Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son tashin hankali dan haka Allah ya fito mata da wani.

*Sanda* ake ta k'ok'arin ganin an had'a Hamna da wanda ya dace, a lokacin kuma Amna taje awo na farko, a cikin tambayoyin da likitar ta mata ne take tambayarta bata jin wata matsala, cikin sanyi jiki tace "Gaskiya ina d'an yawan jin ciwo haka kamar kusan k'uguna da...mtsss ni abun ma wallahi ya fara damuna."

Tambayarta tayi "Kina jin zafi idan kina fitsari?"

Da sauri tace "Gaskiya ina ji, na jima ina jin haka kad'an kad'an."

"Kina zubar da farin ruwa ne masu kamar kub'ewa?"

A hankali tace "A'a."

"To akwai kasala ko ciwon jiki?"

"A'a." Shima ta fad'a, ci gaba tayi da rubutu tana mata tambaya kafin daga bisani ta rubuta mata wata takarda ta bata tare da cewa "Ki samu rendez vous kiga gynΓ©cologue saiki masa bayanin abinda kike ji, insha Allahu idan ma magani ne ko shawarwari duk zai d'oraki akai."

Tunda taji abinda ta fad'a gabanta ya fad'i, a take jikinta taji yayi mugun yin sanyi, sai taji duk ta sare hankalinta da nutsuwarta suna neman barinta, a daddafe aka gama mata awon nan ta dawo gida, daga Ummy har shi babu wanda ta fad'a ma, tunaninta kawai shine idan taje taga docteur d'in za'a jawo mata ciwon da bai kai girman matsalarta bane, dan haka taja baki tayi shiru bata fad'a ma ko da yer uwarta ba, sanda ya dawo gida saida ya tambayeta ya awonta ya kasance, amma sai tace lafiya lau, a haka aka tafi da lafiya lau ta ci gaba da b'oyewa, saida lokacin komawarta awo na biyu yayi ta samu tayi d'ibar jini shi ma dan tasan sai dashi za'a mata awo na gaba, ko da taje asibitin ta kuma yi sa'a da likitar data dubata a farko ta tambayeta me aka ce mata, sai kawai tace ai ta daina ji ma da aka d'orata kan magani yanzu ta warke, anan likitar ke mata murna dan ita kanta da taji ta fad'a mata abinda take ji saida ta d'anyi wani tunanin na daban.

Duk zaune suke a falo sun gama shirin tafiya barka gidan Nura da matarshi ta haihu, kusan duk jikokin nan yanzu Hajia ce ta d'auki nauyin yin kayan barka indai akayi haihuwa, hakan ya ma kowa dad'i inda addua'r sa albarka ke riskar Ammar kowane lokaci, dama tace sai zasu tafi sai su biya a siye kayan a wuce, Zeituna ce ta kalleta babu fargaba babu tsoro cikin farin ciki tace "Hajia dreba fa na jira a waje, kuma gashi baki fad'i me da me za'a siya ba."

Kallonta Hajia tayi ta kalli Ummy dake b'allawa Shureim botira tace "Ga Sa'ada nan ta fad'a miki duk abinda ya kamata saina bayar da kud'in a siya."

Kallonta Ummy tayi ido ciki ido babu wannan sunkuyar da kai ko wani abu tace "Idan mun tafi zai sauke mu tare ai sai mu siya."

Jinjina kai tayi ta kalli Husseina tace "Kiyi sauri ke kuma ki gama shafa kwallin nan kamar wata budurwa kike ta darzashi a ido."

Saida ta murgud'a mata baki tace "Babu ruwanki barni na shafa, kika sani ko na samu miji daga wannan fitar."

Dariya Hajia tayi tace "Ai kuwa dai zai kwashi kabari kusa."

Kallonta tayi tace "Au! Ke a ganni zan mutu da wuri ne? Ai ko zan tafi tare dake zan tafi, kuma ma ai kin fini kusa da kabarin."

Cikin dariya Hajia tace "Saboda me?"

"Saboda ke ce mijinki ya mutu." Ta fad'a tana mik'ewa tana gyara gyalenta, su Zeinabu dai dariya suke har suka rungud'a baki d'aya suka fita, lallai rayuwa yanzu ta sauya sosai.

*Bayan sun dawo* da dare ana zaune ana ta hira gwanin sha'awa, colonel ya diro garin cikin kakinshi marar hayaniya sosai sai tarin galolin nasara da jajircewa, har gabanta yaje zai durk'usa ta rik'e hannunshi da murmushi a fuskarta ta zaunar dashi gefenta, fuskarshi take kallo tace "Hussein an dawo lafiya? Ya aikin kuma?"

Saida ya kalli su Ummy da Zeinabu dake gefe, shi dai baya nan aka samu wannan canjin, hakan bata tab'a faruwa ba sai yau, cikin ldabi yace "Hajia kuna lafiya?"

Cikin murmushi tace "Lafiya lau kowa."

Dafashi tayi tace "Ka shiga ciki ka samu kayi wanka sai ka zo ka ci abinci ko."

Sunkuyar da kai yayi yace "To Hajia, nagode Allah ya k'ara girma."

Da murmushi ta amsa da "Ameen, Allah yayi albarka."

Shigewa yayi ciki yana jin wani sakai a zuciyarshi, ita kanta yanzu wani sakayau take ji data zama mai bin yaranta da addu'a, duk sanda ta musu sai ta ga tsantsar farin ciki a fuskokinsu, yanzu da take jan kowa a jikinta sai taji tafi ingantacciyar lafiya, bakinta baya zama shiru, yara duk suna sakewa da ita har su zauna gabanta suna hira ko da ta shirme ce, yanzu har basa zama falonsu na sama sai falon tara da ita, kuma a wannan zaman da take tare da su ne take gyara musu wasu k'ananan kurakurai ko da na cikin fad'a ne a kalma, lallai ta jima tana rayuwa cikin kuskure.

*Rayuwa kenan*, a cikin wata hud'un nan sau uku ana d'auko maganar auren Hamna amma sai abun ya lalace, izuwa yanzu kam sai kowa ya fara wani tunanin na daban, Husseina da Hassana ne suka mik'e wajen neman taimakon malamai, sai dai duk inda zasu tafi basa tafiya da Hamna sai dai su fad'i matsalarsu kawai, dan Husseina tace ba zata yarda abinda ya faru kanta ya faru kan jikarta ba, da ire iren haka suka fara takura Hamna da turare turare da shaye shayen rubutu da maganin aniya makomiyaπŸ˜‚, inda abun ya fara girman da ana sauke Qur'ani da sadaka da yanka abun sadaka, an shiga kashe kud'i sosai saboda tunanin ko sihiri ko kuma aljanu, sai dai har yanzu babu wani labari.

*Duk* da ciwon kan da take ji bai hanata kama wankin kayan yaranta ba, dan in suka tafi islamiyya kawai take samun damar yin aiki hankali kwance, duk sanda ta duk'a sai taji kamar kanta zai fad'o k'asa ko idonta, idan ta d'ago kuma saita rintse ido saboda jiri ke d'ibarta, a haka dai ta sake sunkuyawa d'aukar wasu kayan dan ta shanya, tana d'agowa taji kamar an buga mata guduma a tsakar kai, daga lokacin bata sake sanin me ke faruwa a duniya ba, fad'uwa tayi da tsohon cikinta wata takwas wanda aka bata sati biyu idan bata haihu ba ta koma asibiti, bokitin ne ya juye inda ruwan suka malale har suka gangaro inda take kwance suka b'ata ta.

Kasancewar yara duk na islamiyya manya kuma basu cika shiga b'angarensu ba yasa ta kwashi tsawon awa uku da rabi a wurin babu wanda ya sani, sai tasowar yara ne daga islamiyya, su Abba da Ameer b'angarensu Ummy ma suka nufa dan can ake basu biscuit da chocolat, Ameera da tafi sarkawhar mahaifiyarta kai tsaye can ta nufa ita ma, ko da taga d'aki rufe ma ta d'auki hanyar da zata sadata da bayan gidan inda suke wanki wani lokacin har su zauna shan iska, ko da ta zagaya ta ganta kwance ta k'arasa, ita dai tasan kwancin nan bana lafiya bane, sai kawai tayi zaune kusanta tana daddab'ata tana kiran "Ummy, Ummy ki tashi k'aca ne fa kika kwanta."

Jin shiru yasa ta k'ara girgizata tana fad'in "Ummy bake ke ana mu wacan k'aca ba? Shine kuma kika b'ata jikinki kema, saina fad'awa Papa."

Tun Ameera na magana har ta gaji ta d'ora kanta akan cinyarta ta kwanta ita ma ta fara kuka.

Shi kanshi Ammar gabanshi yaji kawai yana ta fad'uwa, ya rasa me ke mishi dad'i a duniyar, wayarshi ya d'auka ya kirata da nufin tambayarta yara sun dawo daga islamiyya, saida yayi kira takwas ba'a d'auka ba sai kawai ya d'auki makullin mota ya fito, bai tsaya ko ina ba
sai gidan, shi ma yana ganin k'ofar rufe saiya juya ya shiga wajensu Ummy, yana ganin Ameer sun shiga wasa da uniforme d'in su yace "Sarkin k'iriniya ina uwarka take?"

Saida ya nuna mishi b'angarensu yace "Tana can."

"Ameera fa?" Ya fad'a yana kallon sauran yaran, nan ma nuna masa yayi yace "Tana can."

Juyawa kawai yayi ya sake komawa, wannan karan kai tsaye bayan gidan ya nufa, yana dosa ya hangin tashin hankalin da ko a mafarki baiyi tsammanin riskarshi ba, Ameera dake kuka har ta daina saboda baccin daya d'auketa sai ajiyar zuciya take, da gudun bala'i ya k'arasa yana kiran sunan "Amna, Amna, lafiya?"

Durk'ushewa yayi ya tallabo kanta, luuuuu kanta yayi yana ta langab'ewa, cikin kid'ima ya kamo wuyan hannunta yayi shiru, da sauri ya d'ora yatsunshi biyu kan wuyanta yana saurare, jin akwai alamar harbawar jijiya yasa shi saurin mik'ewa tsaye, janyo Ameera yayi daga jikinta baiwar Allah a cikin bacci ta firgita ta tashi, bai kula yarinyar ba ya tattaro Amna ya rumgume kamar yar beby yayi waje da ita.

Yaran ne suka sanar da fitarshi da Amna, ko da suka fito har ya figi motar sun bar gidan, a tsiyace yake gudu yana juyawa yana kallonta, da hannu d'aya yake tuk'i d'aya hannun kuma ya rik'e nata gam, Allah, Allah, Allah, kawai yake maimaitawa shima a zuciya, komai ya tsaya masa cak ya rasa me zaiyi tunani akai, yana isa bai bari mai gadi ya bud'e masa ba ya fito, mai gadi na shirin bud'e k'ofar yaga mai gidanshi a gigice ya bud'e gidan baya yana k'ok'arin d'auko mutum, da gudu ya shiga asibiti inda ya sanar dasu aka fito da gadon d'ora marar lafiya, yana daf da shiga suka had'e nan ya d'orata suka jata da gudu, ana turata d'akin da za'a dubata sai kawai ya ja ya tsaya, gashi yau asabar Ummy na gida, hannu biyu yasa ya shafi kansa tare da tsayar da hannayen saman kai, likitoci biyu mata ne suka shiga sai d'aya likitan wanda zai shiga ya ga Ammar ya tsaya shima saiya tsaya ya kalleshi, dafa kafad'arshi yayi yace "Muje mana, zamu buk'ace ka a ciki."

D'ago duka idonshi yayi ya sauke mishi su, kallo ya bishi da shi kamar bai gane yarenshi ko kuma yau ya fara ganinshi, ya jima yana masa wannan kallon kafin ya bud'e baki yana son magana sai kuma ya kalli gefe, idonshi yaji sun cika da k'walla sai yayi saurin tsayar dasu ya kalleshi, girgiza masa kai yayi yaja baya baya ya zauna dab'as kan dogon bencin k'arfe dake bayanshi, duk'e kanshi yayi ya tangaleshi da tafin hannayenta, ganin haka sai kawai likitan ya juya zai shiga ciki, da sauri ya mik'e ya rik'o rigarshi, juyowa yayi yana kallon sai kuma ya sunkuyar da kai, dafa kafad'arshi yayi yace "Ammar, ka kwantar da hankalinka mana, kai ma fa likita ne, k'warin gwiwa kake buk'ata."

Iska ya furzar ya d'ago ya kalleshi idonshi sun rine sosai, cikin amon muryar kuka yace "Dan Allah, dan Allah ka ceci rayuwarta."

Jinjina masa kai kawai yayi ya juya ya shige, komawa yayi ya zauna ya dafe kanshi, a hankali yace "Me ya sameta? Me zai faru yanzu?"

D'ago kanshi yayi yana dafe da goshinshi yace "Cikin nan karka zamar mana matsala, ta min k'orafi akan shi amma ban ji ba, idan da nasan haka zata faru da tun farko na saurareta mun samu mafita."

Kafad'arshi da yaji an dafa yasa shi juyawa ya kalli wanda ke bayanshi, Ummy ce tsaye tare da su Hajia Zeituna Zeinabu da sauransu, da sauri ya rik'e hannun Ummy yace "Ummy tana ciki, bansan me zai faru ba."

Kallonshi tayi tace "Me ya same ta?"

Kai kawai ya girgiza bai ce komai ba, shiru sukayi kowa na addu'a a zuciyarshi, likitan ne ya fito da sauri da takardu a hannunshi ya zo ya tsaya gabansu, da sauri ya tashi tsaye yana tambayarshi lafiya? Saida ya kalli Ummy sannan ya bashi takardun yace "Muna buk'atar sa hannunka za'a mata aiki dan a ceto abinda ke cikinta."

Fad'uwar da gabansa yayi yasa shi dafe k'irjinshi, rik'e hannunshi yayi yace "To ita fa?"

Kallonshi yayi zaiyi magana sai Ummy tayi saurin karb'ar takardun tace "Dukansu za'a fito dasu lafiya, saka hannun anan."

Kallon Ummy yayi sai yayi murmushi yace "Yawwa Ummy na."

Da sauri ya saka hannun likitan ya kalleshi yace "Muna buk'atarka a ciki Ammar, da alama ta d'auki kusan awa hud'u ko uku da rabi a sume, hakan ya jawo tsayawar..."

Da sauri yace "Zuciyarta na bugawa?"

Kallonshi yayi yace "Shiyasa nake so ka shiga ciki, zuciyarta na bugawa amma ba daidai ba."

Da saurin bala'i ya tunkari d'akin ya shige ciki, saida ya shiga ya saka rigar aiki da hula da safar hannaye, rintse ido yayi ya bud'e akan ta, an saka mata oxygène tana kwance kamar gawa, saida ya kalli n'aurar dake nuna bugun zuciyarta da numfashi, nan ya shiga had'a allurai da abubuwan da suka dace, inda d'aya likitan kuma yasa aka mata allurar kashe zafi, nan da nan cikin k'warewa ya farkata inda Ammar ya kasa kallonta a wannan halin, bugun zuciyarta kawai yake dubawa yana fad'awa likitan yayi sauri dan ya samu damar yin nashi aikin shima, ana ciro santalelen yaron ya fashe da kuka, da sauri ya juyo yayi saurin karb'arshi, kallon fuskar yaron yayi sai yaji hawayen da yake ta k'ok'arin b'oyewa sun zubo masa, d'aya daga cikin likitocin ne ta amshe shi ta shiga kula da yaron dake ta tsanyara kuka.

Yana gama mata d'inki shima ya shiga dubata, bai tab'a tunanin zai iya nuna k'warewarshi kan wani na shi ba, gashi yana aiki akan matarshi data fara rikid'ewa ta zama jinin jikinshi, yana aiki akan ta cike da son ya ceci rayuwarta ta rayu, yana aiki akanta da niyyar ko tashi zuciyar ce ya cire ya dasa mata, amma kuma hannayenshi rawa suke, tausayinta da k'aunarta sai wahalar dashi suke a lokacin, sai gashi ya kai matakin da ma baisan me yake mata ba, likitan ne ya kula da hannunshi sai rawa suke kamar yau ne ya fara aikin, likitan na shirin dafa shi sai gani yayi ya saki wani d'an tsinken dake hannunshi ya juya baya yana rufe fuskarshi da hannu, da sauri ya matsa kusa dashi da nufin ya mishi magana, ikon Allah sai kawai suka ji n'aurar na kukan dake nuna bugun zuciyar ya fara tafiya daidai.

Tare suka juyo sukayi kanta, hannunta ya rik'e yana murmushi yana fad'in "Alhamdulillah, Allah na gode maka."

Nan suka gama abinda za suyi aka kimtsata, saida aka d'ibi jininshi aka k'ara mata kafin aka fito da ita d'akin hutu.

Yana d'akin tare da ita su Ummy na zaune farfajiyar asibitin, a firgice Hamna ta shigo daga salon da aka fad'a mata, tunda ita dai tasan ba watan haihuwarta bane, Ummy ta kalla tace "Ummy ina Amna? Me ya same ta?"

Da dariya ta kalleta tace "Lafiya lau take yanzu, tana d'akin hutu."

"Amma Ummy me ya sameta to? Lokacin haihuwarta ai baiyi ba?"

Hajia ce tace "Ki nutsu ki shiga ki duba ta, aiki aka mata."

Da k'arfi tace "Aiki kuma? Amma ba tana haihuwa da kanta ba?"

Zeinabu ce tace "Bari kedai wallahi, wannan ce ta zo da matsala."

Da sauri tace "Wane d'aki take?"

Ummy ce tace "Tana d'akin da aka kwantar da Jamila lokacin baya."

Da sauri ta wuce tana gyara kallabin doguwar rigarta dake jan k'asa, da k'arfi ta bud'a k'ofar ta shiga, da sauri ya kalli mai shigowa ita ma idonta cikin nashi dan bata tsammanin yana ciki, babu wanda ya iya canza fuskarshi daga yanayin alhinin da sule ciki saboda halin da ake ciki, sai tausayinshi ma da taji na ganin idonshi jawur kamar yayi kuka, k'arasawa tayi ta zauna bakin gadon tana kallonta, a hankali ta dafa hannunta mai d'auke da zoben azurfa fari irin na Hamnar, d'an satar kallonshi tayi tace "Ya jikinta?"

Cikin muryar jimami yace "Lafiya lau."

A hankali Amna ta bud'a idonta, dishi dishi take gani da k'yar ta saisaita ta sauke idon akan Hamna data fi gani da kyau, murmushin k'arfin hali ta mata cikin muryar da bata fitowa sosai tace " *Saboda ke na dawo Hamna*."

Da mamaki suka kalli juna ita da Ammar suka kuma kallonta, a hankali tace "Ban gane saboda ni ba? Daga ina?"

Ba tare da murmushin nan ya bar fuskarta ba tace "Gidan da ba'a dawowa mana, saboda ke na dawo yer uwa, bana so na barki ba tare dana tafi da sanin kina hannun wanda ya dace ba, sannan ina so na bar amanar yarana hannunki, ko ba komai suna kallon uwa saboda yer uwata ce ke kuma fuskarmu d'aya, dan Allah yer uwa ki samu mai nagarta da kamala wanda zai iya k'aunarki a duk yanda kike kuma har abada kamar *miji na.*"

Hawayen da suka taho ma Hamna ne tayi saurin gogewa ta kalli Ammar tace "Me yasa take magana haka?"

Dariya Amna tayi har hak'oran makkarta ya fito tace "Ki saurare ni mana."

Girgiza kai tayi tace "Kinga kiyi shiru dan Allah baki da lafiya."

Mik'ewa tayi zata fita Amna tace "Yer uwa."

Tsayawa tayi ta juyo, saida ta lumshe ido tace "Ba zan tab'a damuwa da halin da zan bar yarana ba saboda na bar musu ke."

Da gudu Hamna ta fita daga d'akin tana kuka, kallonta yayi ya rik'e hannunta yace "Duniyata kiyi shiru ba'a son magana kinji."

Murmushi ta masa tace "Ina so nayi magana da yer uwata yah Ammar."

Cike da tabbatarwa yace "Shikenan kiyi shiru yanzu, idan jikinki ya k'ara kyau zan kira miki ita."

Wani murmushi tayi mai ciwo tace "Na fad'a maka zan kai gobe ne?"

Kafeta yayi da ido yace "Zaki kai insha Allahu har ma ki wuce."

Wani murmushin ta sake masa tace "Malam taimaka min na tashi ina so nayi sallah."

Saida yayi ajiyar zuciya yace "Kiyi hak'uri Amna, a yanayin da kike zaki iya jinkirta sallah."

Had'e fuska tayi tace "Ba ruwanka kawai ka tashe ni nayi sallah, idan na mutu me kake so na fad'awa Allah, idan kuma ba zaka iya ba ka kira min Ummy."

Zuba mata ido kawai yayi yana kallo, abinda ya lura dashi kawai zafin aikin da aka mata ne yanzu ya had'e mata jiki yasa take sambatun nan, da taji ya k'yaleta sai kawai ta fara k'ok'arin tashi tana fad'in "Ni banga anfanin zamanka anan ba in ba zaka sani yin sallah ba, kawai ka barni na tashi na gaishe da ubangiji na."

Rik'eta ya kwantar da ita yana daddab'ata, kamar wacce k'walwarta ta samu matsala haka take fad'in "Ammar ka sake ni na tashi nayi sallah, bana son haka wallahi ko kad'an, wai kai kake da aljanna ne da zaka saka ni a ciki? Ko so kake Allah ya k'ona ni."

Bai saketa ba bai kuma tashi ba saida Ummy ta shigo dubata saboda Hamna data fita tana kuka kuma ta k'i magana, da sauri ta fita ta d'auko allura ta zo ta mata, ba jimawa bacci ya d'auketa kad'ai ya sake ta.

*Kullum* haka Amna take tunda ta haihu, mai saurin kuka da tausayi baya iya tsayawa kusanta saboda maganganunta masu karyar da zuciya ne, indai idonta biyu ba bacci take ba to maganganu ne zatayi ta sakowa, duk wanda zai zo ganinta saita mishi nasiha, ka kula da yaranka kn kana da su, ka kula da mijinka in kana da shi, ka dage wajen karatunka in mai karatu ne, hakan ne yasa duk wanda yaje ganinta sai dai ya dawo yana zubar da hawaye, a cikin k'ank'anin lokaci kowa maganarta yake. Yaro kam ko da ta haife shi dama aka d'orashi kan madara, da fari anyi hakane saboda ganin jikinta, amma yanzu abinda ya tabbatar ma kowa tana jin jiki shine, duk yanda yaron zaiyi kuka a kawo mata shi ta bashi nono saita k'i, haka zata dage ita ba zata bashi nono ba, sai manya suka fara tunanin ko iska ne dan babu abinda basa yi, addu'a aka dage da mata amma babu abinda ke sauyawa, wani lokacin tana bacci haka zaka ga hawaye na bin fuskarta, data farka sai dai ta tashi da kuka, to fa zata iya yin awa goma ba tace um bare um um ba, haka suka kwashi kwana *bakwai* a asibiti, sallamarta akayi suka koma gida dan sun ce ciwonta bana asibiti bane.

*Ranar da* suka dawo gida...


*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_62_


*A ranar da* suka dawo gida kuma wani ikon Allah sai abun yayi sauk'i, ta ci abinci sosai tayi wanka ta gyara kanta sosai, kowa yayi farin ciki da faruwar hakan, musamman Hamna tafi kowa farin ciki, har yamma dai babu wata matsalar komai, yaro dai ne tana saka shi a nono zata cire shi ta aje, an idar da sallah magriba Ummy ta kalli Hamna tace "Hamna ki taimaka ki siyo mana kayan sanyin da za'a saka mishi mana, dan da alama garin akwai hadari."

Amsawa tayi da "To Ummy."

Mik'ewa Ummy tayi tana fad'in "Bari na d'auko miki kud'in."

Da sauri tace "A'a Ummy ki barshi ma akwai a hannu na."

Da sauri Amna dake zaune k'afafu mik'e ta d'aga rigarta inda aka mata aiki tace "Kin gani ko Ummy, zata kula dasu ko bayan ba raina."

Hararanta Hamna tayi tace "Uwarki zan ci kika sake mana maganar mutuwa."

Da sauri tasa hannu ta rufe baki tace "Nayi shiru to, yi hak'uri tafi Hajia."

Murmushi Hamna tayi ta tashi ta fita, a farfajiyar ta had'u da Shureim da gudu ya tareta, dafa shi tayi tace "Daga ina kake?"

Cikin muryarshi ta yara yace "K'ofar gida ni da yaya Ammar da Appa."

Kallonshi kawai tayi da ido, wanda ya kamata ya kira Appa shi ya kira da yaya, wanda ke mazaunin kakanshi kuma ya kira da Appa, wannan wace irin *BADAK'ALA* ce? Cikin tunani bata san ta fara tafiya ba saida taji ya rik'e hannunta yana fad'in "Aunty ina zaki je? Ina zuwa."

Kallonshi tayi tace "To muje mu siyowa sabon bebynmu kaya ko."

Da gudu ya rigata k'arasawa wajen motar, bud'ewa tayi ta shigar dashi sannan ta shiga, mai gadi na bud'e mata k'ofar anan ta ganshi tsaye tare da Abba da Labaran, sauke gilashin tayi tare "Abba barkanku."

"Ina zaki je?" Ita ce tambayar daya jefo mata, cikin ladabi tace "Ummy ce ta aike ni na siyowa bΓ©bΓ© kayan sanyi, amma yanzu mun dawo dan tace akwai hadari a gari."

Cikin sakin fuska yace "Shikenan sai kin dawo."

Kallon Shureim yayi yace "Hein ba magana?"

Ammar kawai ya kalla yace "Yaya na tafi."

Murmushi ya masa yace "Saika dawo, ka kula da kanka."

Wucewa tayi suka d'auki hanya, sun bar nan kenan Amie ta zo yin barka, gaishesu tayi suka amsa ta tambayi Ammar ya mai jiki da bΓ©bΓ©, cikin amon muryar da yake nuna babu wasa ya amsa mata, ciki ta shiga kai tsaye b'angare Amna ta nufa, nan ta samu Ummy suka gaisa, saida suka gama gaisawa fa Amna sannan tace "Ummy ina Hamna take?"

Cikin sakin fuska tace "Hamna ko bata jima da fita ba, amma yanzu zata dawo nasan ba zata kai ko kasuwa ba."

Hira suka fara tab'awa da Amna sai Ummy data bar musu falon, ba jimawa da fitar Ummy kuma Hamna ta dawo, Zeituna ta ci karo da ita saita fad'a mata yanzu Ummy ta shiga ciki, dan haka saita shiga kawai inda Shureim ke mata rigimar ta koma yawo dashi, kai tsaye d'akinta suka shiga ta same ta tana duba wasu kaya, kallonta tayi tace "Har kun dawo wai?"

"Wallahi Ummy, kinga kayan." Ta fad'a tana mik'a mata ledar, bud'ewa tayi tana dubawa sai Shureim dake kamo hannunta da k'arfi yana fad'in "Ki bani ni, ki bani."

Umly ce ta kalleshi tace "Wai me za'a baka?"

Dan kar Ummy ta dakeshi yasa Hamna sakar masa makullin, yana jin ta sake masa saiya fita a guje ta bishi da kallo, tana juyowa suka had'a da Ummy dake murmushi, cikin taushin murya tace "Ki k'ara hak'uri Hamna, insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe, tunda a
mahaifin yaron nan ya canza al'amuran gidan nake

Please Login or Register in order to submit comment