Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abunda kika san Abba baya so, duk zafin zuciyar Abba kana iya zama kayi hira da shi ku fahimci junanku, amma ko yau Abba zai shigo gari sai kaji hayanuyarshi kin b'ata masa rai."

Haushi ne yasa Zeinabu cewa "Kai ni fita ka bani wuri, tunda kana bayan uban naka saika zo ka bashi kashi."

Tsaki tayi ta mayar da k'ofar ta rufe duk da bata rufu da kyau ba dan ya riga ya b'allata, shi kuma fita yayi ya samu mahaifin nashi zaune ya tangale gwiwoyin hannunshi kan cinyoyinshi ya dunk'ule hannunshi yana dukan d'aya hannun, Hajia ce kawai zaune tana kallon tv da tunanin idan ya sauko sunyi maganar da zasuyi akan tafiyarsu ta gobe, suna haka su Alhaji suka shigo tare da lieutenant, bai ma kowa magana ba kuma suma basu damu ba sun san kayan ne suka motsa, zaune sukayi sai Alhaji daya kalli Junaid yace "Ka kira min uwar 'yan biyu, idan ka dawo ka kira min su kansu yan biyun."

Sama ya haura ya samu Sa'ada can ya kirata ya dawo, b'angaren su ya nufa ya kira Ammar da Amar suma suka zo, Alhaji da kanshi ya kira Husseina da Labaran da suke tattaunawa suma kan auren Jibril da Jamila, saida suka had'u ya kalli kowa da kyau kafin yace "...


πŸ‘πŸ‘πŸ‘
17/06/2020 Γ  22:08 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_19_


"Abinda yasa na taraku dama dan na fad'a muku wani abun alkairi ne daya tunkaro mu, insha Allah nan da kwana uku zamu sake yawa a gidan nan."

Shiru kowa yayi sai kallonshi da suke babu wanda yace wani abu, Husseina ce tace "Masha Allah, ah lallai abun farin ciki tunda zamu k'aru ne, amma ta ina?"

Kallon Hajia yayi data tsura mishi ido tana jiran tajiba daidai ba ta fara masifa, had'e rai yayi sosai dan karta kawo mishi wasa kafin ya kalli Sa'ada yace "Sa'ada, kiyi hak'uri abisa abinda ya faru, laifina ne bana mijinki ba, kamar yanda zaki ji yanzu shima haka kawai yaji na yanke hukuncin, amma na tabbata idan kuka ji dalili na zaku fahimce ni, nasan kina da ilimi kuma ba yarinya bace ke, idan har kin kama girmanki hak'ik'a zakiji dad'i sosai anan gaba, 'ya na d'auke ki kamar yanda babba yake d'ana, ina fatan kema zaki min biyayya."

A ladabce ta kalleshi ta kashe murya tace "Abba insha Allahu ba zan baka kunya ba, nima a uba nake kallonka wallahi, ka isa ka zartar da kowane irin hukunci a kanmu bamu da ja akai."

Cikin jin dad'i yace "Alhamdulillah, nagode da kika fad'i haka, dama ba wani abu bane, yarinyar nan dake muku aiki Zeituna, ita ce a wani mawuyaci hali da tale buk'atar taimako, shiyasa yau d'in nan na nemawa *Baba na* aurenta, kuma kawunta ya amince nan da kwana uku za'a d'aura auren bayan sallah juma'a insha Allahu."

Kowa kallonshi ya sake yi, kusan tambayoyin d'aya ne suke yawo a zuk'atansu, Zeituna? Lieutenant kuma? Meyasa sai shi to? Wani murmushi Sa'ada ta k'irk'iro tace "Masha Allah, Abba wannan abun farin ciki ne daya kamata mu godewa Allah, gaskiya naji dad'i har raina wallahi, Allah yasa alkairi ya bamu zaman lafiya, gata kuwa yarinya mai nutsuwa da ladabi, dan ko ido bata had'awa dani."

Kamar daga sama Ammar dake zaune k'afa d'aya kan d'aya yana danna waya yace " Amma ai tana had'awa da mijinki ko? Kinga Ummy karki fad'i abinda kika san ba haka bane, mu maza munfi kowa sanin yanda kuka tsani kishiya kamar yanda kuka tsani mutuwarku."

Kallonshi kowa yayi amma shi hankalinshi na kan waya bare ma ya ga kallon da bai masa ba ya sake magana, Husseina ce tace "Amma Ammar ai sai mu jinjina mata tunda har zata iya k'ok'arin b'oyewar ma."

Sai lokacin ya d'ago ya kalli lieutenant ya kalli Alhaji yace "Alhaji, yanzu domin Allah meyasa sai Abba zaka had'a ta dashi? Shin kaga yarinyar kuwa? Ita fa yarinya ce shi kuma tsoho, me zai sa idan taimakonta kake so kayi ka k'i had'a ta da d'aya daga cikin matasa majiya k'arfi? Amma ace sai uwar mu ce kawai ake sha'awar ganinta da kishiya, to gaskiya ni dai ban amince da auren nan ba, ai ga Jamil nan, ya isa aure shima, a had'a shi da ita ma tunda shine Hajiar makka bata wa mata ba, idan yarintar shi kuke gani ku had'a shi da ita nan da kwana ukun kuga idan ba'a nuna muku bayyanar ciki gwajin da za ayi mata fa kafin bikinmu, dan haka kawai ku bar maganar nan."

Lieutenant ne ya kalle shi yace " To marar kunya fitsararre, kenan duk wurin nan kai kafi uban kowa bakin iya magana, wai ni wa ma ya gayyato shi wurin nan ne da har zai zo yana mata iya shege?"

Gyara zama Ammar yayi yace "Ni fa ina zamana aka ce na zo, kasan meyasa aka ce na zo? Saboda nine babban d'an ka kuma sanyin idaniyarka na farko, ana so aji ta bakina ne kuma na fad'a ni dai ban yarda a had'a k'azamar yarinyar nan kishi da uwata ba."

Lieutenant zaiyi magana Alhaji ya kalli Ammar yace "Ammar wannan fa hukuncin dana yanke ne, yanzu ja zakayi da ni kenan? Bayan shi kanshi uban naka ya amince."

Mik'ewa yayi yace "Da alama ba zamu fuskanci juna daku ba, amma yarinyar nan tana shigowa gidan nan a matsayin matar ubana kuma kishiyar uwata wallahi saina rabata da mak'ogwaronta in yaso ayi duk wacce za ayi."

Colonel da har yanzu Zeinabu yake hangowa shi dai kallon kowa kawai yake, juyawa Ammar yayi zai fita Hajia wacce farkon al'amarin ita ma daru taso tayi, amma ganin babban jikan nata ya nuna bai yarda ba alhalin gata zaune yasa ta shirya b'ata mishi rai, cikin gadara tace "Ka ce baka yarda ba? To yanda da baka yardan ba ya za ayi kenan? A fasa?"

Juyowa yayi yace "Eh haka nake nufi."

Murmushi ta masa tace "To bari kaji Ammar, wallahi auren nan kamar anyi an gama, yar aikin gidanku zata shigo gidan nan a matsayin kishiyar uwarka, za'a ware mata d'aki kamar yanda aka ware ma uwarka, ubanka zai raba musu kwana, a gaban idonka dana uwarka zai shiga d'akin amaryar shi sai dai in kunga haka ku had'e zuciya ku mutu, kai idan da rabo ma nan da wata tara sai kunga sabon k'anenku da idonki."

_Ina fatan dai kun fahimci inda yayi gadon rashin kunyarshi da fitsara?_

Wata dariyar rashin mutumci ya mata yace "Hajajju mutan makka, ban miki musu ba cewa madarar mahaifina zata iya tasar d'an adam ba, amma gamsar da ita matar kam w..."

Cak ya tsaya da kalamanshi saboda saukar marin akan kumatunshi, Ummy ce tsaye gabanshi tana huci dan ba zata iya saurarenshi ba, da yatsa ta nuna masa k'ofar fita tana fad'in "Fita daga d'akin nan, ka fita nace."

Kallon Ummy yayi idonshi jawur da su kamar zai kama da wuta, cikin wani irin yanayi ya kalli Ummy kai kace ramawa zaiyi yace "Ummy mari na fa kikayi? Akan maganar k'azamar yarinyar da tsabar datti da za'a d'auke ta a jefa a cikin ruwan *Madarunfa* babu abinda zai hana ruwan yin bak'i k'irin, shikenan na fita."

Kallon Alhaji yayi wanda shi kanshi baiji dad'in marin ba yace "Alhaji na zo ne saboda ance kai kake nema na, amma ba dan haka ba da babu abinda zai sa na zo dan duk nan ciki bayan kai babu wanda zai iya kirana domin magana ta arzik'i."

Juyawa yayi zai fita cikin k'arajin murya Ummy ta fashe da kuka tace "Fita d'an iska kawai, duk nan ciki waye sa'anka da zaka zauna kanawa fitsara da rashin kunya."

Tsayawa yayi ya juyo da k'arfi da niyyar magana amma kuma zuciyarshi bugawa take da sauri, k'urawa Ummy ido kawai yayi kamar zai cinyeta d'anya, bubbuga k'irjin ta tayi tace "Eh na fad'a, kai sarkin zuciya ko? Ranka ya b'ace ne? To zo ka dake ni Ammar."

Husseina ce ta mik'e ta kamata ta zaunar da ita tana fad'in "Dan Allah Sa'ada ki daina zubar da hawaye akan d'an da kika haifa a cikinki, shin kinsan tasirin da hakan zai masa kuwa?"

Cikin kuka ta kalli Husseina tace "Hajia menayi? Wane laifi na aikata a duniya dana cancanci haihuwar Ammar? Shi fa ba k'aramin yaro bane, amma kullum saiya b'ata min rai a gidan nan hankalinshi ke kwantawa."

Ammar da har yanzu ke tsaye yana kallonta idonshi ne suka sake rinewa, bugun zuciyarshi kuma ya sake nunkuwa, had'e hannunshi yayi ya dunk'ule shi cikin b'acin rai da neman wanda zaiyi masifa da shi ya juya, ai kuwa tvn Hajia ya kalla ya gabzawa dunk'ulellen hannun nan, abinka ga tvn zamani kuwa wacce ke manne a jikin bango sai kuwa ta gabce ta fad'o k'asa inda ta bugi k'aramin teburin glishin da aka d'ora dΓ©coder da kuma remonte, a tare kayan duk suka fad'o suka watse, juyowa yayi lokacin da wasu hawayen bak'in ciki da takaici suka zubo daga idonshi cikin muryar da zata tashi hankalin mai sauraro ya rik'e murfin k'ofa yace "Idan har kun tsane ni ku kashe ni mana, me ma yasa kika bari na zo duniya baku kashe ni ba? Ku kashe ni mana na huta kuma ku huta, naji ni d'an iska ne, fitsararre, marar kunya, bana da anfani a gareku, baku ga anfanin haihuwata ba, to na mutu mana ina ruwanku?"

Idan ka cire Hajia da lieutenant dukansu mutanen wurin mik'ewa sukayi tsaye saboda tsoron ganin halin da yake ciki, k'ofar daya rik'e sosai ya turata da k'arfi ta bada wata k'ara mai k'arfi, juyawa yayi kamar zai tashi sama ya bar d'akin ya nufi b'angarensu, Amar da d'an sauri ya fito da niyyar bin bayanshi Hajia tace "Shalele rabu da shi, ai dai kasan zuciyar ce ta motsa ko? Kuma kafi kowa sanin cewa yana hucewa kan wanda ma bai ji ba bai gani ba, dan haka rabu da shi karya illatala, ka barshi har ya sauko zai zo ya biyani tvn nan daya fasa bak'in munafiki kawai, dama yana jin haushin kallon da nake."

Lieutenant ne yace "Rabu da shi, ba mai kai ba kar wanda ya kuskura ya tanka masa har zuwa lokacin da zai sauko."

Alhaji dake tsaye ne cike da nuna rashin jin dad'i yace " Dan Allah magana mai dad'i ta dinga fitowa daga bakinku zuwa kanshi, ba kusan komai k'aramtar kalma kuka fad'eta tasiri take akan yaranku ba, kuma ya kamata ace kuna hak'uri dashi, yanzu nan kunsan dan kwana uku ba zai kula kowa ba."

D'an k'aramin tsaki yayi ya nufi d'akin shi inda Hajia ta bishi da harara da gunaguni kuma daga lieutenant har colonel babu wanda bai gani ba, duk da hakan bai musu dad'i ba amma hak'ura sukayi, Sa'ada ma da sauri ta tashi ta shiga d'akin ta tana ci gaba da kuka inda lieutenant ya bi bayanta, Hajia ma mik'ewa tayi ta nufi d'akin Alhaji dan suyi magana, hakan ne ya bawa Amar damar fita ya bi bayan d'an uwanshi da tunanin shi kawai ke kan hannunshi daya rotse yake zubar jini amma shi yaga bai ma damu ba, colonel kuma kallon Junaid yayi wanda shi dama tunda aka fara magana tsaye yake yace "Saika wuce ka d'auko min rigata d'aki, dan inhar zan shiga babu abinda zai hana ni gota uwar nan taka."

Da sauri Junaid ya juya ya shiga d'akin, akan gado ya d'auko rigar ya fito har lokacin Zeinabu na ban d'aki, yana kawo masa ya saka fita yayi ya bar gidan shima.

Yana shiga kai tsaye d'akin magungunanshi ya shiga, zaune yayi akan gadon marasa lafiya dake tsakiyar d'akin ya duk'ar da kai k'asa ya rik'e hannun dake fitar jini, har yanzu ya kasa tsayar da hawayen dake zubo mishi, tafarfasa kawai zuciyarshi keyi na k'una da k'unci, iyayen da suka haife ni, amma kullum babu kalma mai dad'i tsakani na dasu, tun ina yaro na fahimci me kalmar d'an iska take nufi, menayi da suka tsaneni tun ina yaron da bansan daidai da rashin daidai ba? Mena aikata gare su haka dayasa suka k'ini? Shin na zo musu ba yanda suka so bane? Ko kuma guda suka so haihuwa sai ni na fara fad'owa duniyar? Ko kuma dai ni wani sirri ne tare dani da yasa kowa na gidan nan ya tsane ni? Menene shi? Wa zai fad'a min dalilin tsanar da suka min? Iyaye na su hantare ni, kakanta ta zageni ta koreni daga wajenta, da irin haka suka raine ni a gidan nan, babu wanda ya tab'a rarrashi na, babu wanda ya tab'a tambayata damuwa ta ko matsalata, akan me? Akan me! Ya fad'a da k'arfi har da saka k'afa ya ture doguwar kujerar dake gaban gadon saida tayi baya.

Saukowa yayi ya d'auki alcohol ya bud'e ya rintse ido sosai ya dararawa hannun, wani rad'ad'i ne ya ziyarce shi amma a hankali ya bud'a ido ya kalli hannun yace "Wannan rad'ad'in bai kai rabin wanda nake ji a zuciyata ba a duk sanda suka kira ni da d'an iska."

Wasu hawaye ne suka sake taho mishi hakan yasa shi fad'awa kan gadon ya zaune yasa bandeji yana laulaye hannun yana fad'in "Kuna kirana d'an iska a kullum, shin baku tunanin na zama d'an iskan ? Namiji ne fa ni, ina da sha'awa da son jin dad'i, ba kwa tunanin tasirin addu'arku wata rana ya kaini ga aikata b'arna? Idan haka ta faru shima saik ku sake kirana d'an iska?"

Amar na tsaye k'ofar d'akin ya gagara shiga, yasan halin kayanshi ba zai tab'a bari ya rarrashe shi ba, abinda yaji kuma sai yaji kawai bari ya bashi wuri ya fad'i abinda ke ranshi ko yaji sauk'i, dan haka ya bar wurin cike da tausayin d'an uwanshi da kuma jin lallai iyayensu basa kyautawa.


➑️➑️➑️➑️➑️➑️➑️

Suna tafiya kawu Mamu ya tattaro kud'i ya shigo gidan afujajen kamar wanda zaho ya koro ya shiga bukkarshi, kud'in ya aje ya fito yana k'wala kiran Zeituna, ita ko tana can wajen yan bisashen da ake kiwo a gidan tana d'aure su, da sauri ta zo ta sunkuya gabanshi cikin fulatanci tace "Kawu gani."

Shima a fulatanci yace "Me kikeyi?"

Kallonshi tayi tace "Ina d'aure bisashe ne."

Juyawa yayi ya kalli Jumma dake cin tuwo yace "Innar Jumare, daga yau Zeituna karta sake aikin komai a gidan nan, ko da d'auke kara ne daga nan zuwa can, aikinta a gidan nan karya wuce yin wanka ta ci abinci ta zauna ta huta, kinji ko? Har wurin aiki ma surukinta yace karta koma zuwa."

Ya fad'a yana kama kunnenshi alamar taji, shek'ek'e Jumma ta kalleshi cikin k'warewa a harshenta tace "To me kenen zatayi idan batayi aiki ba? Ko mu bayinta ne da zamu dinga mata bauta?"

Cikin d'aga murya yace "To sai me idan kun mata bautar? Ku shekara nawa ta d'auka tana muku bautar? Ke bari kiji wallahi, tuwon ma idan har tana buk'ata a saka mata shi a baki to sai an saka mata ko da hakan na nufin zan biya kud'in hakan ne, idan kuma kika bari na kamata a gidan nan kin sakata aiki, to wallahi zan iya sakinki saki har uku, in yaso in auro yar birni ke kuma ki koma rigarku."

Kallonshi tayi tace "To wai meya faru ne? Akan me zaka ce zaka sakeni akan wannan mayyar yarinyar?"

Cikin karsashi yace "Saboda aure zan mata nan da kwana uku, yarinya mai k'ashin arzik'i ce, yau ma daga babban gidan da take aiki ne aka zo neman aurenta."

Tunda ya ambaci aure Zeituna gabanta ya fad'i ta d'aga kai ta kalleshi tace "Aure kuma kawu?"

Yanda yaga firgici tare da ita yasa yace "Ke kwantar da hankalinki, ba zan had'a ki da wanda ba kya so ba, zab'inki ne zan had'a ko da shi wanda yake sonki kuma kike son shi, ni ban damu da tsufanshi ba tunda dai kina son shi."

Kalamanshi sun k'ara sakata a duhun kai, Jumma kuma cewa tayi "Hum! Ayi dai mu gani Baffan Jumare, wurin son kud'in ka saika kaita inda za'a halakata."

Da k'arfi yace "To ba bakinki ba, yarinya dai mai goshi ce wallahi, ke kinma san waye zai aureta? To Alhaji Hassan ne, babban d'an Alhaji Suley Gaga, nan gaba kad'an nima zakiji na zama Alhaji."

Zeituna tsaye ta mik'e ta dafe k'irji tace "Kawu lieutenant?"

Kallonta kawu yayi yace "Ke ba lantanan ba nace Hassan, tare da babanshi suka zo suka nemi aurenki, ke har ma na amshi sadakinki mun tsayar da ranar juma'a za'a d'aura auren."

Sam ta kasa fahimta komai a zancen, lieutenant kuma? Ya zo neman aurenta? Anya kuwa! Me yake shirin sake faruwa kuma? Jin tana neman fad'uwa a wurin yasa ta juya ta shiga bukkarsu, Jumma kam dariya ta dinga yi tana fad'in "Ikon Allah, yanzu kuma abun ga tsoho ya kuma? To Allah ya kyauta maka."

K'wafa yayi irinta haba dai zaki gama dariyarki ne idan kika ga na shigo gari nima, juyawa yayi ya bar gidan shima zuciyarshi fes saboda yana da kud'i aje a d'aki, sam ya manta da maganar wani Jano, yau ma Zeituna yanda taga safiyar nan haka taga wannan dare bata rintsa ba, tambayoyi ne birjik a ranta amma babu mai amsawa, gashi ma ance kar taje wurin aiki bare tasan abinda ke faruwa, ta rasa me zatayi da jin labarin nan, farin ciki? To akan me domin kuwa bata da tabbas, har yanzu gani take mafarki take ko kuma kawunta ne ya shiga shuhuba, bak'in ciki? To shima akan me? Da haka har asuba tayi mata bata rintsa ba saida tayi sallah bacci ya d'auke ta.


*Washe gari* sammako sosai Ammar yayi ya tafi d'aurin auren Abdullahi, ana idar da d'aurin auren kuma ya d'auki hanya sai Madarunfa, awa d'aya ta kaishi a hakan ma dan baya gudu sosai ne, kamar haifaffen garin haka ya ratsa har ya isa gidan daya saba zuwa, paka motar yayi kai tsaye kuma ya shiga gidan yana sallama, matar dake k'ulla ruwa zaune bakin panpo ta amsa da farin ciki dan ta gane ko waye, mik'ewa tayi ta nufi wajen kujera ta d'auko tana fad'in "Ammar yau kaine da safiya haka? Amma dai sammako kayi sosai?"

Murmushi yayi ya k'arasa yana karb'an kujerar data d'auko ya aje ya zauna yana fad'in "Aunty daga wurin d'aurin aure ne kawai na wuce."

Zaune tayi kan kujerar data tashi ta kalleshi tace "Ina kwana."

Bai amsa ba shima yace da ita "Ina kwana aunty."

Sosai suka gaisa kafin ta sake mik'ewa ta bud'a fridge d'in dake cikin runfa ta sana'arta ta d'auko ruwa da lemu, kawo masa tayi ta aje ta juya ta d'auko faranti ta azo kwanonin abinci da duk abinda ya dace ta zo ta aje, saida ta zauna ta kalleshi tace "Ammar ga abinci ko, nasan dai ba lallai ka karya ka fito ba."

Kallon dattijuwar yayi cike da k'aunarta, hak'ik'a yana son mahaifiyar su Hamna, baiji dad'in rabuwarsu da kawunshi ba amma k'addara ce, ita kad'ai ce suke fahimtar junansu kuma harya fad'a mata wani abinda ya shafe shi, tun yana yaro idan an hattareshi ia ke tarairayarshi tana bashi hak'uri, shiyasa har yanzu bai manta da ita ba duk da tana gidan wani amma yana ziyartar lokaci lokaci, wani lokacin ma idan ranshi ya b'ace ne ko kanshi yayi zafi yake zuwa ta bashi shawara da rarrashinshi, bai mata musu ba domin kuwa kamar gida ya d'auki nan, har mijinta zai iya yin hira dashi hirar da bata tab'a shiga tsakaninshi da mahaifinshi ba, da kanshi ya zuba abinci yana ci suna hira ta duniya harya gama.

Su colonel ma sammako sukayi zuwa Goure, kuma cikin hukuncin ubangiji suka isa da wuri kai tsaye gidan suka nufa dan tare suke da Junaid da kuma Labaran, gidansu Maryama sun sha tarba sosai, kamar dai tarba da ita kanta Maryama ta gani zuwansu jiya tare da 'yarta da k'awarta, nan suka k'arasa gidan malam Rabi'u inda dama ansan da zuwansu domin su gabatar da abinda ya kawosu, suna zuwa can ma tarba suka samu inda suka samu maza uku bayan malam Rabi'u, tunda Labaran ya kalli tsohon yaji fad'uwar gaban da bai tab'a jin irinshi ba, haka suka zauna suka sake gaisawa sannan malam Rabi'u yace "...


πŸ‘πŸ‘πŸ‘
22/06/2020 Γ  17:26 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ’ž _*MASOYA NA*_πŸ’•


_Bismillahir rahamanir rahim_

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_11_

"Nasan zaka gane muryata cikin sauk'i, dan haka ba zan bawa kaina wahala wajen sanar da kai wacece ba."

Jin Sameera a bayanshi yasa shi juyawa ya kalleta wacce ita ma ke kallonshi saboda son sanin abinda ke faruwa, matsawa yayi sosai nesa da ita amma ita da bata fahimta ba saida ta sake bin bayanshi, domin kuwa jikinta na bata wannan wayar nada nasaba da halin da mijinta ke ciki, ganin bata daina biyarshi ba yasa shi fita daga falon ya rufe k'ofa, yana fita yace "Meyasa kika kira ni?"

Murmushi tayi wanda saida yaji sautinsa kafin tace "Jiya mun rabu babu sallama baka kuma biyani kud'in aikina ba, shiyasa na kira dan na tuna maka karka manta da kud'i na."

A k'ufule yace "Karki raina min wayo Nasmat, kiyi gaggawar sanar dani abinda yasa kika kirani, idan kuma dan wannan maganar ne to kiji da kyau, karki sake gigin kiran wayata, idan kuma ba haka ba wallahi zansa rayuwarki a had'arin da kaf danginki sai sunyi nadamar kasancewarsu yan uwa a gareki."

Wata dariya tayi tace "K'arfin halinka na birgeni sosai, amma naga alama ba zaka saurare ni, shiyasa ma na tura maka da muhimmin sak'o a WhatsApp d'inka, zaka iya dubawa saika kirani muyi magana idan har kana son tsira da mutuncinka dana iyalinka."

Kashe wayar tayi inda shi kuma cikin rawar jiki ya fara dubawa WhatsApp d'in, yana bud'e vidΓ©on nan saida ya saki wayar bai sani ba tsabar firgita, da sauri ya sunkuya ya d'auki wayar ya sake kallon abinda ke ciki, take yaji jikinshi ya d'auki rawa, ya ilahi! Meyasa banyi tunanin haka ba? Ita ce tambayar daya wa kansa, da sauri ya nemi lambarta ya kira tana d'auka yace "Me kike so?"

A tak'aice tace "Kud'i, kasan ku masu kud'in nan ba kwa tunanin talakawa da gajiyayyu, duk da kai kana k'ok'ari, to amma kasan dambu idan yayi yawa baya jin mai, kuma karka d'auka talauci ne yasa nayi abinda nayi."

Cike da k'aguwa yace "Ki gaggauta fad'a min nawa kike so bana da lokacin b'atawa a tare dake."

Cike da iko tace "Maganar nan ba zata yiwu a waya ba, mu had'u kawai."

"A ina?" Cewa tayi "Ni ko a titi zan iya had'uwa da kai, bansan ba kai."

Cikin jin haushi yace "Ba zan iya had'uwa da karya irinki a titi ba, zan turo miki da adresse d'in guest house d'ina ki sameni acan."

Dariya tayi tace "Zan so duk inda zaka gayyace ni domin kuwa wannan videon ya shiga hannun d'an uwana."

Tsaki kawai yayi ya kashe wayar ya tura mata adresse d'in ya shiga motarshi, hangen motarshi da tayi yasa ta fitowa da sauri tana so tayi magana, cike da damuwa ta bishi da kallo tace "Ya Allah, meke damunshi ne?"

Saida yayi jiran minti kusan ashirin kafin ta iso, tana k'wank'wasa k'ofar yayi gaggawar bud'ewa

Please Login or Register in order to submit comment