi magana, shiyasa na tuntub'e ka dan kasa baki dan Allah ta koma."

Ajiyar zuciya ya sauke, zai so ya taimaka musu sai dai kuma yaji Hajia tace duk wanda d'aya daga cikin iyalin Innusa ya neme shi taimako ya fara fad'a mata kafin yayi, bai nuna masa komai ba sai cewa da yayi ba komai zaiji da matsalar, godiya ya masa suka koma suka tafi, shi ma aji ya koma da tunanin yanda zaiyi, shin ya fara fad'a mata ne ko kuma kawai yayi? Da wannan tunanin ya kammala ya dawo gida, da rana tsaka ya tarar da tashin hankalin da baiyi tsammani ba.

Yaran gidan na wasa tare da Huda wacce ita kanta bata cika sakewa ba idan tana cikin yaran, Hajia na fitowa ta gansu sai kawai ta musu tsawa tace "Kai, maza ku wuce ciki, karna sake ganinku da yarinyar nan dan matsatinku da nata ba d'aya bane, kuji ni ko."

Kai suka d'aga mata alamar eh suka shiga ciki, wannan magana data fad'a a kunnen Maryama wacce ita ma ta fito kiran Huda dan bata so tana shiga cikinsu, tana jin haka ta matso tace "Da me suka fita Hajia? Kina babba kike fad'in maganar nan a gaban yara, ina ce dai nan daga jikokinki sai jikokin Hajiarsu Jibril, ko ita ma jikokinta basa da damar yin wasa a gidan nan ne?"

Su Zeinabu dake zaune suna gyara kayan da zasuyi girkin dare dashi ne suka kalleta, Husseina ma dake gefensu tana b'are musu tafarnuwa ce ta kalleta, Hajia ce tace "Suna da dama, amma dai banda wannan 'yar taki."

Wani kallo ta mata tace "Saboda me? Saboda ita ba jikarta bace? Na ga ita ma daga tsatsonta ta fito, dan haka ki barta ta wala a gidan ubanta." Ta k'arashe cikin d'aga murya.

Mik'ewa Husseina tayi ta matso kusanta da mamaki tana kallonta tace "Me kike nufi Maryama? Tsatsona daga ina?"

Cikin d'aga murya tace "Eh tsatsonki, ki tambayi Jibril zai fad'a miki yanda akayi haka ta faru."

Kallon Hajia tayi tace "Ba kina ganin karuwa ce ni ba, to d'an gidan nan ne ya mayar dani karuwa, shi ya bani lasisin zama abinda na zama, dan haka shima yana da kamashon duk abinda na aikata, nima da fari 'ya ce kamar kowa, Jibril ne ya tirsasni har na samu yar da ban haifeta a gidan aure ba."

Hajia data kafeta da ido sai kawai ta tintsire da dariya har da d'an rik'e ciki, kallonta kowa keyi da mamakin abinda take ma dariyar, Husseina kuma k'asa tayi da kanta dan tasan ita take ma dariyar sai Inna lillahi da take maimaitawa, Soueiba taso tashi tsaye amma jikinta taji yana rawa rawa sai kawai ta damk'e kujerar da take zaune tana kalmar shahada, a hankali ta kai idonta kan Huda a lokacin ita ma tana kallonta saboda jin tana kalmar shahada, ido cikin ido suka kalli juna ita da yarinyar, ba za tace tana k'in yarinyar ba, sai dai tunaninta ya akayi Jibril ya musu haka. Hajia dake dariyar nan ce ta kalli Husseina tace "Kin gani, illar karuwanci kenan, ke kinyi gashi kuma har yanzu bai daina bibiyarku ba, kin haifeshi a yawon dandi, yayi k'ok'ari shi ya haifi nashi yaran a aure, amma gashi jikanki ya kawo miki yar dakan kuka."

Cike da shak'iyanci ta sunkuya tace "Ina miki barka da k'ara samun k'aruwa."

Wata dariyar ta kece da ita ta juya zata tafi sai kuma ta kalli Maryama tace "Ni ban ma yara da jikokina irin wannan tarbiyyar ba, in dai har kinga d'an gaba da fatiha a ahalin nan to ki tabbatar daga wani k'ugun ya fito amma ba tsatson Zeeya'atu ba, can ku k'arata da matsalarku."

Tana fad'a ta juya ta bar wurin, Maryama ma ta kama hannun Huda zasu juya ta ga Junaid, kallon kallo akayi inda yake binta da wani kallo mai wuyar fassarawa, girgiza kai yayi yace "Ban tab'a kawo haka ba Maryama, zuciya d'aya nake sonki kuma nake zaune dake, ashe Huda yar d'an uwana ce baki tab'a fad'a min ba? Nagode da abinda kika min, amma a gaskiya aurenki ya fice a raina, sam ba zan iya ci gaba da zama dake ba, kawai kije na sakeki."

Tab'e baki tayi tace "Nima ban nemi takardata a wajenka bane dan karka tambayeni dalili, amma ka sani auren gidanka ya jima da fice min a rai, shiyasa ban bari ma na samu ciki da kai ba bare na haihu, hakan zaisa iyaye su dinga tausata da cewa nayi zaman 'ya' ya, ni kuma bana d'aya daga cikin matan da bak'in cikin namiji zai kashe su."

Tana gama fad'a ta kama hannun Huda suka nufi inda Soueiba ke zaune, tura mata ita tayi gabanta tace "Zan koma gidan iyayena nima, nan kuma gidan ubanta ne ta zauna tare da ku, ruwanku ne ku bata guba ta ci ko ku taushe mata kai da matashi har ta daina numfashi, ni dai na sadata daku na huta da bata amsar cewa zai kaita wajen yan uwanta ita ma."

Juyawa tayi ta koma b'angarenta, cikin sauri da kuka da bata san ko na miye ba ta had'a kayanta ta bar gidan ko Huda bata san fitar ta, Zeinabu da surutu ke ciciyarta kai tsaye b'angaren Jamila ta nufa wacce a lokacin ke jin ciwon baya shiyasa ko gaishesu bata zo ba yau, tana shiga ta same ta zaune k'asan carpet ta mik'e k'afafu, ba tsayawa ko tunanin wani abu kawai daga tsaye tana kallonta tace "Ke Jamila, ashe Jibril d'an iska ne shima shiyasa Hajia ta had'aki da shi, yanzu gashi nan asiri ya tonu wannan yarinyar Huda 'yar shi ce."

Kamar ta k'ara sara mata guduma a tsakar baya, sai kawai tayi wani zullo kamar an fizgota tare da dafe baya ta kwamtsa salati ido rufe ruf, hannu ta fara yarfawa tana fad'in "Inna lillahi wa'innailaihi raju'un, la'ilaha illalah, Mama bayana, wayyo Allahana Mama, bayana Mama zan mutu, wayyo Mama..."

A rikice ta fita ta nemo taimako, Soueiba ce tayi k'arfin halin kiran Jibril ya zo a matuk'ar gigice, ganin halin data shiga jikinta sai rawa yake yasa shi lailayarta a hannu ya nufi mota da ita, a baya suka biyoshi da kayan haihuwarta aka nufi likita, Ammar na asibiti a lokacin aka kawota, ko da aka shiga da ita aka ga jininta ya hau ga kuma borin gishiri ta yanda ba zata iya haihuwa da kanta ba yasa docteur d'in cewa kawai a mata aiki, Jibril na kuka yace Ammar dan Allah yasa a dubata ta haihu ba sai an fasata ba, kwantar mishi da hankali yayi tare da umartarshi yasa hannu, yana saka hannu docteur d'in ya shiga d'akin tiyata (tun kafin a bud'a mère et enfants), cikin hukuncin ubangiji saiga santalelen yaro an fito mata dashi sak ubanshi, amma fa uta saida akayi da k'yar aka ceto ta kafin aka shiga bata kulawa, d'akin sama aka kaita tare da hana kowa shiga dan ta huta, a lokacin Jibril da Soueiba suna k'asa ne ta kalleshi da yanayin ka ban mamaki tace "Jibril ashe yaudararmu kake yi, ban tab'a tunanin haka daga gareka ba wallahi, sai ga yarinyar 'yar shekara bakwai wai a matsayin 'yarka."

Jim yayi kanshi k'asa cike da kunya, ya jima haka kafin yace "Kiyi hak'uri Mama, tsautsayi ne da shar..."

Da sauri tace "Sharrin shaid'an ko? Nasan abinda zaka fad'a kenan, wai duk uban daya tsula tsiyarshi a k'arshe sai yace maka sharrin shaid'an, kai yanzu kasan kammaninshi ne?"

Jin yayi shiru yasa tace "Shikenan, yanzu ai ba fad'a zamu maka ba tunda na banza ne, kawai saimu rumgumi k'addarar a yanda ta zo mana."

Cike da son nad'e tabarmar kunyarshi yace "Ko akwai abinda ake buk'ata yanzu?"

Cikin sanyi tace "Akwai mana." Zana mishi tayi duk abinda buk'ata ya tafi zuciyarshi a cunkushe babu dad'i, saida ya kawo komai da ake buk'ata har lokacin Jamila na d'akin hutu ita kad'ai ya juya ya koma, bai zame ko ina ba sai gidan malam Rabi'u, fitowa yayi a soron gidan suka zauna kan tabarma, cikin mutumci suka gaisa kafin Jibril yace "Malam nine mahaifin Huda, maganar gaskiya sanda abinda ya faru har ya faru bansan yer uwata bace, saida nasan waye kakana saina tabbatar da cewa ashe *dara ce ta ci gida*."

Kallonshi yayi da mamaki, Huda yar shi ce dama? Nunfasawa yayi yace "Ikon Allah, 'yarka ce dama? To ya zaayi sai hak'uri ai komai ya wuce, nima waccen d'in daya faru ina mai hak'uri ku yafe min, wallahi daga abinda ya faru yanzu nayi nadama."

Kallonshi kawai yayi bai tanka ba, malam d'in ne yace "Mahaifinka har yanzu bai zo ya ganni ba, nasan shima hushi yake dani kamar Husseina."

Kallonshi yayi yace "Hajia kam tana hushi da kai, amma Abba zai iya zuwa idan kana buk'atar hakan."

Kallonshi yayi yace "Idan ka min haka zan ji dad'i sosai."

Jinjina kai yayi yace "Ba komai zai zo."

Mik'ewa yayi yace "Ni zan koma, da yake matata ta haihu yau d'in nan."

Da fara'a sosai yace "Ah masha Allah, me aka samu?"

"D'a ne, aiki ne aka mata."

Tsaye ya mik'e shima yace "Allah sarki, Allah bata lafiya ya raya kan sunna, yanzu ku nawa ne ga Labaran?"

Murmushin yak'e ya masa yace "Mu biyar ne, maza uku mata biyu."

Ammar na zuwa gida ya samu Junaid zai shiga falon Hajia, gaisawa sukayi sai Junaid yace "Yawwa dan Allah muje tare ka rakani wajen Hajia."

"Lafiya?" Ya tambaya fuska a had'e, nan ya kora mishi bayanin abinda ya faru, kallonshi yayi yace "Yanzu kana nufin baka taimaka ba saika nemi izininta?"

"Ni ba izininta zan nema ba, zan dai fad'a mata ne kamar yanda ta buk'ata."

Girgiza kai yayi yace "Shashashu ta d'aukeku, wallahi na tabbata dan tayi gadara da an nemi alfarma ne a wajen zuri'arta shiyasa tayi haka, ko ka manta abinda Alhaji ya fad'a mana ne wanda yasa shine silar da bata shiga sabgar data shafi Alhaji Innusa da iyalinshi, dan haka kawai kaje ka taimaka musu indai zaka iya yan uwanka ne."

Cikin fargaba yace "To ai ina jin tsoron abinda zata iya yi kuma idan taji, ka fa san halinta."

Tsaki Ammar yayi ya shak'o bakin aljihun rigarshi ya fizge shi har zuwa motarshi ya bud'a ya jefashi ciki, zagayawa yayi ya shiga shima suka tayar, suna barin gidan yace "Allah ya baka dama amma ka kasa anfani da ita wai har saika nemi izinin wata hallita, wannan wace irin rayuwa ce kuke? Matar da ko dukanku ba zata iya ba tsabar k'arfinta ya k'are, yo ni duk hukuncin da zata yanke ko take yankewa a kaina ai alkairi yake zamar min, dan haka ta dad'e bata yanke hukuncin ba."

Bai tsaya ko ina ba sai cikin harabar makarantar, tare suka fito inda Junaid ke gaba har ofishin shugaban makarantar, bayan gaisuwa suka fad'i abinda ya kawosu, sosai suka bada baki tare da alk'awarin jan kunnenta hakan ba zai sake faruwa ba, nan komai ya wuce suka dawo bayan enveloppe d'in da Ammar ya aje mishi a matsayin ya sha ruwa, daga nan tare suka wuce d'an gulbi suka sanar dasu yanda ake ciki, farin ciki da murna basu misaltuwa wajensu.

*Tazarar* minti sha biyar ta saka tsakanin lokacin saukar jirginsu da lokacin data fad'a mishi ya zo d'aukarsu, a wannan tsakanin ne sanda jirginsu ya sauka ta samu ta tura Hamna gida, lokacin na cika kuwa sai ga lieutenant tare da dreba suka d'auketa, tunda ya karb'i Shureim ya kasa saki sai wasa yake

Please Login or Register in order to submit comment