Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

na safe dubbanin mutane ne suka shaida d'aurin auren amare uku da angayensu a k'ofar gidan *Alhaji Suleymane Gaga*, sai auren Maryama da aka d'aura shi a gidan malam Rabi'u dake nan cikin garin, su Husseina duka sun halarci d'aurin auren, bayan an d'aura anata gaisawa har Alhaji ya nemi gabatarwa da malam Rabi'u k'annan shi Hassana da Husseina dan su gaisa, Husseina na daf da shiga mota Labaran zai jasu Alhaji ya dakatar dasu ta hanyar fad'in "Yan biyu ku gaisa da kakan yarinyar mana."

Juyowa Husseina tayi da murmushi a fuskarta, ido cikin ido, ido hud'u sukayi da malam Rabi'u, kakkafewa idonta sukayi a kanshi ta kasa katab'us, da k'yar ta d'aga yatsarta ta nuna shi murya na rawa tace "Kkk...kai, Rabi'u."

Duk da shekaru sunja kuma ta tsufa, amma babu abinda ya hanashi ganeta, sunkuyar da kai yayi da alamar rashin gaskiya tare da cire hular kanshi ya fara firfita da hannun babbar rigarshi, Alhaji ne ya kalleta yace "Husseina, kin sanshi ne dama?"

Labaran dake cikin mota zaune fitowa yayi ya zo ya tsaya gabansu ya k'ura musu ido, ita ma duk'ar da kai tayi ta fashe da kuka, Labaran ne ya sake matsawa cikin tashin hankali yace "Hajia lafiya kike kuka? Meya faru?"

Fad'awa tayi jikin Labaran hakan ya sashi shafata yana daddab'ata alamar rarrashi, Hassana ce ta sake cewa "Husseina wai meke faruwa?"

Da k'yar malam Rabi'u ya d'ago cikin i'ina yace "Ee.h to..ina ga dai.. ko bata da lafiya ne?"

D'agowa tayi ta kalleshi tace "Banda lafiya? Me zai hana ka fad'a musu abinda ya faru."

Alhaji ne yace "Wai me yake faruwa ne? Ku fad'a mana."

Cikin tsananta kuka ta kalli Alhaji tace Ba komai, kawai mu tafi."

Labaran daya kafe malam da ido shi dama har yanzu al'amarin mutumin na gindayar dashi yace "Hajia daga ganin mutumin nan yanayinki ya canza, dan Allah ki fad'a mana ko da wani abu mana ko hankalinmu zai kwanta."

Juyawa malam Rabi'u yayi da nufin barin wurin sai Labaran yace "Hajia ko dai wannan shine..." Shiru yayi bai k'arasa ba dan da k'arfi malam Rabi'u ya juyo yana kallonshi, ita ma Husseina kallonshi tayi, sai Hassana ce tace "Shine me?"

Cike da ladabi yace "Hajia kwanan baya sanadiyar ganinshi yasa na miki tambaya akan mahaifina, jikina yana bani kamar akwai wani abu tsakanina da shi, kuma alak'ar zata iya zama mai k'arfin gaske, amma gudun b'acin ranki yasa bana iya aiwatar da komai."

Duk shiru sukayi sai Husseina data share hawaye ta kalli Labaran tace "Tabbas shine, ba zan tab'a manta kamanninshi ba."

Hassana da Alhaji ne suka ce "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Alhaji ne ya d'ora da "Ya ilahi, malam Rabi'u?"

Husseina shigewa tayi mota ba tare data kalli kowa ba, Hassana ma shiga tayi tana waigen malam, Labaran dake kallonshi rasa abinyi yayi, sai kawai ya juya shima ya shiga mota ya tayar, Alhaji ne yayi k'arfin halin matsawa kusa dashi yana kallon idonshi yace "...


*Alhamdulillah*
09/09/2020 ร  17:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_34_

"Gaskiya banyi tsammanin haka ba, sam abun baiyi min dad'i ba, cikar kamalarka tasa ban tab'a maka wannan zaton ba, tashin hankalin daka jefamu cikinshi Allah kad'ai yasan iyakarsa, amma yanzu a matsayinmu na manya ba zamu ce da kai bamu yafe maka ba, domin kuwa bayyana da kuma tonuwar lamarin nan a yanzu bayan tarin shekarun da aka kwashe ya isa yasa mu fahimci akwai wani al'amari mai girma, kuma gashi a bayyane auren *Maryama* da Junaid yayi, sai mu musu fatan alkairi."

Yana gama fad'a ya wuce shima inda colonel da kanshi ya bud'e mishi mota ya shiga suka wuce. Husseina na zuwa gida d'akinta ta wuce ta dinga kuka, sam bata so had'uwar ta da shi ba, amma gashi yau ta gani, haka farin cikinta ya koma bak'in ciki, haka shima Labaran, kana ganinshi zaka gane yana cikin damuwa, sai dai shi har zuciya yana so ya gana da mahaifinshi, *uba*, wanda ya rasa tsawon shekaru, bai tab'a d'ora idonshi akan ko da dangin ubanshi ba bare uban. Kamar yanda baya b'oyewa Soueiba komai yanzun ma bai b'oye mata ba, ita kanta abun ya d'an dameta sai dai bai hanata karb'an duk wani daya zo gidan dominta ba.

Tako kamar na gwiwa, d'aya bayan d'aya sai kace wata sarauniya, yayin da mai aikinta ke biye da ita a baya rik'e da jakarta, babbar riga ce jikinta mai kama da babbar rigar maza, d'aurin d'an kwalin ya hau kanta sosai, sai yalolon gyalen data d'ora a kafad'a d'aya da manyan waya har biyu a hannuwanta, zobuna da sark'a da yan kunnai duk gwal ne, dogayen takalma a k'afarta da suka dace da kalar kayan, da gani babu tambaya kasan mai yana aiki a wurin, jan nata har ya k'azamce ta yanda take d'aukar ido, ga kuma hodar data d'auka ta k'ara fito da ita, cike da k'asaita da jin kai da isa ta k'arasa tsakiyar filin da ake kad'in guitar. Yau a k'ofar gida ne ake kad'a guitar d'in sai tarin yan zaman biki da suka zagaye mawak'an suna kallon rawar da wasu maza keyi irin ta buzaye, bayan k'arar guitar haka wurin ya hargitse da shewa irin ta buzaye (ma Sajida nasan zaki fahimci irin shewar, ๐Ÿ˜‚) wasu na karkad'a harshe abun birgewa ana rawa wacce tafi kama da tsalle tsalle, dan wani tsallen sai anyi k'asa sosai ake yin sama ana harba k'afafu ๐Ÿ˜‚(abun birgewa). Zuwan *Aissata* yayi daidai da zuwansu Ammar shi da abokanshi wanda suka zo d'aukar abincin da yasa Zeituna ta girka mishi, zai shiga gidan Sayyada yar Fatime da kuma wasu daga cikin yan mata suka taho wurinshi, nan suka tilasta mishi sai sun d'auki hoto dashi, sun d'auki hoton zai shiga sai kuma ya kalli wurin taron, nan ya hangi Aissata ta bud'e bakin jaka tana watsa kud'i kamar hauka, murmushin zaki gane kurenki yayi mata ya nufeta, nan ya kutsa filin taron ya sameta yana murmushi yace "Uwarmu sannu da k'ok'ari."

Kallonshi tayi a sama tace "Cava."

Kallon mai bisa ruwa ya mata yace "Uwa irin wannan lik'i haka, kice dai aljihun uban namu yayi kuka yau?"

A wani yamutse ta kalleshi tace "Qu'est ce que tu remarque (Me ka lura dashi)?"

Murmushi ya mata yace "Eh to, da yake ai a lokacin aurenku da tonton munje Niamey, kuma har gidanku muje kafin ma d'aurin auren, in baki manta ba ai har d'akin Ummynki na shiga na ci abinci."

Kallonshi tayi da alamar rashin fahimtar zancenshi ko d'aya, hakan yasa tace "De quoi tu parles? (Akan me kake magana), je ne comprends rien (Ban gane komai ba)."

๐Ÿ˜‚ _Hyahyahya, bata gane komai ba, yana nufin ya ga gidanku ke d'in ba yar kowa bace bare ace zaki iya fantamawa da kud'in gidanku._

Murmushi ya mata ya k'urawa fuskarta ido yace "Amma uwarmu powder nan fa ta karb'i fuskarki, wallahi yanda kika san wata kyakyawar sarauniya."

Dariya ya mata ya wuce cikin gidan, ganin babu isassar hanyar da zai wuce yasa shi tambayar *Farisa* k'anwar Jibril inda uwa Zeituna take, ita ta fad'a mishi suna gidan da za akai amare suna girki, da mamaki ya kalleta yace "Gidan da za akai amare? Wane gidan to? Bayan kowa da nashi gidan, Ina ne gidan?"

Nuna mishi gidan nan tayi tace "Yah Ammar gaya nan, yanzu ma ana kai kayansu ne ana gyaran d'aki."

Jim yayi alamar tunani, murmushi ya saki yace "Duk yanda akayi wannan aikin Alhaji ne, dan shine kad'ai yake matuk'ar son ya ga iyalinshi a wuri d'aya, baya son ganin sunyi nesa da juna, shiyasa duk da kowa na da hali amma suke manne gida d'aya." Kallon Farisa yayi yace "Je ki kira min ita."

Galala ta kalleshi jin yace wai ta kira mishi ita, Zeituna fa yake nufi, wucewa tayi shi kuma ya fito dan ya jirata a waje, sai dai yana tunanin yanda zasuyi rayuwar aurensu a kusa da iyayensu, a gaskiya ya so ya bar gidan nan ko ya samu salama, amma kuma ba zai iya yi wa Alhaji musu ba, yana cikin tunanin nan Zeituna ta fito cikin shirinta sai dai duk ta had'a gumi saboda aikin da suke, girki ya tambayeta tace an ida dan haka yasa aka fito da manyan kuloli aka zuba musu, su Amar na zaune a k'ofar gida suma suna nasu casun, sai dai ko magana bata had'a shi da ko d'aya daga cikinsu ba, sai Junaid wanda tuni wasu daga cikin dangin Alhaji da kuma dangin Soueiba suka tafi d'aukar amaryarshi Goรปrรฉ tare da abokanshi.

Hajia ce tsaye a d'akin Alhaji ta tisashi gaba tana fad'in "Akan mene zaka musu gini ba tare dana sani ba? Sai yanzu kawai ana maganar gyaran d'akin sai ka wani ce wai ga gidansu nan, sun fad'a maka suna sha'awar zama anan d'in ne?"

Shiru Alhaji ya mata kamar bai jin me take cewa sai jan carbin hannunsa da yake, d'orawa tayi da "Babu wanda baya da lafiyayyen gida a cikinsu, an musu wannan tanadin ba tun yau ba saboda irin wannan ranar, kuma kai ma kasan da haka, amma ka had'e musu gida d'aya su hud'u, kuma wannan kurkukun gidan me zai musu? Sai kace wasu jarirai ne su da ba zasu iya kula da kansu ba saida taimakonmu, to ni gaskiya wannan gidan bai min ba, inhar kana son su zauna kusa da kai ne to sai dai in zaka raba musu gidan ko da hakan na nufin ka siye duk rabin unguwar nan ne."

A hankali cike da dattako ya d'ago kai ya kalleta, hak'ik'a shi d'an halak ne, kuma har yanzu yana tuna hallacin mahaifinta gareshi, wanda kusan shine silar arzik'in shi, ya mishi hallaci sosai a rayuwa, dan haka har yanzu yake iya shanye duk wani wulak'anci da k'ask'anci daga wajenta. Murmushi ya sakar mata tare da mayar da kanshi ya sunkuyar, hakan kuma k'ara b'ata mata rai yayi, cikin hassala tace "Wato ga mahaukaciya ko? Shikenan ba komai, yanzu fad'a min ita kuma waccen k'ofar da naga ana yi ta kusa da b'angaren samari ta mecece?"

Ba tare daya kalleta ba yace "K'ofar da zasu dinga shigowa kai tsaye ba sai sun shigo ta waje ba."

"Amma w..." Kallon daya mata yasa taji ta kasa k'arasawa, ita kanta tasan a cikin zamantakewarsu akwai ragowa da d'aga k'afa, ta kuma san yana k'yaleta ne kawai saboda mahaifinta, amma ba dan haka ba ko a zahiri tasan yafi k'arfin zama lusari a gidanshi, turo mishi d'an k'aramin bakinta tayi mai kama dana Ammar tare da jujjuyashi ta fice da sauri, murmusawa yayi tare da girgiza kai yace "Allah ya shiryaki Zeeya'atu, ina fatan ganin ranar nan."


Duk da a k'afa aka shigar da amare d'akunansu, amma hakan bai hana abokanan angayen yin kururuwa ba a k'ofar gidan kan ababen hawansu, saida suka tayar da k'ura sukayi juyi da motoci, Maryama ma sun iso lafiya ta shiga d'akin ta. B'angare hud'u ne a cikin gidan wanda daga waje ake mishi kallon k'arami, kowane b'angare matsakaicin doron zabuwa ๐Ÿ˜‚ ce aka mishi, a kowane b'angare kuma yana d'auke da falo da d'aki uku a ciki sai k'ananun madafa (cuisine), a kowane d'aki kuma akwai ban d'aki a ciki bayan wasu ban d'akin dake akwai guda biyu a waje, idan ka cire Maryama da ita ma babu laifi an mata kayan d'aki, duka amaren saida aka cika dak'unan da kaya, Gambo da Labaran ne sukayi wannan k'ok'ari bayan doguwar musu da akayi, Labaran yace shi ya d'auka zaiyi musu kayan d'aki, colonel yace shi zaiyi, lieutenant ma haka, a k'arshe dai Gambo da Labaran suka barma, babu ce kawai babu a d'akin su, hatta kayan kallo basu bari ba saida suka zuba musu, kuma kayan duk sanfiri d'aya ne kala da abinda ba'a rasa bane ya banbanta.

*Party*

Kayan da Ammar ya d'inka mata ne ta saka, leshe ne da ak'alla kud'in zasu ishi wani talakan rayuwa na tsawon watanni, kalar ruwan madara ne da bleue wanda ya k'ona sosai, haka shi shi ma tanffatsetsen yadin dake jikinshi kalarsa take, mota dai ba wata tsiya ba kam kamar suyi magana, dan wajen ajiye motoci a babban hall d'in ma kasa d'auka yayi, duk girman gurin saida aka matsu akayita had'a gumi, har ya zama ba'a jin tashin kid'an dake wurin sai jininin mutane da kuma hayaniyarsu. Da gani kasan babban biki ne na manyan mutane kuma masu tarin dangi, kowa daka gani shafar gumi yake saboda matsatsi yayi yawa, abincin kam dama ko da colonel ya samu labarin jama'ar dake wurin ya sake odar abincin a restaurent har guda biyu, da hakane aka samu abinci ya wadata a wurin, duk wanda bai samu ba to baya kusa sanda aka raba. Hasken waya kam ta ko ina ganinshi kake ana d'aukar hoto, ana cikin wannan rak'ashewa aka ce Hamna ta zo a d'auki hoto kuma a dole su sa Ammar tsakiya.

Hamna na tsayawa ta wurga masa harara tana gunguni k'asa k'asa, Ammar dake amsa waya cikin akasi idonshi suka sauka kanta tana harararsa, kashe wayar yayi ya murtuke fuska yace "Ke uban wa kike harara? Allah kankana ki kiyayeni."

Murgud'a masa baki tayi tace "Ank'i a kiyayeka, da wani abu da zakayi ne?"

Kallonta yayi da mamaki yace "Kutumar uba, ke ni kike fad'awa haka? Me..." Bai k'arasa ba ya juya ya kalli Amna dake ta doka murmushi, murmushin ya mata shima yace "Amaryar, ci gaba da murmushi irin haka kinji, bari na gama da kankana."

Bai jira amsarta ba ya sake juyowa kan Hamna ya zaro mata ido ya sassauta murya yace "A waccen ranar me kika gani? Ga dukkan alama kankana ban baki tsoro ba, dan dana tsorata ki da ko ganina kikayi sai gabanki ya fad'i, amma akwai lokaci."

K'wafa yayi ya juya gabanshi ita kuma tace "Tabbas."

Da sauri ya juyo ya kalleta, d'orawa tayi ba tare data kalleshi ba tace "Tabbas akwai lokacin da zan huce haushina a kan ka, kuma tsoro da kake magana, kai a wa zanji tsoronka? Fasik'in? To ai ko abinda ya faru ma ni baisa na kalleka a matsayin namiji ba, watak'ila baka gama k'wari bane ko kuma dai kana da k'arancin lafiya, amma dai ka sani ni banji komai."

Ruf ya rintse idonshi, yawu ya had'e masu d'acin gaske wanda suka sanya mak'walaton dake wuyanshi yin sama da k'asa, bud'a idonshi yayi wanda suka fara d'aukar launin ja, ya kasa d'auke idonshi a kanta saboda so yake ya tattartsa mata mari, amma ya rasa yanda akayi ya kasa d'aga hannun, ya tabbatar da wata ce ko Amna tuni data dafe kunci, to amma me yasa ita ya kasa. A hankali ya sake lumshe ido ya bud'e a kanta, tattaro kuzarinshi yayi yace "Da bana da lafiya da bakiyi kururuwa ba, da ban cika namiji ba da tafiyarki bata canza ba, yanzu kuma zan tabbatar da abinda kika fad'a ne idan har kika ga al'adarki a wannan watan."

Wata mummunan fad'uwa gaban Hamna yayi, kallonshi tayi tsoro ya bayyana a tare da ita, fahimtar haka da yayi yasa ya murmusa ya kalli gabanshi yace "Ba alfahari nake ba, amma inada tabbacin ke bakiyi k'osawar da har madara zata kasa zama d'an mutum a cikinki da zubawar farko ba, musamman ni da nasan na zubata a daidai a lokacin da komai ke bud'e yana maraba da kowane bak'o ya shigo."

Hamna kam fashewa tayi da kuka ta taka zata bar wurin tana fad'in "Allah ya isa, Allah saiya saka min, mugu azzalumi."

Dariya yayi wacce ta fito da kyawunshi murya k'asa k'asa yace "Ba farau ke da zafi ba dama, ramau, kuma nima Allah ya isa da kika rabani da samartaka ta, muguwar kankana kawai."

Amna dai da babu abinda take ji kallonshi kawai tayi, suna had'a ido ya sakar mata murmushi yace "Ina k'aunar ki amaryata."

Kunya ce ta rufeta ta sunkuyar da kai, shi kuma kallonta yayi ya tambayi kanshi "Da gaske *kana k'aunarta*?"

D'an murgud'a baki yayi yace "Ko bana sonta ai ina k'aunar ta, kuma yanzu matata ce sannan zata zama uwar 'ya'yana insha Allah."

Tsam yayi sai alamar tashin hankali daya ziyarceshi lokaci d'aya, abinda ya fad'a mata ne ya dawo kanshi, *yanzu kuma zan tabbatar da abinda kika fad'a ne idan har kika ga al'adarki a wannan watan*! Tashin hankali, to idan fa haka ta faru? Wata zuciyar ce tace mishi "Haka ma ba zai faru ba, ai ka fad'a mata ne kawai dan ita ma taji zafi kamar yanda ta cizgaka."

D'aga kafad'a yayi alamar ko oho sannan aka ci gaba da sha'ani, sai dai har aka tashi daga taron bai sake ganin Hamna ba, wanda hakan ba k'aramin dad'i ya masa ba, dan dama ganinta cikin shigar nan data fito da komai nata yana tayar masa da hankali, sai yaga duk idon kowa a kanta yake. Nan aka koma gida aka raka kowace amarya ta sake shiga d'akinta. Duk abinda aka saka ma rana dai k'ararre ne dama, sai gashi anyi an gama kowa ya kama gabanshi an bar amare da angaye da halinsu.

*12:00* da sallama Jibril ya shigo d'akin da ledoji a hannunshi, Jamila dake zaune tsakiyar gadon kasa amsawa tayi dan gabanta ne taji ya tsananta fad'uwa, har saida ya zauna kusanta bata motsa ba, ganin bata da niyyar magana yasa ya aje ledojin hannunshi ya yaye mayafin nata yana kallon fuskarta, ajiyar zuciya ya sauke ya d'anyi k'asa da kanshi sannan yace "Jamila."

Saida ta had'e yawu yafi sau biyar kafin ta amsa k'asan mak'oshi da "Na'am."

Murmushi yayi jin firgici a cikin muryarta yace "Muje muyi alwala ko."

Jinjina kai kawai tayi alamar to sannan ta sauko a hankali ta fad'a ban d'aki, yana zaune yana jiranta har ta fito, saida ya k'urawa fuskarta ido ganin ta wanke kwalliyar dake fuskar, mik'ewa yayi shima ya shiga, ba jimawa ya fito ya samu ta shinfid'a sallaya, gaba ya tsaya ita kuma daga gefenshi a baya suka kabbara sallah.

A wajensu Junaid ma hakance ta kasance, bayan sun idar da sallah zai janyo ledojin shi yaga ta mik'e, da mamaki yace "Zauna mana, zo ki cika cikinki Hajia ta."

Kallonshi tayi tace "Ina zuwa, zan canza kaya ne."

A gabanshi, yana kallo ta zage rigarta ya rage sai bras a jikinta a k'arshe ma bras d'in cireta tayi ta saka ta bacci sannan ta janye siket d'in ta, yana kallo ta cire pant d'in ta ta saka na rigar baccin, juyowa tayi ta zo ta zauna kusa da shi cikin jijjiga jiki irin na yan duniya, nan suka fara cin kazar yana bata a baki ita ma tana bashi, tun basu ida ba wasan ya sauya ya kuma girmama suka haura kan gadon mulki.

Amar ma har har sukayi sallah suka ci abinci idonsu bai had'u ba, har zuciyarshi baya son Umaimah so na soyayya, amma babu yanda zaiyi duk da yana da halin da zai iya ce ma Hajia bai sonta kuma ta amince, amma yayi hakanne saboda yan uwanshi. Yanzun haka kayan bacci ne ya sanya a d'akin shi ya dawo d'akin, tsaye ya sameta ita ma tayi shirin baccinta, k'ala bai ce mata ba ya haye gado ya kwanta, tana ganin haka ta kashe wutar d'akin ta d'auko bargo a ledarshi ta cire ta shinfid'a k'asa, ta d'auko matashin kai zata koma ya tashi zaune yana kallonta, cike da halin ko in kula yace "Kinga dawo nan ki kwanta, meye na kwanciya a k'asan kuma bayan ga gado?"

Sam bata ji dad'in yanda ya mata magana ba, haka ta taso ta d'an zauna amma bata kwanta ba, shi ma daya kwanta baccin kasa d'aukar shi yayi yana kallonta, ganin haka ba zata gyara su ba yasa shi zura mata hannunshi alamar ta taho yace "Zo k'anwata."

Kallonshi tayi ta kalli hannun, saida ta sunkuyar da kai sannan ta mik'a mishi hannun, jawota yayi ta matso kusa dashi ya rumgumota a jikinshi, d'aya hannun yasa yana shafa kumatunta a hankali, a haka haka kuma sai bacci yayi gaba da ita, a hankali ya gyara mata kwanciyarta ya ja mata lallausan bargon dake kan gadon sannan shima ya kwanta.

A b'angaren *babban yaya* kuma nashi salon daban yake dana kowa, domin kuwa yana shigo ya hangeta tsakiyar gado ta nad'e k'afafu, tsaye yayi ya aje ledojinshi k'asa yace "...

๐Ÿ˜›

*Alhamdulillah*

_Idan naga ruwan comment zakuji wani insha Allah._
09/09/2020 ร  17:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_35_


"Amarya haka ake tarban miji?"

Wani fad'uwar gaba taji, amma sai tayi shiru bata d'ago ba, takowa yayi saida ya tsaya kanta ya janye mayafin fuskarta, tallabo hab'arta yayi ya saka idonta cikin nashi, murmushi ya mata yace "Ai na d'auka kuka ne kike? Dana tambayeki kuka me kike?"

Sunkuyar da kanta tayi tana k'ok'arin mayar da mayafin sai kuma yace "Kinga ta so ki gani."

Hannayenta ya kamo ta sauko daga kan gadon suna fuskantar juna, tsaye k'ik'am ya mata yace "Taimaka min na cire wannan kayan, kinsan fa ban saba saka irin wannan kayan ba, kawai dai dan yana bikina ne ina so na fito a angona."

Kasa kallonshi tayi sai kallon k'asa da take tana shafa wuyanta da tafin hannunta, ita fa wannan tijarar tashi ce tasa take shakkar aurenshi, ya zai ce ta taimaka mishi ya cire kaya? Ba ma zai barta ta mori amarcin ba wannan, kafeta yayi da ido yace "Ke dake fa nake."

Da sauri ta kalleshi cikin tsoro ta zura hannu saman kanshi ta d'auke mishi hular, ajeta tayi kan gado ta kalleshi kamar zata fashe da kuka tana aika mishi da kallon dan Allah ka k'yale ni haka, hannu ya d'aga kamar zai mareta yana fad'in "Dallah ni kar ki min kuka, mage kawai."

Ja baya tayi har ta fad'a kan gadon zaune tana binshi da kallo, cire babbar rigar yayi ya cilla mata ya rufe mata fuska, janye rigar tayi ta hangeshi ya shiga ban d'aki, k'amshin rigar daya daketa ne yasa ta k'ara mannata a hanci tana shak'a tana lumshe ido, tunaninta yanda zata iya wannan bahagon yayan nata take, wani k'asaitaccen murmushi ta saki saboda ganin sam bai b'ata nuna mata k'iyayya ba, tana cikin sakin murmushin nan ya fito ba tare data sani ba dan bai rufe k'ofar duka ba lokacin daya shiga, yana sauke ido a kanta yace "Jikanyar Hajia har na fara kasheki ne? To ai baki ga komai ba, sai ma anjima ko?"

Kamar wata marar gaskiya haka ta lallab'a ta aje mishi rigar bata yarda sun had'a ido ba, matsowa yayi ya kama hannunta ta mik'e tsaye ya turata gaba yace "Je kiyi alwala ki zo muyi sallah, tunda ke ma kina da tsarki yau kwana zamuyi muna ibada."

Juyowa tayi ta kalleshi baki bud'e, ta fara tsoratada al'amarin nashi kam, wani dolon murmushi ya mata yace "Yi sauri mana, ko so kike saina fara nuna miki komai a fili."

K'ara k'ank'ance k'aramin bakinta tayi ta juya kamar wacce k'wai ya fashe ma cikin ciki, kamar a mafarki sai ji tayi an mareta a mazaunai, juyowa tayi da k'arfi ta kalleshi, kashe mata ido yayi yana d'an cije leb'en k'asa, da sauri ta sake juyawa ta shige ban
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment