Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

data durmiyashi cikin siyasa ya samu nutsuwa, yana zuwa tace mishi ta mishi mata aure zaiyi, bai ja da maganar ba shima ya amince, *Hadiza*, ita ce yarinyar data zab'a mishi wacce anan unguwarsu take, sam Hadiza bata son shi dan tana da wanda take so, amma fin k'arfi da ganin matsayinshi yasa babu yanda ta iya, had'a kai 'yan uku sukayi suka had'a k'arfi da k'arfe suka gwangwaza sabon gini na gani na fad'a a wannan zamani, a *ADS* suka buga wannan gini tun lokacin unguwar babu mutane dayawa sai wane da wane, haka akayi tsari mai kyau a lokacin aka d'aura auren Gambo, tare suka dawo gidan dukansu harda su Labaran da suke jin ba zasu iya rayuwa da su ba dan sun zama d'aya, Zeeya tayi farin ciki da hura hanci da k'afafa ganin gidan da yaranta suka gina, sai dai bata ji dad'in tarewarsu tare da su Husseina ba sai taga kamar sun zamar mata k'arfen k'afa.


*I โค u true fan's*
10/06/2020 ร  12:07 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_14_

Tunda Hadiza ta tare gidan ta fahimci sauran matan da ma mutanen gidan baki d'aya hak'uri suke da tsohuwar gidan, ita kuma sai take ganin ba zata iya ba gaskiya, domin kuwa ba zatayi hak'uri da tilasta mata da akayi ba ta auri d'an ta, sannan kuma tayi hak'uri da rashin mutumcin da uwarshi ke darzawa a gidan, duk da bata nuna mishi k'iyayya a zahiri amma dai da gani kasan ba wai dan tana so bane take zaune da shi, dan ko mu'amuma ta aure ya nemeta zakaga tana irin gani kayi yanda zakayi kawai na kama gabana take mishi, haka zaka ga tana wani kakkawar da kai tana gunguni da k'ananun tsaki da baya fitowa fili, ya jima da fahimtar hakan, shi kuma Allah ya san zuciyarshi baisan lokacin data shiga ta shi zuciyar ba, dan haka yake k'ok'ari sosai wajen faranta mata rai duk da bai cika zama tare da su ba, kulawar da yake nuna mata da kaffa-kaffa da rashin son b'acin ranta yasa Hajia lura da hakan, nan ita ma saita fara kafa mata k'ahon zuk'a ta hanyar nuna mata tsana a fili da cewa bata isa ta rabata da d'an ta ba ko da me ta shigo, sam bata kula ta saboda ko ba komai babba ce ita kuma ta haifi mijinta, sai dai ita kuma bata cika yin irin bautar da take saka Zeinabu da Soueiba ba da Sa'ada, ko sun fara aikin tare zata zame ta kawo na ta fi'ilin, a lokacin Sa'ada ita ma hak'uri take sosai, badan ma karatun ta data saka gaba ba wanda Hajiar ta so datseshi, amma da k'yar Hassan ya fad'awa Suley daya fahimci tana son karatun sannan suka shawo kan matsalar, duk da jimawar da tayi bata samu ciki ba hakan bai damu Hajia ba, dan ita a ganinta ma hakan daidai ne, dan yanda ita kad'ai ma ta mallake mata d'a ina ga ta haihu, saidai bata d'aga musu k'afa har zuwa lokacin, duk wata hidima ta gidan sune har da hidimar ita kanta, idan ka same su da rana zaka rantse masu aiki ne ba matan gidan ba, gashi kuma a lokacin Allah yasa duk mazajen nasu babu wanda bai samu k'arin matsayi ba, amma haka suke rayuwar k'ask'anci kamar bayi, ko fita zasuyi sai Hajia ta bada izini, dan haka tun kana jibi zaka fita kake sanar da ita dan ta baka lokacin data ke so, girman ciki ko tsufanshi baya sa ta sarara maka da aikin gida, saika haihu kawai kake da damar yin jego na sati d'aya shima saboda idon mutane, wani ikon Allah kuma har saida Hadiza ta shekara *shida* a gidan kafin Allah ya bata cikin su Hamna, ciki ne daya bata wahala sosai, hakan yasa fa Gambo ya rufe ido ya shirya sai kawai Hajia ganinshi tayi da kaya yace zai tafi da matarshi can ya samu k'wararrin likitoci da zasu dinga dubata, a lokacin Hajia bata iya cewa komai ba saboda Suley dake wurin kuma yace ba komai su tafi Allah ya tsare, daga lokacin ta sa k'afar wando d'aya da su dukansu, ko kiranta sukayi a waya dan su gaisheta sai dai ta kashe kiran, sam ta fita a lamarinsu ta zura musu ido, shi kuma yana can duk da yana damuwa sosai da hushin da Hajiar keyi amma baya hana shi kulawa da ita, sosai yake nuna mata soyayya, amma zuciyarta kamar ta shed'an sam ta k'i saduda ta so shi daidai da k'wayar zarra, suna haka har ta haihu ta samu *Hamna* da *Amna*, yara ne da za ace basuyi goshi ba a wajen Hajia, dan da suka dawo ma dan ayi suna anan ko kallon yaran batayi ba, hakan baya musu dad'i amma ya zasuyi daya wuce rarrashi harta yafe musu, abu ya k'i ci ya k'i cinyewa, sai Hadiza tayi anfani da wannan dama ta hanyar nuna mishi gwara ya rabu da ita danya shirya da mahaifiyarshi, tambayar daya jefa mata a lokacin tasa t saurin kallonshi, domin kuwa cewa yayi "Har yanzu na kasa samun shiga zuciyarki ko?"

Kame kame kawai ta dinga yi masa har yace ta fad'a mishi gaskiya tsakaninta da Allah tana son zama da shi ko bata so, ganin ba zata iya tauye kanta ba yasa ta fad'a mishi gaskiya hak'uri take amma bata sonshi har yanzu, duk da hakan bai mishi dad'i ba amma ba zai iya tauyeta ba, dan inhar zai kasa samun zuciyarta a shekara shida duk da kyautata mata da yake, to fa baiga ranar da zata so shi ba, a wannan lokaci ne ya saketa saki d'aya yace zata iya aure idan ta samu miji, su Hamna kuma da ko arba'in d'in su ba ayi ba yace ta shayar dasu idan ta yayesu zai d'auko yaranshi, gaba d'aya kuma sai hakan bai mata dad'i ba taji jikinta yayi sanyi, amma aikin gama ya riga daya gama kuma, jin wannan labari yasa Hajia shiryawa da shi, rufe ido tayi tace ai dole sai dai ta bar su Hamna ita ta tafi saboda ta nuna mata basa buk'atar ta suma tunda ta nuna bata buk'atar su, irin tarzomar da akayi ba k'arama bace akan yaran, dan ita ma Hadiza zuciya tayi ta aje yaran tace gasu nan ta shayar dasu idan zata iya, Suley kuma da Gambo suna rarrashinta amma ido sun rufe, haka ta fita a gidan daga ita sai kayan da aka kawota da su, tace yara Allah ya raya mata su idan sun girma zasu nemeta, Hajia kuma tace ba zata hana su nemeta ba amma dai ba zata tab'a cin moriyarsu ba, bayan ta barsu da fari Sa'ada tace wai dole ta sha maganin da zai dawo mata da ruwan nono dan lokacin ita ma shiru tun su Ammar saboda ta shayar dasu Hamna, Alhaji ne yace ba zai tab'a faruwa ba, idan kuma yaran suka tasa suka zo junansu fa, kuma ko ba komai ma zasu iya had'a su auren zumunci, dan haka sai dai tasan yanda zatayi da yaran, dan ta nuna musu a shirye take yasa ta samu madara aka dinga basu, amma rainon yaran kuma Sa'ada ce keyi wacce ke karatun likitar ta a lokacin, a haka su Hamna ke wayo suna girma har Sa'ada ta so tafiya France dan zama doctorat, amma Hajia tace ina ba'a gidan nan ba, wanda tayi ma babu yanda zatayi ne, haka ta hak'ura ta barwa Allah, wanda lokacin ne kuma Hajia tace dole sai dai Junaid ya zama malamin makaranta, Amar kuma cikin ruwan sanyi ake ce shalele ya zama ma'aikacin banki, Ammar kuma da kullum suna tare da kawunshi indai yana gari babu abinda yake so daya wuce ya sa hular soja ya daidaita mata zama, sai Hajia tace ya zama likita shi yafi mishi, bore yayi yace sam sai dai ya nemi kud'i ya kai kanshi inda zai zama abinda yake so, amma haka Sa'ada ta rarrasheshi tace ya cika mata burinta sai su zama likitoci suna zuwa aiki tare, badan wannan dubara ba da fa sai dai idan sunji k'arar bindiga su fito suga Ammar ne ya zama soja, gashi Innusa da yasa ta d'auki wannan alhwashin ma ko kula da tsiyarsu bayayi, har yanzu jituwa ta kasa shiga tsakaninsu, su Ramma an jima da barin duniya, amma shi da yan uwanshi sun k'i d'aukar Suley a matsayin d'an uwa, komai zasuyi su kan wareshi ne, lokuta da dama idan zasu aurar da d'aya daga cikin yayansu sai dai yaji a gari, amma hakan baya hanashi fad'awa iyalinshi kuma ya umarcesu da su tafi, amma banda Zeeya wacce baya ma fara cewa ta tafi d'in, sai dai bamu sani ba ko anan gaba zasu iya neman alfarmar ko taimako, domin kuwa a cikin zuri'ar Innusa akwai d'alibai da dama masu neman ilimi, sannan akwai 'yan kasuwa, masu shigowa da kaya, haka kuma 'yan kwangila da wani lokacin kud'in da aka basu suke musu k'aranci dole sukan nemi bashi a hannun banki, sannan shi kanshi Innusa yana fama da ciwon k'afar da har ya fara shafar zuciyarshi.

*CI GABAN LABARI*

Koda suka shiga b'angaren su kowa d'akin shi ya nufa ya shiga wanka, sai dai babu mai kuzari a tare da shi har suka fara fitowa, Junaid ne ya tarar da Jibril zaune ya k'urawa tv ido, zaune yayi shima ya kalleshi yace "Jibril tunanin Amna kake ko? Kayi hak'uri kaji, watak'ila hakan shiya fi zama alkairi a wajenka, muyi addu'a kawai Allah ya bamu hak'uri da juriyar cin wannan jarabawa."

Numfashi ya sauke mai k'arfi ya kalleshi da murmushi yace "Sam d'an uwa ba abinda nake tunani ba kenan, yau ina cikin farin ciki Junaid, ni da ban tab'a ganin soyayya daga wurin Hajia ba, yau sai gashi ta kalleni tace ta bani Jamila, wacce daga tsatsonta ta fito, gaskiya naji dad'in haka, duk da ban samu Amna ba amma nayi farin ciki sosai da hakan."

Amar daya shirya zai fito ne yaji suna hira dan haka ya tsaya yana saurare, Junaid ne yace "Ni ma ban k'i Hamna ba, amma ka tayani tunani mana, yanzu me iyayen Maryama zasuyi tunani? Zasu d'auke ni mak'aryaci kenan d'an k'ananan mutane? Sannan ita idan ta jini shiru za tace na gudu kenan ko kuma dama mayaudari ne ni? Wannan abun nake ta tunani wallahi."

Cike da nuna damuwa Jibril yace "To meye abunyi yanzu? Gaskiya bai kamata ace ka bar Maryama a wannan rayuwar ba, ko da alk'awarin daka d'auka na zaka mayar da ita gida ne ka cika, sauran saika musu bayani yanda zasu fahimta."

Jingina bayanshi yayi a kujera yace "Da ace zata lamunce min wallahi dana had'a na auri mata biyu a lokaci d'aya, sai dai nasan ba lallai ta amince ba."

Ammar ne ya bud'o k'ofa ya fito hakan yasa Amar k'arasa fitowa shima, abun mamaki kayan baccin jikinsu iri d'aya ne, dan dama sau tari sukan samu wannan kamanceceniyar, kallon juna sukayi wanda yasa Ammar yin tsaki yace "Je ka cire kayan nan."

Amar da baya yanayin farin ciki yace "Saboda me? Idan ka damu kai ka cire naka mana."

Wani kallon zakuwa ga sani ya mishi yace "Oho, haka kace?"

Kama rigarshi yayi ta k'asa yayi sama da uta ya zage ya rik'e a hannu, wandon ma dama k'ugunshi roba ce, sab'ule shi yayi ya bar gajeran daya tsaya mishi a cinyoyi, jefawa Amar kayan yayi wanda ke murmushi yana ayyana rashin kunyar da Amna zata gani baiwar Allah, jin kayan a fuskarshi yasa ya yamutse fuska yace "Meye haka kuma?"

Saida Ammar ya zagayo ya zauna d'an nesa da Junaid da suka k'ura mishi ido yace "Ka had'a ka sanya duka, gigin tsohuwar can ya farka yasa ta mana mata a daren nan, kana so kayan bacci ma sai mun saka kala d'aya salon wata rana matarka ta k'wamuso ni a tunaninta kai ne."

Jibril ne yayi dariya yace "To idan ta kama ka d'in ba sai kace mata ba kai bane."

Kallonshi yayi da nufin magana amma ganin kallon da Junaid ke mishi yasa ya had'e fuska yace "Malam ko na mik'e na cire har wannan ma ta yanda za ka ga komai da kyau?"

Da sauri Junaid yace "Kai wa Allah ka rufa mana asiri, ina mu ina ganin wannan al'amari, in a matse kake da kayi tsirara ka jira 'yar k'anwarmu ta zo, wannan ba laifi ba."

Dogon tsaki yayi ya mayar da hankalinshi kan waya, Amar ne dake shirin fita ya cillo mishi kayanshi yace "Dan Allah ka saka kayanka, kasan fa har yara shigowa suke haka ma matan suna iya zuwa yin wani abun."

Kallon Amar d'in yayi yace "To meye a ciki? Duk yaron daya ganni haka ai nima nayi zama kamarshi, kuma shima zai dawo kamar ni d'in, mata kuma da kake magana a kai duk abinda zasu gani suji kunya bai wuce wannan abun ba wanda kuma basa rayuwar jin dad'i sai dashi."

Yanda ya k'arashe maganar yana nuna k'asan gajeran wandonshi da kuma had'e fuskar da yayi kai kace bashi ya fad'a ba yasa Amar cewa "Allah ya shirya ka."

Ba tare daya kalleshi ba yace "Tare da ebolar gidanku ba."

Jibril da tuni ya fahimta ne ya tuntsire da dariya sai Junaid da yace "Wace kuma ebola?"

Jibril ne cikin dariya yace "Wa fa inba Hajia ba, nasan dai ita yake nufi."

Amar ne ya d'an b'ata rai yace "Wallahi Ammar kaji tsoron Allah, ka sani fa kakar ka ce, ya zaka rainata haka?"

Wani kallo ya masa galala yace "Allah ko? To zo ka ci uwani shalelen Hajia."

K'wafa yayi inda Amar ya juya zai fita, muryar Ammar yaji yace "Bani kayana a hannu na."

Juyowa yayi ya kalleshi yace "Kai daka cillo min a hannu na ka damk'a min? Kusa da kai fa suke ka d'auka kawai."

Sake tamke fuska yayi cikin amon muryar da sam babu wasa a ciki yace "Na ce ka bani a hannu na ko."

Tabbas Amar yasan inhar bai bashi ba sai sunyi fad'a, shi kuma yana so ya ga ya cika alk'awarin daya d'aukarwa Ummy na zai dinga hak'uri da d'an uwanshi dan wani lokacin al'amarinshi kamar mai aljanu yake, dawowa yayi ya d'auki kayan ya mik'a mishi kafin ya juya zai fita, kallon bayanshi yayi yace "Idan kaje ka sa mana matar nan ta rubuto maka kalar rayuwar da take so muyi da matan bayan an d'aura auren, dan mu hardace a kanmu ya zauna mana sosai."

Girgiza kai kawai Amar yayi ya fice daga d'akin, d'aukar wandonshi yayi ya saka ya gyara zamanshi kamar zaiyi kwance a kujerar yana danna wayarshi yana shafar shafaffen cikinshi mai shegen fad'i, inda k'irjinshi kuma yace ja bani wuri saboda bud'ewar da yayi, jin su Junaid sunyi shiru yasa ya d'an saci kallonsu yace "Ka fad'a min indai kana sonta har yanzu ni kuma zan karb'omaka aurenta wajen iyayenta?"

Kallonshi sukayi sai Junaid da yace "Ina sonta har yanzu, amma tayaya zakayi haka? Gaskiya bana son wata matsalar Ammar, kuma naga kai kan ka baka tsira ba wajen Hajia."

Murmushin gefen labb'a yayiba tare daya kallesu ba yace "Ku zuba ido kuga ranar da zan fito da wacce nake so, wallahi sai dai ta ganta da ciki kawai ba tare da tasan yaushe haka ta faru ba ma, shirun da kuka ga nayi saboda bana da abin fad'a ne kamar yanda na fad'a ma ita kanta tsohuwar, Amna kuma banda wani dalili na nuna mata tsana ko k'iyayya, dama wannan kankanar ce."

Shiru sukayi dan sun san baida abin fad'a kamar yanda yace, da akwai kuwa daya fad'a ko da abinda zai fad'a zai jawo kwanciyar wani a gadon asibiti.

Amar na fita b'angaren iyayen ya nufa dan amsa kiran da Hajia ta masa, amma yana daf da shiga saiya samu Hamna har yanzu tana zaune tana kuka, tsayawa yayi ya sunkuya kusanta yana kallonta yace "Hamna."

D'agowa tayi ta sauke matsakaitan idontaa kanshi, cikin tausasawa yace "Ke ma kina kukan zab'in da Hajia ta miki ne?"

Saida ta share hawaye da hannunta cikin muryar da tasha kuka tace "A'a yah Amar, yah Junaid d'an uwana ne, ba zan k'i shi, sai dai Hajia ta ruguza min burina na zama gogagiyyar mai tsara kaya (fashion designer) da kuma zama mai kwalliya, sanin kanka ne mu mata Hajia bata yarje mana fita daga garin nan ba da sunan karatu, toya kenan idan nace zan tafi da auren yah Junaid a kai na? Ba zata amince ba, kuma gashi mun riga da mun gama magana da wani compagnie dake *Abuja* zan je a hutun nan da za ayi dan fara d'aukar darasi na kwalliya, shiyasa kawai nake kuka."

Shiru yayi yana kallon yatsun k'afar ta masu tsayi da tudu wanda na kusa da babban yatsan yafi kowane tsayi, ya d'an jima a haka kafin ya mik'e yace "Kiyi hak'uri kinji, zan shiga wajen Hajia yanzu na mata magana, insha Allah burinki ba zai ruguje ba."

D'ago kai tayi ta kalleshi tace "Nagode yahAmar, dan Allah ka min wannan taimakon, idan ba haka ba babu wani abinda nake so sai dai na zama matar gida nima."

Murmushi kawai yayi ya d'an jinjina mata kai ya shige falon, ajiyar zuciya ta sauke dan tasan zaiyi wuya Hajia ta kasa sauraren shalelenta, indai har ya nuna hakan yake so to zata amince ko da ita ba haka ta so ba.

*Fatan nasara Amar*
11/06/2020 ร  17:26 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ’ž _*MASOYA NA*_๐Ÿ’•


_Bismillahir rahamanir rahim_

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_8_


Bud'ar bakin Raudat cewa tayi "Lahh! Ai Ammien mu tana raye, tare suka tafi basraba basraba amma ita bata dawo ba."

Cike da makirci tace "Ayya kunji dad'in ku, kuna da iyayenku a raye suna k'aunar ku, sannan Allah ya muku baiwa ta daula babu abinda kuka nema kuka rasa, sannan na tabbata iyayenku suna farin ciki da junansu bare hankalinku ya dinga tashi idan sun samu sab'ani."

Murmushi Raudat tayi tace "Gaskiya ne aunty, duk da iyayenmu suna yawan fad'a amma dai fad'an nasu na shirme ne, dan duk fad'an su basa awa d'aya basu shirya ba, kuma dama Ammie ita tafi d'aukar zafi."

Ta gefen ido ta kalleta kafin ta d'an zaro ido tace "Kina nufin yanzu nan iyayenku suna fad'a? To akan me?"

Cike da yarinta Raudat tace "Kamar yanda na fad'a miki fad'an su duk shirme ne, amma mafi aksari sunfi rigima akan kishin Ammien mu, wani lokacin kuma bamu san meke had'a su ba sai dai muga Ammie na b'uya a bayan Ammie, idan ita ta tsokani Dady kenan."

Saida ta kamo hannunta tace "Kenan Ammienku batayin duk abinda Dadynku baya so?"

Saida ta firfito da manyan idonta masha Allah kafin tace "Ban sani ba gaskiya, mu dai kawai rayuwar iyayenmu tana bamu sha'awa, suna k'aunar junansu sosai, suna raha da wasa a zamantakewarsu, shiyasa muma muke k'aunar su."

Mik'ewa tayi tace "Aunty bak'uwa saida safe."

Murmushi tayi tace "Aunty bak'uwa kuma? Ki kira ni da *Nasmat*."

Murmushi Raudat ta mata tace "Nice name aunty Nasmat, good night."

Da kallo kawai ta bita harta fita, tana fita ta tab'e baki tana tunano abinda ta fad'a mata, mik'ewa tayi ta cire kayanta ta fad'a toilet, ta jima tana k'arewa toilet d'in kallo ganin kamar ba wajen fitar da datti da k'azanta ba, ko bacci ya kamaka sai kayi a ciki kuma cikin nutsuwa, haka ta fara wanka kafin ta idar ta fito, jakarta da suka taho da ita ta bud'a ta shafa na shafawa ta murza na murzawa sannan ta saka rigar bacci iya gwiwa mai kyau, saida ta zauna kan gadon ta d'auko wasu magungunan mata wanda ta tanadesu dan Abbas kawai tasha sannan ta kwanta.

Suna kammala cin abinci Abbas ya shirya ya tafi taron nan, awa biyu ya d'auke shi kafin ya dawo gida, ya fito a motarshi zai shiga part d'in shi a farfajiyar gidan ya ci karo da mutum, mutum ma mace cikin shirin atamfa tasha ado, wa zai gani inba Harira ba, gidan shiru alamar kowa ya kwanta sai kukan d'awisu da talo-talon dake cikin gidan an ware musu wuri na musamman, tunda ya gane ita ce kawai ya zura kai zai wuce dan haka tayi saurin cewa "Sannu da zuwa yallab'ai."

Tsayawa yayi kawai ya kalleta kamar mai son gane nufinta, wani farrr ta fara da ido tana takowa cikin girgiza jikinta, tabbas kayan sun amshi jikinta musamman yanzu data yi yar k'iba sun zauna mata a jiki, kwalliyar ma ba laifi sai dai kawai in baka sonta ne zaka kushe ta, mamakin irin salon da take taho dashi yake yi harta tsaya gabanshi k'amshin turarenta da baida maraba da na 'yan bori ya daki hancinshi, muryarta ce ta dawo dashi daga d'aukaewar da numfashinshi ya kusa yi saboda bai tab'a jin turare irin wannan mai tayar da hankali ba tana fad'in "Yallab'ai, dama na ga baku dawo tare da Sameera bane, shine nace bara na jira ka dawo ko akwai abinda kake so wanda zan iya yi maka?"

Kallon mamaki da kuma yaushe yarinyar nan ta haukace yake mata? Me take nufi? Sameera ce ma take kira haka babu sakayawa? Saida ya d'an ja baya sosai ya k'are mata kallo yace "Ke! Yaushe aka haifeki?"

Sai kuwa Harira ta sake juya ido ba tace komai ba, dan haka yace "To ki koma ki tambaya dan kisan shekarunki da nawa ba d'aya bane, ki shiga hankalinki tun wuri, dan ruwa ba sa'an kwando bane, idan kuma baki ji ba, u wil regret it, that's my last warning."

Juyawa yayi a sukwane ya shige part d'in ya barta nan, tab'e baki tayi ta juya tace "Can ka k'arata da turancinka, ni inda zaka dinga min magana ma da turancin da zanfi jin dad'i."

Raihan na kwance d'aki sun gama waya da mahaifiyarta, har zata kwanta dai kuma saita turawa Abdul sak'o tana tambayar ya hannunshi? Ko ba komai yaji dad'in tambayar dan hakan na nuna ta damu dashi ne, amsa mata yayi da sauk'i, Allah ya k'ara afuwa shine abinda ta fad'a ta aje wayar ta kwanta abinta.

*Washe gari* da sassafe duk yaran sun shirya suna kan dinning suna jiran isowar Dadynsu, Abbas kuma na shiryawa ya fito falonshi da niyyar fita, yanzu ma wa zai gani sai Harira wacce tunda Sameera tace mata duk aikin da zatayi b sai ya kaita ga shiga sashin Abbas ba take jin haushi, wato a lokacin da suna matsayin ma'aikata ai ita ce ma ke kula da sashin shi, kenan ita ma tana tsoron a k'wace mata miji kamar yanda ta k'wace ma Salma, dan haka yau saida ta gama kimtsa yaran da ba zasu iya shirya kansu ba ta shiga falon nashi da k'ofar ke bud'e ta falon Sameera, babu wani abu da d'akin ke buk'ata amma haka ta zage tana goge goge tana karkad'a jikinta sosai cikin doguwar rigar wani tattausan less bayan ta cab'a ado.

Saida Abbas ya rintse idonshi dan yanda k'ugunta ke rausayawa abin tayar da hankali ne, gashi har shatin mazaunin pant d'inta yana hange daga inda yake, haushi da takaici

Please Login or Register in order to submit comment