Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mishi kai kace yana fahimtarshi, gidan Gambo suka sauka anan suka samu tarba ta musamman kamar wasu sarakai, sun ci sun sha Alhamdulillah kuma kwanansu d'aya, washe gari da safe kuma suka shirya dan jirginsu zai tashi lieutenant yace ba za ayi tafiyar mota da yaronshi ba *(Shureim Ammar)*, Hamna kad'ai ta rakasu filin jirgi, a lokacin da suka juya zasu shiga jirgi sai taji kamar Ummy na tafiya da zuciyarta, bugawar zuciyarta ce taji ya k'aru, bakinta sai rawa yake zuciyarta na karkarwa a tsakanin k'irjinta, suna daf da shiga Ummy ta juyo ta kalleta, idonta kad'ai suka ankarar da ita halin data shiga ganin za ayi mata nisa da abinda ta haifa, dawowa Ummy tayi ta tsaya gabanta ta mik'a mata shi, jiki na rawa ta karb'eshi ta sumbaci ko ina na fuskarshi, k'ura mishi ido tayi tana kallo wanda hakan yayi sanadiyar zubar hawayenta akan jikinshi, Ummy na gani tace "Hamna kuka kike?"

Kallon Ummy tayi tace "A'a." Mik'a mata shi tayi ta share hawayenta, cike da tausayinta Ummy tace "Hamna zan kula miki da shi kamar yanda ke ma zaki kula dashi, ki ci gaba da addu'a insha Allahu komai zai daidaita, ni zan d'auki alhakin duk abinda zai faru, ki kula da kanki kinji ko? Sannan kar kiyi wasa da shan magunanki akan lokaci saboda zasu taimaka miki sosai."

Kai kawai ta jinjina alamar to, tana kallo suka shiga sannan ne dreban da suka zo tare ya fara mata oda, juyawa tayi ita ma suka koma gida sai kuka take. Su Ummy kuma suna zuwa gida suma akayita farin cikin ganinsu, inda kowa ke karb'an beby yana gani.

Har d'aki suka sameta tare da Amna suka gaisheta, zaune sukayi inda Ammar ya k'arasa gaban gadon ya sunkuya ya d'auke shi, a hankali yayi zaune yana kallon fuskarshi, kowane motsi nashi yana binshi da hankali da nutsuwa, shi kam har ga Allah abu na daban yake ji akan k'ananshi da bai tab'a jinshi akan kowace hallita a doron duniya ba, cikin nutsuwa ya rab'ashi a jikinshi ya rumgume sosai ya d'ora bakinshi kan wuyanshi, lumshe ido yayi sakamakon tattausan turarenshi daya shak'i k'amshinshi, bud'a ido yayi ya kai bakinshi kan labb'an shi da nufin sumbata, sai kawai yaron ya bud'a baki ya d'auka nono ne za'a saka masa, caraf ya karb'e leb'enshi na k'asa ya shiga tsutsa da sauri sauri, baisan sanda dariya ta kubce mishi ba saiya shiga k'yak'yatawa ba tare daya cire mishi leb'en ba, Amna na kallonsu sai taji ina ma nasu yaron ne a hannunshi, Ummy na ankarewa da haka ta taro mishi hannaye tace "Kawo shi yasha." Da k'yar ya cire leb'enshi daga bakinshi ya mik'a mata shi.

*Kwana uku*

Duk abin duniya ya shawa Hamna kai, sam yanzu ta daina jurar wulak'ancin Aissata, zuciyarta kawai tafasa take ita kanta bata san dalilin b'acin ran nata ba, yau ma hakane ya kasance da safe ta mata duk abinda takeyi, amma tsabar fitina sai Aissata tace ta gyara mata d'aki, ta shiga tana gyara ta shigo tana mata kinibibi, ganin tayi banza da ita tana aikinta yasa Aissata cewa "Kinga wurin nan bai fita ba."

A k'ufule ta kalleta tace "Saiki gyara da kanki mana."

Cikin d'aga murya tace "Hamna ni kike fad'awa haka? kin rainani ko?"

"An rainakin kiyi abinda zakiyi." Mik'ewa tayi ta kalleta sosai tace "Ke nafa gaji da abinda kike min, tun farko Allah ya isar mahaifina ce ta min katanga da dakuwa dake, amma wallahi badan haka ba ke baki isa ki min abinda kika min ba."

Fad'a Aissata ta fara yi da hausa da zarma da french saboda harshenta bai nuna ba, jefar da abun gugar tayi ta harareta sama da k'asa tace "Matsalarki ce."

Fita tayi daga d'akin ta shiga nata, bata tsaya komai ba ta had'a kayanta tsaf a akwati ta fito, dreba ta samu tace ya ciro mata ticket, shima bai b'ata lokaci ba ya ciro ya kawo mata ta ajiye.

Tunda asuba ko da tayi sallah ta shirya, *07:30* ta fito ta samu dreba yasa jakarta suka bar gidan, Gambo bai sani ba haka ma Aissata dake wurin motsa jikinta da babu wata tsiya da take ragewa. Suna zuwa ta shiga bus suka d'aga zuwa Maradi, ita kanta tasan saboda wannan d'ayan ne zata koma garin nan, wannan d'ayan kuma ba kowa bane sai *Shureim Ammar Hassan Suley Gaga*.


*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.N.A]* β˜†πŸ–ŠοΈ


_Bismillahir rahamanir rahim_

_48_


Tana shigowa gidan ma yer uwarta ce ta fara karo da ita tana d'an safa da marwaa tsakiyar gidan, suna had'a ido dukansu ihu suka saka Hamna ta saki jakarta suka rumgume juna, cikin farin ciki Amna dake tura tulun ciki tace "Ya kika zo mana haka ba zata? Ke da wa kika zo?"

Bata amsa tambayarta ko d'aya ba ta saketa tana k'are mata kallo tace "Amna dama haka kika koma? Yanzu kenan da ban zo ba da sai dai naji labarin haihuwarki?"

Hararanta tayi tana d'an kai mata duka a kafad'a tace "Haihuwata ko haihuwarki dai."

"Me?" Ta fad'a da k'arfin bala'i, ba iya gabanta bane kawai ya fad'i har jinin jikinta ma saida ya matuk'ar hawa, dariya ta mata tace "Idan Amna ta haihu ai Hamna ce ta haihu."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Wai Allah, amma dai cikin nan naki yan biyu ne ko? Wannan abu haka."

Cikin shagwab'a tace "Shiyasa na so nayi Γ©co (scanning) amma yah Ammar yace sam bai yarda ba, yanzu haka gobe zan koma awo har na cinye sati biyun da aka bani, nak'udar tsaye kawai nake fama da ita."

"Karki damu, ai da sati biyu biyu ma kina iya cinye wata biyu, kawai ke dai karki zama lusara mai son jiki, ki dinga tafiya mai tsayi saboda ko nak'uda ta taso miki ma zata zo miki da sauk'i, amma kin fara zubar da ruwan zak'i?"

Waro ido Amna tayi a hankali sai kuma ta k'ank'ance su tana kallonta da mamaki, ba tare data daina mamakin ba tace "A ina kika san haka ke kuma sai kace wacce ta tab'a haihuwa?"

Tsuru Hamna ta mata da ido, saida ta k'ak'alo abinda zata fad'a kafin tace "Kiji
sai kace ba mace ba, to wannan ne sai mace ta haihu zata sani."

Jakarta ta d'auka suka nufi falon Hajia tana fad'in "Muje ki gaishesu sai muje b'angarenmu musha hira."

Sallamarsu tasa wanda ke falon suka kallesu, yan biyu ne dai gasu amma duk sun canza, Hamna ta k'ara haske kan wanda take da a farko, jikin nan nata duk da tana shan wahala a wurin Aissata amma ya kwanta luf dashi, Amna kuma ta k'ara duhu sai kuma cikin yasa tayi muni ba kamar kafin ta d'auki cikin ba tsaf da ita, ana gaisawa ana mamakin tahowarta katsam haka babu sanarwa, Ummy na d'aki take jin kamar maganarta, tana lek'owa ta ga dai ita ce da gaske, saida suka gaisa da kowa sannan ta wuce d'akin Hajia dan tun sallah la'asar bata fito ba jikin ya d'an k'ara nauyi sosai bata san dai nunawa ne, kamar mai sand'a ta shiga tana sallama har ta zaune kusanta a k'asa ba tare data yarda sun had'a ido ba, bata amsa sallamarta ba bare gaisuwarta tana mamakin dawowarta bada izininta ba.

Cikin wani irin amon murya tace "Meya dawo dake? Waya baki izinin dawowa ba tare dana amince ba? Ke ce kika zab'i dawowa ko kuma shi Gambon ne yace ki dawo?"

Cikin sanyin murya tace "Gaskiya Hajia basu san da fitowa ta ba, kawai na gaji da zaman can ne saboda tanti Aissata ta mayar dani kamar wata baiwarta, kuma Abba ma har Allah ya isa ya min idan na b'ata mata rai, jiya ma mun samu sab'ani ne shiyasa na tahowa ta dan nasan Abba na iya dukana idan ta fad'a masa na mata rashin kunya."

Kallonta Hajia tayi ta mik'e tsaye cikin b'acin rai ta gaura mata mari a fuska, dafe kunci tayi da sauri ta k'ara sunkuyar da kai, cikin masifa tace "Hamna kinsan dalilin da yasa na turaki can? To saboda ina so nasan abinda ke faruwa acan d'in ne, ina so naga abinda yasa bata so kowa ya rab'eshi sai ita kad'ai, amma da yake mahaukaciya ce ke shine kika dawo min haka ko? To tashi ki bani wuri, ni kuma zanje da kaina nayi aikin dan ba zan haifi d'a a cikina ba kuma wata ta fini cin moriyarshi ba."

Fita tayi ita kuma ta shiga masifa tana fad'a, tana fita d'akin Ummy ta shiga, tana ganinta bata tsaya komai ba tace "Hamna meya dawo dake? Ya akayi kika zo baki sanar min ba?"

Marairaicewa tayi tace "Ummy wallahi Tanti Aissata ta addabeni, kawai ta b'ata min rai ne jiya shiyasa na baro mata gidan."

"Amma me Hajia tace miki da kika taho ba da umarninta ba?"

Tab'e baki tayi tace "Tana can tana masifa mana, wai zata je da kanta Niamey d'in ta ga wace irin rayuwa suke, wallahi da za taji tawa da sai nace karta tafi, dan matar nan da gangan ma zata iya d'ora mata hawan jini."

Murmushi tayi tace "Hamna ince dai ba yaron nan yasa kika dawo ba ko?"

"A'a Ummy, kawai na dawo ne." Ta fad'a idonta akan Shureim dake bacci, fitowa tayi ta d'auki jakarta ta kai d'akinsu, saida tayi sallah magriba tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar kanti da d'an kwalinta sannan ta fito, Farisa tasa ta gyara mata d'akinta ita kuma ta sauko k'asa, saida ta shiga ta ga Zeituna da Fatima masha Allah yarinyar kamar ka fizge a hannunta ga uban gashi, suna gaisawa ta fito ta nufi wajensu Umaimah.

Mamaki ne ya kusa kasheta data shiga d'akin, yarinya 'yar k'walisa uwar kwalliya da tsabta, amma wai ita ce zaune k'asa da d'aurin k'irji tana cin 'ya'yan tsamiya tana tofar da yawu, kan nan nata yayi daud'a ya tsufa abun ba kyan gani, daga tsaye take k'are mata kallo tana mamaki, tafin k'afarta abinka ga farar fara yayi duhu, a take a wurin taji Umaimah ta fita a ranta, dan duk yanda kake ji dai zaka daure ka gyara jikinka tunda har kana iya cin abu kuma kana taka k'asa, ko baka gyara dan komai ba ka gyara dan kar namiji ya ga makusarka. Daga nan tsaye suka gaisa ta wuce b'angaren yer uwarta, ba wai son kai ba ko dan tana yer uwarta, amma tana dosa b'angaren ma k'amshin turaren tsintsiya ne ya mata maraba.

Tana shiga ita ma zaune take k'asa ta mik'e k'afafu da suka kumbura sumtum, cikinta yafi na Umaimah girma nesa ba kusa ba, cikin nutsuwa take cin bredinta mai yanka nan tana shafeshi da la vache qui rit, zaune tayi ta fizge bredin tana fad'in "Sakarya kawai, kina da ciki kina ta fama da abubuwan da zasu bud'a miki yaronki a cikin cikin, ki zo kisha wahala kafin ki haihu."

Hannu ta tara mata tace "Taimaka ban wannan na k'arasa to."

"An k'i." Ta fad'a tana d'auke d'an kwalin ta aje bayanta ta kalleta tace "Jamila wace asibiti take?"

Cike da shak'iyanci ta wani murgud'a mata baki tace "Asibitin mijina mana."

Sai kawai taji gabanta ya fad'i daga anbaton mijinta, da mamaki ta kalleta tace "Anya kuwa Amna bai koya miki iskanci ba, ke ma fa kin lalace yanzu."

"A'a ni bai koya min ba, kawai dai abun ne kamar a karatu, yana biya min ni kuma na hardace shi a kaina."

Tab'e baki tayi tace "Lallai mai miji." Amna ce tace "Yer uwa dama ina so ki zo, akwai matsala fa..."

Duk da ta kai k'arshen abinda take son fad'a amma saida ta juya ta kalli k'ofar da taji sallamarshi. Yana shigowa ya tsaya kamar wanda aka dakatar dashi, idonshi cikin nata wacce k'afafunta ke tank'washe tana jujjuya wayarta dake hannunta, *sanyin idaniya*, yau ne ya tabbatar da kalmar sanyin idaniya da ake fad'a, domin kuwa sanyin nan bai tsaya iya idonsa ba saida ya zarce har k'ark'ashin zuciyarsa ya isar da sak'on cewa wata mai matuk'ar mahimmanci ta iso wacce akayi kewarta na wani lokaci, dawowa yayi hayyacinshi ya fara takowa yana sauke jakarshi daga kafad'a ya kalli Amna yana fad'in "Duniyata bak'uwa kikayi?"

Kallon Hamna tayi tana dariya tare da bata gefen fumcinta da taga ya nufota tasan me zaiyi, sumbatarta yayi tana cewa "Sannu da zuwa, ya aiki, kayi hak'uri nayi nauyi ba zan iya tashi tarbanka ba."

Jakar ya aje kan kujera ya zauna daf da Amna yana rik'ota jikinshi yace "Je sais ma chΓ©rie, ya kika wuni?"

Cikin shagwab'a tace "Lafiya lau, kai fa?"

Hamna ya kalla wacce a taswirar zaman nasu suna kusan juna ne dukansu inda shi da ita suke fuskantar juna Amna ce kawai ta shiga tsakaninsu, yana kallon ita kuma tana dalla masa harara, wani bala'in haushinshi taji saika mata yake, yanda har taji ya fara tasiri wajen jin haushin yer uwarta ma data biye masa, akan me zasu raina mata wayo haka? Dan ita bata da auren ko me? D'auke idonta tayi daga kansu sai Ammar ne da yace "Ke baki iya gaishe da mutane ba?"

"Eh." Shine ta fad'a tana juya baki kamar zata tsinka shi, d'agowa yayi daga kishingid'en da yayi yana fad'in "Ke kankana ni? Ni kike ce ma eh?"

Da sauri taja baya tana fad'in "An fad'a d'in, kaga malam karka takura min fa, na fad'a maka ka daina shiga harkata, ba wajenka na zo ba ni wajen yer uwata na zo."

Jujjuyawa ya farayi alamar yana neman abunda zai jefa mata, da sauri ta tashi tsaye ta zagaya bayan kujera ta tsaya tana hararanshi, tsayawa yayi daga neman abun ya k'ura mata ido, a ranshi yace "Shegiya har tayi shirin gudu, ass kawai take jira."

Mamakin k'ibar da yaga ta k'ara yake yi, saida ya k'ara kallo da kyau yace "Ke kankana, murguzawa, yaushe kika mulmuje haka? Me tonton ya dinga baki acan kika koma haka?"

Cikin jin haushi tace "Tubarkallah maye ka ci kanka, ina ruwanka da k'ibata inba sa ido ba, to kurwata tafi k'arfinka maye kawai."

Zunbur ya mik'e ya nufeta, tana ganin haka ta tattare rigar bi ta bayan kujerar shi kuma tsalle yayi ya dira bayan kujerar da niyyar tarbanta, cikin sa'a ta zille ta fita da gudu tana fad'in "Jarababbe kawai ka shafa min lafiya mana in kana da zuciya."

Tsaye yayi ya dafe k'ugu da hannu d'aya yana binta da murmushi, wani dad'i yaji na ziyartarshi saboda yayi abinda ya jima baiyi ba, juyowa yayi kan Amna dake binsu da dariya kawai tana kallo, ita kanta tayi kewar wani abu data jima ba tayi ba, kallon dramarsu ba, dawowa yayi ya zauna yana sauke numfashi alamar gajiya.

*01:39* ta farka saboda jin kukan Shureim, tasowa tayi daga kan gadon sanye da gajerar rigar bacci, a hankali ta bud'a d'akin ta lek'o tana hangen d'akinsu Ummy, akan abun matakala ta tangale hannu d'aya ta buga tagumi, sannu sannu wani tausayin yaron taji yana shigarta, *uwa* bata tare dashi, *uba* ma haka baisan dashi ba, ta jima tsaye tana tunani da taji yayi shiru kuma ta sake jin kukanshi, kafin daga bisani ta koma d'aki ta kwanta tana jin sautin har yau.


Tunda ta dawo hayyacinta abun ya tsaya mata a rai, Huda 'yar shi ce dama, lallai ita kam kam ta gama auren Jibril kenan har abada, daga gadon asibitin nan gidansu zata wuce wajen iyayenta, kuma tayi niyya ko kasheta Hajia zatayi ba zata zauna dashi ba, bare ma tasan yanda Hajia bata k'aunarsu ba zata matsa mata ba, tana wannan tunanin ya shigo d'akin da sallama tare da wasu abokanshi su biyu, su Soueiba da Zeinabu suka amsa suka gaisa sosai, zaune yayi bakin gadon yana kallonta ita ma zaune take k'afafu mik'e sai rigarta data d'an d'age kad'an, cikin kulawa yace "Ya jikin naki?"

Kallon da take masa yasa ya fara tsarguwa da shi, saida tayi niyya sannan tace "Jiki ba sauk'i."

Kowa na d'akin kallonta sukayi inda Zeinabu tace "Jamila ba'a cewa haka, da sauk'i ake cewa duk tsananin da ake ji, ko kuma kice angode Allah."

Kallonta tayi a harzuk'e ta nuna shi da yatsa ta d'ago daga zaman da tayi tace "Bayan duk abinda ya min ne zai wani tambayeni ya jikina? Jibril akan me zaka k'i fad'a min gaskiya? Kana ji kana gani 'yar iskar nan ta dinga min buru-uba a cikin gida tana nuna min ta ma fini saninka, ashe gaskiya ta fad'a nice mahaukaciya da..."

Soueiba ce tace "Jamila dan Allah kiyi shiru ki k'yaleshi, d'inki aka miki fa karki tada shi da d'aga muryar nan da kike, ko tari ba so ake kiyi ba bare wannan fad'an haka."

Kallonta tayi cikin zubo da hawaye tace "Amma duk abinda ya faru ai shi ya ja, ni yau bak'in ciki na yana ta hidima da yarinyar nan amma saiya nuna min kawai yana yi ne dan ya ma yah Junaid kara, sannan gabanshi babu irin iskancin..."

Jibril ne yace "Naji na d'auka Jamila kiyi min duk abinda zakiyi, amma dan Allah yanzu kiyi shiru ko dan halin da kike ciki."

Tank'washe k'afafunta tayi ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta ta fashe da kuka, da sauri Soueiba da Zeinabu suka tashi suna bata hak'uri Zeinabu na k'ok'arin d'agata tana fad'in "Ki gyara zamanki mana karki ji wa kanki ciwo a banza."

Tasowa yayi ya tsaya gabanta ya sunkuya ya ja k'afafunta ya mik'ar mata dasu, hannayenta ya b'amb'are ya tallabo fuskarta yana kallon idonta yace "Dan girman Allah Jamila karki cutar da kanki akan banza irina, ki kwantar da hankalinki ki nutsu, ki kula da kanki da yaronki kinji, ba dan ni ba kiyi dan iyayenmu."

Fizge fuskarta tayi ta kawar da kai gefe, ganin ta daina kukan yasa shi zagayawa ya kalli abokanshi dake rik'e da bebyn, fita sukayi inda Zeinabu da Soueiba sukayi ta bata baki kan karta yarda damuwar ta kusa illata ta.

*Safiya* na yi ta gama shiryawa dan zuwa ganin Jamila, dama tare suka shirya tafiya dan haka suka fito duk a tare, Hamna na tare da Ummy wacce yau zata fara zuwa aiki, tayi fes da ita kamar tayi bik'i fa haka ma Shureim yasha shiri tsaf da shi, saida Ummy ta bud'a mota ta zauna cikin mota suka k'araso wurin, da girmamawa dukansu suka ce "Ina kwana Ummy."

Kallon Amna tayi tace "Lafiya lau, antashi lafiya?"

"Lafiya lau." Amna ta amsa, matsowa Ammar yayi kusan Hamna dake rik'e da Shureim ya tara hannayenshi zai karb'eshi, kallonshi tayi da fararen idonta haka kawai ta tsinci kanta cikin jin dad'i yanayi, mahaifin d'anta zai karb'eshi a hannunta, murmushi tayi da ita kanta bata san ya zo mata ba, zata bashi shi cikin had'e fuska Ummy tace "Kawoshi na kusa makara."

Take murmushin fuskarta ya b'ace ta sake kallonshi, wallahi bata san wane irin yanayi ne take ji ba a game dashi, amma dai har k'asan zuciyarta tausayi taji ya bata da Ummy ta k'i yarda ya amshe shi, mik'a mata shi tayi suna kallo ta rufe motar ta tayar ta bar gidan. Amna ya kalla ya kama hannunta yace "Muje."

Suna gaba Hamna na bayansu har suka shiga gaba ita baya, saida suka daidaita ya juyo ya kalleta yace "Dan ubanki ni kike jira na fara gaishe ki kome? Wai ke me yasa baki da wayo ne?"

Saida ta rumgume hannaye ba tare data kalleshi ba tace "Bana da wayon ne, kuma idan kai ka fara gaishe ni miye a ciki indai har kasan darajar mutum."

Da k'arfi ya juyo cikin nasara ya finciko wuyanta had'e da hijabinta ya matse sosai yace "Ni kike fad'awa duk abinda ya zo bakinki, sa'anki ne ni? Tambayarki nake?"

Yanda ya k'arashe da d'aga murya yasa ta rintse ido tace "Kayi hak'uri to, ina kwana."

Turata yayi da k'arfi kanta ya kaiwa kujerar karo, hararanshi tayi shi kuma ya tayar da mota yana baya baya yana fad'in "Shashanci, ita ta raba kanta dani, k'anan nawa ma rabani zatayi dashi, zanyi k'ok'ari na dakatar dashi daga nan, ba zan bari ya ci gaba da faruwa ba, ba zan bari soyayyarshi ta ci gaba da wanzuwa a cikin zuciyata ba, Allah kaine shaida ina ganinshi naji nafi son shi fiye da sauran 'yan uwana, miye laifina a ci? Wane irin virus ne a jikina da har zata nemi nesanta ni dashi? Matsala."

Daga Hamna har Amna sun fahimci abinda ke zuciyarshi ne ya fito, Amna kuma dake kallonshi tuni ta ga idonshi sun fara rikid'a alamar kad'an ya rage ya zubo da hawaye, Hamna ma tasan dalilin Ummy kenan tana so ta nesanta shi da d'anshi ne, sai dai kash gashi daga abinda ya fad'a yanzu ta gane soyayyar yaron ta riga data shiga zuciyarshi, haka suka d'auki hanya tana danna wayarta har suka isa. Tare suka shiga wajen Jamila suka dubata, taji dad'in ganinta ita ma dan haka ta saki jiki suka fara hira, ganinsu ne yasa Zeituna da Soueiba suka ce su zauna anan suje gida su dawo, ita Soueiba tana son yin wanka a tsanake saita dawo, Amna ma shiga tayi wajen awo abinka ga masu abun tuni aka gama mata ta dawo, jiransu sukayi dan dama basu zo da niyyar tafiya da wuri ba.

*Samun* labarin rashin kunyar da tayi a gidan yasa malam Rabi'u tahowa da ita har gidan, yace dole ta basu hak'uri kuma ba zai ba mijinta hak'uri danya maidata ba, duk da babu yara kuma ita kanta Zeinabu likita take kwana wajen Jamila, amma anyi katarin ta zo saboda zuwan colonel da zai kwana d'aya ya wuce *Mali*, gaban Hajia ya zaunar da ita tace "Dan Allah kuyi hak'uri da rashin kunyar dana muku."

Jin wani murmushi da Hajia tayi yasa Maryama d'agowa cikin jin haushi, murmushi ta mata tace "Haba."

Cike da iyayi Hajia tace "Ke ni fa abinda kikayi ko a jikina wallahi, kin tona mana asirin da bamu sani bane, dan haka ni banga abun damuwa ba, ban sani ba dai ko ga ita wacce abun ya shafa."

Ta fad'a tana kallon Husseina, murmushi Maryama tayi ta kalli Hajia tace "Hajia ke babba ce a gidan nan, babu kyau fariya ga d'an adam bare ke musulma, bai kamata ki dinga tsarkake kanki da ahalinki ba, yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, ko matan baki isa kiyi shaida akansu ba bare mazan, to wai ma akan me kike cika baki? Tare dasu kike fita? Ko kuma kina bibiyar duk abinda sukeyi ne a wajen? ko kuma a cikin gidan kina saka ido akan lamuransu? Ko d'aya fa ba kyayi Hajia, kuma a hakane kike ganin ya zama wajibi akansu su kare kawunansu? To ubangijin daya hallicemu ma ai muna sab'a masa bare kuma ke 'yar adam."

Mik'ewa Maryama tayi sai malam Rabi'u cikin barbarci da yace "Mari rashin kunyar ce har a gabana? Lallai kin rik'a."

Nuna Hajia tayi tace "Malam ba rashin kunya bane, ita tana ganin kamar iyalinta sunfi k'arfin aikata laifi laifin ma kuma na zina, alhalin bata san tana tare dasu ba kuma suna kewaye da ita."

A hankali Hajia ta sauke k'afa d'aya kan d'aya tana kallonta tace "Ban gane ba? Kinsan me kike fad'a kuwa? K'arya kike wallahi."

Murmushi tayi tace "Babu maganar k'arya sai gaskiya, ya kamata ki farka daga baccin da kike Hajia ki tabbatar kin gano asalin kowane yaro daya fito daga tsatsonki, dan zai iya yiwuwa akwai yara dayawa wanda aka samu kafin aure kamar irinsu *Junaid*."

Zunbur ta mik'e tana kallonta ido a tsaitsaye, da sauri Zeinabu ta dafe bakinta da hannun dama ta daskare a wurin, Husseina Soueiba malam Rabi'u duka sororo sukayi, Junaid kam bai d'auki abin babba ba ganinshi kawai sharri ne, matsowa yayi kusanta yace "Kisan me zaki fad'a Maryama, dan na rabu dake bashi zaisa ki min wannan sharrin ba, ba k'aramin abu bane

Please Login or Register in order to submit comment